Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata gamshashshiyar bayani na tabbata baza a samu matsala ba.

"To Allah yasa ai hakan muke fata ayi komai cikin kwanciyar hankali za ka iya tafiya Allah ya maka albarka.

Cike da farin ciki ya miƙe yana faɗin "Amin ya rabbi Abbana na gode".


*My Fan's I love u ficika-ficika wlh yanzu rashin comment ɗinku yasa na adama hankali na waje ɗaya bazai yiwu ina faranta muku ku bakwa farantamin ba amma duk da haka ina muku son so domin Allah*😘✨🌹

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212


*TAUFEEK*
NA
*Hafsat A Garkuwa*

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

*Episode 57&58*
… Yana fitowa direct ɗakin su Zarah yana shiga su Zarah ya gani da zugar ƙawayenta sai baza ido yake amma bai hangi Amaa ba gaisuwa suke ta miƙo masa amma da kai kawai yake amsa musu, ganin babu alamarta ne ya kwaɓe fuska ya kalli Zarah
"Zarah ina Amatullah?"
Cike da girmamawa tace
"Wlh nima ban san inda take ba tun lokacin da Ammy tazo ta fita da ita har yanzu bata dawo ba."
Ajiyar zuciya ya sauƙe dan yasan tabbas tana ɗakin Ammyn su ficewa yayi ba tare da ya ce komai ba ya nufi ɗakin Ammy yana fatan ta kasance a ɗakin dan ko bazai mata magana ba shi dai kawai ya ganta.
A hankali ya buɗe ƙofar tare da sallama a bakinsa ɗakin wayam ya gani sai da yayi tozali da fuskanta da take bacci yaji wani sanyi tare da farinciki a zuciyarsa.
"Ina ma an ɗaura mana aure da babu abun da zai hanani haurawa na rungumeki muyi baccin a tare."
Ya faɗa a zuciyarsa tare da kurawa fuskarta ido wacce take bacci cike da wahalar zazzaɓi dan kana ganin yadda numfashin ta ke fita za kasan bata da lafiya.
Kallonta yake ba ƙaƙƙautawa shi dai har ga Allah yana ji yana mata wani mahaukacin so wanda shi kansa bai tantance a wani muhalli son yake ba yana jinta a jikinsa tun randa ya fara ido huɗu da ita har izuwa yanzu Allah kaɗai yasan irin ƙaunar da yake mata dan shi kansa bazai iya tantancewa ba.
"In-sha-Allahu Amatullah zan baki duk wani kulawa da kika rasa tun a baya zan zame miki Uwa uba ƴan uwa kuma Miji a gareki."
"Allah ubangiji yasa Babana."
Yaji muryar Ammynsa ta doshi dodon kunnensa dariya yasa yana sosa ƙeya yace
"Ammy yaushe kika shigo?"
"Ai baza kasan yaushe na shigo ba Babana bata farka bane har yanzu dama nazo dubata ne in ta tashi na bata abinci sai ta sha magani tun da naga ruwan ya jima da ƙarewa ma?"
"Ammy bata da lafiya ne?"
Ya tambaya cike da kulawa
"Eh zazzaɓi ke damunta sai da aka ƙira Dr. Yazo ya ɗaura mata ruwa amma dai naji jikin yanzu ba zafi da alamun ma ya sauƙa.
Cike da tausayinta yace "Allah sarki Allah ya bata lafiya shiyasa naga numfashinta yana fita wani iri."
Ammy dai dariyar ɗan nata take ganin yadda ba kunya suke maganar duk da ta sanshi in dai yana son abu tofa babu maganar kunya cike da zolaya tace
"To ko dai zaka zauna ka min gadinta ne?"
Tun kafin ta ƙarasa maganar ya zauna kan kujera yana faɗin
"Ai kuwa wlh zan yi gadinta har ma ta farka."
Ya faɗa cike da iya gaskiyarsa,dariya Ammy tayi tace
"To sarkin azarɓaɓi mungode tashi ka je kaji da iyalinka ka kuma fara shiri duk da har ga Allah ban so Abban ku yayi haka ba duba da yadda kuke zaune da Nana lafiya.
Kwaɓe fuska yayi yace
"Ammy to ai Allah ne ya haɗa ba Abba ba Abba dai kawai shine sanadi za a ce kuma da ba a kishi ai da wlh bazan bari ke ma a miki kishi ba duk da ni nasan ba irin kishiyarki Amatullah take ba za mu zauna lafiya da su Nana ma akwai ta da biyayya."
Ammy dai tayi matuƙar mamakin jin furucin ɗan nata wato dai son Amatullah gaba ɗaya ya rufe masa ido ɗaka masa duka tayi tana faɗin
"To rasai naji tashi ka ficemin a ɗaki."
Miƙewa yayi yana sosa kai yace
"Ammy na ayi haƙuri suɓutar baki ne."
"Eh naji jeka dai kawai marar kunya.

Fita yayi yana yar dariya part ɗinsa ya nufa sai a sannan gabansa ya faɗi sai yanzu yake jin ba anya zai iya tunkarar Nana da zancen aurensa da Amatullah kuwa? (duk wani namiji muddin suna zaune da matarsa lami lafiya in har ya bijiro da zancen aure in ya tuna da sanarwa matarsa ta gida sai ya rasa nutsuwarsa saboda ba wai dan baya sonta ba ne zai ƙara auren a'a sai dai koyi da sunnar ma'aiki wasu kuma dama da gaiyya za su miki kishiya wasu matan kuma halin su ke sa a ƙaro musu kishiya wani kuma kawai jarrabawa ce ta ubangiji).

A hankali ya tura ƙofar ya shiga yana jin zuciyarsa na tsananta bugawa kamar yadda mahaifinsa ya sanar mata tunda yau yaji abun ita ma ya sanar mata a yau ɗin kar taji a gari da sallama ya shiga ganin bata falon ne ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya ya wuce ɗakinsa da zummar zuwa dare zai sanar da ita.

Sai ƙarfe 3 Amatullah ta tashi zazzaɓin ya sauƙa sai ciwon kai wanka tayi ta ɗauro alwala a nan ɗakin dan Ammy ta hana ta fita a cewarta in ta shiga hayaniya zata takura tunda bata jin daɗi abinci ta kawo mata ta ɗanci kaɗan sannan tasha magani Ammy ta sata ƙara kwanciya, ba dan ta so ba ta kwanta dan ta gaji da kwanciyar amma saboda bin umurnin Ammy yasa ta kwanta, wani abu guda sa take ji sam bata jin kunyar Ammy na kan za ta zama Surkuwarta ita dai kawai ta ɗauketa matsayin mahaifiya ce.

Tunani kawai take na yadda rayuwarta yake juyawa tamkar agogo a da ina zaune cikin ƴan uwana amma sam hankali na ba a kwance ba amma yanzu gani cikin wani dangi wanda su basu da wani abu illa su ganni cikin farin ciki ina ma waɗannan su ne ahalina na gaske? na tabbata da sai nafi kowa farin ciki da haka bani da abun da zan saka musu da shi sai dai biyayya da bin duk wani umurni da suka ba ne.

Haka tayi ta zancen zuciya ita kaɗai sai da aka ƙira sallah ne ta tashi tayo alwala tazo ta gabatar sa sallah tare da fauwalawa Allah duk wani lamuranta fitowa tayi ganin babu kowa a falon ne ta nufi nasu nan ma wayan sai Sumy da take ta zuba Shiri da alamar fita za tayi kwaɓe fuska Amaa tayi tace

"Sumy ina mutanan gidan haka kamar wanda akayi shara."

Dariya Sumy tayi tace

"Yau fa sakun lallanku ba kya ji kiɗa yana tashi ta chan gefen cikin gidan nan duk suna chan ke ma Ammy ne tace baza kije ba saboda baki da lafiya."

Taɓe baki tayi dan Ammy ta yi mata daidai dan koma lafiyarta ƙalau ba ta jin za ta iya zuwa wajen nan.

Ficewa Sumy tayi tana faɗin "ni kam na tafi zan ɗauko miki komai a waya ki gani."

Da kai kawai Amatullah ta amsa mata ta haye gado ta kwanta tare da ɗaukar wayarta ta fara buga game abinta.


Nana ne kwance a jikin Saif gaba ɗaya sai shagwaɓa take masa shi dai kawai jinya yake amma tunaninsa na wajen da zai ɓullo mata da maganar aro jarumta yayi ya yafawa kansa a hankali yace

"Nana ina so za muyi wata magana mais muhimmanci."

"Uhum ina jinka dear."

Zuciyarsa ce ta ƙara karyewa jin abun da yace.

"Um dama..um!

"Abban Amaa dan Allah ka faɗamin mana wai ko dai ba lafiya ba ne?"

Ta tambaya cike da damuwa

Murmushin ƙarfin hali yayi yace

"Lafiya ƙalau dan Allah ina so ki fahimci zance na ki kuma yi masa du ba na tsanake dan Allah Nana Ayshatou kin san ina sonki ina kuma ƙaunarki zan yi wannan abun ne ba wai dan bana sonki ba sai dai yin koyi da ma'aiki sallallahu alaihi wasallama, na san kina matuƙar kishi na amma dan Allah na roƙe ki ki ɗauki hakan a mazannin jarrabawa Ayshatou bari na fito miki a fili nasan kin san an fasa auren Amatullah shine Abba ya yanke hukunci zai auramin ita dan Allah Ayshatou kar ki tada hankalin ki akan wannan kiyi haƙuri dan Allah wlh zanyi adalci a tsakanin ki fiye da yadda kike tunani ni dai roƙona a gareki ki bani haɗin kai mu gudu tare mu kuma tsira tare kinji?."

Murmushi tayi tare da tashi ta zauna fuskartan nan babu alamun ɓacin rai ko tashin hankali.

Yayi matuƙar mamakin ganin yadda bai hango tashin hankalin da yake tunani ba a duk lokacin da ya kawo mata wannan maganar bai tsammaci haka daga gareta ba.

"Abban Amaa meye kake ta bani haƙuri haka? kai fa ka auro ni kuma kana da damar ƙara aure har uku bayan ni kar ka damu in sha Allahu zan kasance mais biyayya a gareka baza kayi kuka da ni ba Allah ubangiji ya bamu zaman lafiya Allah kuma ya baka ikon kwatanta adalci a gare mu."

Wani irin farinciki yaji maras misaltuwa bai taɓa tunani ko a mafarki za ta amince haka cikin ruwan sanyi ba sai kuma ga shi ta fashi mamaki cike da farinciki ya ɗagata ciɗak kamar ƴar tsana ya fara wurgata sama yana chaɓeta kamar ƙaramar yarinya dariya suka fara sosai yana faɗin

"Na gode na gode sosai Nana haƙiƙa ke macece ta gari ke ɗin ta musammance Allah ubangiji ya miki albarka zan kuma kasance adali a gareki bazan taɓa bari ki zubar da hawaye ba Allah ya miki albarka Mar'atusaliha."

"Amin ya rabbil izzati Mijina sabon ango."

Ta faɗa cike da zolaya dariya suka saka gaba ɗaya sannan suna zauna hannu ya sanya cikin aljihunsa ya ciro duk wani kuɗi da yake ciki masu uban yawa ya dan ƙa mata a hannu yana faɗin

"Bani da abun zan iya biyanki na farin cikin da kika sani Allah ne kaɗai zai biyaki Matata."

"Na gode sosai mijina."

Nan suka cigaba da hira fuskanta babu alamun tashin hankali miƙawa tayi tace

"Dear bari nayi wanka na dawo zan sameka a ɗakinka in kuma ban dawo ba sai mu haɗu da safe."

Da "to" ya amsa mata dan dole yabi duk wani umurnin ta dan bai ya fatan ya ɓata mata rai ji yayi ina ma auren zai fasu ma ya zauna da matarsa ita kaɗai suyi rayuwar farin ciki abun su.

Tana shiga ɗakinta ta murzawa ƙofar key ta shige toilet nan ma tasa key wani irin marayan kuka ta sake mai tsuma zuciyar duk wani mai imani haƙiƙa tana son mijinta tana kuma kishinsa amma kuma gashi wata za ta shigo rayuwarsu taya baza tayi kuka ba? sai dai nayi alkawari bazan taɓa nuna masa damuwata akan aurensa ba sai dai na tayashi farin ciki, kuka take sosai wanda ita kanta bata san ta inda suke zuba ba in har kaga Nana sai ta baka tausayi kai kanka sai ka zubar mata da ƙwalla.

(Hattara Mata akwai wasu mata waɗanda in aka sanar musu za ayi musu kishiyi za su fara ihu da gurguwar hauka wanda hakan babu abun da zai sa miki na farko hakan da kikayi ba shi zai sa a fasa auren ba sai dai ma mijin ya ƙara ƙaimi wajen auren kuma kin zubar da ƙima da darajarki a wajen mijinki amma in kina nuna tsantsar farin cikin ki wlh sai mijin yaji ma ina ma za a fasa wannan auren kuma ko da ba a fasa ba wlh kina da ƙima da daraja a wajensa bazai taɓa bari ki wulaƙanta ba, ansan Kishi Halak ne amma kar ya zamana anyi na hauka, ansan kishiya da zafi amma in kika maida komai ba komai ba sai ki samu sauƙi kinuna masa ma kinyi kowa farinciki a inda ba kowa kuma sai kici kukanki son ranki ki rarrashi kanki b tare da kowa ya sani ba kin kuma kafa tarihi kowa zai na kallonki da daraja MATA MUNA SANIN IRIN KISHIN DA ZA MUYI).

Sai da taci kuka sannan tayi wanka ta ɗauro alwala tazo tayi nafilfili tare da roƙon Allah ya sanya mata haƙuri ya cire mata duk wani kishin hauka irin na wasu mata ya sanya mata haƙuri da juriyar zama da Amanullah ta jima tana kan darduma a haka tayi bacci tana sauƙe numfashi irin wanda mutum yayi kuka har ya gaji.

A ɓangaren Saif kuma tun yana zaman jiranta har ya ɗan kwanta gashi baya so yaje ya dameta saboda ta masa abun da har ya mutu bazai mance ba bazai kuma taɓa mancewa da halaccinta ba a haka har ɓacci ɓarawo ya ɗaukesa.


#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
081327612


*TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/


*Episode 59&60*
… A hankali take sauƙowa daga gadon gaba ɗaya yau da wani irin kasala ta tashi duk son ta tashi da wuri domin ta taya Sweetie aiki amma ta kasa tashi har sai yanzu da lokaci ya gama ƙorewa dan ƙarfe 10:30am ake nema tsaki ta ja bayan ta gama sauƙowa sannan ta wuce bathroom bata wani ɗauki lokaci ba ta fito ɗaure da tawul a ƙirjinta, gaban mirror ta zauna ta goge jikinta sannan ta shafa lotion ta murza powder tasa kwalli daga haka ta miƙe dan yau ba ta jin ko lipstick za ta iya shafawa, kayanta tasa na atamfa ɗinkin riga da siket kayan ya amshi jikinta tayi kyau sosai ta ɗan fesa turare flat ɗin takalmi ta sanya ta fito babu kowa a falon sai dai dukka nin alamu an gyara falon dan fes yake sai tashin ƙamshi yake "to waye ya gyara?
Da wannan tambayar da bata da amsa ta fita a hankali take tafiya har ta iso babban falon nasu da sallama ɗauke a bakinta.
Gaba ɗayansu suka amsa mata banda Taufeeq da ya zuba mata ido kamar zai cinyeta wani irin ƙaunar yarinyar gaba ɗaya in ya kalli yarinyar yana jin matuƙar sauyi a tattare da shi, ji yake yanzu kamar ya taso ya rungumeta.
Ƙarasowa tayi ta risina ta gaida Sweetie cike da ladabi.
"Ina kwana Sweetie."
"Lafiya lau Dotar ya jikin na ki? ai tun ɗazu nake so ki taso ki ɗanci wani abu wannan mijin naki ya hana wai a bari ki tashi da kanki kar a takurawa ɗansa.
Sunkuyar da kai tayi cike da kunyar Sweetie sannan ta ɗago a hankali ta kallesa aiko karaf suka haɗa ido ya kanne mata ido ɗaya tare da ɗage mata gira.
Da sauri ta kau da kanta gudun kar Sweetie ta gansu.
Nazmar ta gaisar sannan suka gaisa da su Huda wanda suka nutsu tun zuwan Taufeeq dan in da sabo sun riga da sun saba da hakan.
Sweetie ne ta kalleta tace
"Ma za tashi ki wuce kije ki karya in abun wajen basu miki ba sai ki faɗa.
Miƙewa tayi ta nufi dining ferfesun kayan ciki ne wanda yaji kayan ƙamshi da daddauwa sai kuma chips da ƙwai sai tea zama tayi ta fara ci taji daɗin abincin sosai musamman ferfesun taci sosai sai da ta kammala ta tattare komai na wajen ta dawo cikin falon
"Kin ƙoshi dai ko?
Taji maganar tasa a bazata kallonsa tayi a hankali ta ɗaga masa kai alamar "en."
Shima kan ya ɗaga mata miƙewa yayi yace
"Sweetie zan ɗan fita ina ƙilan zan iya kaiwa azahar, Baby ɗauko mayafinki ki min rakiya."
Ya faɗa a lokaci guda yana kallo Nabeeha ita kuma Sweetie ta kalla ganin ba ta ce komai ba ne yasa ta juya ta nufi part ɗin sa, bata ɗauki lokaci ba ta dawo a hankali tace
"Sweetie sai mun dawo."
"Allah ya tsare Nabeeha, ka dai kula da ƴar mutane kar kaje ka barta da yunwa."
Murmushi yayi tare da kama hannun Nabeeha suka fita yana mamakin wai yau shi ake koyawa kula da abar ƙaunarsa.
Back seat suka shiga jami'ansa tuni suka shiga nasu dama sun san da fitar ficewa sukayi daga gidan har yanzu yana riƙe da hannunta sai da suka hau titi suka fara rausa gudu dan wajen da zasu da ɗan tafiya.
Jawota yayi ta kwanta a jikinsa duk da babu mai cewa uffan dan miskilancin nasa ya sauƙa ita kuwa dama da ba lafiya ba a haka bacci yayi awun gaba da ita jin sautin numfashinta ya sauya ne ya sa ya gane tayi bacci ya gyara mata kwanciya a jikinsa.
Sun yi tafi sosai dan sun ma fita daga cikin gari wani ƙauye suka nufa wanda tun daga bakin hanya za ka fahimci akwai matsala a ƙauye za ka fahimci ruwa ya musu ta'adi ba ɗan kaɗan ba domin duk ga gidaje nan wasu rabu lli sun rushe wasu gaba ɗaya ma wasu kuma saman kwanan ne ya rushe sun shiga cikin ƙauyen sosai wanda a nan kam ma ta'adin yafi yawa dan yawanci gidajen ma babu su sun rushe a ƙofar gidan mai gari sukayi parking inda dubban mutane suke cike a wajen a hankali ya miƙe saboda baya so ya tasheta amma yana sauketa ta buɗe ido murmushi ya sakar mata tare da kama kumatunta
"Baby ban so ki tashi yanzu ba amma da kika ji kin bar jin ɗumin mijinki shine kika tashi ko?"
Dariya tayi tare da rufe idanunta da hannunta dan har ga Allah hakan ne dan yana rabata da jikinsa taji baccin ya fice a idanunta.
Buɗe masa akayi hakan yasa ya gyara  mayafinta suka fita ihu suka faraji mutanan nan suna yi faɗi suke 
"Ba mayi! ba mayi! Ƙaryace ƙaryace!
Bai damu ba illa ƙara damƙe hannun Nabeeha da yayi suka nufi inda mai gari yake.
Mai gari suna ganinsa suka miƙe suna masa barka da zuwa hannu yake ɗaga musu kujera aka ɗauko musu ya zaunar da Nabeeha shima ya zauna bayan sun gaisa ne yayi musu jajen abun da ya faru ya ƙara da cewa
"In-sha-Allahu za mu taimaka muku da na koma za mu fara shirye-shirye domin za a rusa ko ina a tayar muku da sabon gini na block za a muku asibiti da kuma makarantu in Allah ya yarda."
Cike da farin ciki mai gari yace
"Muna godiya sosai Yallaɓo Minister Allah ubangiji ya ƙara girma Allah ya tsare gabanka da bayanka.
Nan aka fara shela ana sanar da jama'a wasu murna suke sosai wasu kuma suna ƙaryatawa shi kanshi mai garin bai gama gaskata maganar ba hakan yasa yace
"Amma yallaɓo kamar fa da kamar wuya wannan lamarin taya za a ce duk ƙauyen nan za a mana gini na zamani har da su asibiti Allah yasa dai kar ka mana na sauran ƴan siyasan su zo su lasa mana zuma a,baki su a hana mu lasa."
Ran Taufeeq ne ya ɓaci sosai jin maganar da mai garin yake faɗa taya ma zai musu ƙarya akan miye? in wasu ƴan siyasan haka suke ya zamana kowa ma haka yake?
Nabeeha ne da ta fahimci ransa ya ɓaci ta kamo hannunsa a hankali tana ɗan murzawa ɗagowa yayi ya kalleta ta girgiza masa kai, lokaci ɗaya yaji ɓacin ran ya kau hakan yasa ta kalli mai garin yace
"In-sha-Allahu zan yi abun da na faɗa.
Daga haka ya miƙe tare da kama hannun Nabeeha suka wuce wajen mota dan da yaso ya zazzagaya garin yaga yadda abun yake amma ɓata masa ran da sukayi yaji bai jin zai iya ƙara cikakken mintuna a garin, rakosa sukayi suna ta godiya wasu kuma na ihun ƙarya ne bai kulasu ba a lokacin da aka buɗe masa motar yasa Nabeeha shima ya shiga tsabar ɓacin rai ma ya mance da abincin da za a raba musu sai PA n sa ne ya sa aka sauƙe musu, suka ja motocinsu suka bar wajen wasu har binsu da gudu suke suna musu ihu sai da mai gari ya dakatar da su, Taufeeq ransa yayi matuƙar ɓaci da abun da ƴan ƙauyen suka musu ina ma zai iya da wlh bazai musu komai a garin ba amma kuma bai jin zai iya domin a duk in da ake buƙatar taimako ko ba a matsayinsa na minister ba yana iya ƙoƙarinsa ganin ya taimaka.
Nabeeha ganin ya tafi tunani ne yasa ta sauƙe ƙyallen da ya raba tsakinsu da driver ta yadda bazai gansu ba suma baza su ganshi ba haɗe bakinsu tayi guri ɗaya tana jin wani son sa da ƙaunarsa na ƙara ratsa duk wani sassa na jikinta sai a yanzu ta tabbatar da tayi dace da nagartaccen miji sai da tayi kissing nasa sosai har ta fara tado masa da abunsa ganin za ta wuce gona da iri ne yasa ya janye bakinsa domin in har ta taɓosa bai jin zai iya haƙura sai dai ayi abun kunya dan tsaf zai turmushe abarsa.
Suna hawa kan titi suka ƙara ɗaukan hanya sunyi tafi na kusan awa uku sannan suka iso wani ƙauye ma wanda shi kam lfyarsa ƙalau sai dai matsalar cikin gida saboda gaba ɗaya matan garin sai sun je sunyi aiki suke samu suci abinci saboda mazan zaman banza suka fi auki akai,bayan sun isa fadar mai gari ne aka musu tarba ta mutunci a nan aka shigar da Nabeeha ciki su kuma suka yi sallah sannan suka dawo suka fata tattaunawa akan lamarin abun da ya kawo su, abinci yasa a ka sauƙe musu mai ɗan karen yawa sannan ya bawa duk wani magidanci jarin da yasan zai ɗanyi sana'ar da zai riƙe gidan sa ya ƙara da cewa nan da ƴan wasu lokaci zai dawo duk wanda aka samu baya riƙe gidansa za a kamashi a kuma hukuntasa sun jima sosai a garin sai da ya tabbatar da ya yi musu duk abun da ya dace ya kuma hana duk wata mace aikin da take zuwa sannan aka fito da Nabeeha suka ɗauki hanya cike da kulawa  yace
"Baby kin dai cinye abun da kika shiga da shi ko?
Dan dama ya saya mata kaza da shawarma da su ice cream da sauran tarkace, dariya tayi tace
"Ni wlh ban ci ba ƴan gidan duk na rabawa ba ka ga murnan da suka yi ba wai su basu taɓa cin irin wannan abubuwan ba har gwanda ma a salla suna cin kaza amma ita ma dai ba irin wannan ba kuma…
Bai bari ta gama ƙarisa maganar ba sa sauri yace
"Ke kuma kika ci miye kuma Baby?"
Dariya tayi tace
"To ka barni na gama baka labarin mana ai za kaji abin da na ci."
"A'a pls faɗamin mai kika ci dan Allah?
"Tom wlh na ci wani dambun su mais ɗan karan daɗi sai da na kusan cinye musu abinci ga wani damun fura da aka min kai Abwaan wlh wannan garin duniya ce duk wani abun gargajiya naci nayi nak nayi kuma bacci."
Cike da mamaki yake kallonta duk da bashi da ƙyamar talaka amma bai jin zai iya cin abincin irin wannan garin domin sake tabbatar da maganar da ta faɗa yace
"Wai da gaske abincin su kika ci?
"Eh wlh Abwaan ba ka ji daɗin da yayi ba ne da kai ma sai ka ci."
Ta faɗa cike da zolaya dan ta sanshi da ƙyanƙyami.
Kwaɓe fuska yayi kamar zai yi amai yace
"Wlh ke ma kika sake cin irin wannan abincin sai na saɓa miki haka kawai ki sauyamin kamannin yaro yazo mai makon ya yi kama da ni sai ya chanza kama."
Ya faɗa da iya gaskiyar sa dan shi har ga Allah bai so ta ci ba.
Murmushi tayi dan sarai ta san shi da ƙyanƙyami cike da kulawa tace
"Tuba nake My Abwaan amma dai babu abin da zai samu Babynka kamanninsa suna nan yadda Allah ya tsara shirin babu wani abu da ya isa ya sauya shi ka ji?"
Kai ya ɗaga kamar wani ƙaramin yaro sai magriba suka shigo angowarsu sun zo dai-dai gidan su maimakon su shiga sai taga sun wuce da mamaki ta ɗago daga jikinsa ta kallesa tace
"Abwaan ina kuma za mu bayan mun iso gida?
Murmushi ya mata yace
"Gidan mu za mu tafi Baby da ma mun san huta gajiyar hanya ne yasa mukayi kwana ɗaya a nan kuma ni gaskiya takura mu za suyi su hana mu rawan gaban hantsi nasan in kika zauna a nan ni da na ganki sai dare, yo ina zan

Please Login or Register in order to submit comment