Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai jin tausayin ki ba za ki mutu a walaƙance hahahahahaha!
Ya ƙarishe maganar da sakin wata wawiyar dariya.
A ɗimauce tace
"Dan Allah Boka Nardamu ka min rai ka…
Cike da ɓacin rai ba tare da ya bari ta ƙarisa ba ya daka mata tsawa 
"Dakata! Balkisu da kinsan da Allah kika zo wajen mu? Wlh kika sake ƙira zan mance wannan girman naki da kuma alheri da kika mana na sauya miki halitta kin jini dai ko?
Da sauri tace
"Tuba nake Boka Nardamu hakan bazai sake faruwa amma dai a duba lamarin nan wlh ko nawa zan biya a dakatar da wannan aikin saboda ba ni da wata hanya.
Ta faɗa cike da nadama maras misaltuwa sai yanzu take ganin aibun abun da ta aikata
Dariya ya kuma kecewa da shi wanda ya ƙarawa fuskarsa wata irin muni fuskar nan taɓ ƙazanta yace
"Hajiya kenan kawai tashi kije mu za mu san akan wa za muyi aikin sannan duk wani abun da ya sameki to mu ne dan bama barin aiki ya tafi a banza sai dai mu mayar kan wacce ta samu aikin."
Cikin kuka tace 
"A'a Boka Nardamu ka tausaya min yauwa a maida komai kan kishiyata Fatima in tayi kaɗan ma a haɗa da yaranta kawai."
Ta faɗa cike da farin ciki dan sai yanzu wannan tunanin yazo mata
Wata jakar dariya Boka Nardamu yayi yace
"Ashe dai kina ganewa kin kuma ce ci kanki dan haka ga wannan kije ki fuskance ta ki watsa mata shi a fuska daga lokacin za ta fita  fita ta har'abada za ta tafi wata duniyar da babu wani mai tausayinta a haka har ta mutu cikin ƙasƙanci!
Cike da farin ciki ba tare da nadamar komai ko tausaya ba tace 
"Yauwa Boka Nadarma na gode sosai Kamkamba ya taimake ka.
Kar ɓar laidan da ya bata tayi ta fice cike da farin ciki da kuma samun nasara sai da tayi tafiya a jejin sosai sannan ta iso inda motarta yake shiga tayi ta kama hanya cike farin ciki maras misaltuwa(Niko nace anya Momy tana so ta gama da duniya lafiya kuwa? Allah ya kiyashe mu aikata aikin danasani) gudu kawai take shararawa so take kafin magriba tayi ta isa gida ta aikata abun da Boka Nardamu ya sanya ta tayi ta bar gidan ba tare da kowa ya ganta ba daga baya kuma sai ta koma kan Alhaji ya maidata ɗakinta su ci gaba da rayuwa da ƴaranta ba tare da ta sani ba kawai taga wata tirela ta nufota gadan gadan cike da tsoro ta fara ƙoƙarin ƙauce masa amma ina kamar ƙara fuskantar sa take yi shi kansa mai doguwar so yake yaga ya kauce mata amma ina kamar ƙara turasa yaji ake ji kake ƙuuuuuu!
Wannan babbar motar tabi ta kan motar Momy tuni motar tayi raga ita kanta Momy tayi fisis jama'a salati kawai suke cikin ikon Allah wannan babbar motar babu abun da ya sameta chan ya samu yayi parking ya sauƙo cike da al'ajabi babu wanda ya ɗaura masa laifi domin yawanci a idanun mutanan wajen akai komai kawai Allah ne ya aiko amma dukkansu sun so su kaucewa ɗan uwansu amma abun yaci tura da ƙyar aka samu aka iya ciro Momy da ko motsi ba tayi ko ka santa zai yi wuya mutum ya iya ganeta in ba dai an faɗa masa ita ce ba domin halittarta yayi mugun sauyawa tuni motar asibiti tazo an ɗauketa duk da yawanci turawa ne amma sunyi matuƙar tausaya mata ana kaita aka fara bata taimakon gaggawa sun shafe awanni a kanta domin ba ƙaramin ciwo taji ba duk wani mahaɗar ƙashi na jikinta ya karye hatta bakinta a karkace yake a yanzu sun yi nasarar dai-dai ta komai na jikin ta ƙarfuna ne ratata a jikinta sai dai kuma wani abun mamaki babu abun da ta samu ƙwaƙwalwarta lafiya lau take su kan su likitoci sun sha mamaki duk da ba a mamaki da ikon Allah amma yanayin yadda take baza ka tsammaci akwai wani abu a jikinta wanda yake da lafiya ba musamman ma ƙwaƙwalwarta sai gashi shi da suke tunanin zai samu matsala ba abun da ya samu sai ƙarfe 2:am suka fito daga kanta suka ɗauketa a nan zuwa I.C.U ɗakin ita kaɗai ne tana nan kwance kamar matacciya babu alamar rai a tattare da ita, sai a sannan suka fara tunanin ina zasu samu ƴan uwanta duk da asibitin ba a zaman jinya amma kuma ya sama dole ƴan uwanta su sani duk da wanda sukayi karo yq bada wasu ƴan kuɗi amma yadda taken nan kuɗin sunyi kaɗan wajen yi mata magani hakan yasa Dr ya ƙira ASP ko an samu wata shaida a cikin motar ta cikin sa'a kuwa ya sanar masa da sun samu wayarta amma tayi kwatsa² sai dai sun cire sim ɗin sun sa a wata waya sun ga number mijinta da kuma na Ƴaranta sai dai har kawo lokacin basu ƙira ba sai zuwa safiya gudun kar ya ɗaga musu hankali cikin dare.
Hamdala Dr. Yayi bayan ya gama sauraren ASP sannan yace
"Ok sai ka sanar musu halin da take ciki in kunyi wayar tana cikin mawuyacin hali sosai ba lallai ta kai labari ba."
"Subhanallahi! ai ni dama tun da na kalli yadda tayi nasan sai a hankali, Allah ubangiji ya bata lafiya, insha Allah da misalin karfe 6 zan ƙira mijinta na shaida masa."
Daga haka sukayi sallama.
A wannan rana gaba ɗaya ahalin gidan Alhaji Tahir Abdulƙadir Maina cike suke da matuƙar farin ciki a yau Alhaji Tahir ji yake kamar bazai mutu ba i dan ya tuna da Amatullah ɗiyar gudan jinin sa ne sai yaji ƙaunarta na ƙara ninkuwa masa a zuciyarsa, kowa ka gani cikin farin ciki har su Raudah sai dai ganin dare yayi ne hankalinta ya ɗan tashi musamman da ta ƙira wayar Momy a kashe tayi matuƙar mamaki domin ita dai tun da ta fara riƙe waya bata taɓa kiran Momy taji a kashe ba sai yau Yayar mahaifiyarta ta ƙira dake nan Dubai wacce tasan baza ta wuce tana gidan ta ba amma cikin rashin sa'a ko da ta ƙira ta shaida mata bata zo ba a haka ya kwana kamar marar lafiya domin tasan ba dai lafiya ba kam Amatullah ma sai da ta ƙira amma duk ɗaya Shamsiyya sai da tayi ƙwalla.
Washe gari kamar yadda ASP ya faɗa ƙarfe 6 ya dokawa Abba ƙira a lokacin ya fito daga toilet yaji wayarsa na ƙara da sallama ya ɗaga Asp ji da yayi an ɗaga ne yasa ya amsa sallama cikin yaren nasara ya ƙara da cewa
"Alhaji sunana Asp Habib Ibrahim a jiya da magriba ne iyalinka tayi hatsari in da babbar mota ta bugeta yanzu haka tana asibiti ana bata taimakon gaggawa na samu number ne a cikin sim ɗin matar ka."
Tun da ya fara maganar Abba yake salati har sai da ya dasa aya yasan ba kowa bace illa Balkisu dan Fatuma babu inda take fita sai ta kama dole da kamar zai kashe wayarsa da ya tuna da wacece Balkisu sai dai kuma yaji tausayinta dan ko ba komai akwai ƴaƴa a tsakanin su hakan yasa yace
"Na gode sosai Asp don Allah ka turomin da address ɗin asibitin."
"Ok."
Yana kashe wayar ba jimawa yaga saƙon sa ko da ya duba yayi mamakin abun da yakai Balki wannan waje domin da tazara sosai a tsakaninsu taɓe baki yayi domin ba buƙatar ya sani domin yanzu babu igiyarsa akanta.
Ammy ya ƙira ya sanar da ita tare da faɗin ta shirya yanzu za suje kar ta sanarwa da kowa har sai sunje sun ga yanayin jikin nata.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun!
Allahuma ajirni fi musibati wa'akilni khairan minha!!
Shi ne abun da Ammy take ta maimaitawa tun da Abba ya fara magana yana katsewa taji wani hawaye na tausayi Momy ya kamata duk da bata san a wani hali take ba amma har cikin zuciyarta take jin ƙaunar Momy, Habiba dake zaune a ɗakin ganin Ammynsu na kuka ne ya tashi hankalinta da sauri ta iso gareta cike da tsantar so da kulawa na tsakanin uwa da ƴarta tace
"Subhanallahi! Ammyn mu lafiya kike kuka wa ya rasu?
Kukanta ne taji ya ƙaru tace
"Habiba Momyn ku ne tayi hatsari yanzu Abban ku ya ƙirani akan na shirya za muje asibitin."
Habiba ma tausayi Momy ta bata ai abun ya mata yawa ga sakin da Abba ya mata ga kuma haɗari cikin tausayi wanda suka gado shi wajen Ammy da kuma Abba tace
"Allah sarki Momy Allah ya bata lafiya don Allah Ammy nima zan je na ganta pls."
"Abban ku yace kar na faɗawa kowa har sai mun je mun duba yana yin jikin nata, amma ki fito in ya yarda to in bai amince ba kuma sai kiyi haƙuri."
Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin da sauri Habiba ta biyo bayanta tana faɗin
"Ai bazai ce ma a'a ba domin nifa Hajiya Inna ce gudu."
Duk da halin da Ammy take na jimami sai da ta murmusa ta ƙofar baya suka bi domin gidan cike yake da al'umma tuni Abba yana mota shi da Saif ko da yaga Habiba bai ce mata komai ba Saif ne yake jan motar sai kuma jami'an tsaron Abba mota biyu gudu suke sharara tafiyan awa guda sukayi duk da uban gudun da suke suna shiga likita ya musu jagora gaba ɗaya fuskarta tayi matuƙar sauyawa ta kumbura suntum kaf ɗakin Abba ne kawai bai koka ba amma yaji matuƙar tausayi Habiba har gunjin kuka take ganin haka ne yasa Dr. fito da su waje kana Abba ya same shi da maganar nan Dr. Ya zaiyane masa duk matsalarta kuɗi masu yawa ya turawa Dr. Dan ba lalle ya sake dawowa ba suna tsaye kawai suka ga Raudah ta shigo da gudu tana kuka da sauri Saif dake tsaye ya riƙeta tare da sata a jikinsa yana bubbuga bayanta alamun rarrashi gaba ɗaya da ido suke binta domin sunyi mamakin ganin ta Abba ne yace
"Raudah wa ya faɗa miki muna nan?
Cikin kuka tace
"Abba jiya na kasa bacci saboda ban samu layin Momy ba hakan yasa da safen nan na sake ƙira shine wani asp ya ɗaga yake shaida min ai hatsari tayi shine ya gayamin inda take naje zan sanar da kai akace kun fita shine na yawo motar haya ya jikin Momyn tawa?
Ta ƙarishe cikin kuka.
Gaba ɗaya babu wanda ya iya bata amsa ganin haka ne jikinta ya ƙarayin sanyi ta kuma fashewa da wani matsanincin kuka cike da tausayi Saif yace
"Jikin Momy da sauƙi sosai ki bar kuka."
"Ya Saif ina so na ga Momy na."
Ta faɗa wasu hawayen na zubowa.
"In har kina so ki ganta sai kin dai na kuka kuma kin min alƙawari in har muka je kika ganta baza kiyi kuka ba kinyi?
Da sauri ta ɗaga kanta alamar eh tare da goge hawayen ta.
Hannunta ya kama suka nufi ɗakin da Momy take cike da tsoro da kuma fargaba take tafiyar har suka iso a hankali ta sauƙe idanunta akan Momy wani irin ƙara ta saki ta faɗi ƙasa sumammiya.
Da sauri ya ɗagota ya fito da ita dai-dai lokacin Dr. Ya fito jin ƙara yasa ya fito ganin su ne yasa cikin ɓacin dai yace
"Haba ya za ki shiga da ita marar lafiyar mu fa za ta iya samun matsala sannan duk wanda ya santa in ba dai yana da dauriya ba bazai jurar ganinta haka ba musamman ma ƴaƴanta."

Duk cikin harshen nasara yake maganar

A hankali Saif yace

"Na zaɓi na nuna mata ita ne saboda ta samu nutsuwa ɗaya in har ba a nuna mata ita ba za tafi shiga damuwa wanda har gwara a nuna mata ita."

Cikin gaskata maganar shi Dr. yace

"Eh haka ne kam ka fini gaskiya ta wannan fanni ku shiga bari na turo a dubata."

Gaba ɗaya suka shiga har yanzu dai Ammy da Habiba basu bari zubar da hawayen tausayin Momy ba Ammy ji tayi ta karaya da rayuwar duniyar.

Suna shiga aka zo aka ɗaura mata ruwa dan tuni jikinta ya ɗauki zafi sai wajen ƙarfe 10 ta farka a hankali ta fara buɗe idonta ward ɗin ta fara bi da kallo tana so ta gaskata abun da ta gani ɗazu ganin bata gani ba ne yasa ta sauƙe nannauyan ajiyar zuciya cike da kulawa Abba yace

"Dotar ya jikin naki?

"Da sauƙi Abba mai ya samu Momy na Allah dai yasa ba gaskiya ba ne abun da na gani ɗazu Abba."

Rungumarta Abba yayi yace

"Dotar kiyi haƙuri ba kuka za kiyi ba addu'a za ki ta yiwa Momyn ki Allah ya bata lafiya kinji?

Wani kuka ta fashe da shi tare da ƙara rungume Abba tana faɗin

"Abba Momy ne fa gaba ɗaya kamanninta ya sauya Abba kamar 'fa ba ita ba innalillahi wa'inna ilaihi rajioun!..

Bata ita ƙarawa ba Dr. Ya shigo da sauri yana faɗin Momy ta farka...

*My lvly fan's kuyi ta haƙuri da ni pls sannu sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗi ba aje ba ina sonku lodi lodi.*🥰

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212.


*TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

*AL,BISHIRINKU, MA'AURANTA,GA NESA TAZO KUSA SHAHARARRIYA KUMA ƘASAITACCIYA, GARKUWAR MARUBUTA BA IYA GARKUWAR MARUBUTA BACE  HADDA MA'AURANTA* _'Yan uwa Mata shin kuna buƙatar kasancewa Ƙasaitattun mata acikin gidajen Auranku?Nasan amsar Eh"Ne.Ga mai buƙatar sayan kayyakin da zan lissafo ga number ta da zakuyi min mgn ta whatsApp domin samun cikakken ƙarin bayani dan gane da duk abubuwan da zan lissafo.09097853276
YAR UWA, ƘANWA, ƘAWA, AUNTY, MANYAN MATA, AMAREN DA ZA'A AURAR BUDURWA KO BAZAWARA, MAI JEGO, UWARGIDA. GA DAMA TA SAMU, Gyara aurenki ta hanyar samawa mijinki cikekkiyar gamsuwa da nitsuwa da ni'imantaccen ni'imarki a shimfiɗar aurenku wanda zesa mijinki ƙauracewa duk kan mata su zamo tamkar 'yan uwansa maza agaban idanunsa.Kasance da tsarabar da,
AYSHA ALIYU GARKUWA, wato GARKUWAR MARUBUTA har ma da ma Aurata,tazo muku da abubuwa na musamman, na kayyakin gyara Auranki dana ƙamshi.
Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu._
*YAR UWA shi ƙamshi Rahma ne yana samar da salama da nitsuwa a tsakanin ma'auranta tare da sanya shaƙuwa me ƙarfi atsakaninku da mazajenku*
Inada Kullacar sirri mai sassayan ƙamshi da janye hankalin mai gida, kana Akwai Baƙar Shu'umar humra mai daɗin ƙamshi, tare kuma da Turaren Al'ajabu na tsuguno oga zai kai hancinsa duk inda yake muradi a jikinkin cikin salama sabida daddaɗan ƙamshin jikinki.
Ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya, akwai haɗin step by step, dai-dai da aljihunki. Shiyasa nake zubasu a manyan da ƙananan robobi masu roggomin farashi. Sayan na gari maida kuɗi gida, duk state da kike kayana zaije gareki lfy lau, ta mota, kana duk ƙasar da kike in dai zaki iya kayanki zaizo gareki ta *DHL ko GIG.* In Sha Allah.
Ga masu buƙata ga number da zakuyi min mgn ta whatsApp 09097853276. Dan Allah ƴar uwa in dai kin san baki shirya sayaba kadama kiyi min mgn mu ɓatawa juna lokacin, akwai set ɗin hawa hawane ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙaramin haɗina,  sai ɗan autan 5k bani da kayan ƙasa da 5k kuma.
Idan kin shirya ga account no 0005388578 Jaiz Bank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276.

_Sayan na gari maida kuɗi gida na tabbata ba zuku taɓa danasanin sayen wannan haɗi ba, sai kunzo_🤝🏻😘😘

                         By
      *GARKUWAR MA'AURATA*

*Episode 65&66*
…Ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali ya nisa yace
"Ayya Sweetie dan Allah kimin alfarma a barni da matata a nan wlh zan kula da ita yadda ya dace kuma kullum zan na kawo miki ita ta na wuni sai dare nazo na ɗauketa dan Allah kiji tausayin first love ɗinki"
Ya faɗa cike da wani irin salo na ban tausayi ya tsuke fuskar nan tasa kamar yana gabanta daga chan Sweetie jin yadda yake maganar ne yaso bata dariya dan tasan halin yaron ta sarai cike da kulawa tace
"To shikenan amma pls kana kulawa da ita kasan mai ciki tana buƙatar kulawa ta musamman yanzu a sabon gidan ka na nan Kaduna kuke kenan?
Da sauri ya furta "eh"
"To ba sai ka kawota kullum ba kana kawo ta dai du sa'i da lokaci tunda muna gari ɗaya gobe zan sa su Samha su kawo mata abun maƙulashen ta da ƴan kayayyakin da za ta iya buƙata Allah ya rabasu lafiya.
Cike da matuƙar farin ciki yace
"Amin ya rabbil izzati"
Ji yake yafi kowa more rayuwa tun da ya samu kamar Sweetie da kuma Papa a duniya ga kuma ƙarin farin ciki na musamman da Allah ya mallaka masa Nabeeha a matsayin abokiyar rayuwarsa sallama sukayi da Sweetie ya sake rungume Nabeeha a jikinsa wacce ta jima da bacci kyawawan idonsa ya zuba mata haka kawai a ƴan kwanakin nan yake jin matsanancin faɗuwar gaba wanda shi kansa bai san ta mecece ba yanzu ma hakan yaji da sauri ya dafe saitin zuciyarsa yana karanto addu'ar neman tsari a hankali ya fara jin zuciyarsa tana dawowa dai-dai bakinsa ya zura a ɗan ƙaramin bakinta wanda ta turo aiko yana sakawa tayi caraf ta cafke ta fara masa wani irin tsotsa kamar ta samu sweet a hankali ya sanya tattausan hannunsa a kan breast ɗinta ya musu wani irin shafa a tare suka ji wani irin zut tuni Abwaan ɗinsa ta fara haniniyar neman ɗauki wani irin miƙa Nabeeha tayi tare da ƙara shigewa jikinsa, bakinsa ya sanya a gefen wuyanta ya fidda tattausan harshensa me fidda wani irin ɗumi da sassanyan ƙamshi a wuyanta yana wasa da shi dariya ta fara ƙyalƙyalwa domin ji tayi kamar ana mata cakulkuli a wajen cikin wani irin murya yace
_"A lokacin da na ga hoton kyakkyawar surarki na kan yi murmushi ko da ina cikin damuwa, na kan faɗa cikin tinanin kyawawan idanuwanki da tattausan murmushinki. Ya kan gusar da hankalina daga sauraren komai da tinanin komai sai naki, ya kuma iza wutar begenki a cikin zuciyata, a karo na barka tai zan ƙara baki hakuri tare kuma da gode miki domin a da ban ɗauki mace wata aba ba na ɗauki mace kawai a kawo ta girka a cini ban ɗauki mace wata duniya ce ta farin ciki ba sai a yanzu da kika nuna min hakan ina matuƙar ƙaunarki Baby na Allah ubangiji ya sauƙe min ke lafiya._
Ya ƙarashe maganar yana sumbatar cikin ta.
Cike da farin ciki maras misaltuwa tare da shagwaɓarta tace
_"Abwaan! da za a raba kaina gida biyu a taradda kwakwalwata na san babu abin da za a tarar a ciki sai tarin tunaninka. Da za a buɗe kirjina a taradda zuciyata na san babu komai a ciki sai ajiyarka. Da za a tsaga fatar jikina jini ya fita na san tabbas sai an ga naka. Mun zama ɗaya, kuma ina fatan mu kasance a wuri ɗaya na har abada."_
Gaba ɗaya wani irin farin ciki suke ciki maras misaltuwa musayar kalamai suka farayi a tsakanin su masu matuƙar sanyaya zuciya ba su ankare ba gaba ɗaya dare yayi sosai yunwa ce tasa Nabeeha duba lokaci zaro ido tayi tace
"Abwaan ƙare ɗaya har da ƴan mintina ba yanzu."
Murmushi yayi yace
"Soyayya ce ta sa har muka kai wannan lokacin yanzu zauna na ɗuma ma miki abincin sai kici muje mu kwanta ok."
Shagwaɓa fuska tayi tace
"Ni ba sai ka ɗumama ba zanci a haka."
"Ok zauna to na baki zama tayi a kan cinyarsa a hankali ya fara bata har sai da ta ƙoshi tasha ruwa ya ɗagata kamar Baby bai sauƙe ta a ko ina ba sai a rafkeken  bed wanda yake mallakin sa rage kayan jikinsa yayi ya kashe musu wuta sannan ya kunna dum! light ya jawota jikinsa tare da musu addu'a ya shafa har kan cikinta babu jimawa bacci mai daɗi ya ɗauke su.
Washe gari da wuri ta tashi ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast mai rai da motsi ta gyara ko ina ta kunna turare sannan ta nufi ɗakinta bathroom ta shiga tayi wanka ta fito ta shafa lotion simple makeup tayi falazo ta sanya wanda yayi matuƙar amsar jikinta ta feshe jikinta da sanyayyan turarenta da ɗan sauri take saboda yunwar da take ji, ji tayi kamar ana kallonta a hankali ta juyo ta kalli hanyar ƙofa aiko karaf idanunsu suka haɗe da na juna tsaya yake cikin shigar ƙananan kaya yayi matuƙar kyau na bam mamaki sai tashin ƙamshi yake ya zuba mata idanunansa ko ƙyaftawa baya yi, shagwaɓe fuska tayi tace
"Uhum! shine za ka tashi ka shirya kan ka bayan sauri nake nazo na tadaka na shirya abuna."
Murmushi ya sakar mata wanda sai da dimple ɗinsa ya lusa a hankali ya tako izuwa gareta ya kwaikwayi yadda tayi maganar yace
"Amin afuwa Baby na bazan ƙara ba ok."
Baki ta kuma turowa ganin haka yasa ya lakuce mata hanci yace
"Oya muje dan nasan saurin nan da kike yunwa kike ji."
A tare suka fito rungume da juna gwanin sha'awa a nan falon suka baje dan anan ta haɗa musu komai shi ya zuba ya fara bata a baki sai da ya tabbtar da ta ƙoshi sannan itama ta fara bashi cike da ƙaunar juna suke komai a tare suka tattare gurin bayan sun gama suka ɗauraye kwanukan tana wankewa yana ɗaurayewa sannan yazo ya zaunar da ita akan kujera ya ɗauko mata atileva freezer da zuma wanda sukayi sanyi sosai a gabanta ya sumbaci kumatunta ya nufi hanyar fita yana faɗi
"Bari naje gida Baby bazan jima ba dan dawo ok."
Ji tayi gaba ɗaya kamar kar ya tafi babu yadda ta iya ta bishi da addu'an Allah ya kiyaye hanya.
Da amin ya amfa ya fice cike da farin ciki maras misaltuwa.
A hankali ta fara cin atilen in ta ɗauko ɗaya sai ta tsomashi cikin zuma ta cire ta kai baki sai ta lumahe ido saboda daɗin da take ji.

Kwanaki nata shuɗewa abubuwa da dama sun faruwa tuni an kammala ginin wannan ƙauye gini aka musu wanda babu ha'inci domin dai Minister Taufeeƙ ya sake bakin aljuhu ba ƴan ƙauyen ba duk wani talaka da mai kuɗi sai da ya jinjinawa namijin ƙoƙarin da Taufeeƙ yayi domin kaf ƴan siyarmu na yanzu da wuya a samu irin sa haka sauran ƙauyukan duk abun da ya faɗa ya cika kama daga rijiyoyin ɓrutsatsai asibiti makarantu duk yayi babu abun da kake ci kama daga gidan rediyo talabijin jaridu abun ta Minister Taufeeƙ yayi kawai ake da sanya masa albarka a ƙanƙanin lokaci ya sake ƙaurin suna babu wanda ba san da shi ba ko bai sanshi ba yasan labarinsa a faɗin nageria har ma da sauran ƙasashen ƙetare, hakan sam ba wai yayiwa Taufeeƙ daɗi bane dan a duniya ya tsani yayi abu ayi ta yayatawa shi dai kawai yafi so in yayi abu a ayi shiru ko za a tambaya ace dai kawai wani ne yayi,ba sai an ambaci sunansa ba amma P.A n sa ne yake komai in har zasu wani wajen to zai sanarwa abokansa ƴan jarida kafin ma suje ƴan jarida sun isa har sun fara ɗaukar rahota (ƴan jarida kunnan al'umma🤣) wani irin rayuwa suke da Nabeeha cike da tsantsar soyayya kulawa tausayi ladabi da kuma biyayya muddin ka gansu sai sunyi matuƙar baka sha'awa tsaftatacciyar rayuwa suke cike da ƙaunar juna a ko ina nunawa junansu kulawa suke a yanzu cikin Nabeeha ya shiga wata na bakwai kenan cikin yayi tulele kai kace haihuwa ko yau ko gobe ta ƙara ƙiba tayi kyau abunta bata da damuwar komai ba sa ƙaunar su rabu duk inda zai je tare suke zuwa babu yadda Sweetie batayi ba akan yana barin ta wajen ta in zaiyi nisa

Please Login or Register in order to submit comment