Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

chan wata zuciyar tace
"Ko dai an sanar dashi baki da kowa ne?
"To waye zai faɗa masa haka nasan Abba da Ammy kam baxa su taɓa faɗa ba tun da ko ni sai da suka min takara akan kada na yarda na buɗe baki na faɗawa wani cewar ni ba ɗiyarsu bace, to taya su za su faɗa? kai hakan ma bazai faru ba sai dai in wani matsalar daban."
Haka tayi ta saƙe-saƙe sai bacci ɓarawo ne ya saceta a wannan rana dan tana cikin matuƙar fargaba.
Washe gari.
Har dare Abba ya kasa tunkarar Amatullah da maganar an fasa aurenta sannan ya gargaɗi Ammy da karta sanar musu zai faɗa mata cikin nutsuwa amma hakan ta gagara dan kansa yayi matuƙar kullewa.
Amatu kuwa haka ta wuni cikin damuwa da faɗuwar gaba gaba ɗaya ta rasa nutsuwarta har yanzu tana kan ƙiransa akashe ma wayar take gaba ɗaya, tasan dai in da ba lafiya ba da za taji aj faɗa tunda Abban Lamir Abokin Abbansu ne na ƙut da ƙut haka dai ta wuni gaba ɗaya ranta babu daɗi.
Shirye-shirye suke tayi duk da bata da wani kuzari har bikin su saura kwana uku rak babu Lamir ba labarinsa saɓanin Angon Zarah kullum sai yazo in ma bai zo ba suna manne a waya tuni ta rame saboda tunani ga bata wani cin abinci duk da tana dhan gyara na amare amma kana kallonta za kaga ramar da tayi tayi wani fayau sai dai kuma hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mata ba.
Abba kuwa zaune yake sai zuba murmushi yake dan ya gama hasaso abun da ya ƙudira a ransa shine maslaha a yau ya yanke shawarar zai sanarwa Amatullah sannan kuma yadda aka sa su biyu zai aure hakan sai ta kasance da izinin ubangiji shigowar Amatullah ne ya katse masa lissafin da yake wanda yasa Ammy ta ƙira masa ita a hankali ta shigo bakinta ɗauke da sallama za ma tayi a lallaushan carpet ɗin da yayiwa ɗakin ƙawanya cike da girmamawa tace
"Abba ina kwana."
"Lafiya ƙalau ɗiyata ya shirye-shiryen biki?"
Cike da kunya tace "Lafiya lau Abba."
Murmushi yayi tare da gyara zamansa gyaran murya yayi tare sa zuba mata ido duk da wani irin faɗuwar gaba da yakeji amma kuma ya danne dan ji yake kamar abun da zai aikata wani babban abu ne a rayuwarsa ji yake kamar wani babban zunubi zai aikata gaba ɗaya zuciyarsa taƙi amincewa da shawarar da ya yanke duk da ta wani ɓangaren wata zuciyar tana ƙara tunzurasa akan ƙudirinsa.
"Amatullahi."
Gabanta ne ya faɗi jin ƙiran da Abban nasu yayi mata a hankali ta ɗago 
"Na'am Abba."
Ta faɗa a sanyaye dan ji tayi gaba ɗaya zuciyarta nayi mata wani irin ƙuna tsoro da fargaba ne suka taru suka yi wa zuciyarta ƙawayanta.
"Amatullahi ina so ki nutsuwa ki kuma fahimci maganar da zanzo miki da ita Amatullah ko wani bawa da irin tasa ƙaddaran kowa wani ɗan adam rayuwarsa tana cikin zanen ƙaddararsa abun da Allah ya tsarama shine zai faru da kai ba wanda ka tsarawa kanka ba.
Fesar da iska mai zafi yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Amatullah a koda yaushe mu zama masu tawakkali masu kuma amsar duk wata rabawa da Allah ya jarabcemu mu kuma yi nasarar cinye wannan jarabawa duk wuyarta duk kuma sauƙinta hakan shi zaisa muyi kyakkyawan ƙarshe."
"Ina so ki kasance ɗaya daga cikin bayin Allah masu yadda da duk wata ƙaddarar da tazo musu masu yarda da duk wani lamari su sashi a mizanin babi na jarabawarsu nasan baki san komai game da abun da yasa Lamir baya zuwa kuma baya ƙiranki ba ko?
Amatullah da tun da ya fara maganar taji taga gaba ɗaya kanta yana wani irin sarawa gaba ɗaya ta kasa gane inda maganganunsa masu matuƙar nauyi da sanyawa mutum wani irin shakkuwa a zuciya suka nufa har sai da taji ya ambaci sunana LAMIR.
Dam! dam! dam!daram! dam!!!
Shine sautin dake fitowa daga cikin zuciyarta wanda zuciyarta ce take fidda wannan sauti saboda tsananin firgita da kaɗuwa a zaburi ta ɗago ta kalli Abban nasu jin yaci gaba da cewa
"Ammatullah kiyi haƙuri Iyayen Lamir sun jima da zuwa su ɗauki kayan auren da Lamir ya kawo miki tana da faɗin dalilin wai an sanar dasu cewar ba mune mahaifanki ba hasalima babu wanda yasan daga ina kike hakan yasa muka kasa faɗa miki sai yau da na yanke wani hukunci a kanki hakan yasa dole na a yau sai na sanar miki saboda sai kin amince da buƙatar da nazo miki da ita tukunna.
Wani irin duhu ta ga yana mamaye ɗakin tare da wani irin zufa duk da tsananin sanyin da yau al tashi da shi amma tsabar tashin hankali firgici kiɗima ɗimaucewa tsoro suka taru suka yi wa zuciyarta ƙawayansa yasa duk wannan sanyin ta daina jinsu gaba ɗaya kunnenta me taji yana fidda wani irin sauti.
Shuuuuuuuuu! Shuuuuuuuu!!
Shine sautin da taji kunnen ta na fitarwa 
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Hasbunallahu wani'imal wakim! Allahumma ajirni fi musibati wa'akilni khairan minha!!!
Shine abun da yake fitowa daga cikin ƙasan maƙoshinta.
Abbane ya iso gareta tare da kamo hannunta a hankali ya cigaba da cewa
"Mu dai munsan muna sonki har cikin zuciyata ina jinki kamar yadda nake jin su Zahra ina jinki kamar dama chan ke jinina ce,hakan yasa na yanke wani hukunci a kanki kamar yadda aka sa ranar aurenku ke da Zarah ku biyu zan aurar kamar yadda na tsara domin na miki zaɓi wanda nasan kuma shine ya dace dake bana fargaba ko shakkan zai barki ki wulaƙanta na tabbata zai riƙeki da amana sai jiƙanki zai kuma maye miki gurbin maraicin ki dafatan zaki amince da wannan zaɓin da na miki…?

A cigaba da wanke hannu My Fan's lamarin fa ya ɗau zafi.🤣🤣🤣🤣🤣😘🥰



#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212


*TAUFEEK*
NA
*Hafsat A Garkuwa*



*Episode 53&54*
... Da sauri yasa hannunsa na dama a saitin zuciyarsa tare da rintse idanunsa ji yake kamar zuciyarsa za ta fashe ƙirjinsa ta fito, jijiyoyin jikinsa ne suka fara wani irin mimmiƙewa duk wani lungu da sauƙo na jikinsa yaji yana bubbuɗewa hannunta da ke cikin hannunsa ya fara kurzawa da ƙarfi ƙarfi ko zaiji sassaucin da zuciyarsa take masa amma ina kamar ƙara angiza ta yake da sauri ya sake mata hannu jin bugun zuciyarsa na ƙaruwa.
Ganin ya saketa ne yasa da sauri ta buɗe murfin motar ta fita wanda a lokacin su Sweetie suka fito dan tuni an shigar da kayansu amma suka jisu shiru hakan yasa suka kasa hakuri sai da suka biyo sawo.
Tana fitowa tayi ido huɗu dasu Sweetie, Ka'aaf, Samha da kuma Huda da Nazmar a guje ta tawo dan ta mance ma da wani cikin da ke jiginta gudun take kamar wanda ba komai dake tattare da ita tana zuwa ta faɗa jikin Sweetie cike da farin ciki
"I miss u so so much My Sweetie."
Ta faɗa cike da bege, so ƙauna.
Rungumeta Sweetien ma tayi cike da ganin Ɗiyartata yadda take fidda wani irin sihirtaccen kyau duk da ta ɗan rame shima kuma saboda laulayin da tayi ne cike da farin ciki tace
"Wai Nabeeha kin mance abun da kike tattare da shine ko so kike mijinki ya ɗauremu har igiya ta saura in cikinsa ya samu matsala?"
Ta faɗa da alamar faɗa tana kallon motar da ɗannata yake ciki wanda yaƙi fitowa.
Da sauri ta sake Sweetie cike da kunya ta nufi Ka'aaf da ya haɗa girar sama da ta ƙasa dan fushi yake akan bata kulasa ba ta kula Sweetie
Sunkuyawa tayi tare da rungumesa a tare suka sauƙe ajiyar zuciya tace masa
"Tuba nake My love nasan nayi laifi ban fara kulaka ba na kula Sweetie a yafe ni."
Gaba ɗaya suka saka dariya ganin ya sake fuskar sannan Samha tazo ta rungumeta ita da Huda cike da farin ciki Nazmar ne ya ƙariso inda take cike da fara'a yace
"Oyoyoo Ƙanwata kuma Auntyna munyi kewarki over wlh."
Dariya sukayi cike da mamaki take kallonsa ganin bata ga Jawaad ba dube-dube ta fara tace
"Bayin Allah banga fa Jawaad ba ina yake?"
Ta tambaya cike da damuwa.
"Yana gidan Mom tun jiya muka tattara muka koma chan nayi-nayi yazo mu tarbeki kuma yace bazai zo ba saboda baya jin daɗi."
Cike da tausayin ɗan uwan nata kuma abokin wasanta tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya."
Dan bata kawo komai a ranta ba falon suka shiga yana nan a yadda yake sai baza ƙamshi yake kamar ko da yaushe dan Sweetie ba baya ba wajen tsafta da ƙamshi a falon suka zauna aka fata hirar yaushe gamo Sweetie kuma kitchin ta shiga ta kawo mata ferfesun hanta wanda yaji kayan ƙamshi da Tambarin juice dan tasan me ciki a falon ta baje tanaci sai da ta kusa cinyewa tas tana zuba hira da santi sannan rasha juice ɗin ganin an fara ƙiran sallah ne Sweeetie ta raraka Nazmar ganin hirar baza ta ƙare ba su kuma suka rankaya ɗakinsu.
Tana shiga tace
"Allah sarki ɗakina nayi kewarka."
Samha ne cike da zolaya tace
"Yanzu dai ba ɗakin ki bane aro muka baki za kuma ki tafi ki bar mana kayan mu.
Hararar wasa ta galla mata ba tare kuma da tace mata komai ba ta shige bathroom Alwala ta ɗauro kana ta gabatar da sallah sai da akayi sallan i'sha sannan suka tashi akan dardumar suka fito falo.
Taufeeq kuwa tun da ta fita yaga gudun da take kamar ta mance tana da jiki ji yayi kamar ya fita ya hanata gudun nan da har cikin ransa yake ji amma kuma ya kasa harara ya wulla mata wanda ita dai bata san yanai ba, bai ƙara jin haushi ba sai yadda tayi ta rungumarsu tana shirin taƙushe masa hancin baby jiya yayi kamar ya fesgota ta dawo kusa dashi, ganin sun juya sun tafi ba tare da sun jira fitowarsa bane ya ƙara ɓata masa rai a fili ya furta
"Wato yanzu ni ba a damu da ni ba ko?"
Ganin babu mai bashi amsa ne yasa ya fito a hankali dan har yanzu zuciyarsa zafi take masa ta ƙofar baya ya shiga part ɗinsa yana nan fes kamar ko da yaushe Alwala yayi ya nufi masallaci dan an fara ƙiran salla.
A masallacin suka haɗu da Nazmar da Papa wanda dawowansa kenan ya ji ana ƙiran sallah shiyasa bai shigo ba ya nufi masallaci a tare suka shigo su ukun bakinsu ɗauke da sallama banda Taufeeq wanda yayi nasa chan ƙasan maƙoshi wanda daga shi sai zuciyarsa fuskar nan kuwa ya dake haɗeta kamar Zaki da fara Papa ya shiga yana faɗin
"Mutanan Abuja kun iso kenan?
Kayinta ta ɗan sauƙar cike da ladami tace
"Eh Papa ina wuni."
"Lafiya ƙalau Dota ya jiki dafatan dai kinji sauƙi?"
"Ai Papa na warke ma."
Ta faɗa cike da kunya tana dake sunkuyar da kanta ƙasa dan har ga Allah a karon farko kunyar mahaifin nata take ji.
Taufeeq ne ya ƙariso falon ya zauna a tare Samha da Hudah suka gaishesu kai ya jinjina musu ba tare da ya musu magana ba fuskar nan babu walwala.
A hankali ya buɗe baki yace
"Sweetie barka da dare."
"Barka dai."
Ta faɗa a ɗakile.
Kallonta yayi jin yadda ta amsa masa kwaɓe fuska yayi kamar zaiyi kuka yace
"Sweetie fushi kuma? ba gashi na kawo miki ita ba dan Allah kiyi haƙuri ni bana son fushin nan."
Ya ƙarisa maganar da alamun magiya.
Dariya Papa yayi yace
"To yau dai za aji kanku kenan?"
Murmushi Sweetie tayi kana tace
"Babu mai jin kammu My son naji daɗi sosai da ka kawo min ita Allah ya muku albarka."
Da "amin"
Ya amsa ciki da farin ciki dan a rayuwarsa babu abun da yafi ƙauna fiye da farin cikin iyayensa a ko da yaushe yana ƙaunar yaji albarka ta fito daga bakinsu zuga garesa.
Su Samha kuma suna zaune kamar gumaka dan ko kyakkyawan motsi basayi numfashi ma a hankali suke sauƙe shi kamar sun ga mala'ila dan fuskar san nan tam.
Nabeeha kuma mamaki take ganin sauyawar Abwaan ɗin nata lokaci ɗaya duk da dama tun da suka taho walwalar fuskar tasa ta ɗauke amma yanzu ya ƙara tamketa.
Papa ne yace
"Wato dai kun sake haɗakan to dai a juri zuwa rafi."
"Watarana tulun sai ya fashe."
Cikin haɗe baki Taufeeq da Sweetie suka faɗa dariya sukayi wanda Taufeeq kuma murmushi yayi dan har yanzu salam yake jinsa idanu ya zubawa Nabeeha wanda yake jin wani abu na daban na ƙara ziyartar zuciyarsa yace
"Ni yunwa nake ji."
Still yana ƙara kallon Nabeeha Sweetie ne ta miƙe ta nufi kitchin ta haɗo masa duk wani abu da ya sabaci a falon ya zauna yana ci amma idanunsa na kan Nabeeha su Samha dai a hankali suka zame suka bar falon Papa ma sama ya haura dan yauɗin a gajiya ya dawo ya rage falon daga Taufeeq sai Nabeeha da Sweetie.
Sweetie ne ta kalli Nabeeha ganin kamar a takure take cike da kulawa tace
"Maza tashi ki shige ɗakin ku naga kamar bacci kike ji."
Aiko kamar tasan a matse take da sauri ta miƙe har ta na haɗa hanya ta nufi ɗakinta na da.
Wani ƙululun ɓakin ciki ne ya tokare masa maƙoshi dan sam baiso hakan ba taya mutum da matarsa za a wani ce ta tafi wani ɗaki ji yayi abincin ya isheshi hakan yasa ya ture plate ɗin daga gabansa a hankali Sweetie ta ɗago tana kallonsa.
Langwaɓar da kai yayi kamar zai sa ihu yace
"Amma Sweetie ya za kice ta tafi chan bayan gasu Samha da Hudah a ciki ai zasu takurata da surutan su na banza da hofi me zai hana ta tafi part ɗina."
Murmushi Sweetie tayi har kuma za tayi magana sai ta fasa tace
"Kuma haka ne bari naje na sa ta tafi part ɗin naka tunda chan babu surutu sai dai tumurmusa."
Ta faɗa cike da gano inda ya dosa.
Shiko a karon farko farinciki ya cikasa dan tun da yazo gidan ba a masa abun da ya sashi farin ciki kamar wannan ba tashi yayi tun kan su fito yayi part ɗinsa damar kuma itace damuwarsa dan yasan bazai iya rintsawa ba in bata jikinsa.
Tana shiga ta samu sai hira suke zubawa babu alamun bacci a tattare da ita cike da kulawa tace
"Taso Nabeeha kije mijinki yana ƙiranki yana part ɗinsa."
Gabanta ne ya faɗi jin haka duk da tana son kasancewa da mijinta amma tasan baza su zauna haka wani abu bai faru ba cikin sanyi tace
"Tom Sweetie."
Daga haka ta fita tare suka fito Sweetie ta nufi ɗakin Papa domin kai masa abincin sa ita kuma ta nufi part ɗin mijintan.
A hankali take tafi kamar baza ta taka ba duk jikinta a sanyaye yake da sallama ta shiga falon a zaune ta hangesa yana zuƙan sigari a hankali yana fesar da iskar.
Har ga Allah bata ƙaunar shan sigarin da yake so take ta masa magana akan shan sigarin da yake amma tana matuƙar tsoro kar ya mata wannan marin nasa da baza ta taɓa mancewa ba.
A hankali ta ƙaro ta nemi kujera chan nesa da shi tana me toshe hanci saboda bata son warin ganin hakan da tayi ne yasa yayi saurin kasheta dan yayi tunanin ko cikin nata baya son warin hannunsa ya ware alamun tazo garesa.
Miƙewa tayi ta ƙaraso inda yake hannunsa ya jawota ta shige jikinsa ajiyar zuciya suka sauƙe cikin mayen sonta ya sanya hannunsa cikin rigarta tare da kama Nimple ɗinta yana wani irin murzawa cike da ƙwarewa.
Dama tasan hakan ce zata faru dan ta gama gane waye mijinta baya tasa gajiya da mace a falon suka gama taɓe-taɓensu da tanɗe tanɗe kana suka shige bathroom a tare sukayi wanka suka zube a kan gado baccin gajiya yayi awun gaba da su.



*******

Sai a lokacin taji wasu hawaye masu matuƙar zafi da ƙuna suka samu damar fitowa daga cikin idanunta a hankali ta ɗago ta kalli Abba cike ƙaunarsa tun da take a rayuwar bayan iyayenta bata taɓa ganin wanda ya sotsa tsakani da Allah ba irin Abba ita kanta tana jinsa a jikinta ji take ina ma shima ɗaya daga cikin ahalinta ne da tafi kowa farin ciki da murna sai dai kuma tasan hakan bazai taɓa faruwa ba goge hawayen da suka zubo mata tayi tare da gyara zamanta tace.
Abba duk wani zaɓin da kaga ya dace dani ka aura min ni mai bin umurnin ka ne in ma makaho ne ko kurma Abba ko da kuturu ne in ka aura min shi zan zauna da shi ni bai biyayyace a gareka Abba Lamir kuma Allah yasa hakan shine mafi alheri a gare mu baki ɗaya Allah ya bashi wacce ta fini.
Ta ƙarisa maganar tana goge wasu hawayen da suka zubo masa.
Abba cike da tausayinta ya kamota tare da goge mata hawaye yace
"Amatullah ba Kuturu ba ne ba kuma makaho bane ba kurma ba ne kuma in sha Allah ke kanki za kiyi alfahari da zaɓin da na miki ba kowa na zaɓa miki ba face ɗana kuma jinina mafi soyiwa a gareni wato Yayanku Saifudden.
A matuƙar firgice ta ɗago tare da dafa ƙirji cike da tsoro da kuma son tabbatarwa tace
"Yaya Saif Abba?"
Kai ya kaɗa mata alamar "eh"
Wani jiri taji ya ɗibeta sai ji yayi ta faɗi ƙasa tim!
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Amatullah! Amatullah Amatullah!!!
Ya ƙirata tare da nufarta da sauri cike da tashin hankali jijjigata yake amma babu alamun rai a jikinta a daidai lokacin Ammy ta shigo domin za ayiwa su Amatullah ƙunshi ganin halin da take ciki ne cike da tashin hankali tayi kanta tana faɗin
"Subhanallah Me ya faru da ita Alhaji?
Ta faɗa tare da riƙota tana jijjagata amma babu alamar motsi a Tattare da ita Abba ne ya ɗauko ruwa tare da watsa mata amma babu alamun akwai wani sauran numfashi a tattare da Amatullah.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun!
"Allahuma ajirni fi musibati wa'akilni khairan minha...!

*My pan's yanzu tafiya ce miƙaƙƙiya muke ba tare da gargada ba in kun bani haɗin kai wajen yin zazzafan comments yanzu zamu kammala wannan littafi ba tare da ɓata lokaci ba, maza ku cigaba da mazgo comment ni kuma naci gaba da sambaɗo muku posting Ina sonku irin jibga jibga ɗin nan.*😘😘💋



#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212


*TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

*Episode 55&56*
... "Amatullahi! Amatullah!! dan Allah ki tashi kada ki tafi ki barmu wlh muna jinki har cikin zuciyar mu innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Alhaji bata motsi fa dan Allah ƙara zuba mata ruwan".
Abba da gaba ɗaya a kiɗime yake ya sake buɗe wani goran ya tiltila mata shi duka a jikinta.
"hhhhhhhhh! hummmmmmmm!!!
Wani irin dogon numfashi taja tare da sauƙeshi a hankali ta fara buɗe idanunta ta buɗesu tar akan Ammy da idanunta suka kumbura tsabar kuka ga kuma hawayen da ke bin kan fuskarta.
Ammy ganin ta tashi ne ta rungumeta tsam a jikinta tana sauƙe ajiyar zuciya.
"Alhamdulillah.!
"Alhamdulillah.!
Alhamdulillah.!!
Shine abun da suke faɗa musamman Abba da yake ganin kamar shine silar faruwan haka wani irin kuka ne wa ƙwacewa Amatullah bayan ta tuno duk abun da ke faruwa kuka tayi sosai a jikin Ammy ba tare da sun tsayar da ita ko sun hanata ba sai dai kuma ganin bata da niyar tsagaita kukan nata ne yasa Abba ya ɗauko mata goron ruwa me sanyi ya buɗe ya miƙa mata.
"Karɓi ki sha."
Ba musu kuwa ta karɓa ta kafa kanta sai da ta shanye tas sannan ta ajiye goron ji tayi zuciyarta ta fara sanyi a hankali ta fara sauƙe ajiyar zuciya sai dai tuni zazzaɓi ya rufeta dan jikintan nan kau kamar garwashin wuta jin hakan da Ammy tayi ne ta ɗago rinanun idanunta ta kalli Abba da sai yanzu ya nemi waje ya zauna yana maida ajiyar zuciya.
"Abbansu jikinta yayi tsanani fa a ƙira likita yazo nan gida dan ƙila dai a ɗaura mata ruwa dan jikin yayi zafi ainun.
Jinjina kai yayi alamar "to"
Sannan yace
"Fatima ki ɗauketa ki kaita ɗakin da kika san babu wata hayaniya yanxu Dr. Zaizo ya dubata ta.
Miƙar da Amatullah tayi amma sai taga Amatun ta koma tq zauna gyara zama tayi tana kallon Abba tace
"Abba na amince da zaɓin da kamin haƙiƙa kai ɗin mutumin kirki ne ka cika adali tabbas bazan taɓa mance wannan halaccin da ka min ba Abba ace baka sanni ba baka kuma san suwa yi ahali na ba baka ma damu da ka sanin ba amma ka ɗauki ɗan ka guda zaka haɗani aure da shi babu abun da zance da kai sai dai na yi muku fatan gamawa da duniya lafiya dan kun gama min komai tun bayan Mutuwar mahaifana kaine mutum na farko da ka fara nunamin soyayya da tausayi da kuma jinƙai na gode Abba.
Ta ƙarisa maganar wasu hawaye masu zafi suka fara sintiri akan fuskarta.
Cike da farin ciki Abba yace
"Na gode Amatullah in sha Allahu kuma baza kiyi ɗan dakin sani ba tashi maza kije ki cire waɗan nan kiƙaƙƙun kayan likita yazo ya baki magani.
Ammy ne ta taimaka mata suka fitoa direct ɗakinta ta nufa da ita dan tasan nane kawai ba tulun jama'a suna shiga kuwa hakan ta tarar ba kowa a ciki sai ƙanwarta Hajiya Mariya ajiya Amatullah ɗin tayi ta fita ba jimawa ta dawo ɗauke da kayanta sabbi na biki da Abba ya musu miƙa mata tayi tana faɗi
"Maza sauya ki haye gado ki kwanta yanzu likinta zai zo".
"Tom".
Ta faɗa a sanyaye dan gaba ɗaya wani irin layi take ji sam ba komai take ganewa ba musamman in ta tuna Lamir.
Fita Ammy tayi ita da Hajiya Mariya da take yiwa Amatullah sannu.
Sauya kayan tayi ta haye gado ta kwanta wani irin zazzafan zazzaɓi na sake rufeta gaba ɗaya ɗakin ne taji yana juya mata ga wani irin sanyi da take ji duk da ta rufu da blanket mai kauri amma bata dai na jin sanyi ba.
Tana a haka Dr. Ma'aruf yazo ya gwadata tare da ɗaura mata drip ya zuba magani a ciki nan take kuwa baccin azaba ya ɗauketa, tana sauƙe wani irin ajiyar zuciya.
Abba kuwa suna fito bayan ya ƙila Dr. Saif ya ƙira yace ya samesa a falon sa ba jimawa kuwa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama duk yayi wani iri da shi ya rame.
Ri sinawa yayi yana faɗin
"Abba ga ni nan Allah yasa dai lafiya?
"Lafiya ƙalau Saifudden sai alheri".
Gyaran murya yayi yaci gaba da cewa
"Ba sai na tsaya yi maka dogon jawabi ba dan kasan komai, kasan dai iyayen abokin ka Lamir sun fasa auren Amatullah ko?
Da sauri Saif ya ɗago cike da kaɗuwa, mamaki, farin ciki domin shi kwata-kwata bai san da wannan daddaɗan labarin ba yace
"Abba wlh bani da labari garin yaya mais yasa kuma suka fasa?
A lokaci guda ya jefowa Abba wannan tambayar wacce mana kallon fuskarsa za ka gane tsananin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa sai da ya fallasa sirrin zuciyarsa.
Murmushi Abba yayi ya sanar masa duk abun da ya faru ya ƙara da cewa
"Haka ne yasa na yanke wani hukunci wanda nasan za kafi kowa farin ciki, domin nasan kana sonta hakan yasa san haɗa ku aure da ita yadda kuma aka sa date baza a ɗaga shirye ba dan haka sai ka fara shiri.
"Wayyooo Allah na! Ihu zanyi ne ko kabbara zanyi? Allahu akbar Allah mai iko Allah mai yadda yaso kana naka Allah na nashi na Allah shine dai-dai Allah na gode maka".
Duk wannan maganar a fili yake yi ba tare da yasan hakan ba dan duk ya ɗauka cikin zuciyarsa yake sai da yaji Abba yana faɗi
"To sannu maras kunya".
Sannan ya dawo cikin hankali sa tare da sunkuyar da kai yana tsotsa ƙeya alamar kunya.
Abba ne yace
"Kaga ka riƙe min ɗiya da amana kar naji kar na gani kamar yadda kake riƙe da Nana hannu bibbiyu itama Amatullah ka riƙe min ita hannu biyu.
"Ai Abba hannu ɗari-ɗari ma zan riƙeta wlh".
A zuciyarsa ya faɗa yana jin wani irin yalwataccen farin ciki so yake kawai Abban nasa ya sallamesa yaje ya ganta so yake kawai ya ganta ko zai ƙara samun nutsuwa fiye da wanda yake ciki yanzu.
Nasiha Abba yayi ta masa mai rasa zuciya ya ƙara da cewa "sai ka sanar da abokanka na kusa tunda abun yazo ba shiri sannan fargabata Nana ce kawai ban san yadda za ɗauki lamarin ba...

Ji yayi gabansa ya faɗi domin sai yanzu ya tuna akwai aiki a gabansa dan yasan yadda Nana ta tsani ayi zancen kishiya ta dinga sababi kenan da ɗagawa kanta hankali balle kuma ace ita za ayiwa dakewa yayi yace

"In-sha-Allahu Abba zanyi

Please Login or Register in order to submit comment