Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naji muryanta tana magana kaman da matan gidan take, abinda najiyo shine inda tace.
"Ku duba min ɗakin A'isha idan yayi kura kusa yara su share bayan sallar isha ku mikata ɗakinta."

              "Alhamdulillah Ummanmu mungode Allah ya kara miki lafiya da karfin jiki Insha Allah yanzun zamu kintsa mata da kanmu bama  sai yara sun yi ba,"Inji Aunty Kaltume,

              Hira suka taɓa sannan suka leko ɗakin Falmata tace.
"A'isha, sunanki sunan Yayar Imamu ce, amma ta rasu bayan a'isha babu wani suna da ake kiranki da shi."

          Kafin na amsa Aunty kaltuma ta amsa da cewa.
"Ai Naiha yan gidansu suke kiranta da shi,"

          Murmushi nayi kawai nan ma hira muka taɓa sannan suka fita, ina cikin karanta wasikar jaki sai gashi ɗakin,

     Zama tayi akan stool, tana kallona cikin sanyi jiki ajiyar zuciya tayi sannan tace.
"A'isha jibine tafiyarku, amma idan bazaki ba bazan bari ya takura miki ba sai mu zauna abinmu ko ya kika ce."

      Shiru nayi kaina a sunkuye tabbas Umma uwa ce guda me sada farin cikin ɗan wani sama da na ɗan da tahaifa idan na auna maganarta na fahimci wani abu guda shine kawaici, tana son naje amma kuma bata son nai mata kallon sonkai, ɗagowa nayi sannan nayi murmushi nace.
"Umma Allah ya kaimu jibin."

             Kasa ɓoye farin cikinta tayi, albarka tayita sanya min sannan ta faɗa min komawa na ɗakina, duk kaina a sunkuye ganin babu alwala a fuskana yasa murnanta ya koma ciki tace.
"Idan ranki baya son tafiyar shikenan sai mu zauna abinmu,"

     "A'a umma nifa komawa ta can ɗinne bana so kawai." na faɗa mata da hanzari.
Tsura min idanun tayi kafin tace.
"Zagina za'ayi ace ina nuna fifiko a tsakaninku, nima ina son zamanki anan amma a ɗakinki hankalina zaifi kwanciya kinji kinga gidanan babban gidane bana son a wareki a cikin sha'anin ciki, duk kusan yaran cikinta Yaran kishiyoyina ne, suka rasu suka barmin,, toh bana son suyi tunanin nafi sonki dasune kin fahimceni."

         Gyaɗa mata kai nayi cikin gamsuwa da bayaninta, dafa hannuna tayi sannan tace.
"Idan muna da nisan kwana wata rana zan baki labarin rayuwata da nagidan nan,"

          Jinjina kai nayi sannan nace.."Allah ya kaimu lokacin"

             Mikewa tayi sannan tace..
"Goma ta wucce bari nayi walaha kafin azahar"

         "Toh Allah ya kaimu." nace mata,

      Tana fita nima na tattara kayan da naci abinci nakai kitchen na gyara kitchen ɗin,

    Dakina koma na kwanta a hankali bacci yayi gaba dani, ban farka ba sai sha biyu saura, wanka nayi na,sake kayw cikin wata super novo, meye manyan ganye da lemon, hoda na shafa da kwali na fito na ɗaurawa su khalil da umma abinci, ciwon shinkafa nayi miyar ɗanyen kuɓewa, dake naga umma tana son haɗa duk abincin da zataci da wake sai na gyara ɗaura a gas, dake naga itama tana da tukunyar nan mi saurin dafa wake ko duk wani abu me tauri a minti talatin ko arba'in a ciki na dafa mata waken yayi kyau, sai na juye a wani abu nakai mata falo na ajiye,   komawa kicin ɗin nayi na kintsa sannan na koma ɗaki sa nawa abinci.......


      *_Nifa bance zan sayar da buk ba asalima kowa yasanni da cewa sai nayi kuɗi da noɓel, dan haka kowa yasa ranshi a inuwa babu batun saida noɓel😎_*
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     

                *Wattpad:Mai_Dambu*

*:~•29*
_ We are Friend foreve_
   Koda nasaka hannuna a cikin abincin sai nagaza ci koda loma ɗaya,sam bana jin daɗin kome tunda umma tace zan tare ɗakina naji damuwa ya shige ni, sam bana son hayaniya kuma na fahimci matarsa hayaki yana yawo akanta ainun, ni kuma bana son abinda zai janyo min zubewr mutuncina a idanun mutanen gidan haka na ɗauki tsawon lokaci ina sakawa ina warwarewa, dole na tsame hannuna da na rufe yar malmalar tuwon wanda bai wuci khalil yaci ba, tsabar bana son cin abinci da kayan zak'i wow da babu abinda zai hanani cinsa.

           Rufewa nayi na kai falo, kamshi turen D&G na shaka lumshe idanuna nayi na waresu kan fuskarshi, yana cin abinci cikin nutsuwa har zai kai lomar tuwon ya fasa zuba min idanu yayi dake Umma bata falon ta shige ɗaya ɗakinta ta kwanta kafin akira sallah, janye idanuna nayi daga gareshi na koma ɗakina, kirjina na bugawa zama nayi na ɗauko handbag ɗina na buɗe, kwaton ledar chocolate nayi daga ciki na. Buɗe zan kai bakina ji nayi an fauce cikin masifa na ɗago kai, rike yake da filet ɗin abinci a hannunshi na dama ya kwace min abuna da hannunshi na gahu, tura baki nayi gaba cikin kunkuni nace.
"Tunda ba mutum bane yasaya min abina ya bani tun ban faɗawa  umma ta kwace min."

           Zama yayi ya janyo stool da kafarshi, yana murmushi ganin yanda nake kumbura fuska kaman wata yar yarinya karama. Toh aikusan hakane, cigaba yayi da cin abincinsa har ya koshi, sannan ya juya yana kallona yace.
"Madam ina son ruwan don Allah."

         
Murguɗa masa baki nayi sannan na mike naje na ɗauko masa, zoɓ'o da ruwa sai da yasha zoɓ'on sannan ya kora da ruwa, sake tura bakina nayi nace.
"Nikam bani chocona,"

Kallona yayi musaman bakina da yaji pink jan baki lokaci guda ya haɗiye yawunsa, sam bai san mi yasa ba a duk lokacin da ya zauna kusadani, yake jin wani mugun sha'awa ya far masa, dukda yana dannewa amma haka bai hana jin zuciyarshi na ingizashi ba, wani irin abu yake ji kaman nafitowa daga jikina yana raɓansa, k'in bani yayi cikin murmushi da salon wayo da dabara, yace.
"Naihaaaa," ya kira sunan kasar makoshi, tsigar jikina ne ya mike, naji yarrr zuba masa idanu nayi cikin nashi, wasu abubuwa na hango masu wuyar faɗi, cire idona nayi daga nashi jikina na ɗan rawa mika min choco yayi har nakai hannun zan karɓa, sai ya mayar baya sannan yacigaba da cewa.
"Zaki rufe idanunki. Ni kuma zan ɓoye a aljuhuna sai buɗe ki duba inda nasaka indan kin amince fine idan bai miki ba fakat sai nakaiwa Yara, dan ke ai an hanaki shan zaki." ina jin wannan maganar sam ban ɗauka wayo yayi min ba, ni kuwa na amince, murmusawa yayi dan ya kwana biyu baiji ɗumina ba, dan haka yau dole yaji ya nake,

Rufe idanuna nayi shi kuma ya gyara bakin ledar ya ɗaga bargon da yake, bakin gadon ya saka yace.
"Toh bismillah,"

Mikewa nayi nazo gabanshi na saka hannuna a aljuhun rigar ta gaba, lumshe idanun yayi, sannam nasaka a aljuhun gefen babu haka nayita lalluɓashi ban samu ba buga kafa na fara zanyi kuka ya fincikoni, kanshi kaman zanfaɗi haka nayi taga taga, na zuɓe jikinshi, ajiyar zuciya ya sauke cike da kewana ya ɗago fuskana yana kallon cikin idanuna, bansan ya akayi hannuna ya kai kan, sajenshi zuwa gemunshi ba, nidai na tsinci kaina da shafawa, dan burgeni suke kuma ina kallon, gashin bakinshi da ya haɗe da gemun, ina zaga yatsar hannuna a tsakaninsu, lumshe idanunsa ya sake a karo na uku, dai daita fuska yayi da nashi ina jin saukar numfashinsa nayi maxa na ware idanuna cikin nashi, yar dariya yayi sannan yace.
"Nana A'ieesha kina son gemun ne?"
Murmushi nayi cikin nutsuwa ina shafawa nace.
"Ina burin na auri miji me gemu da gashin kirji, ina son ganin mijina na dasu, koda ban samu duk biyu ba, toh zanyi fatan samun ɗaya, a ciki."

Wani irin murmushi yayi wanda ya karawa fuskarsa kyau ya saka hanunshi ɗaya ya buɗe botirin rigarshi, sannan ya cusa hannuna ciki, zaro idanun nayi waye tare da cewa.
"Wow Abu khalil kana dasu kenan"

Sabida daɗin sunan da nakirashi bai san lokacin da ya haɗa jikina da nashi ba, bakin shi na rawa yace.
"Nana A'ieesha sake faɗar sunan da kika kirani da shi."

Kifa kaina nayi a kirjinsa ina dariya,cike da kunya na ɗago kaina nace.
"Ai kaima nasake min suna shine nima nasake maka, nikam ba wannan ba don Allah naga gashin kirjinka hiliss."

Rike baki yayi yana dariya yace.
"Mi kike nufi da Hilis,"
Jan gemunshi nayi cikin wasa nace.
"Kai Ya Imamu pls nake nufi nagani mana."

"Hmm a'a ba zaki gani ba ynz d zance zan ɗan taɓaki kin yarda zakiyi amma ke kin dage sai son ganin kirjina kike sonyi nima kunya nake ji." yace,
Dariya na fashe da shi har ina rike cikina ganin haka ya shiga min cakulkuli, zulewa nake kaman zan faɗi akasa yaki kuma ya barni dan dariya har da kwalla,


Duk abinda muke Umma tafito falo tana jin dariyarmu ta koma ɗakinta zauna xuciyarta fari kal,haka take son ganinmu cikin farin ciki.

Mu kuwa a ɗaki zuɓewa gado mukayi, cikin dariya da son shigewa jikin junanmu, bansan ya akayi nima na biye masa haka ba, amma dai naji har cikin raina ina son haka, dariya nayi nasaka hanuna na cire masa botirin rigarsa, nace.
"Cire mana nagani."

Kallona yayi da idanunsa wanda suka kaɗan sun ɗanyi ja yace..
"Hiliss idan kika ga nawa nima zanga nak.."

Dariya nayi sannan nace.
"Ai zan barka kagani, mana idan kacire nima sai na cire nawa tunda kaima kana jin kunya nima kuma da ina jin kunya amma tunda yanzun ka ajiye kunyarka zaka barni naga naka kaima dole na ajiye kunyata kaga nawa, amma abisa sharaɗin daga Yau mun zama abokan juna bazamu cutar da juna ba ka amince."

Mikewa yayi ya zauna yana kallona kafin yace.
"Ina kika ji an taɓa haka."

Gyara zama nayi cikin nutsuwa nace.
"Kayi hakuri haka nake son na tsara rayuwata da Asad, kuma sai muka fahimci juna ta hanyar zama abokai kafin muka shirya zama masoya, lokaci guda kome ya lalace, kuma ina da burin haka kayarda ko a'a."

Kallona yake cikin tausayawa dan yasan an zalunceni, mika min hannun yayi yace.
"Abota" nima dariya nayi na mika masa nace.
"Abota," ai kuwa sufa nayi akanshi nace.
"Oya lemme see"

Cire rigar yayi ya ajiye a gefe, zaro idanu nayi ina shafa gefen shimin da yasaka ina kallon yanda gashi ya, kwanta, ina dariya kasa kasa dan sun burgeni,wasa dasu nake har na dage masa shimin jikinshi, ban fasa ba,

Sauri sauri yake fitar da numfashinsa sama-sama idanunshi ya dadda rufewa ya sakala hannunshin bayana a hankali kaman me raɗa yace.
"Kawata ni bazaki buɗe min naki rigar bane." yayi wani kalar mage da fuska dariya nayi na sumbaci goshinsa, na ɗan ja kumatunsa nace.
"Abokina kaga Yanda kayi da fuskarka sakace mage, toh nikam rigar yana bani wahala najuya ka zuge min zip ɗin."

Gyaɗa kai yayi daga kwance, na juya zuge min zip ɗin yayi na zarw rigar ta kasa, ina kallonshi abinda ya gani yasashi jan numfashi, mika min hannun yayi na shige jikinshi ina wasa da gashin jikinshi, hmmmm ai kaman jira yake ya shiga hidima shin tun hankalina baya tare da shi har naji wani sabon salo daga Malamina, Abokina, kuma mijina, tsorone ya shige ni, ina son mikewa amma wani abin mamaki shine na kasa hanashi, sabida jikina ya karɓi makaman kare dangin da yakw aika musu, yanda ya dace. Take kayan Aunty Maryam suka shiga aiki baji ba gani, bansan lokacin da nasaka masa kuka ba, ba wai dan banaso ba sai dan yanda jikina yake tsuma da al'amarin, jin ina son ɗaga masa murya yasa ya haɗe bakinmu guri guda, Ai Malaman nan da kuke gani, barsu da yar gemunsu, yanda suke kare sunnah haka suke kare love a gidajensu, dan Imamu badan ya takaita kanshi ba, da yayi min kwaf ɗaya an wucce gurin amma da zaran ya kai hannu zai cire underwear sai na saka masa kuka dan dole, ya kyaleni, ganin yanda nake like masa yasa ya ɗago kaina yama rasa yanda zaiyi dani, dan abubuwan suna son fita, dan ya lura da yanda nake rike mara da matse cinyata, murmushi yayi sannan ya kai bakinshi kunnena ya min ɗara zaro ido nayi nace..
"Nidai bana son iskanci kawai we are just friend ne karka ce zaka min wani abu."

"Bazan taɓa cutar dake ba ki bani damar haka aimu abokan junane kuma,zamu iya taimakekeniya,, dan haka ki kwantar da hankalinki idan nayi miki wani abin cutarwa ki faɗawa Umma tahanani tafiya dake Uk."

Gyaɗa kai nayi, ina son yin kuka amma narasa yanda zan iya, bazan iya faɗan kome ba, amma abinda Malamina yayi min, yasani jin wani sabon kaunar kasancewa da shi, dan yana rabani da wannan damuwar yaga yanda jikina ke rawa, zuwa yayi cikin zafin nama ya rungumeni, muna sauke ajiyar zuciya, amma shi baiki samu yanda yake so ba, ganin dai ni nasami nutsuwa, sai dai yasa aranshi a hankali matankaɗi yake shiga gora, wasa yake da gashin kaina jin ana gyaran murya a abin kiran sallah yayi saurin mikewa tare dani a kafaɗarshi ya direni a banɗaki har a lokacin hannuna yaka kirjinshi dan na mayencewa gashin, ruwa yasakar mana, mukayi wanka kaman yanda na hana gashin kirjinshi sakat nima haka ya hanani sakat abanɗaki taɓa can rike can shafa can sai da nace.
"Da alami baka sallah bane ko."


Watsa min ruwa yayi sannam yace.
"Matsar kece kika hanani sakat da sabin abokan danayi gashi nan sai zare min idanun suke, kinsan me, ina son mace irinki sabida kome naki unquid kuma zan iya kiransu da classic, sabida kece mace ta farko da naganki da kome na yan matancinki cin cin, da fata fahimce ni." dariya nayi muka fito t, turus mukayi nida shi sakamakon, zubawa kofar bayin idanu...............

_Toh fa wacece wannan_

*_Yau pagen duk a love ya kare nasan Masoyan ImNai zasu so wanga page, banso takaita shi har haka ba, amma kuyi hakuri zuwa gobe Insha Allah a bisa sharaɗi zan muku Typing Wallahi idan wannan pagen bai samu comments ba da Vote ba Allah bazan sake Typing ba sai bayan sallah sabida kusan ba lafiya ce dani ba nake muku typing, ga hidimar gida da na yaro da mijina nake zama typing ga matsalar da nake dashi na lalurata, idan baku nuna min jin daɗinku ba zan ajiye typing kuma nayi Ofline, har zuwa july, Insha Allah idan kuma bai min ba nacigaba da Typing Na rantse sau dai mu haɗe a Okada ko Amazon babu ruwa da cinikin biri a Whatsp, duk fitinar mutun sai yayi downloading appsɗin okada ko Amazo a Playstor, Gaskiya ns faɗa muku, no me no saida buk a whatspp,_* 😹😹😹😝
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*





*:~•31*


Tunda muka shiga jirgi nake zuba masa surutu, ina bashi labarin har na ɓengire da bacci.

Bansan iya adadin da muka ɗauka a tafiyar ba, sai dai jin yana shafa min fuskana haɗi da hura min iskar bakinshi, buɗe idanuna nayi naga ashe mutane sun sauka sai yan tsiraru, addu'ar tashi daga bacci mika nayi sannan nacire belt ɗin jikin kujeran ina kallonshi mika min hannunshi yayi na tashi muka fita daga jirgin,ina karewa garin kallo, ganin kaman ba london bane na juya gareshi da sinki sinkin tambayoyina kaman kuwa yasan da haka yace.
"Toh dubai ce, anan zamu fara yada zango kafin mu wucce london nasan sune tambayarki."

Gyaɗa kai nayi dan ya riga yagama bani amsar da nake nima miye amfanin bididigi, daga nan na tsuke bakina har muka isa masaukinmu muna shiga ni na shige banɗaki naje nayi wanka na gyara jikina sannan nafito, shima banɗakin ya shiga ya watsa ruwa sannan yafito lokacin ina kokarin shafa mai ajikina rike hannuna yayi yace..
"Wannan ba aikinki bane bani na shafa miki,"

"Au kamanta da zakayi sallane da zaka shiga wani aiki na daban jeka na gode. Nace maasa,

Bai kara ce min kome ba yayi wuccewarshi, jallabiya ya zare a jakarshi yasaka, hannu da kafa nashafa man sabida jin yanayin garin nasan akwai zafi kasance dubai suna cikin kasashen masu sahara da kuma, ruwa dan ba kasafai suke samun ruwan sama ba,
Amma kusan itace cibiyar kasuwancin duniya, buɗe akwatina nayi na shiga duba, kayan da zan saka can na hango wani yar doguwar riga, me siririn hannun irin hannun vest, sai dai yana da santsi kuma kuma ga tsagun da yake da shi har cinya shara shara, dan ko shafin da suka saka ba me kauri bane kana iya hango kome na jikin mutum, kalar brown, kallon rigar nake wato Fahima danace ta tayani ɗiban kayan da zan saka shine, tayi min wannan mugun aikin a hankali na shiga duba kayan, cikin haushi na ɗaura hannuwana akai Atamfufina kala bakwai tazuba min sai lashi biyu da shaddar fitan bikinmu, sauran kayan kuwa idan kacire kayan bacci duk Englishi wearna ta zuba min, tsakin danayi yafi a kirga dakyar na maida kayan, na ɗauki wnnan nasaka, sannan na karasa gyara fuskana, inda nayi kwalliya
Jan baki red nashafa irin dark ɗin nan, koda nagama na janyo hula cream colour nasaka, naje na,zauna a gefenshi har ya idar da sallah, mikewa nasakeyi dan na tuna wani turaren da Umma tabani yar ɗuri, naje buɗe shi garin na ajiye shi ya faɗi kasa ya zuɓe, kaman zanyi kuka na saka hannuna na kwashe na maidashi cikin kwalbar, sauran nashafe a jikina sabida kamshin turaren na min daɗi, *Allah sarki Umma Hankaka meda ɗan wani naka* Umma uwace da ta amsa sunar uwa dan ita ta ɗauki ɗan wani fiye da nata, umma mutum ce guda ba ɓari ba, domin farin cikin ɗan wani zata iya sadaukar da ɗarin cikin ɗanta tabaka kai matukar za' a zauna lafiya, kusan Yayun Imamu da kanenshi a ɗakinta suke fara karyawa ko cin abincin rana ko dare, umma ta iya tattalin mutum, shi yasa kafinsu Imamu su mata abu su Abba lawan sun mata, kuma duk kwanar duniya sai sun ajiye mata naira dubu uku uku, kusan maza biyar da suke gidan haɗi da turaruka masu kyau. Ajiyar zuciya nayi sannan na koma inda yake addu'a na kwanta a kan gwiwarshi shafa addu'ar yayi babu shiri, na riko hannunshi nakai kancikina, sannan na kalleshi a sakalce nace.
"Yunwa...."
A hankali yake murza fatar cikina lumshe idanuna nayi ina jin daɗin haka, shi kuwa kamshin turarena kawai yake shaka tare da jin kasala, hannunshi ya shiga turawa samar rigana nayi maza narike hannunshi nace.
"Nifa Yunwa nake ji,"

A kasalance ya gyara min kwanciyar ta hanyar mikar da kafarshi yace.
"Toh a cici, "
Wayar sadarwan cikin ɗakin zuwa kicin ya ɗauka yayi mana odar abinci, suka ce ajirasj nan da minti biyar,

Ni kuwa tura masa baki nayi tare da cire hannunshi daga jikina ina kunkuni, da cewa.
"Niba A cici bane."

Janyoni yayi yana kallon bakina, haka kawai yake ji kamanya cinye bakin nawa, sake tura masa nayi nace..
"Wato ga mahaukaciyana magan..."

Jin ɗumin bakinshi a cikin nawa yasa na makale sauran maganar, hmm bakina kan yaga takanshi dan cinye min shine ba ayi ba, amma jan bakin kuwa lolx😹 ai shanyewa yayi tass, masu kirari sunawa Imamu kirari da Imamu gatan gawa, amma nawa Imamun gatan sone, sabida ya iya ririta abinda yake so kaman kwai,
Jin ana buga kofarmu yasa ya sakeni zuwa kofar karɓan abincin yayi, inda ya shigo har inda nake ya ajiye min abinci, har lokacin ina kwance, rigana a sabule zama yayi a kusadani yace.
"Tashi ga abincin nan."
Dakyar na zauna na buɗe abincin cokali na ɗauka na fara cin chips ɗin da sauce ɗin namar kazar da aka yanyankata, sosai naci na koshi shima cin abinci yayi kaɗan.

Ruwan da nasha shi ya ɗauka ya karasa, mikewa nayi na koma bakin gado na zauna, abincin ya faɗa shima kusadani yazo yazauna, da na gaji da zama na kwanta tare da kallonshi nace.
"Yaushe zamj bar garin nan."

"Zuwa dare dan jirgin 8:30 muke da shi," yace min.

Kallon agogon ɗakin nayi nace.
"Karfe biyu saura kwata, toh nikam kwanciya xanyi." Juya masa baya nayi na kwanta. Aikuwa da karfi yajuyar dani,yace.
"Karki sake juya min baya"

Gyaɗa kai nayi na kwanta, abuna dawowa yayi kusadani ya raɓu dani yana sauke ajiyar zuciya, nikan bacci yaci karfina ashe har,zare rigarsa yayi, nima ya zare min nawa, amagagi na buɗe idanu nace.
"Nikan kai baka da wani aikine da yafi wannan."

Bai kulani ba yacigaba da jagwalgwalani son ran tun baccina yana tafiya dai dai har ya dawo ya gutsire, irinsu Imamu idan baka faɗa musu zakayi azumi ba, ka ɗauka toh wallahi sai sun karya maka shi, dan fitinarshi na dabance, duk da nasan ina hutun sallah, amma haka bai hanani taimaka masa har yasami nutsuwa ba wani abin ma sai daga baya kunya tasa ni na kifa kaina a kirjinshi ina wasa da gashin jikinshi, janyoni yayi yasa bakinshi dai dai kunnena, yayi min magana sake rungume shi nayi haɗi da rufe idanuna, ina dariya kasa kasa, ganin naki bashi amsa kawai sai naji harshenshi cikin kunnena, yana min tafiyar tsutsa, kamkame shi nayi nace.
"Allah nima wani buk aunty Kaltume tabani, rayuwar aure a muslunci, anan naga yanda zan baka kulawa idan bani da tsarki, don Allah kadaina min."

Zare harshen yayi yana shafa gadon bayana, yana hura min iskar bakinshi, yace.
"Tunda hakane xan duba miki wasu nima ina dasu sai ki karanta yanda zaki cigaba da bani kulawa kaman ɗan jaririnki ko *Haskena*"

D'ago kai nayi ina kallonshi kafin nace.
"Toh nagode Ruhina"
Dariya na bashi yace.
"Ruhinki kuma ai yana jikinki."



3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment