Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Eh nasan da haka, a ynzun haka rayuwata bazata taɓa cika in babu kai ba, koda bana tare da kai, bazan taɓa samun nutsuwa ba, har sai mun kasance a inuwa guda, koda misali kaddara tashigo mana tabbas rayuwarmu zata zame abar tausayine tunda xuciyarmu ɗaya, ruhinmu ɗaya idan baka tare dani gangan jikina ba zaitaɓa moruwa ba,sai kana tare dani,,,, tashi mu zaga garin Dubai."

Na katse maganar nesabida irin kallon da yake min, cike da mamaki har yafito wanka nima na gyara jikina bansaka jan baki ba sai nasaka lips balm, muka fito har wannan lokacin kallona yake yana mamakin yanda nake zaro magana haka, hmm ji shifa ya ma yardani wata yar karamar yarinya.

Haka muka gaza garin dubai da siyayya,karfe huɗu saura muka dawo gida, na gama gaji, watsa ruwa nayi na fito shima ya shiga yayi alola yazo ya gabatar da sallah, nima kwanciya nayi sabida baccin danake ji,


Cikin ikon Allah bacci nayi sosai kaman me sai karfe bakwai da rabi natashi naga yana zaune rike da alkur'anin yana karatu yana kai aya ya ɗago kai yace.
"Ki tashi kici abinci,"

Wanke bakina nayi nazo naci na koshi....


Karfe takwas da wani abu muna airport, lokaci na cikawa muka shiga jirgi


~~~
Ranar monday da misalin sha ɗaya na safe muka isa garin london, bansan haka garin yake da sanyi da sauri na koma jikinshi. Makeleshi nayi shi kuna dariya yayi min muka fito. Juyawa nayi da niyyar komawa ya rike ni tam fuskarsi ɗauke da dariya, yace.
"Da nace kisaka rigar sanyi mi kika ce min, muje kawai ai nan da minti biyar mun isa gida."

Haka muka fito ina rawan sanyi har muka shiga taxi zuwa railway station, daga nan aka kawo min busstop, daga nan da kafa muka isa gida kusan layin uku muka shige, sannan kofar da zai shiga unguwarsu.
Nan motar tasaukemu ya biya kuɗin motar ya ɗauki akwatina, mi kuma naga jakarshi, yana buɗe gidan nashige da mugun sauri, ina niman maboya, dariya na kawai sabida yaga lokaci guda na rikice sabida sanyi, gaba ɗaya na gigice sai rawan sanyi nake hakorana na dukar juna,

Lokaci guda tausayina ya saukar masa, rufe gidan yazo ya zauna kusadani amma ina lokacin nagama birkicewa cire min kaya yayi yasaɓani a kafaɗa dan ina mamakin yanda yake kin kimana ba tare da jin wani nauyina ba, muna shiga ya yaye kyallen da ya lulluɓe gadon dashi, ya kwantar dani shima shiga yayi ciki tare da cire kayanshi body contacing cikin abinda baikai mintuna talatin ba sai gashi ina zufa, zare jikinshi yayi yashiga wanka da alola yaxo ya gabarta da sallar asuba, ni kuwa baccine yayi gaba dani........

*Kuyi hakuri da wannan sabida ina busy yau ɗin nan kusan rabin typing ɗin a unguwa nayi shi..*
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*

       *_Bazan gaji da nuna godiyata a gareku ba Musaman Watpad da Whatsp naga Comments ɗinki mai tafiya da zuciyar mutum dan haka kacokan Buk ɗin Matar Malam sadaukarwane gareku kuma Insha Allah in ba lalura ba zaku cigaba da samun kullum nagode gaku ga ImNai ko Imha💋💋💋_* Inayinku irin na karshen nan👌



*:~30*

       A firgice na sauko daga ɗaukar da yayi har towel ɗina na shirin zamewa, bayanshi na koma still ban daina murza gashin kirjinshi ba lekowa nayi na kashe mata ido ɗaya, tare da ɗaga gira ɗaya, nace.
"Friend wacece wannan? Dan ban taɓa ganinta ba hala bata da lafiyane ta shigo ɗakin mutane babu sallama."

              Hmm yana tsaye ya gaza furta koda harafi ɗaya daga bakinshi, asalima lumshe idanunshi yayi sabida abinda nake masa ba karamin kunna masa wutar fitina nake ba, jin za'a shiga sallah yasa na janye jikna daga gareshi sokuwar tana nan tsaye, ashe nan idanunta yayi kace kace da kwallar bamu sani ba, shashekar kukarta ya dawo dashi daga duniyar tunanin yanda zai min idan na shiga hannunshi, tsuke fuskarsa yayi cikin ɓacin rai yace.
"Baki yi kuka ba,tukun nan ma tunda baki da tunanin da zaki nemi izni kafin kishigo ɗakin mutane, ki godewa Allah da ba mugun gani kikayi ba, kyakyawan gani kikayi da kinyi da nasaniɓ dannowa mutane kai a rayuwarki gaki da kaman mae hankali amma sai baki da shi get out kafin na ballaki."

          Ko ɗar babu a fuskarta sai ma share hawayenta da take ta karaso har gabanshi cikin tsanamin ɓacin rai tace.
"Karya ni, gani nan a gabanka hmm dani kuke zance kaman yanda nayi kuka kuma sai rayuwarku tayi kuka,farin cikin da kuke shirin ginawa sai ta ruguje, Na rantse da Allah sai kazo da kafarka kana rokona, ni kuma...." murmusawa tayi sannanta juya gareni, dariyan takaici tayi sannan tace.
"Ke kam gashi nan kicinye shi ma in zaki iya, zan saki kuka sai nasadaki da kunci, zaki san ni malanta gadon gidanmune nasha a nono, mu zuba Yanxun aka fara shege kafasa."

      D'aga mata kafaɗa nayi da ita tasani ni ko a jikina, fuuuu tabar ɗakin ke kyace guguwa,

         Cikin gaggawa ya shirya yafita daga ɗakin har yakai bakin kofa na biyoshi nace.
"Kayi kokarin ka rarrashi wancar matar dan ta ɗauka da ɗumi,." murmushi yayi tare da shafa fuskana, sannan yace.
"Kark damu zanji da kome."

           Dasauri yafita dan har an fara sallah, nima kayana nasaka na tada sallah dan dama munyi alola a banɗakin.

......
Wato fitan Hauwa daga ɗakin da gudu tafita har tana ture mutane akan hanyarta na shiga ɓangarenmu, ɗakinta tashiga ta faɗa gado sannan ta fashe da kuka, me cikin rai zubur ta mike ta cire wayarta nomber Hajja Yakolo ta shiga nima tana ɗauka ta cigaba da kuka dakay tayi mata bayanin abinda ke faru,

   Daga can uwar tace.
"Ba akwai abinda na baki ba kiyi amfani da shi mana,"  kaman tana ganinta ta girgiza kai tace.
"Ba'a bukatar haka hajja itace kawai nake son na illata bashi ba, ina sonshi sama da kome, hajja bana son su zauna lfy nidai ayi kome kawai, akanta yawwa eh hajja shima ya isa abarta da wannan ma, suje london ɗin, na basu nan da wata biyar suci amarci lafiya."

             Katse kiran tayi tana share hawayenta,...

           Ina zaune na idar da sallah sai gasu khalil sun dawo mikewa nayi na cire musu kayan makaranta nayi musu wanka bayan na umarcesu da suyi sallah abinci na kawo musu, munata hira dasu dan naki yarda infita mu haɗu da umma sabida kunyarta da nake ji. Mun jima dasu a ɗakin kafin suka shirya zuwa islamiyyan dake cikin masalacin gidan,

        Shima ban sake ganinshi ba har dare naji muryanshi, suna sallama da wani ɗan uwanshi, a falon umma, nikam kayana akazo aka kaimin cikin gidanmu sannan matan Yayunshi suka rakani bayan umma taimin nasiha da muzauna lfy da abokiyar zamana, sannan aka fita dani daga ɗakin zuwa wajenmu, koda muka shigo yar shugaban kasa tana tsaye a bakin barandarta, tsaki tayi sannan tace.
"Muna bara muna karuwa gayyan banza arna a idi, dani kike wasa."

            Shareta mukayi muka shige abinmu, inda muka tasa raharmu, kitchen na shiga domin su Aunty sun min bayanin gidan, manyan randunar kulikului da dubulan tawaita tsatsafa, gireba, nakiya da alkaki. Haka na ciko musu Ƙaton bowl da shi, na ajiye musu a gaba ina sosa keyana, cikin jin kunya nace..
"Kuyi hakuri da wannan."

          Dariya suka sannan suka ce, "Ai an raba mana,wanda aka kawo na gara Allah mungode karki ji kome."

         Girgixa kai nayi sannan nace.
"Don Allah ku karɓa indai ba kun raina ba, wancan daban wannan daban,"

       Babu yanda suka iya dole suka amsa, suna godiya sannan suka fita, nima jan kofar nayi na shiga ciki ina rage kayan jikina, sannan na faɗa wanka sabida yanayin zafin da ake a garin, ina fitowa naji motsin kaman an shigo, karan fashewar kayayyakina yasa nafito da sauri, Hauwa ce rike da muciya sai fasa min kayan kallona na babban falo, ina ganinta nayi murmushi na juya abuna, ashe shima ya shigo gidan ina part ɗinshi daga, ɗakinshi wanda window ke cikin falon ya hangota da sauri, ya shigo daidai tana rutse plasma na, babbane,  tv yana zuwa ya rike muciyar, idanunta ya rufe, burinta ta lalata min kaya tunda nafita, yana rikewa ya tsinka mata mari,

           Jin saukar marin ya fito dani, da sauri na isa gurin zai sake marinta na rike hannunshi ina girgiza kaina, cikin sanyi murya nace.
"Kaifa Ubane kuma Wane kai, zaka so ayiwa Yarka ko Kanwarka haka, a matsayinka na Uba da Wa ba girmanka bane taje ai bakome kanta tayiwa bani ba, kaji, kawai kyaleta inyaso sai ka sayo min sabo, tunda matarka ce,"

     Yanda nake maganar ina narke masa a jiki, shi yasa shi surkucewa, kaman wani karamin yaro haka ya koma, aikuwa hankaɗeni tayi da yasaketa, na zube a jikinshi juyawa nayi na sakar mata gwalo, da murmushin rainin hankali dake zuciyarta tana k'una ai ɗaga muciyar tayi zata kwala min ya rike, ya janyeni daga jikinta, waje ya turata, sannan yayiwa kofar key, ihu take zundumawa tana zage zage, tare da Allah ya isa mata cin amanarta da akayi, nidai ban bita kanta ba shima, ciki ya shiga ta falona ya rufe kofarshi dan karta shigo, ina komawa ɗaki naji alamun zubowar bakona, maganina na haɗa duk na sha, lokacin guda, dan in ba haka nayi ba, ni da bacci sai gobe Insha Allah, amma danayi haka zanyi bacci amma da ciwo kaɗan kaɗan.

      A ɓangarenshi kuwa yana gama kitsa kanshi, fitowa yayi ya falonshi ya ɗauki laidojin da ya kawo, ya shigo falona da yaga nan ya bini, ɗakina ya ajiye min ina zaune, ina wayq da innaji, yana ajiyewa ya zauna yana kllon, ledar always tsoron abin yanuna karara akan fuskarshi, sallama  mukayi da innaji na katse kiran ina karanto abinda na gani fuskarshi, dariya nayi nace.
"Ya ka zubawa always idanu haka."

     Ajiye laedar yayi ya janyoni gabanshi yace.
"Kinga zo nan muyi maganar gaskiya, mi kike da wannan abu dan ina ganinshi naji gabana ya faɗi,"

          Kallonshi nayi irin kallon rashin wayon nan nace.
"Ai bakansan mi ake da audugar mata ba?" ɗaga kaina nayi sama ina nazarin me zance masa,  damuwa na hango a kwance a fuskarshi a raina kuwa nace.
*Hmm wannan mutumin yanda yake jinshi nan idan na shiga hannunshi nakaɗe har ganyena, gwara da abin yazo ma kowa ya huta, namiji da gulma bari in lallabashi yaje wnje wanca buleliyar su cinye kansu dan nasan abinda ke haukatata kenan"

       A sararri kuwa nace.
"Masa ai bakona ne yazo, kuma kwana biyar yake, kafin ya tafi, idan kana da damuwa kaje gurin Hauwa ai anfanin mata biyun kenan."

       "Amma bakon nan naki bai kyauta min ba, da yazo a wannan lokacin nida nake shirin amarcewa, sai yazo kuma idan ina tare dake kina kawo min maganar wata mata zan fasa abotar, dan nasan da ita ai."

                Narkewa nayi ajikinshi ina shakar kamshin turarensa, mai daɗi, hannuna na jikinshi ina wasa da gashisa,  ganin ina kara kashe jiki kallona yayi sannan ya mika min laedar naman ya sumbaci goshina yace.
"Ki kwanta ga wannan nakine ina son gobe ki shirya kayanki, na sawa,sai kuma duk abin kike tsamanin zai lalace, kafin nan da wata shida ki fitar dashi, akaiwa Umma, dan ina ganin gobe zamu wucce abuja daga can kuma mu wucce lagos kinji ko."

       Ɗ'aga masa kainayi ina kwance ledar naman sai haɗiyar yawu nake sabida kamshin namar da nake ji, ga kuma ɗaya ledar ice cream ne, ina buɗewa kuwa naga chocolatene ɗago kai nayi cikin marairaicewa nace.
"Zo musha ice cream don Allah."

Girgiza kai yayi alamun a'a, kare masa kallo nayi cikin nutsuwa yana sanye da farar riga da farin wando, sai yar medical glass da ya manna a fuskarshi, ajiyar zuciya na sauke nace kayi kyau ba laifi, kuma duk wa kwanciya kayiwa wannan adon faɗa min gaskiya ko kayiwa yar lukutarkace dan nasan wannan kwalliyar ba tawa bace."


Dariya na bashi jan hancina yayi sannan yace.
"Ai itace yar lukuta,, ke kuma yar firit ko nace kwaila..."

Aikuwa naji haushin abinda ya faɗa min na kuwa tura bakina gaba nace.
"Niba Ƴar kwaila bace, wallahi ko makaho ya shafa yasan na wucce ajin kwaila,na yarda ni yar firitne amma banda kwaila."

Na faɗi haka cike da jin haushi.
"Ai ita wato bata da me rama mata shine zaki ce mata yAar lukuta,"

Mikewa nayi nakai namar frig na ajiye, sannan na ɗauki ice cream ɗina na shiga sha, abuna magana yake amma naki ɗaga kai na kalleshi karshe haka yabar dakin, bamuyi rabuwar daɗi ba.

Aikuwa da yaje gurin Yar lukutarshin sun wau sama sunka faɗo kasa, inda taki bashi haɗin kai, shi kuwa ya cire rigar malanta yayi mata tass kafin kuma ta sauko tabada kai bori ya hau.😹 no class lolz



****
A cikin kwanaki biyu anyi rigima da hauwa ba adadi, dan ma yayi mata barazan nan zai saketa shi yasa ta nutsu sallama mukayi da mutanen gidan inda muka nufi abuja,


Da asuba muka bar abuja zuwa lagos, bayan sallar la'asar muka bar kasarmu ta gado, inda muka lula duniyar Turawa tafiyar da na haɗu da kalubale masu daɗi da marasa daɗi, tafiyar da ya zamemin mara amfani, tafiyar da nayi danasanin zuwanshi, tun daga wannan tafiyar nazata hawayena zasu daina zuba ashe shine mafarin zubda hawayena, mafarin mara karshe, k'addara tana biye damu akoda yaushe, tuna abinda ya wucce yana sosa rai, amma idan kayi dubi da girman jarabawarka sai ka godewa Allah, Ni A'ishatu naga rayuwa daga kankatar shekaru zuwa mafi girman shekari, ku biyo dan jiɓ wata wainar za'a toya a birtaniya..........💋
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*


*Kuyi hakuri ciwon kai ya hanani typing*
*:~•32* No Edit✂
Bacci nayi sosai sabida ya kunna min rum heater, ban farka ba sai kusan uku dake nasan bani da tsarki, bargon naja na dukunkune ina rawan sanyi nake lokaci guda nayi zuwana baida amfani, kuka nasake sabida kowa yasan irin sanyi da akayi har da kankara, labulen window ɗinmu guda ukune, kuma masu kauri asalima ɗakin akwai inda ake hura wuta dan yayi ɗumi, amma haka bai hanani jin sanyin ba ga kuma nauran ɗumams ɗakin.

           Shi kuwa yana idar da sallah yayi addu'o'inshi da yasa ba yafita, zama nayi ina kallon wutar da take ci a ɗakin bakin wutar na koma na zauna hawaye masu zafi na sauko min, jikin motsin ana bude kofa yasa na juya ina kallon kofar rike yake da manyan jakar takardu da kuma, wasu takardu ganin yanda nake zubda kwalla yasa, yayi saurin zuwa gareni, amma abin takaicin baiji magana mai daɗi ba daga gareni abinda ya fito bakina shi yasa yayi turuss dan cewa nayi.
"Daman ka kawoni nan ne dan ka kasheni, ai da kafaɗa min baka sona da bazan damu ba da kawo ni cikin kabarina da kayi, Allah sai ya saka min kuma wallahi ka maidani inda ka ɗauko ni dan matuƙar na kara kwanaki mutuwa zanyi ba zan iya zama a nan ba,"

            Sake kayan hannunshi yayi cike da mamaki ya karaso inda nake cikin fargaba ya durkusa gabana, rike hannuna yayi cikin sanyi murya yace.
"Nana karki ɓata mana farin cikinmu mana, kiyi hakuri sanyin na ɗan lokacine,zaki daina ji, kiyi hakuri ba,zanso wani abu ya sameki ba."

       Nasan sarai maganata tayi masa zafi amma sabida sonda yake min yasa ya shanye maganata, lallaɓani yake kokarin yi amma wallahi atafur naki yarda saima sashi da nayi a gaba da fitina ranar yaga tashin hankali kaman yayi kuka,

              Ga wani mugun zazzaɓin da ya sani agaba abin ba daɗi fa, dalilin zazzaɓin sai da nakwanta asibiti, har na kwana goma sha ɗaya aka sallame ni, muna dawowa wata sabu inji yan caca, ba halin nayi fitsari, idan kuma zanyi sai dai ɗ'iga kafin na gama gabana kaman an sanya min barkono, tun ban fahimci matsalar ba, har dai naje ban ɗakin na duba abinda idanuna ya gane min baxan iya cewa ba amma ranar nayi kuka kaman zan cire idanuna, dake kwanakin da nayi a asibiti mun shirya da Ya Imamu, tunda yaga na ware yashiga rawan kafa akaina, da alamun yana bukatar ya kasance dani, duk sai naji na tsani kaina na rasa inda zan kaina, kuma bazan iya faɗa masa halin da nake ciki ba,

      Kule kaina nayi nabar key a jikin kofar, koda ya dawo ya buga naki na buɗe ga lokacin fitsari yasani a gaba ina ta murkusosa a ban ɗaki, har lokacin bai gama zuba ba, sai nishi nake kozai fita ga uban zafin da nake ji.

        Bugun duniyar nan yayi naki buɗewa ɗakinshi ya koma ya ɗauko key yazo zai ɓuɗe yaji da key a jiki dole ya hakura amma ranshi ya ɓaci ainun tattarani yayi ya watsar dan a tunanin shu salon raine nake ji, dan naga ya damu dani....

     Wasa wasa muka kwashi sati kusan biyu har mun shiga na uku, wanda idan aka haɗa da kwanaki goma sha ɗaya da nayi a asibiti, wata guda kenan aka nima, a ɓangareshi kuwa yana kokarin ya ajiye min kuɗin kashewa ko zanyi odar abinci ko wani abu da ban ga kuma abincin da yake zuwa dashu dukda nima ina girkawa yana zuwa ya samu na ajiye masa abincin....

        Haka rayuwarmu a london ya kasance karshe da yagaji da halina sai ya daina dawowa da wuri tunda ba ganina yake ba sai ya tsiri wani lesson wa ɗalibai a makaranta har zuwa dare sannan ya dawo, ni kuwa na lalace na fita hayacina naki faɗawa kowa matsalata, kullum cikin kuka nake, ita kanta ibadata tana cikin kila wa kala, tunda ban taɓa nutsuwa nayita dai dai ba, kai Anya nayiwa kaina adalci kuwa daga salla sai salla bana ko azkar babu kome, can wani shashi na zuciyata yace min.
_Meye a ciki ai ba kanki farau ba, lokacine idan kika kara mallakar hankalinki zaki daina duk wannaɓ abu ai da yaranta a tare dake_ Da wannan huɗubar zuciyata na zauna hankalina wai a kwance nankuwa nafi kowa damuwa.....

              ♡
     *HYDARABAD INDIA*
     Kimanin wata biyu zuwa uku kenan da suka baro gida zuwa kasar hindu, amma a wannan karon zasu iya cewa Alhamdulillah.

    Dan da alamu kulawar Dr Vasudra yayi matukar tasiri da taimakon ubangiji dukda bai farka ba amma akwai alamomin nasara, inda zuciyarsa take bugawa a hankali, kuma yanda ake bukata, yana kwance da da shuɗiyar riga da wando na majinyata, haɗi da hula, hawayeneke bin gefe idanunshi, shigowar Dr vasu ta zauna a kujeran dake kusada gadon shi, tana kallon fuskarshi, a hankali ta matsa dai dai kunnenshi tace.
"Asad!!! Wata rayuwar tana jiranka karka karaya da saranka da rayuwa, duniya da faɗi take, mahaofiyarka da Mahaifinka suna jiranka, kuma suna ɗaura saransu akanka, karka juya musu farin cikinsu zuwa bakin ciki mana, tashi kasake wata rayuwar tayu wata dama ce kasamu kuma da fatan zakayi aiki da shi, tashi karka maida musu murmushinsu zuwa zibda kwalla tashi karka maidawa iyayenka dariyarsu zuwa kukansu suna bukatarka fiye da kome tashi ka nunawa duniya babu soyayyar da,zata kasaraka wake up Wake up Asad.."

         Jan numfashinsa yayi tare da buɗe manyan idanunshi kafin yayi saurin rufesu, sabida baya ganin kome dishi dishi yake ganinsu, "Thank You  God" tace cikin farin ciki, farin cikin tafita indasu Mamani suke ta rike hannunsu tace.
"Madam Bukar kicigaba da addu'a da alamun yaronki ya kusan dawowa hayacinsa yanzun aikin nakine, kiyi kokarin ki dinga faɗa masa magangganu masu daɗi, zai dawo normal very soon amma karki ce nayi miki shishigi meya kawo masa wannan matsalar"

  

       "Alhamdulillah Allah nagode maka da wannan ni'imar da kaimin."mamani faɗa cikin kukan farin ciki.

         Kallon dr tayi sannan ta share kwallar da ta zubo mata, sannan ta shiga faɗa mata abubuwan da suka faro har zuwa yanzun da yake kwance.

    Ajiyar zuciya dr ta sauke sannan tace.
"Allah ya bashi lafiya" a sanyayye tabar guri ita kuma mamani ta shiga ɗakin inda dr vasu ta zauna nan itama ta zauna, ta riko hannunshi tana matsawa a hankali ta fara magana cikin  sanyi murya tace.
"Bazan hanaka damuwa ba, domin nima na taɓa fuskarta kamancecceniyar matsalarka, amma idan ka barwa Allah al'amarinshi zai sake baka sama da abinda karasa abaya, tuna wasu abubuwan yakansa mutum gane kuskuren da ya aikata, sannan ya gyara ba wai ya nokewa k'addaranshi ba, domin ita tankar rigace tun daga ranar da aka haifeka take biye da kaihar ranar da,zaka koma ga mahaliccinka, tashi kayi kokuwa da rayuwa karka bari ita rayuwar tayi kokawa da kai, kashe matsalarka kafin ita ta kasheka,tashi kayi amfani da damarka kafin damar ta suɓuce maka, dan ita sau ɗaya take zuwa ga ɗan adam idan kaga kasake samun wata damar Allah yana kaunarka cikin bayinshi shi yasa ya sake baka damar Asad ita kanta rayuwar bata yuwa sai da fafatawa, dole sai katashi domin ayi wannan fafatawr da kai, shin damar zaka samu kome ne, da sauki waya faɗa maka kome da sauki ake samunshi toh sai anyi gwagwarmayya kafin ake cinma nasara, ko ita kanta numfashin da kake zukarta sai kayi kaman kanayi kafin ka,zuketa cikin sallama ka godewa Allah da ya ara maka wata damar da ba daukeka yayi ba gaba ɗaya, shin kana kalubalantar k'addaranka ce,, jeka cikin suratu Ankabu, ayar farko, inda  Ubangiji ya saukar da ayar da cewa (shin kuna tsamanin bazamu jarrabeku bane....) tsamanika Allah bai san miya shirya bane, yafika sanin kome kuma ya rabaka da A'ishane dan yaga karfin Imaninka tashi ka gode masa da ni'imar da yayi maka, kaji yarona." sai ta fashe da kuka ta marasa sa da wani kalma zata masa magana dan yasa tana tare dashi.

        Motsi ya fara wanda janyo amsakuwar na'urorin da suke sakale jikinshi, jijjiga jikinshi yake, Amun marin da Naiha tayi masa tare da kalaman da tayi masa suka shiga kao kawo a cikin kwakwalwarshi,, inda take ce masa.
"Kafita A rayuwata kabarni nayi farin ciki da abinda Allah ya bani karka bana sonka...!!!"

              Mikewa ya shiga yi yana wasu sumbatu, da cewa "Karki min haka bansan me ya faru dani ba karki tafi ki barni Don Allah Naiha."

      Shigowr mamani da dr da kuma wasu nurse suka shiga ririkeshi, yana fusgewa dakyar aka tsikara masa allura a gefen hannunshi na dama, tun yana kokowar har ya kome jagwa ya zuɓe a gadon

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment