Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

upstair, Jawaad ne ya kama kunnan Ka'aaf yace "me yasa ka gayawa wannam Man ɗin ba munce kar ka kuskura ka gaya masa ba, to ai shikenam ka jawa kanka ba kai ba gift, kuka Ka'aaf ya saka yana faɗin "ni wlh sai an bani gift ɗina baxan yarda ba ya nufi part ɗin Yaa Taufeeq a guje yana cigaba da kuka, Nabeeha ma ɗakin su ta nufa ranta a ɓace.
     Zaune yake gaban mahaifinsa da kuma Kawun Papa da tun ɗazu su ƙirasa yafi 5mnt da zuwa amma har yanzu Papa baice masa komai ba, shima bai ce masa kanzil ba, sai yanzu Papa ya nisa yace " *Minister Abdullahi Nasir Adam Salwa (Taufeeq)!* a hankali Taufeeq yace "na'am Papa gyara zama yayi dan yasan magana ne muhimmanci za suyi tun da Papa ya ƙira full name ɗin sa yasan ba batun wasa magana ce gaggaruma, nisawa Papa yayi yace "na tabbatar daga ƙiran sunanka nasan kasan maganar da za muyi me matuƙar muhimmanci ne a gareni da kuma kai baki ɗaya dan haka ina so ka saurare ni da kyau ka kuma ɗauki maganata ka bi umurnin da zan baka kana dai jina ko?
   Taufeeq da jikinsa ya gama sanyi jin furucin mahaifin nasa yasan maganar bata wasa bane cikin breaking voice yace "eh Papa in sha Allahu ni mai biyayyane a gareka.
   "Ba wani magana bane da ni da ɗan uwa na Ahmad munyi  alƙawari zan haɗa ka da ɗiyarsa Nabeeha aure, tun yana da rai yaso hakan ya faru amma Allah baiyi ba saboda ƙarancin shekarun ta, kai kuma a lokacin ne ka fara gudanar da aikin ka na Minister, yanzu ma wani abu ne ya ɓullo yasa na kawo lamarin a yanxu gudun kar abun ya zarce ƙima, to Alhmdllh na dai yiwa tufkar hanci dan haka na sanar da kai ka kwana da sanin nam da wata uku masu zuwa in sha Allahu za a ɗaura muku aure, in ma Abujan zaku tare tun da a chan aikin ka yake, in ma a nam zaka barta kana zuwa wannam duk ya rage naka ni dai dama abun da na ke son sanar da kai kenam, Kawu hakan yayi dai ko? Murmushi Kawu yayi yace "hakan yayi sosai Nasiru Allah ya baka ladan zumunci tabbas ka kusa ciki alƙawarin ɗan uwanka haka ake son zumunci wlh. 
   Taufeeq da tun da Papa ya ƙira kallamar haɗi shi da Nabeeha tuni zuciyarsa ta fara azalzalarsa jijiyoyin jikinsa ya fito ruɗu² idanunsan nam ya juya yayi jajazir kamar garwashi zufa ne ta ko ina yake tsattsafo masa, ji yake kamar ya ciro zuciyarsa ko zai huta da azalzalar da take masa, ji yake kamar ya ɗaura hannu a ka ya rusa ihu ko zaiji salama, fata yake a zuciyarsa Allah yasa mafarki yake ba gaskiya ba,  in ko mafarki ne yayi sallama da bacci har ya koma ga mahaliccinsa
Bai tsinke da lamarin ba sai da yaji Kawun mahaifinnasa yana sawa Papa albarka jikinsa na tsuma ya isa wajen Kawun Mahaifin nasa ya riƙe hannunsa yace "don girman Allah Kawu ka jiƙaina ka min rai kasa ya soke zancen haɗin nam wlh bana son ta ko kaɗan hasalima bana ƙaunarta na tsani yarinyar nam bana ƙaunar auren zumunci bashi da wata fa'ida ba riba a cikinsa, nam ya fara karanto masa abun da ya faɗawa Sayyid ya ƙara da cewa wlh kwanan nam akwai case ɗin da na kashe akan auren zumunci Yaron ya zo ya same ni har kuka yake kan cewa an tilasta masa ya auri ƴar uwarsa kamar ni ɗin nam dai, shi kuma ba ya sonta, ita ma bata son sa amma iyayen sun ce dole sai anyi, to ka ga wannam ba dai-dai bane, a matsayin sa na wayayye me ilimi da yayi cuɗanya da mutane da ƙabilu dabam-dabam, kamata yayi a nemi shawararsa, in ba haka ba a ƙarshe sai a zo ka jefa ɗanka cikin matsala kasa ya rinƙa jin haushin ka, ya kuma tsani matar da aka tilasta maka, ita ma ya zamana tana muku fatan ku mutu su huta su raba aure, kun ga hakan ai ba a haɗa zumunci ba sai dai an raba zumunci, dan Allah Kawu ka saka baki pls help me.  
    Tun da ya fara magana Papa yake kallonsa cike da mamakin ɗan nasa, bai taɓa tunanin akwai ranar da Taufeeq zai iya ja da umurnin da ya bashi ba ko a mafarki bai taɓa ba, sai kuma yau gashi nam a gabansa yana nuna masa sam bazai bi umurnin sa ba, Kawu kallonsa yayi yace "Taufeeq banyi tunanin gardama daga gareka ba, nayi tunanin zaka karɓi umurnin mahaifinka hannu biyi bai kamata ka watsawa mahaifinka ƙasa a ido ba cike yake da yaƙinin duk umurnin da ya baka kai me biyayya ne a garesa, gaskiya ka bani mamaki wlh wannam sam ba halin da na sanka da shi ba ne, Taufeeq da zuciyarsa take ƙara tafarfasa ji yake kamar ya shaƙe wuyan tsohon har sai ya daina numfashi ko zai hutu...'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muku nam bada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

_Share Fisabilillah_👏🏻

*ONE LOVE*💞🤞🏻
.
*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

_Wannam shafin gaba ɗaya naku ne *SARAUNIYA HERWIEY* da kuwa *ZARAH ABBA KYARI* walle saboda ku na yi ina matuƙar alfahari da ku ina jin daɗin hot comment ɗinku ina yinku over_✨🌹

*Episode 10*

*…* "Wlh baka ga dogon jawabin da ya dinga yiwa Sayyid akan haka ba, ni dai wlh ban jin son zai amince da wannan maganar" Ajiyar zuciya Papa ya sauƙe sannam yace "Yaya ai ko yaƙi ko ya so aurensa da Nabeeha babu fashi dan sai anyi gwara ma ya bar wannam aƙidarsa ta ƙin auren zumunci. "To Allah dai ya baka ikon cika wannam alƙawarin da ka ɗauka, Allah yasa ya amince ba tare da ankai ruwa rana ba, (ni ko nace wai ku ta Taufeeq kuke kun mance Nabeeha ne da sam bata son haɗa hanya da shi?) Lol.
Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani sukayi sallama akan Oum kar ta yiwa Sayyid magana zai samesa da kansa ya masa bayanin da zai fahimta, da daddare kuwa Papa ya ƙirasa suna zaune a parlon sa, Papa yana kan kujera Sayyid na risine a kan carpet Papa ne ya kallesa a nitse ya fara magana "Sayyid ina so ka saurareni da kunnen basira, kar ka dubi maganata a bai² kayi masa duba na tsanake, Kai Nabeeha da kuma Taufeeq duk ƴayana ne babu bare a cikin ku, ina kuma alfahari da ku, ba komai yasa nake maka wannan maganar ba sai dan share wata ƙura data taso take son bulemu gaba ɗaya, Sayyid! Papa ya ƙara ƙiransa a hankali, Sayyid da tun da Papa yake magana gabansa ke faɗuwa ya ɗago a hankali ya kalli Papan nasu cikin cool voice yace "na'am Papa" "Sayyid ina so ka cire son Nabeeha a zuciyarka ya zamana so na ƴan uwanta ka ne a tsakanin ku, saboda nayi wa mahaifinta alƙawarin zan haɗata da M.T aure in da bamuyi wannam alƙawarin ba da babu abun da zai hanaka auren Nabeeha amma kuma ƙaddara ta riga fata Allah yasa ba itace matarka ba, in sha Allah zaka samu wacce tafi Nabeeha, tun da jimawa na fara zargin kana sonta amma ganin bani da hujja yasa na bar maganar da tun farko hakan ma bazai faru ba zan yiwa tufkar hanci, kayi haƙuri my son. Sayyid da yayi zaman dirshan ya tisa Papa da ido ko ƙiftawa bayayi ya zama kamar mutum-mutumi, tunda Papa ya furta cewa ya cire Nabeeha a zuciyarsa jinsa da ganinsa da kuma hankalinsa suka daina aiki na tsawan mintuwa, gaba ɗaya baya fahimtar me yake cewa. Papa ganin yadda Sayyid yayi kamar ma baya jin me yake faɗa, da ɗan ƙarfi yace "are you okay Sayyid" da hanzari ya ɗagowa yace "sure Papa, but ni dai gani nake kamar in aka haɗasu kamar akwai matsala Papa duba da yadda sam basa jituwa kuma shi baya son auren zumunci, kamar dai baza su jitu ba gaskiya" Murmushi Papa yayi yace "kar ka damu son ko suna son junansu ko basa so dole na cika wannam alƙawarin, in yaso daga baya gaba ɗaya su koyi son junansu, kai ma ka fito da wata pls son sai a haɗa bikin baki ɗaya, murmushin ƙarfin hali yayi yace "a'a Papa ni kam kuma ba yanzu ba sai kuma wani lokacin in Allah yasa muna da rai da lafiya ya faɗa yana furzar da iska, "sorry son" Papa ya faɗa cike da tausayinsa sai yanxu yake jin haushin jinkirin da yayi na rashin auren tun da wuri saboda ƙarancin shekarun ta da kuma yanayin aikin M.T amma yanzu kam dole ayi a gama, Sayyid ne ya katse masa zancen zucin da yake yace "Papa zan wuce sai da safe Allah yasa haka shine mafi alheri. "Amin son Allah ya maka albarka.
  Da ƙyar yake iya ɗaga ƙafarsa saboda nauyin da take masa ga wani irin duhu da yake gani, babu kowa a parlon har zai fita yaji muryar Nabeeha tana faɗin "Yaa Sayyid yaushe kazo? juyawa yayi yaga har ta iso inda yake, kallonta yayi da idanunsa wanda suka sauya kala yayi murmushin ƙarfin hali ya juya ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, mamaki ne ya kamata ta jima tana tsaye tana kallonsa har ya ɓace daga ganinta, baki ta turo sannam ta juya ta koma ciki dafatan Allah yasa lafiya.
             Yana isa gida Oum ya gani zaune a parlor tana kallon tv a hankali ya ƙarasa inda take zubewa yayi a gabanta ya fashe da matsanancin kuka me ban tausayi kamar ƙaramin yaro, hankalin Oum in yayi dubu sai da ya tashi, domin tun lokacin mutuwar mahaifinsu bata sake ganin kukan ɗanta ba sa a wannan lokacin, da sauri ta kamosa ta zaunar dashi kusanta kansa yana kan cinyarta,tana ɗan bubbuga kansa da alamun rarrashi, cikin kuka yake faɗin "ashe Oum Nabeeha ba itace za ta kasance uwar ƴaƴana ba, ashe duk shirin da nake ba ita bace zata kasance tawa ba ta har'abada ba, ashe ta ɗan uwana ce" Cike da tausayin ɗan nata Oum tace "kayi haƙurin son Allah yayi ba kai ne mijinta ba ɗan uwanka ne, me zai sa baza ka rungumi ƙaddarar da tazo maka ba, kar ka mance kowa a duniyar nam, rabonsa yake ci baya cin rabon wani kayin haƙuri Allah zai musanya ma da wacce ta fita. "A'a Oum bazan taɓa samun wacce ta fita ba" "My son kar ka fidda ƙauna daga rahamar ubangiji in sha Allah zaka samu wacce ta fita, haka Oum tayi ta bashi baki da nasihu a haka har ya saduda suka koma wata hirar amma a ransa ya gama yanke hukunci ƙasar zai bari dan bazai iya zama yana kallon Nabeeha a matsayin matar ɗan uwansa ba.
Washegari kuwa ba tare da sanin kowa ba ya tarkata duk wani abu nasa me mafani ya ɗaga birnin London sai da yayi wanka ya hutu ya ƙira mahaifiyarsa ya shaida mata inda ya tafi saboda kar hankalinta ya tashi, ya ƙara da cewa "Pls Oum kar kice in dawo wlh bazan iya zaman Kaduna ina kallon Nabeeha ba kimin rai" Murmushi Oum tayi tace "na maka rai My son dan ita kanta ta tausayawa yaron nata, nasiha tayi ta masa akan ya kula da addininsa da kuma lafiyarsa kar yasa abun a ransa, yace "in sha Allah duk da yasan abu ne mawuyaci ya iya cire abun a ransa amma ya ma ta alƙawarin zai kwatanta haka,sun jima suna waya kafin yayi mata sallama.
  Papa ne zaune shi da Sweetie bayan ya gama shaida ma ta abun da yake faruwa daga farko har ƙarshe ya ƙara da cewa "ni dai yanxu bana son auren nam ya ɗau lokaci tunda kin ga irin abun da yake faru gaba ba a sam me zai faru ba" Ajiyar zuciya Sweetie ta sauƙe tace "ikon Allah! Allah ɗaya gari bam²
      To yanzu Papa'n su anya haɗin nam zai yiwu kuwa? duba da yadda naga sam babu jituwa a tsakaninsu kamar da matsalafa ni nasan halin son kar yaje ya cutar musu da ƴa mu shiga uku fa, Papa yace "in sha Allahu babu abun da zai faru sai alheri duk da nima ina tunanin haka amma mu bisu da addu'a kawai ina ga hakan yafi. "To Allah yasa a dace, Allah kuma ya nuna mana lokacin biki ai ni nafi kowa farin ciki akan wannan haɗin kawai tsoro na yadda basa jituwa ne. Cewar Sweetie tana murmushi, Papa ne ya jawota jikinsa yana faɗin "nima kin manta auren zumunci mukayi? dan haka ki kwantar da hankalin ki babu abun da zai faru, fuskarta ta rufe tana ƴar dariya da alamun kunya Lol.

    Yau ta kama Juma'a tafe yake cikin shirin sa na ko da yaushe sai baza ƙamshi yake, sauri yake amma sai ka lura da hakan zaka gane saurin yake dan tafiya yake kamar bazai taka ƙasa ba wai shi nam sauri yake kar ya rasa salla dan har an gama huɗuɓa kamar daga sama yaji ya gwaru da mutum bai gama sanin waye ba yaji abu me sanyi ya zubu a jikinsa, a hankali ya kalli kayansa yaga duk ya ɓaci da yogurt tuni ransa ya ɓaci, ita ko da sauri taja baya tana zaro ido cike da tashin hankali, baki ta turo tace "sorry Yaa Taufeeq ai naga kai ne kayo in da nake, ni ba ni nayo wajenka ba, kuma kana tafiya ne baka kallan gabanka. Nabeeha ta faɗa tana ƙara turo ɗan ƙaramin bakinta, wani ƙarin ɓacin ran ne yaji ya dirar masa kunnenta ya kama ya murɗa ta saki wani irin ƙara bai sake ba yace "ni dan ubanki sa'anki ne? ko kinga ina miki wasane? wllh ki jirayi dawowa na sai kin gane baki da hankali daga haka ya tura gefe ya koma cika da sauri, a gurguje ya sauya kayansa zuwa jamfa tazarce "masha Allah" ya fito sak! yana fitowa suka buɗe masa Back seat ya shiga suka fice daga gidan a guje saboda ya tuni an shiga, har yanzu still take a tsaya hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, Sweetie ne ta fito cikin shiga ta alfarma gani Nabeeha a tsaye ta ƙaraso tana faɗin "me zan gani haka? ke da waye?"  Turo baki tayi tace "ba Yaa Taufeeq bane ya murɗemun kunne kuma ba ni na bugeshi ba shine ya tawo baya kallon gabansa ya bugeni har yogurt ya zube masa a jikinsa. Ta ƙarasa faɗa tana ƙara turo baki gaba, Sweetie dai haɗin da aka musu ne ya faɗo mata, dan tasan akwai ƙura a gaba, murmushi tayi tace "wlh ke bakya gane halin son har yanzu baya son kuna rashin ji yanzu kinga sauran ƴan uwanki suna haɗa hanya dashi ne ma, su Samha sam yanxu sun daina zaman parlor in kinga sun zauna to baya nam yana dawowa kuwa zasu bar wajen hankalinsu kwance amma ke kamar tsutsa ki wulga-chan-ki-wulga-chan kamar walƙiya. Cike da shagwaɓa tace "to Sweetie mutum bazai fito waje ya wataya ba sai dai ya ƙunshe a ɗaki kuma ma fa bani nayo ta wajensa ba shine yaxo wajena, ta ƙare maganar cike da shagwaɓa, dariya Sweetie tayi tace "to shikenam ki rinƙa dai kiyayewa tunda kin san halinsa. "To Sweetie " suna zaune su Nazmar suka shigo dining suka nufa su taje ta ƙira su Samha suka ci abinci, bayan sun gama ne suka dawo parlor aka fara hira, hira suke akan birthday partyn Nabeeha da kuma Ka'aaf saura sati biyu sun gama tsara komai sai dai roƙo suke Allah yasa ranar Yaa Taufeeq baya gari ta yadda zasu wataya son ransu, suna cikin maganar suka ji sallamarsa shi da Papa da hanzari su Samha suka miƙe har suna gwaral da juna ita da Huda suka nufi ɗakin su da ido ya bisu dan yasan me suka guduwa, Nabeeha dai tana zaune duk da ƙirjinta dake bugawa amma ko gezau batayi ba balle ta bar wajen, kallonta yayi ya taɓe baki, su Nazmar ne suka gaida shi Ka'aaf ne yace "Yaa Taufeeq birthday partyn mu ni da Aunty Nabeeha saura 2weeks ina za ka banu gift? Nabeeha, Jawaad, Nazmar hatta Sweetie sai da ta zaro ido suna rufe baki.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

"Aure kuma Baffa ni kan gaskiya bana son Yaya Sadiq dan Allah kar ku haɗani dashi, ku barni da iya maraicina ya isheni dan Allah kuyi haƙuri, ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani marayan kuka, me ban tausayin me karatu, gaba ɗaya ɗakin suka ɗau salati su Mama Marka harda tafa hannu tace "ke dan uwarki wan mahaifin naki kike faɗawa haka? ko da yake ba mamaki dama halin iyayenki ne gardama da taurin kai da rashin kunya. Baffa ne yace "to ki buɗe kunnenki da kyau aure babu fashi nam da sati uku ko kina so ko bakya so dama na ƙira ki ne dan na faɗa miki ba wai dan naji kina sonsa ko bakya sonsa ba, na gaya miki ne dan ki fara shiri ki kuma kwana da sanin zaki auresa, Baffa Gambo yace "ke da kika tsinci dami a kale ma, in ba shi ɗin ba ma da zai taimaka miki, ke kina ganin zaki auru ne? ko kina ganin zaki samu miji kamarsa ne ai sai dai ne tallan rake ko mazarƙwaila, godiya ya dace ki masa ba ki zauna zaki mana rashin kunya ba, maza tashi ki ɓace mana a nam tun kan na mangareki. Da sauri ta miƙe ta nufi ɗakinta ta faɗa kan gadonta ta saki wani marayan kuka, kuke take sosai tana faɗi "Allah na tuba ya Allah wani laifi na maka da ka jarrabeni da irin wannam lamari, Allah ka ɗauki raina ya Allah bazan iya cigaba da zama a wannan duniya taka ba, rabbi ka kawo min ɗauki ya Allah bani da uwa bani da uba ban san dangin mahaifiyata ba dangin mahaifina sun tsaneni, ya Allah kajiƙai na ka min rai... Wani marayan kuka ta kuma fashewa dashi, sai da tayi me isarta babu me rarrashinta, hakan yasa ta rarrashi kanta toilet ta shiga tayi wanka ta ɗauro alwala tazo tayi ta salla tana kai kukanta wajen mahaliccinta roƙo take Allah ya ɗauki ranta ita kan ta huta, sai da taji ƙafafunta sun gaza ɗaukarta sannam ta dakata, taci gaba da kukanta kwana tayi cir tana kuka idon nam ya kumbura sosai yayi ja, da safe ta kuma yin wanka ta nufi kitchen tana hawaye a haka ta kammala musu ta jeresa bara ɗibi komai ba, dan bata jin zata iya sa wani abu a hanjinta roƙo kawai take ta mutu ta huta, haka tayi wunin ranar ba ci ba sha, da yamma tana kwance taji shigowar mutum ko ba a faɗa mata ba tasan waye turarensa ya sanar da ita, tsaye yake a kanta yana sakin murmushi, da sauri ta tashi jikinta babu ƙarfi, ta iso wajensa gwiwoyinsa ta riƙe tana kuka tace "dan girman Allah Yaya kace musu baka so na baka ƙauna ta kar suyi wannam auren don Allah na roƙeka Yaya kajiƙai na! roƙonsa ta rinƙa yi tana kuka me ban tausayi murmushi yayi dan ko kaɗan bata bashi tausayi ba, kamota yayi ya zaunar a bakin gadon shima ya zauna yana goge mata hawaye, bata hanasa ba dan gani take kamar ya aminci, bata daina kukan ba yace "to naji ki daina kukan nam" Da sauri ta goge hawayenta tace "Na daina Yaya" Murmushi yayi yace "kinci abinci ne?  girgiza masa kai tayi tace "bana jin yuwa Yaya. "um-um in har kina so na haƙura sai kin ci abinci sosai oya sauƙo kici gashi nam na ɗibo miki, sauƙƙowa tayi da sauri ta fara ci da sauri-sauri dan tabbas tana jin yunwa kawai tashin hankalin da take ciki ne bazai barta ta iya cin wani abu ba, tuni ta taɗa plate tasha ruwa ta zuba uban gyatsa, tunda ta fara yake kallonta yana murmushi ga wani abu da yake ji  a game da ita so da kuma sha'awa, ɗagowa tayi tace "Yaya ka gani na cinye tas! dariya yayi marar sauti yace "aiko dai na gani kin cinye ko kefa my preety  yanzu taso kizo ki zauna ba musu tazo kusa dashi ta zauna, hannunta ya kamo yace "yanzu da gaske bakya sona baxa ki aure ni ba? ya faɗa yana kallonta, sunkuyar da kai tayi tace "Yaya kayi haƙuri ni dai kawai kaje kace musu baka so na kaji" Ta faɗa wa su hawayen na ƙara zubo mata,  murmushi yayi yace "Yarinya kenam yanxu kina nufin naje na samu su Baffa nace ban sonki na fasa aurenki? to bari kiji ko gawarki ce sai an ɗaura min aure dake ko kiso ko ki ƙini duk ɗaya amma aure ba fashi,  hannunta ta ƙwace daga rinƙon da ya mata cike da mamaki tace "haba Yaya ba haka mukayi ba dan Allah kar ka juyar da zancen ka rufamin asiri... '''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muku nam ba da jimawa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞🤞🏻

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul💋'''

*Episode 13&14*

*...* Kawu yaci gaba da cewa "wlh ka bani mamaki Taufeeq ni kai na ka bani kunya bare kuma mahaifinka da yake matuƙar alfahari da kai, ni dai shawaran da zan baka shine kawai kayi haƙuri ka rungumi auren nam in sha Allahu za kaci ribar sa ina tabbatar maka kaji ko?

    Taufeeq da haushin tsohon ya gama kamashi bai iya amsa masa ba, Papa ne yaja goron numfashi cikin dattaku ya fara magana "Taufeeq in dai har ni na haifeka umurni na ke baka ba shawara ba ka fara shirye-shiryen auren ku da Nabeeha  kai wlh nam da 2weeks zan ɗaura maka aure da ita, in har na isa da kai, in ma ban isa da kai ba zan gani get out kar in saɓa maka yanzun nam.
  Fitowa yayi duk ransa a dagule bayan gidan ya nufa a bakin swimming pool ya zauna ya kamo lips ɗin sa na ƙasa sai tsotsa yake, lokaci zuwa lokaci yake furzar da iska gaba ɗaya kansa ya gama kullewa tunanin mafita kawai yake amma ya rasa, hannu ya sanya ya cire sigari a aljihun sa ya kunna ya sanya a bakinsa cikin wani irin salo gwanin birgewa yake shan sigarin yana furzar da iskar ko rabi bai gama sha ba ya jefar tare da jan tsaki, Nabeeha da tun zuwansa take zaune a wajen tunanin Yaa Sayyid ne ya addabeta tun ranar da yazo ya shareta har yau bata

Please Login or Register in order to submit comment