Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma yaƙir yace bazai iya nisa da ita ba itama ba kunya take nuna rashin amincewar ta domin shaƙuwa ce ta ban mamaki ta ratsa a tsakanin su ganin haka Sweetie tace kuje chan ku ƙarata tayiwa Nabeeha tas tace "wato akan ina nema miki lafiya shine kike bin bayan mijinki ko to kuje duk inda zaku Allah ya baku sa'a. Nabeeha dai ko a jikinta domin bata jin za ta iya nesa da jinin jikinta bata hanasa kanta a duk lokacin da yake da buƙatar hakan bata taɓa nuna gajiyawar ta tuni itama ya koya mata jarabarsa azumi ne yake ta ƙaratowa babu abun da yake tunani sai Babyn sa dan yasan yadda take cin abincin nan a azumin nan za ta hawala hakan yasa ya fara shirya musu tafiya Saudiya domin suyi azumin a can ko da ya gayawa su Papa sunyi na'am da hakan duk da dama duk shekara Papa yana ɗibansu suyi azumi a can su dawo sai dai wannan lokacin baza su samu zuwa ba.

Saura kwana biyu tafiyar su duk wani shirye-shirye sunyi lokaci kawai suke jira a gobe za su tafi abuja domin ta chan jirgin su zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki murna a wurin Nabeeha ba a cewa komai duk da ba wannan ne zuwanta na farko ba amma kuma ji take kamar shine zuwanta na farko saboda tana tare da Abwaan ɗinta mafi soyiwa a gareta tana jinsa a cancikin zuciyarta bata ƙaunar ko na second ɗaya ne ace basa tare.

Zaune take a falo Sweetie ta cika mata gaba da ciye fiye sai ci take Samha tana tsokanarta wai arunbuɗa sarkin ci kwaɓe fuska tayi tace 

"Sweetie kinji wai nine arunbuɗa sarkin ci ko?

Dariya Sweetie tayi tace

"To ai Nabeeha gaskiya Samha ta faɗa in ba arunbuɗar ba miye ce ke? ni har Allah Allah nake naga wani irin ba samu de zaki haifo mana dan nasan ba ƙarami bane yanda yake cinye mana abincin nan."

Ta faɗa cike da tsokana domin bata ɗauki Nabeeha suruka ba Ɗiyarta take kamar da.

Kuka Nabeeha take har da buga ƙafa kamar ba ita bace mais tiƙiƙin ciki waya ta ɗauka ta ƙira Abwaan yana ɗagawa ko sallama barayi ba ta kuma fashewa da kuka daga chan ɓangaren sa jin kukan ta cikin tashin hankali yace

"Subhanallahi! lafiya Baby ke da waye mai aka miki?

Ya jero mata tambayoyin a jere.

Cikin kuka tace

"Abwaan ba su Sweetie ba ne da Samha suka tasani gaba wai nice arumbuɗa kuma wai inji Sweetie bata san wani irin tuƙeƙen yaro zan haifo ba wai sai cinye musu abinci yake yi."

Dariya ce ta kuɓuce masa 

Wani kukan ta kuma fashewa da shi tace

"Wato kai ma dariya na baka ko to yayi kyau."

Ƙunshe dariyarsa yake dan tun da cikin ta ya fara girma ta zama marar haƙuri ana mata ƙaramin abu za ta mai da shi fushi ga masifa da mita cikin ƙunshe dariyarsa yace

"Sorry baby Sweetie wasa take miki baza kuma ta sake ba ki bari yanzun nan zan zo na ɗauke ki muyi tafiyar mu daga ni sai ke babu mais takura miki kici duk abun da kike so ok."

Sassanyar ajiyar zuciya ta sauƙe tace

"Tom! Abwaan ɗina Allah ya tsare min kai ya kawo min kai lafiya."

Da "amin ya amsa ya katse wayar tun kafin ta kawo wata maganar yana kashewa yayi dariyar da bai samu yayi ba.

Samha dake dariya ta harara ganin Sweetie bata wajen ne tace

"Kinyi asara dai Samha da dariyar mugunta kamar yau dai kema zaki ƙunsa abun da na ƙunsa."

Dariya Samha ta kuma yi tace

"Ku dai da kuka ga za ku iya Allah ya bada sa'a ya kuma raba lafiya."

"Amin mu dai munga za mu iya ina sauƙe wannan zan ƙara ƙunsan wani a to."

Ta faɗa ƙasa ƙasa yadda Samha ne kawai za ta iya ji. Dariya Samha tayi tace

"Sannu jarababbi ko ma nace jarababbu."

Dariya gaba ɗaya sukayi suka cigaba da hira kamar ba yanzu ta gama kuka ba.

Sai dare suka tafiya Abuja da ƴan rakiya Sweetie Papa da su Samha Aunty Sa'a Jawaad ne kawai ban da shi gaba ɗaya ya wani irin rama duk da in yasa manyan kaya baza kaga ramar ba hakan yasa kullum cikin shigar manyan kaya yake duk da yanzu ya ɗan fara murmurewa ya fauwalawa Allah lamarin sa karatun su suke fuskanta.

washe gari ƙarfe 9 jirgin su Nabeeha ya ɗaga ƙasa mai tsarƙi cike da kewar ahalinsu taso tafiya da Ka'aaf amma Taufeeƙ taƙi sam haka ba yadda ta iya suka tafi suma a lokacin suka nufo Kaduna cike da kewa.

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212. *TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

BA EDITING🥺

*Episode 69&70*
… Gaba ɗayansu da sauri suka fice Saif na riƙe da hannun Raudah dan tun farin maganar  Dr. Ta miƙe jin tana jin jiri ne zata faɗi Saif ya riƙe ta suna tafiya a hankali har suka isa ɗakin da Momy take a kwance take hawaye ne kawai yake sintiri a idanunta ji take ta tsani kanta da kanta, Ammy ne ta iso wajenta hawaye na zuba a idanunta tace
"Balkisu ba kuka za kiyi ba addu'a za kiyi Allah ya baki lafiya."
"Hmmm! Ammy kenan baza ki gane kukan da nake ba, ba wai ina kuka ba ne akan abun da ya samen ba ina kuka ne na tsanar kai na don Allah ina so kilu taramin kowa da kuka san ya shafeni a yanzun nan domin nasan ni tawa ta ƙare."
Daga haka ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi Raudah ne tazo ta rungumeta suka cigaban da kukan tare.
Abba ne ya ƙira gidan su Momy ya sanar musu da kuma bukatar ta haka ma gidan sa, ba jimawa asibiti ya cika maƙil bayan sun gama hallarar ne Momy cikin kuka tace
"Ba komai yasa na buƙace ku ba sai dan muyi ganawa ta ƙarshe domin ni dai tawa ta ƙare sannan kuma naja hankalin ku, ni da kuka ganni na kasance mutuwa, azzaluma wacce bata son wani yayi farin ciki in ni banyi ba, Ammy ta riƙeni da zuciya ɗaya amma ni ban sonta bana ƙaunarta hatta yaranta bana so dalilin wannan hatsarin da nayi ma…
Nan ta zaiyane musu duk abun da ya faru cikin kuka ta ƙara da cewa
"Sai kuma gashi abun da nayi ya koma kaina ku kalleta don Allah kafin wani nawa ya fara zuwa kai na itace tq fara zuwa har kuka take na tausayi na amma a haka ni bani da buri da ya wuce naga ta shiga damuwa kaico na! Allah wadaran duk wani mai irin halina don Allah don girman Allah Ammy ki yafemin don Allah ina roƙon ku da ki yafemin!
Gaba ɗaya ɗakin baka jin komai sai sheshsheƙan kuka domin Momy tayi mugun basu tausayi cikin kuka Ammy tace
"Balkisu na yafe miki duniya da lahira Allah ubangiji yq baki lafiya Allah kuma ya yafe miki laifukan da kika aikata ki dai na kuka."
Abba ji yayi hawaye sun zubo masa yasan tabbas yayi dace da mace ta gari wacce aka mata laƙabi da Mar'atu saliha cike da tausayi yace 
"Nima na yafe miki Balki Allah ya ƙara sauƙi Fatima fito mu tafi."
Daga haka yayi waje yana goge ƙwalla.
Kowa sai da ta nemi yafiya a wajen su suka kuma yafe mata dan duk rashin imaninka in ka kalleta sai Momy ta baka tausayi matuƙa anan tq fara yiwa yaranta nasiha da kar su ɗauki hali irin mata domin kaf halayanta ba masu kyau ba, sai 12 suka tafi gaba ɗaya a lokacin anyi mata allurar bacci saboda fisge fisge da ta fara gaba ɗaya cikinsu a matuƙar sanyaye suka tafi cike da tausayin Momy.
Suna komawa aka cigaba da hidimar biki ƙarfe 2 daidai aka ɗaura auren Zarah da angonta Nabil ba zato ba tsammani maroƙi yace an ɗaura auren Amatullah da angonta Lamir Ahmad akan sadaki dubu ɗari biyu lakadan ba ajalan ba nan na hango ango Lamir bakinsa n nan kamar mai tallan makilin yasha shadda fara sai walwali yake sai dai ya rame domin ba ƙaramin jinya yayi ba a lokacin da mahaifiyarsa ta sanar da shi ya rabu da Amatullah yayi magiyar har ya gaji tq kuma kwace wayoyinsa dan ko ƙiran da su Amatullah suke masa wayar tana wajen mahaifiyarsa sannan kuma tace muddin yaje wajen da Amatullah take Allah ya isa bata yafe ba hakan yasa ya shiga matsanancin damuwa baya zuwa ko ina daga ɗaki sai ɗaki
Ana haka Abba ya samu mahaifin Lamir ya sanar dashi gaskiyar lamari akan Amatullah jininsa ce a tare suka je wajen Mahaifiyar Lamir suka sanar da ita tayi matuƙar farin ciki sosai domin dama ba a son ranta ba ne harda zigin Momy da kuma ƴan uwanta da ta sanar musu hakan yasa suka cigaba da shirye shirye har ta kai ga yau an ɗaure aure sai dai kuma ta ɓangaren Abba babu wanda ya sanarwa a gidan sa domin yana so ta musu bazata, koda aka sanarwa Lamir ji yayi kamar an amsa albishir da gidan aljanna tsabar farin ciki ji yake ina ma zai ganta ya san yata a jikinsa ɗumin jikinta da nasa su haɗu, a rana ɗaya ya sanar da abokansa na nesa da na kusa Allah Allah yake gobe tayi yaji an ɗaura aure, zuwa yayi suka taya juna murna shi da angon zara gaba ɗaya kowa fuskar nan tana cikin walwala basu wani jima suka ranƙaya cika tumbinsu sai da Abba ya gama da abokansa sannan ya nufo gida ransa fes.
Tuni Amatullah taji zancen ɗaurin auren ta ta wani ɓangaren tana farin ciki ta wani ɓangaren kuma haushin Lamir take ji saboda yadda ya ɗauketa ya zubata a kwandon shara, Ammy ma da taji tayi farin ciki sosai haka duk wanda yaji har da na Amatullah akayi binsu yake da addu'ar zaman lafiya sai yamma lis Abba ya tarasu ya musu nasiha mai ratsa zuciya sannan ya dawo kan Amatullah ya ɗaura da cewa
"Jikata ina so ki zauna da mijinki lafiya kar ki duba abun da ya faru ki ɗauki hakan a matsayin jarrabawa sannan kuma zancen su Baffa Jibbo in kika yi ƴan kwana biyu za muje da ke da sannan zamu makasu a kotu domin su girbi abun da suka shuka Allah ubangiji ya muku albarka za ki iya tafi."
Gaba ɗaya kuka suke yi Ammy ne ta kamasu suka fito ba jimawa akazo ɗaukar amare Zarah aka fara kaiwa tamfatsetsen gidan ta sannan aka kai Amatullah itama aljannar duniyar gidan ta daga jin sunan ma ba sai an tsaya faɗa muku ba kuma kunsan gidajen karshe ne ku kimanta amare sai dai muce Allah ya baku zaman lafiya.
Gari yayi tsin ko wani ango an masa rakiya yayi kuma duk abun da addini ya tanadar tuni Nabil ya fara kashe arna sai dai kuma duk yadda Zarah ta ɗauki harkar yafa wuce tunaninta ihu ta fara da naiman ɗauki a wannan rana har zagina sai da Zarah tayi lol😅
A bangaren Amatullah kuwa Lamir kamar zai sanyata ciki yake wani irin kulawa yake bata Amatullah taso ta turje amma jin yadda gogan nata yake binta yasa ta lafe a jikinsa aka shiga kashe arna dan Lamir ma ba sauƙi.


Washe gari
Momy wani irin fisge fisge take gaba ɗaya likitocin sun rasa gane kanta sunyi mata allurar bacci amma ina duk baiyi wani amfani ba ƙarfe 8 daidai Momy tace ga garin su nan rai yayi halinsa "innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! rayuwa kenan kayi mal kyau ma ya ka ƙare bare kuma ka aikata maraskyau Allah ka kiyashe mu taɓewa likita ne ya ƙiran Abba ya sanar masa, Abba yaji mutuwar ta addu'a ya mata sannan ya ƙira danginta ya sanar da su ya sanarwa Ammy ma.
Ammy shigewa jikinsa tayi ta fashe da wani matsanancin kuka tana faɗin 
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Hasbunallahu wani'imal wakin! Allah ya jiƙanki Balkisu Allah ya yafe miki kura kuranki Allah yasa chan yafi miki nan."
Da amin Abba yake amsa mata yana bubbuga bayanta alamar rarrashi.
Dangi Momy tuni suka zo aka basu gawarta suka nufi gida da ita cike da alhini basu da wani nisa da gidan Abba hakan yasa su Ammy suka tafi a lokacin Abba kuma ya hana a sanarwa su Zarah.
Su Raudah ji sukayi kamar za suyi hauka musamman Raudah gaba ɗaya ta fice a hayyacinta kowa ka gani a gidan nan idanunsa jajir ba jimawa aka mata wanka aka sallaceta sai dai kuma ba laifi ta samu mutane da dama Allahu akbar duniya ba matabbata ba.
Sai ranar uku su Zarah suka zo sun ci kuka a lokacin da mazajensu suka sanar dasu duk da ba su yi zaman ɗaya da ita ba amma sabo akace turken wawa a ranar duk su Ammy suka watse sai danginta Momy na nesa.


***********
Kwana su biyu a Saudia duk musulman duniya aka fara azumi ba laifi ta samu tana yi wani irin kulawa yake bata na musamman duk da baya wuni a gida amma yana kula da ita yadda ya kamata cikintan nan yayi tul da shi gwanin sha'awa, azumi na ta gangarawa a kwana a tashi ba wuya a gurin Allah a yau in ankai azumi 23 tsaye take a kitchen tana haɗa musu kayan shan ruwa cikin sauri sauri saboda ganin lokaci 5:17pm tuni gida ya ɗauki ƙamshi lemo ne kawai bata haɗa ba cikin sauri ta haɗa musu lemon kwakwa da na kankana ta jeresu rairas ta gyara ko ina ta nufi ɗakinta toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta tsane jikinta lotion ta shafa ta murza powder wani jahilin riga ta ɗauko wanda da kaɗan ta wuce gwiwa samanta me raga-raga ya matseta har tsinin nipple ɗinta ana gani ta cikinta kuka tana da faɗi sai wajen hips ɗinta a suƙe yake rigar tayi mata kyau sosai ga wani storn da yasha sai walwali take duk da batayi kwalliya ba gashin ta ta tufke sannan ta sanya flat ɗin takalmi ta fito a dai dai lokacin ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama a kuma wannan lokacin aka ƙwalla ƙiran sallah tsayawa yayi ya ƙura mata idanu ko ƙiftawa ba yayi itama tsayan tayi ta zuba masa nata idanun sanya yake da jallabiya milk da hularsa tashi ka fiye naci wannunsa riƙe da Al'ƙur'ani da sallaya cike da so, ƙauna, shauƙi sosai kallon juna a hankali ta fara takawa izuwa garesa kafin ta iso ya ware mata hannu tana zuba ta faɗa jikinsa suka rungume juna kamar za su cinye juna cikin sanyin murya tace
"Sannu da dawowa Abwaan! fatan anyi mana addu'a da yawa ko?"
Cikin wata irin kasala da ta sauƙar masa yace
"Uhm! Baby ne ai babu ranar da za tazo har ta tafi ba tare da na miki addu'a ba Allah ya sauƙar min ke lafiya."
"Amin ya rabbil izzati My Abwaan nah muaaahhh!
Ta sake masa sumbata a baki sannan suka shigo falon a ƙasa suka zauna dan dama anan suke dhan ruwa da dibino suka fara sannan suka taɓa abu mai ruwa su dangin fruit kana suka nufi ɗaki alwala sukayi yayi sauri ya fita domin har an shiga ita kuma a nan ta shimfiɗa dardumi tayi sallah, ko da ta idar karatu ta zauna tayi har sai da sukayi i'sha da asham sannan ta fito ta zauna zaman jiransa bata jima da zama ba ya shigo suka ci abinci a wajen kuma aka lula duniyar masoya tana kwance a jikinsa wani irin hawaye yaji masu matuƙar zafi da ƙuna sun biyo kan kyakkyawar fuskarsa da sauri ya goge yana girgiza kai yana faɗin
"Ya Allah! Ya Allah ka dube mu da idanun rahma, nasan ko wani bawa bazai taɓa tsallake ƙaddararsa ba Allah ka bawa bayinka haƙuri rashin wani farin ciki na rayuwarsu Allah ka basu dangana!"
Da sauri Nabeeha ta ɗago cike da mamaki tace
"Abwaan lafiya mai ya faru haka?
"Murmushi yayi cikin kawar da zancen yace
"Yauwa Baby na nace ba  ace muna cikin jin daɗin soyayyar mu kawai sai mutuwa tazo ta ɗauki ɗayan mu."
Murmushi Nabeeha tayi sannan tace
"Amma ina fatan ni na rigaka mutuwa kafin kai dan bazan iya jurar ganin mutuwar ka ba."
Murmushi yayi wanda ya ƙara masa kyau yace
"A'a wallahi ni zan rigaki mutuwa domin nasan mutuwata bazai sakaki damuwa kamar yadda mutuwarki zai saka ni ba."
"Don Allah Abwaan ka bari zancen mutuwar nan ya isa haka wlh kasa gabana sai faɗuwa yake."
Nabeeha ta faɗa cike da shagwaɓa
"Dariya yayi wanda sai da dimple ɗinsa ya lotsa yace
"Baby ai ko ba muyi zancen ta ba dole za tazo ta riske mu ni dai roƙona shine ki kular mana da Babyn mu da kyau."
Kuka ta sanya masa da iya gaskiyar ta ta tashi ta nufi ɗakin su gaba ɗaya gabanta sai faɗuwa yake, binta yayi ya sameta kwanta tana riskar kuka a hankali ya ɗagata cikin tausasawa yace
"Kiyi haƙuri Baby na bazan sake ba tuba nake."
Za tayi magana ya haɗe bakinsu guri guda suka lula duniyar ma'aurata.
Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cike da soyayya da kulawa baya wuni a gidan yana chan masallaci ya so ya shiga ittiƙafi sai dai bazai iya farinta a gida ta kwana ita kaɗai ba yana sallar tarawi zai dawo wata ɗaukanta yake su tafi ya kaita masallacin mata in sukayi salla sai su dawo a haka har aka kammala azumi cike da begen azumi ya tafi masu kuka nayi masu jimami sunayi shikenan ya tafi sai kuma wata shekara in muna da rai da nisan kwana washe gari akayi salla babu wani aiki da tayi shi da kansa ranar jajibere ya musu aikin kaji ita dai aikinta kawai tayi masa hira labari kala kala ranar sallah suka shirya cikin shigar kamala irin na larabawa suka fita zaga gari kwana biyar suka ƙara suka dawo gida najeriya.
A hankali suke takawa a matakalar jirgin tamkar wasu zarah da wata haka suke walwali ƴan jaridu cike a wajen camera ƙyar akansu amma ko ta kan su bai bi ba ya kama hannunta suka nufi inda motarsu take aun zuwa ya sanyata suka tafi yana jan tsaki azuciyarsa yana faɗin
"Shikenan mutun shi dai bashi da surru komai ɗinsa sai aj yaɗawa duniya ni bazan iya ba ina kammala wa ba wani abu da zan ƙara karɓa na wani siyasa siyasan gida na ma ya isheni."
"Allah ya zaɓar da abun da yafi alheri Abwaan!
Kallonta yayi da mamaki dan bai san maganar a fili yayi ba murmushi ta sakar masa shiga ya maido mata tare da lakutar hancinta.

A dai-dai lokacin da suka iso gidan su na abuja horn driver yayi aka wangale masa mota mamaki yayi ganin motoci a harabar gidan ga wasu balon balon masu haske da aka ƙawata gidan da su a tare suka shiga da mamaki sukaga cikin gidan dulum babu alamar haske hannunsa ya yansa ya ciro wayarsa zai kunna haske yaga wani irin haske ya baibaye ko ina da sauri Nabeeha uwar tsoro ta riƙesa tana zazzare idanu cike da farin ciki su Sweetie suka fara tafi suna faɗin

"Happy birthday to you! happy birthday to you! Happy birthday! Happy birthday! Happy to you Minister Taufeeƙ and Nabeeha!!!

Wani irin daɗi marar misaltuwa ne suka ji ya baibaye su rungume Taufeeƙ tayi ciki da farin ciki nan suka shiga cikin falon Sweetie Papa Anti Sa'a Huda, Samha, Nazmar, Ka'aaf, Jawaad suka musu barka da zuwa sannan suka masu zuwa wajen wani tafkeken cake wanda aka ƙawata shi da hoton su a tare suka yanka kowa ya bawa ɗan uwansa a baki sannan suka babbawa su Sweetie Papa ne yaje suje suyi wanka su zo suci abinci ba musu kuwa suka tafi dama Nabeeha kan yunwa take ji wanka suka a kusan tare suka fito cikin shigar kaya masu kyau sunyi kyau har sun gaji dininng suka nufa Sweetie ne da kanta ta sakawa kowa suna ci suna hira bayan sun kammala ne aka dawo cikin falo ana ta zuba hirar yaushe gamo Taufeeƙ in ya kallesu sai ya saki murmushi wani lokacin kuma ya faki idanu ya goge ƙwalla sai dai kuma bai sani ba duk wani abun da yake suna hankalce da shi jikin Nabeeha ne ya ƙarayin sanyi ganin kuma ya ware ne yasa suka cigaban da hirarsu gwanin sha'awa sallah ne ya tada su mazan gaba ɗaya suka tafi masallaci matan kuma suka shige ɗaki.

Washe gari

Da wuri su Sweetie suka shirya suka tafi bayan su Nabeeha sun cika su da tsaba kowa da nasa har da na Ya Sayyid da baya ƙasar duk da ya taya su murna ba yadda Anti Sa'a batayi ba akan ya dawo amma taƙi yace sai nan da shekara ɗaya babu yadda ta iya dole ta barshi.

Zaune suke a falo gaba ɗaya sai suka ji suna kewar ƴan uwa rungume ta yayi yana sauƙe ajiyar zuciya cikin zolaya yace

"Baby ko mu shirya mu bisu ne muma?

Dariya tayi tace

"A'a Abwaan kawai dai ina kewarsu ne."

Bakinsu ya haɗe guri ɗaya ya fara mata wani irin tsotsa hannun sa ya ɗaura a kan breast ɗinta yana kurzawa sannu a hankali ɗayan hannun kuma ya zurashi cikin tsakiyar cibiyarta wani irin miƙa tayi ta ɗan saki ƙara jin da tayi daɗi goma da ashirin ya haɗu mata a lokaci ɗaya shigewa jikinsa tayi tana faɗin

"Uhum!wayyo Abwaan daɗi wlh!

Hannunta ta sanya a ƙasansa ta kamo Abwaan ɗinsa tana murzwa wani gurnani yayi still hannunsa na kan breast ɗinta yana wasa da su sun shima a haka kana suka ziyarci babban birni.

Satin su biyu da dawowa sai da yayi sati kafin ya fara fita a kullum sai ya gurjeta son ransa tana bashin haɗin kao yadda ya kamata bata taɓa musa basa ba a duk lokacin da yazo mata da buƙarsa ba bata taɓa ƙosawa ba cikinta sam bai hanata jin daɗi ba duk da yadda ya fito yayi watoto ga tsini sai dai kuma tana cikin damuwa ganin yadda Abwaan ɗinta ya sauya kwana biyu ta rasa gane kansa ta kuma rasa wa za ta faɗawa dan bata jin za ta ita sanarwa wani sirrin su ta dai zubawa sarautar Allah idanu tana kai kimanta garesa.

Zaune take a falo taci kwalliya sai baza ƙamshi takeyi tana jiran shigowar Rabin ranta a hankali ya shigo falon bakinsa sauke da sallama sai dai in ba a kusan sa kake ba baza ka zaci yayi magana ba da ƙyar ta tashi ta nufoshi domin ta tarbesa kamar yadda suka saba za ta rungumeshi shikuma ya ɗagata sama yana juyi da ita kamar ƴar tsana suna ɓaɓɓaka dariya tare da musayar kalamai da ƙyar take tafiya saboda ƙafafunta da sukayi matuƙar nauyi sunyi sutum-sutum a kwanakin nan tazo dai dai dashi za ta faɗa jikinsa ya riƙe tq tare da mai data gefe yayi wucewar sa fuskar nan tasa ba walwala ta koma ta Taufeeƙ na baya sak da kallo ta bishi cike da mamaki wasu hawaye masu zafi suka sauƙo mata...

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212
*TAUFEEƘ* 
NA 
_Hafsat A Garkuwa_ 
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 
_(Domin Marubuta Mata)_ 
           ✨W.W.A✍🏻 
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

Episode 71&72 
…. Yana shiga bedroom ɗinsa yaji wasu hawaye masu matuƙar zafi da ƙuna d'un fara sintiri akan kyakkyawar fuskarsa dafe kansa yayi yana faɗin 
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Allahumma a jirni fi musibati wa'akilni khairan minhan!! Kiyi haƙuri Baby na hakan shine mafita a gare ni da ku baki ɗaya… 
A hankali ta turo ƙofan bakinta ɗauke da sallama idanun nan nata yayi matuƙar ja ya kumbura kana kallonta kasan ta ci kuka ba kaɗan ba tana zuwa ta sanya gwiwowinta a ƙasa cikin kuka tace 
"Abwaan! Don Allah in har na magana wani abu ne wanda baka ji daɗinsa ba dan girman Allah kayi haƙuri ka yafe min na tuba bazan iya rayuwa kana fushi da ni ba wlh bazan jura ba Abwaan na tuba." 
Ta ƙarisa maganar tana fashewa da wani irin kuka na ban tausaya 
Tun da ta fara magana yaji gaba ɗaya kansa ya masa wani irin mugun sarawa ji yayi kamar ya jawota ya sanyata a jikinsa ya rarrashe ta amma ina lokacin hakan ya ƙore masa

Please Login or Register in order to submit comment