Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sata tayiwa Jawaad guda biyar ai nam ta zage har da tsallenta ta watsa masa biyar, dan tasan in har batayi me kyau ba ta shiga uku
    Kallon Jawaad yayi yace "kai ma kayiwa Nabeeha biyar masu kyau, gaban Jawaad ne yayi wani wawan bugawa dan ko da wasa akace ya mari Nabeeha bazai iya ba, Nabeeha kuwa tuni ta raina kanta dan bata saba wannam horon azabar ba, narai² jawaad yayi da idonsa kamar zaiyi kuka yace "am so sorry Yaa Taufeeq wlh baxan iya marin ta ba.
  "Dan ubanka har kakai level ɗin da zan saka abu kaƙi yi but zaka mareta ko sai na haɗaku daga kai har ita na muku?
   Zaro ido yayi dan yasan ko da wasa Nabeeha baza ta iya jurar marin Yaa Taufeeq ba don dole yaje kamar zaiyi ƙwalla ya mareta, wani irin haushin Yaa Taufeeq ɗin ya turniƙe ta dan ita bata ga wani laifi da sukayi ba da zai musu wannam hukunci,kallonta yayi yace "ma za kiyi wa Huda masu kyau guda biyar.
  Cikin sanyin jiki da kuma rashin ƙarfi tayi mata guda biyar wanda shi a ganinsa kamar kawai shafar fuskarta take dan shi baiga a lamar marinta take ba dole sai ya gwada mata yadda ake mari, tana idawa taji sauƙar mari a fuskarta hagu da dama har sau goma, tuni ta shiɗe ta gigice sam ta kasa kuka sai chan wani irin kuka ya tirnike ta, gaba ɗaya ɗakin sunyi matuƙar tausaya mata tuni Samha da Huda suka saki kukan tausayin kansu dana ƴar uwarsu, ganin kukan yana hawa masa kai ne yasa cikin sauri² ya fara nuna su yana faɗin "wannam ya zama na last da zan zo na sameku kuna jin kiɗa da kuma sa kaya irin wannam" ya faɗa yana nuna su Samha ya ƙara da cewa "domin nam ba gidan arna ba ne in kuma baku ji ba wlh zan yi mugun saba maku dan ban son iskanci, ke kuma "ya faɗa yana nuna Nabeeha, na tabbata yanzu kin fahimci yadda ake mari, sannam kar ko mutum ɗaya yayi gigin ficewa daga gidan nam.
   Daga haka yayi hanyar ɗakin dake ƙasa dan ɗauro alwala yana faɗin  "ku wuce kuyi alwala  kuzo mu wuce masallaci,domin ana shirin shiga.

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

"Babu wata duniya da zaki bi karki damu insha Allah komai zai zama tarihi matuƙar zaki bani haɗin kai.
   Da sauri ta kalli inda taji magana Sadiq ne ɗa ga Baffa Jibbo ita sam bata tsammaci maganar zucin da take ya fito fili ba, ƙaro sowa yayi ya zauna a gefenta ya ci gaba da tayata wankin, murmushi tayi tana faɗin  "Yaya Sadiq da ka bari ai ba girman ka bane wankin mata"
  "Girman kenam taya zan bar Sister ɗina tana wahala ita kaɗai gwara ai na tayata zai fi ko? ya faɗa yana mata wani irin kallon me wuyar fassara wa.
   Daɗi taji har ranta dan tana ganin ta samu ɗan uwa me share mata hawaye, murmushi ta sakar masa tace "na gode sosai Yaya Sadiq (Abun da bata sani ba shine Sadiq ƙasur gumin ɗan iska ne, dan shi yayi wa mace dubu ciki ba damuwarsa ba ne,tun kan mahaifinta ya rasu ya nuna yana sonta amma sam mahaifinta yaƙi dan duk wani abu da yake maras kyau ya sani, ba yadda su Baffa Jibbo basu yi ba akan ya aura masa ita amma yaƙi, sai dai duk abun da ake Amatu bata san anyi ba)
   "Haba ƴar ƙanwata meye kuma na godiya muje muyi shanya mu wuce ciki in baki wani labari.
   Tare suka yi shanya cike da zumuɗi ta samu ɗan taya hira, ɗaki ta shiga tace bari ta sauya kaya ta fito, bin ta yayi da wani shu'umin kallo yana lasar laɓɓa, tana shiga tayi wanka ta sauya kaya, ta buɗe ƙofa zata fito sukayi kiciɓus dashi har suna jin numfashin juna hakan yasa dole tayi baya dan raba tsakanin su, ɗakin ya shiga ya tura ƙofar yana faɗin "ai na jiki shiru ne shine nace bari dai na zo na duba ko lafiya. ya faɗa yana zama a kujeran ɗakin.
   "Lafiya ƙalau Yaya Sadiq ta faɗa domin taji daɗin kulawar da ya nuna mata, itama zama tayi nam ya fara bata labarin ban dariya sukayi ta ƙyalƙyala dariya.
    A kullum suna tare hakan yasa shaƙuwa a tsakanin su dominin baya nam sam bata jin daɗin gidan saboda yana ɗebe mata kewa sannam ta ɗaukesa matsayin Yayanta da suke uwa ɗaya uba ɗaya, dan ta dalilinsa yanzu wahalar da take sha a gidan ta ɗan ragu dan yana taka musu birki.
    Zaune suke a ɗaki yana ta bata labari kamar yadda ya saba, ( dan yanzu kansa tsaye yake shiga ɗakin duk da sam bata son hakan a ranta)
a hankali ya fara matsota har ya zama jikinsu na gogan na juna, ɗan zakuɗa wa tayi ta matsa, ya sake matsota mamaki ne ya kamata tace "Ya haka Yaya Sadiq?
  "Me kika gani? kawai fa daɗin labari ne.
  Ya faɗa yana kamo hannunta yana shafawa, da sauri ta ƙwace hannunta tana zaro ido cike da mamaki tace "gaskiya bana son haka Yaya Sadiq wannam ai bai… bata ida ƙarasawa ba taji ya haɗe bakin su waje guda.'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muki nam bada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

_Share fisabilillah_👏🏻

*ONE LOVE*💞🤞🏻

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Wan da suka ƙira ni da wanda suka min text da masu min magana ta whatsApp ina godiya sosai da addu'arki gareni Allah Ubangiji ya saka da alheri na gode da kulawarku sosai musamman TAUFEEƘ FAN'S GRP 2 na gode sosai Allah ya ƙara mana lafiya baki ɗaya, Hafsat Jiboota😘 ina yinki irin sosai ɗin nam ke ɗin ta daban ce a waje na.*🤞🏻

'''My fan's ina matuƙar godiya a gareku dan gane da yadda kuka amshi wannam labari hannu biyu, banyi tunanin zai karɓu haka ba, na gode sosai da nuna ƙaunar ku gareni Allah ya bar zumunci kuyi ta suburbuɗo comments nima bazan yi ƙasa a gwiwa ba wajen zaɓaɓɓako typing.😹'''
*One love Mutane na*🤞🏻💞

*Episode 07*

*…* Tun lokacin da ta zuba ƙara Sweetie ta fito a guje cike da tsoro da farga ba, turus! tayi ganin yadda Yaa Taufeeq yake ta zuba mata mari, ita kanta sai da tsikar jikinta ya tashi domin ko bata san yadda dukan ɗan nata yake ba tana jin labari tun yana yaro hannunsa yana da matuƙar zafi musannam ma da hagu dan da hagu yake mari, sai da ya nufi ɗakin sannam ta iso, Nabeeha tun tana iya kuka har ta koma na zuci,tuni fuskarta ta tashi abun ka da ba saban ba kuma jiki ɗan hutu, fuskar tayi raɗo² na shatin hannunsa a take wani zazzaɓi ya dirar mata, Sweetie ne tazo ta kamata tana faɗin "wai me tayi masa ne hak?
  Nam Samha cikin kuka ta faɗi mata komai, ranta ne ya ɗan sosu ai tunda ta riga tayi marin bai kamata ya mareta ba.
  Sannu Nabeeha kiyi haƙuri ki barni dashi in yazo sai na tsaɓa masa maza ku tashi kuje kuyi sallah kunji har an idar.
   Miƙe wa tayi tana tangaɗi dan sam bata ganin gabanta sosai Huda ne ta kamata suka shiga ɗakin su, toilet ta faɗa a daddafe tayi wanka ta ɗauro alwala bayan tayi salla ne ta kwanta tuni zazzaɓin ya sake rufeta me matuƙar zafi numfashi take fitarwa cikik azaba, kan kace me ta fara sambatu, Samha ne ta sanarwa Sweetie da hanzari ta shigo ɗakin tsoro ne ya cikata ganin abun sa ƴar mutane take kamar zata mutu a fili tace "na shiga uku Taufeeq zai kashe musu ƴa!
    Hawa gadon tayi ta kamota da sauri ta ɗage hanunta jin yadda jikinta yayi matuƙar zafi kamar wuta, Tsoro ne ya ƙara shigarta dan tasan dole akan sai ta faru saboda tun da take ba a taɓa lafiyar jikin ta haka ba, ɗakin ta ta haura ta ɗauko mata maganin zazzaɓi da ruwa, ta tada ta sha, sannam ta komar ta ta kwanta tana mata sannu, ba jimawa bacci ya ɗauketa domin har da na bacci Sweetie ta haɗo mata, zuwa jimawa jiki dai ya kuma rikicewa dole tasa Papa yace maza su tafi asibiti, suna zuwa aka bata gado ruwa aka sa mata tuni ta saku bacci, Sweetie ne a ɗaki da Papa da kuma Huda da Samha, Nazmar, Taufeeq, da Jawaad duk basu san me ke faru ba sai da Papa ya sanar da su ba jimawa sai ga su Jawaad dan shi yafi kowa damuwa, sarkin miskilaye kuma da aka sanar masa shi haushi ta fashi ma tsabar tsakalci ɗan dukan da na mata ne har zata kwanta a asibiti ai ko in dai haka ne na dinga naɗarta kenam in yaso ta zama ƴar Hospital,tun da aka gaya masa abun da yake ta faɗa kenam.
  Sai bayan i'sha sannam ya iso asibitin nam ma sai da Papa ya masa da gaske tukun na, yanzu ɗakin Sweetie ne kawai dan duk ta kora su gida dan kwana ya kama su saboda yana yin jikin nata bai mata da sauƙi ba, har yanzu bata samu ta farka ba saka makon maganin  da suka sa a cikin ruwan na sa bacci yana da ƙarfi, Sanye yake da blue ɗin shadda wacce ta amshi fatarsa ɗinkin tazarce sai baza fitinannam  ƙamshi yake, gaishe da Sweetie yayi bai ko kalli in da gadonta yake ba bare ya tambayi ya jikin nata,  Sweetie ne tace "ka ga yanda ka mai da musu da ɗiya ko? kai baka san yadda hannunka yake da zafi bane? ta jero masa tambayoyin cikin faɗa, cikin sanyin muryar sa yace "Sweetie naga yarinyar ta cika rawar kai ne shi yasa na gwada mata nawa salon dan tasan ni ba amin iskanci da tsiwa dan naga hakan tattare da ita.
   "Koma dai miye ka kiyayi taɓa musu lafiyar yarinya.
"Tom" ya faɗa a taƙaice.
        Motsi ta fara a hankali da sauri Sweetie ta miƙe dan sanarwa likita dan ya faɗa musu cewar tana farkawa a kirasa, fita tayi tana faɗin "ka zauna a wajenta bari na ƙira likita, bata tsaya jin amsarsa ba tuni ta fice.
      A hankali ta fara buɗe idanunta da take jin sun mata nauyi sosai tar ta buɗe su a kansa dake zaune a ɗaya kujerar da ke ɗakin yana danne danne a wayarsa, a zabure ta miƙe tana ƙare ware idanunta, leƙe² ta fara kamar wanda take neman wani abu, tuni idanunta suka cika da ƙwalla, gani tayi kamar wani marin yazo ƙara mata, tuni ta fashe da kuka, kukan da yaji tana yi ne ya da ɗa ɓata masa rai a hankali ya miƙe yazo in da take, cike da tsawa yace "ke! bana son shashancin banza, uban me aka miki da zaki cikawa mutane da banzan kukanki, bari kiji ni bana ɗaukar raini dan haka tuni ki kama kanki dan naga yana rawa in ba haka ba kuma ni zan daidaita miki zama banza kawai.
   Daga haka yaja dogon tsaki yayi waje, dan sam ko kaɗan yarinyar Baffan nasa bata masa ba, ko kallonta yayi ransa ɓaci yake, duk da hakan ba halin sa bane ƙin jininsa  amma ita sam jinin nasu bai haɗu ba, (Niko nace dama kai akwai wanda jininka ya haɗu da nasu ne, ai sai dai su Ali🤣) Kiciɓus sukayi da Sweetie da doctor baya ya komai domin ya basu hanyar da zasu shigo, Sweetie ne tace "ya zaka fita ka bar min ita kai da na baka ajiyarta.
  Kayin sa ya sosa yace "zan ɗan amsa waya ne"
     Wuce wa kawai tayi dan ta fahimci ƙarya yayi mata, doctor ne ya sake dubata ya tambayi me take ji yanzu, "kai na ke ciwo sosai kamar ana saramin da adda ta faɗa kamar za tayi kuka hakan yasa ya sake ɗaura mata wani ruwan take ta sake komawa bacci, Sweetie zama tayi tayi jigum tana kallonta tausayinta ya ɗaga kamata, yana fita suka bar hospital ɗin, gida suka nufa yana shiga bai taras da kowa a palor'n ba part ɗinsa ya nufa ya sake wanka yasa kayan bacci yayi kwanciyarsa hankali kwance.
   Tun da su Samha suka dawo take neman hanyar da zata bar gidan amma ta rasa, Aunty Sa'a ta ƙira ta sanar da ita akan ta ƙira Yaa Taufeeq tace tana son ganinta, dariya tayi musu sosai tace Allah shi ƙara da ya sauka a chan kuma ita ba ruwanta tayi ƙit! ta kashe ƙiran ganin sun dameta da ƙiran ma ta kashe wayar gaba ɗaya.
Jawaad yafi kowa shiga damuwa akan rashin lafiyar Nabeeha sosai yake jin haushi Yaa M.T dan wani sa'in haka suke ƙiransa, Yaa Sayyid da aka gaya masa bai ji daɗi ba dan sai da ya nunawa Taufeeq ɓacin ransa amma shi ko a jikinsa.
Washegari tun safe su Samha suka gama komai suka haɗa nasu Sweetie a basket haka na Taufeeq ma dana Papa kame² suka fara ta yadda zasu sanarwa Taufeeq tafiyarsu asibiti, dan sun san in suka tafi basu sanar masa ba nam ma laifi ne, gashi kuma tsoron zuwa ta dashi suke dan sun san hakana laifi ne dole suka nemi waje suka zauna, sai wajen 10 sannam ya fito sai baza ƙamshi yake, a tare suka gaidasa Huda ne tace Yaa Taufeeq dama zaman jiranka muke zamu sanar maka zamuje hospital kaiwa su Sweetie abinci.
   Kamar bazai yi magana ba dan har yakai ƙofar fita sai kuma yace "babu inda zakuje ku kawo min basket ɗin cikin mota, ya faɗa ba tare da ya juyo ba ya fice.
  Babu yadda suka iya dole suka kai masa suka juyo Samha kamar za tayi kuka dam ba haka taso ba taso in ta tafi Momynta tazo ta bita ta gudu ko Yaa Sayyid.
   Da Sallam ya shiga cikin ɗakin da suken Sweetie nr a ɗakin dai Aunty Sa'a da Yaa Sayyid dasu Nazmar, gaba ɗaya suka amsa masa ya shigo tare da ɗaya yaronsa dake riƙe da basket ɗin abincin, rusunawa yayi ya gaida Aunty Sa'a da Sweetie sannam suka gaisa da Yaa Sayyid su Nazmar suka gaidashi, kallon gadon da Nabeeha take yayi ya ganta zaune kamar batayi ciwo ba azuciyarsa yace "munafuka dama ai lafiyarki ƙalau ciwon munafirci ne kin sa mutane jelan asibiti haka kawai wlh sai na miki hukuncin zuwa asibiti da kika sa nayi ta jele.
   A fili kuma ya furta "Sweetie ga breakfast ɗin ku I hope za mu iya tafi ko?
   "Eh za mu iya tafi dan sun bamu sallama dama zaman jiran ta muke ta gama shan tea sai mu tafi, sai kuma gaka, ƙara kallonta yayi karaf suka haɗa ido ba zato ba tsammani ta rafka masa wani harara wanda bata san yaushe yayi karam banin suɓucewa ba, ido ya zaro alamun "ni kike harara, kansa ya girgiza sannam ya kalli Sweetie yace "ku tashi mu tafi kawai ai ina tunanin ta kammala, waje ya fita nam suka fito suma suka nufi gida gaba ɗayan su.

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

Sai da ya tsotsi bakin sa son ransa duk yakushin sa da take amma a banza sai da ya bari dan kansa, kuka ta fashe dashi tana faɗin "meye haka Yaya Sadiq? ka mance ni ƙanwarka ce? wallahi kar ka ƙaramin irin wannam abun in ba haka ba kuma zanje na sanarwa su Baffa wannam ai iskanci ne. ta faɗa cike da ɓacin rai.
   Murmushi yayi yana jan sajensa yace "Yarinya kenam kinji daɗi zaki wani lauye da kukan munafurci, zancen zaki gayawa Baffa kin jima baki faɗa ba, ai sai ki bari nayi me gaba ɗaya sannam ki sanar da shi but yanzu yayi wuri. ya faɗi yana fashe mata da dariya yayi waje abun sa.
   Mamaki ya bata batayi tunanin zai mata haka ba, addu'a take ta yi na Allah ya tsareta daga sharrin sa duk da bata gane cewar da yayi, ta bari yayi me gaba ɗaya ba, Tun daka wannam lokacin suke kurun ɓoye dashi, da ya zo waje zata bar wajen ko ta tafi tun kan yazo, wahala kuma kullum cikinsa take baya raguwa sai dai ya ƙaru gaba ɗaya ta fige tayi baƙi tayi wani iri da ita, makaranta kuwa tuni su Baffa suka hanata zuwa sai ƴaƴan su, dole ta haƙura dan tasan bata da matallafi, yau ma kamar kullum zaune take a ɗakinta ta gama girki kenam ta shigo da nata tana ci, kamar daga sama ta gansa a kanta tsaye yana mata wani shu'umin murmushi, gaban ta ne ya faɗi da sauri ta mike ta ɗauki mayafi ta yafa a jikinta ganin yadda idonsa yake yawo a jikinta, murmushi ya sakar mata ya matso inda take yana faɗin "haba ƴar baby na meye kuma na firgita haka? ki dai na wani tsoro na ki saki jiki dani, zan zame miki gata na har'abada, ya ƙarisa faɗin haka yana isa gareta tare da riƙe hannunta, fuske hannunta tayi tace "haba Yaya Sadiq wannam wani irin abu kake min haka karfa ka manta ni ƙanwarka ce kai ma so kake na fara tsoron ka kamar yadda nake tsoron ƴan gidan? ta faɗa hawaye na sulalowa daga idanunta.
   Murmushi yayi yace "ko ɗaya abar ƙaunata kiyi haƙuri ki daina kuka bazan miki komai ba bari naje na samu su Baffa su fara maganar auren mu kawai.
           Daga haka yayi waje ta bishi da idanu cike da mamaki, gado ta faɗa ta saki wani marayan kuka na tausayin kanta.'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muki nam nada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_


*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

'''Dama na faɗa muku ba kullum zan na baku ba dole wataran ya kasance ina da uzurin da bazan iya typing, na dai muku alƙawarin in har ina free zan baku update kuyi haƙuri nasan hakan ma ƙaunace ina yinku irin mazga-mazga ɗin nam😉'''

*Episode 08*

*…* Yana fita bai zarce ko ina ba sai wajen su Baffa zaune suke a compound hira suke hankali kwance, risinawa yayi ya gaidasu sannam yace "Baffa dama na zo ne a kan maganar aure na da Amatullah tun da a wan chan lokacin mahaifinta yaƙi, kaga yanzu da baya nam sai ayi hankali kwance ko? ya faɗa yana kallon mahaifin nasa, murmushi Baffa Jiboo yayi irin nasu na manya yace "zancen ka haka yake kar ka damu kasa a ranka kamar ka auri Amatullah ne ko wata ɗaya bazai kai ba za a ɗaura muku aure ku tare.
  Kansa ya sosa yana ƴar dariya sannam ya musu sallama ya tafi cike da farin ciki, nam su Baffa suka fara shirya yadda bikin zai wakana, ba tare da sanin uwar gayya Amatullah ba, yau ta kama lahadi da misalin ƙarfe 10 na dare kwance take tana bacci cikin kwanciyar hankali bayan ta gama ɗikar wankin su Anty Zee ji tayi kamar shigowan mutum da sauri ta miƙe ta kunna wuta tsaye ta ganshi daga shi sai gajeran wando sai murmushi kawai yake mata, gaban ta ne ya faɗi tace "Yaya Sadiq me ye haka zaka shigo min a wannam uban daren? wannam sam bai dace ba wlh. bata ida rufe baki ba ya turata kan gadon yabi bayanta ya danne ta, zaro ido tayi tace "don girman Allah Yaya Sadiq kayi haƙuri kada ka cutar da ni, nifa ƙanwarka ce dan Allah… bata ida ƙarasa maganar ba ya haɗe bakin su waje guda,kissing ɗinta yake baji ba gani tuni ya fara ficewa a haiyacinsa hannun sa kuwa duk inda yakai nam yake taɓawa, kuka take sosai kamar ranta zai fita amma hakan bai sa ya saurara mata ba, tuni ya rabata da komai na jikinta,nam tsoron ta ya ƙara hauhawa ba yakushin da bata masa ba amma a banza sai mutsitstsikata kawai yake, ji da tayi zai amshi budurcinta wani ƙarfi ne yazo mata wanda bata san tana da shi ba, ta hanka ɗa shi ya gwaru da bango ta kwasa a sittin ta shige toilet ta saka key, numfashi take Mai dawa a hawalce towel ta samu ta ɗaura a jikinta, jikinta zai tsuma yake kamar mazari, gaba ɗaya tayi matuƙar tsorata, duk wata addu'ar da tazo bakin ta yi kawai take ba tare da tasan me take faɗin ba, a hankali ta fara samun sassauci a zuciyarta sai yanzu wani kuka ne cin dai ta zo ma ta duƙawa tayi a wajen ta haɗa kanta daga gwiwa tana kuka me ban tausayi tana faɗi, "Ya Allah ka dubeni da idon rahma, ka dubi halin da nake ciki Allah ka kawo min ɗauki cikin lamura na, rabbi ina buƙatar ne taimaka min wanda zai cire ni daga wannan uƙubar da nake ciki… ta kuma fashewa sa kuka, Yaya Sadiq tun da ta turesa ya bugu da bango sai dai yaji ciwo a ƙeyarsa, haushi da tsanarta suka yiwa zuciyarsa ƙawanya, a fusace ya miƙe ya nufo toilet ɗin, yana turawa ya jisa a garƙame, bugawa ya farayi kamar zai  ɓalla ƙofar cikin fusata yace "wlh in baki buɗe ƙofar nam ba ranki 'in yayi dubu zai ɓaci, kuma bazan fada abun da nayi niya ba wlh, ke dan kin samu kamar ni zan raɓeki har ki tsaya kina min wannam iskancin wlh zan ci miki uba 'in baki buɗewa, Amatullah dake durƙushe jikin ƙofar tayi hanzarin miƙewa cike da tsoro ta ƙara shegewa ciki, ganin fa da gaske ne baza ta buɗe ba hakan yasa ya sassautar muryarshi yace "haba ƴar Amatu na maza zo ki buɗe mun babu abun dake zan miki, nifa Yayanki ne wanda yake matuƙar ji dake maza zo ki buɗe min, haka yayi ta ma ta daɗin baki amma a banza
dan ko gezau ba tayi ba, a fusace yaje 'ya sanya kayansa ya fita a ɗakin yana ƙwafa lol!🤣
Tsoro ne ya hanata fitowa dan a tunaninta har yanzu yana nan, hakan yasa ta rakuɓe a ƙasa, a haka har bacci ɓarawo ya ɗauketa, washegari iyalin gidan sun fito karyawa ganin babu abun da aka girka ran su ya matuƙar ɓaci gashi kamar haɗin baki wata kalar yunwa suke ji, a fusace Mama Marka ta nufi ɗakin Amatullah, tana shiga ga mamaki sai taga ba Amatullah tunani yayi ko tana toilet hakan yasa ta nufi toilet yan murɗawa taji a kulle ƙwanƙwasawa ta farayi sa ƙarfi, Amatullah dake kwance shane² a ƙasa tayi firgigit ta miƙe ta ƙara rakuɓewa dan duk a tunaninta Yaya Sadiq ne, muryar Mama Marka taji tana faɗin "dan ubanki yau rainin wayo ne ya hanaki fitowa ki ɗaura mana abun kari? saboda ba ubanki Jamilu bane zaici

Please Login or Register in order to submit comment