Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya zaman aure da wani ɗa namiji ba har na iya masa biyayya ba, wlh ban jin zan iya yiwa wani biyayya bayan Abwaan, ke macece duk da ba ki san zafin rabuwa da miji ba amma za ki iya hasaso zafin sa, bayan kun gama shaƙuwa da mijinki kuna cikin rayuwar da babu kamarta kwatsam mutuwa tazo ta ɗaukesa, Allah kenan me yin yadda yaso kuma ya ga dama a kuma lokacin da ya so, na sani Yaa Sayyid ya na so na sai dai ba na so na aure sa na gagara masa biyayya wlh ni kai na bazan yafewa kai na ba... Kuka ta fashe da shi me ban tausayi Hudan ma kuka ta fara tare da rungume Nabeeha domin ta ji matuƙar tausayin ta, ta tabbata da ita ce a matsayin da Nabeeha take a yanzu tabbas za ta iya haukacewa tuburan domin rashin masoyi babu daɗi cikin kukan tace
"Kiyi haƙuri Nabeeha na san me kike ji kar ki damu in sha Allahu za ku zauna lafiya da Yaa Sayyid domin ke shaidace akan son da yake miki, kuma duk me sonka komai kayi bazai ga laifin ka ba don haka kar ki damu kiyi ta addu'a Allah ya ba ku zaman lafiya Yaa Taufeek kuma Allah ya jikansa da rahma."
Sweetie da tun ɗazu take tsaye domin ta zo shigowa dan ƙiran Nabeeha domin a fara mata gyara itama ta tarar da su suna yi kuka take riris domin ita ma a yau mutuwar ɗan nata ya dawo mata saboda jin kalaman Nabeeha rungumar Nabeeha tayi cikin kuka tace
"Kiyi haƙuri Ɗiyata haka Allah ya so kar ki bawa Papan ku kunya kiyiwa Yayanku biyayya kin mance akwai tsatson Taufeeƙ a duniya? To ki sa a ranki a ko da yaushe yana tare da ke ki kalli Taufeeƙ karami fa ba shi da maraba da Babanshi har miskilancin su ma shi har yana so ya zarce Babansan ma don haka addu'a ne kawai tsakanin ku kinji ɗiyar albarka.
Cikin dauriya da son kwantarwa Sweetie hankali ta ƙaƙalo murmushi tace
"In sha Allahu Sweetie zan yi ƙoƙarin hakan bazan taɓa ba ku kunya ba."
"Yauwa ƴar albarka ta maza shirya ki fito ga me gyara tazo da ke za ta fara domin za a dawo min da ke sabuwa dal!
Gaba ɗaya dariya suka yi na karfin hali daga ita har Sweetie don zuciyarsu cike take fal da ƙuna, daga haka ta fice wasu hawayen na zubo mata kitchen ta wuce taci kukan ta sannan ta fito, itama Nabeeha toilet ta shiga ta riski kuka kamar ranta zai fita ta rarrashi zuciyarta ta yi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga marar nauyi ta nufi fannin me gyaran aiko ba ɓata lokaci aka fara gyarata tun daga kan dilka da sauran gyara har tukunyar Ƙsaitacciyar Mace aka haɗo musu da sauran haɗin AISHA ALIYU GARKUWA me gigita ogogi da birkita musu ƙwakwale😉.
Washegari
Papa ya sanarwa Anty Sa'a tayi farin ciki sosai nan ta sanarwa Sayyid ji yayi kamar ya goyata dan daɗi fita yayi duk wani kuɗin jikinsa sama da dubu ɗari biyu sai da ya rabar da su sadaka tare da roƙonsa su taya shi da addu'a Allah ya biya masa bukatun sa, ya ƙira Nabeeha ya fi a ƙirga taki ta ɗauka kawai ya shiga jero mata message na farin ciki da kuma zallan soyayya ya san ko yaje baza ta taɓa fitowa ba dole ya haƙura ku yaje gidan ma ba ya neman ta sai dai yayi ta tura mata text nan ma ba ta mai do da amsa amma ko a jikinsa sai in yana son ganinta ne yasa Samha ta mata hoto da wayo ta turo masa su Little kuwa kullum suna wajen sa yanzu kam ma ya tafi da su gaba ɗaya wajin Momy, ko da Jawa'ad ya samu labari ba shiri ya dawo daga tafiyar da yayi ya nufi Papa cike da ƙunar zuciya yana zuwa ya zube idanunsa fal da hawaye ya kama hannun Papa yace

"Papa ka min rai ni mafi cancanta da na auri Nabeeha Papa ina matukar ƙaunar Nabeeha tun na yanzu ba Papa in aka min haka ba ai min adalci ba a wannan karon zan iya mutuwa wlh akan rashin ka taimaka min Papa... Ya fashe da wani matsanancin kuka, mamaki ruɗu ya cika Papa da Sweetie da ke gefe cikin kulawa Papa yace

"Jawa'ad sai dai kayi haƙuri domin lokaci ya gama ƙurewa ka ga Sayyid tun da yake son ta amma alkawarin da mukayi da mahaifinta yasa dole ya hakura amma kuma ga shi da Allah ya rubuta ka ga abu ya sauya don haka ka barma wannan maganar ga mata nan da yawa ka nemo kawai a haɗaku tare.

Kuka ya saka bilhaƙƙi da gaskiya yace

"Papa gaba ɗayansu na rigasu sonta tun muna ƙanana nake son ta kaga ni ya dace na aurenta Papa Sweetie ku taimaka min."

Gaba ɗaya mamaki ne ya kamasu jin furucinsa, Sweetie cike da tausayin ɗan nata tace

"Kana nufin ka jima kana sonta Jawa'ad shine baka taɓa faɗa ba? Yanzu ai ka ga illar riƙe abu a rai kenan, da yanzu ka sanar ai da tuni kai ne za ka maye gurbin Bayanka, amma yanzu kam babu abin da za a iya yi."

Cikin firgici yace

"Papa don Allah ayi wani abun don girman Allah na roƙeku.

"Kayi Hakuri yarona ban isa na tunkari Yaya da wannan maganar ba domin ko a farko ma mun so samun matsala, gashi a na biyun nan ma mun kusa, in ba wani ikon Allahn ba babu wani ɗan adam ɗin da ya isa ya dakatar da wannan auren haƙurin da Sweetie tace ka yi shi kawai za kayi Allah ubangiji ya baka wacce ta fita."

Jiki a sanyaye ya tashi ya fita daga ɗakin gaba ɗaya wani irin jiri yake ji ga wasu hawaye masu zafi da suke sintiri a fuskarsa part ɗin su yayi, yana zuwa ya haye gado ya kwanta ya fara riskar kuka tamkar ƙaramin yaro...
Kuka yayi son ransa Nazmar ba irin haƙurin da bai basa ba amma abun ya ci tura ganin haka kawai shi ma ya fara kuka sai da suka yi me isarsu sannan suka rarrashi juna, Nazmar yayi ta ba shi baki har ya samu nutsuwa.
Shirye-shirye na ta kan kama a kullum sai Sayyid yazo amma sam Nabeeha ba ta fitowa duk da ta haƙuri da auren ta amince za ta masa biyayya amma ba wai don tana son shi ba sai dan kawai ta bi umurnin Papa, sai dai a kullum safiya da maraici sai ya turo mata text kala-kala, yaranta kuma suna wajen sa saye-saye yake musu ba ɗan kaɗan ba a kullum sai aun fita yawo, haka rayuwa ta ci gaba da tafi duk wani gyara da za ayi wa Nabeeha an mata nan da nan ta dawo tamkar budurwa tayi kyau sannan ta ciki ma an sake matseta ta yi zam-zam, an fara shagalin biki amma ban da Nabeeha dan tace ita baza ta yi komai ba, su kam su Nazmar babu abun da ba su yi ba, domin me taka musu birki ya kwanta dama da yana nan ƙarƙari ayi walima mutuwa kenan Allah ya jiƙanka Abwan.
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya a yau ne dubban jama'a suka shaida auren Sayyid da amaryan sa Nabeeha, sannan Abdul-hakim da amaryarsa Huda, sai kuma Nazmar da amaryar sa Samha gaba ɗaya angwayen kana kallon su za ka san suna cikin tsananin farin ciki gaba ɗaya sun sha ado sai tashin ƙamsu suke.
A ɓangaren Nabeeha tun safe take riskar kuka har yanzu da aka sheda auren, yaranta ta runguma tana kuka kamar ranta zai fita, sai da tayi me isarta sannan, da yamma dangin Hudah suka zo ɗaukanta ta ci kuka na rabuwa da iyaye, haka ka Samha duk da ita a kusa da gida take amma sai da ta ci kuka sai kuma Nabeeha wanda yi tayi kamar za tayi kuka duk wani me imani a wajen nan dole ya koka mata, ita kan da tafiya sosai tsakaninta da gida, ko wacce an kaita gida na alfarma wanda tsayawa kwatanta tsarin gidan ma ɓata lokaci ne sai dai kuma gidan Nabeeha duk ha kere na su domin kuɗi Sayyid ya narkar ba kaɗan ba.
Bayan abokai sun gama raka angwaye ko wacce angonta ya nufeta, ba musu Yaa Sayyid ya umurci Nabeeha ta tashi su yi samma duk wani abun da yace ta yi, yi take ba tare da ta masa gardama ba a wannan daren suka raya sunna wannan Nabeeha ta ci kuka son ranta domin Sayyid bai yi mata da wasa ba, yo ba a taɓa gamuwa ba shekara da shekaru, wani irin kulawa yake bata wanda ba ta taɓa zaton za ta samu irinsa daga garesa ba, kulawa ce me cike da so da zallar ƙauna, a dole ita ma ta fara ba shi kulawar da ta dace sai dai duk wani motsi da za tayi Abwaan ɗinta yana tsaye ƙyam a zuciyarta.
Bayan shekara ɗaya
Zaune suke a falo cikin shiga na alfarma sai fidda fitinannan ƙamsu suke tana zaune akan cinyarsa tana zuba masa shagwaɓa shiko sai biyeta yake gata ɗauke da tulelen ciki haihuwa yau ko gobe ta ƙara kyau ta yi ƙiba ga fari da tayi, cike da shawaɓa tace
"Baby ni wlh goyo na ke so.
Ƙunshe dariyarsa yayi yace
"Yanzu tsakani da Allah da wannan tirtsetsen cikin taya zan iya goyonki kiyi haƙuri har sai kin haife min abuna sai na yi ta goyonki.
Cikin fushi tace
"Na san da Abwan ɗina yana nan da babu abun da zai hana shi goyo na."
Gaba ɗaya Sayyid ya ji ransa ya ɓaci bai san me yasa duk da ɗan uwan nasa ba ya raye amma yake jin kishinsa ba cikin ɓacin rai yace
"Ai sai ki bishi kije ya goyakin."
Daga haka ya sauƙeta a kansa ya nufi ɗakinsa duk yana jin zuciyarsa ba daɗi.
Tana zaune mamaki ya hanata ko motsi a tsawan zaman zu na shekara da aure kusan kullum sai ta masa zancen Abwaan amma bai taɓa nuna ɓacin ransa ba sai yau to meye hakan?
Tuni ita ma ta ɗauki zafi ta share sa ba ta bisa ba, ta na nan zaune ta ji sallamar su Huda daman sun sanar mata za su zo ba su jima da gama musu girki ita da Sayyid ba suka yi wanka suka zauna a falo zaman jiransu, cike da farin ciki ta tarbesu gaba ɗayansu da yaransu duk suna hannun mazajen su dan tare su ke dukkan su Mace suka haifa ɗiyar Hudah ana ce mata Ayrah ɗiyar Samha me sunan,Sweetie ana ce mata Yasmeen Nabeeha ne dama ba ta samu ciki da wuri ba, bayan sun gaisa ne ta kawo musu lemo sannan ta haura domin ƙiran Sayyid da sallama ta shiga ɗakin yana zaune yana latsa system ɗin sa, a hankali ta yi sallama ta shiga itama fuskanta a haɗe kamar yadda nasa yake tace
"Su Samha sun zo kuma tare suke da mazajen su."
Bai ko kalli inda take ba ya miƙe ya fita hakan yasa ta biyo bayanshi a tare suka sauƙo a wannan lokacin fuskarsa a sake bayan sun gaisa ne kuma ya musu iso zuwa dining, da taimakon sa suka zuba wa kowa bayan sun kammala ne suka dawo falo aka fara hira duk da cikin su babu wanda yake yi da ɗan uwansa hasalima duk wanda ya haɗa ido da ɗan uwansa sai dai su gallawa juna harara.
Suna haka har lokacin sallah yayi a nan mazan suka tafi sallah suka bar su, nan Hudah take tambayarta abun da ke faruwa dan ta fahimci akwai wani abu, Nabeeha ba ta ɓoye mata komai ba.
Nan Hudah ta yi ta mata faɗa akan babu kyau tana gidan wani kuma tana masa hiran tsohon mijinta duk da ba ya raya bai ma kamata Yaa Sayyid ransa ya ɓaci ba amma tun da ya nuna miki baya so ki samesa ki ba shi haƙuri nan tayi ta masa nasiha har ta fahimci itace da laifi, har dare suka kai sannan mazajensu suka zo suka ɗaukesu, har wannan lokacin ba su yi magana da Sayyid ba gaba ɗaya sai ta ji babu daɗi hakan yasa tq nufi ɗakinsa, yana zaune tana zuwa ta faɗa cikinsa ta saki kuka da sauri ya tarota yana faɗin
"Lafiya me ya faru?
Cikin kuka tace
"To bakai ne ba ne kake fushi da ni don Allah ka yi hakuri bazan kuma ba."
"Babu komai baby na ni kaina sai yanzu na ga rashin dacewar abun da nayi in sha Allahu bazan kuma ba."
Cikin sauri ta haɗe bakin su guri ɗaya a nan salon labari ya sauya aka shiga raya sunnar ma'aiki, bayan sun kammala ne ta ji mararta yana dam damƙewa, nan da nan abu ya tashi gadan-gadan ba shiri suka tafi asibiti suna zuwa kuwa akace haihuwa ne suna shiga da ita tana hawa gadon haihuwa kamar dama jira yake ta santalo Yaronta santalele murna wajen Sayyid ba a cewa komai tuni ya ƙiran dangi da abokan arziki babu wani ɓata lokaci tana hutawa aka sallame su kafin su isa gida ma har gida ya cika da ƴan uwa kowa murna kamar yau ne aka fara samun ƙaruwa a cikin danginsu, su Samha wanda suka zo jiya sai mamaki suke yi duk da ba a mamaki da,lamarin ubangiji, Sweetie ne ta zauna wa me jego tana kula da ita ranar suna Yaro ya ci sunan Papa an yi shagali anci uwar sabada kudi shi kansa sai da yayi kuka tsabar ɓarnarsa da ake yi,yo akwai sun tara.
A gurguje
Bayan Shekara ashirin
A wannan tsawon shekarun abubuwa da dama sun faru da me daɗi da akasin haka ciki kuwa har da rasuwar Jawa'ad wanda ya mutu da tsananin ciwon zuciya ahalin sun shiga ƙunci da baƙin ciki a karo na biyu, gaba ɗaya mutum uku ne suka san mafarin ciwon sa domin garin ya bari gaba ɗaya a chan yayi ta jinyar sa ba tare da sanin kowa ba, sai gaf da zai rasu ya dawo gida, ganin ramar da yayi babu irin tuhumar da su Papa ba su masa ba na ramar da yayi amma yaƙi faɗa yace kawai kewarsu ne, satin sa biyu da dawowa yace ga garin ku, sai da Papa yayi bincike ya gano dalilin mutuwarsa, kuma yasan duk akan Nabeeha ne, hakan Nazmar ma da Sweetie dole yasa suka har abun a zuciyarsu domin babu amfanin faɗar su, suma lokaci su ke jira domin shekarun sun ja.
Nabeeha yanzu an zama manyan mata ta sama cikakkiyar likita ta fannin ciwon kansa dan sai da tayi ƙoƙari ta gano maganin wannan ciwon dan tayi alkawarin babu me ƙara rasa wani nasa ta wannan ciwon yanzu yaranta bakwai in harda du Little, zaune suke ita da yaranta da kuma mijinta abun alfahari a gareta rayuwa suke cike da soyayya ba ta taɓa tsammani za ta samu wanda zai sota fiye da Abwan ɗinta ba sai gashi nam Yaa Sayyid yana mata son da Abwan be mata irinshi ba a kullum ƙara godewa Allah ta ke akan bata Sayyid da yayi a lokacin da ta rasa bango kuma majin gina a gareta,sai yanzu ta tabbatar da duk wani bawa baya fidda rai daga rahamar Allah, sai dai kuma har yanzu in ta tuna Abwan tana kuka sosai domin sunyi rayuwar da baza ta taɓa mancewa da ita ba.
Zaune suke gaba ɗayansu a falo sallama ta ji wanda ya kusa gigita mata lissafi da hargitsa mata ƙwaƙwalwa da sauri ta dubi hanyar shigowa Abwan take gani yana sakar mata murmushi yana nufowa inda take jikinta ne ya fara rawa hannu ta ɗaga tana nunashi tana faɗin
"Taufeeƙ! Taufeeƙ!! Da sauri Alhaji Sayyid ya kalli inda take nunawa, murmushi yayi tare da kamota dan dama yasan za ayi haka watarana domin yasan in dai suka yi ido huɗu sai hakan ta faru, a jikinsa ya sata yana faɗin kwantar da hankalinki wannan ba Abwaan ɗinki ba ne yaronki ne Taufeeƙ da ya dawo daga makaranta tsawon shekara goma sha biyar, a jiyar zuciya ta sauƙe me ƙarfi tare da rungumar sa ta sami wani marayan kuka da sauri Junior ya ɗagota tare da goge mata hawaye yace
"Kiyi haƙuri Momma don Allah."
Da hanzari ta ɗago ƙara jin Muryan Abwan ɗinta ya dakar mata dodon kunne, ba shi da wata maraba da Abwaan marabarsu ɗaya Abwan ya fi shi shekaru.
Murmushi ta yi ta kara rungumesa cike da farin ciki dan ta tabbatar ba Abwan ɗinta ba ne ya dawo mata.
Little tana gefe ta haɗe girar sama da ta ƙasa cike da sallar shagwaba tace
"Wato abun ma wariya ce ni an mai da ni kamar gantalalliya babu wanda ya kulani ba re a rungume ni wayyo ni Allah!"
Ta faɗa tana sake kukan shagwaɓa da sauri suka taho inda suke har sauran yaran ba ki a haɗe suke faɗin
"Wa ya isa ya share uwar masu gidan gaba ɗaya."
Rungumar juna sukayi gaba ɗaya tare da sakin dariya.
A ɓangaren su Amatullah ma rayuwar su suke cike da farin ciki da jin daɗi yanzu yaranta biyar rus suna zaune lafiya sai dai kawai mu ce Alhamdulillah domin rayuwa ta yi kyau!


*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!*

_Allah na gode maka daka nuna min ƙarshen wannan littafin nawa lfy._
_Ya Allah ka gafarta min kurakurai na. Ka jikaina kayi min gafara, abin mai kyau dake ciki Allah ya haɗamu a mizanin._

```dα wαnda nα ѕαni dα wαnda вαn ѕαni вα mαcє kσ nαmiji вαввα dα чαrσ in hαr nα muku laifi ku чαfєmín don Allah```😢

_Sai mun hαdu α ѕαвσn Littafi na mai хuwα amma kafin nan zan fara dawo muku da litattafan da na rubuta domin na gyara su._🫡

_Ina matukar godiya da haƙuri da kuka yi kuna bibiyan wannan littafin ina matukar ƙaunarki masoyana._🥰💞

Vote
Comment
Share
Taufeeƙ

*ONE LOVE*💞🤞🏻
08132761212

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment