Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah."

  Yanda ya sunkuyar da kanshi zaka ɗauka abinda suke faɗane yashiga jikinshi amma ina yana shiga takunnen dama yana fita takunne hagu,
......A ɗakin ramla kasa zaune tayi sai sintiri take, dataga babu mafita sai takira Fasu tafaɗa mata abinda takeso sannan tatura mata kuɗi wato mobil bank,
Koda fasu ta isa gidan bokan ta fada masa abinda yake faru take ya turawa Asad aljani, sannan ya ɗauki wani tulu ya mika mata yace.
"Wannan hawainiyar tsafice tasaka a inda baza'a gani ba, idan wani daga cikin yan uwanshi suka zo tabuɗe bakin tulun hawainiyar zata fita, taje ta shige jikinshi zata sakashi aikata kome, cikin dakika sittin."

Shima makarinsa karta kuskura tabari ya haɗu da wancan yarinyar inba haka ba, kome zai dawo kanta."

"Toh" tace, sannan tafita daga bukkan cikin rawan jiki.
....Koda Irfan yayi gama masa faɗa ya ɗago kanshi ya fara magana da cewa.
"Ina ganin haka na zabawa kaina tunda haka ne, kuwa bana bukatar ganin kowanneku, kufita min a gida kafin na durza muku wulakanci kufitan min a gida nace."
Ya daka musu tsawa cike da mamaki suke kallonshi, tabbas wannan ba Asad ɗinsu bane, wanda suka sani baya haka, jikinsu a sanyayye ransu a ɓace suka fita a gidan.

Tare da alkawarin zasu shiga au fita su ceto abokinsu.

Bayan fitarsu kadan fasu tashigo gidan inda tabawa Ramla sakonta ita kuma ta dinbulo kuɗi tabata,sannan ta sallameta.
_(Idan wasu suka samu duniya mantawa suke da lahiransu.)_
****
A tsatsaye Innaji tafara rashin lafiya wanda sai da ya kwantar da ita, duk yanda taso ɓoye damuwarta haka bai hana ciwon kada ita ba, abu kaman wasa, da asuba ta tashi sallah tayanki jiki ta faɗi, a cikin banɗaki babu wanda yasani, sai da suka dawo daga sallah Abba ya shiga ɗakin yajita shiru shine ya kutsa banɗaki anan yasameta a yashe, da sauri ya kira ya Ishaq suka ɗauketa sai Asibiti, cikin gaggawa aka amsheta,, inda suka shiga bata taimakon gaggawa.

Ishaq ne yakira kannenshi ya faɗa musu halin da mahaifiyarsu take ciki, amma bai samu layin ramla ba, Har sai da yaje gidan dakyar aka barshi ya shiga suna bacci basu tashi ba, bugun da yake yasa ta tashi, tafito ranta a ɓace, tana buɗe kofar taga Ishaq, daga bakin kofar yace.
"Idan kin gadama Innaji tana asibiti ba lafiya."

Yana faɗin haka ya juya yabar gidan yana tur da halinta, ko ɗar bata ji ba, asalima ita mamakin yanda Y'an uwanta suke mata hassada take, kwafa tayi cikin jin haushinsu. A hankali tace.
"Idan ana zuwa dole basai akaini ba."

Komawa tayi ciki takwanta abunta tacigaba da baccinta har zuwa sha ɗaya saura, sai a lokacin wani ɓangare na zuciyarta ya gargaɗeta da ta tashi taje kafin asamu abin faɗa akanta, shine dalilin shiryawanta.

***
*Baby* duniyar tayi mata atishawan tsaki domin kome ya lalace ma, takai zaman gidansu nason fin karfinta, haka ma fita waje domin wani irin bakin jini tayi,idan ta zauna surutu take ita kaɗai tana tona kanta da abinda tayiwa mutane musaman ma ni, dalilin da yasa mutane suka fara tsanarta kenan.

****
*United Kingdom*
A jahar Livepool, duk da lokacin sanyine bashi  ya hana mazauna garin fita hada-hadarsu na yau da kullum daga cikinsu kuwa har da Imamu, sanye yake da wata katuwar jacket me hula, da gashin zaki, rike hannunshi yake da Khalil, da kuma Ummi zai kaisu makaranta sannan ya wucce nashi makarantar, amma kafin ya wucce sai ya biya dasu gidan abinci, suci yayi musu pack ɗin wani a lunch box, abin tausayi yara da uwarsu tunda suka diro london ta fita sha'anin Uba da yaran, idan yana gida kulewa take a ɗaki taki kome, sai shine zai mata shi kuma baya son yawan magana shi yasa yake zuba mata idanun tunda hakkinshi ma kin bashi take, sai ya maida kanshi kullum yana azumi, ya cigaba da zuba masa idanun.

Wani gidan cin abinci ya tsaya yasaya musu noodle da chips sannan ya zauna suka ci, ya ɗaukesu sai zuwa makaranta, yana ajiyesu ya wucce nashi.

Tun zuwanshi makarantar akwai mata yar lebanon da take shige masa, amma haka yake mata fuskarsa ya wucceta, yau sun gama karatu da wuri, sai ga hukumar shara'a takasar ta turo wasu daga cikin mutanenta suzo su nima musu, wanda yake da kwarewa afanin shara'a yazo yataya alkali aiki, abin mamaki a cikin yan kwanakin da yayi har mutane sunyi bincike akanshi, kowa yana niman irin wannan alfarman sai gashi ya faɗa kanshi, abin yazo masa bazata, dan haka suka tafi tare, inda aka fara shari'a alkali ya nime shawaranshi aikuwa ya bada abinda ya dace take hukuncin yayiwa kowa daɗi, kuma suka gamsu da hukuncin, har suka nime yayi aiki dasu zasu biyashi albashi me kyau.
Koda ya dawo gida, ya samu yaranshi abakin kofa alamun uwarsu tafita, kenan buɗe musu kofar yayi ya shige ciki ya fara nima musu abinda zasu ci sannan yashiga ɗakinshi. Ranshi a ɓace, ya rasa yanda zaiyi da Jameesha,

Har ya gama abinda zaiyi bata dawo ba sai can gata sanye da riga da wando, sai jacket tayi roll kanta da yar mayafi, kallo ɗaya yayi mata ya kauda kanshi dafa gareta, wuccewa ɗaki tayi abinta suma yaran sun saba da halinta,

Can bayan wani lokaci ya tashi ya bita ɗakinta fitowa tayi ɗaure da towel, alamun wanka tafito hannunta rike da wani tana goge kanta, ganinshi da tayi sai da ta razana,  shima kallon tuhuma yayi mata, juya kanta tayi ta kalle kusurwan gado(wato sider bed) shima gurin yakalla adugar mata,ya gani a hankali ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya kalleta cikin sanyi murya yace.
"Haka da kika zaɓa mana yayi miki, ko kin manta da hakkinmu nida yarana."

Cikin takaici ta kalleshi ganin irin shigan da yayi wato half janfane da wandonshi, sai takaici ya rufeta taki sake kallonshi, ciki ciki tace.
"Baxan iya wannan kauyanci ba, mutum an haifeshi a cikin city sai kace wanda aka haifeshi a cikin kauyen kayau."

Miqewa yayi yabar ɗakin tabi bayanshi da tsaki.

Wannan mugun halin da tatsiro tun shigowansu takewa Imamu kallon wanda bai san me ake kira da wayewa ba, gani take masa bai san rayuwa ba, kaman yanda mazan turawa da sauran mutanen garin suke tsukewa cikin riga da wando, caras shi yakw rura mata tsanarshi tunda har yaranshi ya hana tasa musu tsukekken kayan, kuma idan tayi shigar da bai masa ba, ya buɗe mata wuta ya hanata fitowa dan karta lalata masa yara, dalilin da yasa tabar masa yaran kenan,

***
Asibiti kuwa duk yan'uwanmu sun haɗu can sai ga Raml, itada  Asad yana rike da basket ɗin abinci, tunda tashiga ɗakin ta gaida Baba bata sake cewa kowa cikanka ba, Aunty Hajra ce tace.
"Abba Naiha tasani kuwa."
Afirgice ta ɗago kanta..........

*_Ba zan gaji da miki fatan alkhairi ba Aunty Sholingayu, Ubangiji ya albarkaci rayuwarki Allah ya saka miki da alkhairi, yaraya miki zuri'arki ta hanya madaidaiciya tsare miki imaninsu a duƙ inda suke, ya karesu da Sharrin zamani, mutum da aljan, nagode nagode sosai_*👏❤


Karku manta ku ɗaga min darajata, ta hanyar vote
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳



    

      *Na:Real Mai Dambu ce*

       _🙆😹 Nafi dotar Sahiba anya  haka zamuyi dake, akaro na biyu tun bayan Qaddaran rayuwata, ban sake cin karo da ma'abota naci irinki ba yaseen har tsoron buɗe data nake sabida ke_😹



*:•~14*

Aruɗe ta mike jikinta har yana karkarwa, kusan dukkansu suka zuba mata idanun muryanta na rawa tace.
"Abba dolene sai Naiha tazo ne, tunda gamu nan yaran Innaji ai mun isa jinyarta tana sonmu tabar gudu tabar garin nan sai ayita damuwa da wanda ɓai damu daku ba."
Kallon mamaki suka bita dashi yanda ta wani hakikance akan kar akira Naiha,

Kallonta Abbanmu yayi ranshi a ɓace da ita daman dannewa yake yace.
"Waye butulu irinki Y'ar kaza samu kak'i dangi, zan kirata sai  kibi duniya asannun zata kaiki tabaroki, dan ba tabbasne da ita ba."

Fuu tafita can wajen asibitin ta kira yar kwangilarta ta faɗa mata, abinda take so yanzun boka yayi mata, akan iyayenmu da Ni tura mata kuɗi tayi ita kuma taje ta cire sai gidan boka, inda yace wannan karon aiki ba zaiyu ba dan akwai wani gaggarumin abinda zai kawoni matuƙar ana son kar nazo sai taje ta binne abu a cikin kabari ko kuma ta mika masa kanta ko sharuɗar da ya gindaya mata kenan.
Koda Fasu takirata ta faɗa mata  shiru tayi sannan tace .
"Zanzo masa kawai, domin bazan iya shiga makabarta ba." Da haka ta yake hukuncin zata bawa wani ƙato kanta, ya murjeta
ba tare da saninsu ba tabar asibitin ta wucce wannan kauyen,  anan tasamu fasu tana ganinta tafita wajen bukkan ta zauna ita kuma ta shige ciki, kallo ɗaya tayi masa ta kauda kanta, inda ta nime guri ta zauna, ranta yana mata soya, babbane dan yafi Abbanmu, mikewa yayi yana tanɗe baki, ya iso gabanta da rawan jiki, dakatar da shi tayi da hannunta cikin tsageranci tace.
"Karka fara tunanin zan mika maka kaina ne, haka siddin, gashi robar kariya ce, dan nasan bokaye irinku ba'a rabasu da kwanciya da mata, dan haka gashi kasaka,"
Wurga masa condom tayi har kwali biyu, da sauri ya amsa, ya shiga  tuɓewa a gabanta, sidikeken katone kome nashi a murɗe yake, cikintane ya murɗa, yana gamawa yayu kanta.....

......Bayan mintuna arba'in da biyar, duk sun jigata, sannan ya mike yace.
"Wannan  layar kisaka abakinki idan kika isa gurin iyayenki ki fada musu abinda kike so, zaki sha mamaki, wannan shine na kabarin zan tura aljanuna sukai susaka."

Miqewa tayi dakyar tana ɗingishi, sannan tasaka kayanta tafito ko kallonshi bata sakeyi ba suka bar kauyen.
Bayan fitarta ya fashe da dariya dan yaji daɗi sosai yanda ya murzata son ranshi dama ta masa shamaki da kanta, da yaji yanda take da ɗumi.

Wai akace tsafi gaskiyar me shi, kuma wnda yayi imani da shi, haka ya faru cikin abinda baifi awa guda ba aka ajiye batuna, kamar bana cikinsu ma, an manta dani,
****
Nima a ɓangarena na manta da ina da dangin uba dashi kansa, idan nacire Annah da Kawuna da sauran dangin Uwata, toh na manta da wasu dangina...    Kuma haka nake rayuwata cikin farin ciki da bakin ciki. Amma Alhamdulillah, dan nasamu madadinsu dan Abban khadija yana kyautata min.
Ga sauran dangi, ga Annah da take zuwa min duk bayan wata uku. Dama yanzun ciwo ya tasota gaba, sai dai muyi Mata fatan Allah yabata lafiya.

    ****
Allah sarki a cikin wannan rayuwar idan nacire kaina mutane biyu suna cikin uƙubar matansu Asad da Imamu, dan Allah ya jarabesu da mata fitinannu, na bugawa a mujalla.

   Kusan shekara guda kenan da suka koma london Iskancin Jameesha sai karuwa yake kaman furashin hannun jari, a shekara guda sukayi a can har mukami yasamu babban limamin jami'arsu, a watan azumi suka rokeshi yayi musu tafsiri asabar da lahadi cikin harshen turanci,

  Still yan unguwarsu suma suka nime alfarma yayi musu, koda sau ɗaya a sati, sun nime izini hukumar tsaro garin domin gudanar da aikin ibadansu. Kuma aka basu damar haka,

    Cikin nasara da kwarin gwiwa ya fara tafsirinsa sai gashi ana samun masu karɓan musulinci, sabida yanda yake jan hankalinsu cikin siyasa da kwarewa,
Alhamdulillah har aka gama azumin lafiya saima lamban yabon da yasamu na wanda yafi kowa son zaman lafiya......

Sai dai kashe dukda haka bai hana Jameesha tsaka mishi mutunci ba dan abinta yakai har rigima take jawowa a kamata, na karshen ne, sukayi faɗa da wata yar south africa akan ta kama jameesha da mijinta sun keɓe, inda sukayi dambe aka kira yan sandan unguwa suka tattarasu, suka tafi dasu,
   Daga can aka kirashi yaje, aka karanto masa laifinta hakuri yabawa matar sannan yayi bill ɗinsu suka fito, taxi suka shiga har gida, yana shigo da ita gida ya kifeta da mari cikin ɓacin rai yace.
"Mi narage ki dashi, da har zaki fita bin mijin wata, anya kina tsoron haduwarki da Allah kuwa mi kike so nayi miki da har kika zaɓi cutar min da igiyar aurena tabbas zan maidaki gida kije sai ki faɗa musu hujjarki nayin haka, amma ko kece autar mata na hakura dake, zan iya zama ba mace da dai na zauna dake."

    Dafe kumatunta tayi cikin jin zafi, ta buɗe baki zatayi masa magana ya juya yabar mata gidan ranshi na masa zafi.

   Dakinta tashiga ta hada kayanta inda ta rubuta masa wasika kamar haka.

_Bazan maka sallama ba amma nasan zaka sami wasikata, nagaji da zama da kai, karkayi tunanin nimana domin kasar zan bari baki ɗaya, idan yayi maka ka sauwake min ka tura min gidanmu, Allah yaba me rabo sa'a_
Tana gama rubutawa ta ajiye a jikin kofa yanda zai gani.

   .......
Karfe sha biyu ya dawo da yaranshi ya sami wasikarta, idanunshine suka kaɗa jajur, bawa yaranshi abinci yayi sannan ya wucce, ɗakinshi ya faɗa ban ɗaki bayan ya cire wayarshi daga aljuhunshi yasakewa kanshi ruwa, yayinda ya kifa kanshi a jikin hannunshi, da ya dafe bangon dashi mutuwar zahira ce ta dawo masa sabuwa fil, sai da ya gama jikan kanshi sannan ya fito ya cire kayanshi yayi yasaka doguwar riga,sannan ya zauna, ɗaukar wayarshi yayi ya kira Umma ya faɗa mata halin da yake ciki, da abinda ya faru.
Hakuri tabashi sannan tace.
"Yayi kokari ya dawo da yaran gabanta, ba tare da gardama ba yace toh.

      ****
Ata ɓangaren Asad kuwa abin ba'a cewa kome, sabida lalacewar tayi muni duk ya koma wani iri, babu cikakke hankali a jikinshi duk ya zama birkitacce sai Addu'a kawai.

   ****
Zaune suke gaban malamin suna jiran jin abinda zaice musu sabida zuwansu na biyu kenan na zuwansu na  farko dakyar suka sami ganinshi sabisa baya gari sai yau, ynz ma yana tare dalibanshu suka zo, zamansu keda wuya sai ga wani yaro da motarsa irin matasa, nan wanda kansu ke ɗaukar hayaki yana zuwa yaja ribas har sai da kura ta tashi, sannan yafito yayi tafiyarshi duk kura tacika gurin, kallo wani yaro yayi a gurin yace.
"Abdurrahman bani dutse karami."
Da sauri yaron ya ɗauko ya mika masa.Addu'a yayi a jikin dutsen sannan yace.
"Ungo jeka makala masa a jikin karfen wanca motar inda zai makale."
Aikuwa yaron yaje ya makala, can sai ga matashin ya fito, yana tafiya yana bounce, yashiga motarshi, yayi juyin duniyar nan taki tashi motar.....

_(Not dagaske ne wannan labarin abinda malam yayiwa motar kuma Ayar alkur'ani ce babu shirka, a ciki sai da kusani akwai abinda idan mutun yayi matukar Allah ya yarda dashi, toh duk abinda yayi Allah yana amsa, musaman Masu kyautatawa Iyayensu Mata, Ubangiji yayi Alkawari ba zai taɓa basu kunya a duniya ba, haka ma a lahira, ku nime wa'azin malam Tijjani yusuf guruntun, wanda yayi hakkin Iyaye, kuji Labarin Sahibuƙ Karni Wanda Manzon Allah (s.a.w) yacewa sayyida umar da idan har Allah yaja da rayuwarsa ya kaishi lokacin Sahibul karni yace masa ya nima masa gafaran ubangiji,  abin yabawa kowa mamaki, ya haka kuma, Umar ɗinda yake cikin masu certificate na gidan Allah.......)

   Kunemi saura kuji yanda lbarin yake.

   Karki manta a ɗaga min darajata ta hanyar Vote....👌
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

   

🌹🌹👳
    *MATAR MALAM*
                           🌺🌺👳


  *NA:Real Dambu ce*

         _Wannan shafin na kowa da kowane, musaman Grp ɗin Aisha Sadan Micika_

      *Ban manta daku ba Zauren Maidambu Idan kun kasance Virus nikuwa Anti virus ce,😂 ida kun kasance bindiga, zan kasance Harshasi, idan aka zama bom nice Nuclear, Ku kasance diga na zame muku shabir, Yanda zamu cigaba da cancanrewa😂😜*

        Dedicated 2 Matar Malam Fans grp.




  *:•~15*

    Kallonsu Irfan yayi wanda mamaki ya gama kashesu,suna kallonshi, hankalinsu yana kan me motar nan, gyaran murya yayi sannan yace.
"Ku manta dashi, irinsu sai da haka inba haka ba kuwa ba zasu shiga hankalinsu ba,..."
      Shiru yayi rike da calbinsa yana lazimi har nawani lokacin kafin yace musu.
"Al'amarin abokinku akwai babbar matsala idan akace da karfin tsiya za'a karya abinda aka masa toh za'a iya, rasa rai kunga kenan, babu amfanin haka, amma kuje kucigaba da Addu'a Allah zai kawo mafita, kuyi hakuri ba naki bane sai dai, babu amfanin haka ne duk da halin da yake ciki, ba daɗi amma dole ayi hakuri da haka."

       Cikin garaje wannan matashin ya iso gurin malam ya durkusa har kasa, domin tunda yayi-yayi taki tashi, gidan da yaje ya koma ya faɗawa abokinsa shine yace.
"Kaje gurin wanca malamin kabashi hakuri.."

   Yana fada masa haka shine yazo jikinshi na rawa, ya durkusa har kasa yana bada hakuri. Kallonshi yayi sannan yace.
"Jeka, bari Abdurrahman ya cire."

          Kiran abdurrahman yayi ya cire yana cirewa kuwa yaron yayi ta godiya yana zuwa gurin motar ya tada ita, a nutse yabar gurin ko raujin da yake ji bai kunna ba (Wato waka, kenan itace Rauji)

                 Ajiyar zuciya Jalal yayi sannan yace.
"Baba mahaifiyarshi tana cikin wani hali wallahi ga abin tausayi, ko lafiya bata dashi ishashe."

             Jinjina kai yayi sannan yace.
"Bari na faɗa muku wani abu guda ɗaya, matukar aka karya sihirin da karfin tsiya tabbas daga shi har Mahaifansa mutuwa zasuyi."

   Zaro idanun sukayi cikin fargaba, suna jinjina alamarin, nasiha yayi musu sannan suka sallameshi,

        Hankalinsu yayi masifar tashi. Kawai sai suka yanke shawaran kowa ya cire layin da yake da nomber Mamani, amma daga gefe zasu cigaba da nimawa abokinsu mafita.

      

          Sam basu cikin farin cikk dan ganin laifin kansu suke da halinda Asad yake ciki..

                *****
Tana zaune a kujera kafanta ɗaya akan cinyarsa,hankalinta kwance kaman wacce taɗaura akan tuntum, hannunta ɗauke yake da abinci, tana ci shi kuma yana zaune sai matsa mata kafa yake.

    Sallamar hibba ce ta tasa ya ɗago kanshi kanwarshi wacce suke uba ɗaya, a hankali tashigo falon kallonsui tayi cikin mamaki da al'ajabi. Dake ita tana da zafi kuma bata ɗaukar rainia tsawance tacewa ramla.
"Ɗ'aga masa kafar dan ubanki, ko na baki mamaki."
      Sai gashi hibba tacika mata idanun ta ɗaga kafar tana kunkuni da cewa.
"Ni dai ba ubana b."

            Aikuwa hibba tafusata ta ɗauketa da mugun mari wanda yaja ta tuntsire kasa.

      Jikinshi na rawa ya ɗago Ramla yana bata hakuri, kallon hibba yayi sannan yace.
"Nagode fita min a gida."

      Cikin ɓacin rai tabar gidan.
Aikuwa tana ganin hibba tafita ta shige ɗakinta ta shiga shirge kayanta wai tagama aure dashi kenan. Dakyar yashawo kanta,


          *****
      A birtaniya kuwa hankalin Imamu ya rabu gida biyu ga hidimar yara gana zirga zirgan dake gabanshi, daman saura wata biyu yaran suyi hutu. Shi yasa bai damu ainun ba, dake yanzun hankalinshi kwance har yar kiba ya ajiye da ɗan karamin tumbi, irin na kwanciyar hankali.

         ****
    Alhamdulillah a bangarena nagama course ɗin da nake sai zaman gida wanda kusan a gidansu Khadija nake rayuwata dan ɗauko babanta tayi yazo ya roka na koma gidansu kuma akayi dace matarsa kaman tacinyemu dan so ko tari mukayi jikinta rawa yake dan jin me yakawo haka.....

   Babu abinda yakai lokaci tafiya sosai ya tafi, kalubalen da nake fuskanta a cikin yan kwanakin nan bai wucce ganin, mutane huɗu suna min kuka da niman taimakona ba, kuma bana ganin fuskarsu asalima idan nace zan isa garesu sai naga sunyi min nisa haka zanta tafiya amma bana cin musu.

          Karfe uku da rabi na dare mike cikin tsoro da firgice sakamakon mafarkin da nayi ana kaman anyi mutuwa, kuma kaman wanda nasani ne, amma bansan waye ba, tashi nayi na faɗa banɗaki nayi alola sannan nazo nayi sallar nafilla, duk jikina   amace ina zaune har akayi sallar asuba, bansan me yasa nake jin sonyi kuka ba, tausayin kaina nake ji, sam sai na tsinci kaina da fashewa da kuka, har da shassheka, abinda ya ɗaga khadi daga bacci kenan, ta shiga tambaya na,

     Kafin na buɗe baki na bata amsa har Abbanta ya shigo, ya kallemu sai ya kauda kanshi yace.
"Maza ku haɗa kayanku ynx zamu tafi katsina."

     Tunda naji har zuciyata tasakw karaya, a daddafe khadi ta haɗa mana kayanmu ko karyawa bamu ba, muka taso bamu iso katsina ba sai karfe biyar na yamma muka iso gidan kawu muka nufa, tunda naga rumfa na fashe da kuka, kafin motar ta tsaya har nafita ina faduwa, da gudu nayi cikin gidan, ɗakin Annah na fara zuwa babu kowa sai an zaman makoki, raba idanuna fara bakina narawa nace musu.
"Ina Annahta take.?"
    Sai suka sunkuyar da kansu, sake tambayarsu nayi a tsawace. Sai ga khadi tashigo cikin kuka tace.
"Annah bab...."

     Na iya jin kalmar farko, amma saura ban jisu ba sai bayan kwana uku a gadon asibiti, ina sonyi kuka amma ina babu ashe kuka ma rahama ce,

    Kwana biyar aka sallamoni tsakanina da mutane ido ko magana bana sonyi, tsintar kaina nayi da ɓoye kaina a ɗakinta nayita kuka, koda akayi addu'ar bakwai aka nemi na koma nace su tafi kawai bana sha'awar zuwa ko ina.

    Sam ko kofar waje bana son fita balle kuma inji wani kawuna yayi kokarin naje gidanmu na gaishesu fir naki, sabida bana son ganinsu.

        Wasa-wasa na shafe wata biyu a katsina cikin kaɗaici dakewar khadi. Ina zaune sai ga Yarinyar kawuna tazo Nabla wai na rakata, kasuwar zamani bana son zuwa amma babu yanda na iya,tsaf muka shirya cikin dogayeɓ riguna bakakke, munyi kyau ba laifi.

       Drvn sune yajamu zuwa kasuwar abin haushi sai da muka fita motar babu mai, kashe motar yayi ya ɗauki galan ya tafi gidan mai, koda yaje can suka ki bashi a galan dole yabar gidan man ya koma wani. Gashi man bar cikin mutane inda muke babu cunkoson mutane, munyi tsaki yafi abinda baki dubu,

       ......
A gidanmu kowa Imamune yaje, kwanansa biyu da zuwa kenan shine yaje sun jima suna hira, sannan Babanmu ya faɗa masa rasuwar Annah, bayan sun gama gaisuwa nan yazo kofar gidanshi suka gaisa da ɗalibanshi na yaushe gamo,

       Daga nan shima kasuwar zamani ya wucce,

        ........
A gidan asad ma, Ramla bala'i tasakoshi a gabane wai ya tashi suje, tasayi wani doguwar riga, shine ya mike dukda kuɗin asusunsa sunyi kasa sosai, amma babu yanda ya isa, ko tabarshi yasake kaya tana gudun kar wata ta yabashi, kallonta yayi sannan yace.
"Wai shin har sai yaushe zaki haifi cikin jikine."

   Juyawa tayi ta banka masa harara take yaja bakinshi yayi shiru suka fita.

           ****
Muna zaune sai ga malam habu drvn nan mukayi ta mita dake kunnenshi ɗaya bayaji,  haka muka gama haukarmu bai kula mu ba,😹 eh mana haukarmu tunda bai san mun ji haushinsa ba.

    Koda muka isa fita mukayi, wani irin faɗuwar gaba naji, a hankali nake takawa yayinda idanuna yake ciko da kwalla. Ina shirin shiga wanda yayi dai dai da fitowarsa.......👌Time Up😝😹

*_Shin Waye ne a cikin mutum biyu nan Asad ne ko Imam ne_*😂

      Come nd bite me😉😜😜😜

         [4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳

*Na:Real Me Dambu ce*

😹😝😝😝😝😝😝
*Ehhheee😹😜😜😜 Na shammacesu Alkur'anan.....*

*_Assalamun Alaikum, na samu korafinku akan haɗin auren da akayi tsakanin Imamu da Naiha, wasu suce naiha tafi dacewa da Asad wasu suce da malam duk nagode da muhawaran da kuka kafta, haka yayi min daɗi, sai dai hanzari ba gudu ba, idan kuka duba sunan Litafin Matar Malam ce, Bansa matar Asad ba, da dan asad zan saka toh da ban jingina labarin akan Imamu ba, nayi amfani da Asad ne dan ya shigo rayuwarta, kuma ya fita a cikin rayuwatar kaman Yanda Catty tq ɗauko Yazeed ya shiga rayuwar Sarah, bayan ga wanda ya tsayawa rayuwarta. Toh ku manta da wannan ma,haka ya isa idan akayi dabi da jigon labarin ba iya kan matar malam lbrn ya tsaya ba,makasudin

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment