Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin shine me faɗa aji a cikin family'n yasa ba yadda suka iya dole suka amince aka ɗaura auren, yanzu ko za a yanka ta da wuƙa bata san su waye iyayen mahaifiyarta ba, a kullum mahaifiyarta tana cikin kuka tare da tsoron fuskantar iyayenta dan tasan abu me sauƙi ne su saka wuyanta gabas su yanka, gashi har ta koma ga Allah bata je ba bare ta nunawa ɗiyarta Amatullah danginta.
   Bayan an sallace su ne aka kaisu gidan su na gaskiya sai dai muce Allah ya jiƙansu da rahma, haka taci gaba da amsar gaisuwa gaba ɗaya lokaci guda tayi ɓaki ta rame bata ci bata sha sai ruwa babu wani me rarrashinta sai maƙwaftan su amma dangin mahaifinta kam ko kallo bata ishe su ba, bayan anyi bakwai ne suka tattaro ya nasu ya nasu suka dawo gidan da zama su uku ne da Babban yayan mahaifinta sai ƙannesa guda biyu kowa da matan sa da yaransa, Babban Yayansa Baffa Jibbo sai Baffa Haruna sai kuma autan su Baffa Gambo su uku  mahaifiyarsu shi kuma Mahaifin Amatullah mahaifiyarsa shi kaɗai ta haifa, tun da iyayensu suka rasu Jamilu mahaifi ga Amatullah shi yake ɗawainiya da su kasan cewarsa ya fisu samu gaba ɗayan su babban ɗan kasuwa ne Jamilu Mutum ne na gari me matuƙar tausayi da jin ƙan na ƙasa da shi ba shi da mugunta kowa yabon sa yake saɓanin ƴan uwansa da suke kishi da shi kasan cewar sa ya fisu ɗaukaka hakan yasa suka tsanesa daɗin da ɗawa sam yaƙi yarda ya amshi tayin da Baffa jibo ya masa na auren ɗiyarsa Fatsuwa duk da zabaransa da Baffa Jibon ba wata me yawa bane kawai ya riga sa aure ne hakan yasa suka tsani Shamsiyya matarsa da kuma Amatullah...'''(Ka dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muki nam nada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞?

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

*_MASOYANA DON GIRMAN ALLAH KUYI MANA SUBSCRIBE DIN WANNAN CHANNEL DOMIN SAMUN LITTAFAN SAURARE DA KOYON SANA'O'IN HANNU DA SAURANSU NAGODE👇🏻_*
https://youtube.com/channel/UCY1pIcI2DlVykTz57m6Q3TA

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Episode 03*

*…* Ko kaɗan basu taɓa jin son Amina da ƴarta Amatullah ba, hatta ɗan uwansu Jamilun ba wai sun so shi bane tsakani da Allah ba, kawai sun so shi ne don abin da yake da shi, a lokacin da yake raye suna nunawa Amatullah so na ganin ido, amma yanxu ƙiri² suke nuna ƙiyayyarsu gareta, gida ne Babba me ɗauke da ɗakuna domin Alhaji Jamilu ya narka kuɗi sosai akan wannam gidan a tsare yake tsaf kowa ya ɗauki nasa da na iyalen sa, Allah ya taimake ta basu kama ɗakin ta ba, tun bayan bakwai bata ko leƙowa parlour'n sai dai tana jiyo hayaniyar su, Satin ta guda baci ba sha sai ruwa tuni ta fita a hayyacinta yanzu ko ruwan tasha ma harar dashi za tayi, ko salla gagararta tayi, a yanzu ma kwance take a kan sallaya tana ta maida numfashin wahala dan yanzu ta gama kela amai na zallan ruwa, Mama Baraka ne matar Baffa Gambo jin har an doshi sati ba Amatullah ba motsin ta yasa ta nufi cikin ɗakin dan ganin halin da take ciki, Mama Baraka ka tana da ɗan tausayi ba kamar sauran matan da mazajen nasu ba, domin su kam summa mance wata Amatullah sharholiyar su kawai suke yi, Mama Baraka tun da ta doshi ɗakin take jin wani tsami gabanta ne ya faɗi tace "kar dai yarinyar nam mutuwa tayi, yau da mun shiga uku.
Da sauri ta ƙarasa daɗin hango ta tayi a chan ƙasa a zube tana mai da numfashi da hanzari ta ƙarasa tana faɗin "innalillahi! Amatullah me yake damunki haka? ta isa tana kamata jikintan nam taji zafi rau, Amatullah bata iya magana ba sai ido kawai, kuka ne yaxo wa Mama Baraka tace "sannu Amatullah bari naje na samu Baffan naki yazo a kaiki asibiti. bata jira jin amsar ta ba dan tasan baza ta samu ba saboda wahalar da tasha, Mama Baraka tana zuwa ta samu duk suna falon ma, hawayenta ta share tace "Amatullah fa ba lafiya dan ko magana bata iyayi dan Allah kuzo muje a kaita asibiti kada ƴar mutane ta mutu, ta ƙarasa tana matsar ƙwalla dan gaba ɗaya tausayin yarinyar ya kamata.
   Baffa Jibo ne yace "to ta mutu man ina ruwan mu ba wani asibitin da za a kaita.
"Ah toh! cewar Baffa Haruna.
   Baffa Gambo yace "kin dai ji abin da Yaya ya faɗa dan haka kiyi maza ki ɓace min da gani baza a kaita asibitin ba.
    Bata ƙara magana ba ta juya ta nufi ɗakinta dan tasan iya gaskiyar su suka faɗa baza su kaitan ba, fita tayi ta samu mai gadi tace maza yaje ya sayo mata maganin zazzaɓi da ciwon kai, dan tasan bazai wuce su suke damun Amatullah ba da kuma rashin abinci, amsa yayi ita kuma ta dawo direct ɗakin Amatullah ta koma a yadda ta barta haka ta sameta, taimaka mata tayi ta shiga toilet ta haɗa mata ruwa tace tayi wanka, ba musu kuwa ta ɗaga kai dan dama tana buƙatar me taimakon ta, kafin ta fito Mama Baraka ta gyara ɗakin yayi fes ta ɗauko mata kaya, bayan ta fito ne tace "maza ki chanza kayanki bari na kawo miki abinci, da "to" ta amsa mata shima da ƙyar dan wankan da tayi ta samu kuzarinta ya fara dawowa, kayan ta sanyi bata ko kalli in da mai yake ba ta koma gado ta kwanta, Mahaifanta ta tuna, ta tuna lokacin da in bata da lafiya gaba ɗaya suna tare da ita wannam na mata sannu wannam na bata abinci a baki a kullum suna manne da ita har ta warke basa yarda ko na second ɗaya ne ta zauna da yunwa, amma yau gashi sati na biyu ban saka abin kirki a cikina ba, wani marayan kuka ta sake a haka Mama Baraka ta dawo ta sameta hannunta ɗauke da plate Da yaƙe shaƙe da abinci wanda sai da suka kai ruwa rana da su Mama Marka da Mama Talatu akan baza ta ɗibi abincin ba in Amatullah ta matsu tazo ta girka mana, sai da ta musu da gaske sannam ta ɗiba ta fito, ajiye mata tayi tace "maza Amatullah tashi ki ci kisha magani sai ki kwanta ba musu ta miƙe dan ba ƙaramin yunwa take ji ba, tuwon shikafa ne miyar ganye da yaji tattaƙwashi da man shanu luma ta fara baji ba gani tuni taci rabin abincin, Mama Baraka kallonta kawai take cike da tausayawa, sai da ta cinye tas sannam ta miƙa mata maganin da Iro me gadi ya sayo sha tayi tasha ruwa sannam taje ta wanke hannunta ta dawo tace "Mama Baraka na gode miki sosai Allah ya saka da alheri.
"Babu komai Amatullah ki kwanta ki samu bacci Allah ya ƙara sauƙi, ta faɗa lokacin da take fita daga ɗakin.
  Da "amin" ta amsa sannam ta kwanta, tana kwanciya bacci ya ɗauketa.
              Cikin bacci taji an ɗira mata wani wawan duka zambar ta miƙe cike da tsoro dan dukan ya shigeta, buɗe idonta tayi Mama Marka ta gani a saman gadon ba shakka tasan ita ce ta daketa gefenta ga Mama Talatu da Baffa Jibbo Baffa Haruna Baffa Gambo da kuma Mama Baraka, mamaki ne ya cikata a zuciyarta tace "waɗan nam ko me suka zo yi ɗaki na oho.
   Baffa Jibo ne yace "sannu maras kunya dan iskance ace muna gida ɗaya tsawon sati biyu baza ki fito ki gaida mu ba ko kuma ki taya matayen mu aiki ba, tsabar iskanci sai dai ki kwanta ki ta sharar bacci to maza ki buɗe kunnenki da kyau, daga yanzu ki za kiyi sharar gidan nam da girki ke dai komai ma na gidan nam ke zaki na yi in kin ƙi kuwa jikin ki zai gaya miki, tun da naga alamu kin ɗau baƙin halin uwarki, gaba ɗaya matan suka sa shewa banda Mama Baraka da tausayin yarinyar ya gama cika mata zuciya a yanzu.
  Baffa Haruna yace "kinji dai abun da Yaya ya faɗa ko? ya faɗa cikin tsawa, da sauri ta buɗe baki tace "eh naji insha Allahu zan yi" ta ƙarasa maganar wani kuka na zuwan mata.
  Baffa Gambo yace "kar ma kiyi mana ai na lahira sai ya fiki jin daɗi sai kin tafi inda iyayenki suka je, daga haka suka fice daga ɗakin damman saƙon da suka zo isarwa kenam gareta.
   Wani marayan kuka take a fili take furta "why? Why? Why? me yasa ku ka tsaneni haka? me yasa baza ku tausaya min ba ko dan maraicin da nake ciki tashin farko a lokaci guda na rasa iyayena duka biyu me yafi wannam ƙuna, bani da wanda zai kula da lamurana, ba ni da wanda zai na sharemin kuka wayyooo Allah nah…
        Tun daga wannam rana ta fara fuskantar uƙu ba da wahalar rayuwa ita ke komai na gidan duk da ga ƴan mata kamarta har ma wanda suka fita amma sam babu me taimaka mata, sai tayi ma suce bashi suke so ba dole zata koma ta sake musu abin da suke so, haka gyaran daɗi ma tana yi zasu ɓata su sake ƙiranta dole sai ta gyara, yanzu ma tsaye take a kitchen tana girkin rana, jalouf rice take da yasha kayan lambu Zainab ce ta shigo ƴar Baffa Jibo wacce zata kai shekara 28 ƙatuwa ce baƙa kana ganinta kasan tsohuwa ce yauƙi take tana yamutsa fuska tace "ke Amatu me kike girka wa ne? maza ki sauƙe ki dagamin Indomie me ruwa ruwa taji hanta sosai.
  Kallonta Amatullah tayi tace "Anti Zainab kiyi haƙuri ki ɗan jira yanzu shinkafar zata ƙarisa sai kici.
  "Dan ubanki ni kike cewa na jira ki kammala?  to bazan ci shinkafar ba Indomie nake so ki dafa min nam da minti biyar ki kawo min falo ina jiranki in kin ƙi kuma jikin ki ne zai gaya miki wawiya kawai. ta faɗa tana jan tsaki ta fita, ba yadda ta iya dole ta ɗaura mata dan tasan ba abu me wuya bane ta kamata ta jibga, tsoron kar a taɓa mata lafiya yasa tayi hanzarin gamawa ta kai mata a falon ta sameta tana zaune ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, rusunawa tayi ta ajiye mata, Shema ce da ke zaune gefen Anti Zee tace "Nima Amatullah ki girka min kamar yadda kika yiwa Anti Zee ɗin nam yaji hanta da kifi sosai…

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

A haka suka shiga gidan a dining suka hangi su Sweetie da suke zaman jiran su dan ƙa'idar gidan ce basa fara cin abinci sai gaba ɗaya wanda suke cikin gidan sun hallara, da sallama suka shiga direct suka nufa inda suke zama sukayi Papa yana cewa "ashe dai har yanzu ana so mu,an tsaya jiran ƙara so war mu"
"Ba dole a so ku ba" cewar Sweetie tana haɗe fuska, Nabeeha ce ta zubawa kowa amma banda Papa Sweetie ne ta zuba masa da kanta, white Rice ne da stew sai kuma haɗin salad, da ita da Sweetie ne suka girka dan sam Sweetie bata yarda ƴar aiki ta dafawa ke gidan ta abinci ba, tafi so komai tayi masa da kanta…

*Note…*
'''Da yawa wasu matan sukan bani mamaki wai dan kuna da kuɗi zaki ɗauko ƴan aiki masu gyara miki gida shara wanke² girkin oganki gyaran room ɗinsa zai zamana bakya aikin komai a gidan ki, wannam wani irin zaman aure kike? bakya samun ladan aure sai dai na sex🤔 ƴar uwa komai da kika yi a gidan ki me kyau kar ki manta lada kike samu tun daga shara wanke² wanke musamman tsaftace shimfiɗar me gida da kuma girkinsa, duk kuɗin ki ace dai a babu a babu ke kike yiwa me gidan ki girki da hannunki ki kuma gyara masa muhallinsa sauran aikin gida kuma kya barwa ƴar aiki, amma dan sakarci ace ƴar aiki babu abun da bata sani ba na mijinki tun daga room ɗinsa har izuwa cimarsa, wlh mata mu gyara kar daɗin duniya ya shagaltar damu, za kaga mace wai tafi ƙarfin yin aiki a cikin gidan ta ita ga me kuɗi hmm ai ko ba kiyi komai ba kyayi aikin me gidan ki, wannam aiki da muke yiwa mazajen mu su kansu ba ƙaramin daɗi suke ji ba ace yau ga Matarka ta gyara maka muhalli sai zuba fitinan ƙamshi yake gata a kitchen tana tsara maka abinci me sa motsin kunne, ko ace gashi ta kammala ta jeresu kai kawai take jira, wlh ko da ɓacin rai ya dawo sai kin ga murmushi ya kuɓece masa, amma yau ya dawo ya tarar ƴar aiki ce me gyara masa room sannam ita take haɗa masa abinci ita zata zo ta zuba masa abinci ke kina chan ɗaki ko kuma ma bakya gidan baga ɗaya🤔 ko bashi da niyar ƙara miki kishiya wannam abun shi zai ja hankalin sa izuwa ya dan ƙara miki kishiya ni dai ba ruwana.'''🤣🚴🏻‍♀️

Papa yana cin abincin yana zuba santi sai dariya suke masa Sweetie tace "ko dai mu saka maka waiji ne Papa? dariya suka yi yace "ai girkin ne na rasa da me zan misaltashi wajen daɗi wlh, sai da suka kammala sannam suka dawo falo aka ci gaba da hirar gaba ɗayansu, Kaa'af ne yace "Papa yaushe Yaa Taufeeq zai dawo ne? Papa ne ya kallesa yace "nam da 1month insha Allah my son kayi missing ɗinsa ne? tun da Papa ya ambaci Yaa Taufeeq zai dawo bara'ar matasan gidan ta ɗauke Nabeeha, Jawaad, Nazmar dan sam basa ƙaunar ace yana gari sun fi so kullum ace yana chan wata ƙasar su kuma suna nam dan koman su yafi tafiya dai² acewar su.
  Su Papa duk sun gane me ya dishar da fara'ar da suke yi, Yaa Sayyid ne yace "an ƙira muki mutuwar ku ko? Su Khairat ma hakance take faruwa da su in har akace Taufeeq zai dawo sai kace wani ance gobe zasu mutu, aiko suma zanje na basu wannam labarin. ya ƙarasa yana dariyar mugunta.
   Sweetie ne tace "ba dole suyi haka ba tun da yana maganinsu ai ni wallahi Allah Allah nake ya dawo domin ya min maganin waɗan nam ja'iran kana gani gida suke mayar min kamar wani club. ta faɗa tana dangwarin goshin Nazmar da yayi kicin² kamar zuciyarsa zata fito.
  "Wato so kike yazo ya hana min yara sake wa ko? aiko zance ya ƙara shekara guda a chan muga ta tsiya, cewar Papa yana ƙunshe dariyarsa dan shima yasan sarai abun da suke aikatawa da ya dawo zasu koma zana firzin...'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muku nam ba da jimawa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞🤞🏻
*TAUFEEƘ*
 

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

*MASOYANA DON GIRMAN ALLAH KUYI MANA SUBSCRIBE ƊIN WANNAN CHANNEL DOMIN SAMUN LITATTAFAN SAURARE DA KOYON SANA'O'IN HANNU DA SAURAN SU NA GODE*👇🏻
https://youtube.com/channel/UCY1pIcI2DlVykTz57m6Q3TA

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Episode 04*

*…* Domin in ya dawo duk wani shi ge da ficen su sai ya sa ni har ta kai ta kawo ma in har zasu fita sai sun sanar dashi har inda zasu shi kuma zai faɗa musu lkcn da za su dawo, hakan yasa sam basa so ya dawo ƙasar sun so kawai yana zama a chan in ganinsu yake su yayi ya ƙirasu video call, yana mamakin yadda yaran basa so su ganshi a gida Kaa'af ne kawai ke son kasancewa dashi a ko da yaushe.
    Nazmar ne yace "wlh Papa kawai ka ƙara masa shekaru yaje yayi ta zaman sa ka aura masa ƴar cham ma su tare a chan ba sai ya dawo ba mu sai muna zuwa muna duba shi.
   Dariya gaba ɗaya sukayi saboda yadda suka ga yayi maganar, Papa ne yace "in ban da wauta irin  taka ai dama bani na turashi ba Shugaban ƙasa ne ya turasa, saboda shi bazai samu damar halartar taron ba, ni nayi mamaki ma da wannam karon ya jima haka, haka suka yi ta hira akan Taufeeq ya zauna a chan Papa yana musu tsiya Sweetie kam ta cika tayi fam saboda ita bata ƙaunar Taufeeq yayi nesa da ita ko kaɗan amma su burin su ya zauna a cham ma kar ya dawo, amma kuma ba ranar da baza su ƙirasa a waya su jima suna waya ba, amma kuma basa ƙaunar dawowan sa oh! har ƙarfe goma da ƙyar Papa ya kora Yaa Sayyid dan hirar tayi daɗi an bar batun Yaa Taufeeq an shiga wata hirar duniyar.
    Haka suka cigaba da guda nar da rayuwarsu cikin farin ciki da ƙaunar juna, lokacin Taufeeq na dawowa yana ta ƙara towa yanzu haka saura 2weeks Yaa Sayyid in bai zo yau ba zai zo gobe, gaba ɗaya ya mace akan son Nabeeha ita kuma yanzu sam bata sake masa fuska kamar da, dan tana jin kunyar sa da nauyinsa sosai, yanzu ma zaune take a parlour sanyi take da doguwar riga ash color an ƙayata sa da stone work red sosai ya mata kyau kanta babu ɗan kwali bata yi wani kwalliya ba amma tayi kyau, chat take da friend ɗinta sai ƙyalƙyale dariya take kana ganinta kasan abun dariya take gani a cikin wayar tata, Sallamar sa taji gaban ta ne ya faɗi sai kuma ta dake tace "wa'alaikas salam Yaa Sayyid sannunka da zuwa.
"Yauwa sannu My Queen"
   Ya faɗa yana ƙaraso wa cikin parlou'n sanye yake da t-shirt white me ratsin dark blue da jeans kannan sai yalƙi yake alamar yasha gyara murmushi ya sakar mata sai ta tsinci kanta da maida masa, zama yayi ɗan nesa da ita yace "My Queen yau ke ɗaya ce a gidan?"

  "Eh wlh Yaa Sayyid sun tafi Habila cream gaba ɗayan su ni yau sam ban jin fita ne shiyasa ban bisu ba.

"Kece rabun dai nazo na ganki ne yasa baki je ba ko Queen? ya faɗa yana dariya.
     Dariyar ita ma tayi tace "ai kuwa dai Yaa Sayyid, "yanzu sai ki tashi mu tafi mu bisu ko dama tafiyar masoya tafi daɗi, dan haka ɗauko mayafinki mu tafi.
   Kwaɓe fuska tayi cikin shagwaɓa tace "wlh ni Yaa Sayyid bana son zuwa ko ina yau zaman gidan yafi min daɗi, ta faɗa tana ƙara turo ɗan ƙaramin bakinta.
  Murmushi yayi a zuciyar sa yana faɗin "me yasa ita ko me tayi ƙara kyau take ne? ganin bazai samu amsar tambayar sa bane ya ƙarasa ya kama ɗan ƙaramin bakin tan ya matsa cikin sigan wasa yace "aiko dole sai kinje maza je ki ɗauko mayafin ki kinji *My Queen*.
  Ƙara ta sake dan yadda ya riƙe bakin nata ya ɗan mata zafi, baza ta iya masa gardama ba dole taje ta ɗauko mayafi ta yafa a kanta ba tare da ta ɗauki ɗankwali ba kyanta ne ya sake fitowa, hannunta ya kama suka nufo far fajiyar gidan su Sani sai zuba hirarsu suke kamar yadda suka saba, gaban mota ya buɗe mata ta zauna sannam shima ya shiga ya tada suka tafi, suna tafe suna hira, basu zarce ko ina ba sai *NAF Club Kaduna 4.9* Sosai wajen yayi mata kyau duk da ba yau ta fara zuwa ba amma an sake ƙa wata wajen yayi kyau sosai cike yake maƙil da mutane, sayyaya sukayi sosai duk da tayi masa ƙorafi akam ya barshi haka amma fir yaƙe sai da gaji sannam ya bari biya sukayi suka nufo motar zama tayi ta buɗe ice cream tana sha shima ya zauna yana fuskantar ta fuskarsa ƙunshe da murmushi, dan shi mutum ne me matuƙar fara'a a ko da yaushe baza kaga fuskarsa a tsome ba kullum cikin fara'a take.
   Kallonsa tayi ganin ya ƙure ta da ido tace "wai Yaa Sayyid kallon me kake min haka ne?
   "Uhumm! kin ƙaramin kyau ne Queen, ya ƙara da cewa "na rasa miye lefina dan nace ina sonki ko dai ban miki ba ne? Murmushi tayi tace "kai Yaa Sayyid wace macece za tace baka mata ba, kawai dai in kayi duba da ƙarancin shekaru na, sannam kuma ni Ƙanwarka ce halak malak kaga ba aure tsakanin Yaya da kuma ƙanwarsa.
    "Wannam ba hujja bane Nabeeha wlh ina matuƙar ƙaunarki ni babu ruwa na da wani ƙarancin shekarun ki ai auren yarinya ɗanya sharaf wanda kai zaka raineta da kanka yafi daɗi, nasan ni Yayanki ne amma kuma akwai aure tsakanin mu tunda ba ciki ɗaya muka fito ba.
   "Ni yadda na ɗauka ciki ɗaya muka fito Yaa Sayyid kaga ba aure kenam, dan Allah mu bar wannam maganar. ta faɗa da ɗan ƙarfi.
   Ran sa ya sosu amma ya danne domin yarinya ce dole sai ya fuskanci haka dama, kuma ba ya so ya mata dole ko kuma yasa a mata dole da sai yaje ya sanarwa iyayensu, amma zai bi da ita a hankali har ya shawo kanta, a fili kuma yace "I'm very sorry My Queen bazan ƙaraba. ya faɗa yana kama kunnen sa, dariya haɗe da kunya ya bata ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana cewa "kayi hakuri Bro na ɗaga maka murya.
"Ba komai Queen. A haka suka ƙarasa gida yana janta da hira saboda ta ware suna isa motar su Papa na shiga a tare suka shiga, mamaki ne ya cika su Sweetie ganin Nabeeha domin ba magiyar da basu yi ba akan tazo su safi amma fir taƙi sai gata kuma da Ya Sayyid, gaban Papa ne yayi mummunar faɗuwa…
     A zuciyarshi yace "ba dai abin da nake zargi bane yake shirin zama gaskiya? Allah kasa ba haka bane, domin in har hakan ta kasance zumuncin mu zai iya taɓarɓarewa, wanda bazan taɓa lamunta ba, Alƙawari nayi kuma insha Allahu sai na ciki wannam alƙawarin da yardar Allah… Sweetie ne ta katse masa zancen zucin da yake tace "Papa baka ga Nabeeha bane? ta faɗa tana son tabbatar da ya ganta ne ko bai ganta ba.
  Dariya yayi yace "na ganta kun san halinta ai ƙila gidan ya mata shiru ne shiyasa suka fita da Sayyid amma muje muji dai, Nabeeha dai dariya taƙe ƙasa² dan tasan za tasha magana wajen su Jawaad wanda ba magiyar da basuyi ba amma taƙi binsu, Jawaad ne yake jefa mata wani banzan kallo na kin raina mana hankali, Nazmar kuwa zungurinta yayi yace "ya miki kyau Nabeeha"
  Gaba ɗaya suka ɗunguma sukayi cikin gidan sai mita Nazmar yake akan yaƙi binsu tabi Yaa Sayyid, zama sukayi gaba ɗayan su a falon, Sweetie ne tace "wai ina kuka je ne?"
  Yaa Sayyid ne ya kwashe komai ya faɗa musu ya ƙara da cewa "da ƙyar fa

Please Login or Register in order to submit comment