Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

        Komawa yayi mazauninshi ya zauna, sannan ya kalleni, har zuwa lokacin ban daina kuka ba girgiza kai yayi sannan yace.
"Nifa sauri nake ina da abinyi."
Buɗe kofar nayi na sako kafana waje, yayinda ya zubawA bayana ido, har zanfita sai na juya nace.
"Allah ya kara buɗe." sannan nafita daga motar bai tsamaci haka daga gareni ba, dan yaga yanda nake kuka ba lallai bane nayi magana ba, amma sai gashi nace masa Allah ya kara buɗe, a kasar makoshinsa yace.
"Amin."

        Rufe kofar naƴi na juya ina tafiya a hankali cikin nutsuwa, har na kule ina bina da ido, dayaga na ɓacewa ganinsa, a hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunshi cikin nutsuwa sam ya gaza fahimtar yanayin da yake ciki, duk da Zahira sun ɗan taɓa love da ita kafin aure, amma baiji kome akanta ba kaman yanda yake ji akaina ba, asalima yana nishaɗantuwa idan yaga ina kuka, tun farko bai taɓa jin tsanata ba, shi rawan kaina ma burgeshi yake, kuma ya nime aurena ne, dan kar mutanen unguwanmu su lalata min suna, sai dai yasan zai fama dani ne, dan ya lura ni zuma ce, sai an bini da wuta........ Da wannan tunanin yabar asibitin,

       Tunda nashiga ciki sai kunyan Innaji ya hanani sakewa, sai raɓe raɓe nake kamar mara gaskiya, kaina a sunkuye Aunty hajra ce ta mike tayiwa Innaji sai da safe, sannan tafike hannuna muka fita, cikin xolaya tace.
"Kanwata irin wannan jimawar haka kuyi hakuri a tare mana, keda malam, karku ajiye mana ɗan tariya."kunya ce tasa na sunkuyar da kaina, har muka fita napep na muka hau zuwa unguwarta, ina son magana amma kunya ya hanani, a falonta muka baje kolinmu mukayi dake mijinta ba mazauni bane, haka yayi min daɗi, kwanciya nayi a falonta ina tuna abinda malam ya faɗa min, a hankali bacci yayi gaba dani.

        Koda Aunty ta kawo abinci tuni baccina yayi nisa.

          .......
  Koda ya koma masaukinshi wanka yayi ya sake kayanshi sannan ya ɗauko wayarshi ya shiga niman Ummanshi kiran na shiga Khalil ya ɗauka tare da sallama yace.
"Abbi yaushe zaka mu tafi."

      Murmushi yayi mai sauti sannan yace.
"Yaron Abbi zan dawo but ba daku xan koma ba, kaji good boy."

        Cikin muryan kuka yaron yace.
"Abbi ina Mamanmu take har yanzun bata dawo ba."

          Tausayin yarone ya hanashi cewa wani abu, sabida kewar mahaifiyarsu da suke dafe goshinsa yayi cikin tashin hankali idanunshi sun kaɗa jajur ga jijiyar goshinsa sun tashi a hankali yakashe wayar, Yana tunanin ina jameesha tashiga tabarsu shida Yaranshi,

            Duk wani fari cikin da yake ciki ji yayi ya kaurace masa,

        .....
      Acan yobe kuwa duk abinda khalil yake faɗa Umma tana jinshi sai da yaga uban ya kashe wayar sai ya koma jikin Umma ya fashe da kuka, tausayin yaron ya cika zuciyarta shafa kan yaron tayi a  hankali tace.
"Da sannun Allah zai muku sakayya abinda tai muku, Ubangiji dai ya nuna mata iyakarta, Yanda duniya ya rufe mata sai ta shayar da ita mamaki, sai ta juya mata baya inda duniya ce."

     Rarrashin yaron tacigaba dayi har ya ɓingire da bacci.

         ......
        Washi gari tare da Aunty mukayi abin karyawa, sannan muka tafi asibiti, Innaji tana zaune a kan kugera Abba na tsaye abakin kofa sai rama da take kwance, idanunta biyu, jin motsin shigowanmu yasa ta juya cikin nutsuwa ta kura min idanun qwalla ke wasan tsere akan fuskarta, cikin sassarfa na isa gareta, abin mamaki juya min baya tayi tare da runtsa idanunta alamun bata son ganina, komawa ɗaya gefen nayi ina kallonta, cikin rawan murya nace.
"Shin nayi deserve abinda kike min ne miye laifina na baki hakuri wallahi bazan tab'a farin ciki ba inda ina ganinki a haka don Allah Karki juya min baya, ban cancanci haka daga gareki ba, don Allah yar uwata."

           Buɗe idanunta tayi  cikin kuka tace..
"Wani irin zuciya kike dashine haka, mai ɓoye laifin da aka miki, taya halayarmu ya samu banbancine haka mi yasa kika yafe min abinda nayi miki, shin ban cancanci hukunci bane daga zuciyarki, da har kika manta da abinda nayi miki." Murmushin karfin hali nayi ina rike hannunta zan buɗi baki nayi magana sai ga Imamu sanye da sky coloure shadda, wanda akayi aikinshi da farin zare,sai hularshi fari haka ma takalminshi farine,tunda ya shigo kamshin turarenshi ya cika min hanci, gaisawa sukayi da mutanen ɗakin, ni kuwa na ɗauke wuta baki ɗaya kaman bana ɗakin.

          Kallon ramla yayi cikin sakim fuska yace.
"Ramla ya jikinki? kema zata koya  miki cutar kuka ko." Murmushi tayi cikin karfin hali tace.
"Da sauki sosai,A'a, ai ba wani abu bane idan nayi dubi da takaitaciyar lokacin da nake dashi, zan koyi wani abu daga gareta ko nima zan rabauta."
     Yanda tayi maganar sai jikin kawo yayi sanyi ban dani dan ban fahimci yarenta ba, karkuyi mamaki aifa ba kome nake fahimta ba gani bahaushiya amma ban gane kome ooo.

        Nasiha ya shiga mata cikin nutsuwa da kuma nuna mata muni laifin da tayi, da kuma yanda aka tanadi, hukuncinsa anan duniya, idan aka maka hukunci Allah zai sassauta maka nashi hukunci, cikin kuka tace.
"Nayi kuskure kuma na amince a sauke hadin zina akaina, dan ba zan iya fuskarta ubangiji da datin dake jikina ba."

        A tsorace na rufe mata baknta jikina na rawa girgiza mata kai nayi ina,zare mata idanu, zare hannuna tayi daga bakinta cikin murmushi tace..
"Son zuciya kike nufin zan sakeyi bayan wanda na aikata a baya, haba ai an wucce wannan level ɗin, Matakin tuba nake karki lalata min zuciyan, amma kuma nasan zaku manta dani ko, ina rokonku don Allah duk wansa ya haifi y'a mace ya maida mata suna na,"

          Hannuwana biyu na ɗaura a kaina na fashe da mugun kuka cikin tashin hankali yaushe ramla tasan da wannan batun.

                Riko hannuna Innaji tayi, cikin rarrashi tace min.
"Jiya bayan tafiyarku ta farka nan ta shiga nimanki keda Asad, toh munce mata ke,zaki zo da safe nan saidai Asad Babanku ya kira mahaifinshi ya nime izin ganinshi da take sonyi shine Babanshi ya bawa Babanku hakuri ajiyan aka wucce da shi abuja za'a fita da shi, waje ganin likita, wai suna isa gida ya yanki jiki ya faɗi.................



         1,708 words ba sauki fa.


             _Fatan Alkhairi gareku Yan grp ɗin Aisha Sada Michika_

      *Godiya tamusaman ga Ahalin Zauren Mai Dambu*

         *Har Abada kuna raina*
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

           🌹🌹👳
             *MATAR MALAM*
                           🌺🌺👳

        *Na:Real Me Dambu ce*

    _Aunty A'i bani da bakin ce miki kome, dan kina biya to kowani fuska nagode sosai_😍

   Kuyi hakuri ina busy ne😘
            *Wattpad:Realmedambuce*
*:~•18*
        Sunkuyar da kaina nayi  inda nacigaba da share kwallata, muryanshi na tsinkayo kaman yana magana cikin ladabi, ina son ɗaga kaina amma ina jin a jikina ni yake kallo, har zuwa wannan lokacin bai daina zubda kwalla ba, musaman idan natuna irin abinda Ramla tayi min.

                 Ban ankara ba kawai sai naji kaman zan zauna very closing dani kamshin turaren, boss ya sannar dani, haka wato turarenshi a hanzarce na ɗago kaina,miqa min wayar yayi cikin kasa da murya yace.
"Ummata tana son magana dake, sannan ki daina wannan kukan dan bazai kareki da kome ba sai ciwon kai,"

       Yana gama faɗin haka yabar falon baki ɗaya sabida lokacin sallah da yayi, kara wayar nayi a kunnena tare da sallama. Sautin murmushinta naji kawai tsigar jikina ya tashi, cikin ina ina na gaisheta.
       Kafin ta amsa min tace min.
"Jekiyi sallah, lokaci yayi inyaso sai na amsa miki gaisuwarki."
  "Toh." kawai nace mata cike da jin kunyarta,

             Nima tashi nayi nafita zuwa ɗakinmu, inda nasamu su Innaji suna kan Ramla zasu kaita asibiti, tare dani aka shiryata, cikin tausayawa na rakasu waje ni kuma nadawo na gabatar da sallar magrib. Tun inasa ran zai dawo ya amshi wayarshi idan Ummansa takira, shiru kake ji daga shi har ita babu wanda ya waiwayeni, dana gaji kuwa na ɗauki wayar nashiga manu inda na fara bincike babu iyaka dukda zuciyata tana hanani bincike haka baisa na hanu ba, kusan babu kome akan wayar da yawucce Apps ɗin alkur'an da azka, tafsirin malaman sunnah, da kuma hadisai sai video na wa'azi da lectures na manyan malamai, haka ma dana shiga cikin audio tafsirinsu Imam masur sokoto, Imam Isah Aliyu Pantami,Imam Ahmad Tijjani yusif guruntu, Malam Gero Argungun, Imam Kabir Gombe, Imam masur Yalwa, haɗi da wani wai Malam Zubairu Madaki, kaiii Amma Imamu yana shan wa'axi, can kuma nace ba dole ba, duk malam da naga tafsirunsu sunsha Madaran Sunnah sun tumbatsa, afage ilimin Addini dana boko, babu abinda yaja hankalina kaman Apps ɗin Hadisai wanda Dr Sani rijiyan lemo yayi gabatar dake apps ɗin na audio ne,   har ina shirin kashe wayar sai naga Apps ɗin Sheik jafar, jikina na rawa na buɗe nashiga, inda naji Tafsiranshi guda bakwai a cikin har da hadisin Ummu zar'i matar abu Zar'i sosai na, xauna ina jin tafsirin kusan Awa uku da wani abu, dan har kusan tara da rabi banyi Isha ba, da sauri na mike naje nayi alola nagabatar da sallar, haɗi da shafa'i da wutir.
        Gashi har lokacin bai dawo ba ga gidanma ba kowa tashi nayi na fita tsakar gida, ina zare idanuna, wani mugun tsorone ya lulluɓe ni, gashi ba wuta sai na rasa nutsuwata, tunanin inda zanjene yazo min, ina cikin raba idanun sai ga nepa sun kawo flashin wal nagani, wanda ya haskani inuwata tayi gefe can ai ganin haka na kwalla ihu, nafita a guje, yayinda shima jin ihuna ya tawo da sauri, sabida na ruɗe bansan akwai mutum a gabana ba, shima bai lura dani ba mukayi tawo mugama, aruɗe na k'amk'ame shi ina sake, ajiyar zuciyata, take duk wani kafan sadarwan jikinshi ya tsaya cak, dakyar yake sarrafa numfashinsa, cikin wani irin yanayi me wuyan fassaruwa, zuciyarsa son halatta masa abinda bai niyya ba, dan tursassashi take da yasaka hannunshi biyu ya rungumeni amma ya gaza haka asalima, kokarin janyeni yake daga jikinshi yayinda nake jin zuciyarsa tana wani irin bugawa mi ban mamaki dan bantaɓa ganin haka, ba a hankali ya xare jikinshi daga nawa ya ɗago kaina, wanda kunya ya hanani buɗe idanuna ina tsoron kar ya min muguwar fahimta, sunkuyar da kaina nayi cikin muryan kuka dan har bakina rawa nace.
"Kayi hakuri an tsoratani ne, a cikin gida, kuma ban lura dakai a gabana ba."

                 Taɓe baki yayi cikin ko inkula yace.
"Idan mutum ya fitgita ko yarazana,ba ihu yake ba addu'ar niman tsari yake daga sharrin shayaɗin, ba irin ihun da kika danna ba, sai kace ba matar aure ba Allah kaɗai yasan Mutanen da suka jiyo muryanki dan haka ki daina Inba haka Azabar Allah xai tabbata akanki anya kin....,"
     *(Aunty A'i kinji wani wayyo kishi a mubayyana)*😂
        Sai kuma yayi shiru bai karasa ba, haushi yabani na raɓa gefenshi zan wucce rike min hannu yayi cikin kasa da murya yace.
"Malama dawo nan ina da zaki."
           Rasa abinda zance masama sai kawai na fashe da kuka, juyoni yayi yana kallon yanda nake kuka kaman  wacce aka aiko min da sakon mutuwa, shi mamaki ma nake bashi, tunda haɗu dani babu ranar da bazai ga ina kuka ba, kaman bishiyar ɓaure, asalima ya lura dani babu abinda nake kauna sama da kuka, jinjina kanshi yayi sannan yace.
"Mrs Kuka indan kingama ki sameni amota sai na kaiki inda su Ummanki suke, daga can saiki cigaba da kuka ko."

         Juyawa nayi, naje na rufe gidan sannan muka wucce asibiti koda narufe naje na shiga motar, tunda ya amsa sallama ko inda nake bai kalla ba. Kuma ba wai dan baya kallona bane a'a kawai babu yanda zaki lura da yana kallona, sabida ta wutsiyar ido yake kallona, yanda bazaka taɓa sanin haka ba, sai kayi dogon sabo dashi.

           Karatun alkur'ani yasaka a cikin motar, kara'a Sheik Jafar, dan dafarko ban fahimci haka ba sai da na ɗauki gidan faifan C.d naga full kur'an na Sheik jafar, mamakine ya cika min fuska ga tambayoyi sun cika min baki, bani da inda zan juyo sai naja bakina nayi shiru. Fahimta ina son karin haske yasa ya shiga min bayani a takaice yanda zan fahimta,

           Har muka isa asibitin hankalina yana kan karatu yayi min daɗi yana parking na juya na ajiye masa wayar sannan nace.
"Kayi hakuri nayi naka shige shige,hmm humm" zuba min tikitattun idanunshi yayi cikin salon ɓacin rai, yace.
"Dana baki wayata nace ki min shige shigene, salon ki ɓata min waya sani ko da kika danna ihunki nan kinbi takanta, hmm indan wani abu yasami wayata sai kin biyani yarinya dan babu rangwame a tsakanina dake."

       "Kutt nice yarinya ma?" nace ni a tunanina a raina na faɗi abun ashe daga zuciyana harshena ya faɗo.

         Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya danna min harara kafin yace.
"Inba Yarinya ba wacece ke, wacce abinda bai kai kuka ba kikewa kuka taya ba zankiraki yarinya ba, kisani tun wuri tsarin gidana na mata biyune idan kika ce zaki zauna da wannan ɗabi'ar wallahi kishiya ta gama dake, har buzunki ni jarumar mace nake nima wacce take iya maida kukanta dariya agaban dunbu makiyanta da masoyanta jajirtacciya wacce babu abinda zai karya mata zuciya, amma kina nan ke kenan cikin kuka wani irin zuciyane dake mai rauni haka, toh kisani ni bazan tsaya miki ba kuma ban miki alkawarin zama dake ɗaya ba, ni mutum nw mai sun jinsin mata biyu ko sama da haka."

    Koda ya gama zancensa wallahi ban fahimci kome ba, dan hankalina baya tare da shi, naji abinda ya faɗa tsaf amma duk da haka bawai sun dameni bane kodan ban gama sanin ciwon kaina bane kaman yanda ake faɗa, domin duk cikakkiyar mace idan taji abinda ya faɗa zata shiga hankalinta Amma bandani Naiha Ibrahim Daura. Dan maganarshi ban fahimta ba,

      Dana gaji da jin maganar sai na sunkuyar da kaina haka ya gama bambamin shi sannan ya fito muka shiga asibitin yana gaba ina baya har ɗakin muka shiga, ina ganin Innaji naje na zuɓe a jikinta yana matsar kwalla sai kace wacce aka min wani abu. Kaɗai kanshi yayi yana nazarin yanda zai rabani da wannan mumnunar ɗaɓi'ar kukan da na ɗaurawa kaina, tunda na gaida Innaji da Babanmu da Ya Ishak, sai Aunty Hajra, na maida kaina cinyan innaji cikin kewarta, tattaunawar Baba da Imamƴ naji, inda Imamu yake cewa.
"Ya jikinata da fatan ta daina sosawa."

      "Eh Alhamdulillah tunda aka shafa mata ruwan Addu'ar bata sake ba saima ciwon da suketa fashewa, wasu kwari nafita a ciki, suma sun mutu." Inji Babanmu kenan.

           "Masha Allah abu yayi kyau, a hankali sauki zai samu." Ya faɗa haka cikin jin daɗi,

           Girgiza kai Baba yayi cikin takaici sannan yace.
"Malam kai malamine kuma alkaline ina rukon Alfarma akan a yankewa Ramla hadin zina da ya hau kanta, haka shine zairage mata nauyin abinda yake kanta Don Allah karki ki inma baxaka iya ba, ka haɗamu da wani alkalin a yanke mata hukumcin."

       A razane na mike cikin tashin hankali shima Imamun halin da yake ciki kenan tunda itatafa da bakinta tayi haka kuma hukunci ya ɗanne kanta,( idan akayi dubi da hadisin manzon Allah wanda wata mata tazo masa da cewa tayi zina kuma ta taɓa aure a lokacin tana da juna biyu, sai manzon Allah yace taje idan tahaihu tadawo. Bayan tahaihu tadawo lokacin jaririn yana tsoma yace taje idan ta yaye ta dawo, tana yaye yaron ta dawo Manzon Allah ya karɓi yaron ya rike sannan yace aje a jefeta, bayan anjefta an dawo sai yaje kan gawanta yana kuka sosai har da shasheka sai abin ya ɗaurewa sahabanshi kai, kuma shi ya sallaci gawanta, bayan andawo sahabai suka rasata yanda zasu tambayeshi, *Karku manta an saukar da Suratu hujurat ne sabida masuwa manzon Allah tambaya marasa ma'ana, sannan ɗa masu kawo maganar da ba gaskiya ba,kuma an tsoratar dasu haka inda Allah maɗaukakkin sarki ya tanadar musu azabarsa akan masu ɗaga muryansu sama da ta annabi,*
            Sai manzon Allah yace musu matar da tazo aka yanke mata hukunci yar aljannace, tayi laifi a madadin ta ɓoye sai tafito da shi har tazo daniman a sauke hakkin dake kanta, bayan tana ɗauke da juna biyu na umarceta da takoma gida inta haihu ta dawo nayi haka ne dan naga zata iya dawowane da ta haihu tadawo, sai nayi dubi da kaunar dake cikin tsakanin ɗa da uwa nace taje sai ta yayeshi ta dawo, sai gashi tasake dawowa, imannta yafi karfin kaunar da takewa  ɗan data haifa imaninta yasa ta manta rayuwar da ɗanta zaiyi bayan mutuwarta ita burinta a sauke hakkin Allah dayake kanta, lokacin da nasaka aje a jefeta a lokacin na yard da imaninta Allah yarda da ita, har angina mata katafaren gidanta  Ci
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳


          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*


*Page:~•20*

"Ya faɗi yana aman jini shine suka kai shi asibiti daga nan aka turasu India, ba son, Naiha ki gane abinda za'ayiwa Ramla gatane, ba dan bamu kaunarta ba, sai dan soyayyar da muke mata kenan. Ki godewa Allah da yasa tafahimci kuskurenta harta amsa laifinta, yanxu abinda zai ja mana lokaci shine mijinta."

      Kuka nake sosai har da shasheka yayinda na kifa kaina a jikin Innaji, faɗa ta rufe ni dashi amma bana jin mi take cewa sabida kuka, zare jikinta tayi ta fita tabar ɗakin ita da Aunty da Babanmu, zuwa yayi ya zauna kusadani, kamshin wani turare naji mai shigen humra tsabar wauta ni danake kuka sai ɗagi kaina nayi cike da mamaki nace masa.
"Dama maza suna sha humrane?"

       Na jefa masa tambaya cikin son sanin abinda, na tambayan ɗin.

     Daga shi har Ramla mamakina ne  ya hanasu magana. Gashi na tsareshi da idanun, murmushin gefen baki yayi sannan yace.
"A'a mi ya haɗa namiji da kayan mata, ai humra takuce ni kuwa sai dai sultan hakeem, ko Ramla."

     Ya jefota cikin maganar. Gyaɗa masa kai tayi, ni kuwa danaji amsan bai min ba sai na mike da niyyar barin ɗakin, ganin haka sai ya janyoni na koma na zauna har muna gogan juna, a tsorace na kalleshi haka kawai sai kunyar haɗa idanun dashi ya kamani noke kaina nayi kasa kamar mara gaskiya, shirune ya ratsa tsakaninmu, jinshi nayi yana magana ni ban zata dani yake ba, dan nafi zaton waya yake, ashe wai dani yake, sai da yace.
"Anya kina jina ma, kuwa"
       Kallonshi nayi sannan nace.
"Hmm mi kace, dan ban zata dani kake ba, na ɗauka waya kake."

         Ramla da take kan gado sai zubda kwalla take,inda a ranta take cewa
_Ina da hannun agogo zai juya da bata faɗa sharrin kawaye ba, da itace da wannan damar,da tayi amfani dashi gurin kyautatawa kanta. Da kuma sauran mutane sai dai kash  son zuciya da kaddaran rayuwarta ya kaita inda batayi zato ba, ya ajiyeta inda bata shirya,_ "Ya Allah" ta furta a hankali,

        Ni kuwa ina nan inata bugawa Imamu buhun shirme, can da ya gaji da ɗirkaniyata kawai ce min yayi.
"Shekarunki nawa?"
        Turo bakina nayi gaba ina kunkuni, inda nake cewa.
"Ina ruwanshi da shekaruna ko dan yaganni ba bukekiya ba, shine xai wani raina min ajawali", cikin hasala nace.
"Goma sha sha bakwai." inda na kasa na tsare fuskana alamun bana son ya kawo min maganar da,zai ɓata min rai, shi kuwa jinjina kai yayi, sannan ya mike, kallon fuskana yayi, cikin mamaki yanda na tsume. Murmushi yayi akaro na biyu sannan yace.
"Toh nikam zan koma yobe, maybe  cikin wannan wk ɗin za'a kawo kaya daga..." Yana faɗin haka ya juya gurin Ramla sannan yayi mata yar nasiha sannan yafita, ina zaune kaman kayan wanki,  ranƙwashi Aunty Zubida ta kafa min wanda yasani mikewa ciKin tashin hankalin da ban shirya masa ba, har idanuna sun kawo ruwa kwalla harara Innaji ta watsa min wanda yasa nafita babu shiri.

         Riƙe habarta tayi cike da mamaki tace.
"Ohhni Yasu, yaushe shatu zatayi hankali yarinya sai kace goyon gauro, sam bata san abinda ya dace ba hmm lallai bawan Allah nan zaisha fama, tunda ya ɗauki Indo aiki yasameshi. Ya Allah ka shirya min Yar bataliyanka nan, wautarta yayi yawa." Dariya duk suka saka suna ce mata innaji zan daina,.

       Ni kuwa da nafita sake ɓata rai nayi inda nashiga harare-harare,ina kumbura baki ina hura hanci. Yana kallona dariya yayi a cikin motarsa har yana kifa kanshi, tambayar kanshi yayi toh wannan fushin duk na meye haka, da na damu kaina da jin haushi, haɗi da rashin jin daɗi,

          Ina isa gurin motar na shiga, garam na rufe motar ta wutsiyar ido ya kalleni, kaman bazai tankani ba, can yace.
"Yaro man kaza, ki gama hucce haushinki akan motata, ni kuma na ɗaukeki bayan an kawoki gidana, na kaiki gurin masu sayan kan mutane su sayi karamin kanki nan, a kuɗi me yawa yanda zan sake katuwar motar da tafi wannan sai nafaɗawa Abbanku da Ummanku ai namun daji sunyi watandar namarki, kinga daga ranar babu labarinki,"

      Kallonshi nayi ina nazarin maganarshi mantawa nayi ina fushi nace.
"Toh yanzun idan suka sayi kaina mi zasuyi dashi toh.?"

         Bayi mamaki da jin abinda na faɗa ba dan ya fahimcini tsaf, yarinta na ɗawainiya dani, shi yasa bai damu ba asalima sai ware min idanunshi yayi cikin rashin damuwa yace.
"Eh baki san mi akiye da kan mutum ba dama ? Idan aka yanke akanshi." gyara zama nayi sosai kafin na,zaro ido nace.
"Ina zan sani, tunda babu wanda yake wannan sana'ar a inda nake,." Jinjina kai yayi inda ya gyara zama sosai yanda zai cigaba da zurmani, rike bakinshi yayi sannan yace.
"Naiha yanzun vaki san mi ake da kan mutum ba, lallai da sauranki ynz ki koma ciki zan tafi yobe, nayi miki alkawarin duk lokacin da muka,sake haɗu zan vaki labarin."  Rau rai nayi da idanuna cikin, jin ba daɗi nace.
"Yanzun don Allah bazaka faɗa min ba,haka zaka bar min zuciya cikin zullumi da son jin labarin."

      Ɗaga kafaɗarshi yayi cikin ko in kula, yace.
"Toh ai nayi miki alkawarin ko,toh nama fasa shi kenan "

          A razane na ɗago kaina cikin takaici nace..
"Daman ba fada min zakayi da ba shine kasaka min rai ko ba damuwa ai kafini sanin muhimmacin alkawari."

          Tada motar yayi sannan yace.
"Naji ban fasa ba, amma kiyi min alkawari ba,zaki sake kuka ba idan kuka kikayi, toh ba zan fada miki ba," murguda bakina nayi cikin jin haushi nace.
"Kabar labarinka mana, inda sai na daina kuka."
          Saka hannunshi yayi cikin aljuhun rigarshi ya ciro kuɗi ya laluɓo hannuna ya,saka minsu. Sannan yace.
"Idan akwai wani abu ki kirani, zan turo miki, akwai yarona a unguwarku."

        Girgiza kaina nayi cikin damuwa nace.
"A'a bazan karɓa

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment