Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba innaji faɗa zata min, tace na rokeka don Allah kabarshi." Sosai tsarin gidanmu ya burgeshi zare medical glass ɗinsa yayi cikin sakin fuska yace..
"Ai yanzun ke ɗin nauyina ce, babu wanda zan ɗaurawa nauyina, dan haka amsa, ba'a maida hannun kyauta baya."

       Babu yanda na iya dole na amsa sannan nayi masa godiya da Allah ya kiyayye hanya,, sannan nafita a motar sai da ya tafi sannan nima nabar gurin, cike da son jin mi akeyi da kan mutane idan ancire. Jan jikina nayi na shige cikin asibitin, cike da tunani marasa ma'ana da tushiya har na isa ɗakin, inda na samesu jun jun, sunayi shiru ina shiga na mikawa Innaji kuɗin sannan nima na koma gefe, kallona tayi amma dake a tsorace nake nayi maza na mata bayanin yanda mukayi dashi ban ɓoye mata kome ba, ganin maganar yaki karewane yasa ta make min bakina, cikin fada tace.
"Toh sannu uwar magana, wa ya faɗa miki ana faɗan kome ne, ana barin wasu abubuwan a ciki dan, samawa mijinki daraja a gaban mutane, ba dan kome ba." Sosai taji haushina, ni kuwa abinda ke damuna yafi karfin faɗan sa tayi min, toh waye zai faɗa min mi akeyi da kan mutane..........😂


       *_Bakin rai Bakin Fama kinji Mamanki ko Inkan nace Naiha Allah Wai ni, dan Imamu ya haɗata da hard work_*
 
      Kuyi hakuri, Abubuwane yau sunfi karfina, da nayi muku yafi haka.......Thank You🌹
       Karku manta da d'aga min Darajata ta hanya dangwale d'an taurarron nan💋
      #Mai_dambu
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*

      *_Godiya da fatan alkhairi ga ilahirin Abokan arxiki wa'inda nake jinsu tankar Y'anuwana najini ba xan taɓa manta dunbu alkhairinku da addu'o'inku ba a gaskiya bani da bakin da zan iya cewa kome ban taɓa tunanin samun kulawa haka ba sai da dalili me karfi ya taso min lallai naga tsantsar kulawa ta musaman daga gareku, wanda yasa na nime ciwon narasa😂 ban faɗi haka dan raha ba, na faɗane iya gaskiyar dake bakina,A da ina tunanin book ake bi amma a ynx nayi Imanin da yardan ba wani abu kuke bi a tare dani ba sai ɓuruntu irin nawa 😂 wnda nasan kunyi kewarsa Aikan ko ban faɗi haka ba nasan kunyine dan Allah da kuma zumunci nagode da gaggarumin kulawarku wanda yasa na mike babu shiri😁 musaman Nafi nijar wacce takanas ta kwaɗamin kira ga Aunty Safara wacce sai da mukayi kusan 10m muna magana akan lafiyata, kai idan nace zan kira sunayensu ɗaya bayan ɗaya zan cika buk ɗin ban gama ba domin Yawwa suke dashi Nagode nagode nagode Allah yabaku ladan ya kuma cika muku mizaninku da alkhairorrinku_*

     

Fatan Alkhairi gareku...
       Mommy Sayeed & Noor
       Mommy Ahmad
      UmmuNass
     Maman Huda
        Baby Maryam my Kishiya(Tuzuruwa lamba ɗaya kenan)😂
      Maman Ansar
       Ummu Aman
         Sister Nafisa Salis
         Auntyna Maman Faruq kano
           Meema Autar brilliant
          Haleematul Sadiya Leema
               Ummu hani(Baby Hotiho😂)
Leemart &Asmen
                 Zauren Mai_Dambu
                   Aisha Sada Michika Novel Group
             Aisha Novel Group.....

      Da sauran inda suka min fatan alkhairi nagode Allah yasaka da alkhairi......

         Saura kiris nayi tuya na manta albasa....
         My Watpad Frnd bani da bakin cewa kome nagode da addu'o'inku wanda tsabar yawanku ba zai barni na ambaciku ba but ba zan manta da wasunku ba....
Abulram, Aunty Sholing, Sis heedaya Halimamusa Aunty Binta k Mamman........Kuyi min afuwa duk wanda baiji sunansa ba,,,,zakuji a gaba.
Not editer🔨
  *:•~21*
Ba xan iya cewa ina cikin nutsuwa ba, domin tunanina guda ɗayane mi ake da kayukan mutane kai da naga ba sarki sai Allah sai tattara ala'amarin na watsa gefe guda na maida hankalina jikin Ramla, inda muka maida asibiti gidan makoki dan ita ke jinya amma nike rama duk na kara kaɗewa kaman kuɗin guziri,

       Kwananta goma sha hudu aka sallameta, inda na cigaba da kulawa da ita, Allah sarki rayuwa kenan kayi mikyau ya ka kare balle kuma kayi mara kyau duk sai ta koma wata iri, kwana uku tsakani sai ga bak'i daga yobe sun kawo kayan aurena, inda suka nemi alfarman asa bikin cikin satin nan dan zai koma dani ne, lokacin da aka kawo kayan Ina gidan Aunty Zubaida, tunda naje gidan aketa ɗura min kayan damuwa, a bakinta nake jin wai ankawo kayana kuma  an basu rana, wato nan da sati biyu masu zuwa ai take hankalina yayi dubu ya tashi, na rasa inda yake min daɗi, kuka nasaka mata inda nake cewa," wallahi ba zanyi auren ba akan me za'a taƙura min da maganar auren wanca mutumin ni nafasa sai dai ya sake ni."
          Sororo tayi tana kallon yanda nake mata ɗiban albarka, ga mutanen gidansu kowa najin abinda mukeyi, ranta kara ɓaci yayi, kawai tashige ɗakinta sai gata tafito ɗauke da wayan cherge ai kuwa ta rutsani da duka baji ba gani, sam Aunty Zubaida bata iya ɓacin rai ba, ga baki ɗaya idanunta rufewa yake kuma tun tana gida haka take ba wai aurene ya canxata ba,

            Dakyar Uwar mijinta da matan gidan suka kwace ni, jikina duk ya fashe,wani irin mugun tsorone ya kara rufeni ina shassheka, kallon Uwar mijinta tayi, wacce tunda ta shigo faɗa take mata, tace.
"Ba'aba kiyi hakuri amma tashige ɗakin takwanta inda kuma tafita daga wannan ɓangaren wallahi sai na karya mata sawu..."

    Tana gama faɗin haka tashige abinta, kukane yasake kwace min, inda na bi bayanta,  a falo. Wani mugun tabini da shi niman guri nayi na zauna cikin muryan kuka nace.
"Aunty kiyi hakuri!" ina zaune na haɗa hannuna guri guda ina murkusasu, sannan na sake muskutawa gabanta nacigaba da cewa.
"Aunty kiyi hakuri ba xansake ba, kawai bana son na tafi wani abu Ya sami ramlane zuciyata ba zata min daɗi ba, ku kyaleta haka babu wanda yafi karfin kuskure."

       Zuba min idanun tayi cikin mamaki wato duk wannan uban rigimar da nayi duk badan kaina nayi ba sai dan ramla,sake jefa min wani hararan tayi cikin sanyi murya inda ta sassauto daga fushin da take, tace.
"Amma kinsan irin zaman da nake a cikin gidan nan ina laifi kiyi rashin hankalinki a cikin daɗina ba xan kulaki ba amma sai a cikin mutane kinsan yanda za'a maida maganar tagulma. Hmm da kinsan halin da nake ciki da bazaki fara ɗaga muryanki akan wannan maganar ba, dan nima bani da niyyar taɓa lafiyarki, batun ramla kuwa babu ruwanki a ciki ku nutsu ayi komi cikin kwanciyar hankali."

            Kuka nacigaba dayi inda na roketa tabarni naje gida, bata ki ba, da yamma nashirya, ni tafi hmm na manta da Wai ya bani waya.

Sai da nazo zuge side bag ɗina na gan wayar siririn tsaki nayi, cike da tsanar shi wanda bansan dalilin haka ba, koda nazo gidan rigima na tadawa Innaji cikin, "ni nafasa bana son auren " bata ce min kome ba sai ma shareni da tayi, da na isheta kuwa bata san lokacin da ta ɗauki bulogari ta jefeni dashi ba ihu nasake fasawa wanda yafito da ramla daga ɗakin a firgice zaka rantse rotseni akayi nan kuwa, ko samuna batayi ba kwanciya nayi a kasa ina birgima,, zaro idanun Innaji tayi cike da mamaki haɗi da tsoro cike da mamaki tace.
"Anya bakiyi gamo ba kuwa, A'i wannan haukar da me yayi kama ni Saratu naga takaina," cikin shasheka nace.
"Wallahi ku fasa auren in ba haka ba kuwa."

Ran tane yakara ɓacci bata san lokacin da ta ɗauko, wani zageggen itace marke ta yo kaina ba, cikin ihu ramla tace.
"Naiha tashi gata nan ba ita."
Ai na makara dan kuwa ta rutsani idanunta a rufe ta shiga jibgana babu k'akkautawa, tun ina ihu da niman taimako har nayi laushi ko ihu bana iyawa. Ruwan hawaye ke kara kaina a idanuna.
Yarda itace tayi ta juya cikin ɓacin rai, ta koma bakin aikinta, da taimakon ramla nashiga ɗakinmu, ruwan wanka ta hada min na shiga nayi, ina kuka duk jikina yayi tsami, ina fitowa zazzaɓi ya rufeni. Kwanciya nayi ta rufa ni da bargo, sannan ta fita can sai gata ta shigo da kofi ta mika min tare da magani. Karɓa nayi nasha sannan na koma na kwanta, tunawa nayi da wayar tashi nayi na cire dan yanda nake jin zuciyata dole na cirewa imamu gwango, maka wayar nayi jikin socket sannan na koma na kwana baccine mi karfi yayi gaba dani, ban tashi ba sai da aka kira sallar magrib na mike kaina sai ciwo yake,

Alola nayo sannan na gabatar da sallah, ko addu'a ban shafa ba na mike, na ɗauki wayata raina kara ɓaci yake, kunan wayar nayi, can da ta gama sitting na shiga gurin text..

*_Hmmm ba lallai maganata tayi maka daɗi ba amma ni dai nasan zatayi min tunda daga bakina ya fito, ni Bana sonka kuma bana son aurenka, Nifa ina zargin Anya ba wani kudireni a ranka ba kuwa inba haka me ye dalilinka na makale min inma kayi haka ne dan kaciremu kunya toh bana bukatar haka gwara na zama karamar bazawara da na zauna a karkashinka mitssssw banda rashin adalci mata nawa suke bin mazan banxa ba a yanke musu hukuncin kisa ba sai akan wacce ƙaddara ta faɗa mata, har da zakewarka ni dai wallahi na tsaneka tsana me tsananin ka datse igiyar da aka kakkabamin naka dan na maka alƙawarin ganin bakin ciki mara iyaka_*

Na tsaneka......

Da wannan kalmar narufe sakona. Sannan na kashe wayar baki ɗaya na kwanta jiran sallar isha.




*
*
*Yobe*
Bayan sallar magrib duk sun hallara a falon umma ana ta hiran yanda zasu gudanar da karɓan bakinsu musaman y'an kawo amarya yana gefe shidasu Khalil yana duba masa, hannun yaron da ya kone ɗazun a gidan Iyayen Jameesha, yaji karan sako ciro wayar yayi daga aljuhun bakin wandon kaftanin, dake jikinshi yasaka wata yadi cream colour, wanda har kana hango farin shimin jikinshi, ya gyara gashin fuskarshi har da na kanshi sai suka kwanta luɓluɓ, zubawa wayar idanu yayi sannan ya cireta daga key ya buɗe sakon, yana karantawa amma fuskarsa ɗauke yake da murmushi, dan ya gama gano yarantata zarriyan, murmushi yasake akaro na biyu yana girmama wautata, jaraba kirana yayi sai yaji wayar akashe a ranshi yace.. _Sarkin rikici zan biyar dake Insha Allah yanda ya dace._



Mikewa yayi yabar falon ya koma ɗakinshi ya shiga hidima a laptop ɗinshi.




Kallon Mansur Umma tayi cikin nutsuwa tace.
Ɗazun ban fahimci maganar da shatima yake ba, sabida hankalina yana kan hannun Khalil da ya kone.

Gyara zama yayi sannan yace.
"Wato bansan mike damun shatima ba, amma nafi zargin tsofa ce tasako shi a gaba, wai akan auren da Imamu yayi bai sanar da kowa ba, sai kawai tarewa shine wai toh tunda yayi gaban kanshi shima ya kara masa auren Y'ar gurin Hajja Yakalo ta maiduguri."


Shiru tayi kaman ruwa ya cinyeta sam haɗin bai mata ba Yanxu tana magana za'ace dan ɗantane yasa tak'i amincewa. Kauda damuwarta tayi sam tace.
"Wacce kenan a cikin Yaranta.?"
Ta jefa masa tambaya a takaice.
"Hauwa'u yar autarta, ai bana ta gama sakandiri, kuma suma mahaifinsu baya bari sukara gaba sai a gidan mazajensu, bansan Yanda akayi har ya yanke hukunci nan ba, amma lokacin rasuwar zahira tazo har sau biyu kuma mun haɗu da ita a gidan, ba mamaki abinda ya kawota kenan."

"Allah yasa haka ce mafi alkhairi, amma naga kaman Imamu bai da matsala akan haka ko?" ta tasake jefa masa tambaya akaro na biyu,


"Eh gaskiya bai da matsala, wallahi koda shatima ya faɗa masa murmushi yayi yace Allah yasa haka shine mafi alkhairi amma ba zai tafi da dukkansu biyu ba sabida yariga yayiwa A'isha visa, zai tafi da ita in yaso daga baya zai zo ya tafi da hauwa'un. Shine dake tsohon tsufa ya sakoshi a gaba wai akan mi ba zai tafi dasu dukkansu ba, yaso yayi masa bayani amma bai kula shi kinsan imamun shima ba gwanine a fagen shariya sai ya wucce shi yabarshi ya cigaba da ihunsa da faɗa. Allah mutumin nan yana da zugurerriya matsala."


Tunda ya faɗa mata yanda sukayi da shatima bata sake cewa kome ba har ya bar falon ɗaukar sabida kiran sallar isha, shiru tayi ta kurawa Ummi idanu wacce take wasarta cikin kwanciyar hankali, shigowa yayi yana goge ruwan yake bin fuskarsa sallama yYi sannan yace.
"Khalil taso muje masjid."

Mikewa yaron yayi sannan ya shiga ban ɗakin falon yayo alola ya fito rike hanunshi Imamu yayi, sannan yace.
"Umma mun tafi sallah."

Kallonshi tayi sannan tace .
"A dawo lafiya, idan ka dawo ina son ganinkA."

Tana faɗin haka itama ta mike tabar falon tashiga ɗakinta domin gabatar da sallar itama.


.
. Bayan sun dawo daga sallar, ya shigo zama yayi a gabanta kanshi a sunkuye yana jan yatsun hannunshi suna k'as, gyara murya tayi sannan tace
Ban fahimci abinda yake shirin faruwaa ba, daman kana da burin zama da mata biyune. Dan shatima ya sameni da wata magana wanda ban gane masa ba, asama na gane amma kasan rashin jutuwar da yake tsakankina da hajja Yakolo, tuntuni bata soni ba sai Yanzune zata so haɗaka da yarta, gaskiya bana son wannan haɗin dan ina hango ɗinbun damamaki dasuke tun karoka, bakai ba har dani ma balle kuma yar mutane da kake shirin haɗata da damuwa. Shatima dai kanin kakankune banxe karka masa biyayya ba dan shima ubane, amma da ko a jikokinsa ya nima maka wata ba zai dameni ba da ka auri Yar yakolo." Fuskarta cike da damuwa, takarshe maganarta,


Gyara zama yayi cikin nutsuwa sannan yace.
"Ummana!!!" a hankali ya kira sunanta ɗago kai tayi ta kalleshi sannan ta kauda kanta, sabida sam ranta baya kaunar auren Yar kanwar Babansu.

A hankali ya fara magana yace.
"Nasan irin rashin jituwar da yake tsakaninku tun ina Yaro har zuwa yanzun danake gabanki a matsayin ɗan yaro karami, ko a lokacin baki taɓa cewa mu nuna mata ba mayinta ba asalima nuna mana darajarta da kimarta haɗi da girmanta, kike nuna mana, baki taɓa nuna ɓacin ranki akan tayi miki wani abu ba, asalima baki damu da abinda take maki ba.!" shiru yayi haɗi da jan numfashi, cikin nutsuwa juya hannunshi yake cikin damuwa ya ma rasa ta yanda zai fahimtar da ita.
Cigaba yayi da cewa.
"Har zuwa yanzu da girma ya cin muku bata daina ɓata miki ba, amma duk da haka baki damu ba, Yau an wayi gari wacce bata kaunarki ita ke niman alfarman ɗakin Ya auri yarta Umma shin wannan ba alfarma bace,?"

D'ago kai yayi yana kallon fuskarta cikin nutsuwa yaga ta murmusa sannan ta gyaɗa kanta tace.
"Alfarmace."


Shima murmusawa yayi sannan ya cigaba da cewa.
"In baki manta ba, shekaru talatin baya lokacin ina makarantar sakandiri kin taɓa ce mata Allah ya ara muku nisan kwana sai taci alfarmanki, sai taci arzikinki sai ta moreki, Shin wannan addu'ar da kikayi Allah ya amsa shine zaki maida masa kayanshi. Bayan kece kika roki haka,"


Mamaki da al'ajabine suka rufeta lokaci guda ita ta manta ma tayo wannan addu'ar ashe shi bai manta ba, lumshe idanunta tayi cikin nutsuwa. Sannan tace..
"Natuna zunnur"


Sake murmushi yayi cikin jin daɗi dan yana kaunar jin ta ambaceshi da sunar.

Cigaba yayi da cewa.
"Yau gashi Allah ya amsa miki addu'arki, idan kika fito kika ce baki kaunar auren me saukine a gurina nima nace bana so amma kinsan baza'aga laifina ba saima ace ai biyayya nayi tunda kece bakya son auren kinga kenan amadadin raina ya ɓaci nakine xai ɓaci, Ummana ki duba maganata da idanun basira karki k'i amincewa ki amince yanda koda A'ieesha tashigo bazatayi bakin jini ba, idan nida ke da Yan uwana muka so a'ieesha toh ya,zamu samo mata soyayyan dangi bayan ke kika ka janyo kowa ya kita, sabida za'ace k'inki naki ya auri yar danginshi amma k'in bashi goyan baya har ya shigo da bare kuma kinfi son bare akan na gida Ummana wannan shine iya abinda zan tuna miki_


#Mai_Dambu
Karku manta min da ɗaga min darajata💃💃💃


#Na Dawo#Voter#Share
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

        🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*

      *_Hmmm_*

              _Wayyo Allah na Yanzun tsakaninku da Allah hana Imamu kara aure kuke shirin yi fa?😹 Wato daga dawowana sai mugun Abu 😝 Amma dai kunsan malamai dai sai da ɗabakka sunnah ai bayan Naiha ma kamata Yayi ace matasan huɗu russ fa amma na gode da kuka tuna min sai Yayi huɗu rak rak nagode da comments ɗinku musaman zaurena Fatan alkhairi sinki sinki💋💜_

Didi rigima ga shi keda Mamien Khalil,
Yau ma babu editin
*22*
  Tsura masa idanun tayi cikin farin ciki da godewa Allah mabuwayin sarki da ya azurtata  da samun ɗana gari murmusawa tayi wanda kwalla ya zubo daga idanunta, tace.
"Zunur nagodewa Allah da bai makantar da tunanina ba, naji daɗin da kafarka dani daga nauyayyar baccin da nake kuma na Amince da wannan nakaAllah yayi muku albarka."

         Shima cikin farin ciki yace..
"Amin Ya Allah Ummana, sai dai kina da aiki dan A'ieesha babu wanda ya kaita wauta, bansan Yanda zamansu zai kayya da Hauwa'u ba."

          Murmushi tayi akaro na ba adadi sannan tace.
"Wannan ba aikina bane nakane."

  Shafa kanshi cikin nutsuwa yana me danne dariyar da ya taso masa yayi sannan ya mike zai bar falon can yace.
"Ina so...." makale maganar yayi a kasar makoshinsa inda ya maida cewa.
"Ina tausayintane dan ba wayyone da ita ba."

          "A'a ai da kalmar farko ka karasa na kana sonta ba wai ka buge da raina min hankali ba, ta faɗi haka tana me tsareshi da idanunta,

    Dariya yayi sannan yace.
"Ummana yaushe kika fara aikin jarida irin wannan titsiyen ai sai na rasa abin cewa, mu kwana lafiya."
           "Allah ya tashemu Angon A'ieesha Baban khalil da Ummi. Zunur ɗin Ummansa."Juyawa yayi kaman zai fasa ihu, matukar yana gaban ummansa toh maida kanshi yake kaman Khalil dan wani uban sakalci yake zabga mata,dake itama bata ɗaura kanta damuwa k'in jan yaranta a jiki ba, shi yasa duk yaranta basu da abokiyar shawara sama da Ummansu ba su ba har sauran Yaran gidan a hanxarce yabar falon xuwa ɗakinsa.

      *
      *
       A kowani shashi hidima suke sosai idan kacire Ni da na tsangwami kaina dan har abinci bana iyaci sai Ya Ishaq ya tasani a gaba duk nakara ramewa, nayi wani firit kaman ba ni ba, sai ɓasaka ramla a gaba nayita kuka, ko kuma mihaɗu tare myita kuka,

              Duk wanda ya ganmu sai ya tausaya mana domin, banda Innaji dan duk lokacin da tazo tasamemu sai takafa mana kusa😹 Wato rankwashi dukkanmu biyu kuma, haɗi da masifa cikin kwando dubu, nidai ko a jikina........

*
*
   *India Medical Hospital Mumbai*
             Kwance yake cikin wani irin hali na rai kwai-kwai mutu kwai-kwai, na'uran bugun zuciyane kawai yake aiki a ɗakin abin tausayi lokaci guda Asad kaman bashi ba, likitotti ukune akanshi suna ta tattaunawa, can ɗaya a cikinsu Dr Vikram Ajey, an rubuta sunansa a jikin labcoat ɗinsa, ya kalle ɗaya liktan cikin kwarewa yace.
"Wannan likitan zamu turasa Babban Asibitin zuciya dake Hydarabad Inda zaiga Dr Vasudra Abhnash, ita ɗaya ce kawai zata iya shawo kan matsalarsa."

     Gyaɗa kai suka sauran biyu dansun gamsu da abinda ya faɗa.
          Wani takarda ƴa ɗauka yayo rubuce rubucce yana gamawa ya mikawa Mamani cikin tausassawa yayi mata baya, sannan ya fita kuka tasaka cikin tashin hankali da damuwa, alola ta mike tayo,

     A daren ranar aka maidasu Hydarabad, inda zasu ga Dr Vasudrah.

                Dake tafiyar jirgin sama ne, sun tarda da jami'an asibitinta suna jiransu a Airport.
          Suna isa asibitin kuwa suka sameta tana jiransu abubuwan da ya dace tayi masa, sannan ta ɗauki file ɗinsa ta tafi gidanta da shi.

           Akalla zata kai kimani shekaru arba'in da tara zuwa hamsi. Sai dai yanayin fatarta zaka fahimci yar Yankin madaras ce, dan tafi kama da tamiland wato black indian ce, amma tana da matukar kyau da kwarjini, abu guda biyu ta tsana shine kashigan mata aikinta bayan ga abinda tace ko kuma sakaci gurin, kulawa da majinyaci.

           Amma mace ce mai matukar hakuri da taimaka dukda Allah yayi mata baiwa da ilimi da arziki toh tana matukar taimakawa mutane sosai. Musaman Marayu da gajiyayyu.

  *
  *
  Bidiri tusan tsaye na zaune me yaga zani, Hidimar da ake a maiduguri ba nawasa bane dan dagaske Hajja Yakolo take shirya autarta(Ai zanso ganin wannan bidirin a gidan imamu lolx😹😝)

       Dan ba karamin kashe kuɗi take ba,

               Aurin aurensu zai dai dai, da tarewana kenan kuma dukkan bai wucce yan kwanaki ba.

            Sosai ake mulke yarinyar da Dilke ko ina najikinta yans karɓan abinda ake mata, kai ko zama tayi kusa da kai sai ka gane amarya ce, balle kuma kayanta da take sakawa.

        Acikin yan kwanakine ya xiyarci maidugurin,da yamma suka sauka a gidan cikin rawan jiki Hajja tashiga hidima da shi, kawo wanca ajiye wanca,haka suka cika masa gabanshi da abinci.
         Kallon abinci yayi cikin rashin yarda yace.
"Ina Hauwa'un take tazo muci abincin tare."
         Cike da mamaki hajja tace.
"Kaman ya? Ai dan kai nayi kawai kaci itama taci nata, kagama sai naturota."

        

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment