Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin laidar ki rufe jakar shi knn."

Juyawa tayi ta koma ciki kaman yanda tace min haka nayi ina gamawa na saka a jakar na rufe, nakoma ɗaki salla nayi daman alolata da wankana duk lokaci ɗaya nayi, doguwar riga nasaka, sannan na zauna nayi yar kwalliyata dai-dai, shima khalil, ya shirya da taimaka Ummayo, muka fito falo, muka zauna muna karyawa sai gashi ya shigo cikin siririyar murya yayi sallama, duk muka amsa masa, gaida umma tayi sannan ya gaida Ummayo wacce zai dauketa a maiduguri, itama ya gaida ita mukuma muka gaidashi, kallon a gogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yayi yace.
"Umma bako zai halinshi a yafe mana, jirgin takwas da rabi muke dashi zuwa kano"


Mikewa khalil yayi ni kuwa na gaza mikewa sabida kukan da yake son kwace min, fita yayi aka shigo aka kwashe kayanmu, nasiha tayi min da ban hakuri, kiranshi tayi ta tsare gida cikin shan kamshi tace.
"Aisha idan aka miki wani wanda bai miki ba ki kirani ni can zan kwatar miki yancinki."

Murmushi yayi tare da kauda kanshi yana cewa.
*Zakuyi ku gama inda nine*
Fita mukayi matan da yayunshi da kannenshi suka rakamu har gurin mota sai kuka nake,

Haka muka bar garin yobe cikie da kewar mutanen cikinta.

Takwaa saura kwata muka isa, har Airport tare da Hassan da zai dawo da motar gida, niman layin Hauwa ya shiga yi, amma bai samu ba ranshi ya ɓaci amma bai damu ba, kusan takwas da ashirin da biyar sai gata, tana cike tana batsewa kallo ɗaya nayi mata nayi banza da ita dake tare da uwartane Barbanci suka juya, wai ashe Cikine da hauwan jin batun ciki ya shiga rawan jiki sai ya tsina fiska take wai tana jin kamshin turaren da zaisata amai, dan bakar jaraba har gurina tazo nan tashiga kakarin amai, da iskanci juyowa yayi cikin damuwa yace.
"Noor turarenki nefa yasata jin amai, ya zamuyi kenan."

Dake ɗanyen kai dani banyi nazarin maganar da zan mayar masa ba nace.
"Whynot tazo ta kwaɓeni na zauna ba kaya maybe she with be ok."
Ba itaba har shi maganata ya dakesu Hassan kan darawa yayi cikin jin daɗi, dan ko shi abin da Yayan nashi yayi yashake shi balle kuma ni, shiru Imamu yayi bai sake magana ba har ita yar Ikon da Uwarta lokacin tafiyarmu nayi ta noke ita bazata iya tafiya ba jiri take ji nan uwar tashiga bori dole sai da ya rungumeta suka fara typing murmushi nayi nace dani kuke zance dama takalmin kafata hill ce, aikuwa nayi kicin kicin nabuga tuntuɓe ai bansan lokacin da ya tureta ba ya kwala min kira da" Noorrrrrr"

Aikuwa kafin nakai kasa ya tareni,😹 fashewa da kuka nayi ina yarfe hannuna, karshe dai cak yayi sama dani, lekawa nayi na kalle Hassan 👌 yayi min da hannunshi alamun kome yayi yanda ya dace. Yar air sai gata ta ware lafiya lau amma ranta ya baci dani kike Yarinya.


Har cikin jirgi ya kaini, dakyar ta iso muna haɗa ido na kashe mata ido ɗaya, cikin murya kasa kasa, nace mata.
"Ya kika ga salon,"

Bata kulani ba tayi zamanta kusada khalil ni kuwa ina kusa Imamu, shigewa jikinshi nayi, inata zuba masa sakalci da kiriniya, wani abu ko khalil bazaiyi ba amma dolenshi yake jure min, danshi haka danake masa, tafiya dashi yake.


Tara da rabi muka isa kano, nan tasashi a gaba wai zataci abinci dakyar ya nima mata abinda zataci da gayya na ciro mana dambu namar da Umma tayi min da meatpie, da dunot, mukaci abinmu abinka da ciki sai taki cin abincita wai dambunmu xata ci har da zubda kwalla ni kuma ina da saurin karaya da mutumin da zanga yana kuka, ɗiba mata nayi da kome na bata, babu nagode ko ajikina, muna zaune khalil yace min..
"Mommy zansha alwar madara."

Dake akwai a jakar hannuna na ciro masa da sauran tarkace yashiga sha, wannan karon ma rigima tasawa mijinta shi kuwa ya baɗe idonshi da toka yace.
"Dazun da tabaki dambu ince da tsaki kika karɓa, sabida baki san alkhairi ba ni kuwa bazan tambayeta ba, tunda baki da kirki." tass yayi mata nima kuma naki bata, har lokacin tafiyar saudiya yayi, nan na kyale mata mijinta inda tayita zuba shirmenta har muka shiga jirgi.

Bamu isa saudiya ba sai huɗu na asuba dake a jiddane mun sami Abokinshi a airport yana jiranmu, daga nan gidanshi muka wucce inda aka mana tarɓa me kyau, ɗakuna biyu aka bamu inda nida khalil dukda nasan Gogon ba haka yaso ba nikuwa da gayya na kauce masa, nabarshi me wify ɗinshi yanda zasu darji juna (😜....) Aikuwa bakar munafuka da suka shige ɗaki makale masa tayi suka kashe arna, dukda sallar dake kanmu baki ɗaya, tashi yayi, ya shige banɗaki, sam ya kasa ganewa kanshi, tunda muka haɗa shimfiɗa, konace ya lakatoni yake jinshi wani daban bai damu da haka ba sai da ya turmushe hauwa yaji gabaki ɗaya batakai ni ba....(Ooo Imamu ansha daɗi, za'a juyawa hauwa ba anya maza kirki ya ishesu kuwa) wanka yayi ya fito tare da gabatar da sallah ajebo tana naɗe ita zazzaɓi. Nikuwa da yarona bamu kwanta ba sai bayan sallar asuba muka bi lafiyar gado, shi yana kan kujera ni kuma ina gado, kusan karfe ɗaya, ashe khalil kan sun tasheshi guraren goma suka kashi makrnt, nice naketa baccina, ina cikin bacci naji wasu bakin al'amura suna kusantoni, gyara kwanciyana nayi, cikin nutsuwa sabida gani nake kaman mafarkine, Malamina kuwa shima gyara salonshi yayi a nutsu, ya shiga bin lungu da sako, ganin zan hanashi sake ya rabani da hijab ɗina sai rigar baccin mai buɗaɗɗiyar gaba, kare min kallo yayi, cike da kewana ya shiga hidimarsa kawai, yaseen aikin da Umma tasa akamin ba karamin tasiri yayi ba dan lokacu guda na fita hayacina, buɗe ido nayi ina tura masa jikina baki ɗaya sabida karfin maggungunar, Wato bana jin yana larabci ainun amma yau sanadin aikin Ummayo har dasu Ukhti😂 kai Malamanmu ba damane, sai da abin ya kankama ns tuna sa uban ɗinki danasha ai bansan lokacin da na gantsara masa cizo ba sabida ji nake kaman tinkani xaiyi dole yabarni na fashe da kuka jikina har yana rawa,😉 Yaseen nazata yabarni ashe kwanton bauna yayi min, duk wannan abu da muke, hauwa tana mana laɓe, ina cikin kuka na hangota ta jikin window, ganin haka bansan lokacin da na faɗa jikinshi ina kukan shagwaɓa da sakalci haɗi da cewa.
"Sugar karka min da zafi."

"Ok My Hot milk bazan miki da zafi ba,kisaki jikinki kinji My Noor." Tsorone cike da cikina amma fansan na gumawa hauwa bakin ciki yasa na mika masa wuka da nama, dafe muna wani part ne daban na gidan kuma daga matar gidan har mijin basu zaman gida sabida duk suna aiki ita likitace shi kuma malamin jami'a.

Dan haka da gayya ya shiga ɓare baki ina masa kuka da "wayyo wayyo dazafi ni kan na fasa,."

Malamina kan sai da ya kashe arna son ranshi ya kuma kashe bakin tsiwa, dan sosai ya haɗa min zafi, ko kukan danake babu sai zubda kwalla, koda ya kaini ban ɗaki, nan ma banji da daɗi ba, tunda nake bantaɓa laushi irin na yau ba, ko na farkon da kuzarina amma na yau kam, sai da ya cusa min sonshi, da kaunarshi fiye da Da.


Lallaɓani yake kaman kwai ya nimo min riga da zani na atamfa dake kusan duk kayana umma tasani na ɗinke wasu kuma nayi kyauta da turame biyar,.

Duk wani abinda zan saka sai da ya ɗauko min, ɗagoni yayi yana shafa min mai na ɗaga kai naga tabar window nace zaki mutu baki ga kome ba, shagwaɓe fuska nayi ina matsar kwalla yace.
"Ya dai HotNoor."
Tura masa baki nayi ina murza idona nace.
"Ni dai zafi yake min"

Janyoni yayi tare da rungumeni, yace.
"Kiyi Hakuri xai daina kinji,Allah yayi miki albarka, tashi muje kiga cikin gari, keda Maman khalil."

Komawa nayi na kwanta sabida nifa wannan maganin da suka bani, yana shirin maidani irinshi ɗan rungumeni da yayi yasani a cikin wani hali, kwanciya nayi nace.
"Bani zuwa ko ina."

"A kan me?" ya tambaye ni.
Shiru nayi nace.
"Babu"

Juya masa baya nayi cikin kuka ina rike marana, raɓa gefena yayi ya kai hannunshi yana murza min juyawa nayi ina sauke numfashi a kirjinshi dama ya lafiyar kura,

Koda ya nima komawa banki masa ba amma nagaji numfashi nake saukewa a hankali bayan nafito wanka danshi ya rigani shiga wanka, ya tafi masjid, nima mamakin kaina nake bayan na idar da sallah, sai gashi ɗauke da tiren abinci ya ajiye min dake hauwa taci nata tun ɗazun, tea kawai nasha na kwanta, sabida jikina a mace yake.

Murmushi yayi cikin sigar zolaya yace.
"Yan mata yau kece har da mika kai."

Lumshe idanuna nayi sabida bazan iya masa tsiwa ba dan na lura lafiya ta isheshi, baccina nayi da dare bayan dawowarsu khalil, yaso ɗakina ya kwana amma haka naki sabida na lura wani kallon da yake min kasa kasa bazan iya masa ba,.....

Kwananmu biyu a jidda muka tafi cikin makka muka gudanar da Umrah abin mamaki yanda hauwa taki aikin ibadan ta makalewa ciwo, ni kuwa nayi ibadata cikin nutsuwa tare da niman yardan Allah, kuma nayi addu'a Allah ya mallakamin mijina, dan ynx kam ina matukar jin daɗin shi, amma fa da zaran nayi mishi tsiwa, sai nayu kuka da idanuna, dan sai ya min abinda bazan iya ko takawa ba, ba ruwanshi da duka ko zagi, akwai Babbar bulala mesa mace ladab ɗin dole,........


Kafin mubar saudiya muka fara cin karo da wani sabon fitina da hauwa ta tsiro sabon iskanci a makkan fa, duk ranar da yake ɗakinta lfy suke kwqna dazarqn yace aje masalaci zatq fara amai da zazzaɓin karya, idan.kuma ya dawo ɗakina dake ya kama ɗaki me ciki biyu ne a hotel ɗin, sai falo, toh yana shiga ɗakina zata shiga ihu da firgice tans cewa zasu kasheta gasunan....................


*Ku biyo ni domin jin wani fitina ne wannan*
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*

    ```Ummu Rahma kenan kin rufe min baki kuma kin hanani magana sai dai zan faɗa miki gaskiya ni har Ynx yar koyo ce kuma ina farin cikik haka Nagode da cewarki```


*:~•43*
Dake a firgice take zuwa mana sai nace yaje gurinta ya kwana haka muka kwashe kwanaki a makka sannan muka fara shirin komawa london kuɗi mai yawa ya bamu mukayi tsaraba, amma nikam wa mutanen katsina da Yobe nayiwa sayayyana, kuma shi ya biya kuɗin cargo, ana gobe zamu tafi muna zaune a falo ya ɗauko biro da takarda yayi yan rubutu har pepa shida, sannan ya watsa a gabanmu yace.
"Ina son kowaccenku ta ɗauki ɗaya kawai."

                  Mikewa tayi jikinta na rawa ta shiga ruwan ido ts ɗauki wannan ta ajiye karshe dai sai da ta hautsina kome kafin ta ɗauka, ina zuwa na ɗauki ɗaya, cewa yayi.
"Ku buɗe kuga abinda kuka zaɓa"
     Da farin ciki ta buɗe, taga an rubuta ɗakin kasa da manyan harufa, mika masa tayi tana kallon hannuna, ni kuwa katsaye na buɗe nawa na kalleshi nace.
"D'akin sama na samu fa."

         Murmushi yayi sannan yace.
"Shi knn, tunda kowacce ta zaɓi abinda take so ai ba damuwa," janyo systerm ɗinshi yayi ya kunna sai ga hotar gidan akan computer ɗin gallary ya shiga ya fara, nuna mana gidan aikuwa nan Madam tacika tayi fam, inda ta fara magana da cewa.
"Ni wallahi bazan yarda ba akwai munafinci wannan abin asake nima na ɗauki sama."
       Baice mana kome ba ya mike abinshi ya fita daga hotel ɗin, ɗakina na koma, dan nikam banso saman ba Allah ya gani, dan ma na lura saman ma akwai kitchen basai ka sauka kasa ba,......

           Yau kam naga matsuwarshi a gareni dan ana idar da sallae isha sai gashi, tana jin alamun ya dawo, ta fara iskancinta da hauka, dake Uwarta takirashi tayi masa magana a daina barinta ita kaɗai dan jifarta akayi dan a rabata da cikin jikinta kuma a raba aurensu, dan ba kananun aljanu bane aka turo mata, irin masu zama a makabarta nan ne, kaii maganan dai ba daɗi, dake yana ɗauki cikin sai ya biye musu, idan ya shiga gurinta babu abinda bata masa, ga cikin yasata fitinar tsiya Hamdalla nayi tare da godewa Allah sai bida fitinarsa tsuma min jikina yake, idan baya tare dani bana jin kome, sai an kashe arna......

           Allah sarki ina ganin yanda yake rawan jiki amma haka ya koma gefe cike da bakin ciki rashin samu biyar bukatarshi. Haka yafita gurinta ya hucce haushinsa akanta (oho dai can dasu gada zomo yaji kiɗan maharba)

                   Washi gari lau ta mike har muka tafi jidda daga can kuma muka wucce abinmu......

               Bamu isa ba sai washi gari, inda motar da,zatana hidima dashi tazo ta ɗauke mu, ashe gidan a computer ta rage masa kyau, koda muka shiga gidan kowa sai ya shiga santi, da gudu na nufi sama naje naga kome na gidan farine kaman zanyi ihu nashiga nan nafita nan, ina juyawa nayi karo dashi da sauri ya haɗeni da bango hannunmu suka sarkafe da juna, ɗaya hannun kuma na ɗaura a kirjinshi, kallon cikin idanunshu nayi tare da ɗage masa gira ɗaya,

     "Are you happy" yace min.

      Ban iya bashi amsa ba sabida jin bakinshi cikin nawa, wayyo Allah Malamina yana shirin kaini garin da bazan iyakai kaina ba, nima biye masa nayi har muka kai kasa bai fasa ba, yaki wasa da damar da yasamu a kitchen dan gani yake kafin yace zai shige ɗaki kome zai faru, aikuwa abinda yake gudune ta faru dan antayo mana kitchen tayi tana ihu ban taɓa jin ciwon haka ba sai yau, tureshi nayi a kaina, dan da ciwo mijinka yana tsaka da raya sunnah ace wata tashigo kanku, mikewa nayi na rufe jikina na isa bakin kofar da take, cikin ɓacin rai nace.
"Ina dabobi a,duniya ban taɓa haɗuwa da irinki ba mi zaki gani wanda ba'a miki Allah ya isa min"

   Ina faɗan haka bangajeta na fita daga kitchen ɗin ɗagowa yayi da jajjayen idanunshi tun kafin yace wani abu tafita da gudu, zuwa kasa.....

      Ni kuwa ina shiga ɗaki na zuɓe akasa ina kuka me cin rai da bakin ciki abinda hauwa take min, wallahi nidai bazan taɓa mata haka ba, koda kurɓi da zafi nasha,

               Mikewa nayi na shiga ban ɗaki na wanke jikina na fito, gyara ɗakin nayi nacire ɗan farin kyalen da aka rufe kome na gidan, zama nayi tare da naxarin abinda ya dace nayi nan gaba, kawai sai naji gwara nafita harkansu kawai,


            Har zuwa dare ban fito ba sabida narufe ɗakina na kwanta, toh inada abin taɓawa kuma ni gaskiya ba ma'abociyar abinci bane,

                  Jin ana buga kofar ɗakina a karo nahuɗu tare da kiran sunana na mike cikin ɓacin rai na buɗe kofar rike yake da kular abinci ya mika min tare da son ganin fuskana, ni kuwa na sunkuyar da kaina na karɓi abinci, riko hannuna yayi ya shigo ɗakin, ajiye kular yayi yana me matse ni a jikinshi tare da sauke ajiyar zuciya, dukda baice min nayi hakuri ba amma na fahimci haka ta yanda yake daɗa haɗini da jikinshi, kukane ya kwace min tare da tureshi daga jikina ina me juya masa baya, shi kamsa abin na damunshi dan koda yabita yayi mata faɗa da haka kiran Uwarta tayi tazageshi tass, sannan tace matukar wani abu yasami cikin Hauwa toh wallahi sai takai ummanshi kotu dan tasami labarin Ummansa ce ke kitsa min kome, tunda tafi sona akan Yarta, tana gama waya dashi takira umma tayi mata tass, abin ba daɗi fa.......


        Duk yanda yaso ya mantar dani kuma ya jani na sake dashi naki firr, dan dole ya hakura yafita daga ɗakin.........

            Abubuwa sun kwaɓe min fa dan tunda ta lura da cewa bana shiri shikenan ta shige masa, ni kuwa ko kasan bana saukowa sabida gudun ɓacin rai........

                   «»
      Watanmu guda da dawowa ta sake fito da wani iskanci, bayan hanashi shigowa ɗakina, sai ta shiga kitsa masa cewa ita girkina take so, fa sannan bata iya kome sabida lalaci da tafaɗa masa kin kulata yayi sai da ta faɗawa Uwarta, tasameshi da cewa toh matukar bai kula ba cikin zuɓewa zaiyi, sabida mahaifarta a buɗe take tun a maiduguri aka ce kartana aikin wahala, shiru yayi yana mamakin wannan al'amarin sabida yana ɗaure masa kai ta iya kwanciya dashi amma ace girki ya gaggareta babu yanda ya iya da su, dan haka yazo min da maganar, ina karatun alkur'ani ya shigo idan banyi karya ba rabona dashi wata ɗata harda kwanaki, niman guri yayi ya,zauna nakai aya na rufe alkur'anin.

            Kallona yayi cikin mamaki yanda nakara kyau da murjewa, yana cikin kitsi mawa kanshi irin shagalin da yabari ya wucce shi nace masa.
"Ya Mijin me ciki, da fatan kuna lfy"

       "Hm lafiya lau." ya faɗa min ina lura dashi tsaf dan haka na mike na shiga hidimar da babu sabida kar ganinmu haka yace zai kawo min shirme, dakyar ya iya faɗar abinda ta turoshi dashi, ɗagowa nayi ina kallonshi sannan na maida hankalina kan abinda nake, sake mai maitamin yayi yaji ko banji bane,

                  "Naji ka, saidai bazaiyu takwana da miji ni kuma nazama yar aikinta ba, idan haka yayi muku toh idan kuma bai muku ba kuje kucigaba da shiga hakkina Akwai Allah." Ina faɗa masa haka na cigaba da aikina,.

       Koda ya faɗa mata yanda mukayi shiru tayi takira Uwarta ta faɗa mata kome suka ce karshe tasameshi ta faɗa masa bayan ya dawo daga mkrnt...

        Shima yasamini da maganar nace shi knn, haka muka fara rimi rimi, ko sati bamu rufa ba ta fara ihu da faɗuwa tana shureshure karshe dai idan yana ɗakina komawa ɗakinta yake da safe nayi musu girki ta ɓuɗe ciki ta kwashi gara, sannun sannun tafiyarmu yayi nisa inda muka ɗauki sati uku  ranar nafita zuwa gurin wanka nayi nagama dai dai windowta sai naji suna hiran ita da mahaifiyarta a waya ina jin haka kuwa tadazo dubawa ko nayi abinci nayi banxa da ita, ganin bani da niyyar mata magana takira mijinta tafaɗa masa, koda yazo ya tambayeni rashin yin girkina nace bazan girka mata ba bayan lafiyarta lau har tana iya kwana na miji ba.


 

        Cikin ɓacin rai ya hauni da masifa nacika kishin banza ina bakin cikin da cikin jikinata ne idan nayi zuciya nima nadaina gudunshi a shimfiɗi, mana ita da take kyautata masa wato itace nake ganin bakinta wai har dacewa ni yar karama dani har nasan daɗin namiji ina kishin banxa duk a maganarshi babu wanda yayi min ciwo kamar haka, cikin tsiwar da na manta dashi na amsa masa dacewa.
"Eh mana lokacin da kazo ka kwanta da yarinya karama ince har sai da kaji mata ciwo sabida tabaka abinda duk sauran matanka bas...."

       Tauuuu naji saukar mari a fuskana cikin mamaki naɗago fuskana wanda babu ɗigon hawaye akai har cikin kwayar idanuna, cikin tsantsar rashin kunya nace..
"Wallahi na rantse da Allah bazan mata girki taci ba idan kuma na girka taci toh nayi maka alkawarin cikin jikinta ya zuɓe kenan"

          Fisgoni yayi ya haɗani da bango har sai da na bugu sosai, ya shakeni fa, murmushi na takaici nace.
"Yau da ace Asad ne ya aureni da babu wanda ya isa ya sashi dukana balle akai da ys shakeni, wallahi da ina ganinka a matsayinda yafi na mijin da nake aure amma a yau ganinka nake mutum mara kima da daraja, bazan taɓa niman saki ba, amma na haramta maka kaina har abada kaje inda sukafini su shayar da kai farin ciki me ɗorewa, Ubangiji yana madakata kuma shi zai bi min hakkina cikin ruwan sanyi.",

      Gume ne yashiga karyo masa cikintashin hankali yasake ni yafita yabar min ɗakin, zama nayi tare da fashewa da kuka, karkuce asirine fa a'a logona ta gane, tare da amfani da rauninshi nason yara, kuma duk abinda muke akan kunnenta, tana jin yasakeni tayi maza ta sauko, ɗakinta baibi takanta ba yabar gidan baki ɗaya, kiran Uwarta tayi ta fesa mata, can suka sake kintsa wani, yanda zan bar gidan baki ɗaya,

              Koda yafita ummanshiya kira ya faɗa mata kome jin maganar tayi wani banbarakwai, aikuwa ta buɗe masa wuta da masifa da koda wasa yasake dukana Bata yafe masa ba, dan bata ga abinda nayi da,za'a dake ni ba ai gaskiya na faɗa, banda rashin adalci akan gaskiyata zai dake ni, kashe wayar tayi sannan ta kirani duk yanda taso taji abinda zance kawai ce mata nayi babu kome, ranta yayi mugun ɓaci hakuri ta shiga bani, nace mata ba kome ya wucce.


                    A hankali abubuwa suke faruwa tare da wuccewa amma tsakanina da Imamu da matarsa ido sannu wannan bans musu kuma ba karamin damuwa ya shiga ba dan bin mutane yake waisu bani hakuri ni abin dariya yake bani,.......

           Da yaga naki saukowa sai ya rabawa kowa kwanta, tare da zuwa kowacce kayan abincinta a store ɗinta, dake kitchen ɗin, dukda taso ɗago bori shima ya haukace mata dole ta hakura bayan ta faɗawa mahaifiyarta, daga kaina ya fara, kwanaki biyu duk yanda yake rawan jiki na nuna masa bansan wannan batun ba, asalima kuka nasaka masa tare da tuna masa abinda ya faɗa min *Har ina yarinya karama nasan daɗin namiji* shiru yayi ya ɗauke wuta, da wannan maganar muka gama kwanaki biyun mu yana gado ina kasa, dan nasan halina da son jiki idan nasan muna tare toh shige masa zanyi, ni kuma shawaran Umma nake aiki da shi,.

     Itama yaje yayi mata kwanta, babu abinda yayi mata karshe sai naji da safe tana kuka da ihu, tare da kiran Uwarta ta faɗa mata, ina jinsu,ashe jiya ba harkane shine ya masa magana ya bige mata baki......🙊

     *Hmmm vote yayi kasa ba karya

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment