Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Hajja kenan keda baki so Yaran Batula ba sai yaune zaki so Ɗanta har kiyi tunanin aura masa Ƴ'arki nayi mamakin da Shatima ya nace akan na auri y'arki dukda nasan kin tsani Ummana,amma ina son kijawa ita Yarkin kunne babu macen da ta isa tayi min iko a gidana tabar ganin muna Yan uwan toh wallahi takuskura tayi min ɗanyen kai jibganta zanyi kuma nasakota, Na amince da aurene sabida kar kuɓatawa Mahaifiyata suna kaman Yanda kike burin haka, toh na hanata tayi magana dan kar tayi bakin jini."

       Kallon abinci yayi cikin nutsuwa sannan yacigaba da cewa.
"Nasan shirinku akaina, ni da Uwata da Ita yarinyar da na aura, toh kuyi shiri me kyau."

      Yana gama faɗin haka ya zaro bunce ɗin kuɗi ya ajiye mata yace.
"Ga kuɗin lefenta, kuma naji sakonki nacewa sisin gwal kike so abiya asadakin wancan Yar taki toh ni bazan biya ba idan haka bai muku ba, sai a fasa kalas."

      Yana gama faɗin haka yafita daga gidan baki ɗaya,

    Jikinta yayi mugun sanyi da abinda ya faɗa amma wani shashi na zuciyarta yana zugata da tasan yanda zasuyi su mallakeshi ko ta halin k'ak'a.

      Cikin sauri tafita zuwa ɗakin da Hauwa'u take tace.
"Uwar kwalliya sai kifita kafin ya tafi."

       Jikinta narawa ta dauko mayafi ta yafa sannan ta,saka wani hill ɗinta tafito tana yanga haɗi da yauki. Har tafito waje, ba laifi itama kyakyawa ce, sai dai tana da jiki, cikin sakalci ta gaisashi sannan ta shiga zuba masa, shagwaɓa duk sai yaji ta hau masa kai haka ya jure har sukayi sallama ya ciro mata kaya daga mutane ya mika mata, kallon kayan tayi sannan tace.
"Ya Imamu wai ba dani zaka koma ba."

           Cike da mamaki ya zuba mata ido,kauda kanshi yayi sannan ya ce.
"Ke a garinku idan aka bawa mutum abu yana godiya ne."

        Turo masa baki tayi cikin jin ba daɗi tace.
"Toh nagode."
        Tsaki yayi sannan ya shiga motarsa bai sake ce mata kome ba yaja yayi gaba abinshi. Bai kwana a garin ba sai a yobe.

             Cikin gidan su takoma nan suka zazzage kayan da ya kawo mata, raina kayan tayi ta kalle Mamanta tace.
"Hajja duba kayan nan fa, dukkansu basu wucce dubu 50k ba ni da nazata zai kashe min zama da 100k sai ya buge da haka anya zan wataya a gidan kuwa."

      Tsaki hajjan tayi tana hucce tace.
"Yaron zai kawo mana matsala, amma zanyi maganinshi yanda sai yaji a jikinshi."

                  Cikin murna Hauwa'u ta zuɓe a jikin uwar da farin ciki.

*
*
     Kwana biyu a tsakani ya dira a katsina duk gidan babu wanda ya sani ina kwance ina kuka dana saba, dan yanzun babu abinda nake jin daɗinsa sama da kuka ko magana nasonyi, sallama bilya yaron makontamu naji inda yake cewa.
"Ana sallah da Naiha wai inji Malam Imam."

      Ji nayi cikina ya murɗa ai bansan lokacin da na shige banyi ɗakinmu ba inda na shiga kela amai ina gamawa na hau kan inda zanyi pupu aikuwa sai suuuu, sabida tsabar tsoron abinda zai min da abinda na tura masa,dakyar nafito jikina babu karfi, haka nafito nasamu innaji a tsaye kaman wacce aka sassakata, mika min doguwar riga tayi, sannan ta ɗauko hijab ɗina ta mika min, humra ta mika min na shafa a jikina sannan tace min.
"Ya shigo falon babanku saura kije ki masa abinda kika saba."
              Gyaɗa mata kai nayi cikin kuka nafita daga ɗakin, juyawa tayi ta kalli ramla cikin ɓacin rai tace.
"Duk sabida ke take wannan abun wallahi kin zalincin A'i kuma kisan yanda zakiyi da ita ayi bikin nan babu matsala."

     Tana gama faɗin haka tafita daga ɗakin tabar Ramla cikin kuka.

      A hankali nake takawa sabida mugun tsoron da ya mamaye zuciyata, dan nasan nayi abin kunya amma da natuna dalilin haka sai na ji karfin hali a zuciyata,ina shiga falon nasame shi zaune yana rike da wayarshi.

         Kamshin turarenshi ƴa cika ɗakin ya kara kiba da haske alamun dai yana jin daɗin yanayin da yake ciki sallama nayi can kasan makoshina, ɗago kai yayi ya amsa shadda ce a jikinshi dark blue, wanda akayi mata aiki da farin zare sai hular da ya murza akanshi har wani ɗaukar ido yake (Lolx Naiha taga Imamu, har ya tafi da hrt ɗinta)

         Niman guri nayi na zauna kaina a sunkuye ina share kwalla. Share ni yayi ya cigaba da abinda yake da wayarsa.

        A kalla sai da muka kwashe kusan mintuna goma kafin ya ɗago kanshi,
"A'I!!!"

     Kwala min kira Innaji tayi dake na takuro a ɗakin da sauri nafita daga ɗakin, ina share fuskana, mika min tire tayi cike da kayan ciye-ciye, tace.
"Ɓaure a nan ana sana'ar kukan ki toh Allah ya baki sa'a."

     Tana faɗin haka ta wucce abint ni kuma na shige falon da tiren gabanshi naje na dire masa, sannan na juya da niyyar barin gurin ya kamo hijab ɗina, juyawa nayi cikin rau rau da idanuna bakina na rawa nace.
"Nikam kasake min hijabina."

        "Zan sake miki hijabinki but sai na kai karanki guri Abbanku nace kin tura min zungurerriyar wasika na buhun ashariya ko kuma ki zo nan ki zauna." Yanda yayi maganar fuskarsa a tsuke da inda ya nuna min na zauna naji kunya ba zan iya  zauna ba a gurin. Wato cinyarshi yake nufi  kaina a sunkuye ina mutsike hannuna cikin kuka da yaci karfina nace.
"Kayi hakuri ba zan sake ba."
     
    Shiru yayi ya cigaba da latsa wayarshi cikin kwanciyar hankali kaman baya xaune a gurin, can na jiyo muryanshi yace.
"Kenan na faɗa musu abinda kika turo min."

        Zuɓewa nayi a gabanshi ina kuka, abin ba karamin daɗi yayi masa ba, ganin Yanda nake kuka wiwi ina rokonshi da yayi hakuri.

            "Shi kenan tunda ba zaki zo a cikin saukakkiyar murya ba toh zan kirga uku zuwa ɗaya idan baki zo ba zanje nasami Ummanki da Abinda kika turo min." Ya faɗa,

      Ganin da gske baxan tashi ba yasa ya fara kirga daga kan uku.
"Uku," ya faɗa sannan yayi shiru ji nake kaman zuciyata xata fito waje. Sannan yace.
"Biyu" mikewa nayi jikina na rawa. Na isa gabanshi, nuna min cinyarshi yayi ba tare da ya kalleni ba, yace.
"Ko nakarasa sauran ɗayan ne"
        Zama nayi akan cinyarshi kaman wacce ta zauna akan wuta,na cukwikuye hijab ɗina ina kuka share ni yayi, can ya ajiye wayarsa a akan hannun kujera sannan ya gyara zamanshi inda ya zagaye hannuwanshi akan cinyata, yana shakan kamshin humra da na shafa, har na tsawon minti biyar sannan ya saka hannunshi ya shiga zare min.......
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
        *Wattpad:Mai_Dambu*

     *_Ayya Bansan yanda zan faɗa muku ba ɗan tsaikon da nasamu na kwana biyu bana online shi ya hanani baku matar malam daga farko ba wai naki kulaku bane duk me bukata gaskiya sai dai yazo Wattpad ya krnt yaki buɗuwa ma balle na cire daga can na kawo Whatsp Kuyi hakuri Don Allah_*👏

   😹 Nifa ina kaunar batun kishiyan nan fa ku kuma wai kar awa naiha Kishiya😉

*23*
Girgiza kaina na fara cikin shakakkiyar murya nace.
"Na haɗaka da Allah kabarni bana so."

           Kifa kanshi yayi a kafaɗana yayi can kasan makoshinsa yace.
"Bazan iya ba, ba kuma kome xan miki ba kawai zanganki ne"

    "Ni dai gaskiya bana so" nace masa tare da zubda hawaye masu zafi.
           Shi kansa ya rasa dalilin da yake sashi jin wani iri akaina, tsuke fuskashi yayi sannan yace.
"Amma ai basabon abu bane a gurinki, wasu ma suka taɓa a banza sai ni da nabiya halalliyata maza cire da kanki ko na baki mamaki."

       Juyawa nayi na zuga masa idanuna cikin kaɗuwa da tsoro mikewa nayi cikin ɓacin rai na zare masa hijab na ajiye a can gefe, sannan nasaka hannuna baya na zuge zip ɗin rigata idanuna a rufe rigar ya sauka kasa, gabanshi naje na durkusa, ina zubda kwalla masu zafi, shi kanshi sai da yasha mamakina, gashi babu brz a jikina iskar fankar falon yana kaɗawa da karfi har tsigar jikina na mikewa zuba min ido yayi, ni kuwa cikin juriya nace.
"Gashi ka fanshi halallinka karka ji kome kawai k'iyayyarka ce yasa bana sake jikina da kai but inda akan hakkinka ne ni me saukine na baka amma abisa sharaɗin ba zan kara minti ɗaya da igiyar aurenka ba akaina tabbas kayi gaskiya da kace wasu ma sun taɓa aɓagas balle kai da kabiya ɗukiya me ɗinbin yawa zan maka shamaki da abinda ya zame naka,, sai dai kasani gangan jikina ka aura ba dai ni A'ishatu ba, dan ba zan taɓa kaunarka ba." ina gama faɗin haka na mike na xauna akan cinyarshi kaman yanda yaso ɗin.

             Duk sai jîkinshi yayi sanyi cikin jin kunya yasa hannunshi ya rungumeni yana cewa.
" Kiyi hakuri da abinda nayi miki."

       Can kasa yayi maganar bakinshi dai dai kunnena, babu abinda yafi ɗaga masa hankali sama da furicin da nayi masa na bana kaunarsa Uwa uba suran jikina da yayi tafi da imani, dan lokaci guda hankalinshi yayi kololowar tashi amma sabida maganar da na faɗa masa take yaji kome ya fita masa akai. Mikar dani yayi cikin nutsuwa sannan ya mai dani inda ya tashi kayana ya kwaso min, ya ɗaga ni ya saka min,sannan zaunar dani a kasa shima ya sauka kasan yana kallona tausayi na bashi, cikin son na,sake dashi yace.
"Baza'a bani ruwa nasha ba?"

    Mikewa nayi na shiga masa hidima ina share kwalla, har na gama na ajiye masa a gabanshi sannan na koma jikin kujera, na zauna, duk nahaɗa kaina da gwiwuwena ina matsar kwalla, ruwa yasha sai fruit ɗin da yaci kaɗan, sannan ya zuba min ido.

Sai yake jin ba daɗi da ɓata min da yayi janyoni yayi ya shiga rarrashina, ni kuwa nasake narkewa ina zuba kuka duk ya rasa yanda zai mu da yagaji da rarrashi kawai sai naji bakinshi a cikin nawa, ware idanuna nayi cikin faɗuwar gaba, ina son kwace kaina amma ya haɗe fuskarmu dan dole na daina shegen kukan. Kai Malamai ma sun iya farlatan luv ba zan iya faɗa muku yanda bawan Allah nan yayi dani ba, dukda ina son kwace kaina amma na kasa, abinka da gwauro😂  bai san lokacin da yasake layi ba dan kafin na farga naji hannunshi a cikin rigana, yunkurin tureshi nake amma bansan ta inda zan fara ba, shi kuwa ko a jikinshi dan janyoni yayi ya shige dani jikinshi sosai ban kuma abinda yake min gaba daya ya fara kure tunanina bansan lokacin da na fashe da kuka ba, wanda firgitar dani dan alamarinshi yana shirin kure tunanina ne,a galaɓaice ya zuba min idanu wanda sukayi jajur gashi sunyi kananu wanda ya nuna abukace yake dani. Taya ma ba zai sussuce ba da  a riga yake ganinsu yau kuma ya bani haushi na kwaɓe masa ai dole ya hauka ce min. Dakyar yake maida numfashi, cikin wani irin murya wanda har bari yake yace.
"Kiyi hakuri da Al'amarina, kinji basan ya akayi na wucce gona da iri b..." mikewa yayi cikin rashin kuzari ga rigarshi duk ta sha squeezing, mikar dani yayi janye hanuna nayi naja da baya, cikin muryan masifa nace.
"Daman kace jikina kake hari shi yasa ka damu da ka aureni gashi tun banje gidanka ba ka...."

   Ban kai karshen maganar ba ya haɗani da bango kauda kaina nayi dan wani dunkule hanunshi yayi sannan ya naushi bango tsorone ya kamani nasa hannuna na kare fuskana cikin tashin hankali, ranshi yayi mugun ɓaci fisgo hanuna yayi cikin ɓacin rai yace.
"Insha Allah ba zan taɓa rabaki da Kimarki ba sai da amincewarki amma kisani dalilina na,zuwa katsina nazone na shaida miki kishirya dan ranar da aka kawoki ranar za'a kawo min wata wacce nasan babu abinda zaki nuna mata, na Y'a mace, bazan miki dole ki soni ba kuma bazan takuraki ba. Sai dai kisan irin kalman da,zaki na faɗa min domin gidan da zaki shigo gidane da ko y'ay'a ka sake layi toh kallon mara ɗa'a zasu maka, sannan da kike cewa jikinki nake bi me,zanyi dake mi kike da shi miye a jikinki da zai dame ni har ke macece da zaki ce ina bin jikinki toh ba zan kuma bin inda jikinki yake ba balle har ki raina min hankali."

    Fita yayi daga gidan baki ɗaya ni kuwa na durkusa a gurin kuka na cigaba dayi sosai kaman raina zai fita.

    Koda yafita almajirai ya samu ya mika musu kayan da yazo min dashi inda yayi tafiyarsa. Ranshi yayi matukar ɓacci amma bayajin zai bar katsina a wannan ranar.

             Tunda yafita na durkushe a gurin ina kuka, wiiwii mikewa nayi cikin azama nafita, na shiga ɗakinmu ganin tulin kayan da aka jibge min yasa na tsallake na shiga, ɗakin wayar da yabani na ɗauka layinshi na shiga nima, koɗa kiran ya shiga, yayi har ringing uku bai ɗauka ba, sai can kaman zai tsinke ya ɗauka kukane ya daki kunnenshi shiru yayi, can ya ce.
"Zan kashe wayar fa."

                  Bansan mi yasa ba sai nacire wayar a kunnena na kashe, kallona Ramla tayi cikin kuka tace.
"Bansan mi yayi miki ba kuma bana son sani amma kisani Babu namijin da zai ɗauki wannan kukan naki. Haba ke kuwa kinsan fitina a ranki kinsan Allah matukar kika shiga gidan da wannan halin naki zaman gidan sai ya fi karfinki dan na lura baki da hankali haba don Allah kuka sai kace ɓaure wallahi ko kishiya yayo miki da wannan kukan naki zata gama dake sam baki da hankali."

      "Toh nidai nace bana sonshi dolene" faɗa mata nayi katsaye babu wani shamaki.
        Baki sake take kallona cike da bakin ciki, taɓe bakinta tayi sannan tace.
"Sai me dan baki sonshi? Allah ya bashi wacce zataso shi kaman me ke kuma su maidake bora, kina ji kina gani suta shagalinsu kuma baki da tacewa Wawuya kawai wallahi idan kika ɓata ruwanki Yanzun hmmm sai kin rasa na kwaɓi nan gaba."
Tana gama faɗin haka ta juya, min baya, wani sabon kukane ya kwace min na zauna a gurin.

*
*
Koda ya isa masaukinshi xuɓewa yayi akan kujera,dafe da kanshi yayi cikin damuwa yaushe A'ieesha zata bar shirme wani shashi na zuciyarsane ya ce.
_Ba dole tayi shirme ba, yarinya ce fa, kaine kayi shirme da zaka zo mata ta haka_

Zubur ya mike ya rage kayan jikinshi sannan ya faɗa wanka dan, yana kokwanto kanshi dangane da abinda ya faru, shi da yake wanka sai ya buge da murmusawa cikin jin daɗi da wani shauki, gaba ɗaya sai yaji shi cikin wani irin yanayi na daban amma tunowa da kundin rigimarta sai yaji kome ya kunce masa. Haka ya gama wanka ya fito, yana tsane jikinshi. Bai kuma bin takanta ba,


Washi gari.....
Sako ya turo min akan ya tafi, ban gani ba dan wayar a kashe take Yan uwan Baba na nan katsina da Yan uwan mamana sunzo a cikin yan kwanakin da suka rage.....




*
*
Biki bidiri yau takama Al-hamis dan haka waleema aka shirya dan akwai bakin Yobe suna hanya, duk wata hiɗima da zirga zirga da Amarya keyi toh duk banyi ba, sai dai su Aunty Zubaida, rigima na tsiro da shi, na duk abinda akace za'ayi min toh sai na ɓata musu lokaci tun suna sharewa har suka gaji suka fara mita ko ajikina, tun ranar talata suka kaini gurin gyaran gashi, shima nayi ta kiriniya daƙyar me saloon ɗin ta gama min, dake da Aunty Hajra ce, rankwashina tayi, da aka gama, koda aka fara lalle nan ma, nayita mutsul mutsul, har sai da aka sake kifa min mari,(😂 wannan aure ko jaraba) dakyar aka gama min, muka dawo gida yanxun kan na daina kuka sai buhun iskanci da nake musu, muna shigowa Wata cousin ɗin Innaji suna Aunty Maryam ta mika min, wani kwanin sha, da madaran shanun wai nasha da ɗuminsa ta miƙa min. Tura mata baki nayi na fara kunkuni ina mingira kaina na fara cewa.
"Nifa an fara damuna da shaye shaye, haka kawai anaso a lalata min kayqn cikina, idan cancer ta kamani waye zai zauna dani don Allah kubar asaran kuɗinku dan cututtuka sun yawaita akayan itace, ni tsoro nake ji kar kodata ko hanta su lalace."

Duk gidan suka sake baki suna kallona yanda nake sake magana a sakalce, lekowa innaji tayi ta min dakuwa tare da cewa.
" Zakice kwal ubanki idan na kama shegen bakinkin nan me kama da na saurayin Kada."

Aikuwa sake turawa nayi gaba ina kunkuni, haka suka titsiyeni na shanye, har da lashe baki dake bani da birbiɗin kunya nacewa Aunty Maryam.
" Don Allah ina kika sami fresh milk haka wallahi yayi min daɗi ga garɗi har wani kamshi kamshi kanunfari yake."

Mika min wani gora tayi fuskarta a haɗe tace.
" A gidan kanoyarki nasamu, karɓa maza ki ajiye kita lasa bance ki masa shan ruwa ba, lasarsa zakiyi kina jina ko yar banza mara kunya zaki sani indai halinki nan baki sake ba wucce kije kiyi wanka ga sabulu nan kiyi dashi."


Wuccesu nayi ina kunkuni abuna, sukuwa suka shiga hiran shirme na, wasu nagani tsabar iskancine wasu naganin Yaranrace kawai kw ɗawainiya dani.



Musaman suka ɗauko me kyalliya tazo ta fente min fuska, ana cikim kwalliyar aka ce Yan yobe sun iso nan aka shiga kai musu abinci gidan Imamu dake can gefen unguwarmu, aka kaimusu sannan aka shaida musu,akwai waleema ko zasu samu zuwa. Suka ce toh.




Karfe hudu aka fita dani gurin waleema wanda akayi shi a kofar gidarmu. Yan uwan Imamu duk sun hallara manyan cikinsune basu samu zuwa ba, Amma matar Abba lawan tazo, da Balkisu da sauran yan uwanshi da suke yan uba mata da matan wasu kanensa, wasunsu kuwa sunyi gudun zuwa maidugurine, shine suka zo nan.

Duk wacce ta ganni sai kiji suna cewa "Masha Allah Baba Imamu Ya iya zaɓe," sannan su juya da barbanci nan zasu ta yabona, dake naga yanda suke haba haba dani, take nima nasake dasu har nakarɓi Yarinyar Balkisu dake bata da kiwuya muka zauna abinda ya daɗa burgesu kenan har aka tashi a waleeman aka ware musu nasu kome na gidan maza, an basu jakuna kusan talatin da dukda basu kai haka ba, sai aka musu tuwon girma miyan Nama, yan uwana da dangina suka saya min kima a idanunsu.



Tunda aka tashi nake kuka dan jikina yayi matukar sanyi da irin nasihohin da akayi na mace tabi mijinta koda bata sonshi sai naji kaman dan ni akayi wannan wa'azin.

Koda muka koma gida nan ma iyayena suka ɗaura min akan wanda akayi min musanan yanda zanja Yan uwansa a jiki dan izuwa yanzun sun sami labarin yau aka ɗaura masa aure da Yar uwansa inda sukayita bada hakuri, akan haka dan kar iyayena suga kaman cin fuska aka masa tohfa nan Yan uwana suka min Caaa kuma a yanda Yan uwanshi suka nuna basu son auren babu yanda suka iyane dan sunfi sonshi dani, haka ya kwantar da hankalin Iyayena da sauran mutane kunsan nasihar da akayi min a daren yau akan Yanda zanja yan uwanshine a jikina banda rashin kunya ko rashin hankali ta hanyar kyautatawa,zalla bayan sun gama suka buɗe babin Mahaifiyarshi. Nan ma haka suka cika min kunne da abu ɗaya Kaiiii dakyar suka bar ni na kwanta a ranar, karfe uku aka tashe ni nan nayi wanka dan sunce hudu da rabi zasu ɗauki hanya su isa da wuri tunda akwai hidima a can. Ina farkawa na samu an gama haɗa min kayana wanka nayi nazo na karyawa a nan na,fashe da kuka..........#Vote#Share#Comments##Mai_Dambu........
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
        *Wattpad:Mai_Dambu*

*24*
Abincin da ban iyaci ba kenan suma sai da nabasu tausayi, mika min kwanon shan irin najiya Aunty Maryam tayi karɓa nayi na kafa kaina sai da nashanye, sannan ta kamo hannuna, tace.
"Cire rigar jikinki jiya kinyi bacci naso na mikii kafin ki kwanta amma naga kinga."

     Cikin kuka nace mata.
"Nikan mi ye amfanin wannan abubuwan da kuke bani ne, ni nagaji indai dan wancan mutumin ne ku daina dan basonshi nake ba."
         Ɓata fuskarta tayi cikin jimami da abinda nace taɓe bakinta tayi sannan tace.
"Ai wannan sabida mugun nufin kishiya da mugayen mutane ake miki tsarin jikine namu na fulani idan kika k'i amiki toh ba makawa kishiya rainaki zatayi tasa miji da mutane su juya miki baya ko bakya sonshi bazaki so ya wulakantaki ba ko? Toh tunda haka ai dole aja miki mutunci a idanun kishiyarki da mijinki amma idan bai miki ba sai mu bari."

     Ɗaga kai nayi sama ina nazarin abinda tace shiru nayi itama ganin haka ta mika min towel tace na ɗaura nacire kayan jikina, ba musu nacire towel ɗin Iya cinyata wani roba ta buɗe wanda takwaɓa lalle a ciki wani farin roba me murfi nan tashiga shafa min a jiki, cikn mintuna goma ta gama, sannan ta ɗauko kaskon wuta ta zuba wasu turarrikar irin yan maiduguri. Umartata tayi na tsuguna, akan gaushin nan nayi. Can da zafi ya dame ni nayi wiki wiki, da idanu nace.
"wallahi konewa zanyi fa, zafin ya dame ni." Banza Aunty Maryam tayi dani kaman bata ɗakin, zani ta ɗauko ta rufa min aikuwa na fasa mata ihu" wayyo zan mutu" da sauri Innaji ta shigo taga halin da nake ciki ɗaga rufuwar tayi tace.
"Barta haka Maryam in nice ma sai tasan ciwon kanta zan nima mata wasu abubuwan yanzun bata san darajar abinda kike mata ba, ku hanzarta, dan har an fita da kayanta waje ana sakawa a mota.



Wani munafikin kuka nasake ina kunkuni, abin mamaki lalle har ya bushe tasa keyana tayi zuwa ban ɗaki ta murje min lalle sannan ta kwara min ɗanye madaran shanuwa ajikina, ta wankeni tass dashi, tana gamawa tazuba min rankwashi haɗi da cewa.
" Dan ubanki da kudinki xaki zo niman wannan abinda nai miki babu mijin da za taɓaki ya hakura dan ɗumin jikinki ma ya isheshi balle kuma ni'ima munafukar banza, irinkune masu maƙelewa miji yar banza ina nan ina jiranki zanci kaniyarki duk ranar da kika ɗibu bulogarin kafarki zuwa gidana da sunan niman wani abu zaki gane baki da wayo."


Rike kaina nayi ina sosawa, bakina a turo

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment