Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nidai na shiga uku daga fara bikin nan zuwa yanzun naga kokarin kwakwalwata da bata tashi aiki ba, sabida tsabar rankwashin da nasha, wani lokacin har shafawa nake ko yayi kulu(😂) sabida kwaɗeshi da ake,.

Wanka nayi da ruwan da tabar min sannan nafito nasami kayan da zan saka nan shafa mai, a jikina sannan na ɗauki kayan nasaka tsaf, goran da aunty maryam tabani na ɗauka ina lasa, cikin jin daɗi wayo zak'i har wani mingira kaina nake sabida daɗinsa kawai Auntƴ Zubaida ce tashigo tasamu inata lasar zumar na tafin hanuna nakarewa zan zuba wani. Talle keyata tayi sannan tace.
"Allah ya kawo miki sauki cikin rayuwarki ke kam sai gyaran Allah wucce muje Baba na kiranki sakarya zaki faɗa musu idan maranki ya fara ciwo wucce muje"

Rufe goran nayi na wucce ina tura baki, atamfar super wax ne a jikina a min ɗinki riga da zani sai lafayya da aka ɗauko wanda yayi kalar kayan ,amma hijab na ɗauka muka fita zuwa ɗakinshi. Dawo dani tayi ta ɗaura min lafayyar sannan muka fita tare, takaini ɗakin ita kuma tazo ta kwashe kayana tass ta mikasu waje aka zubasu a mota.



:::: Tunda na shiga ɗakin kaina a sunkuye, da addu'a ya buɗe bakinshi sannan ya ɗaura da nasiha, sosai suka min faɗa dan yana gamawa innaji takarɓa itama. Sai da tasambaɗe min kunnuwana dan har gyangyaɗi na fara, sannan aka fitar dani sukace nayi alola muyi sallarmu tunda hudu da ashirin da biyar muna idarwa sai ga motarmu yazo ɗaukarmu ɗakin innaji na shiga dan taki fitowa, zuwa nayi na zuɓe a jikinta cikin rawan jiki nace.
"Innaji karki bari sutafi dani, ni bana son zuwa ba zankara muku shirme ba da sha-sha-shan ba, na tuba don Allah ki barni na,zauna."
D'aurewa tayi cikin sakin fuska tace.
" Kin manta nima gidanmu na bari nazo gidan babanku ko kin manta cewa Mahaifiyarki itama aure ya rabata da danginta baki ga su, Zubaida a gidan wasu suke ba, muje na raka yarinyata ko." kuka na fashe da shi sabida itama naga idanunta cike da kwalla amma take boye min kuka nake ina bata hakuri ba xan tafi ba tabarni na zauna dasu. Amma ina sharewa tayi takaini har cikin mota, sannan ta juya da sauri nafita zanbi bayanta Aunty hajra tashiga motar ihu nake ina mike musu nikan bazanje ba, aikuwa mutane da zasu tafi suka shiga aka tada motar ina ji ina gani aka rabani da gidanmu, kuka kuwa da nayi babu iyaka dan dama suma sunyi sallarsu tafiya ake ba kama hannun yaro, ba mutsaya ba ko wani abu sai karfe shabiyun rana muka tsaya lokacin har baccin wahala nayi koda muka tsaya a gidan mai dakyar nafito naje nayi fitsari sannan akace tunda sha biyu da rabi tayi ayi sallar azhar, aikuwa haka mukayi, aka ɗan taɓa abinci sannan muka sake mikewa.

Aikuwa karfe uku da arba'in muka isa garin Yobe,munsami karɓa cikin mutuntaka da karamanci sai son aga fuskana ake, shashin Abba lawan aka saukemu inda daman da matarsa muka dawo ina jin wata tana mata, magana ashe da gayya kuka gudu katsina su Husaina nacan maiduguri suna shan tujara,, dariya tayi sannan tace.
"Kinsan dai Yanda muke da jameesha wallahi yakolo nagani na,zatace nazo da mugun nufi akan zan dami kaina baki ga irin tarɓan da aka mana akatsina ba."


Take suka juya harshe zuwa barbanci,(Lolz daga Indawatulu sai barka shine na iya 😂) aikuwa sai yabo muke sha, banɗaki mukayi alola, muka gabatar da,sallah sannan ta kwashisu Aunty da goggonina suka nufi part guda uku na tsakiya nashi na gefe hagu da daman kuma na matanshi nuna musu tayi sannan tace.
"Ina ganin ku zaɓe na hannun damar yafi kusa dashi kuma ta cikin falonta zai shiga side ɗinta kuma wannan shine dalilin da yasa mukayi samakon zuwa, tunda ita babba ita ya dace ta fara shiga ciki, koda marigayi take nan itace a ciki shi yasa mukayi tunanin haka akan Naiha." godiya sosai sukayi cikin jin daɗi yanda take nuna kaunarta a gareni,


Sawa akayi aka sauke kayana suka shiga aiki ka'in da na'in, kafin magrib sun haɗa, gado wasu na falo wasu na ɗaki wasu na kichin, ana kiran salla sukayi salla a part ɗin suna idarwa,, Yan maiduguri suna isowa,, kai tsaye suka wucce da ita, part ɗinta dan su suna tunanin zasu rigamu zuwa ne,sai gashi sunzo sun samemu a ɗakin, abin mamaki da ya faru tunda muka zo nake ɗaki a kunshe amma ita daga zuwa ta figar da mayafita, tashiga masifa akan ita ɗakin dama take so dan har shigowa tayi taga kofar shashisa a cikin nawa ita kuma dole sai tafito tsakar gida tazo wajenshi komawa ɗaki tayi ta fashe da kuka takira Mamanta a waya cikin kuka tace.
"Hajja part ɗin zahir suka bata fa."

Can uwar ta lallayo ashaeiya sannan ta maka tayi ta masifa sannan ta shiga rarrashinta inda tace.
"Kwantar da hankalinki ince wannan kwaɗo da makulin Yana hannunki, toh kiyi shiru naji wai nan da kwana biyu zasu tafi toh ai namiki bayanin Yanda zaki sarafa shi, ai insun san wata basu san wata da dani suke zance kirufe kwaɗon Yanzun kina jina ko karki barshi a buɗe, Allah yayi mki albarka shalele na bazaki taɓa zama bora a gidan miji ba, sannan karki saka jigidan nan fa har sai ya shigo hannunki nan zaki maka damu yake maganar ki huta autata."

Wani irin farin cikine ya kamata cikin yarda da uwarta tace.
"Nagode hajjana me share min hawayena, Ina sonki Uwata takaina sai anjima." kit tashe wayar ta share idanunta, ta koma tsagar gabanta itama a cikin dare akaƴi mata jere, ɗakuna ukune a sidena da falo biyu, ɗaya babba ɓa ciki karami ita kuma biyu, ne da falo ɗaya, Allah sarki Baba yayi min gado daya ɗan kamfani haka ma kawuna yayi min, shima ɗan kamfani sai wanda Annah tayi min shi kuma kafinta yayi amma zaka iya rantsewa na kamfani ne, babban falona aka jera kujerun babanmu karqmin kuma aka jera na kawuna, sosai suka kintsa gurin sannan suka fito,


Kayan gara suka cire aka ware namu sannan suka kira, Kaltuma matar Abba lawan nan suka shiga tambayarta yanda ake abu bayani tayi musa sannan tace.
"Amma ba lallai bane sai kunyi wasu abubuwan tunda ku bakine ba Yan gari ba,"

Dariya goggo rabi tayi sannan tace.
"Ai mukuwa zamuyi dan mahaifinta ya bada kuɗi ga duk abinda babu asaya, muna nima mata daraja ne a gurin mutane kar wata rana a mata gori ta kasa a gurin kayan gara."

Haka sukayi kome cikin al'ada kafin suka koma ciki abinci suka ci sannan suka kayi sallah bayan su idar Kaltuma tashigo tace.
"Idan kun gama ko zaku kaita ɗakin Umma ku gaisa, itace mamar mazajenmu."

"Toh insha Allah ynz zamu miki magana bari mu kintsa kishiyar taki," Inji Aunty Maryam kenan.
Dariya tayi rike da haɓɓa tace.
" Wai ni Kaltuma rufa min asiri da Malam Imamu kar ya fara tura min hularshi gaba dan yace min saura amaryanshi ta rame da aka kawota shashina dan yasanni da rowa, Yasamu sabuwa ya manta da tsohuwar zuma."

Dariya suka saka inda Aunty Hajra tace.
" Aikuwa kece Original Naiha ce fake." Cikin mutuntaka suka gama barkwacensu sannan ta koma part ɗinta, Inda taje tasami mijinta sai mita yake abinda Hajja yakolo tai musu, akan sadaki, tsaki yayi yace..
"Shima imamu da taurin kai yace ba zai biya sisin gwal ba,dan matarso Ake biyawa sisin gwal matar cushe kuwa sai dai takardan kuɗi. Babu yanda banyi da shi ba akan yabi amma fir yaki karshe haka aka ɗaura auren a sasakin da yabayar, da nayi masa magana kuwa, murmushi yayi min kawai." Dariya take kaman cikinta zai kulle, tace.
" Ai A'isharsa da Yabiya sisin gwal ai taci abiyane haka,sabida koda bai biya ba wallahi ku masu karawa Iyayentane, dan karfi Iyayenta nadashi, amma kasan mi yakara musu karfi mutuntaka da karamci duk abinda muka musu bamu biyasu ba dan taci gwal har da diamon, kai Daddy munga hidima fa, mutanen nan sun biya shi sama da sisin gwal dan sun karɓemu da hannu bibiyu kuma sun kyautata mana fiye da kima har nayi fatan da suna da wata Y'a da mun shiga nimawa Fadeel ɗinmu"


Sallamar Aunty Zuby ya katse musu hiran....... ..



#Voter#Share#Comments😇
[4/26, 19:39] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*


*_Da yawwanku suna son na gama buk ɗin da wuri kuma haka ba samuwa zai yi ba dubi da halin da nake ciki ina matukar takuruwa sosai dan na faranta muku ni kuma kuntata kaina nake dukda haka bai dame ni ba dan haka yana sani farin ciki amma da yawa basu sanda haka ba A gaskiya zan faɗa muku wata guda ya kasa min da na gama matar malam abin mamaki naga kuna iya bin wasu buks masu tsayi amma sai gashi kuna korafen na gama da wuri  gskiy banji daɗin haka kubarni nayi abinda ya dace idan na takaita labarin bazaiyi ma'ana ba akwai buks ɗina guda uku da na takaitasu Wallahi idan ina karantawa bana jin daɗinsu sai naga akwai abinda ya dace na saka amma haka na gamasu, Don Allah kubarni nayi rubutuna Yanda na tsara, dan a cikin kashi ɗaya banyi kome ba,_*

     _Wannan shine korafina na farko don Allah karku kara min damuwa akan wanda nake ciki Ina muku fatan alkhairi_🙏

*:25*
"Wa'alaikumun Salam, bari na har kun fito." tacewa Auntt,
"Eh mun gama."
    "Toh muje"
         Jagora tayi musu har zuwa babban part ɗin Ummansu, a hankali Aunty maryam ke rike da hannuna har cikin tangamemen falon Umma wanda yake cike da kayan kawaya da kuma na tunawa akwai Allah dan gefen palon labrery ne cike da litattafan addini sai frame wanda suke ɗauke da sunayen Allah da Ayatul kursiyu, haɗi da Yasin kujerun falon set biyu ne sabida girman falon ga tv wanda zan iya ceasa cinema ba kome ke tashi a fuskar tv ba sai wa'azin Malam jafar, wanda sunnah tv suka saka, kowa ya nutsu yana saurarro, _kutt_ nace a raina  lallai akwai duyun uwa,dan wallahi ba zan iya wanga rayuwa babu nishaɗi ba,ga wani uban kamshi da ya doki hancina bazaki ce turaren wuta bane sabida kamshi mai rikitarwane. Ko ita kanta Aunty Maryam da take auren ɗan sudan sai da ta jinjina kamshin turaren,  dan manyan haɗine na musaman murmushi tayi da ta tuna nima Innaji tayi min haɗin girma sai taji kwarin gwiwa da haka, Allah sarki Innaji na, ina kwance ɗazun naji Aunty Hajra take cewa dukkansu basu sami haɗin turare da humra kaman yanda na samu ba, ai gaskiya suna alfahari da samun uwa irinta dan kusan kayan kitchen bibiyu tayi min hatta wuka, set biyu tayi min bayan wanda dangin mahaifiyana suka min, gaskiya ni yar gata ce dan har wash machin aka saya min ga manyan frig ɗina guda biyu, Baba yayi min baba kawuna shima yayi min na tsaye babba, plastma na guda biyu kome na biyu, Yar gatarere kenan, Inji goggo rabi tace" Kaza kanki da motsi " haka take kirana,

        Ji nayi ana zaunar dani sabida dogon tunanin da na shiga a hankali na zauna cike da kunya, raje karan tv akayi sannan suka shiga gaisawa, ina sanye da lace ruwan golder, sai babban mayafina cream wanda ya dace da shigar, kaina a sunkuya naji muryanta tana cewa.
" Taso kizo nan A'ishatu aini ba surukarki bace wa'incan ne surukarki ni Uwace zo nan uwata, kusadani zo nan A'ishatuna, jikina ne ya shiga rawa, haka Aunty Zuby ta mikar dani amma kamar mai karaya a kafafunta na gaza mikewa, rarrafawa nayi na isa gareta janyoni tayi sosai jikinta sai Addu'a take zuba min abinda yasa na fashe da kuka nasake narkewa jikinta kenan, sabida lokaci guda naji kaunar matar yasami muhali a zuciyata mutuntakarta ya kara min sonta fiye da kima, tana gamawa cikin jin daɗi tace.
"Bar kuka haka kar Falmata da Kaltuma su sami abin tsokanar dan ma ummul khairi bata fito ba ai yau da kinsha zoyala,"

    Dariya duk falon akayi ita wacce aka kira da falmata tayi karamin dariya sannan tace.
"Ni babu ruwana akan Ya ustaz zan fanshe dan cike nake dashi, yazo ya biyani kuɗin wayata da aka sace garin ɗauko amaryansa ni yanzun bana ta wannan ɓauren dashi uban gayyan nake tukun."
     Dariya sukayi nan dai suka yar barkwace sannan goggo Rabi tare da Inna Talatu, Goggo lantana Yayun Babanmu sai Inna Talatu ita kuma Yayar Innaji suka ce.
"Hajiya ga yarinya nan mun kawo muku, cikin amincin Allah idan tayi kuskure karku ji kome ku tsawata mata, dan nan ma gidane  sosai hajiya A'isha yarinya ce karama sosai ni a tunani na bata cika sha takwas ba tana tsakanin sha bakwai ne, don Allah ku sata a hanya yanda zata gane kanta yanda kuke ganinta ba haka take ba Yarinya ce ɗanya wacce shiririta yayi mata katutu. Don Allah ga A'isha nan mudai zamu bisu da Addu'a sauran kuma Allah zai gyara."

Kanwar Umma me suna Umma Khadi itace tace..
"Insha Allah A'isha tazo gidanan dakafar dama, domin itama yanzun Y'ace a cikin gidan nan da Yardan Ubangiji kaman yanda kuka kawota Insha Allah ba zakuyi danasanin kawota ba, tazo gidansune kuma idan ta fita daga cikin shi Muna fatan babu inda zata sai makavarta,  da yardan Ubangiji  ba zakuyi na dama ba idan shiriritane ai shima Imamun aikinsa kenan yarinta kuma ba damuwa gasu Kaltuma da Falmata insha Allah ta shiga sahunsu zata daina. Baku ga Yanzun Falmata itama tayi nata ba ai dukkansu Yarintar ce ke ɗawainiya dasu."

       Turo baki tayi tana kunkuni cikin raha tace..
"Umma khadi duk abinda,zaki ce kice amma sai ya biyani wayata."

   Tana rufe baki sai ga sallamar Yarta Zakiyya cikn siririn murya gaida kowa tayi sannan ta mika mata  farin laida tace.
"Mamie gashi inji Baba Imamu wai don Allah ki shika masa kurwa ya huta."

           Karɓa tayi ta buɗe murmushi tayi sannan tace.
"Kice masa ai kurwan da nashi da na A'isha na kama dan haka ba zan kunce ba sai nayi tsayuwar dare dan karta kwace min shi, sannan kice masa Allah ya dawwamar dasu shida ita a karkashin Al'arshin Ubangiji nagode duk shekara sai suɓ haifa mana Yan tagwaye masu albarka.'"
     "Amin "dukkan yan falon suka ce,

          Hmm farin ciki ta shiga yi, inda ta mikawa Umma khadi, da sauran Yan falon kowa sai san barka suke mata, barbanci Umma tayiwa Husaina ta mike ba musan me tace ba amma naga har dasu Falmata suka shiga ɗakinta sai gasu ɗauke da wasu ture masu ɗauke da kaya, suna zuwa suka dire a gabanta, buɗewa na farko tayi awarawarone da set na abin wuya, sai ɗaya shi kuma, lifayya ce ja, ɗaya kuma zunzurutun kuɗine, haka ta janyo tiren awarwaron ta shiga saka min a hannuwana, kallona tayi tana murmushi sannan tace.
"Nasan bazaki so ki buɗe fuskarki ba toh gashi kije kisaka, gobe da wannan lifayyar kiyi ado dashi."


Aikuwa ɗakin ya ɗauki "masha Allah" Yan uwana da dangina sai godiya suke, da zasu koma tace.
"A'a kubar min ita anan kuje da kayan ita anan zata kwana."

Cikin farin ciki suka ce "ba kome ai duk ɗaya ne," sai da safe suka musu sannan suka fita suna masu farin cikin dace da nayi na uwar miji tare da mamkin kyautar da tayi min na set ɗin gwal," lallai Naiha tayi dace da uwar miji." Inji Aunty Maryam, Aunty zuby tace.
"Ai ita matsala ɗaya gareta shine wauta amma indai dan girmama na gaba da itane bata damuwa yarinta da rashin ji ke damunta, kuma naga shima Ai yana sonta kuma danginshi suna sonta kuma itama ai bata da rashin kunya, kawai zasuyi fama da rashin kan gadone,kuma ai gidan malamaine bazatayi wannan gangancin ba, duk wautarta zata kare shi da itane, batun kishiya kuwa ai Naiha ba kanwan lasa bace, idan ta juye miskilancinta babu yanda zata iya mata, mudai Allah ya basu zaman lafiya."

"Amin Ya Allah" duk suka ce,

........
Dake ni ɗin Yayar mage ce, zamewa nayi na kwanta a jikinta sosai ina shirin bacci.

Su kuwa hiransu suka shiga yi ahankali kwance har na fara bacci Aunty Kaltume ta tashe ni, a hankali na mike rike hannuna tayi zuwa ɗakin Umman tace..
"Kwanta ki huta,"

Tana gama faɗin haka wayarta na kara, ɗauka tayi tana dariya cikin zolaya tace.
"Wallahi kaji kunya Imamu, kira goma toh gata nan a ɗakin umma bari na mika mata."

Mika min wayar tayi, kaman ba zan krɓa ba na karɓa na kanga a kunne na, ita kuma tafita, shiru nayi bance kome ba, hura min iska yayi "humm" nace masa,
Sautin murmushinsa naji inda yace.
"Naihaaa." yarrr naji tsigar jikina ya mike, har sai da nacire wayar a kunne na, sannan na maida cigaba yayi da magana.
"Barka da zuwa Yobe da fatan kin iso lafiya"
"Lafiya" nace tare da sake wani hamma dole yayi dariya yace.
"Kora da hali yafi kora da sanda, toh nasan bacci kike ji gani nan zuwa muyi baccin tare."

_Kan uban_ nace a zuciya ina zare idanu, wannan ba kunya ce da shi ba, ynz sai yazo ya yakura min. Kashe wayar nayi na ajiye mata a,side bed ai kuwa ina jefa kai a pillow dakyar nayi addu'a tuni bacci yayi gaba dani, jin shi yasa ta shigo tasami wayar a kashe murmushi tayi, sannan tafita, komawa falo tayi tana basu labarin irin abinda aka musu a katsina, kowa a falon sai da suka yaba irin kokarin da mukayi, gyara zama Husaina tayi sannan tace.
"Wato tun karfe uku muka isa maiduguri, har muka je kamu ba'a kawo mana ruwa ba, kai sai da nakare nakira Ya Abubakar na faɗa masa take sai gashi ya kawo mana abinci daga hotel ɗin da suka sauka, sai dare aka kawo mana biski miyar kuka, ai kuwa nayiwa Ya Imamu waya nace ko zan mutu bazanci abincin da aka kawo mana ba yasan yanda zai damu ina kashe waya sai ga Khalifan Ya Ali da manyan ledojin shake da namar kaji da drinks, shi muka ce, da safe ma akwai abokin Ya Imamu a g.a.r, shi ya kawo mana abin karyawa tare da Matarshi Fannah, kai munga tujara ai nun, haka mukayi hakuri, har aka ɗaura aure inda suka saka rigima sai ya biya gwal a madadin sadaki shi kuma yace ashirye yake da ya fasa auren dan bai ɗaga shi yanana da kasa ba, dakyar muka fito fa ana cikin wannan turmusheshen aka sace wayar falmata Lg ɗinta, ai danasan haka ne wallahi da zamana nayi banje ba,"


Mika musu jakunar waleemar da aka basu acan katsina Aunty Kaltuma tayi guda ashirin da uku sannan tace.
"Wannan na waleemar da mukaje anayi ne, daman mu bakwai ne nacire mana saura kuma gashi nan, sauran kuma gashi."

Buɗe jakar sukayi nan suka ciro kalanda wanda yake ɗauke da hotonshi dani, haɗawa akayi duk muna dariya, sai litafi,wanda babu hotonmu sunanmu ne kawai sai memo, da karamin litafin yasin, da 40 rabbana da husnul muslun, sai wasu litattafai na addu'o'i, sai roban cincin wanda yake ɗauke da har nakiya dubulam alkaki, gireba."

Rike baki Umma khadi tayi ta kalle sauran Yan uwanta tace.
"Mutanen nan sun san kan hidima, irin wannan abu haka."

Murmushi Umma tayi sannan tace.
"Keda bakije rasuwar Zahura ba ai nan zaki san mutanen dattawane,har kwana bakwai hidima Hajiya Saratu take mana, ai banyi mamaki ba,."

"Umma wallahi dai dae da ruwan shanmu nagorane, munzo da kayan drinks ɗin suna firji ɗina, sun san me sukeyi." inji Aunty kaltume,

Sallamarshi ya katse musu hira, a gurguje ya gaishesu ya wucce ɗakin Umma dake akwai kayanshi a ciki dukkansu basu damu ba, aikuwa yana shiga ya hango ni............




*Don Allah kuyi hakuri jikin yaki min sannan ku tayani sharen ɗinshi*

Voter,comments👍

[5/4, 06:19] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*


*_Da yawwanku suna son na gama buk ɗin da wuri kuma haka ba samuwa zai yi ba dubi da halin da nake ciki ina matukar takuruwa sosai dan na faranta muku ni kuma kuntata kaina nake dukda haka bai dame ni ba dan haka yana sani farin ciki amma da yawa basu sanda haka ba A gaskiya zan faɗa muku wata guda ya kasa min da na gama matar malam abin mamaki naga kuna iya bin wasu buks masu tsayi amma sai gashi kuna korafen na gama da wuri  gskiy banji daɗin haka kubarni nayi abinda ya dace idan na takaita labarin bazaiyi ma'ana ba akwai buks ɗina guda uku da na takaitasu Wallahi idan ina karantawa bana jin daɗinsu sai naga akwai abinda ya dace na saka amma haka na gamasu, Don Allah kubarni nayi rubutuna Yanda na tsara, dan a cikin kashi ɗaya banyi kome ba,_*

     _Wannan shine korafina na farko don Allah karku kara min damuwa akan wanda nake ciki Ina muku fatan alkhairi_🙏

*:25*
"Wa'alaikumun Salam, bari na har kun fito." tacewa Auntt,
"Eh mun gama."
    "Toh muje"
         Jagora tayi musu har zuwa babban part ɗin Ummansu, a hankali Aunty maryam ke rike da hannuna har cikin tangamemen falon Umma wanda yake cike da kayan kawaya da kuma na tunawa akwai Allah dan gefen palon labrery ne cike da litattafan addini sai frame wanda suke ɗauke da sunayen Allah da Ayatul kursiyu, haɗi da Yasin kujerun falon set biyu ne sabida girman falon ga tv wanda zan iya ceasa cinema ba kome ke tashi a fuskar tv ba sai wa'azin Malam jafar, wanda sunnah tv suka saka, kowa ya nutsu yana saurarro, _kutt_ nace a raina  lallai akwai duyun uwa,dan wallahi ba zan iya wanga rayuwa babu nishaɗi ba,ga wani uban kamshi da ya doki hancina bazaki ce turaren wuta bane sabida kamshi mai rikitarwane. Ko ita kanta Aunty Maryam da take auren ɗan sudan sai da ta jinjina kamshin turaren,  dan manyan haɗine na musaman murmushi tayi da ta tuna nima Innaji tayi min haɗin girma sai taji kwarin gwiwa da haka, Allah sarki Innaji na, ina kwance ɗazun naji Aunty Hajra take cewa dukkansu basu sami haɗin turare da humra kaman yanda na samu ba, ai gaskiya suna alfahari da samun uwa irinta dan kusan kayan kitchen bibiyu tayi min hatta wuka, set

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment