Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan huta nima nagaji, body nobe firewood*
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*


Dominku my Wattpad fans😍 ina muku fatan alkhairi




*:~•44*

Dake Allah ba azalumin sarki bane sai gashi yau sun kaure nidai nawa ido, haka ya gama kwanaki biyu ya dawo ɗakina, tuwo nayi miyar kuka ina zaune ina ci hankalina kwance sai gashi ya hauro sama duk sai ya diririce ko nasan da mutum a gurin na cigaba da cin abincina,motsuwa yayi har inda nake yazo ya zauna, cikin inda inda, ya kai hannunshi cikin filet ɗinda nake cin tuwo ɗagowa nayi cikin tsantsar ɓacin rai, ina yake, nace.
"Har akwai abinda zaka ci daga yarinyar da tasan daɗin namiji? Ina ga me zai hana kaje gurin wacce batasan daɗin namiji ba, zai fi sauki, kuma matukar kacigaba da shige min zan kira Umma na faɗa mata, kome kaje bana son ganinka a rayuwata, dan baka san darajar Y'a mace ba."

Ina gama faɗa masa haka ns mike zuwa kitchen, raina nazafi, kwallace take son zubo min amma na hanata sauka so nake na koyawa kaina juriya,


A kitchen nakarasa cin abinci, ina wanke filet ɗin naji kamshin turarenshi mai suna Chancer, zuwa yayi ya haɗe bayana da kirjinshi, ina jin yanda zuciyarsa ke bugawa,kanshi ya sauko da shi dai dai kunnena yace.
"Kiyi hakuri mana Noor"?
Juyawa nayi a fusace na tureshi nace masa.
"Stop call me noor, Ni Aisha ce, bani bace na dace da haskenka tana kasa ɗauke da juna biyunka donAllah get out" na nuna masa hanya saukar da fuskashi yayi yana kokarin kallon idanuna, matukar nabarshi ya kalle cikin idanuna zai sauya min manufata, akanshi. Ni kuma bana jin haka ynx.

D'ago haɓana yayi cikin wani irin murya yace.
"Noor kalle cikin idanuna, ki faɗa min duk abinda yake bakinki zan jureshi nayau da har abada."

"Eh mana zaka iya jurewa sabida ka ɗibo jarabarka zaka juye min akaina ba, ka maidani injin saduwarka da,zaran ka matsu ga baiwarka nan, wai na tambayeka, tunda kake mu'amala dani, na taɓa nuna maka ina jin daɗinka da har kake da bakin da zaka faɗa min nasan daɗin namiji wow haka yayi ma jeka gurin wacce bata san daɗin ba," na faɗa masa haka nayi wuccewata.

Mamaki nabashi yanda nake iya faɗa masa magana son raina....

Fincikoni yayi na kwace kaina na shige ɗaki ina tafiya ina juya masa mazauni yanda zai cigaba da jin ba daɗi har na shiga na cire kayana sabida zufar da nayi na ɗauro towel, nafito na rufe kitchen ɗina, dan hauwa tana shigo min tana ɗiban abinci, yana zaune a falo nazo na wucce na rufe sannan na koma ɗaki da keyna ai kuwa ganina a haka yasa ya mike zubur yabi bayana, ina kokarin tattara kayana naji anjanyo ni da karfi mun faɗa gado,, cike da ɓacin rai na ɗago na dalla masa harara, sannan na mike na faɗa banɗakina, ina cikin wanka ya shigo yayita nimar maganata ban kulashi ba, har na fito na,zauna na sauya kayana a gabanshi nayi komena kai tsaye, mamaki yanda na fita harkanshi yake.......



«»
A cikin yan watanin nan da bana shiga damuwar kowa, na fahimci har shi kunyata da shakkana yake, balle kuma matarshi, wacce ta rasa yanda zata kuntata min,

Ina zaune a ɗaki dake dankalin turawa nayi da safe madafa da mai da yaji, yazo yasamu ina ci shine yasa hannu ni kuwa na mike nabar masa, dan dama naci nafarko da ban koshi bane na karo, abinka da manja, ya taɓa masa whiter shirt ɗinshi shine dake maiyace yana sauka ta gani shine ta tasoshi a gaba wai su zo abata nata, ban kulasu ba dan ina ɗaki kuma na rufe kitchen ɗin,


Fitowa nayi sanye da wani gajeran wandon iyakarshi cinya da dake jeans dark blue, sai pink body hook, na ɗaure kaina da wani siririn pink ɗin ɗan kwali, babu kwalliya a fuskana, harɗe hannuna nayi a kirjina ina kallonsu, dana ga sun tsaya kallona daga shi har matarshi sai najuya na koma, bayan rigar netne me sharp ɗin hrt, haka ma gaban rigar dan kana iya hango brz da nasaka, fari,

Dukkansu an rasa wanda zai min magana, shi kam gabaki ɗaya ya ɗauke wuta, yana lissafin rabunshi dani ina yace a ranshi, nike aurenki bake kike aurena ba..
.

Ita kam mahaukaciya kamar zatayi hauka sauka tayi taje ɗakinta tashiga niman kayan wanka,...

Tunda na fahimci babu abinda yake tafiya da hankalinshi kaman ya ganni cikin kananun kaya ba karamin tafiya da ruhinshi yake ba, da wannan nake masa gashin ƙuma,



Tun da yafita bai dawo ba sai dare, nafito kenan daga kitchen dake umma ta haɗani da tsumi na sai nasaka a frig duk dare nake, sha, wani lokacin da madara nake sha, wucce ni yayi ya shige kitchen can sai gashi rike da kofi ya mika min share shi nayu na cigaba da shan zumana, zama yayi a kusadani ya kamoni ya matseni sai da ya tabbatar na shanye ɗanye kwai da lipton....

Jefa min wani alawa yayi me tsame tsame na shiga yawo dashi a bakina, shine naji dama dama, tun daga ranar yasani a gaba da bani ɗanyen kwai da lipton, a ɓangare guda gashin da nake masa ya takurashi kiran Umma yayi ya faɗa mata gsky abinda ya faru, faɗa tayi masa sannan ta masa hannunka mai sanda. Inda ta nuna masa toh idan bayi a hankali ba matarshi da uwarta kashe masa aure zasuyi yayi nazarin wasu abubuwan mana, take ya shiga nazari bayan sunyi sallama da Umma, lokaci guda ya faɗa kogin tunani, wato idan ya fahimta gadar zare aka saka masa, ni nasan da haka shine bai sani ba, koda ya shigo dake ranar asabarne kai tsaye sama ya hauro,



Ina kwance a falo yazo ya kwanta kusadani yana tura hannunshi cikin rigana, idanuna a rufe, ina jinshi nayi banza dashi, juyoni yayi muka haɗa ido yace.
"Don girman Ubangiji kiyi hakuri baya ga Ummana sai Zahira sune kawai nake iya basu hakuri Noor kiyi hakuri mana, bazan sake ba, kinji ina cikin begenki da kewarki."

"Hmmm kace jarabar ta motsa kenan sabi sabi, kaga tashi min bana jin daɗin jikina, bakona Yazo min,"

"Eh naji ni jarabbabe ne amma idan a gurinki nake haka a ko ina ni normal mutum ne don Allah kiyi hakuri da kuskurena kinji."


"Bazan iya ba tashi bana son ganinka, a rayuwata."

"Amma Aisha mi yasa baki manta bya ki fuskanci gabanki, ina ganin mu manta kome ma gyara gabanmu"

"Akan me zan manta baya tunda banji daɗinshi ba ai baxan taɓa mantawa dashi ba, kaga malam kafita min daga falo."


"Kiyi hakuri kinsan Allah nason masu hakuri, kuma yana tare dasu, saikiga a dalilin haka Allah ya yafe miki wasu kurakuranki....."
Kaɗa idanuna nayi kafin na amsa masa da cewa.
"Ai Allah da yace yana tare da masu hakuri bai ce acutar dasu ta kowani fuska ba, dan haka kafita bana son kara ganinka"


"Haba Noor kimaida abinda ya faru matsayin kaddara, wacce ta riga fata, babu wanda yake wuccewa kadɗaransa matukar yana raye."

" Datakar Akaramalla ita kaddaran dake bata da dangi iya balle baba shine za'a sakota akan abinda aka aikata da son zuciya, ita kaddaran wato maraininyar wayon mutane ko, dan bata anga bata,da wanda,zai tsaya mata ko yayi kyau"



Shiru yayi sabida ya fuskanci magana nake faɗa masa a fakaice, sunkuyar da kanshi yayi a kan wuyana yana sauke numfashinsa, dai dai kunnena yasa bakinshi yace.
"Ki saurareni mana"

Mikewa nayi sabida jikina yana ɓaciwa, maidani yayi na faɗa kanshi muku zubawa juna ido yace.
"Ki saurareni nace"

"Ɓaxan saurareka ba sabida nima baka saurara min ba, ai ynx bani da wani amfani a gare sabida abinda nake tutiya dashi karabani da shi, toh akan mi zanyi daraja a gurinka"


"Amma Aisha" nayi maza nadakatar dashi da cewa.
"Amma me mi zaka faɗa min mi zaka ce min dukana kayi fa, har da gori mi zaka faɗa min dan kare kanka, sabida ni bani da uwar da zata tsaya min, bani da wanda zai kwatar min yancina, ko ce maka akayi zan kira Ummanka na faɗa mata halin da nake ciki, tarbiyar da aka ɗaurani akai ba'a koya min kai kara ko suka."

"Toh ynx akwai abinda ake miki kenan bayan wanda ya faru."

Murmusawa nayi na mike cikin zafin nama nabar falon tare sai da na isa bakin kofana nace.
"Wannan kuma kuta dama, dan bani da lokacin kai kara ko faɗar korafi,"

"Don Allah ki tsaya mu fahimci matsalarmu tare mana," ya faɗa kaman zai rusa ihu .
Daga masa kafaɗa nayi da cewa. " matsalarka ce ba tawa ba"

Duk ta inda ya ɓulo min toshewa nake, sabida naki bashi damar wanke kanshi, sai bibiyata yake, haka kawai zai shirya mana fita shan iska, ko nida shi ko dukkanmu, dukda haka naki kula al'amarinsu abu ɗaya nayi masa, shine ɓoye tsamarmu a gaban hauwa amma a bayan idanunta toyashi nake son raina, yau ina takfin wanka dake cikin gidan nazo hutawa, toh ya dawo bai ganin ba shine yabiyo sahuna gurin, ashe taga wuccewarsa ni kuma ina cikin ruwan, ina wanka a ciki, na hangoshi sai nayi fuska na cigaba da wanka, kaman ance ɗaga kai sai naga tana biyoshi da sauri na isa bakin inda ya duka yana min magana mika masa hannu nayi nace.
"Taimaka kafito dani,"

Kallon kayan jikina yayi, can kuguna na ɗaura wani kyalle kaman ɗan kwalli, sauke numfashi yayi ya mika min hannu aikuwa nayi baya na fincikoshi muka nutsa cikin ruwan, dai dai ta iso kenan,


Mikewa mukayi muna dariya ni badashi nake ba da ita nake da tabiyoshi, kafin yace zai min wani mgn tuni na sunkuyo da kanshi, na haɗa da bakina, rungume ni yayi cikin mugun kewana ya tallafi fuskana,..........Tsundum mukaji am faɗo cikin ruwan, aikuwa sai da ya famtsama ko ina tana huci ta shiga tsakaninmu, dama aɓinda nake so kenan. Ganin bai ɗauki wani mataki ba nafita nabarsu a gurin bin bayana yayi da ido, cikin kaɗuwa, dan salon yanda nake tafiyar ma abin kallone, fita yayi yabarta a ciki, ya biyo bayana ina cikin ban ɗaki ya shigo, duk yanda yaso yakai hannunshi taɓani naki, fir dan dole ya hakuri har muka fito birkice min ya nime yi aikuwa nima nabirkice masa ina kuka tare da haɗa kayana nace.
"Tsakaninka da Allah na taɓa shiga kanku idan kana wani abu da ita, mi yasa ni take min haka baka taɓa ɗaukar mataki ba ji bi fa, ranar da muka zo gidan nan abinda tayi mana mi kace mata sai nice ka maidani sauna ki kaje Zunnur bana son ganinka."


Janyani yayi muka faɗa gado, cikin idanuna ya zuba nashi muryanshi na rawa yace.
"Humaira sake nanata sunana kinji? Sake faɗar sunan, don Allah karki juya min baya kiyi hakuri dani wallahi zan tsaya miki daga yau bazan sake barin wani ya cutar min dake ba."

Abin tausayi kwalla naga yana bin fuskarshi,bansan lokacin da na mika masa duk wata yardata da amincewata ba, na bashi duk wata kulawa a wannan ranar, tabbas munyi kewar juna, dan kamar bazamu hakura da juna ba, haka muka kasance, sai dai kafin ya shiga ban ɗaki yafito bacci yayi gaba dani, yaso mushiga tare amma naki bayana ya dawo ya kwanta yana kwantar min da gashina da suka hautsine......


Da yaga baccin yaki karewa ne ya ɗaukenk cak sai jina nayi cikin ruwan ɗumi, nan ma wata muguwar kasala ta sauko min, shi yayi min wanka ni kuma nayi saura koda na gama kin fita nayi a cikin abin wanka na gyara kwanciyana, sai bacci gajiya yayi da shiruna ya shigo dariya yayi ya ɗaukeni cak,



Sau gadona anan muka tare, har dare yafita yayo mana abinci, ya kaiwa hauwa kasa nima ya kawo min tawa, dakyar naci, sabida baccin da ya tun karoni, sallar magibri da isha suma dakyar nayi nashafa addu'a na kwanta na,zata mutumin nan zai kyalleni ne amma ina a daren sai da ya hanani sakat, na wani lkc nikam bacci ya dame ni bana fahimtar kome har yayi min wanka yadawo dani sai da asuba yake faɗa min murmushi nayi masa kawai.


Koda muka kwanta danaga take takenshi wani abu yake bukata tuni na ware ɗaya ɗakin, ina fitowa naganta a bakin window ɗayar ɗakin dake kofar yana kusada matakalane, bata tsaya da kyau ba nace mata.
"Malama lafiya"

Sabida tsabar rashin gaskiya ta tafi da baya aikuwa ta daku da maxaunanta sannan ta cigaba da dunkurawa, ihu da salati muka sake nida ita sakamakon jinin da ya ɓalle, tana isa kasa ta fasa ihu da "wayyo Allah na ta kasheni ta turoni daga sama, ta,zubar min da cikina."


Ana kukan targaɗe ga karaya tasamu, Nace ku huta lfy
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*

  *45*

Cikin tashin hankali ya fito da gudu, gani na nasauka da gudu nima nayi kanta yasa ya zuba mana idanu yana kallonmu abinda ya fara zuwa kanshi.........
        *Mi yakawo Hauwa sama dan ga takalminta*

Sakowa yayi tana ihu, cikin ɓacin rai yace.
"Kiyi min shiru mi ya kawoki sama, a wannan lkcn ko bazan sauko bane"

      Ciwon ciki ya hanata magana  kaman zai rufeta da duka, idanunshi sunyi jajjur, kallon yayi cikin ɓacin rai wanda yasa naja da baya ina girgiza masa kai, cike mugun tsoron ina yarfe hannuna kwalla na bin fuskana, biyoni yayi har nadangana da bango, kai hannunshi yayi ya ciro min wani kwaro da ya makale min, sannan ya koma sama ya ɗauko wayarshi, kiran motar asibiti yayi, can sai gasu nan muka kintsata aka ɗauketa, zuwa asibiti tun tana yarfe hannunta da cewa na zubar mata da ciki har bakin ya mutu, nima abaya nasaka muka, bi bayanta har zuwa wannan lkcn yaki min magana sai share kwalla nake ina kallonshi, cikin damuwa kuma yaki bani damar da zan faɗa gaskiya.

     Koda muka isa har an shiga da ita ɗakin wanke ciki, sabida gabaki ɗaya cikin yafita, a ciki kuwa scanner suka mata, inda suka fahimci, cikin ya lalace tun kusan mako biyu sakamakon wasu abubuwan da tasha na karin, ni'ima wato dai a takaice maganin mata, kuma har jinin ya fara sauka kafin wannan faɗuwar, babban abinda ya damesu matsalar da suke hangowa tattare da mahaifar, dan ba lallai bane ya sake rike ɗa koda na awa arba'in da takwas......
Sun kirashi suka masa bayani sanadin lalacewar cikin, godiya yayi musu sannan ya fito ina zaune ne amma sabida tsoro ina ganinshi na mike jikina na rawa, tare da sunkuyar da kaina. Ina shasshekar kuka kasa kasa, yana isowa yasa hannunshi duk biyu ya rungumeni, kaina nakife a kirjinshi a hankali na ɗago ido ina kallonshi tare da girgiza kaina nace.
"Wallahi ban taɓ...."
"Shhhhh ya isa haka muje gida nan ba'a zama a jikin majinyace su suke kome, muje gida kibani abinci yunwa nake ji" ya faɗi haka ne dan ganin yanda hankalina ya tashi, kuma baya son ya sake rasa damarsa da yasamu, jiya shi yasa bai tanka maganar da Hauwa take ba.

Dakyar nake tafiya sabida wani baccin da ya cika min ido, hamma nake akai akai, har muka isa gida, kunun tsamiya nayi tare da dankali da kwai, ni kunun nasha nazuba na hauwa idan zai kai mata, ina shan kunun ina gyangyaɗi yana zuwa ya kalleni, cikin sigar tsokana yace.
"Zo nan, yar kwailar amaryata wacce batasan daɗin miji ba amma jiya naga harda kuka aka min...Don Allah karka bari don Allah kaci gaba wayyo zaka kashe ni da daɗ...."

Toshe masa baki nayi da hannuna ina zare ido, cikin jin kunya cizon hannun yayi yana dariya, yace.
"Allah bakarya nayi miki ba abinda kika faɗane jiya, toh nidai abinda bansani ba dama ina da sweet ne haka"


Ajiye kofin nayi cikin jin haushi tare da zubda kwalla nace.
"Nikam karabu dani ban sani ba, karka dameni. Ai kaima kayi ta surutu dan ban rike abinda kafa bane amma ai har da ihu kayi"


Zaro ido yayi tare da dafe kirji kaman wani karamin yaro, yace.
"Na shiga uku, don Allah karki faɗa kowa yaji nasan baki manta ba"

"Ai wallahi na tuna," nace tare rufe fuskana ina dariya, dariya yayi da son jin abinda ya faɗa, "hmm sharri ko Humairah, inba tsoron ba ki faɗa mana." yace tare da tsareni.


Mikewa nayi sai da na isa, bakin kofa nace.
"Hmm Nana Aishana sarauniyar daɗi, zumata, haka kike dama wayyo nayi kewar wannn....."


Da gudu na kule ɗaki, dariya yayi cike da farin ciki, yanda yaga nasake shima ya sami nutsuwa karyawa yayi sannan ya leko ya samu ina bacci, sumabarta goshi yayi sannan yafito, zuwa asibiti yana shiga ya ajiye basket ɗin sannan ya zuba mata abincin taci, dakyar ta amsa tayi tana kuka, shi kuwa ko tausayinta bai ji ba, mikewa yayi zuwa jin window ɗakin yana leken waje, ya juya mata baya hannunwanshi duk ya zuba a aljuhun wandonshi......


"Wato ke kin ɗauka zan saki Aishane dan ta turoki daga sama ko, sabida kun maidani sauna kuka zauna kuna sani ina zaluntar Yar mutane, idan kece tayiwa haka zaki ji daɗi, toh ai badamuwa abinda kashuka shi zaka girba," isa inda take yayi ya damka mata sakamakon binciketa, yace.
"Ai nasan kina da ilimi ku duba abinda suka rubuta," a hankali ta warware, kin dubawa tayi cikin kuka tace.


"Wallahi karyane turoni tayi, daga sama dan nazo dubaka shine yanxun zaka kareta."

"Abubuwa da dama kinyi min ban ce miki kala ba, kuma nayi shiru ban ɗauki mataki ba ba wai dan bana son ɗaukar wani mataki a'a sai dan maganar da Hajja ta faɗawa Ummana, yanxun kam kina shirin wucce gona da iri, daga yau kar nasake ganinki a sama, kuma idan wani fitina ya kunno kai tsakanina da matata, abakin aurenki, koda wasa kika cewa hajja wani abu akan matata da Uwata shima a bakin aurenki, sannan ki faɗa mata abinda yajanyo zubar cikinki kika kuskura sunan Noor Ya fito, abakin aurenki ke koda kallon banxa kika mata," murmusa mata yayi sannan ya juya yabar ɗakin da asibitin kuka ta fashe da shi,


Shi kam da ya dawo gida yasamu ina bacci , gefena ya kwanta muka cigaba da baccin tare, agogon falona ne ya buga wanda yayi dalilin farkawana naji mutum a bayana juyawa nayi na sake shigewa jikinshi, ina sauke numfashi, zuba masa ido nayi ina kallon fuskarshi, bakinshi na ke kallo,ina dariya nace.
"Mutum ba mace ba amma Allah yayi masa baiwar gashi haka, dubi yanda gashi ya saka ɗan bakin a tsakiya, bakin da yake cinye na mutane"

"Wato gulmana kike ko?"

"Ni? Yaushe? Dawa kuma? Nifa banyi gulmarka ba" na tura masa baki, daman abinda yake nima kenan tuni ya shiga aikin lada, nikam nagaji da halinshi musaman yanxun da nake yawan baccin nan.......


Da dare aka sallamo hauwa naga tashiga hankalinta dana tambayeta ya jiki ta amsa min cikin sakin fuska,


***
Alhmdulillah mun sami nutsuwa a,cikin watanmu na hudu da zuwa london, Imamu na kokarin kamanta adalci a tsakaninmu idan kacire hanya ɗaya da yake hora hauwa nice dai nake fama da bacci da cin abinci musaman tuwo, kaman zan cinye da kwanon nake ji, gashi nayi wani munafikin kiba, daga sama zuwa kasa, nayi fam har bana saka brz dan ciwo kirjin yake min......

Zubawa kayana ido nayi kaman zanyi kuka, kowani riga da skirt na ɗauka zan saka sai zip ɗin rigar yaki rufewa, daga dogayen riguna ɗauko guda zan saka da murna na yana zuwa kirjina ya tsaya kuka na fashe da shi, na ɗauki wayata nakira Umma ina kuka nace.
"Umma kinga kayana fa sunki shigata"

Dariya tayi tace.
"Da alamu yata tayi kiba kenan kai abin yayi min daɗi,Allah ya buɗi Idanu lafiya."

Ina na fahimci maganarta nanna shiga rabtaɓo mata bayani, abinda ke damuna ita kam sai masha Allah take faɗi tana dariya sannan nace mata.
"Umma ina kewar kununki fa"


"Toh ya knn Nana" aikuwa nasakata a gaba da rigima da kuriniya, shigowanshi yasa nayi mata sallama na koma kanshi ina bubuga kafa na fara ina shirin ɓare masa baki yayi maza ya rufe min da hannunshi ihu na kwalla masa tare da bori haɗi da kuka, ruɗewa yayi ganin yanda na baza kaya a kan gadon yace.
"Zuma faɗa min mi ke faruwa."


Kallon kirjina nayi sannan na kalle gadon ina nuna kayan da na fito dasu nace.
"Duba fa, duk kayan sunki shigata wai mi nake ci da nayi kiba haka, kaga fa ban isa saka brz ba haka

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment