Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zan baki ki daina kula irin mahaukatan yaran nan irin su wannan da ta miki shirme ya faɗa yana nuna Raudah da gaba ɗaya kunya ta gama rufeta dan bata tsammaci ƙaiƙayi zai koma kan masheƙiya ba harara ya balla mata.
Cike da burin kunya tace
"Ai kai ne mahaukacin wawa kawai kai kasan waye ubana a garin nam kuwa? kasan matsayin mahaifini kuwa?
Harara ya ƙara watsa mata cikin ko in kula yace
"Ke ƴar gidan ɗan adam ne me kunne biyu, ido biyu, hanci ɗaya, da kuma baki ɗaya, hannunsa guda biyu haka zalika ƙafansa biyu a ko wanni ƙafa da hannu suna ɗauke da yatsu biyar, kin tabbatar na masa farin sani ko?
Ya faɗa yana ɗage mata gira gaba ɗaya wajen suka sa dariya, Zarah ta kama Hannun Amatu tace
"Kunga mu shige a nan wlh ni yunwa ta isheni kuma yau ban jin zan iya cin abincin skul d'in nan.
Wuce wa sukayi da sauri ya biyo su yana faɗin ni ma ko bazan iya ci ba ko za muje wani eatry ne mu samu abun taɓawa da sauri Kausar tace
"Wlh kuwa kamar kasan abun da ke raina"
Harara Amatu ta galla mata tana faɗin
"To ni dai ba dani za ayi haka ba
"Bare kuma ni! cewar Zarah tana nuna kanta da hanxari ya dawo gefen da Zarah take yace haba "Sis wannan wacce irin mugunta ce haka ya ina ji ina gani za kisa na rasa damar da na samu a yau.
Murmushi Zarah tayi dan ta gane mai yake nufi sarai dan tun ba yau ba ta gane take-taken shi kawai damace da bai samu ba cikin zolaya tace
"To ni dai babu abun da zance in Lil sis ta amince to nima na amince.
Ɗaka mata duka Amatu tayi tace "wato ni so kuke yaga baƙi na ko? In nace baza mu je ba shikenan sai kusa ya ƙullace ni a ransa to baruwa na.
Dariya yayi yace "yanzu dai kin amince ko?
Kai ta ɗaga tare da faɗin "to ya na iya.
Cike da farin ciki ya ɗaga hannunsa ɗaya tare da naushin iska yana faɗin

"Godiya nake maras adadi bismillahn ku ga mota ta chan muje
Jim Amatu tayi tace
"Kaje kawai za mu tawo a motar gida kaga bazai yiwu mubar ƴan uwan mu ba
Ɓata fuska yayi kamar zaiyi kuka ya kalli Zarah.
Dariya Zarah tayi tace "to ai kinga drivern bai zo ba kawai muje 'in muka kammala sai ya ajiye mu gida su kuma in driver yazo sai yaɗauke su, ba haka taso ba but ba yadda ta iya dan ta fahimci Zarah na ɓangaren wannan Akun dan sunan da ta lankaya masa kenam.

Wai ina labarin Yaya Sadiq ne?🤣

Tun da Amatullah ta bugesa ya gwaru da gini ya faɗi sumamme saboda mugun buguwar da yayi shine bai farfaɗo ba har sai asuba, a hankali ya fara buɗe idanunsa tare da rike kansa dake barazanar ɓallewa, dube-dube ya fara amma ba bu Amatullah ba labarinta sai kayan da ya yage a jikinta a hankali ya laluɓi kayansa ya sanya ya nifi bathroom yana murɗawa ya buɗe shiga yayi amma bai ganta ba mamakin inda ta tafi yake ganin bai ganta ba yasa ya fice a ɗakin yana tsaki, da jin haushin Amatullah dan a yau ya gama shirin yadda zai shige duniyarta amma kuma sai gashi haƙansa bai cin ma ruwa ba, part dinsa ya nufa yana zuwa ya shige bathroom ya hada ruwa mai uban zafi ya gasa jikinsa saboda ciwon da yake masa ga goshin sa yadda ya kumbura suntum sai ƙyalli yake zubawa, bai iya fita salla ba a ɗakin yayi saboda wani irin zazzaɓi da ya rufeshi da ƙyar ya iya shan magani ya kwanta cike da haushi da tsanar Amatullah
Washe gari iyalan gidan ganin har ƙarfe 8 Amatullah bata fito ta ɗaura breakfast ba ne yasa Mm Baraka tazo babu inda bata duba ba amma ba Amatullah sai kayan baccin ta da yake a yashe a ɗakin, su Baba Jibbo ta sanarwa hakan yasa suka dubata a cikin gidan wannan yayi chan wacchar ma tayi ce, neman da suke mata ba wai don su san tana ina bane sai dan su kamata su hukuntata, amma ba bu inda basu duba ba babu ita ba labarin ta,hakan yasa suka tambayi mai gadi, sanar da su da ya fito dai yaga an buɗe ƙofa ganin bai ji wani hayaniya ba yasa ya rufe ƙofan ya koma ya kwanta dan dama fitsari ya fita yi, jin haka yasa suka dai na nemanta suka koma falo suna faɗin Allah yasa ta tafi kenam har'abada kowa yana faɗin albarkacin bakinsa, gaba ɗaya murna suke da tafiyarta, Sadiq bai san me ake ba, yana chan yana jinyar kansa, yunwa ne ya tashesa yayi wanka ya fito goshin nasa ya sabe ba kamar da ba, ko da ya fito aka sanar masa bai wani damu ba haushin sa ɗaya bai sha romonta ba amma yayi alƙawari idonsa idonta sai yasha zumanta son ransa, haka kowa yaci gaba da harkokinsa cikin kwanciyar hankali babu wanda yake tunawa da Amatullah sai Sadiq shima ba dan Allah ba sai dan zumanta da yake hangowa, tuni suka ɗauki mai aiki, kudi kuwa cinsa kawai suke ba kama hannun yaro, yanzu an doshi wata uku ko a jikinsu da ɓacewar Amatullah duk wanda ya tambaye su ita amsa ɗaya suke bashi wai ta tafiya yawon duniya.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Yana nan zaune Nabeeha ta fito tana tafe tana haɗa hanya dan yunwa dan har ga Allah bata wasa da cikinta in dai ta wuni bata ci ba to kana kallonta zaka gane hakan dan tuni zata fice a hayyacinta, ko in da yake bata kalla ba ta wuce shima hakan bai damesa ba, dan da ta masa magana ma zai iya mangareta, tana shiga kitchen taliya ta dafa wanda yaji hanta da kayan lambu ta juyo shi tare da ɗaukan drink tazo tayi wucewar ta tana tafe tana rire ƴar waƙarta Tana shiga taci tayi haniƙan tabi lafiyar gado tv ta kunna a ɗakinta tana kallonta cikin kwanciyar hankali da ƙarfi taji yana rafka mata ƙira a hankali ta miƙe ta fita a ƙasa ta hangesa yana zaune inda ta barshi, sauƙa tayi ta isa gareshi tare da faɗin
"Ga ni"
Fuskar ta a haɗe, shima tashin haka take, bai kalleta ba yace
"Abun da kika zo dama kenan?  Ki dafawa kanki sannan kici kiyi kashi ki kwanta, to ba abun da ya kawo ki ba kenan, akwai Larai da take girkawa ƴan aiki abinci da kuma sharan falon nan to daga yau na soke mata zata ci gaba da kula da shashinta ke za kina wannan aiki, zaki ƙirata kiji adadin da take musu da kuma lokacin da ake musu dafatan kin jini?
Ko a jikinta dan dama in dai aiki ne ta saba sai dai girki ne baza ta iya mai yawa ba, amma haka ta dake dan kar ma yaga wata alamar da zai rainata in jita ba inji Hafsat Garkuwa ba🤣
Cikin dakiya tace
"Aiki ba matsalata bace zanyi daga haka ta haura sama har ta kusa isa ya dakatar ta da faɗin
"Yau zaki fara domin na dakatar da Larai dan haka yanzu ma jiran abinci suke.
Da "tom" ta amsa masa ta wuce ɗaki ta ɗauko mayafi ta nufi fannin su Larai, part ɗin n su ɗan madaidaci ne irin na masu aiki chan gefe kuma shine na maza, matan su huɗu ne, amma manya ne sosai hanasu aikin yayi saboda yanzu baza su iya sannan ya hana su tafi hakan yasa suka zauna yana basu ci da sha kasancewar basu da kowa, ko ita Larai dama mahaifiyarta ce take aiki, amma da ta rasu hakan yasa Laran take yi, zaune suke suna ta hira tayi sallama, gaba ɗaya suka miƙe suna faɗin
"Hajiya ke da kanki ai da kin bari munzo da kan mu"
Murmushi Nabeeha tayi tare da jin haushin Taufeek da ya ɗauki dattijawan nan aiki mai makon ya taimaka musu yana minister ƙarawa tayi tana faɗin "ba komai ai wlh ina kwanan ku"
Cike da fara'a suka amsa da "lafiya ƙalau ya kuma kwanan baƙunta?
"Lafiya lau ta faɗa tana murmushi
Larai ne ta gaidata ta amsa tana faɗin "shine tun da kika gudu baki dawo ba ko?
Rufe baki Larai tayi tana fadin "Hajiya ai doka ce in har na gama abun da nake to ba zama, yanzu kam gaba ɗaya zaki daina gani na ma amma ni dai banji daɗin hakan ba, ban sani ba ko wata me aikin aka kawo ba.
Murmushi tayi tace
"Babu wata me aiki ni zan rinƙa musu yanzu ma nazo ki gayamin yadda ake ne.

Cike da mamaki gaba ɗaya suke kallon ta dan gaba ɗaya basu taɓa tunanin Matar Yallaɓai guda zata yi aiki ko da na ɗaga ƙwayan tsintsiya ne balle kuma shara da girkin ƴan aiki.
Larai bata iya yin shiru ba tace "ke kuma Hajiya? taya zaki iya girkin masu aiki suna da yawa fa.
"Kar ki damu muce ki sanar min lokaci na tafi, mikewa tayi ta musu sallama tana fadin in ta gama zata dawo suyi hira, da Larai suka fice tana cike da mamaki.

Aiki ne bana wasa ba amma cikin ikon Allah da taimakon Larai suka kammala suka zuba musu ta kai musu sannan ta kaiwa su Baba nasu ɗaki ta nufa a matuƙar gajiya kana kallonta zaka gane tayi matuƙar wahala idanun nan nata daga fari suka rine suka koma ja,cikin haɗaya hanya ta shiga ɗakinta tana shiga wani jiri ya ɗibeta sai ji kake luu! ta faɗi ƙasa sumammiya.

_Sanarwa! Sanarwa! Sanarwa!!_

*Ina sanar da masoya cewar zamu fara class na matsalolin ma'aurata tare da hanyar magance su, da kuma gyaran jiki da sirruka da dama sai dai fa gidan ba kunya za ayi bayani yadda kowa zai fahimta ina tabbatar miki ƴar uwa baza kiyi asarar kuɗin ki ba za mu fara ne da zaran mun shiga sabuwar shekara wato 1st January 2022… zaku iya fara biya tun daga wannan rana cikin farashi me sauƙin biya, domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan number* 08132761212

_Kaɗan daga ciki_👇🏻
'''Akwai mata da yawa da basu san dadin saduwa, idan aka raba matanmu na arewa kashi ɗari da ƙyar zaka samu kashi sha biyar da zasu ce maka suna jin daɗin saduwar aure, wannan babban lamari ne sannan idan mukayi duba da hadisi da yake cewa. "Babu kunya a cikin addini, dole mu warware wannan matsalar bakin gwargwadon iyawar mu,
Da akwai dalilai da dama da kan sanya mace taji ita sam bata jin daɗi duk lokacin da mijinta ya kusance ta gashi kamar haka...'''
Insha Allahu zaku samu dalilai da kuna hanyan da zaku magance ta da kan ku hajiyata kar ki bari ayi babu ke a wannan tafiya😁

*ONE LOVE*💞🤞🏻

*TAUFEEK*

NA

*Hafsat A Garkuwa*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*Episode 27&28*

*...* "To fa! ko ina za mu je oho gashi ba halin tambaya dan wannan fuskar nasa bazai bar mutum ya tambaya ba, ko gida zai kai ni? Allah ma yasa gida ne da walle in na tafi bazan dawo prison ba, yo ni mahaukaciya ce da zan dawo ai sai dai su Papa su gaji su raba auren amman dai ni na gama zama, haka ta ƙaraci zancen ta.
Washegari tun da tayi sallah tayi wanka ta shirya cikin riga da sket na lace pink colour tayi kyau sosai ta ɗanyi simple makeup tayi kyau sai baza fitinannam ƙamshi take bakwai saura ta fito janye da akwatin ta madaidaici da ƴar ƙaramar jaka cike da ɗokin zata gida, ko ta cikinta yau bata yi saboda farinciki ya gama cika cikin nata, falon ba kowa sai yaƙar A.C ganin akwai sauran lokaci yasa ta tafi bangaren su Baba domin tayi musu sallama, kamar kullum sun jima da tashi har sun gyara matsugunin su, gaisawa sukayi cike da farin ciki take sanar da su zata tafi gida, addu'a suka mata tare da fatan dawowa lafiya, a zuciyarta tace
"Taɓ! ai ni da ku kuma sai dai wani ikon Allah, dan ni da Abuja sai dai hanya ta biyo da ni, a fili kuma tace "Amin ya Allah na gode bari naje ƙilan ya sauƙƙo.
Larai ne ta rakota har bakin corridor da zai sada ta da part ɗin su tare da karɓar number juna, tana isa ta samu ya sauƙo cikin shigar suit  mai ɗan karan kyau sai zuba fitinan nan ƙamshi yake, duk kyan da tasan tayi sai ta raina kanta domin yakereta nesa ba kusa ba, ganin ya sauƙo tayi saurin ɗauke kanta, bai kalleta ba cikin harcen turanci yace
"Muje ko"
Jan akwatin ta tayi tana binsa a hankali yake tafiya hakan yasa bai yi mata wani nisa ba, tuni masu tsaron sa sun buɗe musu mota,in da taga ya shiga ita ma nan ta shiga bayan ta miƙawa ɗaya daga cikin su akwatin ta, tana shiga ya falla mata a harara yana fadin "uban wa yace miki ki shigo motar nan duk motocin da ke wajen?
Kwaɓe baki tayi kamar za tayi kuka cike da shagwaɓa tace
"To ai naga baka ce na shiga ba ne shiyasa ban shiga ba.
"To nan d'in ni na baki izini da kika shigo?
Baki ta turo tace "to wanne zan shiga?
Harara ya balla mata yace "ban sani ba munafuka kawai!
Nan da nan idanunta ya ciko da ƙwalla dan a duniya ta tsani a ƙirata da kalmar munafuka ta tsani wannan kalmar dan ji take ƙasƙanta mutum ne ba ɗan kaɗan ba, bata yi auni ba sai ji tayi har sun hau titi.
a hankali take sa hannunta tana goge ƙwallar idanunta basu zarce ko ina ba sai filin jirgi, mamaki ne ya kamata ganin ba ƙaramin jirgin sa da suke zuwa Kaduna bane wannan babba ne, suna isa aka fara ƙiran fasinjoji sune farko cikin kujerun VIP ko kallonta baiyi ba ya tafi,ganin haka ne yasa tabi bayansa kujerun su a haɗe yake shine a dungu ita ce a baki-baki kowa kallonsu kawai yake dan duk wanda ya kallesu dole su baka sha'awa dan ba ƙaramin dacewa sukayi ba, basu wani jima ba jirgi ya lula, tun tana lumshe idanu har baccin yazo da gaske, hakan yasa bata san lokacin da ta ɗaura kanta a kafaɗarsa ba, ban ka mata harara yayi duk da bata san yanayi ba tureta yake shirin yi sai ya tuna a jirgi yake, kuma baza a rasa ƴan jarida ba yana hakan zasu fahimci wani abu, wannan yasa ya ƙara gyara mata kwanciya a jikinsa, ita ko cikin barci ta da ɗa rungumeshi tana sauƙar da numfashi, wani ƙululun abu ne ya tsaya masa ga ba halin tureta dole ya haƙura, 11hrs ya dirar da su a birnin Mumbai
Ganin an fara sauƙa ne kuma bata farka ba yasa ya zage iya ƙarfin sa ya mintsineta a gefen cikinta, wani ƙara ta sake a gigice dan ba ƙaramin azaba ne ta ziyarce ta ba, da sauri ya haɗe bakin su waje ɗaya, ɗif! wutarta ta ɗauke ido kawai take zarowa tuni jikinta yayi sanyi, mutanan wajen tuni suka juyo suna kallonta jin ƙararta, amma ganin abun da yake wakana yasa kowa ya juya da murmushi akan fuskar su wasu suna fadin dama sune, wasu kuma suna fadin ai sa bari su bar cikin jama'a wannan ai rashin kunya ne (ni dai Hafsat garkuwa nace ko dai kuka sani) ganin tayi tsin jikinta yayi sanyi yasa da sauri ya cire bakinsa a nata tare da jan siririn tsaki a hankali yake fadin "mahaukaciyar banza kawai yayi ficewar sa,kasa tashi tayi dan gaba ɗaya baƙon al'amarin ya gama kashe mata jiki, wata wacce baza ta wuce sa'arta ba ne dake gefenta tana jiran su wuce ita ma ta wuce ganin Nabeeha bata da niyar motsawa ne yasa ta ɗan ta ɓata tana fadin
"Sis ke nake jira ki wuce na samu na fita ko oganki ya kashe miki jiki ne?
Ta faɗa tana ƴar dariyar wasa.
Sai a sannan hankalin Nabeeha ya dawo wanda ya dade da tafiya hutun rabin lokaci, murmushi ta sakar mata tare da tashi da ƙyar dan iya sauyi taji sauyi a jikinta.
A tare suka sauƙo tana fadin "sunana Fannah munzo yawon shakatawa ne da da oga na wani uziri ne ya maida ni nigeria.
Murmushi kawai Nabeeha take binta da shi tana zaro idanun ta inda zata hangi Ogan nata, hangoshi da tayi ne tayiwa Fannah sallama ta nufi inda yake, shiko tun da ya fito yake tsintar da yawo  tuni ya fara jin tashin zuciya amai kawai yake so yayi, mota ya shige tana zuwa ita ma ta shiga suka tafi, sunyi tafiya me nisa sannan suka iso wani tankamemen hotel, kyau, tsada, tsari, ba a magana duk wanda ka ganshi a wajen to yayi filo da naira ce, key ya karba dan tuni an gama masa komai tafiya suke tana bin ko ina da kallo mamaki ne kawai yake cinta tare da tambayoyi masu tarin yawa sai dai kuma babu wanda za ta iya yiwa wannan tambayar, ɗaki mai number 5 yasawa key ya shiga ta bisa, babban falo ne mai ɗauke da ɗaki ɗaya da toilet sai kujeru da kayan kallo da duk wani abun buƙata, kujera ta samu ta zauna tana ƙarewa ɗakin kallo, wasu hawaye ne suka zubo mata ganin ba inda take tunanin suka zo ba, shiko yana shigowa direct bathroom ya nufa ya wanke hannayen sa tare da zirasu cikin bakinsa ya fara ƙaƙarin amai ruwa kawai yake hararwa, wanke bakin yayi sosai sannnam yayi wanka yayi alwala ya fito, har yanzu tashin zuciyar yake ji ya rasa me yake masa dadi, ga wani ƙarin tsanarta da yake ji, lotion ya shafa sannan ya zira kaya marassa nauyi ya fara rama sallar da ake binsa yana idarwa ya fito ganinta yayi har yanzu tana inda take sai goge hawaye take, cikin tsawa yace
"Ke dan ubanki baza kije ki rama sallar da ake binki bane kika zauna kike kuka, ba kinsa Papa ya tilastani akan sai na taho da ke ba wlh za kinsan kin biyo ni sai kin gwammace na binne ki da ranki stupid girl kawai...
Yana faɗar haka yasa kai ya fice yana jan guntun tsaki, kuka ta fashe da shi sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe tana faɗin "ni da nasan ba gida zaka kai ni ba ai babu abun da zai sa na biyo ka, wa zai so zama inuwa ɗaya da kai mugu kawai azzalum, bathroom ta shiga tayi wanka ta ɗauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga, sannan ta shafa lotion da powder ta rama salla, ta haye gado sa a sannan taji wani irin masifaffen yunwa, tuni idanunta sukayi zuru-zuru kamar na zomo(mutumiyar fa yau ba a cika tumbi ba🙀😹)
  Nan da nan ta fara kuka dan dama abun kuka baya mata kaɗan bare kuma yau da cike bai ɗauka na, kuka take kamar ƙaramar yarinya tuni ta fice a haiyacinta, sai ƙarfe 11pm sannan ya shigo tun daga falo yake jiyo kukanta hakan yasa ya ɗanyi sauri, yana zuwa ya ganta kwance sai mutsu-mutsu take wani irin ɓacin rai ne yazo masa, ya ɗaga hannunsa ya sauƙe mata mari…

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Kamar daga sama suka ji Yaya Saif yana faɗin "daga gidan uban wa kuke? wato kuma kun zama ƴan iska ko har kuna ƙiran saurayi yana zuwa school kuna fita dashi ko, ƴan uwanku suna ƙiranku kuna sanar musu cewar holewa za kuje ko?
Tuni Amatullah cikinta ya ɗura ruwa dan ta tsorata sosai ganin yadda yake maganar cikin tsawa, haka ma Kausar Zarah ko ko a jikinta cikin sanyin murya tace
"Yaya koma me ta faɗa wlh ba gaskiya ba ne ni… bata kai ga ƙarasa maganar ba taji ya tsinketa da mari, a tsorace ta ɗago rike da ƙuncinta tuni hawaye suka wanke idanunta dan tun da take Yayansu bai taɓa ɗaga hannu da sunan zao daketa ba sai yau gashi a karon farko ya mareta, riƙe ƙuncinta tayi tana girgiza kai cikin tsawa yace
"Ƙarya zan miki kenan in da ba kuyi haka ba ai baza su zo su faɗa ba, tambayar ku nayi gidan uban wa kuka ce?
Amatullah ce ta fashe da kuka tana fadin "wlh Yaya babu inda muka je wajen cin abincin abokin ka ya kai mu bayan ya gama yi mana magiya sannan muka shiga kuma yanzu haka shi ya ajiye mu a ƙofar gida yace da ba dan yana sauri ba da ya shigo sun gaisa da su Ammi amma yace a gaishe su wai sunansa Lamir.
Ta ƙarasa maganar tana ƙara fashewa da kuka ita ma kawai jira take taji sauƙar marin da yayi wa Zarah amma sai taji shiru, cike da mamaki Saif yake kallonta jin sunan da ta faɗa masa,dan tabbas Lamir abokin sa ne sosai sai dai baya ƙasar, wata zuciyar tace "ba mamaki ya dawo bai neme ka ba ne kawai.
Da sauri ya ciro wayansa ganin haka yasa Hajiya Balkisu tace "babu wani abokinsa kunje yawon iskancin ku ne zaku fake da wani abokinsa, ke Zarah a da bakya yawo amma zuwan wannan ƴar iskan yarinyar yasa kin fara ɗaukar halinta wa ya sani ma ko iskancin take a gidan da take yasa suka korota mu kuma Alhaji ya kwaso mana ita gashi zata gurɓata mana tarbiyar yara.

A fusace Hajiya Fatima tace
"Haba Hajiya Bilki wannan abun da kike san bai dace ba in ƴarki aka yiwa haka ko wasu naki za kiji daɗi ne? komai muke fa mu dinga sara muna duban gatarin mu kar muje muyi abun da daga baya za muji kunya.

"Sai dai in kece za kiji kunya Hajiya Fatuma amma ba ni Balki ba kunya ai sai ku da kuke da abun kunya.

Saif ne cikin ɓacin rai da danasanin maganar yasa yace " dan Allah kuyi haƙuri ku bar wannan cece kucen na ƙira abokina ya sanar min duk abun da ya faru Raudah ƙarya take, ku kuma kar ku sake tafiya kubar ƴan uwanku.
Daga haka yayi sauri ya fice daga part ɗin dan san baya jin dadin faɗan da iyayen nasa suke amma ba bu yadda zai yi.
Amatullah da tun da Hajiya Balki ta fara jifanta da muggan kalamai take riskar kuka tare da girgiza kanta, Zarah ne ta kama hannunta suka nufi ɗakinsu, kuka take kamar ranta zai fita iyayenta ta tuno in da suna nan babu abun da zai kawo ni wani gida har ana jifana da kalmar ƴar iska tabbas duk wanda yayi rashin iyayensa ya cika maraya,rungumarta Zarah da Kausar sukayi suka fashe da kuka suma cike da tausayin Amatullah, Sumi ma dake gefen su tana kukan sharrin da su Raudah suka laƙabawa su Zarah gashi ba halin ta musa hakan yasa ta shige ɗaki take ta kuka, ita ma matsowa tayi dan taji duk me yake wakana a falon ita ma kukan take, su huɗun duka an rasa me rarrashin ɗan uwansa
Sai da suka yi kuka me isarsu sannan suka sarara Zarah ce ta gogewa Amatullah wayaye tana fadin
"Duk nine na jawo miki wannan abun in da ban dage sai mun je ba da hakan bata faru ba dan Allah kiyi haƙuri kinji Amatullah"
Ɗagowa Amatu tayi ta riƙe hannun Zarah tana faɗin "babu abun da kika min Zarah Allah ne ya ƙaddara hakan kuma dole sai ya faru dan haka ba komai wlh karki ɗaurawa kan ki laifi"
Kausar ne tace "nice duk naja wo wannan abun wlh duk ni nafi zaƙewa akan sai munje, hararar wasa Amatu ta mata tace "kaji wata ƴar sharrin yanzu dai komai ya wuce tun da Yaya bai zabga min mari ba, dan ni na gama tsorata na ɗauka nima zai maren kamar yadda yayi wa Zarah.
Gaba ɗaya suka kwashe da dariya, Zarah ce ta goge sauran hawayen idonta tace "wlh marin ya sosa min rai Yaya Saif bai taɓa duka na ba amma a yau saboda abun da Raudah tazo ta faɗa yasa ya mance halina ya mance abun da zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba ya sauke min tafi, wlh bazan mance wannan ranar ba, ta faɗa tana share ƙwalla.

Kausar ne tace "to wai ma Sumy me wacchar munafukar ta faɗawa su Yaya Saif ne da yasa ya ɗauki wannan zafin haka?
_Sanarwa! Sanarwa! Sanarwa!!_

*Ina ƙara sanar da ku cewa zamu fara class na matsalolin ma'aurata tare da hanyar magance su, da kuma gyaran jiki da sirruka da dama sai dai fa gidan ba kunya za ayi bayani

Please Login or Register in order to submit comment