Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki ɗinki kamar kwarya."

Mikewa yayi shiga bandaki wanka yayi yafito yana tsaki dubi gidanki babu mara da bola, ji ban ɗakinki, wannan bazan ɗauki raini da kazanta ba, zan shigo an jima ki faɗa min waye munafiki shima kumaki shirya masa dan bazan miki tawasa ba,"

Fita yayi daga ɗakin ya koma ɗakinshi wanka ya sake, sannan ya shirya cikin kananun kaya, yana murmushi ɗakina yashigo yanda yabarni ina nan a gurin, ko kayana ban saka ba, ya daka min tsawa da cewa.
"Tashi kibani abinci matsoraciyar banxa kawai"


Jikina na rawa nasaka kayana nafito nashiga haɗa masa abinci sannan na shiga kitchen naɗauko kunu aya, har lokacin jikina baidana rawa ba, "Ki ɗiba ki kawai jarumar mata wacce take iya ɗaukar lalurata bake da rashin.kunya yayi miki katutu ba."

Filet na ɗauka nasa mata malmala biyu sannan na, saka miya a wani karamin bowl, tire na ɗauko a kitchen na kai mata sallama nayitayi bata waje can naji muryanta tana waya kuma cikin kuka ban tsaya tsintar kome ba na shiga ɗakin da sallama ɗago ido tayi cikin rashin mutunci tace.
"Aha kashe zan kiraki hajja"

Mikewa tayi cikin cijewa tana ya tsuna fuska babu kaya a jikinta ajiye tiren nayi na juya cikin sauri sabida yau dai Mugun gani nake, "Kee!!!"

Tace min cak na tsaya gabana tazo ta tsaya runtsa idanuna nayi cikin matsanancin kunya da faɗuwar gaba muryantane ya daki kunnena tace..
"Allah sarki da alamun dai aiki kikazo yi a gidan nan da gadin gidan ko, koda yake ai shima ya faɗa min sabida ƙyalƙyal banxa ya kwasoki ga mace har mace, tsakaninta da miji, sai hoto kinga yanda yake min kuwa salon kwanciya iri iri, gashu har ce min yake da yasan haka nake da zaki kamar zuma da babu shi babu karo aure, dan yace idan ya kusanceki kaman yana ruftawa ram...."


Tureta nayi na fita da gudu ko kallonshi banyi ba na shige ɗakina na rufe kofana tare da fashewa da kuka, sai da nayi yq isheni kafin na fara nazarin abubuwa wanda karshe na rasa amsarsu Aunty Hajra na tuna kawai sai na ɗauki waya zan kirata wata zuciya ta kwaɓeni dole na hakura amma har dare babu alamuna,


Ganin yanda nafito ina kuka ya shima shareni yayi cikin gida, Umma kuwa sai jajena take,


Bayan sallar magrib suka haɗu a falon Umma aka sake gaisawa tare da masa jaje, nan suka rufeshi da faɗa akan abinda ya faru nan Aunty balki take faɗa masa halin da nashiga, sosai jikinshi yayo sanyi ɗan fushin da yake dani ya manta, kiran sallar Isha ya fitar dasu, bayan sun dawone ya keɓe da Umma yayita bata hakuri murmushi tayi sannan tace.
"Ni baka min laifi ba Matarka ce zaka nima yafiyarta."

Sun jima suna tattaunawa kafin ya shigo ganina A falo yasa ya shigo tunda yayi sallama na amsa ban sake kallonshi ba abu uku suka haɗu min lokaci ɗaya kunyarshi, tsoronshi, da uwa uba haushinshi, wato nice ma yake ruftawa dani, hmmm.


Magana yayi naki kulashi yayi juyin duniyar nan na kulashi amma naki da ya takurani kuwa kuka nasaka masa dan dole ya kyaleni ya leka kan denni ya hango wasu kulolin abinci mikewa yayi yaje ya zauna zai fara ci yace.
"Zaki zo kisa min ko sai nazo da kaina"

Jikina narawa naje na,zuba masa, faten dankali turawa wanda yaji kifi bushashe da nama nayi chop ɗinsu kanana, sai, zoɓo,

Ina gama zuba masa Khalil yayi sallama goge kwallana nayi dan matukar ya gani zai tuhumeni da Mummy wayasaki kuka, dan haka yake min duk lokacin da yaga ina kuka, kitchen na shiga na ɗauko kwandon abincin Umma nace.
"Muje kaci naka sai ka kai mata nata."

Ja masa kujera nayi ya kalle Baban yace.
"Abba barka da dare." bai amsa ba ya jinjina masa kai sabida ya cika baki da loma (lolz)


Abincin na,zuba masa sannan na ajiye masa zoɓonsa nima nazuba nawa mukaci, kaman an jefota muka ganta a kanmu kallo ɗaya nayi mata a raina nace.
*Sai narama nima,*

Abinci na ciko a cokali nakai masa baki ba musu ya kuwa buɗe,, mikewa khalil yayi da abincinshi ya koma falo hankalinshi na kan tv, bata ce uff ba nima kuma bance ba, tsul na koma kan cinyarshi na shiga tura masa abinci sannan na ciko kofi da zoɓo na bashi, juyawa ina kallon shi itama ina kallon mamakinta karɓan kofin nayi na sumbaci bakinshi irin na fashion ɗin nan.....


"Babban abu kazan kazan ni zaki nunawa karuwanci......"


Game Ove👌


🙆😱 Tohfa gidan Imamu ana zuba kishi da kirsa kenan ko kuma kawai shirmena nake am sure that zaku cigaba da zubo min dubun dubanta vote ko👌😹
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*

     *_Chaiiiiii Toh bari mu gani ko xan kai labari_*

*:~•38*
Not editing
         Zanga zanga suke abinda ya ɗauki hankalin yan jaridun kasar baki ɗaya bama iya su ba, har dana ketare, irinsu CNN, DW,France24h, Aljazira hankalin duniya ya sauka akan abinda ke faruwa, yayinda aka shiga yayata fuskarshi a talabijin, abin bai tsaya ba sai da aka shiga turawa kafar sadarwa internet, kafin kace kobo garin Liverpool ya hautsine, take aka shiga muhawara da lauyoyin kare hakkin bil'adam tare da kungiyar Amnesty international abin yayi tsamari, su Ya Abubakar daga abuja aka kirashi ya kunna tv,   falonshi ya shiga ya kunna yana ganin Yanda mazauna England suke faɗar albarkacin bakinsu....

                Nikuwa babu abinda ya sauya dan tunda na farfaɗo naki magana da kowa sai kuka,...

       «»

      Zaune yake sun sanya masa camera ta koina yana addu'a bayan ya idar da sallah, mikewa yayi ya naɗe abin sallar yana koma mazauninsa ya zauna duk ya fita hayacinshi babu duka babu zagi bincike kwafkwaf kawai suka tasashi dayi shi kuma iya gaskiya san yake faɗa musu, shigowar magajin garin london tare da lauyoyi uku, da wasu alkalai guda bakwai yaja duk aka mike, har shi mikawa shugaban bincike yayi wani takarda, yasa hannun sannan ya mikawa masa tare da kallonshi yace.
"Muna matukar baka hakuri abisa kazafin da aka maka, karka ji wani abu a ranka shima wanda yayi maka sharrin mun kamashi ynx, gashi ana nimanka a can london kayi hakuri da abinda ya faru."

     Murmusawa yayi sannan yace.
"Babu kome wannan ai jarabawata ce, kuma Allah ya kaddara sai haka ya faru dan haka babu kome ai haka yasake bani wani ilimi na zaman duniya nagode."

      Yana faɗin haka suka fito agogonshi da wayarshi haɗi da wallet ɗinshi suka bashi cike da borin kunya.
      

      Suna fitowa daga cibiyar bincike ana shigo da Mr Moris, sai ikirari yake da cewa...
"Matukar Ina raye sai na ɓatawa musulunci da muslmi suna a duniya sai na goga muku bakin fenti, idan banyi haka ba ban cika cikeke bayahude ba."

        Gizgiza kai Imamu yayi dan yasan moris yayi zurfe a kafirci, wata irinta alfarma aka buɗe masa ya kallesu nuna masa suƙayi ya shiga babu musu ya shiga,airport suka tafi dashi daga can suka wucce garin london inda, musamman aka ajiye masu tarɓanshi.

      Daga nan aka wucce da shi, fadar preminister, inda ya haɗu da jakadar najeriya dake nan london ɗin, da wasu manyan malaman jami'o'insu, kai abin ba'a cewa kome ga sojojin yan naija da yan sanda da likitoti da sauran wasu manyan ma'aikata da suke aiki dasu,

       Gaisawa sukayi daga nan aka shiga tattaunawa akan sharrin da aka masa, kusan hakuri akaita bashi, daga karshe suka ɗauke shi, aiki a babban kotun dake nan london, da kuma dawo dashi cikin garin london a madadin da, da yake Liverpool, har karatunshi, sannan aka kara masa da Peace Ambassador, duk wannan abinda ke faruwa ana haskawa kai tsaye a gidan Tv Bbc world, da Cnn, ganin irin cigaba da Imamu yasamu Yan uwanshi babu wanda bai zubda kwallar farin ciki ba, sabida anso a wulakantashi lokaci ɗaya Allah maji rokon bawanshi ya juya al'amarin,

            Shiru Umma tayi  kafin ta furzar da iskar dake bakinta kafin tace..
"Karku nunawa A'isha wannan kubari itama tayi nata abinda taga ya dace, ina son yasan da tana da muhimmanci a rayuwarshi, addu'a aka sake masa inda aka cigaba da raba abinci da saukar alkur'ani...

        A can kuwa bayan an gams meeting ɗine aka kaishi sabon gidan da aka bashi, kusada jami'ar Oxford, gidane irin wanda bature ke kira da Mansion dan daga wajen gidan kana gani basai ance maka ga yawan kuɗin gidan ba, dan gidan samane, irin wanda yake manne da kasa, ɗakuna huɗune a gidan sama biyu kasa biyu, sai ta bayan gidan inda aka kewaye gidan da rumfa da wajen wanka nan ga kuma gurin wasan yara, gidan zagaye yake da flowers kome na gidan ba laife, sai ɗakunar, wanda aka zuba musu wasu gadaje na musaman ga banɗakinsu ma gari gudane, zaga gidan yayi sannan ya shiga niman hanyar da zai bar garin dan bayajin zai iya kwana bai saka Mahaifiyarshi da Yan uwanshi haɗi da mahaɗin rayuwarshi ajiyar zuciya ya sauke, sakamakon tuna katotuwar guguwar rigimar da zai tarar a gareni.😂

      Fita yayi daga ya kalli drvn shi yace.
"Airport zaka kaini, ina son zuwa liverpool"

       Tafiyar mintina goma ya kaisu daga can sukayi tafiyar mintuna arba'in, koda ya isa mkrntshi ya fara zuwa inda yayi godiya ga ɗalibai da malamai.
   Haɗi da inda yake aiki, sosai yaji daɗin bajintar da suka masa, tare da musu sallama, ya dawo gida kafin nan gidan dr Halima yaje yasamu sun tashi an maidata cikin london, sannan ya isa gida, su Baban Husna da yan unguwar sukayi masa jajje, daga nan ya shiga gidanshi, wani babban mota ya ɗauko aka kwashe masa kaysnsu, har ya dawo Hauwa bata iya ce masa ashe abinda ya faru kenan sai ma ce masa tayi taci bashin kaza bata biya ba, babu yanda ya iya yabiya, a dare ko kwana basuyi ba suka bar kasar zuwa naija, ya horu kafin  ya taso ya faɗawa Yan uwanshi.......

     «»

    Ranar juma'a wanda yayi da kwana na uku da dawowa daga asibiti, naga gidan sai walwala suke, nikuwa tun kafin nadawo aka gyara min part ɗina da nashi, na hauwa kuwa ba'a gyarq ba dan bata bar key ba, ina kwance sai ga Fahima da Aunty bilki wai ko ina da wani abu da zanyi su tayani kallonsu nayi kafin nace musu.
"A'a babu abinda zanyi" na faɗa musu araunane,

     Aikuwa suka ce yau girkina suke son ci, babu yanda na Iya dasu dole na shiga kitchen ashe su sunyi hakane dan na tarbi miji🙈🙊 ni kuwa sakarya ban sani ba, take na fito da doyar da nazo dashi, guda biyar aka ferre sannan aka fito da babban tukunya aka hura wuta  a kitchen ɗin waje, kallon doyar sukayi cike da mamaki wai aunty balki tace.
"Matar Mi zaki mana da wannan doyar."

           Murmusa mata nayi sannan nace.
"Sakwara!!"

        Babban turmina nafito dashi na zuba ruwa zan wanke fahima ta karɓa ni kuma na shiga kitchen da biro da takarda na fara rubuta abinda nake bukatar yin miya dashi,
         Egusi, egu, alayahu, ganda, fresh  meat, stock fish, dry fish, cry fish,, sai kayan miya nasan akwai dan jiya naji Umma tana cewa akwai kayan miya da ɗanye nama da kaza wanda aka yanka toh an rabawa kowa har dani ba lallai sai nasaya a kasuwa ba,

         Dakina na nufa na ciro bandir ɗin yan ɗari biyu, kusan dubu ɗari da ashirin ya bani daren da,zasu tafi ni kuwa naki karɓa shine ya buɗe, wajen ya zuba, nan na ciro kusan dubu huɗu, nafito na mikawa fahima bayan nagoge nama,

           Da sauri tafita, ni kuma naje na wanke nama na yanyanka, nasaka a  tunkuyar nasaita lokaci, sannan, nafi muka cigaba da aiki, kallona Husaina tayi tace.
"Ba zakiyi mana drinks bane,"

    Mikewa nayi na tuna ina da aya shi nafito dashi na wanke, na ɗauko bushashiyar citta, can na tuna Umma nada ɗanye hijab ɗina na janyo na shiga cikin gida, ina zuwa nasamesu a falo suna tattaunawa sosa kai nayi zan juya tace .
"Idan wani abu kike so jeki ɗauka duk nan yan uwane da Yayun Mijinki."

       Gyaɗa kai nayi na shige kitcheɓ ɗinta na ɗauko cittar a firj na fito nace..
"Umma citta nake so na ɗauka "

     Jinjina kai tayi min, sannan nafita cikin jin kunya Ya Ali yace.
"Ummana nima don Allah kiyi min addu'a nasami kyakyawan mace mai hankali yarinya karama irinta Imamu"

       Dariya suka saka masa tare da cewa.
"Kaji kunya, geme geme kake maganar nimar aure ina Zaka saka Fahimar wanda kake cewa nan da shekara biyu masu zuwa Insha Allah zaka aurar da ita." Inji Ya Abubakar kenan.
"Kalan yaja mana yaki da Ummu khairi ina zaman lafiya, tace mana munafuka ni rabani da hidimar karin aure nan Hajja Yakolo har annamimai takira akan auren Yarta da Imamu babu ruwana,"Cewar Abba lawan kenan.


     Karfi da yaji sukq ki bashi goyan baya😂 Kuma yana da rufin asirin da zai rike mata hudu, kowa tsoron kar akirashi da munafiki yake😂 sam sune basuyi ra'ayin Aure aure ba, amma idan akace namamajo ai sai Imamuna, Injini da faɗa nakan kirashi da J.F.,.

               
    Ina,zuba cittar aka kai min markaɗen shi, namar da ns ɗaura yana nuna sai ga fahima ta dawo juye tafashe nayi na wanke ganda na zuba, stock fish kuma na wanke na zuba masa ruwan zafi, dry fish shima haka na masa,, wanke kayan miya mukayi inda Fahima tashiga nikawa a blender, ni kuma na fita muka cigaba da aiki tana gamawa takirani na ɗauko babban tukunyar tower na wanke nazuba manja, na soya da albasa, sannan na zuba kayan miyana da namar suka shiga tafasa, nan nabisu da tafarnuwa, da garin citta,, a waje kuwa  gyaran alayahu suke, da egun,  a ciki kuwa ganda na nayi na juye stock fish suma na bashi mintuna biyar, yana nuna shima na sauke na maida hankalina kan miyar kacokan, murmushi nayi ina godewa Innaji yanda ake kai ruwa rana dani kafin na shiga aikin gida,  garin egusi na kwaɓa a wani roba da ruwan ɗumi na zuba, sannan ajiye a gefe nafita ganin doyar,.
Ganin Aunty Balki nayi da matasan gidan harsu huɗu zasi daka sakwaran, komawa ciki nayi nasamu miyar tayi na zuba gandar da Kifin da kuma egusin na kara ruwa na rufe, kunun ayar naje muka tacce na ɗibawa Umma sai kallon jug ɗin nake haka kawai sai naji kwalla ya cika min idanu, a hankali nace.
"Allah sarki farin cikin rayuwata,"

Kallona suka tsaya yi, mikewa nayi na ɗauko wani jug ɗin nazuba nakai frig, na bawa fahima suga tazo tazuba ɗaurewa nake amma kuka nake a ɓoye dakyar na haɗa miyar nafito da ɗari biyu suka sayo laida aka shiga daka sakwarar, ana juyewa mu kuma muna malmalawa a laida, saura kaɗan mugama na koma ciki nafito da kular da,zasu zuba da kuma wani wanda shima tsintar kaina nayi dabada wa, azuba masa nashi,


Kukane ya taqo min nace musu bari nayi wanka ina fitowa ina shiga na fashe da kuka, sai danayi me isata sannan nayi wanka lokacin biyu saura nafiti nayi sallah, sannan na saka wata english ɗina mai ruwan zuma, riga da skirt ɗin na,zauna na buga ɗaurin A'isha buhari na shafe jikina da humra,


Tozali na saka a idanuna sannan na yafa gyale babba nafito, wajen nasamuhar suɓ wanke kome har kitchen ɗin, miyar na shiga,zubawa babbar kular cikin gida aka ahiga dashi sai ɗaya akakai gidan Baba shatima. D'ayar kuma aka wucce dashi gurin Umma, sai ɗaya kular na matasan gidan sukan waje aka fitar dashi, sai nasu Aunty balki wai nazo naci nace na koshi, sun fahimci hankalina yanxun yana gurin mijina ne basu dameni ba suka ɗauki kunun ayarsu da ta Umma suka tafi, tv na kunna na maidashi sunnah tv dake duk mazan basu dawo masalaci ba, nima gyara kwanciyata nayi bacci da gajiya suka rufeni...
...




«»
Karfe ɗaya da rabi suka dira a maiduguri inda aka tura jami'an tsaro tarɓanshi, lokaci guda Imamu ya zama mutum mai daraja a yanki arewa maso gabar,


Daga can suka nufi gida, biyu da mintuna 55 suka iso yobe, tare da manyan mutane, gidan Governo ya fara zuwa, aka tawo da hauwa gida, tunda ta iso babu wanda tayiwa magana, ɗakinta ta wucce taje ta zauna tana mitar tana jin yunwa.

Bayan sallar la'asar ya shigo gidan dan har lokacin ina bacci yan sannu da zuwa da jajje suka ragu nan Umma ko fuska bata bashi ba, a ranshi yace.
*Umma ai nasan logonki A'isha ce ina biyar da ita naki me saukine*

Dakyar yasamu yafito ya,shiga sider ɗinmu a tsaye ya ganta tana ɓata rai kallo ɗaya yayi mata sannan yace.
"Lafiya?"
Tayatsuna fuska sannan tace.
"Yunwa"

"Kije wajen Umma akwai abinci a gurinta idan kuma bai miki ba kishuga kitchen ki dafa da kanki" yana faɗa mata yayi cikin falonshi ban ɗakin ya shiga yayi wanka sannan ya sauya kaya, kai tsaye falona ya shigo,zuba min ido yayi har ya iso inda nake, kallon ɗankwalina sa ya zame yayi gyara min yayi sannan yasaka hannunshi yayi sama dani, ina cikin bacci naji kaman ana yawo dani asama ban buɗe idanu ba, naji an ajiyeni, kamshin turarenshi naji a hankali na buɗe idanu fess akanshi tsaki nayi na gyara kwanciyata, ji nayi an daki bakina buɗe idona nayi sosai ganin shine bansan lokacin da nace.
"Aikan na shiga Uku Jarababe Fitinanne ya dawo."

Gyara kwanciya nayi na cigaba da baccina dan har ciwo kaina yake, kallona yayi yana murmushi, yace.
"A'isha duk ɗokin danake dan na ganki nine jarabbabe fitinanne,"

Buɗe idanuna nayi na tashi na,zauna cikin tsiwa nace.
"Eh ɗin an fada maka kaga malam ni nagaji ka shafa min lafiya, wani laifi nayi na cancanci sharewarka wata kusan shida, bazan zauna da ka..."

Kukane yaci karfina, da kuma katse min abinda zan faɗa ta hanyar sumbata, kuka nacigaba dayi ina dukarshi ina ya kushinsa, sabida mantawa dani da yayi, mai dani yayi kan pillow, inda yayi nasaran haɗa hannuwana cikin nashi tare da zuba min nauyinshi, sosai yake biyar da bakina kuma babu alamun tausayawa, dan dazaran nayi wani yunkuri cizone haka nayi lakwas,bakina ciwo dazafi suke min ɗagowa yayi yana kallon fuskana yace.
"Idan Mutum baida Karfin kwatar kanshi rashin kunya bana shi bane, yarinya nayi miki tanadi na musaman amma kafin nan bari naji da bakin tsiwa wanda baisan kome ba sai rashin kunya."

Wannan karon kan bansa ya akayi ba amma nasan nayi kewar *My Man* nima dan a zauna lfy ban ɗaga masa rigima ba, nan dai na biyeshi, muka shagalta da farantawa kanmu wasa wasa sai ga imamu yana shirin wucce gona da iri, dan sai da ya kaini kwalolowar inda bazan iya kai kaina ba,

Ina ganin aka turo kofa domin kaina na kafaɗarshi, murmushi nayi a raina nace.
*Kin zo daidai gurin*

Janye fuskana nayi nakai dai dai kunnenshi nce.
"Pls kacire min rigar yana hanani jin daɗi"🙈🙊

Kayya baisan gadar zare bane yasin sai gashi yayi yanda nace ina satar kallon ta yanda take lekko mu....

*Hmm ynx zaki danasanin leke mutane, tunda ɗabi'arkice*

Sashi nayi yayita biye min ina cewa cire kasa, abinda nasan ko mi zaiyi min bazan iya ba shi nashiga masa, wani abu baki bazai iya faɗarshi ba, iya tsiya nayita sashi yana biye min sai jinta mukayi............



😹😴🙈😁😂 Maganin me leke.........
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
      *Wattpad:Mai_Dambu*



*A koda yaushe karka yarda da Nasara ka rungume faɗuwa nasara tana biye da ita da zaran ka rungume nasara tohfa.......*

*:~•40*😎 Finally page😜

      Bala'i tacigaba da yi, shi kuwa kasake yayi idanu a buɗe, yarasa yaushe haka tafaru, a ranshi yace.
*Wato Nana ta inda tafi kauri kenan niman rigima Insha Allah bazamu bar kasar nan ba sai na gyara min zama*
Tureni yayi ya tsuke fuska zai rufeni da faɗa maida shi nayi ya zauna na kuma kara masa wani sumbatar datafi nada, hannuna na tura kirjinshi ganin zan kunna masa wuta yayi karfin halin zareni daga gareshi, tare da daka min tsawa.

"Ke!! Bana son ranshin hankali kinsan kina sona kika gaza ɗaukar lalurata, ita da take ɗauka zaki wulakanta min ita toh ahir ɗinki, Matata ce ita kuma matar da take kwantar min da hankali koda wasa kika sake yunkurin kuntata mata toh wallahi zan baki mamaki " tsaki yaja min yayi gaba da ita tare da sakala hannunshi akan kugunta.


Basan lokacin da nayi wacakali da kayan kan dennin ɗin ba, watsar da kome nayi na shige ɗakina,


Nayi kuka kamar zan shiɗe, tun daga ranar imamu ya ɗauke min wuta bana gane masa ko nayi abinci baya zuwa ci, ko da nakai masa falonshi tsawa yake buga min yace nafita masa dashi, sosai ya fita harkana a ɓangarenta kuwa kaman ta,zuba ruwa akasa sabida farin ciki da murna, kaman yanda takeso itama ya tsotseta haka yake mata ai nan haukar tayi tsamari, haka kawai zata shigo min ɗaure da tawol kanta a jike dake itama tana da gashi, amma ni nafita yawarshi da cika da tsayi, hmm a cikin kwana biyar zuwa bakwai naji bakin ciki kaman zanyi hauka, gashi ko ɗan lekowan da yake da yanzun duk ya daina, idan nazauna sai na rasa yanda zanyi da shi, toh taya zan iya ɗaukar laluranshi, nima ina son na masa abinda zai daina jin haushina,



Karewa nayi nakira Aunty Hajra, muka gaisa sannan nayi shiru can tace min.
"Auta lafiya kuwa faɗa min mike faruwa."

Kuka na fashe da shi sosai narasa ta inda zan faɗa mata sai na kashe wayar,

Hankalinta a tashe takirani tace.
"Kunyi faɗane dashi"

"A'a" nace mata,
Shiru tayi dake tana da matukar hakuri ba kamar aunty zuby bace sarkin faɗa,...




3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment