Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirjinshi ina kuka kasa kasa, ga hancina da yake haɓo hannuna duk biyu suna dafe da kirjinshi, hankaɗeni yayi ya wucce ciki abinshi, a hankali na mike nabar falon, kwanciya nayi a gado ga uban ciwonkan da ya rufe ni, dakyar na samu na shiga ban ɗaki na cire kayana sannan nayi wanka da alola, nazo nayi sallar magrib, na haɗa da isha sannan na ɗaura da shafa'i da wutiri, komawa nayi na kwanta ina kuka _yau nakaishi karshe har ya gaza hakuri ya mareni mutumin da ko fushi ya gani a fuskana sai ya san yandan ya maidashi dariya, tayu har ynx bai ci abinci ba,_ ni kaɗai nake wannan zance a zuciyata riga da wando na baccine a jikina, a hankali na zura hijab nafito, zuwa kicin abincin na nan da zafinshi sai zoɓon da yake frij, ɗakinshi na nufa cike da tsoro yana kwance a kasa, samar abin sallar, gabanshi naje na zare hijab ɗina na kwanta a gefenshi ina kuka a hankali, juya min baya yayi ban fasa ba nakai hannuna ina shafa kirjinshi da nake jin bugawarshi juyowa yayi a fusace yace.
"Me Kike so A'isha? Mikike bukata kuma ki kwantar da hankalinki cikin satin nan zan mai dak.."

Ban bari yakai karshe maganar ba na tareshi da abinda bazai iya bijirewa ba, shiru yayi bai kulani ba har nagama iya yina, na barshi cikin dishashiyar murya nace.
"Tashi kaci abinci don Allah, zan iya jure fushinka amma baxan iya ganinka cikin yunwa ba don Allah"

"Kije na koshi." ya faɗa min duk yanda naso mu sulhunta abun ya gaggara dole na kwanta nima, a gurin cikin dare kuwa na farka na ganni a samar gado shi yana kasa, sauka nayi na koma jikinshi na kwanta, ce min yayi.
"Koma sama ki kwanta." kin kulashi nayi na gyara kwanciyana inda duk na,zuba masa kafafuwa,



Fushi sosai imamu ya ɗauka nakira Aunty halima na fɗa mata, abubuwan ta turo min yanda zanja hankalinshi har ya wucce. Amma fir yaki sannun sannu muka share kwana biyar ko kallon abincina bayayi.


Ranar da muka cika shida bayan na idar da sallar asuba, kuma ranar ya kasance asabar yana ɗakinshi nima ina nawa, fitsarine ya matseni kaman banyi ba da zanyi alola da gudu na shige ban ɗaki ina tsugunawa sai naji kamar fitar abu, da kuma fitsari tsarki nayi na kalli kasar sai naga abu kaman nama kamar jini hantane ni ban tsaya tantancewa ba nafita zuwa ɗakinshi yana kwance na tadashi ina faɗa masa ya fito da sauri, ya ɗauki abu yasaka alaida yaje yasa hakk'a rami yajefa tare da addu'a ciki ya koma nima nabi bayanshi, ɗakinshi ya shige nima naso shiga nashi sai na mike nawa dan kar ya min fassara(😂)

Ai ashe shima can yana tunanin biyoshi zanyi, sai ya na wucce abuna.

Tunda na shige nima na kwanta bacci yayi gaba dani, cike da wasu irin mafarkai, Ummi yar shi, ga wata mata ta jefata cikin ruwa, tasa kafarta tadanna kan Ummi....

"UMMI........." Nakira a razane tare da mikewa zaune shine a xaune kusadani yana kallona idanunshi sunyi ja, jikina narawa na faɗa jikinshi a hankali nace.
"Ummi nagani wata tajefata a ruwa ta danne kanta kafarta kira min Umma naji ko Yarinyar lafiyarta lau."

Rungume kaina yayi a kirji ina jiyo sautin bugun zuciyarshi, ɗumin da naji a kafaɗana yasa na ɗago cikin tashi hankali na ɗago kaina ina kallonshi, shima ni yake kallon sahannuna nayi ina share masa kwallar da yake zubowa nake, sunki tsayuwa rungume shi nayi tsam a jikina ina kuka kasa kasa nace.
"Waye Ya rasu..........?"

*_Uzuri kaina na matukar ciwo don Allah karku min korafi akan rashin yawan pagen sabida labarin nada tsayi yasa nayi muku typing sai zuwa Monday Insha Allah da babu gwara ba daɗi fatan alkhairi masu karatu🌹*




*Jumma'atu Kareem*🕋🕌
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*



🙆😱*_Don Allah idan zaku ji haushina karku tambayi adireshina dan nafara hango masu shirin min duka_*😹



_Fatan alkhairi gareki Aunty Batul Mamman_

*Yau zanga masu saurin kuka*😜
Not edit
*:~•36*
Da sauri suka shigo cikin falon suna salati, "Shi kenan abinda nake gudun faruwanshi ya faru Amma Yakolo kinyi Asaran rayuwarki wallahi baki ji daɗin rayuwa ba Allah ya isa tsakanina dake, Kifitan min a falo kafin na nuna miki zallar ɓacin raina." Inji Umma ta faɗa.

"Bazan fita ba ko kashe ni zakiyi wallahi babu inda zanje sai an kawo min gawar Y'ata adake ka a hanaka kuka taɓ ɗijam baki isa ba Binta wallahi kinyi kaɗan" Yakalo ta maida mata martani a fusace,


Wayyo Tashin hankali wanda ba'a samasa rana,duk ruwan da suka watsa min ban farka ba sai da suka dangana dani da asibiti, Abba lawa da Ya Ali sun wucce maiduguri zasu nufi lagos kana ganinsu kasan labarin hatsarin ya wajajjagasu, Umma takira Innaji tafaɗa mata halin da nake ciki kwana biyu tsakani sai gasu duk yan gidanmu sunzo....


Har zuwa wannan lokacin ban farka ba, sai da suka kwana washi gari nafarka da mugun ciwon kai dafe goshin nayi sannan nafara taryo abinda ya faru, kuka nasaka musu tare da mikewa nacire karin ruwan da ake min, nasauka daga gadon rikeni suke kokarinyi amma kamar me aljanu zubar dasu nakw ina tsalla ihu, aguje likitan ya shigo tare da nurse ana rike dani ya tsikara min allura,a gejen hannuna na dama, ban fasa ihu ba ina cewa.
"Ku sakeni naje nasan bai mutu ba don Allah karku hanani zuwa wayyo Imamuna wallahi ina jin zuciyata tana faɗa min bai mutu ba."
Wani irin baccine ya mamaye min idanuna a hankali nashiga rufesu ina cewa.
"Ina sonka Imamuna, rayuwata da komena mallakinkane, kaine duniyata kar....ka....taf...fi...ka....bar..ni"


Kwalla Umma tashare komowa tayi inda nake kwance tana shafa kaina a hankali tace.
"Nayi miki alkawari A'isha bazan taɓa barin Zunnurani ya juya miki baya ba, bazan taɓa kauda kaina akanki ba, A'isha matukar ina raye babu wanda ya isa ya cutar dake akanshi ba zanyi kokarin na sadaukar da farin cikina domin naki...." Kukane ya ci karfinta kifa kanta tayi tana kuka ita ba mutuwar da akace Imamu yayi yasata kuka ba, halin da nake ciki yafi kome damunta,

Dafa innaji tayi cikin juriya tare da ɓoye tashin hankalinta tace.
"Ayya hajiya kema da kanki keda zakiwa A'isha faɗa ke kike kuka, don Allah kiyi hakuri balle kuma bana tunanin yana cikin jirgin da yayi hatsari, mucigaba da Addu'a har Allah ya fitar da gaskiya amma kuka ba naki bane sai du'a'i."


Girgiza kai umma tayi cikin shaye kukanta tace.
"Maman A'isha!!!" shiru tayi sabida kukan da yake shirin kwce mata girgixa kai tayi kwalla nabin fuskarta sannan tace.
"Idan Usman Ya mutu bazanyi masa kuka haka ba, sabida kafinshi wasu sun mutu" suna kallon juna, cikin matsanancin kuka tacigaba da cewa..
"Sai dai nacigaba da binshi da addu'a amma idan sanadin mutuwarsa ya nakasa rayuwar A'isha bazan taɓa farin ciki a rayuwata ba, ki dubi halin da take ciki ai ido ba mudu ba amma yasan kima, xanyi farin ciki idan ace zasu rayu tare, zanfi kowa murna idan suka gina rayuwar aurensu, Ina tausayin kaina ina tausayin A'isha sabida da kuruciyarta tafara shiga wata rayuwa, idan yau aka tabbatar Imamu ya mutu, zan iya hakuri itama zatayi amma ya mijinda zai aureta zai cire soyayyar dake cikin zuciyarta duk wanda ya aureta zai ji ba daɗi ainu, Amma kiyi hakuri ina matukar kaunar A'isha da imamune,"


Idanu Innaji ya cika da kwalla gogesu tayi tana kallona danake barcin magani, a hankali tace.
"Allah yana tare da masu hakuri shine abinda zan iya faɗa miki Allah ya tabbatar mana da alkhairi."


Daga haka basu sake magana ba duk sukayi shiru........
Kwana biyu tsakani suka koma gida tare da alkawarin zasu sake dawowa.
«»
Kodasu Abba lawan suka isa lagos sun samu tabbacin jirginsu Imamu dayayi bookingne yayi haɗari but su basu san ko suna ciki ba ko basa ciki dan tabbas jirgin da zashi zuwa Uk shine ya samu crash, amma akwai wasu fasunjoji da basu bi jirgin ba a ranar sun wucce dubai.


Abin mamaki koda ake je duba sunayensu ansamu a jirgin da ya tashi zuwa london jikinsu a sanyaye suka bar airport ɗin zuka dawo abuja Gidan Ya Abubakar.

Anan kuma sukaita gwada layinshi yaki shiga dan dole suka dawo gida, da muguwar sakamako, inda wasu suka raja'a akan yana raye wasu suka ce ya mutu.


«»
Alhamdulillah jikin Asad kan yayi kyau har yana fita waje shan iska Ba'a barinshi shi kaɗai, kullum yana tare da Mamani tana kwantar masa da hankali ganin hankalinshi ya dawo jikinshi yasa aka sallamesu akan duk bayan wata uku zai zo ganin likitarshi.


Ranar alhamis suka diro naija cike da ɗauki son ganin Mahaifinshi da Yan uwanshi gefe guda na,zuciyarsa ina makale nan yana kokarin ɓoye ni a cikin zuciyarshi da ruhinshi.


Kuma haka da yayi yasamawa Iyayenshi nutsuwa har suka gabatar masa da jiran da ake masa akan sakin Ramla bai ɓata lokaci ba ya saketa, nan baba ya shigar da ita kotu dan a sauke nauyin da yake kanta, Allah sarki idan kaganta sai ka zubda kwalla tayi kyau ta maida kibarta, an saka ranar za'a jefeta ranar jumma'a Allah da ikonshi ranar jumma'ar da Asuba ta rasu, bayan ta idar da sallar asuba tana cikin addu'a,tana shafa addu'ar tasauke a jiyar zuciya shi kenan, ta zuɓe a gurin gefen alkur'aninta da casbinta, shiru shiru bata fito ɗaukar abin karyawanta ga lokaci yana tafiya, da Innaji taga haka shine ta leka taganta kwance, tashiga ta hau mata sababi taga bata motsa ba sai da ta ɗago hanunta ya koma, jikinta yayi matukar sanyi ainun durkusawa Innaji tayi tana kallon fuskata cikin murmushi tashafa kanta sannan tace.
"Allah ya Amshi tubarki Ramlatuna na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe miki hakkin jama,ar dake kanki...."


Addu'a tayi mata sosai kafin tafito ta faɗawa Babanmu shiga ɗakin yayi ya gyara mata kwanciyarta sannan ya fita yasanarwa mutanen unguwa.

Kafin wani lokaci gidanmu ya cika shima Asad ɗin yazo cikin tashin hankali tare da Mamani yana cewa.
"Ramla nayafe miki Allah ka amshi bakuntarta ka yafe mata kura kuranta..."

Innaji takira Umma ta faɗa mata kuma taroketa karta faɗa min halin da suke ciki.

Haka suka gama zaman makokinsu banda labari.....


«»
Zaune nake gaban umma ina zubda kwalla ina kuka can na haɗiye kukan ina kallon Umma nace mata.
"Umma laifina ne, bana kowa ba."

Rike hannuna tayi cikin nata sannan tace.
"A'isha ki daina faɗan haka kinji ko babu kyau."

"A'a Umma barni na faɗa umma tunda muka tafi Uk bamu zauna lafiya ba, ina sonshi ammq narasa yanda zan nuna masa umma kin me kitaɓa nan ɗina kiji yanda yake bugawa wallahi Abu khalil yana raye taɓa kiji" hannunta nakai dai dai kan zuciyata ina kallonta murmushi nake tare da zubar hawaye, nace.
"Kinji ko ai nasan yana raye kawai akwai abinda ya farune amma bana tunanin ya mutu, Umma kinsan me hmm nifa Ina matukar son Abu khalil bakin idan akace nabada rayuwata dan fansar tashi ba, kiyi magana sai kallona kike ba mamaki zaki ce na haukace ai ba damuwa inda akan son Imamune ku kirani zararriya wallahi zan amsa muku,"


Kuka kuma na fashe mata dashu ina cewa.
"Duk laifina ne, gashi ranar da zai tafi naki na tsaya muyi sallama da rigima muka rabu nikam bansan mike damuna ba, shi kenan ba kome tunda bazaki magana ba."


Komawa gefe nayi na cusa kaina a tsakiyar cinyoyina ina rera mata baitukar kuka daman kowa yasan wannan ɗabi'atace........


Mikewa tayi daga bakin gadona zata fita haduwa tayi da Abba lawan Ya Ali Ya mansu Aunty bilki, Hassan Husaina, Aunty Mummy Ya Abubakar duk sun zuba mata idanu bata hanya sukayi a falo ta zauna tana ajiyar zuciya tare da ɗaukar goran faro tasha kusan rabin ruwan,

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.
"Ina nazarin maida yarinyar nan gaban ahalinta kozata samu saukin damuwarta ko me kuka ce "

"Ummana korata kike daman baki son ganina ko toh shikenan sai nafadawa Imamu kina korata ni wallahi babu inda zanje sai kunemo min Mijina," a razane suka juya basuyi tsamanin ganina ba shigewa tsakiyarsu nayi naje nayi pillow da cinyar Umma ina kuka, suma tausayina ya hanasu magana sai kallona suke,
"Shi kenan A'isha bazaki je ko ina ba,kinji zamu zauna a nan har sai an nemo miki mijinki, wa yace miki umma bata son ganinki" Ya Abubakar ya faɗi haka cike da tausayi,

Ya ali ya girgiza kai cikin karfin hali dan masifaffene amma yana da raunin zuciya,dukda likitane shi amma haka zaka ganshi yasa mara lafiya agaba yana kuka, yau ma haka yayi yana son min magana amma ya rasa yanda zaiyi sabida kukan da taci karfin shi mikewa yayi yabar falo ya shige ɗakin matarsa yana kuka kamar karamin Yaro,
Hassan ne yasaka hannunshi a aljuhu ya ciro chocolet ya mika min kallon abin nake kamar dodo girgiza mai kai nayi nace.
"Abu khalil ya hanani sha, kuma dan baya nan bazan sha ba, nidai ku nemo min shi ina jin yunwa."

Ranar nasasu kuka ainun dan naki cin kome na koma tankar mahaukaciya, kaina ya juye baki ɗaya idan ba imamu ba bana tunanin kome abinda ke kara dagula min lisafi ba kome bane sai gizon da yake min, haka zan wuni ina rigima da fita abokin hirana kenan Khalil wanda shima yake fama da rashin kanwarshi......


Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba duk inda ake tsamanin abu yaci tura dole aka shiga min alluran bacci ina samu hutawa, suma suna hutawa...... Ana cikin haka Innaji da Baba da Ya Ishak suka zo ganin halin da nake ciki basu zauna ba suka musu jaje sannan suka ɗauke ni sai gida,

Ayya Umma ashe lalurata ce ta ɓoye ta umma bayan tafita hawan jini da Sugarta ya tashi, karshe Abuja Ya Abubakar ya tafi da ita Khalil ya koma hannun Ya Abba lawan.

Ni kuma Innaji suka dufufa min rokon Allah da kaine asibiti abin kan ba daɗi fa......



«»
*Mu koma baya*
Lokacin da su Imamu suka rasa jirginsu suka shiga na dubai har suka sauka Hauwa na makaƙe dashi kaman dai yanda muka zauna na wancan lokacin haka wannan karo, tana fakonshi tun airport ta zare wayarshi ta jefa a bin shara, koda suka sauka a masauki ya lalubi wayarshi da niyyar kira yaji wayam, yayi niman duniyan nan bai samu ba gashi yayi asaran abubuwa masu matukar muhimmaci a cikin wayarshi da nafasa, bai damu ba amma ɓatar wannan wayar itama sai da ta fuskanci matsala gaggaruma dan kaman zai maketa yake ji dan yafi tunanin like masa da tayine wayar ta fadi gashi yana son kirana, ko har ynz fushi nake......




Ya fita niman koda karama ce amma sabida tsadarsu yasa ya hakura, lokacin tafiyrsu na cika suka tafi tashar girjin anan ake nuna suka ga labaran hatsarin da akayi take hankalinshi ya tashi, ya ɗauko jakar laptop ɗinshi abin mamaki tayi rugurugu, screen ɗinta kamar zaiyi hauka aka yaji a ranar haka suka tafi yana tunanin hanyar da zai tura sako.


Koda suka isa london yasamu sakon post mail a kofar gidanshi makarqnta ya tafi bayan ya buɗe mata gida, bai dawo ba sai dare tun daga ranar abubuwa suka sha kanshi bayi da lokacin kowa har ita kanta dalilin da yasa bai nemi gida ba kenan ga karatu ga aiki, abubuwan sunyu masa yawa wani lokacin goma yake komawa gida, Ga Riyya tasashi agaba da fitina yar lebonis ce,tana matukar son Imamu shi kuma yaki bata fuska..... Karshe fatafata yayi mata yace mata yana da mata har biyu shine ta kyaleshi........




«»
Yanzun an sami wata hudu kenan da faruwa al'amarin dan har an shiga na biyar, saka iyayena nayi agaba da kuka lokacin da na fahimci ramlata rasu nayi kuka sosai karshe nace su maidani gida kawai.............




2009word kuka samu

Share/Voter/Comments
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*


         *_Dominki Sister Nana ta grp ɗin Musha karatu_*

        _Fatan Alkhairi ga Mom littel Tambayarki ta jiya amsarki tana cikin wannan shafin_
              ```Bayan wani jinkiri ban sake ban sake litafin da ya wucce page talatin da biyar ba Sai matar malam, shin ya abu Yake```😂
*:~•35*
Not edit🔨
      Kam'kameni yayi yana sauke ajiyar zuciya akai akai, ɗago fiskarshi nayi cikin rawan murya nasake tambayarshi waye ya rasu.

         Sassauta riko da yake min yayi cikin murya yace
"Fatima ce taɓa jiya sun kirani sun faɗa min ana nimanta, toh har gari yawaye ba'a sameta ba, sai ɗazun aka ga gawarta a cikin magudar dattin cikin gidanmu, Allah sarki yarinyar batasan dadin uwa ba, Allah yayi mata rahama"

     D'an kwanakin da nayi a shashin Umma yarinyar dakyar tasake dani, asalima ita tsoron mutane take, abin tausayi niman kukana nayi narasa, yau nice mai rarrashin imamu can wani zazzaɓi ya rufeshi, amma dukda haka yana rungume dani, dakyar nasamu ya kwanta naja masa bargo muka kwanta ya bani tausayi ainun.


     Ina son tashi amma ya kisake ni, dole na gyara kwanciyana muka kwanta,ina shafa bayanshi cikin tausayi a hankali na aro wasu kalmai na shiga faɗa masa, wanda zasu kwantar masa da hankali.... A cikin ikon Allah sai gashi yana salati da hailala tare da tasbihi,... Dakyar na lallashi nasamu na ciro wayata daga chaji niman layin Umma dakyar ta ɗauka cikin sanyi murya nayi mata ta'aziya nan nake gaya mata ai shima imamu bai shida lafiya amma yasamu yin bacci.

              Mun jima kaɗan a wayar sannan mukayi sallama,ranar a haka muka wuni da shi ina jinyarshi, sai magrib yafita sallah bai dawo ba sai bayan isha, ina kan sallaya, koda ya shigo ɗakina ya shigo nan na shafa addu'ar da nake na tareshi har ya zauna ina masa sannu kallonshi nayi akaro na biyu nace.
"Mi kake so adafa maka, ya dace kaci wani abu ba daɗi xama da yunwa."

        A hankali ya ɗago kanshi yace.
"Ki bani black tea da brown sugar kawai ya isa."

     Jikina narawa na nufi kicin na haɗa masa sabida akwai ruwan zafi a flask, kayan ganyen tea na haɗa na zuba ruwan zafi a cikin tukunya, sannan nasaka citta da kanunfari, ganye da kayan kamshin na dafuwa na juye a karamin flask na ɗauko kofi na nufo ɗakin  a kishingiɗe nasame shi yana addu'a har gabanshi naje na mike xan bar gurin ya riko hannuna cikin sanyi murya yace..
"Zoki zuba min, idan kin gama ki haɗa min ruwa zanyi wanka."

Gyaɗa masa kaina nayi cike da kunya, na zame hannuna daga rikon da yayi min nayi masa yanda yace sannan na mike na shige bayi,na haɗa masa ruwan wanka sannan nafito na zare hijab ɗina na zauna ina jiranshi ya shiga wankan nima nayi na kwanta,

        Yana gamawa ya shige ni kuma na fita zuwa ɗakinshi na ɗauko masa, kayanshi nazo na zuɓe masa a nan , can yafito nima na shiga nayi nafito sai dai matsalar ina ɗaure da towel, dakyar nafito nasameshi yayi kwanciyarshi,kaya nasa nima na kwanta a gefenshi na kwanta.

       Janyoni yayi zuwa jikinshi tare muka sauke ajiyar zuciya, sannan yace min.
"Kwanta kiyi bacci kinji."
        Haka muka kwana har zuwa asuba sannan muka tashi a gida yayi sallah, komawa mukayi bacci yayi gaba damu,

     Sai karfe sha ɗaya muka tashi dukanku babu me kuzari haka muka wuni har zuwa ranar monday......

        Ya tafi mkrnta daga can ya wucce aiki ko ya akayi sai gashi wurarren karfe biyu ya na rana ya shigo ko zama baiyi ba yasake fita da passport ɗinmu, bai shigo sai goma na dare, yana shigowa yayi wanka tea ya bukata, kafin nakawo masa har yafito daga wanka dan dama zai shiga wanka ya umurceni da na haɗa masa, koda yafita yasa kaya ya zauna yasha tean kwanciya yayi dan har na fara bacci matsowa yayi jikina ya kwanta,....


        «»
Washi gari da kanshi ya haɗa min kayana ina kallonshi kukane ya kwace min dan banga alamun zan dawo ba kome nawa sai da ya tattara min bai kalleni ba balle na karyar masa da zuciya zuwa nayina rungumeshi tabaya ina kuka,

       Nace. "Daman baka hucce ba ko, kayi hakuri zan gyara kurakuraina."

       Dawo dani gabanshi yayi sannan ya zaunar dani ganin yanda nake kuka mika min tissu yayi na goge kwallar dake fuskana sannan yace.
"Kiyi hakuri,kema nan da wata uku masu zuwa zaki dawo adalci nake son na kwatanta a tsakaninku, A'isha ina matukar sonki amma dole na ki koma gida Yar uwarki tazo itama."

      Rikice masa da kuka kaman zan shiɗe ina rokonshi da yabani dama amma ina yaki saurarona haka naci kukana har na godewa Allah take naji raina ya ɓacci naji nima ina son komawa gidan tunda ya gama har yace min mutafi, ko kallonshi nayi alkawari ba zan sake nunawa na damu dashi ba da yardan Allah.


        Koda muka isa kaman mu ake jira, muka shiga......


               «»
     Ranar talata da dadare muka iso lagos a nan muka kwana, washi gari muka bar

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment