Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarda a min haka."
Turo baki tayi dan har ga Allah bata ji daɗi ba taya ma za ayi su wuce ba tare da sanin Sweetie ba.
Bakin sa ya haɗe da nata ya fara tsotsa kamar zai cire mata, gaba ɗaya suka fara shiga wani yanayi dan wani irin salo yake mata mai birkita kwanya ganin ba sauƙi ne yasa ita ma ta ƙara jan ragamar da zira hannunta a…


                       **********

Ko da Momy ta ji Saif ne zai auri Amatullah taji baƙin ciki sosai wani bare chan ma yace zai aureta sai da ta raba amma kuma ta dawo kan ɗanta yo ɗanta mana tun da ɗan mijinta ne hakan yasa ta yanke hukunci ziyartar boka abun da bata taɓa yi ba a rayuwarta kenan kissa na munafurci da tungu babu abun da bata iya a fannin ba amma ban da fannin boka amma yau akan Amatullah za ta jefa kanta ga halaka hakan yasa ba shiri ta nemi shawarar ƙawarta ta kuma bata ta ƙara da cewar za ta mata rakiya haka kuwa akayi ta rakata boka kuwa duk da ya gano wani gaskiyar lamari a dan gane da Momy da kuma yarinyar haka ya rintse ido yace zai mata aiki kamar yadda ta buƙata a futar da ƴar daga zuri'ar su gaba ɗaya ta koma in da ta fito kuɗi ya chajeta ba ɗan kaɗan ba ta bashi cike da farin ciki ta dawo gida.


Cike da farin ciki ya tashi ki yake ina ma yau ne gobe a ɗaura musu aure ko zai samu salama a zuciyarsa jin sa yake tamkar wani sabon ango ga Nana ra fashi haɗin kai ga kuma amarsu ta ango sam yau ban jin zan fita office.

Sam kuma ya kasa sanarwa da kowa ɗaurin auren sa domin yawanci ya sanarwa abokansa auren ƙannansa so in suka zo aka ɗaura sai ya shaida musu da haka ne yasa bai damu da faɗawa kowa ba fitowa yayi ya nufi ɗakin Nana domin ta fito suyi breakfast da sallama ya shiga zaune ya tadata cikin ado kamar yadda ta saba tana bawa Amaa abinci zama yayi kusa da su yana jin son su da ƙaunarsu na ƙara ninkuwa a zuciyarsa.

"Ina kwana Dear."

Ta faɗa cikin yanayin sanyi.

"Lafiya ƙalau Baby fatan kun tashi lafiya?

"Ƙalau muka tashi ya shirye-shirye?

Murmushi yayi yace

"Wani shiri kuma bayan dama an shirya."

Ya faɗa yana miƙewa ya karɓi Amaa daga hannunta ya nufi hanyar fita.

Itama miƙewa tayi ta bi bayansa ba tare da tace masa uffan ba suka nufi dining a tare suka karya suna yi suna hira kamar dai yadda suka saba har tsokanarsa take dan san bata ƙaunar ya hango damuwarta ganin bashi da niyar fita ne yasa ta miƙe tace

"Za mu shiga cikin gida mu gaisa, sannan ko da abun da za a yi."

Miƙe yayi yace

"Ok nima bari naje part ɗin Abba.


Yau haka ta tashi da wani irin faɗuwar gaba gaba ɗaya ji take kamar sam baza ayi auren nan ba, gani take kamar wani baƙon abu zai faru da ita dan tayi mafarki gidan gaba ɗaya kowa kuka yake har Abba wanda ta gasa gane kukan me ake haka  Kukan baƙin ciki ne ko kuma tsansar farin ciki oho hakan yasa duk wani addu'a da yazo bakinta karantawa take gaba ɗaya sai taji zaman ya gundureta hakan yasa ta fito zuwa harabar gidan tana gaf da fita ta zo dai-dai wani ɗaki da tun zuwanta gidan bata taɓa gani an buɗe shi ba ba a kuma taɓa mata magana akan ɗakin ba ita kuma bata yi dogon bakin tambaya ba kawai ta hango Nana tana tahowa ai da sauri ta yi hanzarin ƙarasawa wannan ɗaki domin samun mafaka dan ji tayi tana matuƙar tsoron Nana dan tasan yadda take da matuƙar kishi wa ya sani ma ko zuwa tayi ta dake ni.

Wata zuciyar ta faɗa mata hakan yasa ta ƙara sauri da adduar Allah yasa ɗakin a buɗe ne aiko tana murɗawa cikin sa'a ya buɗe ta kutsa kanta ciki ta rufe tana sauƙe ajiyar zuciya.

Tsoro ne ya ƙara kamata ganin ɗakin dulum babu haske ko kaɗan tunawa da tayi akwai waya a hannunta ne yasa ta kunna hasken tare da haska inda makunnin wutan ɗakin yake chan ta,hango shi a dungun ɗaki zuwa tayi ta kunna nan take haske ya gauraye ɗakin a hankali ta fara bin ko wani kusurwa na ɗakin da kallo ɗaki ne babba da bed ƙato da ya kusa cinye rabin ɗakin sai kuma drower ita ma doguwa ce da mirror duk wani kaya na amfanin mace a kwai a ɗakin fes yake tamkar da mutun a ciki babu alamun datti ko kaɗan ɗaga kanta tayi karaf ta hangi wani hotona wani irin zabura tayi tare da sakin wani ƙara ta zube ƙasa sumammiya.

A falo kuwa su Ammy ne zaune da ƴan uwanta suna tattaunawa ƙarar da suka jiyo a wannan ɗaki ne yasa suka nufo shi da hanzari gaban Ammy na wani irin bugawa suna buɗewa suka hangi Amatullah kwance ko motsi ba tayi da sauri suka ƙarasa Ammy ta kampta tana ƙwala mata ƙira amma shiru hakan yasa ta aika a ɗauko mata ruwa ba jimawa aka kawo mata ta zuba mata gaba ɗaya wani irin gauron numfashi ta sauƙe tare da fashewa da wani irin kuka ta ɗaga hannunta ta na nunawa faɗi take "Ummi na! Ummi na! Ummi na!!!

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212


*TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

Episode 61&62
…Ummina ne wannan wlh wannan Ummina ne wayyo Allah na! 
Ta ƙarishe maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki shiru cike suke da mamaki, al'ajibi da kuma fargaba Ammy ne tayi ƙarfin hali ta ɗagota tace
"Amatullah ki nutsu ki faɗa mana abun da ke faruwa kin har mu cikin duhu ba."
Cikin kuka tace
"Ammy wannan itace mahaifiyata ita ta haifeni gashi kuma ta tafi ta barni."
Ta faɗa tana nuna wata matashiya kyakkyawa da ita rungume da Abban gidan wato mahaifin su Zahrah.
"Mahaifiyar ki kuma na shiga uku."
Momy ne ta faɗi haka da ƙarfi tare da ƙarisa shigowa ɗakin dan tun ƙarar da taji ta fito ganin abun da ke faruwa sai yanzu ta samu damar magana cike da kiɗima taci gaba da magana tare da kamo Amatullah.
"Ban ga ne me kike nufi ba kina nufin kice Shamsiyya ita ta haifeki? ke ɗin ɗiyarta ce?"
Kai Amatullah ta ɗaga alamar "eh"
Wani uban ƙara Momy ta saka tare da faɗi ƙasa sumammiya.
Ammy ne tayi saurin sanar da Abba abun da yake faruwa cike da ɗimuwa yace gashi nan dan dama yana kusa yana wajen baƙinsa da suka zo ɗaurin aure a gobe.
Ba jimawa ya shigo ɗakin da suke cike da ɗimuwa shi da Saif gaba ɗaya suna yadda suke Momy dai ta farka tana ta riskar kuwa ganinsu a haka yasa yace 
"Ku fito muje falo na."
Yana kaiwa nan ya juya yana jin kansa na wani irin sarawa.
Gaba ɗaya wanda suka san lamarin gidan ya shafesu suka ranƙaya suka tafi wanda bai shafe su ba kuma suka yi nasu wuri.
Zama sukayi gaba ɗaya Amatullah tana jikin Ammy har yanzu tana riskar kuka domin ta tuna mutuwar mahaifan ta da irin kisan gillan da aka musu.
Momy kuwa kamar tayi hauka take ji duk da har yanzu bata gama gaskata maganar Amatullah ɗin ba ƙila ma ƙarya take a ranta addu'a take Allah yasa ba gaskiya ba ne, in ko aka ce gaskiya ne bata san inda za ta sa kanta da tulun kunya ba.
Abba ne yayi gyaran murya tare da kallon Amatullah a nutse yace
"Amatullah taya kika san wannan itace mahaifiyar ki um?"
Wani yawu ta haɗiya tare da gyara zama tace
"Abba a ko ina naga hoton Ummi na ko a yaya take zan gane ta balle kuma a inda komai na kamanninta ya fito taya zan gagara gane mahaifiyata Abba."
Jinjina kai yayi yace 
"Amatullah a yau dai ina so ki bani tarihin rayuwar mahaifanki da kuma na ki."
Goge fuskarta tayi tace



"Abba ni dai tun da aka haifeni na taso cikin iyayena da ƴan uwan mahaifini amma ban taɓa sanin ƴan uwan mahaifiyata ba mahaifini sunansa Jamilu mahaifiyata kuma Shamsiyya na taso cikin so da ƙaunar iyayena ban da na dangin mahaifi na wanda suke nuna min kyara da tsangwama saboda mahaifina ya fisu arziƙi sannan kuma basa son mahaifiyata sun fi son ya auri ƴar uwarsu, a duk wannan zaman da muke mahaifiyata bata taɓa faɗamin ina danginta suke ba sai dai a duk lokacin da na tambayeta tayi ta kuka tana faɗamin a duk lokacin da Allah ya haɗani da danginta na roƙesu da su yafe mata a haka zancen zai galgalce ni kuma in tambayarta ne domin nima nasan dangi saboda su wanda na sani basa sona saboda ƴan uba suke duk sanda ake wani taro a family gaba ɗaya ni da Ummi na a rakuɓe muku bama taɓa sakewa mu uku muke rayuwar farin ciki daga Ummina sai Abie na sai kuma ni a wani dare da bazan taɓa mantawa ba suka zaunar dani suna min nasiha mai ratsa jiki da jijiya akan ko bayan basa raye na riƙe mutuncina kuma duk rintsi duk wuya kar da yarda na guji dangin mahaifini.
Mahaifini ya ƙaramin da cewa nasan basa ƙaunar mu duka amma dole dai ƴan uwan mu ne ya ɗauko wasu takaddu yace waɗannan kadarori na ne a yanzun nan zanie na bawa lauyana domin ina ji a jikina kamar bazan rayu ba in kika yi aure kika zauna da ƙafarki zai mallaka miki kadarorin ki domin ke kaɗai na mallaka kuka nake sosai domin ji nake kamar wasiya suke ba ni a daren ya ƙira lauyansa aka saka hannu akayi komai ya tafi.
Mun jima muna tattaunawa har wajen 12 ya kama hannuna ya buɗe wani ɗakinsa na sirri yace "Mamana duk wani motsi da za kiji kar ki yarda kiyi magana ko tari karkiya sannan duk abun da ya same mu ba kowa ba ne face su Baffan ki Jibbo ina so duk rintsi kar kice zqki rabu da su domin sune ƴan uwanki na jini matuƙar ba yunkurin kashe ki suke ba haka yayi ta min nasiha ni dai kuka nake kawai na kamashi ina faɗin
"Abie dan Allah ka barni koma me zai sameku ya same mu tare, in wani abu ya same ku bansan ya zanyi ba.
Rungumar ta yayi yana bubbuga bayanta shiga hawaye yake yasan duk rintsi bazai taɓa tsallake ƙaddarar sa ba da ƙyar ya ɓanɓareni a jikinsa ya kulleni ta waje, kuka nasanya mai ban tausayi gani nake kamar nayi bankwana da su kenan windo na leƙa naga har ya shiga bedroom ɗinsu ya kulle ina nan tsaye a wajen domin bazan iya rintsawa ba har wajen ƙarfe 2 ina zaune akan windo wanda ni ta ciki zan iya ganin komai na waje amma wanda suke waje baza suga komai ba sai duhu.
Chan naji motsin mutane ƙarti har su biyar riƙe da manyan makamai sun nufi ɗakin su Ummi.
Chan naji ƙaran Ummi tana duk addu'ar da tazo bakinta kokawa sukayi da Abbana sosai na kare kai amma ina har falo suka fito ina kallonsu ɗayane ya zagayo ta bayan Abbana ya buga masa ƙarfi a kayi hakan yasa suka samu nasara kisa suka masa mai muni bayan sun caka masa muƙa suka sassareshi haka ma Ummina suka yanka wuyanta sai da suka tabbatar basa motsi sannan suka lelleƙa ɗakuna suna nemana ganin basu fanni bane yasa suka ƙira Baffa Jibbo suka sanar dashi yace su taho kawai suka tafi.
A lokacin naci kuka kamar raina zai fita ina zaune ina hango gawar iyayena waɗanda a gabana aka musu kisan gilla ba tare da na iya dakatarwa ba sai da gari ya waye su Baffa suka zo nayi ta bubuga ƙofar suka buɗemin har da kukan ƙarya wai na tausayina semana ya kai goma a lokacin da na riski gawawwakin iyayena kwance cikin jini…
Nan taci gaba da sanar musu har dalilin da yasa ta fito da dare da kuma dalilinta n ɓoye musu gaskiyar labarinta saboda kar suce za su maida ta gurin dangin mahaifinta ne ta ƙarisa maganar da cewa
"Tun ranar da na ganku nake ji tamkar kuɗin jinina ne amma rashin shaida yasa ban nuna ba.
Gaba ɗaya ɗakin kuka suke ba kama hannun yaro kuka ne na tausayin kan su da kuma na kisan gilla da kuma na tausayin Amanullah hatta Abba Momy kuwa ji take kamar tayi hauka dan ji tayi duniyar gaba ɗaya tayi mata zafi Zarah ne ta zo ta rungumi Amatullah tana fashewa da wani irin kuka, sai da sukayi son ransu suka dakata Abba ne ya nisa yace

"Tabbas babu mai yi sai Allah a yau Allah ya nuna mana ikonsa ana gobe aure Allah ya fallasa komai da yanzu Ƴa ta auri Ubanta wa'iyazubillah! haƙiƙa Allah shi ne abun godiya da anyi wannan aure da Balkisu kin shiga uku domin duk wannan abun ba kowa ne sila ba sai ke saboda a dalilinki ƴarki ta bar gida ke kikayi sanadiyar da har tabar duniya bata sake samu a idanunta ba Yarinya mafi soyiwa a gareni ni dai babu abun da zan ce miki sai dai nace miki na...

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212


*TAUFEEƘ*
NA
Hafsat A Garkuwa

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/


*Episode 63&64*
… "Na barki da fitowar rana da faɗuwarta domin kece silan komai."
Ya faɗa zuciyarsa na wani irin ƙuna ji yake kamar ya shaƙo Momy har sai yaga bata motsi ko zai ji sanyi a zuciyarsa.
Amatullah ce tace 
"Abba dan Allah ku bani labarin Ummina da kuma abun da tai muku dan Allah."
Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata.
Abba ne ya gyara zamq yace
"Jikata zan sanar dake wacece mahaifiyarki Shamsiyya ƴace ta gari wacce kowa yake yabonta ƴan uwa da abokai fata suke ace Shamsiyya ƴarsu ce saboda nutsuwarta da kuma kamun kanta ga ladabi da biyayya ga kyau ga kuma farin jini tun da ta taso bata taɓa saɓamin ba komai nace shi take yi a haka har ta girma manaima suka fara sintiri manyan mutane amma san Shamsiyya bata son su sai wani bawan Allah Jamilu wanda yazo garin nan neman kuɗi da kuma karatu Allah ya ɗaura musu son junansu ba yadda mahaifiyarta ba tayi ba wato Momy akan su rabu domin ta washi talaka ta kuma washi bafulatani tafi so ko Shamsiyya za tayi aure to ta auri yare kamarta amma Shamsiyya taƙi fur tayi jinya sosai akan rabata da Jamilu da akayi daga farko mun ɗauka sun rabu hakan yasa mahaifiyarta ta nema mata ɗan uwanta beyerabe aka fara shirin biki duk Shamsiyya tana shiru nan muka zauna da ita akan maganar auren tace ita sam bata son shi za ta iya kashesa idan aka aura mata shi, jin haka na samu Balki da maganar ta inda take shiga ba tanan take fita ba hakan yasa cikin dare ta biyo Shamsiyya da wuƙa sai ta kasheta a daren Shamsiyya ta bar wannan gidan tare da Jamilu suka gudu ashe dama a ranar suke shirin guduwa don ta bar mana takarda akan ita ta tafi za suje suyi aure da Jamilu, babu kalan bakin da Balki ba tayi mata ba tace insha Allahu auren nan ne zai yi sanadin mutuwarki Shamsiyya naji baƙin ciki sosai domin ni dai har ga Allah ina matuƙar son ta da Jamilu kawai a lokacin ban san me ke damu na ba na kasa yin wani abu naji ciwon guduwarta baby inda ba ayi cikiyarta ba amma shiru a haka har na kwanta jinya kullum sai nazo ɗakinta nayi ta kallonta a hoto har kawo yanzu kullum sai na shiga yau ma na shiga da san fita ne na mance ban rufe ƙofar ba, Allah ya jiƙanki Shamsiyya na yafe miki duniya da lahira nayi matuƙar farin ciki da akace yau gani ga tsatson ki.
Amatullah tayi kuka sosai tace
"Abba dan Allah ku yafewa Mamana don Allah."
"Kar ki damu jikata na yafe mata duniya da lahira."
Momy ne ta jawo Amatullah ta rungumeta tana ƙara fashewa da wani irin kukan nadama maras misaltuwa gaba ɗaya ɗakin sai da suka tausaya mata Amatullah ma kuka tasa cikin kuka Momy tace
"Jikata don Allah kiyi haƙuri ki yafe min abubuwan da na miki ace wai Jikata nake wa baƙin ciki duk cikin rashin sani wayyo Allah na!"
Ta faɗa tana kuma fashewa da kuka
Abba ne yace 
"Balkisu shiyasa a kullum nake nuna miki kar ki na kyarar ɗan mutum domin baki san wanene ba kar kiyi wa wanda baki sani ba mugunta domin kuwa wataran za kiji kunya za kuma kiyi ladamar da bata da amfani ni dai kin gama cutata domin bakin ki shi ya jefa Shamsiyya a wannan halin."
Cikin kuka tace "Alhaji don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min na tuba dan Allah Fatima kisa baki don Allah."
Ta faɗa tana nuna Ammy da take zaune hawaye na sauƙa a kuncinya har yanzu bata iya cewa komai ba da ido kawai take binsu goge hawayen ta tayi tace
"Abban su don Allah kayi haƙuri ka yafe mata tun da komai ya riga ya faru Allah ya jiƙan Shamsiyya, ai ita kanta yanzu ta gane ta kuma yi nadama shiyasa a kullum nake sanar da ita ta guji ƙyamar talaka yqnzu gashi duk abun da tayi ya dawo kanta wa gari ya waya kenan?
"Wlh haka ne Fatima kuma ko auren ta da aka fasa na Lamir ni naje gidan su na sanarwa Hajiyarsa Ƙarya da gaskiya hakan yasa aka fasa ashe jikata nayiwa mugunta."
Ta faɗa tana kuma fashewa da kuka tuni aikin da tasa boka ya mata akan Amatullah.
Cike da ɓacin rai Abba ya ɗago yana nuna ta da yatsa yace
"Ke kina sa aka fasa auren? kai Balkisu kije na sakeki saki biyu kuma kar ki kuskura ki tafi da kowa a cikin ƴaƴana da Jikata yadda kika zo haka zaki koma."
Daga haka ya miƙe Ammy za tayi magana ya dakatar da ita ya fice a ɗakin.
Momy ba ta wani ji zafin sakin ba domin bala'in da ke shirin tunkarota gwara ayi ta jero mata saki da wannan bala'in, gaba ɗaya ɗakin suka watse aka bar Momy da yaranta wanda suke ta kuka jin an saki mahaifiyar su.
Momy dai tana rungume da Amatullah cikin kuka ta kuma cewa
"Don Allah Amatullah ki yafe min kin ji?
"Na yafe miki Momy amma kema dan Allah ki yafewa Ummina."
Tafaɗa tana gogewa Momy hawayen ta.
Cikin kuka tace
"Na yafewa Shamsiyya tun ba yawa ba amma bari na maimaita na yafe miki Shamsiyya Allah ya jiƙanki da rahma Allah yasa chan yafi miki nan nima ki yafe min Shamsiyya ta."
Ta faɗa wani kuka na kufuce mata kamar an tsikareta ta miƙe ta fita ɗakinta ta shiga ta ɗauki mayafi da wayarta ta fice a gidan gaba ɗaya.
Su Raudah kuma rungumar Amatullah sukayi suna bata hakuri musamman ma Raudah dariya Amatullah tayi tace kar ku damu komai ya wuce fa a tare suka fito suka shiga ɗakinsu suka fara hira kamar basu Raudah ba Zarah ma da ƙawayensu hirar suka shiga nan ɗakin ya kacame da farin ciki.

Saif tun da aka fara wannan lamari mai makon yaji ɓacin rai sai wani irin farinciki yake ji maras misaltuwa tare da godewa Allah da ya fito da komai fili tun kafin lokaci ya ƙure sai yanzu ya samu amsar son da yake iyawa Amatullah ba wai so ne na aure ba so ne na Ƴa da Uba domin ko sau ɗaya bai taɓa jin sha'awa akanta ba kawai yasan yana mata son dacbai taɓa yiwa kowa ba dalili kuwa shine mahaifiyarta Shamsiyya tayi masa wani irin son da ko iyayensa albarka nan take yaji ƙaunarta na Ɗiyarsa ya ƙara ninkuwa a zuciyarsa, suna shiga part ɗinsu Nana da ke jikinsa ta rungumesa ciki da farinciki tace

"Alhamdullah! ashe dai da rabon baza a min kishiya ba wayyo daɗi!"

Ta ƙarishe maganar cike da farin ciki dq ɗan ƙara.

Dariya Saif yayi yace

"Allah ne ya dubi niyarki Dear domin kinyi abun da ba ko wacce Mace bace za ta iya, kin goyi bayan mijinki duk da bakya son abun amma haka kika danne kika ɗauki komai ba komai ba, in da bori kika tayar sai kiga babu abun da zai hana sai Allah ya nuna miki iyawarsa, (Za kuga wasu matan sun tada bori sai an sake su akan za a ƙara aure ana sakin kuma sai kiga ba ayi auren ba kinga kinyi biyu babu kenan in da kin zauna kin miƙawa Allah lamarinki sai kiga ya dubeki ya kawo sanadin da baza ayi auren ba wani kuma za ayi auren sai kiga Allah ya sanya miki haƙuri da kuma nutsuwa ki zauna lfy da abokiyarki wani kuma za a samu ƴan ƙalubali a zaman nasu ba yadda Allah bayayi mu dai mu kasance a ko da yaushe masu haƙuri da kai zuciya nesa).

Ƙara shigewa jikinsa tayi tare da haɗe bakinsu guri guda tana masa wani irin tsotsa wanda tunda suke bata taɓa masa irin wannan salo mai birkita kwanyar ba gaba ɗaya ta jiƙasu da wani shu'umin salo mai wuyar mancewa gaba ɗaya su n fice a hayyacinsu sun lula duniyar ma'aurata ba ka jin komai sai gurnani da nishi ana kashe arna...😹

      ****************
Babban Gida ne da ya amsa sunan gida wanda duk ji da kudi da kake baza ka gina gidan da yafi wannan ba da iya tsaruwa ya tsaru ga kuɗi da aka narka a ciki yana rungume da abarsa suka shiga gidan wanda yake mallakin sa a nan Kaduna, wani irin ƙamshi ne ya daki hancin su wanda a tare suka sauƙe ajiyar zuciya direct sama suka nufa yana rungume da iya wanda jikin ƙarfen step ɗin aka jera masa flowers masu fidda wani irin haske kala-kala wani ɗaki suka shiga wanda shine mallakin sa babban ɗaki ne wanda yasha kayan more rayuwa wanda tsayawa faɗarsa ma ɓata lokaci ne bathroom suka shige wanda shiɗin ma fa ɗakin wata hamshiyaƙiyar bai kai wannan toilet ɗin haɗuwa ba a tare suka wanka tare da ɗauro alwala ya ɗaukota kamar ƴar tsana yaso ya kashe arna amma babu lokaci saboda aj fara ƙiran sallah hakan yasa cikin sauri ya shiryata cikin kayan bacci shikuma ya sanya jallabi ya feshe jikinsa da turare ya fito, itama sallar ta tayar bayan ta idar ne tayi lafiyar gado domin ta gaji sosai ba jimawa kuma bacci ya ɗauketa.
Cikin bacci taji ana shafa breast ɗinta da sauri ta buɗe ido ganinsa ne yasa ta sauƙe ajiyar zuciya.
"Wa kike tunani zai shigo har nan ya taɓa min Baby na? Ai duk wanda yayi gangancin haka ma hmmmm!
"Oya tashi muje mu ci abinci dan nasan kina jin yunwa gajiya ce tasa kika kwanta."
Ba musu ya kamata ta miƙe dan har ga Allah kan tana jin yunwa gajiyar da tayi ne yasata kwanciya duk da tasan duk dare sai ta tashi neman abincin.
Ƙasan suka sauƙo ya baje musu abubuwan da suka saya a hankali yake bata tana ci ita ma tana bashi suna sakarwa junansu tsadaddan murmushi suna cikin haka ne wayarsa ta fara ruri kamar bazai ɗauka ba ganin sunan da ke yawo ne yasa ya saki murmushi tare da ɗauka wayan bakinsa ɗauke da sallama.
Sweetie jin ta ɗaga ne cikin fushi tace
"Kayi hanzarin dawo min da yarinya duk inda ka kaita nan da minti ashirin...

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212

*TAUFEEƘ*
NA
Hafsat A Garkuwa


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/


Episode 67&68
…Zaune take a gabansa kana kallonta kasan a matuƙar tsorace take gaba ɗaya ta fice a haiyyacin ta duk yadda ta so ta daure abun ya faskara wani irin kuka ta sake jin abin da ya kuma faɗa mata
"Balkisu dole ki bada wanda za ta fanshi Amatullah zaɓi biyu gareki ko ki bari muyi aikin mu akan Amatu ko kuma ki bada wani in kuma kin ƙi to ina tabbatar miki a kan ki zai sauƙa za kiyi nisa da wannan duniyar za ki rayu cikin azaba da baƙin ciki baza ki taɓa samun

Please Login or Register in order to submit comment