Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuni ta fito mata da kaya doguwar riga na shadda wacce ta sha aiki sabuwa dal mai kawai ta shafa ta sanya kayan kamar an gwada ta, Zarah ta kalleta tace "wow! Sis kinyi mugun kyau sosai wlh
"Na gode ta faɗa tana sakar mata murmushi basu ɗau lokaci ba suka fito suka samu ƴan gidan a dining gaba ɗaya suka gaidasu da farko Amatullah ƙin zama tayi sai da Hajiya Fatima tayi da gaske sannam ta zauna Abba dai sai murmushi yake, Amatullah kewar mahaifanta ne ya dawo mata sabo tuni idanunta suka tara ruwa a ɓoye take fakar idanunsu tana gogewa
Momy wato Hajiya Balkisu duk abun da take tana kallonta mamaki ne ya cika ta da taga tana kuka a zuciyarta tace "ko kukan uwar me take oho! ko dai ma cikin shege tayi ta gudo shi kuma da kwashe-kwashen sa ya kaso mana ita oho! bayan zun gama ne Abba ya ce su taru a parlor yana da magana da su, ya ƙira Saif ya sanar dashi yana jiransa yanzu, zaune suke a parlon kowa yayi shiru yana saurare   gyaran murya Abba yy bayan ya buɗe taro da addu'a ya ƙara da cewa "wannam Yarinya da kuke gani sunanta Amatullah Allah ne ya bani ita daga sama, nam ya fara basu labarin duk abun da ya faru har labarinta da ta bashi har izuwa yanzu da take gabansa ya ƙara da cewa kamar yadda na sanar da ku na ɗauketa ita ma tamkar su Saif ita ma ta zama ɗiyata ina so kuma ku ɗauke ta kamar yadda kuka ɗauki yaranku ku riƙeta amana saboda marainiyace lada zaku samu ba ɗan kaɗan ba dan Allah ku tayani riƙe wannam babban nauyi dana ɗauka dafatan zan samu hakan?
  Hajiya Fatima ne ta goge ƙwallan idanunta domin Amatullah ta bata tausayi sosai (ni kuwa nace dan ma bata faɗa muku gaskiyar labarinta ba) cikin sanyin murya tace "Allah sarki Amatullah in sha Allah zan riƙeki tamkar ni na haifeki Allah yasa nima zaki ɗauke ni kamar uwa a gareki?
Ƙwalla Amatu ta goge tana faɗin "in sha Allah Ammi na gode sosai
Hajiya Balkisu ta taɓe baki tace "ni dai banyi alƙawari ba  nawa ma ban gama iya riƙesu ba tukunna balle karere marar iyaye, wannam lbrn da ta bayar ma ban yarda da shi ba Allah ka ɗai yasan me ya fito da ita daga gidan su ta zauna ta gilla maka wannam ƙaryar, daga haka ta miƙe yaranta suna mara mata baya ran Abba ya ɓaci sosai cikin tsawa yace "Raudah ku dawo ku zauna ban gama ba, da sauri suka juyo suna ƙunƙuni Momy kuwa tuni tayi shigewarta ɗaki tana mitar Abba ya iya kwashe-kwashe,
   Abba ne ya kalli su Raudah fuskarsa babu alamun wasa yace "wlh daidai da rana ɗaya kuka yiwa Amatullah abun da ba daidai ba sai nayi matuƙar tsaɓa muku tunda kuma naga kan ku na rawa kamar na uwarku, to wlh ku kiyayeni ku ɗauketa tamkar ƴar uwarku, kuna jina dai ko?  
  "Eh suka ce a taƙaice
Fatima ke bana jin ta ɓangarenki dan daga ke har yaranki baku da matsala kuna da ƙoƙari amma don Allah ku ƙara akan wamda na sanku da ita.

"Insha Allahu Abbansu Allah ya bamu ikon riƙe wannam amanar gaba ɗaya suka amsa da amin, ban da Amatu da ta sanya wani irin marayan kuka.
Cike da tashin hankali gaba ɗaya suka nufota suna tambayarta lafiya, wani kukan ta sake ganin yadda suka damu da lamuranta bata kuma da wata alaƙa da su, Saif ne ya iso gabanta ya kamo hannunta cikin sassanyar murya yace "lafiya me ya sameki? me ya saki kuka?
da sauri ta janye hannunta ta goge fuskarta tace "babu komai na gode sosai da nuna karamcin ku a gareni Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alheri ya saka muku da gidan aljannah dan ni bani da abun da zan iya biyanku da shi, murmushi Saif ya sakar mata suka amsa da amin, daga haka  su Zarah suka kama hannunta suka nufi ɗaki su Saif ne suka rage shi da Ammi murmushi Abba yayi ya kalli Saif da ya gyara zaman sa yace...

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Tun da Taufeeq ya fita bai zarce ko ina ba sai birnin tarayya dan gaba ɗaya ji  yayi garin Kaduna ya masa matuƙar zafi, duk da yadda yake son mahaifar tasa amma a wannam karon gaba ɗaya zafin garin yake ji, babu yadda ya iya washegari ya sa a buga masa I.V sannam ya sanarwa me girma Shugaban ƙasa, ya nuna fushinsa sosai akan sai yanzu zai sanar da shi, shi dai haƙuri kawai yake basa dan miskilancin sa baxai bari ya faɗa masa gaskiyar lamari ba...
Sweetie ne ta tisa Nabeeha akan sai tasha wani haɗi da Hajiyar maiduguri ta bata haɗin zuma ne da dibino da kwakwa sai sauran ƴan haɗe-haɗe amma duk ta fice a haiyyacinta wai ba daɗi har da kukanta, Sweetie ne ta haɗe fuska tace "Nabeeha zaki shanye ne ko dai sai na tsaɓa miki in da ɓangaren kwaɗayi ne ai ba yake maza ki shanye ki ajiye min cup ɗina ki ƙara gaba
Babu yadda ta iya dan dole ta kafa kanta ta shanye tas ta ajiye cup ɗin ta fita tana ƙunƙuni ita a dole tayi fushi, ɗakin su ta shiga ta samu su Samha suna bacci hankali kwance, nan ta taƙarƙare ta zabgawa Samha tafi,
Da sauri Samha ta miƙe cike da tsoro tana zauro ido ganin Nabeeha da tayi a kanta ne ta tabbatar itace ta daketa, baki ta zunɓuro gaba tace "me na miki zaki dake ni? dan kawai za a haɗaki aure da Yaa Taufeeƙ sai kina hucewa akan mutane to wlh sai na rama
Ta faɗa tana nufowa kan Nabeeha da take tsaye ranta duk a jagule dan har ga Allah sam bata ƙaunar wannan aure amma kuma babu yadda ta iya dole tayi haƙuri ta dai yi alƙawari yadda ya bi da ita, itama haka za tabi da shi, Samha tana zuwa ta ɗira ma ta dundu ita ma, kawai sai ta fashe da kuka daman hawaye n a kusa suke ta faɗa gado ta saki marayan kuka, Hudah dake bacci da sauri ta miqe tana salati, a tsorace tace me ya faru Nabeeha? Samha ce tayi dariya tace.
    "Wlh Aunty ba komai kawai sakalcin ne ya motsa kuma aure ne dai babu fashi tana faɗar haka ta sa dariya, Huda ma dariyar take tace "yo ai gwara ma ki daina kuka dan kinsan dai wannan auren ba fashi dan ko shurawa kikayi na tabbata sai Papa ya kaiki gidan Yaa Taufeeq domin cika wannan alƙawarin da sukayi da Uncle, tun tana ma ta dariya har dai ta fara bata tausayi dan duk wanda ya auri Yaa Taufeeq ai dole a jajanta mata dan tana cikin ƙuncin rayuwa.
Janyo ta tayi jikinta cikin muryar lallashi tace
"Nabeeha haƙuri za kiyi babu yadda kika iya babu kuma abun da za ki iya akan wannan lamari illa haƙuri da rungumar ƙaddarar da ta hauki, tabbas auren irin Yaa Taufeeq wa mace kamarki ba ƙaramin abu ba ne, duk da Yaa Taufeeq bashi da wata makusa kyakkyawa ne ajin ƙarshe ga kuɗi ga mulki ga ilimin arabi da boko ga nutsuwa da hankali uwa uba kamun kai, matsalar sa ɗaya miskiline ne na gaske, amma in kika bi shawarin da Sweetie ta baki insha Allahu za ki shawo kan abunki kiyi haƙuri kukan bashi da amfani.
   Tashi zaune tayi tuni fuskarta da idanunta sun kunbura cikin kuka tace
   "Aunty Huda taya kike tunanin zan iya zaman aure da Yaa Taufeeq mutumin da baya ƙaunata ko na second ɗaya kuma ace da shi zanyi rayuwa ta har'abada ga wanda yake sona nake son shi amma a haɗani da wani… wani kuka ta kuma fashewa da shi, tuni Samha ma idanunta suka fara zubar da ruwa ita kanta Huda daurewa kawai tayi amma duk da haka idanunta sun kaɗa haƙuri tayi ta bata tana lallashinta da ƙyar ta haƙura.
Shirye-shirye suke ba kama ƙafar yaro, Sweetie da ƙanwarta basu dubai basu london sayayya kawai suke zubawa domin daga ango har Papa sun buɗe musu aljihu ɗiba kawai suke, su Samha ma suna shirin su amma ban da uwar gayya Nabeeha dan sam taƙi zuwa ko ina kuma tace ita babu abun da za tayi, su sukayi ta jelen raba anko da katin abun da za suyi, sai dai fa duk wannan abun da ake babu Taufeeq babu labarin sa yana Abuja sai dai kuma tuni duniya ta ɗauka auren *Minister Abdullahi Nasir Adam Salwa (Taufeeq)* da yawa suna mamaki daman bashi da aure gashi kuma yana minister wasu faɗi suke ina ma su zai aura wasu kuma fatan alheri suke masa kowa dai yana tofa albarkacin bakinsa.
    Saura kwana uku biki su Sweetie suka samu dawowa tuni gida ya jima da cika da ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa da na kusa, mamaki ne ya cika Sweetie ganin duk ƴan uwa sun sha lalle da kitso amma ban da amarya dan sam taƙi bari a ma ta, gyaran kan ma da ƙyar taje sai da Sweetie tayi da gaske sannan aka ma ta, tuni ta fito a amarya sai sai baza sheƙi take ga wani fitinan nan ƙamshi dake fita daga jikinta duk wani motsi da take domin Hajiyan maiduguri gyara tayi ma ta bana wasa ba domin an sake mata kuɗi.
Ranar laraba sukayi Kamu a cikin gidan wanda da ƙyar Nabeeha ta fito dan tace ko za tayi wani abu ma walima kawai zatayi faɗa muku irin kyan da tayi ma walle ɓata lokaci ne washe gari akayi walima inda malamai suka baje basirarsu akan zaman aure, an raba gift bana wasa ba fiye da wanda aka raba wajen kamu anci ansha kuma an tafi da kyauta, kamar daga sama na hangi Zarah abba kyari da su Mom abulkhairi da su Sarauniya hauwa dasu Mrs Nura da su Sasoro gaba ɗaya ƴan Taufeeq fan's grp sun hallara  sai kokawa suke akan kyautar da aka raba musu mom abulkhairi harda cizon Minert sai da naman wajen ya fita kamar wata mayya🤣 kokawa suke iya ƙarfin su sai da jami'an tsaro suka rabasu suka korasu da cewar kar wacce ta yarda gobe tazo musu tunda faɗa suke,Mom Misrah ne tace "wlh sai mun dawo haka kawai ka hana mu cin kaji mugu kawai ta faɗa tana murguɗa baki suka sa gudu suka shige motarsu suka ƙara gaba, a motar ma basu bar faɗan ba, kowa na faɗin gobe bazai bi kan ɗan uwansa ba shi kaɗai zai taho lol.

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212
[5/15, 10:33 PM] Hafsat A garku: *TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*Episode 17&8*

*…* Duk wannan abun da ake babu Taufeeq ba labarinsa Papa dai ya zuba masa idanu kawai tare da kasa kunnan ta inda zai jiyo ɗan nasa, Sweetie dai duk dauriyarta sai da ta sare dan shirun yayi yawa ko a waya ba a samunsa, balle ajiya inda yake, da daddare ta samu Papa da maganar shi kanshi dauriya kawai yake amma ya damu yasan halin da ɗan nasa yake, dan basa wuni basu ji muryar juna ba amma yau kusan sati biyu bai masan wani hali yake ba, cikin lumana tace
"A gaskiya ni dai ina ga, ba lafiya ba ace wai yau Taufeeq ni yayi sati biyu ba muyi waya ba kuma bamu gansa ba, gaskiya akwai matsala gwara dai a san abunyi Papan yara.
Ta ƙarishe maganar kamar za tayi kuka, Papa bai ce ma ta komai ba illa wayarsa da ya ɗauka ya shiga danna ƙiran layin Taufeeq ya ko ci sa'a ta shiga amma har ta gama ringing bai ɗauka ba ya ƙira yafi sau biyar ana bakwai aka ɗauka, cikin faɗa yace "Taufeeq kana ina?
"Ba hallaɓo bane, P.A sa ne, shi ɗin yana kwance tsawon sati ɗaya ba lafiya yanzu haka ruwa aka sake ɗaura masa, bayan waɗanda yasha.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'oun"
   Shine abun da Papa yake ta nanata wa Sweetie tuni ta firgita cikin tashin hankali tace
"Alhaji lafiya me ya samu Taufeeq ɗin?
Papa ne ya nisa yace "Yanzun kuna ina ne? Kuma ya jikin nasa?

"Muna Abuja yana gidan sa jikin da sauƙi ai yama warware kawai an ƙara samar ne saboda ya samu ƙarfin jikinsa"
P.A ya bashi amsa bai ƙara magana ba Papa ya kashe wayar.

Sweetie ya kalla da tuni ta ruɗe kamota yayi ya sanyata a jikinsa cikin muryar lallashi yace
"Ba dai wani abu bashi da lafiya ne yanzu haka ma ƙarin ruwa yake sha amma da sauƙi sai ki kwantar da hankalinki kinji?

"Hasbunallahu wani'imal wakin! wlh yanzu haka nasan akan auren nan ne ya ƙaƙalowa kansa jinya, sam in yaƙi abu aka tursasa sa tofa sai yayi jinya na rasha gane lamarinsa.
"Ai sai dai yayi ta jinya dan aure kam ba fashi insha Allahu gobe uwar haka suna ɗakinsu, gobe zan je naga jikin nasa sai mu dawo tare ta jirgi ma kawai zani dan mu dawo da wuri.
Bata da ta cewa illa binsa da addu'a da tayi ta lafe jikin mijinta aka shiga filin daga lol.
Washe gari tun ƙarfe 8 Papa ya isa a falo ya yadda shi yana zaune sai fitar da numfashi yake duk da mugun rama da yayi amma kyansa da kwarjininsa ƙaruwa sukayi, Papa ne ya zauna yana ƙare masa kallo dan sosai ya rame shima Taufeeq ɗin kallonsa yake ya kama leɓensa na ƙasa sai tsotsa yake kamar ya samu sweet cikin harshen nasara ya gaida mahaifin nasa, Papa gaisawa yayi ba yabo ba fallasa ya ƙara da cewa
"Ya jikin naka?

Kamar bazai amsa ba yace
"Da sauƙi yasu Sweetie?

Papa bai amsa masa ba yace "ashe Taufeeq baza ka iya bin umurnina ba? ita yarinyar ya dace tayi haka ba kai ba sai kuma gashi tun ba aje ko ina ba ka nuna min iyakata ashe ban isa da kai ba Abdullahi?

Taufeeq kamar zaiyi kuka yace "Papa wlh na amince kawai ɗan zazzaɓi nayi kuma ko baka zo ba ma, tasowar da nayi shiryawa zanyi na tafi Kadunan sai kuma gaka dan Allah Papa kayi haƙuri pls.

Papa yaji daɗi sosai cike da fara'a yace "tom Allah ya muku albarka tashi maza kaje ka shirya mu wuce kar baƙi suyi ta zuwa ba ma nan.

Miƙewa yayi yana haɗa hanya ya haura sama yayi wanka ya shirya cikin janfa ash colour yayi matuƙar kyau duk da kana kallonsa za kaga rama tattare da shi, amma duk gulmarka baza ka gane a ɓacin rai yake ba ko farin ciki ya ɗauki abun da zai buƙata suka tafi.
    Tun da suka isa ya nufi part ɗinsa ta baya saboda mata da maroƙa sun cika gidan sosai wani haushin su yake ji yake kamar yabi ta kan su ya wuce yana faɗin "su auren ma daɗi ya musu gashi sai washe baki suke kamar wasu birirrika ko wa ya gayyace su oho! a haka ya ƙarasa yana ta sababi yana shiga ko ina tsaf yake sai baza ƙamshi yake dan duk ranar duniya sai sweetie ta gyara masa da kanta, kwanciya yayi kansa yana kallon sama, gaba ɗaya har yanzu ji yake kamar mafarki yake ba gaske ba, zan so mafarki ne da bazan taɓa komawa ba, taya za ace za a aura min wacchar ficikar yarinyar furzar da iska me zafi yayi daga bakinsa, yana a haka Sweetie ta shigo da sallamarta amsa mata yayi ba tare da ya tashi ba bai kuma kalleta ba dan itama yaga murna take da auren karɓar kuɗi kawai take a wajensa kaf gidan murna suke da auren bayan Jaawad da shi sam baya son auren, a hankali ta ƙarasa ta zauna kusanshi ta sanya hannu ta kamo nasa tana murmushi tace

"Ashe akwai ranar da zata zo har ta tafi ba tare da ka ji muryar mu ba Minister? ta faɗi tana dariya

Miƙewa yayi yana sosa kansa da ɗan dariya yace
"I really so sorry Sweetie nayi tunanin hakan da nayi zai sa Papa chanja ƙudirinsa  na mun auren dole ashe hakan ba me yiwuwa ba ne, ya faɗi yana dariyar yaƙe dan yayi alƙawari bazai ƙara nuna musu ƙin auren ba sai dai ita ta gaji da azaba tazo tace a raba auren.

Sweetie ne tace "to ya jikin naka Malam ango"

"Da sauƙi dan ko ba sauƙi ma ba fasawa za ayi ba dan haka na ware Allah yasa haka shine mafi alheri Allah ya bawa fafa ladan zumunci.

"Amin ya rabbil izzati my son naji daɗi sosai da ka amshi wannan aure hannu biyu Allah ya maka albarka"

"Amin Sweetie Sayyid yazo kuwa?

Jim ta ɗanyi sannan tace
"A'a bai zo ba ya dai muku fatan alheri da ya ƙirani yace bazai samu zuwa ba.

Sam Tawfik bai ji daɗi ba saboda tun ba yauwa Sayyid yake zancen shagalin da za suyi a auren Taufik duk da kuwa Taufik ya nuna baza ayi komai ba amma haka ya nace yace dole sai sunyi shagali auren Minister guda sai kuma gashi auren yazo amma ba bu shi, yaji ba daɗi sosai.
Sweetie ne tace "ma za ka shirya kaga abokanka gasu chan sun cika falo, daga haka ta fice cike da farin ciki.
   Jikinsa a sanyaye yake shiryawa cikin wata ɗanyen shadda fara sol mai babban riga wanda tasha aiki sai maiƙo take da ɗauke ido komai na jikinsa fari ne har hular kansa da takalmi sai baza ƙamshi yake fuskar nan tana nan yadda take kamar kullum yana fita abokansa suka fara masa shega amma ko ci kanku bai ce musu ba, suma basu damu ba dan sunsan halin kayansu dama haka suka rankaya zuwa wajen ɗaurin aure inda yake cike da mutane maƙil kama daga shugabanni, gwamnoni, Malamai, Sarakai, babu wanda babu a wannan waje,mutane ne kamar kiyashi ba jimawa aka ɗaura auren *Abdullahi Nasir Adam Salwa* da amaryarsa *Nabeeha Ahmad Adam Salwa* akan sadaki Naira miliyon biyu lakadan ba ajalan ba, Papa wani irin farin ciki ne ya rufeshi wanda bai taɓa riskar sa ba, faɗi yake "a yau dai na cika alƙawarin da na ɗaukawa ɗan uwana mafi soyiwa a gareni Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, duk wanda yayi ido huɗu da Papa yasan yana cikin tsantsan farin ciki, saɓanin mai gayya me aiki da fuskar nam tasa tana nan yadda take a ko da yaushe take a wajen aka ta bawa Nabeeha kyaututtuka daga miliyoyi yayi sama domin su n san in Taufeek ne yana da ninkin su Papa dai ya rasa dame zai gode musu kawai kirari yake tayiwa ubangiji kaf! a wajen mutum biyu ne suke yanayi na baƙin ciki daga Taufik sau Jaawad dan sai da fidda ƙwalla daga ƙarshe ma barin wajen tuna aka fara gaisawa da ango ana masa fatan alheri bayan sun gaisa da manyan wajen ne ya shige motarsa ya nufi gidan dan yace sam bazai je dinner suke son yi ba, sun san halin kayansu hakan yasa suke je sukayi abun da ya dace, yana isa gida ya nufi part ɗin sa ta baya duk da mutane da suke ta zolayansa sa amma baibi ta kansu ba yayi wuce warsa yana zuwa ya cire babban rigarsa ya kwanta a gado yana maida numfashi.

A ɓangaren Nabeeha kuma tun da aka sanar mata an ɗaura aure take riskar kuka tuni kanta ya fara ciwo su Samha da ƙawayensu sunyi rarrashin har sun gaji amma a banza hakan yasa suka barta sai da ta gaji dan kanta tayi shiru wanda dalilin kukan da tayi tuni zazzaɓi ya rufeta ta kwanta ruf gwanin tausayi, Sweetie da kanta tazo ta bata abinci da ƙyar taci tashi magani ta sake kwanta wa, cikin gidan kuwa sai hada hadar biki ake wasu na tiƙar rawa, ba jimawa Papa ya shigo cike da farinciki, Sweetie ta taresa suna yiwa juna murna taimaka masa tayi yayi wanka yaci abinci sannan ya sake ficewa domin sallama da baƙin sa dan duk a yau za su wuce.

Taufik kuwa a waya yayi ta sallama da abokan nasa suna masa tsiya wani abokinsa me suna Abdul yace  "to mu dai sai munzo suna nan da wata tara dan nasan ka ba wasa oga, bai jira cewar Taufik ba yayi sauri ya gintse wayar dan yasan me zai biyo baya.

Da misalin karfe  5 na yamma Taufik zaune yake gaban mahaifinsa da Sweetie, Nabeeha nasiha Papa yake musu mai ratsa zuciya akan su zauna lafiya daga ƙarshe ya kalli Taufik a nutse yace

"Abdullahi ga amanar Nabeeha na damƙa maka kar naji kar na gani ka riƙe mun ɗiya da kyau dai-dai da second ɗaya kar ka bari hawayenta ya zuba, sannan kar ka bari tayi kukan maraici ka zame mata uwa da uba yayye da ƴan uwa ka zame mata bango 'in har ka mata haka to tamkar ni kayiwa in ka wulaƙantata ma kamar ni ka wulaƙanta ka tabbatar kana bata kulawa fiye da wacce zaka bamu mu iyayenka kana jina ko?

Muryarsa na rawa yace "Naji Papa insha Allah zan kamanta ya faɗi domin maganar ta masa tsauri ya masa nauyi ba haka ya so ba amma duk da haka bazan fasa abun da nayi niya ba, Papa ne ya katse sa da faɗin

"Allah ya maka albarka

"Amin"

Kallon Nabeeha Papa yayi wacce take zaune kanta a ƙasa cikin sanyin murya yace "Saura ke Nabeeha ki kasance me biyayya ga mijinki yi nayi bari na bari, a ko da yaushe ki zama kece ƙasa dashi domin shiɗin mijina a gareki kuma Yayanki, shine komai naki haka yayi ta musu nasiha daga ƙarshe ya kalli Sweetie yace "Queen ko kina da abun cewa?

"A'a bani da sai dai na bisu da addu'a dan ka gama komai duk da nayi wa ɗiyata

"Barakallahu laka wa baraka alaika wa jama'a bainakuna fil khair!

Suka fadi atare su kuma suka amsa musu da "amin"

Papa ne yace to maza kuje ku tafi zaku tafi da wasu ne a jirgin suga gida su dawo ko sai wani lokaci zasu je ya faɗa yana kallon Taufik da yayi hanyar fita.

Kafin yace wani abu Sweetie tace "A'a za su tafi da ko mutun biyar ne mana dangin mahaifiyar Nabeehan uku nawa biyu in yaso sauran sai suje daga baya tunda ba zama yanzu za ayi ba suna kaisu sai su dawo.
Tuni Taufik kam ya wuce Nabeeha ne ta kasa miƙewa kuka kawai take kamar ranta zai fita da sauri Papa ya wuce ɗakinsa da ƙyar aka raba Nabeeha da jikin Sweetie dan ta riƙeta gam haka Ka'aaf ma yaci kuka kamar ransa zai fita domin kaf gidan sunfi shaƙuwa da ita sosai basu ɗau lokaci ba suka isa birnin tarayya.
_Ga dai kaɗan ba dan halin kuma in naga comment ɗinku zuwa anjima zan baku na dare in kuma ban gani ba hikenam._🥳

Share pls👏🏻

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212
[5/15, 10:33 PM] Hafsat A garku: *TAUFEEK*

NA

*Hafsat A Garkuwa*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

_Walle ba yawa kuyi haƙuri da wannam_🥳

*Episode 19&20*

*...*"Saif ina so kamar yadda kake kula da ƙannenka ita ma ka ke kulawa da ita duk wani abun da zaka yiwa su Zarah ya zama da Amatullah a ciki domin ita ma ta zama ƴar gidan nan insha Allahu har'abada aure ne kawai zai raba mu da ita dafatan dai ka fahimce ni?

"Eh na fahimta Abba insha Allah kuma zanyi ƙoƙarin hakan dan wlh ta bani tausayi nima sosai gaskiya duk wanda akace mahaifansa basa duniya kuma bai samu iyayen riƙo nagari ba yana cikin gararin rayuwa Allah yasa mu dace, ya faɗi cike da tausayawa.
   Da "Amin" su Ammi suka bisa, sannan Ammi tace

"Wlh nima ina mugun jin tausayinta kuma na karɓi ragamar zame mata uwa kuma tagari in sha Allahu baza tayi kuka da ni ba"

"Masha Allah, Allah ya miki albarka na gode muku sosai Saif zaka iya tafiya ka gaishe da Nana da jiki"

"Za taji Abba ya faɗa tare da ficewa daga part qin

Washe gari Amatu suka fita da Zarah siyayya duk wani abu da mace take amfani dashi sai da Zarah ta saiwa Amatu, Amatu dai kallonta kawai take dan Zarah tace kada ta yarda ta mata zancen kayan sunyi yawa sai dai suka cika mota maƙil da kaya, basu zarce ko ina ba

Please Login or Register in order to submit comment