Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana son kai hanunshi jikina amma yana tsoron rigimata yake kar nafarka na, birkice masa,kundubala yayi ya koma gefen siket ɗin ya zuge zip ɗin, zamemin yayi bansan lokacin da na buɗe idanuna ba sai akanshi, mikewa nayi zubur zan gudu, yayi maza ya danne ni, yanda yasamu damar taramin nauyinshi baki ɗaya,

      Aikuwa na buɗe baki da niyyar ihu, yatsarshi ya samin a bakina yana ce min "shhhhh karki tarawa kanki kayan kunya dan ni ba kunya ce dani ba, kiyi shiru na na cire miki abinda naga ya shige jikinki, dan kinsan nayi alkawari ba zan sake kallon kwailar jikinki ba dan babu abinda zanyi da shi, dan ma baki ga amaryata ba hmm Masha Allah tayi daga sama har kasa, sannan daga gaba har baya hmmmm ba acewa kome, kema na shigo ɗaukar kayana ne naga wani katon tsaka ya shige cikin kayanki kina bacci."
    Da dume shi nayi cikin tashin hankali har jikina na rawa, abinda yasa ya katse maganarshi kenan, bai shirya ba, cikin muryan dake nuna alamun kuka zanyi nace.
"Na haɗaka da Allah ka cire min, wallahi ina tsoron tsaka sosai,"

            Janye jikinshi yayi a ranshi yans cewa.
_Nasan za'arina ga rashin kunya ga tsoro kamar farar kura, dama ya same ni nasha lagwada_

       Mikewa yake shirin yi nayi maza na rukunkune shi cikin kuka nace.
"Ayya haka zaka barni dashi baka cire min ba, tsaka fa kace kuma kowa yasan yanda yakewa mutane lahani don Allah ba dan halina ba ka cire min kaji."

       Yanda nayi maganar ba karamin kyau yayi masa, ɓata fuska yayi sosai sannan yace.
" Karki tara min mutane su ɗauka wani abu nake miki, zan taimaka miki abisa sharaɗi, idan kin amince."

      "Naji na amince meye sharaɗin" Na tambaye shi cikin kuka,

            Kauda kai yayi irin zan takura masa ɗin nan, yace.
"Sharaɗina guda ne,"

         Duk na k'agu ya faɗa min langwaɓe kai nayi cikin kuka nace.
"Ina jinka."

          "Toh ba wani abu bane, zan" yayi shiru yana kallon fuskana yanda zan karɓi maganarshi, nace.
"Toh ka faɗa min mana," dan ji nake kaman abu na yawo a jikina tsabar tsoron tsaka da nake,

               Ajiyar zuciya ya sauke irin abun babba ne, sai wani tsume fuska yake kaman an sashi ɗole bayan shi yasa kanshi wannan aikin,
"Toh ba wani abu bane ila zan chajeki kaman yanda ke chaje mutun idan yayi sata domin ina zargin ya shige ta tsakankanin kafafunkine." Saka hannunshi yayi a haɓarshi yana nazarin fuskana ganin naki cewa kome ya mike da niyyar barin ɗakin wuf nayi na rikoshi tare da sauke hawaye masu zafi a raunane nace.
"Shikenan na amince kayi yanda kaga ya dace."

        Farin cikine kal ranshi, cike da kwarin gwiwa yayi ta dube dubenshi kafin ya dangana da jikina hummm Imamu kenan yo bansan mi zance ba dan tsakanina da Allah na amince a cire min, tsaka amma Malam Imamu kuwa ina ya shiga niman tsaka sai ma shagala yayi da, taɓaiya dan duk inda hanunshi ya kai ba sauki, tun abin bai damuna dan ni damuwata ɗaya ce a cire min, tsakar kawai, amma wasu bakin al'amura wanda tunanina da hankalina suka gaza ɗauka ne yasani tsorata da duba min tsakar da ake, na shiga zubda kwalla ba ji ba gani, dan kashedi yayi min da nayi shiru inba haka ba su Ummanshi suka ji nice da jin kunya ba shi ba,

                     Mai niman tsakane ya buge da zuge zip ɗin riga kai naga takaina, rike hannunshi nayi cikin kuka nace.
"Nikan kabarni haka na hakura daniman tsakar sam bana jin daɗin abinda kake min, jikina yana min wani iri don Allah ka barni."

            Janye hannunshi yayi cikin murmushi sannan cikin zolaya yayi min rumfa da kirjn shi bansan lokacin da na fasa masa ihu ba nace.
"Don Allah kabarni haka, bana so karka min kome don Allah, nifa yarinya ce kuma kai kace kayi alkawari bazaka sak...."

          Dif na haɗiye maganar da nake runtsa idanuna nayi, sakamakon jin bakinshi a cikin nawa, hawaye ke bin gefe idanuna sosai Imamu yasamawa kanshi nutsuwa dan ma yaji muryan Ummanshi tana cewa.
"Wai nikam me kake ɗauka ne a cikin ɗakin nan da har yanzun baka fito ba,"

       Kaman bazai magana ba dan muryanshi ta toshe can kasa irin na wanda yake cikin buga da bukatuwar Iyalinshi yace.
"Ummana ina wani aikine a jikin computerna" (😹) dan rainin sense nice computer ma.

       Sake maida kanshi yayi Allah ya bani sa'a na hantsila can kuryan gadon naja bargo na rufe jikina da yake rawa kallona yayi cikin tashin hankali bakin shi shima rawa yake yace.
" Don Allah zo nan kinji A'ieesha zaki taimake ni a cikin halin da nake cikin,kece kawai zaki iya taimakona kinji."

      Kaman zai saka min kuka haka yake maganar ni kuwa girguza masa kai nake, ina sake cusa kaina cikin cinyoyina na sake kuka, dan ko ba kome ai ɗakin Mahaifiyarshi ce, gashi ko shagalin bikin ba'a gama ba, yana niman wani abu daga gareni nifa bazan iya ba wallahi da wani idanu zan kalli Yan uwana da sauran *danginsa* (Buk ɗin Mrs Aliyu)    ganin da gaske ba bashi haɗin kai zanyi ba, take ranshi ya ɓaci ya mike ya saka rigarshi da ya cire yasa kai zai fita sai kuma ya dawo ta inda nake ya fizgoni har sai da na mike tsaye yace.
"Idan abin naki kanwce kijika kisha daɗin abu ina da wata matar bake ɗaya bace balle raina ya ɓaci,ki rike kayanki."

      Ya fita a fusace kuma duk masifar dayake duk su Ummanshi suna jinmu haka ya fita ko kallonsu baiyi ba, ya mike cikin gidanshi part ɗin Hawwa ya isa ya buga da karfi, wanda ya firgitasu a ciki aka ce "waye?"
      Tsaki yayi sannan yace.
"Kifito bana son Iyayi koma waye zaki ganshi."

         Jin muryanshi yasa ta leko tana wani yauki kauda kai yayi sannan yace.
"Wucce muje." Ba musu tabi bayanshi har sider ɗinsa, suna shiga, ciki ya fincikota, cikin zafin nama, idanunshi yayi jajur yace..
"Ina bukartaki ko bazan samu bane."

          Lakwas tayi a jikinshi, yayi ɗaki da ita,(Ynx sai kuce nayi sonkai da yawa ko)

               Dake da haushi a ranshi haɗi da ɓacin rai, dakyar ya bida ita a sannu dan sai da ya hucce haushinsa akanta kaf kafin ya sarara mata, duk abinda yake shi hankalinshi baya kanta A'ieesha ce a cikin ranshi, abinda yakara bata haushi yanda yake yasa ta mike cikin kuka da gajiya ta shiga tattara kayanta zata bar masa ɗakin, buɗe idanunshi yayi ya zuba mata ganin abinda take mikewa yayi cikin sauri ya riko hanunta yace.
"Ina zaki baki ga halin da kike ciki bane."

       Fauce hanunta tayi cikin kuka tace.
"Sai me Ya Imamu, kana tarayya dani amma hankalinka yana kan wata har cikin kunnena kake kiran min sunar wata bayan ta gaza baka abinda kake muradi ni da nayi hka shine sai na sami tukwicin cin fuska wato bani da muhalli a cikin zuciyarka da kwakwalwarka sai ita matar so ai ba wani abu bane tunda bani da daraja a gurinka kaje gurinta, tafini amma kasani kowacce mace tana alfahari da darenta na farko a gidan mijinta, cike da so da kauna amma ni nawa daren cike yake da bakin ciki na godewa Allah da nakawo maka pride ɗina da bansan wani irin matsala zan fuskanta da kai ba, kuma Allah zai saka min abinda kai min domin zalincine zalla gaka ga A'ieeshar zaku gani bazaku taɓa samun farin ciki da junarku ba indai ina raye."

      Juyawa tayi tabar ɗakin tana kuka, tana shiga side ɗinta ɗaya dakin ta shige inda ta zube a gadon tana kukan bakin ciki.

       Sai da tafita ya dafe goshinsa cikin tashin hankali dan sam bai lura da katuɓar da yayi ba jikinshine yayi mugun sanyi mikewa yayi ya saka jallaɓiyarsa ya bi sawunta, a hankali ya tura kofar shashekar kukanta yaji ya bi ɗakin, yasameta a kife, komawa kitchen ɗinta yayi ya ɗauko kettel da wanda ya gani a cikin kwali ba'a cireshi ba, a kitchen ɗin ya wanke sannan ya cika da ruwa ya fito zuwa ɗakin ya jona,

             Gadon yabita ya ɗago cikin sanyi murya yace..
"Kiyi hakuri bazan sake miki haka ba, Allah yayi miki albarka da kyautar da kika bani a cikin wannan daren," sumbar goshinta yayi sannan ya gyara musu kwanciya yana shafa bayanta yayinda yake faɗa mata kalmai masu daɗi, amma kacokan hankalinshi yana gareni duk wannan abinda ya samu, bai manta dani ba, dukda kuwa abinda nayi masa baisa yaji koɗar akaina ba saima, ɗaura laifin akan yarinta da yayi.

    Koda ruwan ya tafasa, janyeta yayi yaje ya juye sannan ya sake zuwa yasaka wani, yana ganin wannan ɗin ya kusan tafasa yajuye yazo ya mikar da ita yace.
"Muje ko na tayaki gyara jikinki,"

            Ɗ'an gafe kafarta tayi idan ta fashe da kuka, ita bazata iya tafiya ba, kallonta yayi a ranshi yace.
_Wannan bata kalle kanta bane amma da bazata ce a ɗauke taba_

      Runtsa ido yayi ya saɓi tuleliya😹 hasasso ni yayi cikin rqnshi sai da ya sake murmushi baisan lokacin da yace." Babydoll"

     Aikuwa sakaryan tasake narkewa ta zata itace babydoll😹
           Wajen wankane akasha daga da ita dan kuka tayi ta masa irinta sakalci da shagwaɓa haka ya lallaɓata har suka fito, yana son yaje ya kwanta amma haka ta kanenaye shi ta hanashi fita, dole ya kwana a ɗakin.......


~~~~
Bayan fitarshi kowa a falon mamakine ya rufesu yanda ya gwada gazawarsa a fili, sabida suna jin duk abinda yake faɗa so loud, jikinsune yayi sanyi duk sirukunayen suka gudu kowa ta koma sidensu suna dariyanshi, Umma khadi ce ta shigo a firgice na ɗago kaina,sannan na sunkuyar na fashe da kuka, matsowa tayi har inda nake taxo da ɗagoni, ganin yanda aka hautsina gadon duk ga kayana A kasa sai lokacin Ummansa ta shigo, ita ta tsince kayan Umma khadi ta riko hannuna ts xaunar dani, sannan ta ɗauko goran ruwa da yake ɗakin ta mika min nabuɗe nasha, a hankali na ɗago kaina sannan na sauke, kafin nace.
"Shin Mamana nayi lefine har haka da zaice...."

           Girgiza kai tayi tare da murmushi sannan tace.
"Ai abinda kikayi kin nuna mana cewa kinfito a gidan da akasan meye kunya kuma haka da kikayi bai rage kome daga son da muke miki ba sai ma kara miki darajan da yayi."

    Mika min doguwar riga tayi wanda Ummanshi ta ciro daga wardrob, sabo kal, tace.
"Saka ki kwanta zamuyi maganinshi kinji ko,dan kina yarinya ba zai takaki muna gani ba."

       Sakawa nayi sannan na mike ya sauka nakoma na kwanta, sai ajiyar zuciya nake saukewa.

     Fita falo sukayi nan ummanshi take ta faɗa zai shigo yasameta,

       ~~~~
Washi gari......
Tun bayan sallar asuba Umma khadi ta maidani inda muka sauka, koda na koma ban iya kome ba sai bacci, su Aunty da suka karya komawa sukayi, suka rasa gyara gidan, abin mamaki suna aikinsu Yan uwan hauwa sai shigowa suke suna, yada musu habaici Husaina sun shigo kawo musu abinci suka sami yan uwan hauwa sai habaici suke jefawa inda suke cewa.
"Ashe matarsu batayo rana ba tunda an gaza nunawa miji soyayya sai gurin wacce aka raina toh kenan acin sisin gwal a banza kenan hmmm mudai tamu takawo budurcinta gidan mijinta..."

     Kai maganggun ba daɗi, ashe ita hauwar ce ta faɗa musu har da kara narke musu jiya ya dagargajeta kamar me sai wai ya faɗa mata ai ni fanko ce dan yaje niman hakkinsa naki sai kuka nake wai ya rufa min asiri shi yayi danasanin biyan sisin gwal da yayi ma da wa ita yabawa.

   Ran husaina da Mariya ne ya ɓaci nan suka shiga faɗa, dakyar aka raba rigima da niman ba'asi Allah sarki ganin haka su Aunty da Goggonina suka mika musu duk wani abinda ake badawa suka ce bazasu kara kwana ba, anyi juyin duniyan nan suka ce A'a dan ran goggo rabi ya ɓaci ainu da Shatima yake bata hakuri  tace.
"Alhaji kayi hakuri ai abin kunya ce musake kwana a gidan Yarmu, Idan mahaifinta ma yaji faɗa zaiyi kawai su kawo mana mota mu tafi."

         Hannuwana na ɗaura akai ina kuka wiwi don Allah karsu tafi amma ina dan har an kawo motar, duk mutane gidan babu wanda yaji zafin abinda sukayi asalima kowa yabamusu yake, yanda akayi musu rashin Mutunci har suka haɗiye toh abarsu sutafi kawai, kamar mahaukaciya haka na koma, Allah sarki yayuna suma kuka suke sosai, kaman me,.

            Ina ganin motar ya tafi kuka na ya tsaya cak ina bin motar ido har ya kulle, hawaye ke zarya a fuskana, ji nayi an ɗagoni a hankali nasaki a jiyar zuciya, sharaf na zuɓe a jikin Umma.

             Da sauri ya karaso zai taɓa, cikin ɓacin rai tace.
"USMAN!!! Karka taɓa min ita kaje inda zaka samu biyan bukatarka, ita kuma kabar min ita, idan ka kuskura katako inda take, Na rantse da Allah zan baka mamaki fiye da kima kowacce amarya tana rabuwa da Yan uwanta da danginta cikin farin ciki, amma A'isha tarasa haka sabida gajen hakurinka jeka inda za'a baka duniya da abinda yake cikinta" tana gama faɗar haka ta mikawa Kaltume ni tace.
"Shiga da ita ciki"

Fatan alkhairi ga,Aunty Binta K Mamman nagode,da,kulawa

Masu jiran Update gashi nan, da fatan bazaku ga laifina ba ainun ba amarya dai kota buzuzu ce sai anyi ɗokinta kuma hauwa ce tasami wannan damar💃💃💃💃💃💃💃💃


Kuyi hkr zuwa ranar talata Insha Allah
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*

*:~•28*
      Not edit⏳
       Ina jin sautin dariyarsu baki ɗaya suna cewa. "wato rank'washin da kuke matane take kewarshi amma anyi ja'ira anan" Jin Inna Talatu kenan duk sai dariya suke,
        Sallama nayiwa Aunty na kashe wayar tare da alkhawarin ɗaura ɗamara yin aiki da abinda ta faɗa min,

          Mikewa nayi na shiga cire kayana sannan na faɗa banɗaki nayi wanka sannan na fito nasaka doguwar rigar bacci, ns gyara kwanciyata jimawa kaɗan bacci yayi gaba dani,

             Wasa-wasa sai da muka kwashe kimanin kwana uku bamu saka Imamu a idanu ba, dan har Umma tana tunanin ko ya koma ne,
     Ranar da muke da akwana huɗu, ina kitchen ɗin Umma dake cikin ɗakin, na tsokayo muryan Umma tana cewa.
"Abubakar har zaku tafi ko, toh Allah ya bada sa'a naji Abba lawan suma gobe zasu wucce abuja dan gidan ba wasu manyan sai yara suka bari a gida ba, Ynzun kuma sai yaushe."

         Banda naji takira sunan Abubakar ba da wallahi zan iya rantsewa Imamu ne sabida ynda muryan mazan gidan baki ɗaya ke masifar kama da juna, dan ko shekarajiya sai da nayi abin kunya inda naji muryan Abba lawan na fito da sauri ina lekenshi, Allah ya taimakeni babu wanda ya ganni ajiyar zuciya nayi sannan na juyo kosan da ya fara soyuwa a matsamin, sannan na zuba na karshe lunch box ɗin Khalil da Ummi naɗauka na juye musu indomie da soyayyar irishi, sannan na raba musu kwan da na soya musu na fito daga kitchen ɗin na ajiye khalil ya kalleni yace.
"Mommy baki saka mana juice ɗin da snack ɗin ba,"
    Yanda ya maida fuskarshi irinta mage yasa nima nayi masa haka yanda yayi nace.
"Babu yau su Yaya khalil zasu makaranta babu juice babu snack, ya kare,"
           Kanwarshi ummi ce ta zaro idanunta tana kallona sai ta kalli Umma da khalil, dariya nayi sannan na durkusa na gaida Ya Abubakar da yake dariyan Ummi dan ta rasa mi zatace sai zare idanun take,

              Komawa kitchen ɗin nayi na haɗa Kunun tsamiyar da nayi na juye a flask, sannan na sauke na Umma wanda na dama mata da garin alkama sabiida tana da ciwon sugar, sannan na kawo falo na jera, da kofe a gaban Ya Abubakar sannan na kawo masa kosai ɗinsa na koma na zubo na yara na ajiye musu nace.
"Maza kusha time na tafiya," snack ɗinsu na kawo nasaka musa sannan na kalle Khalil nace.
"Da fatan ka fahimci home work ɗin da nayi maka, ko"

     Gyaɗa kai yayi sannan nace.
"Umma nayi miki alale ganye alayu, ga kuma kosai toh naga kina kukan ulcer shi yasa ban saka miki kosan da yawa ba, na kawo miki yanzun,"

           Murmushi tayi sannan tace.
"Eh duk zanci toh wannan da kika jera fa nasu waye,"

    "Ai she nakawo miki," nace kaina a sunkuye ina wasa da gyalena,
        Komawa cikin ɗaki na koma nan na gyarashi tas sannan na shiga wanka, sosai nayi fitowa kenan shima ya shigo ɗakin ɗaukar wasu abubuwanshi Allah ya taimaka da hijab a jikina kallon kallo muka tsaya yi da wacce take shigowa ɗakin, sai magana take cikin rashin ɗa'a ban sake bin ta kansu ba na shiga shafa mai, tunda ta ganni hankalinta ya kara tashi a raina nace.
_Ai wannan itace matarsa hmm can musu_
             Ina tsakiya da zancen zuci naji tace
"Wai mi kake nufi dani ne, yau kwana huɗu kenan tunda kafita baka sake juyowa ba dama ku maza haka kuke, bukatarku na biya zaku tsakalla mace kuyi gaba abinku"
       Ta zata zai amsa matane amma yayi kunnen uwar shegu da ita, cikin hasala tace.
"Ina magana ka bawa isa ajiyata."

        "Toh wakike so nabaiwa  ajiyark..." Maganarshi ce ta makale sakamakon zare hijab ɗina da nayi na kunna hand dryer ina busar da gashina, shiru ɗakin yayi dan naga idan nacigaba da jiran subar ɗakin wallahi ba fita zasuyi ba haka kawai zasu hana rayuwata sakat daman ta juya min bayane. Tana fusksrtasa ganin ya tsaya cak yana kallona yasa itama ta juya taga mi yakewa wannan kallon kamar wanda ya tashi cutar makanta, juyawa da tayi idanunta ya sauka akaina, dai dai lokacin da gashina ya bushe shafa masa coconut oil sannan na tattara na kama da karamin bom, pink sannan na buɗe akwatina na ciro wani arabiya gown pink da mayafinshi,hula na ɗauko shima pink ɗin sai wani irin ado da kayi masa da wani flower silver, nasaka sai da nagama shirya tsaf na tuna ban saka dogon wando ba buɗe akwatin nayi na ɗauko bakin wando iya gwiwata nasaka, a gabansu dake Allah yayi ni ba micika son kwalliya ba hoda na murza sai jan baki pink, ina gamawa na ɗauko turaren Madeenatu Munawara,wato alharamin na fasa, sannan nashafa na amshi, nafita nabar musu ɗakin, tsaki taja cikin nuna kishi karara tace.
"Karuwancine ya mutsa daɗin abu musan asalinsu."

     Bai bita kanta ba sabida gabaki ɗaya nai masa kwaf ɗaya, abinda zai ɗauka ya ɗauka sannan ya dawo falon ya zauna a gaban umma kanshi a sunkuye cikin raunanniyar murya yace.
"Kusan kwana uku bana gari, jiya Allah ya nufa na dawo cikin dare umma jibine tafiyarmu, duk hukuncin da kika yanke dai daine,amma umma ina kara baki hakuri da abinda ya faru nice me laifi don Allah kar fushinki yayi yawa akaina, zan iya faɗawa cikin wani garari mara tushe balle makama,"

      Yanda yake maganar yana taɓa min zuciya dama haka Yara suke rarrashin iyayensu idan sunyi laifi, ɗago kaina nayi naga sam abin bai ɗaɗata ya buga da kasa ba,sannan ga hauwa da tayi mana kerere akai sai cika take tana batsewa, lokaci guda sai naga laifin umma nakin saukowa dan har wannan lokacin hakuri yake bata,mikewa nayi tsam daga karyawan da nake zanbar falon ɗagowa tayi cikin kulawa tace.
"A'Isha ina zaki kuma bayan baki ci kome ba, yanzun fa kika sako abinci amma har kin koshi dawo ki zauna idan kuma dan idanu suɓ miki yawane zoki ɗauka ki kai ɗakin kici."

      Girgiza kai nayi cikin kukan da yake shirin suɓuce min nace.
"Na..na..na koshine"

      Kallona duk sukayi cikin mamaki mi akayi min da zanyi kuka yanxun fa nake cikin abinci amma har kuka yazo,

           "Dawo nan ki zauna" tace min kusa da ita,

         Komawa nayi na,zauna sannan na fashe da kuka har jikina narawa, ganin haka hauwa tayi tsaki tabar falon cike da bakin ciki,  roko hannuna tayi cikin lallashi tace.
"Mi yasaki kuka."
         Shi nakalla sannan nace.
"Umma kiyi hakuri yace babu wanda baya kuskure sannan kowani ɗan adam ajizine, umma ke kika ce min nakasance cikin mutane masu yafiya da hakuri dan Allah yana son masu yafiya."

           Ganin yanda ta gimtse fuska yasa jikina ya ɗauki rawa, shareni tayi sannan tacigaba da karyawanta, a ranta kuwa cewa take.
_Wato ita me tausayi zan kwata mata yanci amma ya kashe mata zuciya tausayi shine take kuka zaku ga tsiya nidakune_

       Banza tayi damu har ta koshi sannan ta juya gareni tace.
"Toh kince kar nayi fushi nayi hakuri da abinda yayi miki ko,zanyi hakuri da abinda yayi amma idan gobe ya kuma, mi zan masa."

         Sunkuyar da kaina nayi kasa sannan nace.
"Kiyi hakuri, kince min sama da shekara Hamsin da ɗaya kina hakuri ba'a taɓa jin kanki da kowa ba umma sai wannan lokacin umma indai har wannan lokacin kinyi hakuri ya wucce toh umma ki kara a wannan lokacin akan nada,"

          Ajiyar zuciya tayi sannan tace.
"Na hakura tashi kishiga ciki ki karasa karyawanki."
     Kwashi kayan karyawan nayi na barmusu falon, ina shiga ɗaki ta juya gare shi tace.
"Ka gani ko? Ka ga dai tarin mutuntakarta, wallahi koda wasa ka cireta a cikin rayuwarka hmm bazance maka kayi asaran mace ba amma har abada bazaka taɓa cike gurbinta ba,ba iya nasaba ake nima daga mace ba hatta halaya ana bukata uwa uba kunya, ina jiye maka kar ka, kuskura ka aikata kuskuren da zai saka kuka....."

     Shiru tayi bata sake magana ba har ya karaci zamanshi ya mike sannan tace.
"A cikinsu da wacece zaka tafi?"

      Tasan dani zai tafi amma tana son jin mi zai ce, ko ya sauyane daga yanda yace da farko sunkuyar da kai yayi yana shakkun fitar da abinda zaice gefe guda tsoron karta balbale shi da faɗa yake, a hankali yace.
"Da A'isha zamu tafi."

       Shiru tayi sannan tace.
"Toh waye zai faɗa mata xaku tafi tare, jin ka nice zan kirata na faɗa mata tafiyarku, kaje kasameta idan ta amince laba'asa idan kuma tace bazta b toh kasan babu dole sai ka ɗauki matarka kutafi"

       Shiru yayi wato faɗan da bata masa bane shine ta fake da niman wani rigima shi ɗaya yake aiyana haka a ranshi, mikewa yayi da niyyar shiga ɗakin cikin sauri tace.
"Alaramma karka shige mata ɗaki abinci take ciki karka katse mata uzurinta kaje can matarka tana jiranka kuma koda wasa karka ce zaka faɗawa A'isha bakar magana idan tace ba zata bika ba dan wallahi fushina da tasa na danne zan fitar dashi kuma na rantse da Allah bazai maka daɗi ba, Yawwa gwara kasani babu wasa a cikin maganata.(Kaii jama'a Umma fa tabirkicewa Imamu Zauren Me dambu ku kawo ɗauki kar abin ya ta'azara😹lolx)   jikinshi a sabuƙe ya fita duk abinda ke faruwa ina ji tausayi ya bani dama suma manyan mutane haka Iyayensu suke musu fatafata, kai jama'a abin ba daɗi dai dan umma ta ɗau zafi ove,

         Can

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment