Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

labarin akan Uwace,,,,,,Kunga yanda Mamani take ji da ɗanta amma ramla tashiga tsakanin ɗa da uwa,wannan abun zunubine babba, sabida girman darajar uwa koda mutuwa tazo ɗaukar rayuwar yaro, matukar Uwarsa tana gurin bata iya amma cikin ikon Ubangiji sai a ɗauke hankalinta ta wani gurin daban kafin mutu ta ɗauki ransa, dukda wannan hikima na ubangiji baisa mutane sunn halkanta ba, su burinsu su shiga tsakanin ɗa da uwa, karku manta da hawayen da ya,zuba daga idanun Mamani, kusan ba karamin bala'i bane ga rayuwar ramla, sabida ta zalunceta tarabata da ɗa ɗaya tilo mata, taya idan abinda take takama dashi, zai kareta, Ni ban karya Asirin dan Naiha ba, sabida Mamani nayi haka zama nayi nafahimci abu guda akan labarin,gaba ɗaya mamani bata da inda zata kai kukanta da ya wucce Allah kuma tayi haka,da Yau Asad bashi ɗaya bane yanada kane bazan lalata asirin da wuri ba zan barshi ya cigaba da jin ba dadi a taskon Ramla, amma dole na bar haka,da farkon abokanshi sunyi iyawarsu hakkansu bai cinma ruwa ba sai gashi sun kashe wayoyinsu dan basu santa yanda zasu fahimtar da mamani, idan kuma da nace ankarya asirin da karfin tsiya toh idan wannan koyayyen suk fashe daɓ dole daga shi har mamanin Mutuwa zasuyi, mutuwa kan ai tana kan kowa amna meye amfanin baɗi barai, da akayi hakuri gashi an ribanci abun, shi rayuwa saukine dashi, dalilin da yasa asirin yayi tasiri akan Asad ba kome bane sai yana cikin ɓacin rai, ya nime Naiha, akan tunda saura kwana biyu, su mallaki juna koda sunyi wani abu aiba kome bane, ita kuma taki, da wannan ɓacin ran kome ya same shi, mukaddara ra amince dashi sai akayi rashin sa'a ya mutu kafin bikin mi zata cewa iyayenta da mijin da zata aura idan rabo ya ratsa, sannan idan nacw sai Ramla ta gama ganin irin cigaban da naiha tasamu sannan zata girbi sharrinta ai masu irin halinta bazasu ji ko ɗar ba, idan akwai mai niyyar haka sai ya ɗaura dan maran , dan duk daren daɗewa Allah vazai barka ba, ko a haka nabarta taribanci abinda ta aikata ai ko! ina ganin duk baku fahimci dalilin farun kome ba, shi yasa nayi muku gwari-gwari....._*

_Da fatan kun fahimci bayani na😜_

*Page 17*
Tsoron abinda na aikata yasani komawa bayan Imamu na kifa kaina yayinda na rike rigarshi ta baya, ina shashekae kuka, a hankali Asad ya fita daga ɗakin tabbas so masiface ina jin zafin abinda nayi amma bani da yanda na iya, juyawa imamu yayi ya rikoni ya zaunar dani a bisa gado yarasa ta inda zai fara magana, sai bina yake da ido, ni kuwa kuka nake har da shasheka, asalima bana son ganin kowa a kusadani.

Waje kuwa Asad bai san inda yake jefa kafarshi ba sabida tsananin tashin hankali, da mamani suka haɗu ita tayi saurin riko hannunshi suka koma ciki bai masan waye yarikeshi ba, a ciki kuwa an bazama nimanshi. Hankali tashi, ganinshi tare da mamani likita yayi maza yazo zai tsikara masa alura yace.
"Karka taɓani sai an faɗa min taya akayiwa Naiha aure ba tare da sanin kowa ba."

Birkicewa yayi musu cikin tashin hankali Babanmu yace.
"Aje gida a tattauna, maganar nan dan bata asibiti bace."

Sallamarmu akayi zuwa gida, inda duk muka sauka a gidanmu, a babban falon gidan Babanmu.

Da addu'a aka buɗe taron dan har da Yayuna kaf, suna gidan.
Babanmu yayi gyaran murya cikin nutsuwa ya fara da cewa.
"A ranar da mukaje asibiti naji da kunnena Asad ramla yake so, hankalina ya tashi da nasake ganin halinda Aisha take ciki sai naji zuciyata ta karaya. Fiyye da kima, ban ɓata lokaci ba na nufi gidan Malam Usman, hankalina a tashe nan da yamma yana tare da almajiranshi na nemi keɓawa da shi, mikewa yayi muka shiga falon shi, cikin damuwa nace masa.
" Malam ina cikin tashin hankali, yaron da zai auri Aisha ya faɗi ya suma, koda ya farka yace shi baya son Aisha Y'arta yake so."

Cikin tashin hankali yace.
"Subhananlillah, kwanta da hankalinka Allah shi yafimu sanin dalilin haka."

Kwantar min da hankali yayi.
Cikim karfin hali nabar gidan, washi gari da asuba yace min.
"Alhaji idan bazaka dami ba ina niman auren Aisha,"
Bansan iya adadin godiyar dana masa ba,

Sannan muka rabu. Kaman yanda aka saka auren haka kuwa aka ɗaura, inda ya ɗauko abokanshi harsu huɗu,tare da Alhaji Uballe aka ɗaura auren Aisha ranar da aka saka, a takardan gayyata, ranar bata wucce ba aka ɗaura auren Malam usman da Aisha, akan sadakin, sisin gwal,arba'in.
Kuma karfe sha ɗaya aka ɗaura auren Asad da raml..."

Bai kai karshen maganarsa ba muka ji ihun Ramlan, tashigo gidan. Ihu take haɗi da kururuwa.
Da gudu nafita, tsirara naganta, da sauri naturata, ɗakinmu nasaka key cikin tashin hankali, na ɗauki zani na lulluɓa mata,

Cirewa tayi ta, cigaba da sosassonta, buga kofar ɗakin akayi da sauri ns buɗe Innaji ce takalleni fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Toh mi yasami matar masu kuɗi,"shiga ɗakin tayi tana dariya haɗi da tafa hannunta sannan tacigaba da cewa.
"Ai duk wanda yace ruwan wani bazai tafasa ba,yo ai ko wutar tashi baxata kama, wallahi bana tausaya miki, dan baki ga kome ba."
Tana gama faɗar haka ta juya zata fita riketa nayi cikin tashin hankali nace.
"Don Allah kirufa mana asiri karki juya mata baya a wannan halin da take ciki taimakonmu take bukata ba wai fushi b."

Fauce hannunta tayi cike da mamaki haɗi da al'ajabi tana kallona kafin tace.
"Anya kece kuwa Naiha kina da zuciya kuwa, kina da hankali ma tukun,toh inbaki dashi kiyi dan bazan taimakawa wacce tayi sanadin raba ɗa da uwa ba, ki cigaba lusara mara zuciya."

Tana gama faɗin haka tafita daga ɗakin inda tasami su, Baba suna jiran ba'asinta nan ta faɗa musu abinda Ramla ta aikata, sannan tayi wuccewarta.
Jikin Asad ne yayi sanyi yana kallon mamani, cikin muryan kuka yace.
"Mamani ki yafe min wallahi da hankalina ba zan miki haka, bansan kome ba."
Murmushin karfin hali tayi sannan tace.
"Babu kome Allah ya yafe mana baki ɗayanmu."

Cikin kuka ya mike har bakin kofar ɗakin ya buga Naiha tazo ta buɗe masa, shiga ɗakin yayi yaga yanda Ramla ta koma cikin tashin hankali ya isa gareta, yana kallon yanda jikinta yake wasu irin manya kuraje,suna fesowa a jikinta kukane ya kwace masa yace.
Ramla laifin me nayi miki haka da zafi haka da kika cutar da rayuwata, sannan kika rabani da farin cikina,ba kome nabarki da Allah,"juyawa yayi gareni kaina a sunkuye muryansa na rawa yace min.
"Naso kizama abokiyar rayuwata, a duniya da lahira, nayi fatan samun zuri'a daga gareki, naso gina rayuwata a dake, ashe kana naka Allah yana nashi, kuma nashine gaskiya, Naiha bansan iya adadin kukan da kikayi ba, amma yau da natsinci kaina a cikin tashin hankali da rasa wanda kake so, na fahimci girman halin da kiƙa shiga, amadadin haka ina rokonki da kiyafe min, abinda nayi aikata miki."
Rufe bakina nayi sabida kukan da yake shirin kwace min, miqewa nayi nabar ɗakin, a bakin kofa naci karo da imamu raɓa gefenshi nayi idanuna cike da qwalla. Na wucceshi, ɗakin Innaji na faɗa, itama kuka na sameta tanayi sosai har da ajiyar zuciya, zuwa nayi na zuɓe a jikinta ina kuka itama tana tayani.

A ɗakin kuwa cikin azaba da magagin ciwo ramla take faɗe faɗen abin ta aiƙata takaici yasa yafita ko kallon inda take baiyi ba,zuciyarsa yana masa zafi sosai kai tsaye yabar gidan, inds yasamu su mamani a tsaye mota ya buɗe ya shiga, tare da jingina jikinshi fashewa yayi da kuka mi cin rai so yake ya zauna alone baya bukatar kowa kusadashi.

.....
A falo kuwa kowa hankalinshi a tashe yake, musaman yanda Ramla take faɗe faɗenta, ruwa imamu ya bukata aka bashi a kofi,a hankali ys karanto ayatul shifa yabawa Babanmu yace akaiwa Ramla ido da ido Ya ishaq ya sambaɗe ruwan abinshi cikin ko inkula yace.
"Imam kamanta da batun ramla, nima daman ina fama da wasu al'amura kaman na aljanu, kuma na rasa inda zanje inkai kukana, nagode."

Yana rufe bakinshi Babanmu yace.
"Ishaq fitar min da wanca yarinyar daga gidana bana kaunarta taje nasallamawa duniya ita."

Miqewa yayi da niyyar isar da aikin da aka sanyashi, Imamu ya hanashi zuwa inda yayita rokon Baba da yabarta amma fir yaki, karshe bawa imamu hakuri yayi tare da kawuna yafita yabar gidan, kawuna ma bai xauna ba yabar gidan, ina kwance akan cinyar innaji, Ya ishaq ya shigo cikin kwanciysr hankali yace.
"Auta kije, mijinki yana falon baba,"

K'in motsawa nayi inda nacigaba da *kukana* (Asmeent) ban daina ba, har sai da buga min tsawa na mike Aunty Zubaida ta ɗauko turaren innaji ta shafa min a jiki hijab ɗina sannan ya ishaq yasani agabs har bakin falon, sannan ya juya ni kuma nafi minti biyar a gurin ina nazarin yanda zan shiga falon, dakyar nashiga cikin jikina na rawa,jin yanda nayi sallamarne yasa shi ɗaga kanshi yana kallona, can ya kauda kanshi sannan ya cigaba da latsa wayarshi cikin kwanciyar hankali, niman gurin zama nayi na zauna, kaina a sunkuye. Hannuna nasa nashare hawayen da suke wasan tsere a idanuna......
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

   

🌹🌹👳
    *MATAR MALAM*
                           🌺🌺👳

       *Na:Real Me Dambu ce*

  
         _Kuyi hakuri ba son raina bane nake  yanke labarin a 1 read more da kaɗan ba, hidimar me iyali da fatan kun fahimta_

*Page 16*

*Not Editi*

   Kicibis mugun gamo,fuskar da  ba zan taba mantawa bakenan a rayuwata shi mukayi karo na baya nayi, ina dafe goshina yayinda ya,zuba masa ido nayi cike da mamaki, hmm wani irin hali ya shiga dan take ya dafe goshinsa, ganin haka yasa nayi maza na juya a kiɗime, wanda yaja hankalin. Mutane yayi kaina kafin na ɗaga kafana na dama, ya kwala min kira da "Naihaaaaa"
Cak na tsaya, cikin tashin hankali da ɗimauta ilahirin jikina rawa yake, a guje ya isa inda nake kai hannunshi da niyyar juyani gareshi, kawai sai muka ji ance " Ance karka kuskura ka taɓa min Matata," tashin hankali wanda bashi da rana, ji nayi kafaffuna bazasu iya ɗaukata ba, lokaci guda duk wani haske ya koma min duhu, wanda ko tafin hannuna bana gani, tsakanina da numfashina kukuwa muke, yana kokarin barin gangan jikina ina kokarin cafkoshi, sauƙar mari wanda yayi dai-dai da faɗuwana kasa, sai gashi ana rigaye ɗaukata, wannan marin ba nakowa bane sai na Yar uwata Ramla, tana sauke hannunta Asad yana ɗauketa da mugun mari, yayinda Imamu ya sunkuce ni sai cikin motarshi, ture ramla Asad yayi ya biyo imamu cikin hucce yace.
"My frnd ajiye min matata, kafin nasa a ɗaureka sai igiya yayi saura."

        Da taimakon Nabla imamu yasani a motarsa sannan ya juya yayiwa Asad murmushin gefe baki yace.
"I'm no that u are not drunk, balle na maimaita maka, kuma da simple language nai maka bayani, idan baka fahimta ba, kaje ka duba, kamus na hausa maybe you with understand what I said. "

Yana gama faɗin haka ya shiga motar ya figa a tsiyance, ai shima asad ɗin da mugun gudu ya shiga nashi motar, yabi motar imamu wani irin gudu yake kaman zai banke kowani mota da yake kan hanyar.

Hannu biyu ramla tasaka akanta ta kurma uban ihu, ta shiga cewa.
"Wallahi baki isa ba, idan ma wani asirin kikayi wallahi sai nakarya, shegiya karuwa kawai."

Zaman tayi a kasa daɓas tana  kuka, an lalata mata aikinta, can da taga kukan ba mafita bane da sauri ta mike, ta tari, keke napep ta faɗi sunan unguwarsu, babu ɓata lokaci ya ɗauketa,

     .......
Alhikima clinic imamu ya kaini inda aka karɓeni cikin gaggawa, ina shiga dani ɗakin taimakon gaggawa sai ga Asad ya shigo a rikice, yana tawowa ya danna kanshi zai shiga ɗakin Imamu ya fincikosa waje, aikuwa take suka nime bawa hammata iska, sai da aka shiga tsakaninsu, Imamu ya kafe wai ni matarsa ce, shima Asad ya kafe kai da fata.

      Da nabla taga tashin hankalin yayi yawa shine takira Babanta tafaɗa masa, shi kuma Yakira Abbanmu ya fada masa halin da ake ciki.

Tare suka iso lokaci guda, ganin tsakanin Asad da Imamu ina ƙallon hadarin kaji sai abun ya basu dariya amma suka waske,
   Duk sai aka rasa wanda zaiwa Asad magana, duk sukayi shiru tunda sun sunsan meke faru iyayen Asad suka nima, kafin Abba ya isa ga Asad yace masa.
"Yarona ka manta da auren Yar uwan Aishane da kakeyine ramla, kaga kenan koda babu auren Malam Usman akan Aisha, dole kayi hakuri da ramla tunda itace kaddaranka, itace Allah ya nufa matarka, Aisha ba matarka bace haka Allah ya tsara al'amarinsa."

     Tankar wanda yasha kwaya haka ya dinga rangaji idanunsa a rufe yazo ya zuɓe a jikin Babanmu cikin wani irin murya me kama da fitar numfashi, dan ta shake iyakarta wuya yace.
"Baba karufa min asiri karka tona min, idan ban samu Aisha ba Wallahi rayuwata bata da amfani, mutuwa zanyi don Allah karku min haka."

             Sororo sukayi, malam Manu kuwa ko ajikinshi dan ko kallon inda suke bai bayi ba Naihace dai ba zai saketa ba Yaga Wanda ya isa yashi shi da nake shari'a akan aure shine Yau za'ayi nashi. Kutt sata a gidan ɓarawo rance ne,

         Can da Asad yaga sun kasa magana kuma suna kallon Imamu sai ya juya gurinsa cikin rarrafe ya fashe da kuka kaman karamin yaro, ya haɗa hannusa duk biyu yana son ya roki  imamu amma tsananin kukan da yake, ya hanashi magana, shi kansa Imamu sai da yaji ina da ace Zahira tana raye da ya sadaukar da auren Aisha ga Asad kodan irin son da yake mata, amma ina shima wani shashi na rayuwarsa yana bukatarta.

       Miqar da Asad yayi sannan ya zaunar dashi, cikin sanyi murya yace.
"Asad da wani abu kanima xan baka amma banda Aeesha.,"

     Yanda ya kira sunan yasa Asad zuba masa idanun yana girgiza kai yayi cikin kuka yace.
"Shikenan na rasa kome nakenan."

       Shigowar Mahaifinsa yasa shi mikewa ya isa gareshi, zubewa yayi a jikin Uban babu numfashi.

          *****
        Kamar mahaukaciya haka tafita a cikin nafef ɗin sannan tashiga cikin gidan.
        Da gudu ta nufi ɗakinta, inda ta ajiye k'oyayyenta taje nan tasamesu a fashe wasu irin kwari ke fita daga cikinsu, gurin tulun nan ta duba tasamu ya fashe, ga hawainiyae nan awaje tana feso mata wani irin abu daga bakinta.

            A guje ta juya da niyyar fita taji kaman an rike mata kafarta, ba kome bane ya rike mata kafar sai kwarin cikin k'oyayyen suka yanyameta, suna hudar fatanta, suna shigewa jikinta.

      Ihu take amma babu wanda ya jiyota.

        ****
        A ɓangaren boka kuwa shima wasu irin halittune suka mamayeshi, suna hudar fatarshi suna zukar jininshi, take sai halittun sukara girma, cikin tashin hankali ya mike yafita da gudu suna binshi.

Kafin ya samu kafar gudu tuni jikinshi yayi fari fat, sai shure shure, yake, wata yar karamar ce ta faɗa cikin bakinshi, inda tacigaba da shigewa har cikin cikinsa, take cikin yayi mugun girma, wanda yaja ya fashe tafito waje, yan uwanta suka rufa mata suka cinyeta haka suka dinga cinye junarsu, har suka kare sai ɗaya jal, shima karshe ya fashe.

      *Tun A duniya ake hisabi Allah ka iya mana, karka barmu da iyawarmu, karka barmu da ragamar zuciyarmu dan zata kaimu inda ba mukai ba Amin*👌
          ****
        Fasu na tsaka da wanka taji abu na shigewa gabanta, damam wanke sukarta take a guje ta kai hannunta tashafa, jin wani abu tayi kaman maciji, watsa ruwa tayi a fuskarta da sauri takai idanunta kai, hawainiyar nan ce amma dake bata kai hankalinta sosai ba jin yanda take nutsawa jikinta yasa ta fincikota tare da kwala kara, yanda kasanta yake zafi jini na zuba, kaman anbuɗe famfo,ai kuwa ta fyaɗa abin a jikin bango ɗakin tafita da gudu, tana yarfe hannunta, da gudu abin yasake zuwa ya shige baki ɗaya aikuwa ta faɗi kasa bayan tayi wurgi da zaninta tasa hannunta tana janyo abun shi kuma shigew yayi baki ɗaya, wani razananne ihu tayi wanda yasa mutane gidan suka fito kanta, Yayunta maza komawa ciki sukayi, sakamakon yanda ta wangale sawayenra. Matansune da Mahaifiyarta suka rufeta akayi asibiti da ita.

             Cikin tashin hankali aka karɓesu, yayinda drs suka rufa mata cikin tashin hankali sun rasa ta yanda zasu fara mata,

          Suna tsaye sun dallara mata haske a gabanta sai ta fara. Nishi can tayi wani mugun nishi sai ga Hawainiyar tazama katuwa jajjur, tasha jini ta koshi, sai kallonsu take, suma baya sukayi ganin sun mata kuri da idanun ai kawai ta juya zata koma ciki take wani, Likita yayi shahadar kuɗa ya raka mata wani karfe wnda ya hudata,

    Fasu tayi fari fat, sai kiran mamanta take kiran mamanta sukayi dan sun lura bazata kai labari ba,

   Ƙoda uwar tazo, yafitota tayi har dai dai bakinta nan ta labarta mata abinda tayi, a tsorace uwar ta janye jikinta cikin kallon Allah, ya wadaranki fuskarta cike da tashin hankali ta kalle yar wanda zuwa yanzun babu birbishin tausayinta a ranta tace.
"Wallahi kinji na rantse miki da Allah baxan yafe miki ba kuma hakkin raba ɗa da uwa baki ga kome ba anan duniya kenan kika ga wannan ki jira zuwanki gaban Mahaliccinki, Allah ya isa min ɗaukae cikinki da haihuwarki da nayi."

    Tana gama fadin haka tajuya tabar ɗakin cikin tashin hankali, har bata san inda take jefa sahunta ba wannan masifar da me yayi.

          Tana isowa gurin sauran Yaranta tace.
"Mu koma gida,kawai."

      Zaro idanun sukayi cikin kaɗuwa babban yace.
"Baba fa'izan fa."

      Zuwa musu idanun tayi sannan tayi magan cikin ɓacin rai tace.
"Duk wanda ya ɗauki koda gawartane ban yafe masa ba."
Juya tayi ta bar asibitin cikin zafin rai.

                ****
Wani irin hali Ramla tashiga dan abun sun shige jikinta da gudu tafita tana ihu, tana cire kayan jikinta, tana birgima kamar mahaukaci, yayinda Yara suka rufa mata a baya,



              ****
          Asibiti kuwa nurse da likitane suka rufu akan Asad, Yayinda Abbanshi ya kira Mamani, tana tsaka da azkar, ta ɗauki wayar jin halin da Tilon ɗanta yake ciki yasa ta maza takira drvta tace.
"Maza katsina zamu nufa."

......
A ɓangarena kuwa Alhamdulillah, dan numfashina ya dawo normal sai godiyar ubangiji amma har wannan lokacin ban farka ba

     A ɗakinshi kuwa ba'a jima ba ya farka, koda ya tashi cire drip ɗin hannunshi yayi ya fito ana rike shi, yans fizgewa,

     Kai  Ramla da Baby sun shiga rayuwarmu sai dai muyi faɗan Allah ya yafe mana sannan ya bamu ikon cinye jarabawarmu,
   Kiran sunana yake tsakaninshi da Allah dan ya zauce nafita hankali, kiran da yake min, har ya iso bakin kofar ɗakina duk tareshi dake bai hana shi banke kofar sa nake ba ya taho da gudu ya hau gadon tare da rungume ni,

      Yana me fashewa da kuka, yana k'ank'ameni, fincike shi Imamu yayi cikin ɓacin rai da wani wutar kishi tana azalzalarshi cikin muryan ɓacin rai yace.
"Kafara wace iyarka, karka shiga iyakar ubangiji mana, ai mahaifinta ya faɗa maka da aurena akanta ya kamata kashiga hankalinka inba haka ba za'a jimu, Naiha  mat..."

   Zuciya ce taciyo asad yakaiwa Imamu duka cikin zafin nama ya kauce masa, sannan ya rike hannunsu ya kifeshi da mari,

   Take kokuwa tasake sarkafewa tsakaninsu, duk idanuna biyu mikewa nayi jiri na ɗibana, ga iyayenmu da likitoti sun kasa shiga tsakaninsu sai nice na mike, hankali na isa gurinsu na rike hannun imamu na girgiza masa kai dan ya dunkule z
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

           🌹🌹👳
             *MATAR MALAM*
                           🌺🌺👳

        *Na:Real Me Dambu ce*




      *Wattpad Mai_Dambu*

           _Toh me zance wanda ya wucce kuyi hakuri da samun tsaikon da nake muku kuma ina kara baku hakuri akwai wani uzirin da yasha gabana na ajiye ɗayan buk ɗina sai nagama wannan da fatan xakuyi hakuri da haka_ Nagode...

   

*Page:19*

    A gigice na ɗago kaina ina kallonta, ina sonyin magana bakina ya gaza furta kome asalima ita nake kallon cikin tashin hankali, na marasa mi zance tunda natashi ban taɓa fuskantar haka daga gareta ba,ita dai burinta ta kyautata min ko ya-yane, sunkuyar da kaina nayi ahankali na saki kuka mi cin rai, wanda yasakasu duk jikinsu yayi masifar sanyi. Imamu kuwa tsayawa yana kallon
yanda kwalla ke bin fuskana  cikin, sanyi murya yace.

      "A'a kuyi hakuri kubarta itama ayi mata yanda akewa ko wacce y'a mace itama tayi alfahari da haka, idan aka mata dole ya kamata ta wani gurin a kyautata mata, sannan akwai yarinta zirriyan a tare da ita kuyi hakuri sam ban ɗauki maganarta da wata fa'ida ba asalima shakuwace sila yasa tayi haka." Jikinmu ne yayi sanyi sabida maganar da yayi Babane ya juya ya bashi hakuri, murmushi yayi sannan yayi mana sallama ya fita, wani mugun kallon Innaji tayi min tare da buga min tsawa tace.
"Maza tashi ki rakashi mara kirki kawai." Jikina na rawa nabi bayanshi, da murmushi ta rakani, cikin sanyi murya tace.
"Insha Allah sai kinyi alfahari da auran nan da aka miki, kuruciya ya cika rayuwarki fam, sai yayi hakuri dake sosai."

     Juyawa tayi ta kalle Aunty hajra tace.
"Ya kamata ki tafi fa, lokaci na tafiya kuma idan zaki tafi ki tafi da ita gidanki, Ni zan zauna a nan Ishaq da babanku zasu koma gida." gyaɗa kai Aunty tayi cikin share qwallar dake bibiyar fuskarta.

           Koda nafita na same shi jingine da jikin motarsa, irin kallon da yake bina dashi yasa naji kafafuwana sun harɗe da junansu kaman zan kifa, ɗago kaina nayi, muka haɗa ido sai naga ya cika min ido ga wani uban kwarjinin da yayi min, komawa yayi ya buɗe motar ya shiga mazaunin, cikinane ya murɗa cikin tashin hankali na shiga rarraba idanun *mi yake nufi da nashiga motar, ba shi yace abarni ba toh mi yake nufi da haka.* Katse min zance zucina yayi inda ya sauke gilashin inda nake yace.
"Ranki shi daɗe, gobe zan koma ki shigo muyi abinyi."
             Cikin inda inda na buɗe motar nashiga amma ban rufe murfin ba, wani kallo yayi min cikin murmushi sannan yace.
"Amma da kika bar kofar abuɗe kina gudun kar na miki wani abune, toh kuma ai naga ba wani abu bane a gurinki,tunda ba yau kika fara keɓewa da wasu maz."
Birki yayiwa maganarshi sabida ɗago kan da nayi ina kallonshi, amadadin yaji kunyar abinda ya faɗa sai ya basar, kuma yayi shiru nima sunkuyar da kaina nayi, cikin tashin hankali kokari nake na buɗe kukan da yaci karfina, amma ina na gaza, haka ashe daman duk abinda kayi koda shekara nawane xai sake dawo maka. Takar alkhairine kayi ta wata fuska Allah ya daeo maka dashi ta wani fuska, haka ma sharri, cusa kaina nayi cikin cinyoyina na sake kuka mara sauti, shiru yayi yana sauraron kukan nawa, kuma shi bai hana ba kuma bai masan ta inda zai dakatar dani ba, yasan abinda ya faɗa min ne yasani kuka dan haka sai ya shiga kokarin tada motar ɗago kaina nayi cikin sauri ina kallon inda zai kaini, cikin ko in kula yace.
"Sarkin kuka kenan, gaskiya kika da baiwa ta musaman ace mutum kuka baya damunshi,hmm ga wayar nan na cire layina nasaka miki layin Mtn, akwai kuɗi a ciki,!" shiru yayi cikin son isar da wani sako yace.
"Ban amince ki buɗe wata kafar sadarwa ba,,,,," kasa yayi da murya ya matso kusa dani, yace.
"Idan naga haka raina zai ɓaci matukar haka ya faru."
       

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment