Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gyara mata kwanciya ta kashe mata wuta sannan ta ja,mata ƙofa.

Jama'a da yawa sun cika gidan maƙil haka waje ma babu masaka tsinke tun daga kan masu mulki a haka akayi sada kan uku aka fara watsewa ya zaman saura ƙalilan ne tuni Papa ya yiwa yaran huɗu ba Namijin aun Mahaifinsa Macen ma sunan mahaifiyarta hakan ya yiwa kowa daɗi duk da suna cikin yanayi maras daɗi Junior Taufeeƙ da  Little beeha...

*My fan's ina matuƙar baku haƙuri da tun farkon sallah ba ku jini ba saboda ba na so na fara kuma na
[6/1, 12:15 PM] Hafsat A Garkuwa💫🥀: *TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
       ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/

'''My Hauwa💘 wannan page gaba ɗaya sadaukar wa ne a gareki ina miki sahihiyar ƙauna'''💫🥀

*Episode 75&76*

Bayan Sati ɗaya
...Nabeeha har yanzu ba ta um ba ta um-um kullum tana ƙunshe a ɗaki, ba ta da wani aiki sai tunanin Abwaan ɗinta a kullum gani take kamar zai dawo gareta sam ba ta ƙaunar abun da zai zo ya katse mata tunaninsa, su Junior Taufeeƙ a ƴan kwanakin sun ƙara girma shugaban ƙasa da kansa ya aiko da shanaye aka yankawa yaran tare da raɗin suna duk da ba ayi taro ba amma sun sha kuɗi sutura kamar za a buɗe katafaren shago daga mahaifiyarsu har su kansu, gaba ɗaya dangi sun fauwala Allah lamarin sa sun ɗauki dangana akan rashin Taufeeƙ sai dai duk wani minti yana tasowa a zuciyar su manta shi abune mai wuya a zuciyarsu hatta masu gadin gidan su su Sani sunyi kuka kamar ransu zai fita domin sun san sun yi rashin uban gida na gari.
Zaune take a ɗaki ta ƙurawa yaranta idanu da suke ta wutsilwutsil a kan gado ji tayi murmushi me haɗe da kuka ya kuɓuce mata tunisa da maganar da Taufeeƙ ya faɗa mata
"Baby na tanadar mana wani rayuwa me cike da farin ciki fiye da wanda muke a yanzu a duk lokacin da Allah ya sauƙe ki lafiya tare da mu reni yaran mu, mu ba su tarbiyar da al'umma za suyi alfahari da su, za mu basu kulawar da kaf faɗin duniya babu wanda ya bawa ƴaƴansa kwatankwacin wanda za mu ba su, sai da kafin ki yaye wanda kika haifa zan ɗirka miki wani sai mu rene su tare kin ji Baby."😄
Zun ɓuro baki tayi gaba cike da zallan shagwaɓa kamar yadda ta masa a lokacin da suke tare tace
"Um-um Abwaan ne dai gaskiya sai na yaye sannan in ɗauki wani ka ji Abwaan."
Sweetie da shigowar ta kenan dan dubasu ta tadata tana wannan abun wani irin hawaye masu matuƙar zafi ne suka zubo mata da sauri ta juya ta bar ɗakin.
Firgigit! Nabeeha ta dawo daga duniyar da ta yi nisa jin kamar motsin mutum ya fita, wasu hawaye ne suka zubo mata masu matuƙar ƙuna rungumar yaranta ta yi a tare suka saki wani irin kuka mai matuƙar tsuma zuciyar me sauraro😰.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum tana ɗaki ita da yaranta ranar da Taufeeƙ ya cika kwana arba'in a lokacin ne gaba ɗaya ahalin gidan sai da,Mutuwar sa ta dawo musu sabo musamman Nabeeha wanda ta ƙara ji duniyar ta yi mata zafi matuƙa, a washe gari ta shiga takaba, kullum cikin karatu take da addu'o'i ga Abwaan ɗinta cikin ƙanƙanin lokaci tayi masa sauƙa  haka akayi ta gurgurawa har ta fita a takaba, a ranar da ta fita ji tayi da ma ba ta fita ba duk rashin daɗin zaman takaba amma a yau saboda babu Abwaan ɗinta ta gwammace ta kasance cikin takabar sa washe gari gaba ɗaya suka ɗunguwa Kd domin dama saboda ita suke nan, ɗakin ta aka gyara mata yaran kuma suna ɗakin Sweetie shan nono ne kawai yake kawo su suma a ƴan watannin sunyi wayo sosai kyansu sai ƙara fitowa yake ga farin jini da Allah ya musu kowa ƙaunar yaran yake.
Zaune take a ɗaki ta zuba uwan tagumi Papa ne ya shigo ba kinsa ɗauke da sallama da sauri ta ɗago tare da amsa masa, zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin cike da kulawa yake kallonta gyaran murya yayi kana yace
"Nabeeha zaman kaɗaicin da kike ya isa haka shin kina fushi da hukuncin Allah ne?"
Da sauri ta girgiza kai hawaye na taruwa a idanunta.
Murmushi ƙarfin hali yayi kana yace
"In har bakya fushi da hukuncin Allah ya kamata a ce kin ɗauki dangana ki bisa da addu'a wannan abun da kike bazai taɓa dawowa da shi ba ya tafi ya barmu na har'abada don haka ki fauwalawa Allah komai kici gaba da masa addu'a kamar yadda kike saba dan yanzu shine abun da yake buƙata daga gareki da mu ba ki ɗaya... Cike da hikima da kulawa da kalamai masu daɗi ya cigaba da kwantar mata da hankali har ta samu ta sake sannan ya kamo hannunta suka fito falo in da gaba ɗaya suke zaune zama tayi cikin su Ka'aaf ne yace "Aunty Nabeeha kema za kije wajen shan ice cream yanzu Yaa Sayyid zai kai mu.
Murmushi tayi tare da jawo shi jikinta tace "In har kana so muje ai sai muje ko Ka'aaf ɗina.
Gaba ɗaya sun ji daɗin hakan, hakan yaza gaba ɗaya suka rakaɗa suka tafi a domin su samar mata da farin ciki da su kan su baki ɗaya, tun da suka fita duk wani motsin da tayi Yaa Sayyid yana kallonta gaba ɗaya ya kasa ɗauke ido a kanta haka ma Ja'waad, sun ziyarci wajen wasanni da dama tun ba ta sake ba har ta sake gaba ɗaya a wannar rana gaba ɗaya sun shiga farincikin da suka jima ba su shiga ba salla ne kawai yake tada su, sai magriba suka dawo gida duk a gajiye kowa ya nufi ɗakin sa.
Bayan shekara ɗaya
Nabeeha yanzu ta sake sosai musamman da Yaa Sayyid yake zuwa a kullum domin ɗebe mata kewa kun san shi gwanin barkwanci hakan yasa take matuƙar samun nutsuwa sam Ja'waad ba ya jin daɗin zuwan da Yaa Sayyid yake wajen ta, shirye-shirye aka fara na auren Huda da kuma Samha da Nazmar, in da Huda za ta aure wani Abdul-hakim, Samha kuma ita da Nazmar ba yadda bai yi ba akan Ja'waad ya fitar da mata amma sam yaƙi yanzu auren saura wata ɗaya kenan.
Kamar kullum zaune suke ita da Yaa Sayyid yana ba ta labari sai dariya take juyowa yayi ya fuskance ta da kyau sannan ya ce
"Nabeeha ina so muyi magana da ke amma kuma ina tsoron amsar da zai fito daga bakin ki...
Gaban ta ne ya faɗi, cikin dauriya da son kautar da maganan tace
"Yaa Sayyid to ba sai kawai ka haƙura da maganar ba tun da tsoro kake ji ta faɗa tana ƴar dariya dai bai kai zuci ba.
Dariya shima yayi sannan yace
"Ai dai sai ki ƙarfafa min gwiwa ba wai ki sare min ba Nabeeha ina sonki ina ƙaunarki kuma a shirye nake na baku kulawar da ta dace daga ke har su Junior za saku farin ciki zan...

*************************
Rayuwar su Amatullah da angwanta na tafiya yadda ya kamata domin suna bawa junansu kulawa tare da tattali da ƙauna watan su biyar Abba da Nabeeha suka tafi garinsu yana zuwa aka haɗashi da hukuma domin daman ya sanar musu da komai tun kafin yazo direct gidan suka nufa me gadi ne ya buɗe musu ganin Amatullah cike da matuƙar mamaki yake kwallonta ganin sauyawar da tayi tayi wani ƙiba taƙara kyau, shigowa sukayi Amatullah ne ta fara shiga falon zaune suke gaba ɗaya kamar yadda suka sa ba sai dai kallo ɗaya za ka musu ka fahimci suna cikin ƙunci ma talauci domin kuɗin da suke facaka da shi ya ƙare babu kuma takardun kadarorin sun yi neman duniya har sun gaji, da sallama a bakinta ta shiga cike da mamaki suka kallota jin muryar wacce ba su taɓa tsammani ba, a guje Sadiq ya taso yana ga abar ƙaunata ta dawo yau sai kwanan hotel wayyoo daɗi ya faɗa yana tsalle kamar wani zautacce yanzu ya zama asalin ɗan shaye-shaye ga sata ga iskanci duk ya rine yayi baƙi ya rame, Baffa Jiboo ne yace
"Alhamdulillah ga arzikin mu ya dawo ke dan ubanki zo ki ba ni takardun kadarorin nan sannan ki juyo in da kika fito shegiya gantalalliya.
"Sannu shege gantalalle jikar tawa kake zagi haka?
Da sauri suka ɗago jin abun da wani wanda ba su sani ba yake faɗa sake baki suka yi ganin wanda yake gabansu domin babu wanda bai san shi ba, in ma baka taɓa ganinsa a zahiri ba ka ganshi a T.V ko a jarida mamaki ne ya kama su Baffa Gambo yace "Kamar ya Jikarka?
A fusace Abba yace "kamar yadda in muka je kotu za kayi bayani Acp ku shigo gasu nan gaba ɗaya ku tarkatasu har matan."
Wani ihu Mama Marka ta zuba za ta kwasa a ɗari tana "wayyo Allahn mu wannan wacce irin baƙar rana ce ga ci ga kwanan yunwa don Allah ku rabu da mu da iya yunwa n da muke ji ku tafi da mazan dama sun fi mu ƙarko kai jama'a zalunci bai yi a rayu ba."
"Yo ina zalunci yayi kuma Marka tun da ga karshen me yin ta nan za a kulle mu da yunwa a cikin mu wayyo ni Baraka.
Haka suka yi ta iface iface Sadiq kuwa baƙin cikin sa ɗaya na ganin Amatullah bai ɗanɗana ta ba ya so a ce yau kwana zai yi yana shan lagwadar daɗinta baƙin cikinsa kenan.
Gaba ɗaya aka tafi dasu babu wanda aka bari har ƴan matan aka kulle sai da aka musu jina jina tuni kamanninsu ya sauya Mata iyayen tsoro gaba ɗaya sun yi nadamar gallazawa Amatullah da sukayi domin ba suyi tunanin akan kisan iyayenta aka kamasu ba haka su Baffa jiboo ma shiyasa abun bai ɗaɗasu da ƙasa ba dan sun san in shine ma ba ta da wata hujjar da za ta tabbatarwa da kotu su suka kashe mata mahaifa, su kansu wa ɗan da suka kashe sun ma suma su n aika su lahira sakamakon tsoron kar su tona musu asiri domin kuɗi kawai suke karɓa a wajen su suna musu barazana hakan yasa Baffa Jiboo suka gayyatosu har gida suka sa musu guba a abinci gaba ɗaya suka mutu, hakan yasa suka tabbatar babu wani me hujjar da zai tabbatar da su ne suka kashe iyayenta.
Sai da suka yi sati sannan aka shiga kotu gaba ɗaya su n ƙaryata tahumar da ake musu na kisan iyayen Amatullah sai da Lauyan Abban Amatullah ya kawo hujjoji har ma da videos na kisan cike da matuƙar tsoro da nadama da tazo musu nan take, yanke musu hukunci akayi na kisa ta hanyar rataya shi kuma Sadiq ɗaurin rai da rai, su Mama Marka kuma gidan gyaran hali akaisu domin a dai-daita su na tsawon wata guda har yaransu gaba in ance su hora wata ko da kuɗi aka ba su baza su yi ba.
Satin su Baffa jiboo ɗaya aka ƙaddamar musu da hukunci sun nemi yafiyar Amatullah ta kuma yafe musu amma sam Abba yaƙi yafe musu dan dole sai sun girbi abun da suka shuka a chan lahira, rayuwa kenan yan uwa mu ji tsoron Allah kar duniya ta ruɗemu mu mance da lahirar mu a aikin banza, ka mu biyewa kwaɗayi da son zuciyar mu su kai mu su baro mu, Allah ya kiyashe mu aikata aikin danasani.
Lauyan Abban Amatullah ya damƙa mata duk wata kadarar da mahaifinta ya dan ƙa masa amanarsu, Abba ya masa godiya matuƙa tare da kyauta me tsoka tare da ba shi Auren Raudah don ya yaba da hankalin sa matuƙa, dama Br. Musa ba shi da mata bai taɓa aure ba, ba jimawa aka sha biki dan yanzu Raudah ta zaman ta Allah da taimakon Ammy…

Vote
Comment
Share
Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻* 
08132761212
[6/1, 12:15 PM] Hafsat A Garkuwa💫🥀: *TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
_(Domin Marubuta Mata)_
_✨(W.W.A)✨_
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/

_End! End!! End!!!_😰💃🏻

*…* Cike da firgici kaɗuwa ta miƙe jikinta na rawa cike da ɓacin rai tace "Sayyid ka san kuwa abun da ke fitowa daga bakin ka kuwa? Shin ka mance ni ɗin matar waye a gareka? To in mafarki kake kayi hanzarin farkawa domin hakan bazai taɓa faruwa ba… Da gudu ta bar wajen tana fashewa da wani irin marayan kuka, gaba ɗaya ta fice a hayyacin ta ta mance waye Sayyid a gareta, mamaki abun ya masa duk da dama yasan hakan zai iya faruwa amma bai tsammaci abun ya kai hakan ba, jiki a sanyaye ya fice ya bar gidan ba tare da ya yiwa su Sweetie sallama ba dan bai jin zai iya buɗar baki a wannan lokaci ya yi magana, haka ya fice duk ranshi a jagule, amma ya ƙudura a ransa a wannan karon duk rintsi duk wuya sai ya mallaketa da izinin ubangiji bai jin a wannan karon akwai wanda zai kayar da shi ƙasa ya ɗauketa a wannan karon ya ƙudiri fito na fito da duk wanda ya masa iyaka da ita dan ba gudu ba ja da baya da wannan ya fice daga gidan.
Ɗaki ta shige kuka kawai take ci a yanzu ne mutuwar Abwaan ta dawo mata sabuwa, ta ji mugun ɗacin kalaman Sayyid tasan da Abwaan ɗinta ma raye babu wani wanda ya isa ya mata maganar yana sonta, amma sai gashi daga ɗan tafiyarsa duka-duka bai fi shekara biyu ba amma ana mata zancen wani soyayya, ai har abada bazan yi aure ba matuƙar ba Abwaan ɗina ne ya dawo ba, kasancewar duk wannan maganar da take a fili take yasa su Samha sanin halin da take ciki suma kukan suke domin su n san tsananin shaƙuwar da ke tsakaninta da Abwaan rungumeta Samha ta yi tace "don Allah Nabeeha kiyi haƙuri na san me kike ji amma duk da haka ba zai yiwu kina yarinyarki ki zauna haka ba aure ba wlh bazai yiwa ba dole za ki fidda miji kiyi aure Abwaan ya tafi kuma bazai dawo ba Nabeeha sai dai mu mu jirayi lokacin da za mu je mu tarar da shi, don haka ki sassauta wa zuciyarki tare da bata haƙuri akan rashin da tayi kiyi ƙoƙari ki gyara rayuwarki wlh su Sweetie suna matuƙar shiga damuwa matuƙar suka ganki a damuwa kawai ba yadda suka iya ne.
Cikin kuka tace "Samha kina nufin na yi aure na bar Abwaan ɗina? Wannan abun bazai taɓa saɓuwa ba don Allah ki daina ma min wannan maganar tun kafin mu samu matsala da ke."
Samha sanin hali yasa ta yi shiru dan yanzu za a iya uwar watsi.
Samha na fita ta kwanta ta ci gaba da kukanta tare da tunanin Abwaan ɗinta dama babu ranar da za ta zo ta wuce ba ta tuna shi ba a haka bacci barawo ya ɗauketa.
Yana zuwa gida ya sanarwa Momy wato Anty Sa'a ta ji daɗi sosai, sai dai jin amsar Nabiha ya sa ta ji babu daɗi duk da dama tasan hakan dole zai faru, amma a take ta ɗauki waya ta ƙira Papa bayan sun gaisa ta zai yane masa halin da ake ciki, shiru Papa yayi na ɗan wani lokaci sannan ya nisa yace Yaya ban wi ta taki ba amma wai da ina so na mai da auren kan Ja'waad ne kuma…
Cikin ɓacin dai ta dakatar da shi tace "Kuma me? Wai kanka ɗaya kuwa shin shi Sayyid ba jininka ba ne kenan in har alƙawarin da kukayi ne shin baka cika ba ne ko mi? Ko kuma warayya za ka nuna min kul karma ka fara, in kuma kayi gigin haka za ka sha mamaki na wlh."
Ƙit! Ta kashe wayar zuciyarta na mata zafi, cike da damu Sayyid yace "Momy lafiya?
"Ina ko lafiya Sayyid Papan ku ne yake so ya ɓatamin dai a banza wai ka ji da zai haɗa Nabiha da Jawa'ad ne kai ka ji wani zancen iska."
Gaban Sayyid ne ya faɗi cike da tsoro ya kamo hannun Momy yace "don Allah Momy kada a rabani da Nabiha a karo na biyu wlh yanzu ba garin zan bari ba duniyar zan bari dan baxan iya jurar ta kuma auren wani ba don Allah Momy."
Cike da damuwa tace "kar ka damu Sayyid a wannan karon in sha Allahu kai za ka auri Nabiha ku zauna tare na har'abada."
Haka suka cigaba da hira suna cikin hira Papa yayi sallama bayan sun gaisa ne Sayyid ya ba su guri zuciyarsa na wani irin bugawa.
Cikin girmamawa Papa yace "Yaya ba ki tsaya kin fahimce ni ba shiyasa na zo na miki bayani.
"Babu wani bayani da zaka min wanda ban gane ba kawai kana so ka nuna min ba kai ka haifi Sayyid ba shine kawai dan haka ni ka tashi ka ba ni guri."
Ganin ran yayarta sa ya ɓaci ne yasa ya sauƙar da murya yace
"Don Allah kiyi hakuri Yaya abun da kika ce shi za ayi daga Nabiya Jawa'ad Sayyid ƴaƴana ne babu warayya a tsakanin su Allah ubangiji ya tabbatar da alheri in sun dai-daita sai kawai a haɗa da na su Huda duk da saura satikai.
Murmushin jin daɗi ta yi tace "yanzu ka yi magana Allah ya tabbatar mana da alheri, nan suka ɗan taɓa hira na ƴan uwantaka daga bisani ya mata sallama ya tafi, yana fita Sayyid ya dawo dan dama bai bar gidan ba cike da tsoro yace
"Momy Allah yasa dai ba hanani itan za kuyi ba wlh in aka mim haka ba a min adalci ba."
Ya faɗa kamar zai yi kuka, dariya Momy ta yi tace "kwantar da hankalin ka kayi ta ƙoƙari har ƙwallonka ta shiga raga in har kuka dai-daita kan ku ƙila a haɗa auren ku da na su Huda."
Wow! Alhamdulillah wayyoo daɗi!!! Ya faɗa da wani irin kara ya ƙara da cewa "in sha Allahu ma tare za a haɗa Momy ba ri ma naje na ƙirata dan na barta da ɓacin rai.
Daga haka ya fice ya nufi part ɗinsa cike da matuƙar farin ciki gani yake kamar ma an mallaka masa ita ne, yana shiga ɗaki wayarsa ya ɗauka ya ƙirata bata ɗauka ba har wajen sau 5 ganin baza ta ɗauka ba ne ya tura mata text kamar haka
_Amincin Allah ya tabbata a gare ki, mace ta farko da ganin kyawunta a karon farko ya hana ni bacci a tsawon dare, ya hana ni sukuni a tsawon yini, macen da ta tsaida zuciyata daga tinanin komai sai nata, macen da nake so kuma zan cigaba da so har karshen rayuwata, Ke ce babbar kyautar da a tarihin rayuwata na taɓa samu wadda ba zan taɓa mantawa da ita ba. Ina son ki. Ina fatan tabbatuwar murmushi a saman fuskarki tare da kasancewarki cikin walwala da farin-ciki a ko da yaushe. Ina matukar ƙaunarki My Nabiha kiyi bacci lafiya.😍😘_
a take ya tura mata ya kwanta cike da farin ciki kamar ance yau ne auren su haka yake ji a haka yayi bacci cike da begenta.
Washegari
Da kasala ta tashi duk tana jin babu daɗi sam sai da ta kammala duk wani abun da za ta yi sannan ta ɗauki wayarta da ta ji alamun saƙo ya shigo, dubawa tayi taga saƙo ne kuma Sayyid ne ya turo su ɗaya tun jiya ɗaya kuma minti talatin da ya wuce, na jiyan ta duba ta karanta ko da ta gama tsaki ta yi sai kuma ta shiga na yau ɗin ta fara karantawa kamar haka
_*My Heart* fatan kin tashi lafiya?ina neman alfarmar da ki mallaka min zuciyar ki, na dad’e da mallaka miki tawa lokuta masu yawa da suka shud’e abokai ma shaida ne, bayan ya kasance kin mallaka min ita ni kuma zan had’a su na d’aure su waje guda da sarkar soyayya mai ‘karfi na jefa makullin a cikin tekun maliya. sannan ina so in bayyana miki cewa so tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take d’auke a jikin gangar jiki ma’abociyar zuciyar da take ‘kunshe da So. Kasantuwar so a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin zuciya bayan bayyanar sa, wato bakin-ciki da kuma farin-ciki. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi, ki shirya min yarana an jima zan zo mu fita._💞💞💗🤍
Tagumi ta yi gaba ɗaya kan ta ya kulle ta rasa me za ta yi guda ɗaya ta shi ta yi ta fito falon ta taras da su gaba ɗaya bayan sun gaisa ne ta kalli yaranta cikin shiga ta alfarma wani son su Sweetie da ƙaunarsu yake ƙara shigarta yanzu ta ƙara tabbatarwa da ta yi dacen dangin mahaifinta suna matuƙar ƙaunarta ba su ƙaunar baƙin cikinta saɓanin wasu dangin uban da suke maka riƙon sakainar kashi, a tare suka karya duk da ba ta wani ci na kirki ba, bayan sun kammala ne Papa ya ƙirata suka nufi part ɗinsa bayan ya zauna sannan itama ta zauna a wajen ƙafafunsa zuciyarta na wani irin bugawa duk wata addu'ar da tazo bakinta ita take karantowa gyaran murya Papa yayi kana ya fara da cewa
"Mamana ina so ki san duk wani abu da kika ga ya faru muƙaddari ne daga Allah, ki rungumi kaddara a duk lokacin da tazo miki ki mika komin ki garesa zai miki magani, Mamana a karo na biyu ina so na roƙeki wata alfarma bazan miki dole ba amma alfarma nake nema akan ki auri Yayanku Sayyid na tabbata zai cike miki gurbin marigayi, Sayyid mutum ne na gari me tarbiyya ban jin wata matsala daga garesa domin kin sa ni tun ba yanzu ba yake sonki kawai anci ƙarfin sa ne da kuma rabon su Little Beeha ina fatan kin fahimce ni?
Cikin danne kukanta tace
"Na amince Papa Allah yasa hakan shi ne mafi alheri a gare ni na kuma gode sosai da kulawar da kuke ba ni na 9tabbatar da ko iyayena ba za su min fiye da yadda kuke min ba, Allah ubangiji ya biya ku da gidan aljanna.
Cikin farin ciki da ƙara yabawa da tarbiyar da Sweetie ta bata ya shafa kanta tare da faɗin
"Allah ubangiji ya miki albarka Nabeeha Allah yasa yadda kika mana biyayya kema yaran da kika haifa su miki ninkin sa, sai dai wani hanzari ba gudu ba ina so za a haɗa auren ku da su Nazmar dafatan babu matsala ko.
Wani irin faɗuwar gaba ta ji sam ba ta so hakan ba, amma kuma babu yadda ta iya cikin dauriya da muryan kuka tace
"Allah yasa shine mafi alheri Papa."
"Amin Mamana ta shi kije Allah ya miki albarka.
Kamar dama jira take da sauri ta miƙe har ta na haɗa hanya ta fice a guje tq nufi ɗakin ta tana zuwa ta kife a gado ta ci kukanta son rai ta godewa ubangiji su Samha sun yi rarrashin har Huda ta gaji Samha ne gwanar tausayi kawai itama ta kama kukan yaushi da ya ishi Hudah tace
"Yanzu Nabeeha akan auren ki da Yaa Sayyid ne kike kuka kamar ranki zai fita? Shin kuwa kin mance waye Yaa Sayyid a gareki? To in kin mance bari na tuna miki, tun kina ƙarama Yaa Sayyid yake ɗawainiya dake, ke hatta kashin ki Yaa Sayyid ya wanke miki shin laifi ne dan Yaa Sayyid ya so ki? Ko kuma bai chanchanta da ki so shi ba ne, menene laifin sa akan son da yake miki? To a gaskiya in dai hakane kin cika butulu wlh dan haka yanzu zan je na sanarwa su Papa kawai gwara Yaa Sayyid ya haƙura ya nemi wata shine kawai... Daga haka ta nufi hanyar fita da sauri Nabeeha ta riketa tana kuka tace
"Don Allah Aunty Huda ki tsaya ki saurare ni ba ina kuka don ina ƙin Yaa Sayyid ba ne a'a ina kuka ne akan babbar rashin da na yi a yau mutuwar sa ta dawo min sabuwa ji nake bazan ta ɓa

Please Login or Register in order to submit comment