Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinta da yake zubda jini, cikin tashin hankali Sara ke ɗagata amma sai ta sake komawa ta kwanta sabida yanda cikinta yake azabar ciwo, da gudu wani magidancin Bature ya shigo ya ɗagata yayi waje da ita cikin tashin hankali ya fita da ita yana murza hannunta tare da fadin...
"Meesha buɗe idanunki karki bari musake rasa wannan cikin a karo na huɗu ina sonki ina son abinda ke cikinki, sabida ke narabu da kowa nawa na musulunta sabida ke, pls ki taimaka ki buɗe idanunki..."

A kiɗime suka isa cikin asibitin aka wucce da ita ɗakin kulwa da masu irin matsalarta.....
Ko kun manta da itane......
Lokacin da jameesha tabar gidan Imamu, garin tabari baki ɗaya,ta nufi USA....
Inda ta sauka a calfonia, nan ta shiga niman yan naija mazauna can kuma tasamu, dan sun haɗu da Sara, sun haɗu a gurin cin abinci a nan take nuna mata tana niman abinyi itama sarah bata da wani abinyi sai rawa a club ana biyanta dan haka ta ɗauketa zuwa club ɗin da take, ba tare da wani jinkiri ba suka ɗauketa aiki dake son abin duniya tasa a gaba sai ta faɗa hulɗa da mazan turawa a cikin haka ta haɗu da Nicolas, shahararren mai kuɗi wanda yayi kaurin suna gurin kera motoccin yana da branch a cikin jahohin irinsu Mexico city, Machengahm, Indian, New york da Miame, kuma yana samun kuɗi ainu, tun sau ɗaya da ya kwanta da ita shi knn ya haukace ya hanatq hulɗa da kowa kuma ya hanata, rawa kuɗi yake sakar mata na na fitan hankali..



Da sabida ya huta da ita ya kebiyanta daga baya sai suka koma soyayya, ya bata kome na rayuwa kuma suna tsula tsiyarsu dashi, Jameesha ta zama babbar mata son ranta take murza nairori, ta manta kowa sai kanta suna cikin wannan zaman ta wayi gari da son da ya musulunta ita ta gaji da harkan sabida wani wa'azi da taji a wani gidan raidiyo, shine tq nuna masa zata rabu da shi, haka kawai karshe da yanima ba'asi sai ta fashe da kuka tace ita ko ya musulunta ya aureta ko kuma su rabu, dake yana masifar sonta bai damu ya amince koda ya faɗawa Iyayenshi suka ce basu yarda shi kuwa yace yanzun yaga rayuwa,

Gurin Limamin unguwarsu suka je masa da bukatarsu nan ya msuluntar da shi ita kuma yace sai tayi istibira'i, nan suka amince suka bar gurinshi koda suka tafi amadadin takame kanta tunda tana da iliminta a,a sai take biye mishi suyita shafe shafe dakyar dai sukayi wata huɗun nan ranar da ta gama aka ɗaura musu aure,


Tun daga ranar suka buɗe shafin rayuwa, shekaranta guda ta fara samun matsalae yawan mugayen mafarka da Yaranta musaman Ummi da zaran ta ganta a mafarkin shi knn cikin jikinta ya zube knn, gashi Allah ya ɗaura musu jarabar son baby, sau uku ana ɗaure mahaifar, amma abin mamaki tana ganin ummi a mafarki ta tashi a razane shi knn cikin ya tashi aiki, tayi kuka tayi addu'a har aikin hajj taje, amma Cikin ikon Allah tasmi cikin jikinta, a hanyarsu ta dawowa ne suka haɗu da wata mata, kallonta matar tayi cikin ko in kula tace mata.
"Bazaki taɓa samun biyan bukatarki ba sai kin koma kin nemi wanda kika zalumta.."

Dake a airportne shiru tayi kanta a sunkuye ta ɗago da niyyarwa matar magana, sai ta nemata ta rasa, abinda ya mugun tsoratata knn, ta riko mijinta cikin tsoro haka suka koma Usa cike da tashin hankali......
Ko sati bayi da dawowa ba suka nufi Liverpool, domin niman Imamu da Yaranta, bata sameshi ba amma sun gaisa da Mmn Husna ita ta bata nombeta....

«»‹›
Wayyo jego da daɗi yasin ga daɗi ga cima mai dadi, kusan satin mu huɗu munyi kyau man gyagije yaran tabarkalla kowa ya gansu sai yayi magana.........
A hankali muka cinye sauran kwanakin inda muka shiga bin Yan uwa muna musu bakwana dan tafiya Japan....



............
Allah sarki hauwa ta koma abin tausayi kamar mahaukaciya ga duka ga zagi haɗi da horon yunwa, kuma a haka mutane ke zuwa mata Anita tana amsar kuɗi, ba maza ba, ba mata ba..
Tayi kuka tayi danasani mara amfani
........
_Nifa Allah bacci nake ji, da zaran naci na koshi toh na zama lazy😂_
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*
     

*54*      No editing
         Barin gurin nayi na shige falon Ummah kowa abin ya basu mamaki ɗai ɗaikune basu damu ba, asalima suna tunanin muna tare, ni kuwa ina shiga na,zuɓe a gaban Umma kamar zan fashe da kuka na mika mata Yarinya kaina a sunkuye, karɓa tayi ta umarce ni da nabata ruwan sanyi a frig da sauri na ɗauko na mika mata buɗe bakik goran tayi wanda yayi dai dai da shigowarshi tare da sallama,

          Umma khadi da tafito daga ɗakin Umma itace ta amsa sallamar, cike da mamaki.....

     Daga nk har Umma bamu damu dashi ba, ruwa ta gumtsa ta fessa mata aikuwa tasake ajiyar zuciya, Amatul na ganin haka taje ta rike hannunta suna dariya, mikewa nayi Umma tace.
"D'auketa kiyi musu wanka dan itama wancar sha zumaminyar taje kan madarah tayi nata shagalin, Allah yayi musu albarka ya shiryesu shiriyar Addinin musulunci, Amma Abba lawan ko Hassan ko mansur sai sun biyani madarata da ovelte na, in haka ba toh Allah sai dai kutattara kuje gurin Hajiya Saratu itama taji yanda suke min, yara da kiriniya sai kace ana jona musu chaji,"

      Dariya nayi cike da kunya nace.
"Kayya Umma zan tafi da Amatul zan bar miki Amah."

     Zaro ido tayi tace.
"Ni ban isa ba wata rana ni za'a samu a birkice sai dai Ko Khadi tana niman yar taya hira."

           "Ni Khadijatu zan ɗauki wannan yarinya da dai yar uwrtace xan ɗauka amma wannan da idanunta yayi kama da ɓarna ce zan ɗauketa ta karasa min sauran gwiwata dai ko?" Inji Umma khadi,

       Mun manta da Imamu na gurin, shigowar Aunty balki da dariya tayi tace.
"Ai wallahi Umma wato dana ɗaukesu suje kwana biyu, saura kaɗan ta sako show glass akanta, na koretaa gurin sai ta koma ɗakin Daddy taje ta sami medical glss ɗinshi ta saka, bai isheta ba kawai ta shiga yaga masa takardu Allah yasa gama amfani da su, yana shigowa yace mata sannu ɓuruntu toh jeki wurin Mami nakawo chocolater, shine tafita, ashe ɗakina tashige taje tayita wasa da kayan kwalliya, Tabarkallah ɓarna ko dangin ɓera sai haka."

     Daukarta nayi ina dariya bayan na gama basu labarin irin abinda tayi tamana a can,kamo hannun Amatul nayi ta fincike ta ɗage kafa itama a ɗauketa, durkuwa nayi ta hau bayana muka shige ɗakin, rasa da wanda zan farawa nayi gwara Amatul ita bata da matsala, dole ita nafarawa wankar tare da ajiye bulala nace yayi min gadinta, kafin mu fito tayi bacci sabida sumar da tayi ya saukar mata da zazzaɓi.

   .......
        Jingina yayi da jikin bango yana mai sauke nauyayyar ajiyae zuwa, me cike da nadamar abinda ya aikata, karasawa yayi gaban Umma ya zauna kanshi a sunkuye hakuri ya shiga bata amma ko ɗaga kai ba, da taga zai dameta tsuke fuska tace.
"Da fatar zaka sallami yar mutane ko, dan bazaka sake tafiya kabarta cikin tsaka mai wuya ba, sannan matukar ina raye bazan sake barinka ka ci mutuncin Yar mutane ba, nabaka nan da kwana uku kadawo min da takardanta, idan kuma kaki toh zan zareka daga cikin Yarana."

      A razane suka ɗaga kai cike da tsoro ita kam ko ajikinta mikewa tayi tabar musu falon ,

     Nima wanka nayiw yarana kafin nima nafito ina goge gashina wnda na wankeshi ganin mutum nayi a gabana, kauda kaina nayi na cigaba da goge jikina, tsuma nake a raina da kuma jiran ya ce min wani abu, kamar yasan ina rike dashi sai hayewa gadon yayi gurin yaranshi,
           Sumbarta Amah yayi sannan ya juya ga Amatul, itama ya sumbacin kumatunta ina lura dashi yanda yake goge kwalla, dai-dai inda yanake ya sauko, ya zuba min ido ganin yanda nake shafa mai da kuma lura da yayi nakara girma kara zama big madam, ga wani uban gogewa da nayi, dan ya lura wani ji ji dakaina nake, yanzu.
      
      Ina gamawa na ciro inner wear nashiga sakawa cikin kwanciyar hankali, mikewa yayi yazo ya shiga jan zip ɗin rigata tabaya juyawa nayi a fusace, ina wani hucci na bar gurinshi na dawo ta inda Amah ke kwance, biyoni yayi ya zuba gwiwuwinsa a kasa tare da zuba hannunwashi a kan cinyata, ciki ciki nayi da fuska, ina kallon gefe hawayen da nake kokarin hanasu saukane suka zubo,  kuka ne ya kwace min sosai nake kukan sosai, bai ce min kome ba, sai danayi mao isata sannan na zare hannunshi daga cinyata zan bar ɗakin baki ɗaya, rike hannuna yayi cike da damuwa yace.
"Wallahi na azabtu, da rashinki na ganki na shigo da kwarin gwiwa kukanki da shirunki zai cutar dani, don Allah kiyi min magana bazan iya juran shirunki nan ba."

       Aikuwa tunda ya faɗi haka nayi gum da bakina yayi rarrashin duniyan nan ko zan kulashi amma firr naki, har yaran suka farka goge fuskana nayi na kakkaro murmushi na mikawa Amah Hannu, ɗaukarta nayi zuwa ban ɗaki tayi fitsari sannan muka fito nakai Amatul, itama kafin na fito ta isa gurin da taga an ajiye turaren wutar Umma jikinta har rawa yake taga ɓarna, daka mata tsawa nayi. Ta juyo tare da kankance fuska, kamar zatayi kuka nace.
"Maza mufita, Allah ya shiryeku."

         Amatul tana jikinshi sai shafa kanta yake cike da kaunar yaran baki ɗaya, juyawa nayi naganta raina ɓaci yayi naje nafinciko y'ata nace suje gurin Umma  sannan na juya gareshi cikin rashin kunya nace.
"Daga yau karka kara taɓa min yara, idan kuma kacigaba toh Allah ya isa min, ban yafe ba zanje na nima musu uba adali wanda zai rikeni dasu ba ir......"

          Jina an haɗani da bango cike da tsananin tsoro na zaro idanuna, amma dake raina ya ɓaci hankaɗeshi na shiga yi, cike da masifa, ajiyar zuciyarshi naji a dai dai kunnena, kaucewa nayi na hankaɗashi amma ko gizau bai ba, sai ma sake matseni dayayi sannan ya fara magana a hankali wanda saukar numfashinsa ba karamin jefeni yake cikin wani yanayi ba, tsagar jikina ne ke mikewa, kuka nasaka masa ina jin ya fara magana wanda yake can kasar makoshinsa..
"Ki nutsu muyi magana na fahimtar juna daga ni har ke mun wucce, ɓatawa juna lokaci nasan nayi kuskure amma ashirye nake na gyara kura kuraina."

              Jin bakinshi nayi a wuyana basan yana kasheni da wani mugun sumbarta da naji kafafuna kamar bazasu sake ɗaukata ba, rike rigarshi nayi nasake masa kuka me ban tausayi cikin kukar nace.
"Har abada bazan taɓa karɓan tubanka ba sabida abaki kafaɗa, kasan abinda ka faɗa min kuwa, babu wanda ya taɓa sani kuka sama da kai, ka cutar da zuciyata ka sani kukan zuci da nasarari, *Jahila, Zina* baka ji kunyar faɗa min wannan kalmar ba, inda yau ni jahilar ce bazaka sake kwaso kafaffuna zuwa inda nake ba, amma dake ba kunyane daku ba, Alhamdulillah kaine wanda yasan Aisha ciki da waje da yau na zo maka kofar qbuɗe da har abada bazai daina kuka ba, kafita a rayuwarmu nida Yarana kayi tafiyarka kabarmu dan wallahi na gama zama dakai gwara na zauna da wanda yasan darajata koda kuwa babu soyayya, amma kai Allah yayi min tsari da sake zama karkashin inuwarka, dake yanzun kana cikin tashin hankali da tsaka mai wuya shine kaɗebo kafarka ga jahila mazi......"

     Haɗe bakinmu yayi guri guda, shi ya hanani karasa abinda nayi niyyar faɗa dukar kirjinshi nake tare, da ya kushinsa, ganin bazan nutsu ba ya sarkafe hannumu guri guda, sannan ya haɗa da bangon ɗakin, duk masifar da nake ji yahanani katabus, zamewa mukayi har kasa, sai jikina duk ya mutu murus, sannan ya sauka izuwa wuyana  yana abu ɗaya, hawaye ke bin fuskana domin jikina ya gama amsar sakonshi, numfashi nake saukewa akai akai, kamar wacce tayi tsare, bansan ya akayi ba naji na rike rigarshi gam ina sake shigewa jikinshi, duk yanda naso karta masa rashin mutunci amma ina na gaza haka sai niman yin abin kunya muke, *Ke wata irin mutum ce mara ilimi, jahilar ina ce ke, A ɗakin aurena kika kawo min wani namiji akan mi zaki zaɓi zina Aisha* wannan sune kalmomin da bazan iya mantawa ba basan lokacin da na tattara karfina na tureshi ina haki, cikin masifa nace.
"Wallahi bazan taɓa zama da mara adalci irinka ba wanda bai san darajar mace ba, na baka nan da kwana biyu ka sauwake min wannan kaddararriyar Aurenka in ba haka ba, kuwa toh Wallahi kowa sai ya jimu dakai, kuma ka cire a ranka Yarana kasansu dan tafiya zanyi da kayana sabida basu da wani haɗi da kai, nice uwarsu nice Ubansu matukar ka takura min zan haɗaka da Umma dan sabida da ita nake zaune da wannan auren naka,"

         Ina gama faɗar haka na shige ban ɗaki na buɗe ruwa akaina don ko kayana ban cire ba, nasake kuka sosai har sai da nasami nutsuwa, fita yayi daga ɗakin hankalinshi a jagule ......

     Tun daga ranar bansake jin ɗuriyarsa ba toh ana ta hidima wake ta wani,

         Kwana biyu tsakani sai ga hajja, ranar munga tashin hankali dan ba karamin rikicewa tayi sai mun fito mata da Yarta wato nayiwa Yarta kurciya, dan na mallake imamu, gefe guda ga Ummanshi hura masa wutar da  ga kuma nima, Ga Yan uwanshi da suka babu ruwansu yaje can sukarata abin ba daɗi, ganin fitinar takici takincinyewa yasa Umma ta shiryamu muka bar yobe, zuwa katsina, ranar wuni,  da safe, koda Hajja ta ganmu mun fito tare da zakanyoyina wato yarana sai tashigs zagina ko inda take ban kalla ba nayi sallama da mutanen gidan muja fita,.......


         Shi kuwa bai san mun bar garin sai da ya haɗowa Yaranshi kayan kwalam, akace masa ai mun bar gari, baice kome ba ya zuba kayan a gurin, damuwa tayi masa yawa ya rasa inda zai cusa kanshi, sun shiga sallar azhar ya yanki jiki ya faɗi a guri.......

                 *_Alhamdulillah duka duka anan na dakatar da rubuta matar malam Allah ya bamu aron numfashi bayan sallah mu cigaba, Ina mai rokon duk wanda na ɓatawa rai yayi hakuri ajizancin aɗan adam, Allah yasa mudace da fatan zamuyi azumi lafiya da kwanciyar hankali...._*

                  *Godiya gareku Masoya na hakika, My Wattpad Friend, and Whatspp Allah yasaka da alkhairi da bibiyar matar malam*

       Nagode My Kishiya, Sister Nana, Maman Sadeeq, Sisteer Dausayi, Sister Ferteemer(Mommy Naseem,) Mutane ghana, sister Hadnoor, Da sauransu

        *Zauren Mai dambu Jam'i zan muku amma dukda haka ina muku fatan alkhairi*

       *Ban mata da Matar Malam Fans Club One da Club Two, kuma kuna raina,*

       *Kacokan nakune wannan shafin masoyan Huguma*

     
            *Wannan littafin gaba ɗayanshi Sadaukarwa ne ga duk Mai suna Aisha dasuke online baki ɗaya nagode da bibiyar wnnn lbarin*


           *Tukwacine gareku Aisha Sadan Michika da Aisha Novel grp ina alfahari daku nagode*

                 ```'Ina mika gaisuwa ga Sidiya an Fans member grp ɗin Aunty Jamila safyanu da Aunty Jamila, Muh'd tare da Ummi Aisha, da kuma Aisha ebonyi nagode kwairai

          Toh fa Matan quarts ganaku gaisuwar fatan alkhairi ga Yar mutanen Azare Sister Fauziya nagode.......


         Alhamdulillah👌```🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳

*Bismillahi Rahamanin Raheem*

Barka da Sallah..

*Page:~•55*

Cikin tashin hankali aka sungume shi zuwa asibiti, cikin gaggawa aka amsheshi, hankalin kowa ya tashi a gidan amma banda Umma da Hajja, wacce ta kekashe idanunta akan karya Imamu yake babu wani ciwo dan yaga Matarshi da Yaranshi basu kusadashine......

Kwanarshi uku umma taje asibitin, dan yasamu sauki yana zaune tasame shi a zaune, rike da malt a hannunshi zama tayi a kusadashi ta kalleshi na wani lokaci kafin ta maida hankalinta kofar ɗakin, a hankali ta fara magana, tace.
"Zuwa kayi nan ka kwanta ko? Bayan kabar tarin matsaloli a gabanka ni bazan rabaka da iyalinka ba amma dole kacire wannan damuwar kaje ka nimo mata yarta, kadawo min da ita, ni kuma zan baka damar fuskantar matarka, Aisha mutum ce kuma! na yarda nagartanta zata fahimce ka sosai Ammna kaji tsoron Allah A al'amuranka ka daina yanke hukunci cikin zafin rai da fusata badan Allah ya dube zuciyarmu ba ai daba san hannun da zata faɗa ba."

Ba tare da kara ko uffan ba tabar asibitin, jikinshi ba karamin sanyi yayi ba haɗi da nadam.

****
Ni da yarana muna katsina hankalinmu kwance sai ma, tunanin Imamu da yake niman zautar da nidi Jama'a ina cikin tashin hankali, duk shekarun da nayi bama tare ban taɓa jin kome a raina ba, amma ganinshi d nayi a Yobe ya hanani sakat banda tunaninshi bani da wani aiki ga wani irin Feeling da nake ji da zaran na tuna shi, dole yasa na fara azumi baji ba gani, abinda na lura mutumin nan ya koya min halinshi, dan har na fara fahimtar haka,

Kullum Idanuna nakan wayata ko zai kirani babu shi ba labarinshi,....
Har muka dawo yobe babu wanda yace min wani abu akanshi nan ma haɗa kayanmu mukayi sai abuja daga can muka wucce Japan.

***
Shi kuwa kwananshi shida yabar yobe zuwa london, inda ya shiga niman Hauwa cikin gari da gefen gari da yaga zai ɓatawa kanshi lokaci sai ya nemi hukumar shige da ficcen london inda ya basu hotonta da ranar da tabar gida, cikin abinda baifi kwana huɗu ba, suka sama masa inda take tare da taimako masu sifurin jirgin kasa, daga nan Liverpool ya nufa inda nan suka dukufa nimanta har ya cire rai asamunta, sai gashi yasami labarin tana asibiti ba lafiya, asibitin suka je, inda sai da ya kusan zubda kwalla gyaɗa kanshi yayi cikin raunaniyar murya yace.
"Kinga hakkin Aisha ko? Bata zalumcemu ba muka zalunceta Allah ba zai taɓa barinmu a haka ba."

Itama kuka take duk tafige ta lalace, baka ganin kome sai ido da hanci, niman likita yayi aka sauya musu asibiti zuwa london a can ya hadata da likitoti suka rufa mata akanta, ana bata taimako yanda ya kamata.....

Satinta uku ya dawo da ita Yobe gurin Uwarta ya zuba musu kuɗi tacigaba da jinya.

*****
Daga nan bai tsaya a ko ina ba sai gurinmu garin Tokyo wani irin sanyi me shiga jiki dan har dusae kankara ake, dake sun bashi cikakke adress ɗina dan haka bai sha wuyar gane indauke ba, ni ina kitchen ina sarafa mana abincin dare, Ashe yar ayi taje tasami ɗan makociyata Yar kasan China, mai suna Chan ɗan lukutin yaro amma babu wayo, tana ta dukarshi tare da ja masa gashi dake Baban Yaron Mrs Jun yana koyar da faɗa iriɓ karetin nan, wai ita akan yaron zata koya, sai chaskele musu yaro take tsakaninta da Allah tana cewa.
"Chan iye isha, gusha ahh."
Mutuwar tsaye yayi ganin irin tabargazar da Yarshi take aikatawa, ai kuwa Uwar yaron mai suna Mrs Huxg ta kwala mata kira da Jabbarrrrr a razane taɗago kanta da gudu ta koma bayanshi ta rike rigarshi dan tasan halin matar bata da kirki idan ka taɓa mata Chan, koda ta iso kallonshi tayi tuni yayi mata kwarjini cikin murmushin dole da harshen turanci tace.
"Yarinyar nan bata jin magana uwarta nada kokari ba ruwanta da kowa amma kaga wannan mai ido a tsakar kan nan har twins sisternta bata barta ba yarinys sai kace ibilishiya duk ta buwaye mana yara, sai kace akanta aka fara koyar da Chaskale, toh mun dakatar da ita da zuwa ajin machaskala" tana gama faɗin haka ta juya da ɗanta tana sababi, juyawa yayi ya riko hannunta yace.
"Kainin gurin Mamarki."
Da harshen barbanci dan Aunty Kaltuma ta faɗa mishi yaran suna jin barbanci sosai dan man nima na mai da hankalin sosai na iya amma batakai nasu karko ba,

Amatul na tayani da hira ni kuma ina juye mana abincin naji jikina yayi sanyi juyawa nayi naganshi jingine da kofar ɗakin, ya naɗe hannunwnshi a kirji yana kallona, cigaba nayi da aikina ko kallonshi ban sake yi,

Shirun da naji Amatul tayi yasa na juya da niyyar dubata sai ganinshi nayi dai dai fuskana kamar zamu shige jikin juna, kallona yake cikin nutsuwa janye kaina nake shirin yi naji ya riko kuguna ya haɗani da kirjinshi sauke kanshi yayi akan kafaɗata zuwa wuyana, yayinda yake zuba min wani mahaukacin sumbata, rike rigarshi nayi hawaye na shirin saukowa daga idanuna sabida yanda sakonshi yake sauka a jikina da ruhina sake shigewa nayi sosai jikinshi bnsan nayi kewar mijina ba sai da na susuce na shiga mika masa kaina, a hankali shekaru kusan huɗu suka shiga giftawa akaina bansan lokacin da nature shi daga jikina ba nagyara zamar rigana da hular kaina tare da tsuke fuskana na cigaba da aikina, rungume ni yayi ta baya yana vani hakuri cikin wani irin murya murmushi nayi sannan nace.
"Ai nasan dalilin zuwanka kazo having sex ni ai sabida yanzun nice kaɗai na rage maka, ni kuma na daina wannan ganganci!" dan haka ina baka shawara da ajiye min sakina, dan bana son kara ganinka a rayuwata kai ba kai ba mai kama" ina gams faɗa masa na juya nabar kitchen ɗin zuciyata ns tafasa,

Turuss nayi sakamakon irin ɓarnar da Amah tayi, daka mata tsawa nayi.
"Keee wata irin yarinya ce haka mai shegen ɓarna kinci kaniyarki."

Tun kan na isa gurinta ta bushe sai zare idanu take, kafin na kai mata mangari yar ya sunkuceta, wani katon a jiyar zuciya ta sauke, tare da shigewa jikinshi haushi suka bani nabar musu falon, Ipad ɗinshi ta buga da kasa, sauketa yayi yana mata addu'a a kunnenta,, ita kuwa wasa take da kasumbarsa tana kallon yanda yake addu'ar idan yayi ya tohfa mata sai ta mamula bakinta ta tofa masa,murmushi yayi ita kuma ta fashe da dariya, sannan ta juya ta kalle kofar ɗakina, sai tayi rau da idanu a hankali tace.
"I wnn say sorry for mohh"
Shafa kanta yayi sannan yace.
"Is ok,"

Girgiza masa kai tayi hawaye na zuba daga idanunta tace.
"She angry with me?"

Dariya yayi ya juya mata barbanci yace.
"Ba dake take fushi ba dani take fushi muje mu bata hakuri."

Ba musu suka ɗibo jiki dai dai nfito banɗaki knn, juyawa yaga yaran sunyi suka fita ni kuwa masami damar kintsa kaina dan watsa ruwane nafitar da warin girki, zama yayi a bakin gadon yana kallon cikin wani irin matsanacin damuwa ni kuwa ko a jikina, nagama shirina na fito na barshi a ɗakin.
****
Hmm ban taɓa tsamanin zan iya gasa imamu haka ba, gashi dai ɗaki ɗaya muke kwana gado ɗaya, wani lokacin idan bacci yayi daɗi shigewa jikinshi nake, ga mahaukatar dress ɗin da nake, ga magana mara daɗi, ga baki ɗaya ya rasa tudun da fawa, dan rana,zafi ina kuna, nake masa sai da muka kusan wata guda har da wani abu, ina masa ɗiban albarka dake bashi da zuciya ko ya damu sai ma bina yake.

****
A yobe

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment