Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yarda muka tafi sai da na mata da gaske.
  A ɓoye Papa ya sauƙe ajiyar zuciya jin ba zargin da yake bane, dariya yayi yace "ai halin Nabeeha sai ita muma baka ga magiyar da mukayi ta mata ba akan mu tafi amma taƙi ai kai kaci sa'a ma wlh, gaba ɗaya suka saka dariya, nam suka baje abun da suka sayo suka fara ƙaramin party sai a sannam Jawaad ya saki fuskarsa (Ni ko nace oh kai kuma miye naka na ɗaukar zafi haka🤔)  sai da sukayi sallar i'sha sannam Yaa Sayyid ya tafi, anguwar Rock road ya nufa domin anam gidan su yake, a wani katafaren gida yayi horn duk da gidan baza a taɓa haɗasa da gidan Papa ba amma shima ya amsa sunansa gida, me gadi ne ya leƙo ya gansa sannam ya koma cikin sauri ya buɗe masa, filin gidan nasu ɗan madaidaici ne wanda a ƙalla zai ɗauki mota 7 yana Parking bayan sun gaisa da Kamilu me gadi ya nufi cikin gidan, yahaniya yayi ta jiyowa yasan kuma bazai wuce Huda itace me bi masa wanda take da shekara 24 sai kuma Samha da take shekara 19 sa'ar Nabeeha sai kuma autarsu Nihal me shekara 5 da sallamar sa ya shiga, Aunty Sa'a ne da ke zaune chan gefensu tana kallon ta amsa masa, babbar mata ce wanda a ƙalla za takai shekara 68 tana da ɗan jiki kana kallon ta za kaga kamar da suke yi da Papa, murmushi ta sakar masa tace "har ka dawo ɗan gidan Papa? (da yake kowa sunan da yake faɗa masa kenam Papa tun daga kan Taufeeq) "eh wlh Oum na dawo suna gaida ki ma, ki shirya duk da nasan kin sani ɗan gidan ki saura sati biyu ya dawo, ai ɗif ɗakin ya ɗauke wuta babu hayaniyar su Huda ko motsi ƙwaƙwara babu sai TV dake aikinsa, gaba ɗaya shi da Oum suka fashe da dariya, Oum tana cewa "Ƴan ƙaniya tun ɗazu nake binki ku min shiru amma sam ƙun ƙi saurarena ma yanzu da kuka ji dodonku ya kusa dawowa ai kun nutsu tun kafin yazo, Allah dai ya dawo min da yaro na gida lafiya.

"Amin ya Allah" cewar Sayyid yana dariya.

  Samha ce tace "wlh sam bana son Yaa Taufeeq ɗin nam ya dawo ya cika takura, Allah yasa yanxu ba anam zai sauƙa ba dan in anan ne wlh tattarawa zanyi na koma gidan Papa dan bazan iya wannam takurar tasa ba. ta ƙarasa maganar ƙwalla na taruwa a idanunta.
      Huda ne tace "ai ni tun yanxu zan fara haɗa kayana dan nasan ba makawa a nam zai sauƙa, ni wlh na so Shugaban ƙasa a ko da yaushe ya rinƙa turasa yana wakiltar sa, ya zama kawai shine me zuwa duk wani taro da ake.
   Nihal tace "yeee! Yaa Taufeeq zai dawo, saboda ita dai tasan yadda yake janta a jiki su ne dai yake musu abubuwa na azaba kala² dan duk da yarintarta ta fahimci komai, harara Samha ta balla mata tace "ke dama ai dole kiyi murna tunda duk abun da kike so yi miki yake nima ina ma kamarki ce ni da bani da wata matsala wlh rigimata zan nayi son rai na.
     Yaa Sayyid ne yace "duk zaku gama ai dama ni sam bakwa jim maganata shiyasa nake ta addu'ar dawowan ɗan uwana yaxo ya cigaba daga inda ya tsaya, su Nabeeha ha ma suna chan suna baƙin ciki da dawowarsa.
 
Oum ne tace "Kai wannan yaro nawa Allah ya zuba masa farin jini, ta faɗa da alamun tsokana"

"Um su farin jini manya wlh wannam ba farin jini bane tsantsar baƙin jini ne ita tausayawa wanda zata auri miskilin mutum kamar Yaa Taufeeq ga mugunta ga bai son mutane😏 ta faɗa tana murguɗa baki.
   Ya Sayyid yace "to ko dai da ke za ayi ne dama Papa yana cewa in ba mu fito da mata ba zai sa ayi wuf! damu, ya faɗa suna saka dariya baki ɗaya.
   Zaro ido Huda tayi tare da dafa ƙirjinta tace "na shiga uku! Yaa Sayyid ka rufa min asiri kada a binneni da rai na, wlh ko a mafarki bana fatan nayi mafarki zan auri irin me halin Yaa Taufeeq bare kuma shi da kansa ai na ma haƙura da auren, bari ma kaga tun yanzu na fara haramar haɗa kayana dan wlh gobe²n nam zan bar gidan nam ba sai lokacin dawowarsa yayi ba kar ya mana bazata kamar yadda yawancin yake yi. ta faɗa tana nufar ɗakinsu dan bilhaƙƙi da gaskiya take.
  Samha ma meƙewa tayi tace "ai ƙafata ƙafarki Aunty Huda a barin gidan nam.
  "Ni kam babu inda zani zan jira Yaa Taufeeq ɗina,cewar Nihal tana kwaɓe fuska.
   "Yauwa ɗiyar Albarka rabu dasu su suka sani mu dai muna murna da dawowarsa, cewar Oum.
  Nam suka ɓingire da hira ita da Yaa Sayyid.

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

   Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo ganin yadda ake almubazzaranci da abinci, su ko tunanin taya aka samo abincin basayi su dai kawai su banzatar dashi kawai suka sa ni, muryar Shema ce ta katse mata tunanin da ta ke tana cewa "ko dai baza ki girka bane na ɗauki mataki? da sauri ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "kiyi haƙuri yanzu zanje na girka.
Daga haka tayi tafiyarta bata ji me suka ce ba sai dariyarsu da taji, tasan kuma maganarta sukayi, tana zuwa ta kwashe jallof ɗin da tayi a food flack's sannam ta ɗaura mata ba jima ta kawo mata ta gyara kitchen ɗin ta ɗibo abincin ta tayi shigewarta ɗaki, cike da tunanin baƙar rayuwar da ta fara a cikin gidan ubanta wanda ko a mafarki bata taɓa mafarkin irin wannan rayuwar ba sai gashi tana riskarsa wanda bata san ƙarshensa ba addu'arta a kullum bata wuce, Allah yasa komai da  zai zo mata yazo mata me sauƙi, tana cikin wanna tunanin taji an banko ƙofar da sauri ta kalli ƙofar Mama Marka ne fuskar nam ta ta tamau da ɓacin rai, cikin masifa tace "ke dan uwanki har kin isa su Shema su saka ki abu amma ki ƙiyi ke ga ƴar iska ko? Mamaki ne ya cika ta a zuciyarta tace "me kuma nayi musu? duk abun da suka sakani babu abunda banyi ba, ko dai akwai abun da suka ce na kawo musu ne ban jiba? kafin ta kai ga samun ansa taji wani irin sanyi yana rasa ɓargo da jikinta wani sanyi ne da bai taɓa riskar jikinta Mama Marka ce hannunta ɗauke da plastic tana ƙara kuza mata ruwan sanyi me haɗe da dusar ƙanƙara…'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muku nam bada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞🤞🏻

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

*MASOYANA DON GIRMAN ALLAH KUYI MANA SUBSCRIBE ƊIN WANNAN CHANNEL DOMIN SAMUN LITATTAFAN SAURARE DA KOYON SANA'O'IN HANNU DA SAURAN SU NA GODE*👇🏻
https://youtube.com/channel/UCY1pIcI2DlVykTz57m6Q3TA

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Episode 05*

*Washe gari*
*…* Tun ƙarfe goma suka gama shirin su na barin gidan, dan kwana sukayi cikin ɗa-ri-ɗa-ri dan ji suke kafin safiya za su iya ganinsa, fitowa sukayi da jaka niƙi² da kaya Oum dake falo ita da Yaa Sayyid mamaki ne ya cikata, dan batayi tunanin haka ba yaran da sam basa son nesa da ita yau ace za su tafi su barta, Yaa Sayyid bai yi mamaki ba dan yasan kaɗan daga aikin su dariya ya farayi sosai dan sun matuƙar bashi dariya, nuna su yayi yana cewa "kaga matsoratan banza wlh in kukayi wasa babu wacce zata bar gidan nam.
  Ai kafin ya rufe baki tuni sun iso wajensa durƙusawa sukayi suna magiyar dan Allah ya bar su baza su iya zama a gidan nam ba, Oum ne tace "to ai shikenam dan in dai akan ɗanane sai fai kubar gidan kam ku tashi ku tafi Allah ya tsare ni in ɗana ya dawo zai maye min gurbin ku. "Eh mun yarda" suka faɗa a tare.
  Dariya Oum tayi suka musu rakiya Yaa Sayyid yace "ku tsaya dai dan ba dan halinki ba naje na ajiye ku, godiya suka masa suka shiga Nihal ma tace zata raka su amma ita zata dawo ta jira Yaa Taufeeq, haka suka rankaɗa suna tafe yana zolayarsu, mutum ne da babu ruwansa kowa ma tsokanarsa yake ba ƙannensa ba koma waye, duk abun da ka masa bai cika ɗaukar zafi ba sai dai in yaga zaka kauce hanya yanzu zai saita maka zama ka dawo taitayinka.
  A haka suka ƙarasa gidan ba kowa a parlour'n sai ƙarar AC da ya karaɗe falon da wani sanyayyan ƙamshi, zama suka yi  suna ƙwalawa Nabeeha ƙira, Nabeeha dake ɗaki tana kwance tana chat da friend ɗinta taji kamar muryar Huda ai da gudu ta fito falon ko tsayawa ta duba wani irin sutura ne a jikinta batiyi ba, burin ta kawai ta isa garesu ta tabbatar muryar da taji da gaske ne ba ƙarya kunnenta ya mata ba, turus! tayi wani farin ciki na mamaye dukkan wani sassa na jikinta, da sassarfa ta ƙarasa garesu cike da murnar ganinsu tace "wlh Sister's nayi missing ɗinku over Allah yasa dai kun dawo nam da zama dan na ganku da jaka niƙi² ta faɗa da yanayin ta na shagwaɓa.
         Kafin suyi magana Yaa Sayyid da tun fitowarta daga ɗaki yake binta da wani mayataccen kallo na wani irin kyau da ta masa, sanye take da kayan bacci  rigar me ɗan duhu wacce tazo mata gwiwa ya fidda shafin boobs ɗinta  sai wandon wanda da kaɗan yafi gwiwa kayan duk da na bacci ne yayi mata kyau sosai kanta babu ɗankwali sai gashinta da ya bazu har fuskarta, gaba ɗaya ta tafi da imaninsa wani nufaji ya fesar sannam a fili yace "Masha Allah tubarakallah Allah Ubangiji ya bani ke a matsayin mata my Queen.
  Mamaki ne ya cika su jin furucin sa Nabeeha batayi mamaki ba dan tasan kaɗan daga aikinsa, su ko su Huda dariya suka sa Samha tace "lalle Yaa Sayyid ba mu gane in da maganar ka ta dosa ba ka ganar da mu.
  Harara ya wullo mata sannam yace "wannam karatun baza ki iya ɗauka ba domin har yanzu ƙwaƙwalwarki ƙaramace.
    Su Papa ne suka sauƙe rungume da juna kana kallonsu kasan auren soyayya sukayi kuma suna tsaka da cin soyayyarsu kamar ma yanzu suka fara, sai sheƙi suke kamar wasu tarwaɗa, bakin su a haɗe wajen cewa "Allahu Akbar Allah ka ƙarawa Annabi daraja.
  "Amin ya Allah"
      Cewar su Sweetie da suka iso su, gaba ɗaya suka gaidasu cike da girmamawa, Papa ne yace "ya na ganku da kaya ko tafiya za kuyi?

   "Papa wai sun dawo nam ne saboda Yaa Taufeeqqqqq a gidan Momy zai sauƙa" Nihal ta faɗa cikin gwarancinta.
  Dariya Papa da Sweetie sukayi Sweetie tace "lalle yaran nam ban san me ya tsare muku haka ba wato gudowa kukayi saboda a gidan Aunty Sa'a zai sauƙa ko? ni kuma Allah yasa a gidan nam wannam karon zai sauƙa naga ta tsiya.
  Gaba ɗaya annurin fuskarsu ta sauya, " Sweetie ya za ki mana wannam mummunar fatan, wlh dan de bake yake sawa zaman prison bane da baza ki faɗi haka ba, kema da bayan mu za ki bi, cewar Samha kamar za tayi kuka.
Papa ne yace "ku kwantar da hankalin ku ba ma anam zau sauƙa ba sai dai fa nima bazan bari kuyi abun da ranku yake so ba ahto, sannam ganin ku baxai hana musha soyayya nida Queen ɗita ba ah toh!
  Gaba ɗaya dariya suka sa shiyasa suke son zuwa gidan Papa ko ba komai za kaci dariya kuma zaka ɗauki darasin soyayya, Yaa Sayyid bai wani jima ba ya musu sallama ya wuce dan wajen aikinsa suna ta ƙiransa suna da wani taro kuma shi kaɗai ake jira, dan dole ya tafi ba don yaso ba.
      A ɗakin Nabeeha suka sauƙa duk da ɗakuna birjik dake gidan, amma sunfi so su haɗu su ukun su su wataya son ran su.
   Nihal sukayi ta wasa da Ka'aaf sai dare sannam yazo ya ɗauki Nihal suka tafi bayan ya gama yiwa flower'sa bayi, duk da ita flower'n bata amsar bayin da ake mata, shi dai ya ƙudiri aniyar haka zai ta binta har Allah ya bashi nasara.

*Bayan kwana goma*

Su Ali ne suke ta zuba musu a farfa jiyar gidan horn aka danna da sauri me gadi ya leƙa ganin jerin gwanon motoci ya sanar masa da wanda yake ciki, wani fara'a ne ya suɓucewa fuskar sa, da sauri ya wangale gate ɗin nam motocin suka fara shigowa a sukani, motoci ne masu numfashi guda uku na farko ta jami'an tsaro ne sai kuma ta tsakiyar wanda me hawanta sai wane da wane fara ce sol na ukun ma ta hukuma ce a parking space suka tsaya, da gudu su Garba suka nufo inda motocin suke, sukayi charko charko cike da farin ciki, gaba ɗaya jami'an tsaron suka sauƙo ɗaya daga cikin su ne ya nufo wannar motar ya buɗe ƙofar baya sannam ya ɗan ja baya, da alamu mamallakin motar ya buɗe wa, ya jima kafin ya sauƙo da ƙafarsa ɗaya wacce take sanyi da takalmi sau ciki fari sol me matukar sheƙi da ɗaukar ido.
    Sai da ya ja ƴan second kafin ya fito gaba ɗaya "Hasbunallahu wani'imal wakin!" wani kyakkyawan Mutum ne me matsakaicin tsawo fuskar sa me tsawo ce me cike da saje me matuƙar sheƙi da ɗaukar ido haka kayin sama kana kallo kasan bafulatani ne idon sa da suke ƴan madaidaita me matukar maiƙo da kyawu da kwarni ga duk wanda ya kallesu ɗauke yake da ɗogon hanci, bakinsa ɗan madaidaici jajazir kamar ta jinjiri sanye yake da red nd white suit, hannun sa sanye da agogo me matuƙar tsada na kamfanin gucci fuskar nam a haɗe take in ba kallon ƙurilla ka masa ba baza ka ganu tsananin farin ciki dake kan fuskar ba, nam su Ali suka fara rantaɓo gaisuwa hannu kawai yake ɗaga musu ya nufi cikin gidan, take ransa ya jagule jin wani irin kida dake tashi a cikin gidan, tayi yake cikin nitsuwa da burgewa chak ya tsaya a parlour'n yana ƙare musu kallo...

      Zaune suke a falon Nabeeha, Huda, da kuma Samha da su Nazmar sun ƙure sautin kiɗa sai tashi yake yau basa jin rawar sun zauna dai suna ɗan taɓa hira cike da ƙaunar junan su, kamar daga sama suka ji Ka'aaf na faɗin "Oyoyo Yaa Taufeeq
   Da sauri suka kalli inda yaron ke kallo chak suka miƙe suna zaro idanu waje…

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun" abun da take ta maimaitawa kenam domin ruwan ya matukar ratsa duk wani sassa na jikinta cike da ruɗewa tace "Mama Marka don girman Allah kiyi haƙuri wlh ban san me na musu ba, sun ce na dafa musu abu kuma na dafa na kai musu, wlh babu abun da suka kuma faɗamin, ta ƙarasa magana wani kuka na kuɓuce mata, wani ashariya Mama Marka ta ruga mata ta kifa mata wasu tagwayen mari tace "dan uwan ki wato ƙarya suka miki zaki ce ko? to ko yau za kici ubanki dan sai kin gane baki da wayo, maza ki tashi ga chan wankin su kiyi maza kije ki wanke musu da hannunki ba wani inji da za a ƙara saka kaya domin suna kuɗewa daga yau ke zaki na wankin gaba ɗaya, zaki tashi ko sai na maujeki?
   Da sauri ta miƙe tana goge ƙwalla tace "to bari na sauya kaya,
   "Babu kayan da zaki sauya a jikinki zasu bushe maza fice ki bani guri.
  Fitowa tayi tana goge ƙwalla ta nufi bayan gidan nasu wanki ne tili guda wani kuka me raɗaɗi ne ya kufce mata, cikin zuciyarta tana faɗin "yanzu haka zan ci gaba da zama a cikin gidan nam kullum cikin azabtarwa? anya bazan gudu in bar gidan nam ba? To in na gudu ma ina zanje? kawai ki gudu ki bi duniya!…'''(Ka dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muki nam nada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞🤞🏻
https://t.me/joinchat/sCRdiaOyYgkyYmE0
'''Wannam shine link ɗin grp ɗina na Telegram kuyi hanzarin tsauƙe Telegram ku shiga domin samun littattafai na.'''🥰

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

*MASOYANA DON GIRMAN ALLAH KUYI MANA SUBSCRIBE ƊIN WANNAN CHANNEL DOMIN SAMUN LITATTAFAN SAURARE DA KOYON SANA'O'IN HANNU DA SAURAN SU NA GODE*👇🏻
https://youtube.com/channel/UCY1pIcI2DlVykTz57m6Q3TA

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Episode 06*

*…* Tsaye yake ya harɗe hannun sa a ƙirji ya zuba musu ido ko ƙyaftawa ba yayi, tsantsar bacin rai ne baiyane akan kyakkyawar fuskarsa wanda in har baka tsorata ba zaka ga kamar kyan sa ƙaruwa yayi ma, gaba ɗaya sunyi zuru² tsoro da fargaba, dana sa ni, nadama a tare suka duro cikin zuƙatan su Tuni suka fara fiƙi fiƙi da idanu, a hankali ya fara takowa izuwa cikin falon tafiya yake kamar me tausayin ƙasa ya iso gaban su a hankali kamar bazai yi magana ba suka ji ya furta "ku fara tsallan kwaɗo" ganin basu da niyar yi dan kamar ma basu ji ba cikin tsawa ya sake faɗin "dan ubanku nace kowa ya kama tsallen kwaɗo, daga haka yabi wani hanya da za ta  sada shi da cikin falonsa, fes yake kamar mamallakin wajen yana ciki sai ƙamshi yake, domin duk kwanan duniya Sweetie sai taje da kanta ta gyara masa, dan tasan halin yaronta da ƙin ƙazanta daɗin daɗawa sam bai son aikin ƴan aiki, hakan yasa dole ta amshi ramagar gyaran part ɗin nasa, komai na falon fari ne sol, room ɗin sa ya nufa a hankali ya fara rage kayan jikinsa ya saura daga shi sai ɗan gajeran wanda "Hasbunallahu wani'imal wakim" sai a wannam lokacin baiwa da kyawun halittarsa ta ƙara baiyana, fatar sa ce ta baiyana me matuƙar laushi da sheƙi tamkar na jariri ƙirjinsan nam cike da gashi me laushi da santsi ƙirarsa kana kallo kasan jarumin maza ne,😜 toilet ya faɗa ya haɗawa kansa ruwa me ɗimu da ƙamshi ya shiga ya ɗauki tsawon lokaci kafin ya kammala ya fito ɗaure da towel ɗaya kuma yana goge jikinsa da shi, gaban mirro ya zauna cream ya shafa a jikinsa me ƙamshi drower ya buɗe bangaren jallabiyoyin sa ya ɗauko ash color  da singlet  ya sanya ya feshe jikinsa da perfumes masu matuƙar sanyi da ƙamshi wani sihirtaccen kyau yake fitarwa wayoyinsa ya ɗiba ya sanya flat ɗin takalmi ya fito yana baza ƙamshi tuni wani ɓacin rai ya gushe daga zuciyarsa, dan shi tuni ya mance da su Nazmar da ya sanyasu tsallan kwaɗo sai da yaji yo kukan da su Samha suke zabgawa a falon
    Dan tun da ya basu umurni suka fara ba kama hannun yaro tun sunayi da ƙarfin su har ƙarfin ya fara ƙarewa, kuma ba halin su tsaya dan ko da wasa sukayi gigin tsayawa zai gane hakan yasa suka cigaba da fari Nabeeha ne ta fara fashewa da kuka dan bata saba da azabar sa ba hasalima bata gama saninsa ba sai kuma Samha ita ma ta fashe da marayan kuka, Huda ne ta ɗan daure ganin itace baba amma itama da azaba tayi azaba tuni ta fara zabgar kuka, kuka suke me matuƙar ban tausayi, Nazmar da Jawaad ne suka yi jarumta kasancewar su maza, amma Jawaad tuni idon sa yayi ja ba wai dan yana jin wahala ba sai dan na tausayin Nabeeha dan kaf ciki ita yake tausayawa, tun ƙarfe 9 da wani abu suke abu ɗaya har yanzu da ake neman ƙarfe 12 tuni fuskar Nabeeha yayi ja kasancesar ta fara, Samha ne tace "wannam shine mun gudu bamu tsira ba, mun gudu a chan muna tunanin a chan zai sauƙa ashe a nam zai sauƙa, wlh bazan kwana a gidan nam ba, dare ma a gidan Oum zata min. ta kuma fashewa da kuka.
   A hankali ya iso falon ko inda suke bai kalla ba yaje ya kashe sautin kiɗan da har yanxu yake ta faman aiki, sannam ya dawo ya zauna a falon ya buɗe system ɗinta ya fara turawa Shugaban ƙasa yadda taron ya wakana ta email ɗin sa, bai jima da zama ba Papa suka fito kamar yadda suka saba cike da ƙaunar juna, su Samha suka hango sai sharɓar kuka suke mamaki ne ya kamasu Sweetie tace "Innalillahi yau kuma me zan gani haka? Me yake faruwa? wa ya saku wannam aiki mata da ku? ko dai gamo kuka… bata ida ƙarasawa ba ta hangi Taufeeq a zaune a kan kujera sai danne²sa yake hankalinsa kwance mamaki ne ya cikata, a haka suka ƙaraso falon Papa yana dariya yace "ashe dodon nasu ne ya dawo, yau akwai ciwon jiki kenam" ya faɗa yana dariya.
Da sauri Taufeeq ya nufosu Sweetie ya runguma yana faɗin "I really missing you my Sweetie" bayan sa ta ɗan bubbuga tace "nima haka my son shine kuma sauƙa babu sanarwa, sakin ta yayi yaje yayi hugging ɗin Papa ma yana tambayarsa ya taron nasu ya wakana.
"Alhamdulillah" yace masa sannam suka zazzauna, daga haka bai ƙara cewa kanzil ba yaci gaba da aikin sa, Papa kuma yayi waje dan yasan laifi sukayi shiyasa bai ma tambaya ba ( dan shi haka yake in har babba yana yin hukunci to bai cika shiga safgar ba dan yasan akwai abun da suka yi ba banza ba) Sweetie ma kitchen ta shiga dan samawa yaron sana abun da zai ci dan tasan baxai ci na ƴan aiki ba,  har sai da aka ƙira sallar azhar sannam ya miƙe ya taka ya isa gabansu, sai da ya gama ƙare musu kallon da ɗai-ɗai shigar matan ya ƙara ɓata masa rai dan duka sanye suke da riga da wando wanda wandon bai je ƙasa ba ya kuma ɗamesu, cikin ɓacin rai yace "kowa ya tsaya" kamar dama jira suke tuni suka tsaya kallon Huda yayi wacce idonta ke cike da ƙwalla yace "You! come here" a hankali ta tako tazo gaban sa kallon Nazmar yayi yace "kai ma zo"
"Ga ni" ya furta yana kallon ƙasa (dan sam basa iya haɗa ido da shi) "Huda ina so ki yi masa mari masu kyau guda biyar in har baki masa me kyau ba ki tabbatar nizan miki har da ƙari.
Gaba ɗaya ido suka zaro dan basu tsammaci haka ba, cikin tsawa yace "oya! ki fara mana.
  Hannunta ta ware tayi masa mari guda biyar lafiyayyu dan sai da ya rintse ido, kallon sa yayi yace "oya kai ma kayiwa Samha guda biyar me kyau"
  Tuni Samha ta fashe da kuka tun kan afara guda biyar ya mata wanda sai da ta saki fitsari tsabar azaba, ita ma ya

Please Login or Register in order to submit comment