Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara sa shi a idon ta ba kuma ko ta ƙira layinsa baya shiga, hakan yasa ta shiga damuwa shiyasa tazo wajen ta zauna, ta kafesa da idanu tana kallon abun da yake sai dariya take ƙasa-ƙasa dan kar yajita, mamaki ne da kaɗuwa suka taru suka mata yawa, idanunta ta zaro me matuƙar sheƙi da ɗaukar idanu, ganin sa da tayi yana shan sigari, taɓe baki tayi a fili tace "ashe ma ɗan iska ne Yaa Taufeeq ɗin tun da gashi har sigari yake sha, sai yana yiwa mutane wa'azi kamar na Allah mtsww ta ɗan ja tsaki ta tashi ta bar wajen dan karma ya ganta.

   Ya jima zaune a wajen a juma yace "why? why? why!! Papa zai min haka kamar ni a rasa da wacce za a haɗani da ita sai wacchar figigiyar yarinyar wanda hankali bai gama isarta ba, gaskiya ni ba a kyauta min ba wlh.
    Sai da aka ƙira magriba sannam yabar wajen wanka yaje yayi ya nufi masallaci har yanzu ransa a dagule yake, ko da dare tayi kasa bacci yayi juyi kawai yake a gado amma sam bacci yaƙi ziyartar sa, kalaman Sweetie da ya tuna ne suka ɗan kwantar masa da hankali dan da yaje ya sanar mata taje ta samu Papa ta masa magana a fasa maganar aure nasiha tayi ta masa dangane da bin umurnin iyaye tare da azabar duk wanda ya saɓawa iyayensa duk da ya sani amma jin zancen ta yake sabo kamar bai taɓa jiba ranar dai bacci ɓarawo ne ya ɗaukesa.
Washe gari da yamma Nabeeha sukayi shiri za suje shopping Sweetie suka sanar wa tace sai dai taje ta gayawa Yayansu ita ba ruwanta, su Samha suka ce su dai babu inda zasu gwara a haƙura da zuwan, Nabeeha kuwa tace dole sai anje domin sayayyan kayayyakin partyn su za suyi, part ɗin sa ta nufa rai ɓace, knocking tayi har sau uku shiru hakan yasa ta tura ƙofar ta shiga, parlorn fes yake sai tashin ƙamshi yake, ido tayi ta warewa chan ta hangoshi kwance a kan kujera ya lumshe idonsa, kallonsa tayi taga kamar ya ɗan rame, taɓe baki tayi ta ƙarasa wajen sa tace "Yaa Taufeeq ina wuni dama za muje supermaket ne shine Sweetie tace sai munzo mun gaya maka, ko motsi baiyi ba balle tasa ran ko ya jita, da ɗan ƙarfi tace

"Yaa Taufeeq ka ji muje ko?"
     "Yaa Taufeeq!
A fusace ya miƙe ya kifeta da mari ya sake kifa mata mari yasa ƙafa ya jideta ji kake guf! ta ɗagu ta rimu da ƙasa wani azababben ƙara ta sake sai kuma ta sulale ƙasa sumammiya, cikin matsanancin ɓacin rai yace

"Dan ubanki da kin san tsanar da na miki baza kina dosowa inda nake ba, ke in ba marar hankali ba a kwance kika zo kika sameni fa, kin san dai da yamma bana bacci tunda ni dai ba jahili bane, tun da kika yi maganar farko da kika ji ban amsa ba, sai ki koma in da kika fito salin alim, amma da yaje ƙwaƙwalwar kifi gareki ai ga abin da kika jawa kanki wawiya kawai wlh na tsaneki!

"Dan ubanka da ka tsaneta sai ka kashe ta, cewar Papa da tun ƙarar da suka ji Nabeeha tayi suka shigo ɗakin gaba ɗaya cikin ɓacin rai Sweetie tace
   "Abdullahi ashe baka da hankali? ashe kallon da muke maka ba haka kake ba? kowa yabonka yake ashe kai abun gudu ne ban sani ba? wlh tun wuri ka zubar da wannam halin da ka koyo dan ba me kyau ba ne tun ba a je ko ina ba za ka kashe musu ƴa tirrr! da halin ka wlh"
        Ta faɗa tana nufar inda Nabeeha take kwance kamar gawa jijjigata ta farayi amma shiru kake ji ko gezau Nabeeha batayi ba Samha da take tsaye fuskar tan nam shaɓe-shaɓe da hawaye da sauri ta ɗauko ruwan sanyi ta miƙawa Sweetie, Sweetie ta ma mance da wani ruwa, da sauri ta buɗe ta yayyafa mata har sau uku sai a na ukun ta ja gwauron numfashi sannam ta fashe da wani irin marayan kuka ta rungume Sweetie.
   Papa da ransa ya gama ɓaci ya kalli Taufeeq da yake tsaye fuskar nam ɗaure yace

   "Na gode sosai Son Allah ubangiji ya maka albarka"

Daga haka yayi waje rai babu daɗi yana jin takaici da mamakin ɗan nasa da ya sauya hali tashi ɗaya.
Sweetie ne ta miƙar da ita sukayi waje Nabeeha na kuka kamar ranta zai fita, bedroom ya nufa ransa a jagule, toilet ya faɗa ya sakarwa ƙansa ruwa ko zai samu salama but maimakon ya samu nutsuwa sai ƙara jagulewa da zuciyarsa tayi sai yanzu yake ganin illar jayayya da yayi da iyayensa, hakan yana nufin yana jayayya ne da hukuncin mahaliccin sa, istigfari yake tayi a zuciyarsa domin yanzu ne komai yake dawo masa, yasan ya mugun ɓata ran mahaifinsa, yasan kuma bazai sauƙo ba har sai ya amince da auren "dole na nuna masa na amince amma wallahi sai ta gwammaci mutuwarta da zama dani, sai ta gwammace dama ba a haifota tazo duniya ba, ni Abdullahi Nasir Adam Salwa wlh sai na shayar da ita maɗaci sai na gigita rayuwarta wlh... Zancen da yake tayi kenam a hankali ya samu zuciyarsa tana ɗanyi masa sanyi
Sai yanxu yake jin haushin koran duk wani aboki da zai raɓesa sam baya son yi aboki Sayyid ne kawai abokinsa kuma ko da wasa bazai tinkaresa akan ya bashi shawara game da auren nam ba, tun da shi yake sonta gsky ni dai ba a kyautamin ba ko kaɗan.
Washe gari zaune Sweetie take gaban Papa bayan ya gama yi mata bayani, cike da farin ciki tace "gsky nayi farinciki Allah ubangiji ya sa ayi damu Allah kuma ya basu zaman lafiya amma kuma kamar sati biyu yayi kaɗan ko? "baiyyi kaɗan ba so nake na nuna masa ikon da nake dashi akan sa in yaga dama ya min biyayya in bai ga dama ba kuma duk zan gani, shiru Sweetie tayi sai chan ta nisa tace "to kuma an sanar ma Nabeeha ne? anya ita ma zata amince da auren kuwa duba da duk basa son junan su, "Ta Nabeeha me sauƙi ne na san baza ta bani kunya ba in sha Allah zata amince yau nake so na sanar da ita dan haka ku fara shirye-shiryen ku na mata, ko nawa ake so a masa magana ya fito dasu tun da shi zai amfana da abun, Sweetie tace "yanzu kuwa ai baza mu tsaya sanya ba bari na ƙira me gyaran jikin nam ta maiduguri dama tazo garin nam gyara wata amarya ta ƙirani ko za tamin gyaran nace ba yanzu ba, Allah yasa dai bata koma ba, ta faɗa tana dialing number Hajiyar Maiduguri bayan sun gaisa ne ta sanar mata da buƙatar ta aka ci sa a kuwa gobe take shirin komawa, suka yi sallama akan gobe za ta shigo da yamma za taje kasuwa ta ƙaro wasu abun, godiya Sweetie ta mata sosai cike da farin ciki, ta sanarwa Papa "Alhamdulillah sai kisa ɗan naki ya mata transfer in ma cash zai bata wannam shi ya jiyo, ana haka aka fara knocking a ƙofar Sweetie tace shigo, da sallama ya shigo kansa a ƙasa ya zauna chan gefe a hankali ya ɗago ya kalli Papa yace "Papa ina kwana a daƙile Papa ya amsa ya ɗauko wayarsa yana dannawa dan fushi yake da ɗan nasa da gaske, Sweetie ya kalla yace "ina kwana Sweetie ba yabo ba fallasa tace "lafiya lau kallonsa tayi da kyau ya rame sosai kamar wanda ya kwanta jinya, taɓe baki tayi cike da mamaki Papa ne ya miƙe yace "Queen zan ɗan fita nima ina da nawa shirin, har zai fita da sauri Taufeeq ya riƙe ƙafafunsa yace "dan girman Allah Papa kayi haƙuri ka yafemin fushinka a gareni babban zunubi ne, wlh fushin ku ba abu me kyau bane a gurina, na gwammace mutuwa ta da ku cigaba da fushi da ni, dan Allah ku yafemin in dai akan wannam auren ne wlh zan muku biyayya wlh na amince zan aureta, ya faɗa wani hawaye masu zafi wanda bai san daga inda suke ba ya zubo masa, komawa Papa yayi ya zaune yace "Son ba wai dan na cutar da kai ba ne na haɗaka aure da Nabeeha nayi haka ne saboda cika alƙawarin ɗan uwana, in da bai ƙwallafa rai akan ka ba kar ka manta tana fa da saurayi shima kuma ɗan uwanta ne, amma alƙawarin ba zai cika  ba in ba da kai ba, ni dai umurnin da zan baka shine ka riƙe mun ƴa da amana, in har ka zalunceta tamkar ni ka zalunta ne sannam yanxu ka tashi kaje ka fara shirin ka kamar ko wani ango Allah ya maku albarka, miƙewa yayi a sanyaye yace "amin Sweetie ne tace "ango fa muna son kuɗin gyaran amarya da kuma na lefe da sauran su za ka mana transfer ne? cikin cool voice yace "tam! a taƙaice ya fice a ɗakin da sauri kamar an korosa.

   Papa ne ya kalli Sweetie yana murmushi yace "ni dama nasan zai amince domin bai taɓa saɓawa umurni na ba sai wannam karon nasan shi kansa abun zai damesa saboda bai taɓa ba, alhmdllh yanxu kin ga zamu fara shirin mu cikin farinciki, yanzu maza ki ƙiramin Nabeeha kar ayi ta shiri ba tare da an sanar da ita ba, na tabbata za suyi alfahari da wannam haɗin, miƙewa Sweetie tayi tace "to Allah yasa haka muke fata ai, ba su ɗau lokaci ba suka shigo tare da ita zaunawa tayi ta gaidashi sannam tace "ga ni Papa na Allah yasa kyauta za amin ta faɗa tana dariya Papa yace

"Babbaɓ kyauta ma kuwa Dota Allah yasa dai baxa ki ƙi karɓar sa ba?

   "Taɓ! Papa ai ko wani kyauta ce ina murna da zuwansa ta faɗa cike da zumuɗi.

  "To alhmdllh Maryam! da ni da mahaifinki mun yake wani hukunci ba tare da munji daga gareku ba, saboda a tunanin mu mu muka haifeku zaku amince da duk wata magana da muka gaya muku sannam za kubi umurnin mu haka ne ko?
   Kanta ta sunkuyar tace "haka ne Papa"

"Maryam munyi alƙawari da mahaifinki za mu haɗaku aure da ke da Yayanki M.T to yanzu lokaci yayi da zan cikawa ɗan uwana alƙawarin da na masa, yanzu haka mun yanke nam da sati biyu masu zuwa za a ɗaura muku aure.

Da sauri ta miƙe tana girgiza kai cike da firgici. Da kaɗuwa so take tayi magana amma ta kasa kanta taci gaba da girgizawa tuni hawaye suka wanke mata fuska sai chan ta fisgo magana tace

"A'a Papa bazan iya auren Yaa Taufeeq ba wlh ni Yaa Sayyid nake so Papa Yaa Taufeeq fa ya tsaneni baya ƙaunata dalilin haka nima naji na tsanesa bana ƙaunarsa bana son ganinsa, ta ya za muyi zaman aure da shi, wlh ni Yaa Sayyid nake so kabi Abba na kuje ku warware alƙawarin da kuka yi ni dai bazan iya auren Yaa Taufeeq ba Sweetie ne ta riƙota dan dama tasan hakan zai faru, jikin Sweetie ta faɗa ta fashe da kuka sai da tayi kuka me isarta babu wanda yace mata ƙala ta jima tana kuka sannam ta fara ajiyar zuciya, kallonta Papa yayi yace

"Maryam kiyi haƙuri babu ta yadda zan je wajen mahaifin ki in dai ina raye,  Yayanki kuma ba wai tsanarki yayi ba kawai bai son rashin ji da kike yi ne amma shi me ƙaunarki ne tun kina ƙaramarki
halinki yake so ya gyara miki shiyasa amma kuna aure komai ya wuce zaku zama abun burgewa ga kowa kinji Maryam?
  "Ni dai wlh Papa ba ya ƙaunata nima bana son sa ta kuma fashewa da wani kukan
     Papa kallonta yake da mamaki ganin ta watsa masa ƙasa a ido tashi yayi ya fice ransa duk a jagule, ya rasa yanxu wani irin ƴaƴa aike haifa ko wani yaro sai ya nuna kai baka isa da shi ba.
   Sweetie ne ta kalleta rai ɓace tace "ina kukan baku da kunya, bakwa jin nauyin yin faɗi in faɗa da ubanku, yanzu dai kin ga yadda kika ɓatawa mahaifinku rai hakan ya miki daɗi ko? ashe ku baxa a gaya muku magana karon farko ku ɗauka ba sai kunyi gardama, sanyaya muryarta tayi taci gaba da cewa
    "Nabeeha M.T ɗana ne ni na haifesa amma a gaban mu kike nunawa kin tsane sa amma duk da haka Papan ku ya zaɓi ki zauna tare dashi saboda yasan bazai cuceki ba alƙawari sukayi shekaru da yawa baya akan za su haɗa ku aure, nasan dai kin san girman alƙawari kina so Allah ya kama iyayenku akan ƙin cika alƙawari da sukayi?
  Da sauri ta girgiza kai alamar a'a murmushi Sweetie tayi ganin jikinta ya fara sanyi nam ta gyara zama tace
    "Yauwa ɗiyata ai kinga biyayya za kiyi wa iyayenki sai kiga kinyi albarka sannam da kike faɗin Yayanku baya sonki karki damu ni zan koya miki yadda zai so ki ai ni babbar ƙawarki ce ko?
   Da sauri ta rufe fuska da hannunta tana dariya tace "eh Sweetie sai kuma ta haɗe fuska kamar za tayi kuka tace "to Sweetie ya zanyi da Yaa Sayyid kuma wlh yana so na fa, ta faɗa wasu hawaye masu zafi suka zubo mata
   "Kar ki damu Sayyid ya haƙura ya bar wa ɗan uwansa ke yanzu shi ba sonki yake na aure ba ke ɗin ƴar uwarsa ce yanzu babu aure tsakaninku.
   "Allah sarki Yaa Sayyid tun yaushe yake bi na akan na amince da soyayyar sa amma naƙi da mun jima da aure, amma gashi yanzu zan auri wanda baya so na, ta faɗa tana turo baki wasu hawayen na zubowa

Dariya Sweetie tayi dan ta san har yanzu Nabeeha yarinya ce akwai yarinya tattare da ita in ba yarinya ba wa zai yi haka😹 

✨✨✨✨✨✨✨✨

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'oun" ta faɗa tana dafe kanta da yake barazanar tarwatsewa Dr ne ya matso yace "sannu baiwar Allah a hankali ta ɗawo ta kallesa ta ɗaga masa kai yace "me kike ji yanzu?

"Kai na ne yake ciwo sosai sai kuna ƙafa ta, ta faɗa tana nuna masa ƙafarta
   Yace "eh dama dole za suyi  ciwo saboda kin bugu sosai amma yanzu  alhmdllh in kina shan maganinki za kiji sauƙi bada jimawa ba dafatan za kiyi ƙoƙarin shan maganin?
  Kan ta ta ɗaga alamar eh Dattijon ya kalla yace Alhaji za ku iya tafiya yanzu za mu ƙara rubuta mata magani amma in kuka ga wani sauyi za ku iya dawo da ita domin mu ƙara dubata Allah ya ƙara sauƙi
   Godiya yayi masa ya fita, ƙarasawa yayi wajen ta yace "sannu Dota ya jikin naki?
  Cike da girmamawa tace "Na ji sauƙi sosai Abba yaji daɗi sosai jin sunan da ta ƙirasa da shi
Murmushi yayi yace "za dai kiji sauƙi Dota amma baki gama warewa ba ni ban so su sallameki ba ma sai kin ware gaba ɗaya amma yanzu ma alhamdulillah to ni dai sunana *Alhaji Tahir Abdulƙaɗir Maina* ni babban ɗan kasuwa ne ina da kamfanoni na Jirgin ruwa motoci mashi keke napep da dai sauran su ina na biyu daga jerin masu kuɗin najeriya daga *Alhaji Nasir Adam Salwa* sai ni na biyu sai kuma yaronsa duk da ƙarami ne amma yana da tarin arziƙi na bam mamaki *Minister Abdullahi Nasir Adam Salwa* da ni da mata na da yarana muna zaune a Dubai ina da mata biyu da yara shida Babba ɗana yayi aure yana zaune nam tare da mu sai kuma ƙannensa mata guda huɗu mai binsa ita ma tayi aure tana chan da mijinta sai saura ukun suna nam tare da mu su na karatu, ina gaya miki labarin nam ne dan kisan waye ni, sannam jiya mu ne muka buge ki ba tare da mun sani ba shine muka kawo ki hospital yanzu sai ki sanar mana ina ne gidan ku sai mu maida ki ko ɗiyata?
Gaban ne ya faɗi tunawa da tayi da abun da ya fito da ita daga gidan su ko giyar wake take sha baza ta faɗawa Alhaji Tahir gaskiyar labarin  ta ba, cikin kuka tace "Abba sunana Amatullahi ban san iyaye na ba, sun mutu tun ina ƙarama, wani kukan ta fashe da shi me matuƙar ban tausayi daga Alhaji Tahir har Kabiru sunyi matuƙar tausaya mata, Alhaji Tahir ne yace "to duk tsawan lokacin nam a ina kike rayuwa? zaro ido tayi dan ta mance zai iya tambayar ta haka cikin ƙarfin hali tace "Aikatau nake a wani gida, shine yaron gidan zai lalatamin rayuwa shine na gudo jiya har kuka bugeni, cike da tausayi Alhaji Tahir yace "Allah sarki me yasa wasu Mutanan duniyar ba Allah a zuciyar su ne meye ribarsa dan ya lalata miki rayuwa? Allah dai ya shiga tsakanin nagari da mugu, to Dota in har zaki yarda kuma zaki amince ni zan riƙeki a matsayin ɗiyata ke ma kuma ki ɗaukeni a matsayin mahaifi, in har kin yarda da ni kuma kin amince yanzu sai a miki komai na barin ƙasar"
   Cike da farinciki tace "na amince Abba na gode sosai Allah ya ƙara girma"

Kabiru ya jinjinawa baiwa irin ta Alhaji Tahir ba ya ƙyamar Mutum ko ya yake godiya shima ya tayata sannan ta sauƙo tana ɗingisa ƙafarta suka fito suka nufi gidan sa tayi mamaki sosai duk yadda gidan mahaifinta yake bai taka kwatan-kwatan wannam ba, anyi mata komai na barin ƙasa abun ka da masu gari da naira a hannu, washe gari da misalin ƙarfe 10:00am zasu ɗaga Dubai.
   Washegari da wuri suka shirya Kabiru ya sayo mata abaya me matuƙar kyau da takalmin sa tayi kyau sosai duk da ba kwalliya tayi ba, ƙarfe 10:00am suka ɗaga jirgin su ya lula sararin samaniya.
*Tofa! wannam Aure na Taufeeq da Nabeeha zai yiwu kuwa?*

*Me ye dalilin Amatullah na yiwa Alhaji Tahir ƙarya?*

*Shin ko Iyalan gidan Alhaji Tahir zasu karɓi Amatullah hannu biyu?*

_Ina jiran comment naku game da sharhin ku a wanga lamari_

'''Ayi hutun weekend lafiya sai mun haɗu Monday insha Allah'''✨🌹

_Share Fisabilillah_👏🏻

Vote
*ONE LOVE*💞🤞🏻
08132761212

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul 💋'''

_My fan's kuyi haƙuri da rashin jina kwana biyu hakan ya faru ne saka makon wasu dalilai, amma yanzu dai Alhmdllh ga ni na dawo za mu ɗaura daga in da muka tsaya fatan dai kun shirya bani daddaɗan comment? to a kafta!🤾🏻‍♀_

*Episode 15&16*

*...* Sun sauƙa Dubai lafiya Amatullah wani irin iska me daɗi da ƙamshi take shaƙa, sam sai taji iskar duniyar da ta baro da wanda take ciki sunsha bam² tuni motocin Alhaji Tahir sun iso Yaron sa Saif ne yazo ɗaukan su da mamaki yake kallon Amatullah da ta gaishe shi, sannam suka ranƙaya gida "hasbunallahu wani'imal wakin" gidan Alhaji Tahir anguwa ce guda me zaman kanta, gida ne me girma wanda ya amsa sunansa gida, tsayawa fasalta muku yadda gidan yake ma ɓata lokaci ne masu karatu ku ƙiyasta shi a mizanin fahimtar ku, parlon gidan suka nufa Alhaji Tahir yana gaba Amatullah tana bin sa a baya, su na shiga wasu ƴan mata wanda sa'annin Amatullah ne suka yiyo kan Alhaji Tahir cike da farincikin dawowar sa, suna zuwa suka faɗa jikinsa suna faɗin "sannu da dawowa Abba ya hanya?" "lafiya ƙalau my Ɗaughter's fatan dai na sameku lafiya?
"Lafiya lau Abba"
"To masha Allah, Allah ya muku albarka ya faɗa yana shafa kansu jerowa sukayi suka shigo falon, duk abunda suke Amatullah tana kallon su wani abu ne ya tsaya mata a rai sun burgeta sosai, hawaye tuni ya cika mata ido tunowa da tayi da mahaifinta mafi soyiwa a gareta, Abba ne yace "Raudah! Zarah! baku ga da baƙuwa nake ba, ya faɗa yana nuna musu Amatullah da ta rakuɓe a gefe, ya ƙara da faɗin "Daughter tashi ki zauna a sama mana ki daina zama a ƙasa nam gidan ku ne.
Tashi tayi ta zauna tace "na gode Abba"
Zarah ne ta kalleta cike da fara'a tace "sannunki da zuwa"
"Yauwa na gode"
Ta bata amsa a taƙaice, Raudah ne ta mata wani banzan kallo ta dauke kai ba tare da tace komai ba, Abba ya ganta sarai kansa ya girgiza ya juya wajen matansa da suke fitowa suna masa sannu da zuwa Hajiya Fatima itace uwar gida mutumiyar kirkice faran-faran take da mutane kowa nata ne yaranta uku Saif shine babba sai Habiba dake aure a London sai kuma Zarah da autarta Ruƙayya saɓanin Hajiya Balkisu bata da mutunci ko kaɗan ta tsani wani ya raɓe su tafi son komai daga ita sai ƴaƴanta, ko su Hajiya Fatima ta rasa yadda za tayi da su ne shiyasa ta bari har yanxu take zaune a gidan yaranta uku ita ma ita suka gado duk abunda suke cikin tarbiyarta ne Raudah sai kuma Shamsiyya
cike da farinciki suka iso parlon Hajiya Fatima ne ta kalli Amatullah cike da fara'a tace "Abbansu da baƙuwa kuka zo ashe? sannu da zuwa baƙuwa Zarah maza kuje ɗakin ku tayi wanka sai ta fito taci abinci.
Cike da girmamawa Amatullah ta gaidasu Hajiya Fatima ne kawai ta amsa saɓanin Hajiya Balkisu da ta mata banzan kallo kamar yadda ɗiyarta Raudah ta mata, Amatu ganin kamar Hajiya Balkisu bata ji gaisuwar bane yasa tace "Mama ina kwana?
Wani tsawa Hajiya Balkisu ta mata tace "ke dahalla dakata min ban san ko ke waye ba ki ƙirani da wata Mama kul ko da wasa kama kanki"
Zarah ne tazo ta kama hannunta tace "Sis tashi mu shiga ciki kiyi wanka"
"Tom" tace a taƙaice suka tafi
Hajiya Balkisu ne ta wurga mata wani harara tana faɗin "haka kawai ba a tsaya anji waye ita ba kuma daga ina ta fito ba har an fara janta a jiki a jawo mana masifa tsabar gwaninta tayiwa mutum yawa, ta faɗa tana wurgawa Hajiya Fatima harara, murmushi Hajiya Fatima tayi tace "ai hakan shine girmamawa kuma shine karamci, nasan dai duk abun da me gidana ya shigo dashi har muhallin iyalansa nasan ba ƙaramin muhimmanci ne da shi a gunsa kinga dole mace ta gari ta ɗauki abun da muhimmanci
Ke komai ma da ya fito daga wajen me gidana me muhimmanci na ɗaukesa, kuma a ko ina ana so ka girmama baƙonka saboda baƙonka annabi ah to!
Taɓe baki Hajiya Balkisu tayi tace "kya dai ji dashi a rage shishshigi dan Allah..."
Abba ne ya wurga mata wani kallo wanda yasa tasha jinin jikinta, Hajiya Fatima ne tayi gaba ya bita a baya domin ɗakinta yake yau, da tsaki Hajiya Balkisu ta rakasu ta kalli Raudah da ke zaune tana kallonsu dan haka mahaifiyarta ta koya mata duk abun da ake kar ta yarda ta bar wajen har sai taga ƙarshen abun.

'''Hmmm. Iyaye muna kuskure babba wlh akan tarbiyar yaran mu musamman ma mata, taya zaki koyawa ɗiyarki in manya suna magana ta tsaya tana sauraren duk wani maganar da kuke yi, kinsan hakan kuwa babban tallafawa yake wajen taɓarɓarewar tarbiyya, sam wannam ba tarbiya me kyau bane tun yaro yana ƙarami zaki saka masa ƙin abun a ransa sai kuna zaune in kuna magana kice tafi wasanki babu kyau in manya suna magana yaro yana zaune wajen, a haka za kiga yaro ya tashi da rashin son jin gulma, sannam wataran akwai maganar da za kuyi wanda yafi ƙarfin ƙwaƙwalwar wannam yaro amma yana zaune yana saurarenku kuma tuni zai gama haddacewa, in marar kyau ne shikenam kin gurɓace ƙwakwalwar Yarinyarki kuma a haka zata ta tafi har tsufanta, Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da yaran mu ta hanya me kyau.'''

    Murmushi Raudah tayi tace "wlh Momy kin min dai-dai da kika gaya mata baƙa na so ki haɗa mata da mari ma wlh, dariya Hajiya Balkisu tayi tace "ai a juri zuwa rafi watarana tulun sai ya fashe wlh, ita kuma waccar me zubin aljanun za muga me ya kawota gidan daga wata nahiya ta fito dan Alhaji ma ya iya kwashe-kwashe... Tun da suka shiga Zarah ta nuna mata toilet ta shiga tayi wanka ta fito

Please Login or Register in order to submit comment