Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juyo ya shigo bedroom ɗin har ta tashi ta gyara zama tana haɗiye miyau
Kallonta yayi da mamaki sannan ya miƙa mata ya zauna amsa tayi ta buɗe wani ƙayataccen roba ne me kyau an cikasa da ferfesun hanta, tun kan ta fara ci yawunta ya fara tsinkewa da sauri sauri ta fara cin zallan hantan me matuƙar daɗi da ƙamshi ganin ta kusan tada roban ne ya ɗauke yana faɗin
"Haba acici ai kya bari haka kar cikin ki yayi bindiga"
"Dan Allah ka bani na ci wlh ban ƙoshi ba ta faɗa cike da shagwaɓa"
Ganin har idanunta sun cika da hawaye ne yasa ya miƙa mata ta cinye tas! sai dai cikin ikon Allah yanzu bata yi aman ba, har da suɗe roban ba wai dan ta ƙoshi ba sai dan kawai ya ƙare ne babu yadda ta iya, kamar yasani yace
"Ko baki ƙoshi ba ne"
Da sauri ta ɗaga kanta yan faɗin
"Eh wlh kamar banci komai ba Abwaan"
"Sannu Ƴar tsana baby Allah ya miki albarka.
Kallonsa tayi da mamaki sai kuma tace 
"Amin" dan a duniya babu kalmar da take sanya ta farinciki kamar kace mata Allah ya mata albarka tana matuƙar jin daɗi.
Miƙewa yana faɗin 
"Maza ki kwanta kinga dare yayi gobe sai muke asibiti muji meye matsalar da kike amai haka.
Kallonsa tayi kamar za tayi kuka tace
"Abwaan kar ka tafi pls kazo mu kwanta tare sanyi nake ji.
Ba musu ya kashe wutan ɗakin dan dama hakan yake so dan ko ɗazu ya kasa bacci saboda kewarta, gefe da ita ya kwanta ya rufe su a hankali ta mirgino ta shige jikinsa a tare suka sauƙe ajiyar zuciya, jikinta yaji zafi zau, shima rungumeta yayi a haka sukayi bacci duk da yana cike da buƙatar ta, amma dole ya haƙuri saboda jin zafin jikinta da yaji kuma sannan bata sha maganin da yake sa mata ba.
Washegari tun sassafe ta tadashi akan yunwa take ji, Osim ya turawa text kamar jiya ba jimawa sai gashi ya kawo, shirye yaje ya amso mata ya miƙa mata ferfesun hantan ne irin najiya sai dai yafi na jiya wannan roba biyu ne sai biredi da tea me kauri, zama tayi sai da ta kusa tada roba biyun nan sannan ta haƙuri ta ƙarasa da tea, tunda ta fara yake kallon yadda take cin abincin haka kawai ya gaza ɗauke idanunsa a kanta ji yayi yadda take cin abincin ya birgesa duk da da sauri sauri take kamar za a ƙwace mata.
Tana gama ko kamar jira yake ta fara jin amai ya taso mata da sauri ta miƙe ta shige bathroom ta fara kela amai kamar zata fitar da ƴan hanjinta sai da ta amayar da abun da taci tas, sannu kawai yake jera mata ya ɗagota keta ta sulale a jikinsa ta suma.
Ciki da tashin hankali yake jijjigata amma ko motsi bata yi dawo da ita kan gado yayi ya kwanta ya ɗauki waya ya ƙira Osim ya shaida masa gashi fitowa za su fito.
Mayafi ya sanya mata ya ɗauketa kamar wata ƴar baby ya fito, kowa na ta harkokin gabansa ba kamar najeriya bane da wasu zasu har duk abun da suke su zubo maka idanu, kallon su kawai suke ganin dacewar da sukayi ba wai dan ɗaukarta da yau ba, yana fita ya samu Osim ya buɗe masa backseat sanyata yayi sannan ya shiga yana faɗin 
"Oya kai mu asibitin dake kusa da mu"
Gaba ɗaya ma ya mance akwai asibiti a cikin hotel sai da yaga Osim yayi parking a cikin asibitin ya tuna dan gaba ɗaya ya ruɗe, da gudu nurse biyu suka zo da gado suka sanyata suka nufi emergency
Basu wani ɗau lokacin ba suka fito da ita a gadon majinyata suka nufi wani ward da ita, wani likita ne ya fito yana faɗin "wa ya kawo wannan?
Da sauri Taufeeq yace 
"Gani nam!
Kallonsa likintan yayi sai yanzu ya gane sa yace
"Sorry sir ban san kai bane da bamu barka a wajen nan ba.
"No babu komai meye matsalar matata kawai nake son ji!
Ya faɗa cikin ƙosawa da maganar likitan.
Likitan yace 
"Sir mu isa daga office sai na maka bayani"
Duk cikin yaren nasara suke
Ba musu yabi bayan likitan sai da Taufeeq ya zauna sanna shima ya zauna domin Likitan yasan waye Taufeeq dan shima ɗan Najeriya ne.
Nan Likitan cikin fara'a yace
"Congratulation sir! ina taya ka murnar samun ƙaru wife ɗinki tana da ƙaramin ciki na 2weeks, bayan haka bata da wani matsala.
Taufeeq duk da yayi hasashen haka amma sai yanzu ya tabbatar miƙewa yayi ya kalli gabas tare da kai goshinsa ƙasa tare da yayi Allah sijjada na gode masa da ni'imar da tayi masa, murmushi Likitan yayi yana kallonsa sai da ya gama addu'a sa sannan ya dawo yace 
"But komai taci sai tayi amai fa?
"Eh ita haka nata cikin yazo mata da shi, sai dai kar hakan yasa bata jin abinci ko za taji tayi aman ta daure taci c ko tayi aman ba duk abun da taci ba ne zai fita dole babyn zai ɗan samu wani abu, yanzu in ta shanye ruwan nan za ku iya tafiya.
Kallon Taufeeq yayi duk da yana cikin farin ciki amma fuskar sannan dai tana nan kamar kullum a hankali ya sanya hannunsa a aljihu a cire wayansa tare da miƙawa likita yace
"Sanya min account ni ɗinka"
Jikin likita na rawa ya karɓa ya sanya dan yasan kakarsa ta yanke saƙa.
A take yaji alert na miliyon biyar
Hauka ne kawai likita da bayyi ba duk da yana da rufin asiri amma ba ƙaramin daɗi yaji ba nan ya dinga yiwa Taufeeq godiya tare da addu'ar Allah ya sauƙi wife ɗin sa lafiya.
Da "Amin ya amsa masa ya fece direct ward ɗin da aka kaita ya shiga, ita kawai ne a ɗakin kwance take tana bacci fuskar tan nan tayi wata fayau ta faɗa, a bakin gadon ya zauna ya ƙurawa fuskarta ido yana jin wani irin sihirtaccen sonta na shigarwa duk da shi dai bai sani ba amma yaji wani abu yana ziyartar zuciyarsa me sanni a duk kallonta da yake yi, hannunsa ya zira a cikin rigarta ya shafo cikinta da yake lafe a fatar jikinta kamar ba komai amma a haka wai mutum ne sukutum a ciki, idanunsa ya lumshe yana yawo da hannunsa a cikinta motsin da yaji ta fara ne yasa ya buɗe idanunsa.
A hankali ta fara buɗe idanu ta sauƙe su a kansa shima ita yake kallo, kallon ɗakin ta fata ganin ba inda suke bane tace
"Abwaan me ya kawo mu nan?
Rasa abun da zai ce mata yayi sai ya tsinci kansa da faɗin
"Na kawo ki ne a dubamin lafiyarki da na babyna!
Babynka kuma wani irin Babynka?
Murmushi yayi wanda ya ƙara bayyanar da sihirtaccen kyansa zaro ido Nabeeha tayi tare da faɗin
"Wow! Abwaan haka dariya take ƙara maka kyau shine bakayi kake sama kullum fuska a ɗaure kamar hadari"
Murmushi ya kuma yi dan yau bai jin akwai kalmar da za a faɗa masa da zai ɓata masa rai yace
"In har kina so kullum zan na miki matuƙar zaki kulamin da babyna.
Shagwaɓe fuska tayi tace
"Eh wlh ina so amma wai wani babynka kake faɗa ne ban gane ba?
"Uhum za ki gane ranar da yazo duniya.
Ya faɗa kamar bashi yayi maganar ba
Da mamaki take kallonsa tace
"Dan Allah ya gayamin mana wlh ban gane ba.
Ta faɗa kamar za tayi kuka
Cikin cool voice yace
"To kina da ciki na tsawon sati biyu wannan dalilin yasa duk abun da kikaci sai kinyi amai amma yanxu wannan ruwan da aka sa miki da maganin nan za su rage miki aman.
Ya ƙarasa yana ajiyar zuciya domin dogon maganar da yayi
Tun da ya fara maganar take kallonsa da mamaki cikin kiɗima da matuƙar damu ta miƙe tana faɗin
"Wai kana nufin ni nake ɗauke da cikin wanda ba ya so na a duniyar nan? Ni nake ɗauke da cikin wanda ya tsaneni baya son ganina ina murmushi a faɗin duniya ni ni ni!!…






★★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★



"Kamar ni Lamir kike tunanin zanyi soyayya da ke to in mafarki kike ma gara ki farka kina dai jina Amatullah! Amatullah tun da ya fara magana taji duniyar tana wani irin juya mata hakan yasa ta sanya a handfree Zarah taji har ya gama, cikin ƙarfin hali Amatullah tace
"Lamir me kake faɗa ne haka dama kace kana so na ne domin ka wulaƙanta ni? ashe ba don Allah kake so na ba Lamir? Sai da ka bari zuciyata ta fara sonka sannan zaka zo min da wannan maganar to tsakani na…
Da sauri ya katseta ta hanyar faɗin
"Da kata Jinin jikina wlh wasa nake miki dan Allah kar ko min Allah ya isa.
Wani dogon ajiyar zuciya suka sauƙe ita da Zarah tare da murmushi amma a wayan ta ƙara ɓata fuska tace
"Gaskiya Lamir wannan ba wasa bane daga furucinka wataran na sai munyi aure zai sakeni sannan daga baya kace wasa kake dan haka kawai kayi haƙuri Allah ya raba kowa da rabon sa tayi sauri ta katse wayar ta kalli Zarah kamar za tayi kuka tace
"Wlh baki ji yadda gabana yake dukan tara-tara da ya faɗamin wannan maganar.
Dariya Zarah tayi tace 
"Wlh ni kai na gaba ba ƙarin faɗuwa yayi ba, amma me yasa kika sanar dashi kun rabu?
Saboda yaji abun da naji kuma in banyi masa haka ba ai ya dinga min haka kenan.
Suna a haka ya ƙira yafi sau goma amma taƙi ɗagawa ƙarshe ma ta miƙawa Zarah wayar ta gargaɗeta kuma da kada ta ɗaya wayar ba jima sauƙon text ya shigo Zarah ce ta buɗe ta fara karantawa da ƙarfi kamar haka



Son da nake yi miki tamkar madubi ne a cikin zuciyata, do da a ce ya fashe, idan kika sanya idanuwanki a kansa za ki tarar da ke a cikinsa, Son ki ya zamo jini a jikina ya bi ta jijiyoyin jikina ya narke a cikin zuciyata, wlh bazan iya rabuwa da ke ba ke tamkar duniya tace dole sai dai zan rayu dan Allah kiyi haƙuri abar ƙaunata😥.



Dariya Zarah tayi tace 
"Allah sarki soyayya kiyi masa uzuri pls kin san Lamir sarkin wasa ne gashi da tsokana.
Ɓata fuska Amatullah tayi tace
Barshi kawai sai ya gama jin abun da naji tukunna.
Ba jimawa wani saƙon ya ƙara shigowa daga Lamir kamar ɗazu da ƙarfi yadda tasan Amatu za taji Zarah ta fara karantawa kamar haka



Dan Allah! Dan Allah! Dan Allah!! my Amaa ki jiƙaina kiji tausayi ki amsa min wallahi wallahi!! wasa nake miki ni kaina sai yanzu naga sam hakan bai dace ba amma ni na kasance mutum me yawan tsokanar makusanci na dan Allah kiyi haƙuri wlh bazan iya ruwa babiu keba wlh in har baki ɗaga ba yanzu zaki ganni a gidan ku.




Bayan Zarah ta gama ne ta kalleta tace 

"Ke Malama sham ƙamshin ya isa haka tun da har ya baki haƙuri kin dai ji abun da ya faɗa wlh zai iya zuwan yauwa kinga gashi ma yana ƙira dan Allah ki amsa a wuce wajen.

Juya baya Amatu ta dake haka yayi ta ƙira amma san taƙi ta amsa ana haka suka ji sallamar Kausar da sauri Amatu ta miƙe tana raba idanu dan duk a tunaninta ba zuwan zaiyi ba.

Shigowa Kausar tayi tana ƴar dariya me makon su tarbeta sai harara da suke binta dashi gaba ɗayansu

Dariya tayi dan dama tasan haka cikim dariya tace

"To hararar isa haka tuba nake yanzu dai ki taso kizo Jinin jikinki gashi cham kamar zai yi kuka wai kin si amsa wayan sa.

Duka Zarah ta kai mata tace

"Wlh Kausar baki da mutunci ai ko baki gayawa Amatu Lamir Bros ɗinki ba ne ai ni kya faɗamin amma haka kika bar mu a duhu yanxu da bai faɗa mana ba shikenan baza ki faɗa mana ba.

Dariya tayi tace

"Wlh shi ya hanani faɗa muku sai da yamin taƙata sosai da badan haka ba da tuni na sanar muku amma yanxu ba gashi kunzo kunsan gaskiya ba, yanxu dai kisa baki wannan Auntyn tamu da tayi haƙuri ta miƙe taje ta samu bros dan wallahi sai kin gansa ya zama abun tausayi wai dan kawai taki ɗaga wayarsa kamar zaiyi kuka 'fa.

Ta faɗa yan dariya

Zarah ne tace

"Wlh nima kinga zaman da nayi haƙuri nake ta bata amma kamar zigata nake ƙarayi tsabar iskanci taƙi ma tace min kanzil ko cikanki bata ce min ba.

Harara Amatu ta valla musu tare da miƙewa tsaye fuskanta ta gyara ta feshe jikinta da turare ta yafa mayafi ko kallon inda suke batayi ba ta fece daga ɗakin.

Dariya suka bita da shi suna faɗin

"Yayi dai sabbin masoya kunayi muna jin daɗin"

Ko juyowa batayi ba balle susa dan zata amsa musu, fitowa tayi ba ta taras da kowa a falon ba taji daɗin hakan sosai da sauri ta fece a falon tana fitowa ta hangesa a jikin motarsa yana tsaye sai kaɗa key ɗin hannunsa yake yana sanye da kananan kayan da suka ƙara masa kyau, a hankali take tafiya ya ƙureta da idanu hakan yasa ta sauƙe kanta tana tafiya kamar ta arta da gudu dan yadda taji idanunsa suna yawo a kanta da sallama ta ƙarasa ya amsa yana faɗin

"Tuba nake gimbiya sarautar mata dan Allah a yafewa ɗan marayan Allah nan.

Murmushi tayi tace

"Anƙi ya yafe sai kayi tsallen kwaɗo, ta faɗa da salon wasa.

Ai nan ya kama kunnensa ya fara tsalle yana faɗin 

"Ai dole nayi matuƙar gimbiya zata yafemin ko ma miye zan aikata.

Idanu ta zaro ganin da gaske yan yasa tace 

"Ya isa haka na yafe maka amma duk ranar da ka sai kayi tsallen kwaɗo ba adadi.

"Ai bazan ma sake ba wane ni iya yau kaɗai ai na gwaltu ina ni ina sakewa ai sai dai tarihi.

Suna a haka Yaya Saif ya fito turus yayi yana kallon su da mamaki cikin tsawa da ɗaga murya yace…

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212


*TAUFEEK*
NA
*Hafsat A Garkuwa*
_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
*Episode 43&44*
… Bai jima ba ya fito ɗaure da tawul a ƙugunsa yana goge kayinsa da ƙaramin, lotion ya shafa ya sanya farar jallabi tare da feshe jikinsa da turare ya nufi ƙofa domin tun da ya shiga yake tunanin a wani hali take, karo sukayi tana ƙoƙarin shigowa a jikinsa ta fata kela amai sosai
Da sauri ya riƙeta tare da zaunar da ita a jikinsa taci gaba da kela aman sai da ta amar da duk wani abu dake cikinta sannan ta fara mai da numfashi, sannu yake ta jera mata cike da tausayinta ya ɗagata ya nufi bathroom da ita wanka ya mata sannan ya cire kayan dake jikinsa dan gaba ɗaya sun ɓaci da amai, gyara wajen yayi tas sanna ya shiryata cikin doguwar riga gaba ɗaya jikinta ba ƙarfi, kwantar ta yayi tare da faɗin
"Me kike so ki ci yanzu tunda kinga kin amayar da wanda kika ci!
Ya tsine fuska tayi tare da faɗin
"Babu komai ni dai kawai bacci nake don yi, ta faɗa tana turo baki.
Cike da tausayi yake kallonta yace
"Ki dai faɗi abun da kike so bazai yiwu ki kwanta baki ci komai ba.
Kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin
"Ni kam Abwaan ba abun da nake son ci bacci kawai nake son yi ka fita kawai.
Da sauri yace
"To shikenan bari na zauna a nan nayi gadinki.
Ya faɗa tare da zama a gefenta ba jimawa bacci ya ɗauketa saboda a maganin da tasha su n sa bacci sosai.
Kallonta yake cike da ƙauna da tausayawa shirye kanshi mamakin kansa yake dan bai zammaci zai iya sonta da wuri haka ba, ya tabbatar ita ɗin ta musammance irinta ƙalilan ne a duniya sai a yanzu ya godewa Papa da nacewar da yayi da sai ya aureta amma shi kuma ya tubure kunya ce ta kamasa gashi tun ba aje ko ina ba yarinya ƙarama ta birkita masa lissafi yana cikin wannan tunanin Sweetie ta ƙira cike da ƙauna ya ɗaga bayan sun gaisa ne take tambayarsa
"Ina Nabeeha ko bakwa tare ne?
Kayinsa ya sosa kamar tana kallonsa cikin ƙinƙina yace
"Da…da…da…dama ga…gata tana… bacci neeeee.
Ya faɗa tare da jan ƙarshen
Murmushi Sweetie tayi wanda sai da ya jiyo sautin tace
"Dafatan dai tana lafiya?
"Eh lafiya ƙalau kawai dai bata ɗan jin daɗi ne.
"Subhanallahi shine baka sanar da ni tun da wuri ba mai yake damunta? maza maza kayi gaggawar dawo min da ita na kuma da ita kar ka kashe min ƴa tunda ba sonta kake ba.
Cike da tashin hankali yayi saurin cewa
"A'a Sweetie wlh ina sonta san kula da ita fiye da yadda za ki kula da ita wlh baza ta mutu ba.
Dariya Sweetie tayi duk da Taufeeq babba ne amma har yanzu wanda ya fi shi zai iya masa wayo dariya Sweetie tayi me sauti tare da hamdala tace
"Dan Allah ka kula min da ita da kyau to wai ma me yake damunta?
Kayinsa ya kuma sosawa tare da kamo lips ɗinsa na ƙasa ya tsotsa cikin kunya yace 
"Dama amai take tayi shine muka je hospital aka dubata wai tana da… sai kuma ya tsaya sai da ya ɗanyi jim yace "na 2weeks"
Dariya Sweetie maganar ta bata amma ta dake tace
"Alhamdulillah ka gaishe min da ita sosai dan Allah kana kula da ita yadda ya kamata kasan masu juna biyu suna matuƙar buƙatar kulawan mijinsu in ta tashi ka gaishemin da ita Allah ya muku albarka.
"Amin Sweetie mun gode.
Daga haka sukayi sallama ya kashe tare da sauƙe ajiyar zuciya, kallonta ya cigaba dayi bakinta sai motsi yake kamar wanda take shan sweet ji yayi sha'awarsa ta motsa a hankali ya haye gadon tare da haɗe jikinsu guri guda ajiyar zuciya suka sauƙe a tare a hankali ya fara shafa kayanta da yake a tsefe sai tashin ƙamshi yake, bakinsa ya zira a wuyanta tayi wani irin miƙa tare da ƙyalƙyala dariya, dan cikin barci taji kamar yana mata chakulkuli a wuyan, harshensa ya ƙara zirawa a wuyanta tare da yawo dashi ta ƙara fashe da dariya domin ji take kamar chakulkul a hankali ya sanya hannunsa ya shafo cikinta yana yawo da hannunsa a cikinta zuwa mararta ya zarce saman breast ɗinta wani irin murza yake musu cike da kwarewa, wasanni yake mata cikin shauƙi yana daidai da zira ƙwallansa a daga ta miƙe da sauri tana kallonsa tace
"Kana tunanin na gama yarda da kaine da har kake tunanin zan baka kaina a sauƙi ka ce dai kana sona amma ba n gama tabbatarwa ba dan haka kar ma ka sake tunanin za ka ƙara kusanta na.
Cike da ɓacin rai yake kallonta dan bai tsammaci hakan ba ya ɗauka a yau ne za su fata gurzar soyayyan su, cikin ɓacin rai yace
"Wannan ai rainin hankali ne to bari kijk in sha Allahu nima bazan ƙara kusantar ki ba matuƙar bake kika kawo kanki ba.
Daga haka ya miƙe fuuuu! kamar iska ya shige bathroom yana jin zuciyarsa kamar za ta fada ƙirjinsa ta fito, ruwa ya sakarwa kansa ko zai ji daɗi amma ina zuciyarsa sai zugashi take akan yarinyar ta gano lagonsa ta gama rainashi dole sai ya nuna mata bai damu da abun ba, da wannan tunanin ya samu yayi wanka ya fito.
Yau gaba ɗaya bashi da niyar fita amma ɓata masa rai da tayi ya sanya shi shiryawa ya fita harabar wajen da mutane da dama suke zaune suna shaƙatawa yana zaune a wata ƙayataccen kujera yana kallon wanda suke wasa a cikin ruwa yara a lokacin ne ya tuna da cikin da ke jikin Nabeeha wani ƙayataccen murmushi yayi domin yana matuƙar don yara bare kuma yau ace nasa ne mallakinsa halak malak.
Gaba ɗaya sai yaji duk wani ɓacin rai da haushin Nabeeha ya wanke daga ciki zuciyarsa wani sonta da ƙaunar abun da ke cikin ta yaji na ƙara zagaye ruhi da ɓargon jikinsa.
Ya jima a wajen sannan ya tashi ya koma domin lokacin sallah yayi, yana shiga ya taddata ta na sallah bathroom ya shiga ya ɗauro alwala yazo ya gabatar da sallah bayan ya idar ne ya ganta zaune a bakin gado ta haɗa tagumi sai ɓata fuska take alamar za tayi kuka.
Cikin sanyi yace
"Me ya faru ku yunwa kike ji?
Da sauri ta ɗaga masa kai alamar eh, haɗe fuska yayi yace
"Baki da bakine da baza ki buɗe baki ki amsa min ba?
Cike da shagwaɓa tace
"Wlh Abwaan yunwa nake ji kamar zanci babu"
"To ba sai kici babun ba in za ki iya.
Kuka ta sanya masa tana faɗin "dan Allah Abwaan ka tashi ka amso min.
"Me kike so ki ci?
Ya tambayeta a taƙaice
Turo baki tayi tace 
"Ni Ice~cream nake so da Shawarma"
Zaro ido yayi yace
"A wannan sanyin Baby?
"Eh ni kam shi nake so, ta faɗa cike da shagwaɓa.
Wayansa ya ɗauka ya turawa Osim abun sa suke buƙata ba a sauki lokaci ba ya kawo ya ajiye mata, da sauri ta sauƙo zama yayi shima cikin kulawa yace
"Dan Allah yanzu kam in kinci kada kiyi amai ki bar Babyna ya ɗan taɓa shima.
Ɓata fuska tayi tace
"To ai nima ba ni nake sa kaina aman ba zuwa yake!
A tare suka ci duk da ta fishi ci da yamma ya ɗauketa suka zagaye birin Mumbai tun da tazo sai yau ta fito taji daɗin hakan sosai duk da ba wata hira suke ba amma sun zagaya wurare da dama sai dare suka dawo gida.
Yanzu sun fi sati bakwai amma har yau bata ji ya fara maganar za su koma gida ba duk da ya gama abun da ya kawo shi, sai dai yanzu ba laifi suna ɗan taɓa hira yana kuma bata kulawar duk da ya dace, yanzu cikinta yana sati na huɗu laulayin sai abun da ya ƙaru, dan gaba ɗaya ta sama wani iri duk ta rame bata iya cin komai sai ice cream shima tana sha za ta harar da shi a wajen, sai dai har yau bai dake tunkarar ta da buƙatarsa ba duk da yana cikin mawuyacin hali amma yayi wa kansa alƙawari bazai ƙara zuwar mata ba.
Kamar kullum zaune take a falo tana shan Ice cream gaba ɗaya yau kasala take ji, ga wani rin sha'awa da take ji kawai dauriya take kar ya fahimceta, dan baza ta kuma bashi kanta ba har sai ta fahimci gaskiya son da yake mata duk da kawo yanzu ta fahimci akwai gaskiya a kalamansa saboda kulawar da yake bata cike da soyayya amma duk da haka sai ta gama tabbatarwa duk da ita ma a yanzu tana matuƙar son shi amma dole sai ya gama gane kuskuren da ya aikata na wulaƙancin da yayi mata kafin su dai-dai ta.
Tana zaune taji sallamarsa amsa masa tayi tare da faɗin
"Sannu da dawowa Abwaan"
"Yauwa sannu Baby ana nan ana sana'ar shan sanyin ne?
Murmushi tayi sanna ta gyara zama cike da kulawa tace
"Abwaan ni kam baka kammala abun da kazo yi bane naga kai shugaba ne akwai nauyin talakawa da yawa a kanka fa.
Cike da jin daɗin kalamanta yace 
"Na sani amma ina so ki gama warwarewa ne kafin mu tafi"
"A'a ni kam na ware kawai mu tafi.
"Kin tabbata?
Ya tambayeta tare da ɗage mata gira.
Dariya tayi tare da fadin
"Eh wlh na warke.
"Tom ki fara shiri a cikin satin nan za mu tafi.
"Allah ya kaimu ta faɗa cike da farin ciki domin har ga Allah ta gaji da zaman bu ɗaya daga falo sai ɗaki.
Haka kuwa akayi a cikin satin suka ɗaga gida Najeriya.
A hankali suka fara sauƙowa cikin shigar alfarma gaba ɗaya jami'ai sun cika wajen da jiniyarsu tafiya suke yana riƙe da hannunta gaba ɗaya jama'a kallonsu kawai suke cike da burgewa a ransu suna fatan dama su ne kamar daga sama suka ji ana faɗin
"Taufeeq! Taufeeq! Taufeeq!! a tare suka juya domin kallon me ƙiran gaban Nabeeha ne ya faɗi ganin wata budurwa me zubin karuwai ne take ƙiransa.
A bangaren Taufeeq kuma tsaki yaja bayan ya kalli wacce take ƙiransan a fili ya furta "Mayya kawai...

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212


*TAUFEEK*
NA
*Hafsat A Garkuwa*
_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
*Episode 41&42*
… "Yau nice na ke ɗauke da cikin wanda baya sona wanda yake min tsana mafi muni wai nice da cikin sa a jikina! 
Ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani irin kuka me ban tausayi.
Ruɗu, mamaki, tausayi, kunya a tare suka ziyarci Taufeeq dake zaune kamar hoto yana kallonta gaba ɗaya jikinsa yayi matuƙar sanyi bai taɓa tunanin hakan daga garetan ba, sai yanzu yake tuna duk wani irin tsana da yake mata, sai yanzu yake jin kunyar abun da ya mata, ya sani bai cancanci ta haihu da

Please Login or Register in order to submit comment