Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damuwa buguwace kawai a cinyarta amma shima ba matsala zai warke." likitan ya faɗa musu.

       Godiya sukayi likitan nabarin gurin sai ga Innaji da Ya ishaq suka iso, godiya sukawa Imam Usman, sannan suka shiga ganina, shima Mutumin da ya bigeni,  hakuri ya basu.

         Bayan yaga halin da nake ciki yayiwasu Innaji sallama ya dawo gida,

               Mutumin da Ya bugeni kuwa, ya zauna har na farka yana ganin farka gurina yazo sannan yace.
"Preety sannun ko ya jikinki Allah yabaki lafiya."

        Sun innaji sannu sukayita min sallama yayi musu akan sai dare zai dawo, kafin ya tafine ya kalle ni yace.
,"Toh bazaki faɗa min sunanki ba nidai sunana Asad,"
     dake mutum ne me bakwarce tuni ya samu shiga cikin zuciyan yan gidamu, ni kuwa ko kaɗai bai burgeni ba dan akalla shekarunsa zaikai talatin da bakwai, kusan Imam Usman zai bashi irin shekaru hudu, dan shima bazai wucce, 45 ba, kin kallonshi nayi na kauda kaina, sabida irin kallon da yake min haushi yake bani,

      Ina jin lokacin da Ya Ishaq yace masa.
"Sunanta Aisha amma muna kiranta da Naiha,"

       murmushi yayi cikin nutsuwa yace.
"Nice name, sunan Mammyna sunan Yar autanmu suna me daɗi da daraja."

         kara jin haushinshi nayi na rufe idanuna, inajin yayi musu sallama ban buɗe idanun ba, balle yasan inajin shi.

        Asad Aminu Shema, ɗane ga mataimakin gwanar katsina, yana da kanne, maza da mata, kafin mahaifinshi ya zama maitaimakin gwana tsohun jami'in difulomasiyane, sannan ya zama jakadar naija a Zurich da Canada.

        Sannan ya ajiye aikin ya dawo mahaifiyarshi kuwa,lauyace mai zamankanta, kuma malamace a jami'an ɗan fodio,, Amma sun rabu da mahaifinsa. Kusan rayuwarsa a kasan turai yayisu amma mutune mai mutunci dakamun kai, Gashi tuzurune🙊

                 ......Da dare kuwa sai gashi sunzo shida mahaifinshi da kannenshi sun zomin da kayan dubaya, na ban mamaki sosai suke jana a jikina tare da bani wani irin girma na musaman, shi kuwa gogan sai wani lagwaɓar da kai yake, yana kallona, cikin wani irin yanayi sunkuyar da kaina nayi kaman zanyi kuka, dan ban taɓa ganin ana haka ba, sai ma kunya da ya kamani, shigowan Abbanmu da kawu Ubale, yasa na ɗago kaina sannun suka min, sannan suka shiga gaisawa hiran suka koma irin nasu na yan boko da kuma cigaban taɓangaren sha'anin mulkin, sun jima sannan Mataimakin gwana ya mike alamun zasu tafi, fita sukayi aka barni dashi, zuba hannunshi yayi cikin aljuhun rigarshi yana kare min kallo, can yakira sunana kaman me ciwon baki yace.
"Nai,,,,,ha, kin sace min zuciyata.."

        Yana faɗin ya tsuguna a gabana yace.
"Kallo ɗaya danayi ya haifar min da soyayyarki don Allah karki k'i amsar soyayyata zan iya shiga gararin rayuwa, Pls kisoni ko ɗan kaɗan ne, inyaso zanyi maneji da wanda nake miki,."

       Miqewa yayi sannan ya sumbaci goshina yace min.
" Akwana lafiya kiyi mafarkina."

....
Fita yayi cikin kasaita murmushi nayi a raina nace.
"_Nasamu miji irin wanda nake mafarkin samu."

  Lokacin da iyayenmu suka fita Mahaifin Asad Alh Aminu Shema baiyi kasa a gwiwa ba gurin nimawa ɗansa nima ba cikin mutuntaka Abbana da Kawuna suka bada aurena amma an bari sai na gama karatuna.....


           *Matar Usman*
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO 🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


      ~Na~
           *Real Mai Dambu Ce*

    🌹🌹👳
     *MATAR MALAM*
                       🌺🌺👳


*:~5*
          Murmushi na sake masa mai narkar da zuciya girgiza kai yayi cikin farin ciki ya lakuci hancina yace.
"Don Allah Naiha karki juya min baya dan mutuwa zanyi idan haka ya faru dani,"

                Juya idanuna nayi cikin son burgeshi , sake gyara tsayuwta nayi sannan nace.
"Mine bazaka taɓa mutuwa ba sai mun tarawa Mamani, jikoki masu kyau da ban sha'awa ko my mine." Fari nayi masa da idanuna, wanda yasake susutashi, kaman ys goyani haka yake ji kaman  ya cinye ni sabida son da yake min, ina alfahari da haka domin  samun  irin Asad babban  sa'a ce fa duk  ya mace wacce tasan ciwonta gashi cikin sa'a Ubangiji ya bani shi ba wayona ba balle dabara, murmushi nayi  sannan nace.
"Ya kamata ka koma gida kaga yamma tayi kat a nimeka."
      Na fad'i haka ne cikin  sigar tsokana, hararata yayi shima cikin  tsigar tsokana yace.
"Ai bawa abu bane k'insan ni d'in d'an farine kinga kenan ba wani abune dan an nimeni " d'aga min gira d'aya yayi shima. G
Tura masa baki nayi cikin shagwab'a  ina bubuga kafata, tallafar kanshi yayi cikin wani irin shauki, wanda baisan yana da ita ba, sai da ya kasance dani, 
          Babu abinda ya shagalatar dashi kaman yanda jikina ke girgixa, jinjina kanshi yayi sannan ya tako har gabana, dai-daita kanshi yayi sannan ya ɗan sunkuyo, da fuskarshi dai-dainawa har ina jiyo fitar numfashinsa, ja da baya nayi, sakamakon hango Imam Usman, wanda duk abinda mukeyi akan idanunshine, kauda kanshi yayi daga garemu dan makarnace ya ganmu, wuccewa yayi, yayinda na hango tsanata akwance cikin idanunshi ɗaga kafaɗa nayi sannan nayi maza nacewa.
"Malam sai anjima, ka gaida Daddy, da Mamani idan kunyi waya zan shga daga ciki."  
      "Toh princess muje kirakani tunda kinga masu kula dani sun iso tun ɗazun." yace min,

        Murmushi nayi cikin jin daɗi na wucce gaba yana bin bayana har na buɗe masa motar nace.
"Ka gaishe da gida maxa antaya ciki kusanbaɗi hanya,"

       Shiga yayi tare da banka min harara, yace.
"Ba sai kimin koran kare ba, nima nasan hanya malama maza fecce."
          "Oho dai kai kauce."  Nace masa, dakyar yabar kofar gidanmu, yana tafiya, nima na juya da niyyar komawa cikin gida, nayi karo da Baby tanaɗe hannunta a kirji tana bina da yaudararren murmushi, cikin rangaji da takun kasaita nazo ns raɓa gefenta, zanshiga gida riko hannuna tayi cikin raunaniyar murya irinta mayaudara, tace.
"Naiha don Allah kiyi hakuri bazan sake ba, sharrin shaiɗane,"

       Rike haɓana nayi nace.
"Haba dai? dagaske sharrin shaiɗane yasaki kulla min sharri well anyway, tunda hakane kije dan yanxun ma bansan da wani nufi kika dawo gareni ba, kije bana son ganinki yanda kika buɗe baki kika kulla min sharri, Allah natuba me zaki faɗa min na yarda dake, kije bana kaunar ganinki dan kina fama min abubuwa da dama arayuwata nagodewa Ubangiji da yakareni da ban taɓa ɗaukar shawararki ba balle ya kaini dayin danasani mara amfani."

        Ina faɗin haka na wucce nabarta cike da mamaki, kwafa tayi sannan tace.
"Indai ina raye sai nasaki zubda kwalla muje zuwa shege kafasa,"

          Tun daga ranar ban sake ganin kafar baby ba,ni kuwa na tattara kashinta na zuba a kwandon shara.

          *••••••°°••••••*
Rayuwa ta mike min sosai nake tsula tsiyata babu wanda yake taka min burge har na shiga ss3 Ramla ita kuma ta gama, koda akazo sake jarabawa Asad ya biya min kuɗin Neco d waec, koda Iyayenshi suka sami labarin zan zana jarabawa sunyi farin ciki da haka, sai ma zuwan da sukayi nima masa aurena inda akayi kome cikin girmamawa da mutuntawa,

           Wata biyu tsakani muka fara exam, cikin nasara muka fara waec, wanda ya ɗauke mu  tsawon mako biyar (wato sati biyar kenan,) muka gama sati biyu tsakani muka fara Neco, bani da lokacin kaina, a cikin wannan yanayin har aka kawo kayan aurena, hmmm kusan abun mamaki, Yayuna mata da akayi aurensu kwanaki kosu basu sami irin kayan da nasamu ba, domin abin ya baws kowa mamaki, ga Ramla wacce ido da ido ta nuna min.Yan ubanci taya zan sami irin wannan kayan, abinda yaja har Innaji tayi mata mugun duka, tare da Yaya ishaq, bana gida suka mata duka amma da safe yar magana ce wacce baifi ayi dariya ba, take ta juya min maganar zuwa wani fassara nada ban ce mata nayi.
"Yarinya tare dake zamu zauna a gidan Asad kinga babu wanda zai damu idan kina tare dani, kafin kema Allah ya kawo miki mr Rigth ɗinki wanda yafi mine haɗewa da jin gayu, amma ba zance wanda yafishi kyau ba."😝 na zaro mata harshe ina gwalo, shiru tayi can nasake takalota nace.
"Aunty Ramluv me yasa baki ga kayan da aka kawo ba, muje ki ɗauki wanda yayi miki kinji."

      Wai ni, dole sai nasata tasake dani, ga wani abun mamaki shine kawanceta da Baby can you imagine ace kawata kuma abokiyar gabana itace best frnd biological sisterna, mikewa tayi cikin azama ta ɗauke ni da wani irin mari wanda yayi sanadin kosan dake hannuna ya faɗi, dafe fuskana nayi cikin yake, nace.
"Tabbas kin sauya halinki daga Ramlatu zuwa ta fasashiya, meye laifina me kikeso na baki wallahi zan bar miki kome nawa indai bazakiyi fushi dani ba don Allah yar uwa karki juya min baya," abinda ta faɗa yayi matukar girgizani ashe bani ɗaya bace abin ya bawa tsoro zuwa mata ido nayi hawaye na sauka A idanuna, tace.
"Ni na tsaneki Aisha bana kaunarki ke jinki wata dan kinsami D'an mataimakin gwana shine kike jinkanki you pass everybody ko, bana kaunarki nafi kaunar mutuwata akanki kuma ki zuba ido kiga abinda zai faru ina faɗa miki dani kike zance."

      Daman makaranta zan tafi ɗaukar jakata nayi nafita daga gidan hawaye na zuba daga idanuna, tafiya nake kawai, har na iso kofar gidan Imam, kallona yayi sannan ya buɗe motarshi ya shiga, ganin hawayen dake zuba daga idanuna yasa tafasa tada motar yafito,kirana yayi da cewa.
"Aessh!!!" tsayawa nayi cak sabida yanda ya kira sunan ya taɓa min zuciyata ainun, ji nayi duk wani kafan sadarwan jikina ya tsaya a lokacin domin sunan da yakira ya girgizani, takowa yayi har inda nake, ya ciro hankin daga alhujun rigarshi ya mika min,kaina a sunkuye na amsa, sannan na wucce ko godiya ban masa ba.

          ........A gida kuwa bayan fitata Ya ishaq ya fito daga ɗakinshi yana kallon Innaji cikin ɓacin rai yace.
"Kinji abinda tace kuwa, haka zamu zuba mata ido hassada muraran fa kenan yau da Naiha ce bata sami miji ba wallahi nayi imani da Allah bazata tsangwami Ramla dan tasamu miji ba Amma ita qarara ta nuna batayinta."

         Kwallar da suka taru a idanun Innaji ta goge sannan tace.
"Idan baka karya min Ramla ba tabbas baka haifu a cikina ba ka gyara min zamanta sosai."

          Komawa ɗaki yayi ya ɗauko dorina, yafito ya shiga ɗakinmu lokacin suna tsara, yanda zasu cutar da farin cikina, batare da tasan da zuwanshi ba ya rufeta da bugu tako ina tana ihu tana kome sai da ya fasa mata jiki sosai sannan yafita daga ɗakin Innaji itama ta shigo da muciya ta rufeta da bugu ta ko ina sai da suka mata liliss sannan innaji tace.
"Kika kuskura naji labarin kin cutar da Aisha toh na yafeki duniya da lahira nacireki a cikin yarana, Yarinyar nan tayi miki kome me kike so da ita kuma, toh koda wasa." Tana gama faɗin haka tafita,

     duk abinda ake akunne Baby kashe wayar tayi sannan tasake kiran Ramla cikin kuka ramla ta ɗauka zata faɗa mata abunda ya faru da kadatar da ita tayi sannan tace.
"Listing to me carefully, kina son Asad?"
     Jim tayi sannan tace.
"Nop, nidai kawai ina jin ba daɗine idan naga abinda aka kawo mata."

         Ran babyne ya ɓaci toh ya zatayi ta cusa min ɓacin rai tunda ramla ba son asad take ba sai kawai yanke hukuncin tusawa Ramla banxan tunani akan asad kasa da murya tace.
"Wallahi nayi imani kishin Asad kike kuma alamu ya nuna sonshi kike, karkiyi wasa da damarki ni nan zan miki hanyar da zaki mallaki Asad amma sai da amincewarki idan kika bari aka saka auren Naiha da Asad toh har abda zaki zauna a gida babu miji karshe ma bazaki samu irin Asad ba, matsalar gidanku, ki barshi a hannuna Insha Allah kin mallaki kowa har Asad ɗin........"

       *Shin me kuke tunani game da Baby,*


       Pls nd Pls Share.........



OFFICIAL MAI DAMBU CE👌

    
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

   

🌹🌹👳
    *MATAR MALAM*
                           🌺🌺👳

        *Writtern*
                   By
         Mrs Fulani🐄
                  

_Ina kike Ummul khairi ga shafin nan dake kawai da kuma jin daɗinki_👌💋❤

*:~4*

    Kafin asallame ni kuwa kowa yasan irin Son da Asad yake min, basan yanda zan kwatanta ba, dan Mahaifiyarshi sau uku tana zuwa dubani tare da alkhairori na ban mamaki, take wani jin kai da wani ɗagawa ya karu min, makarantar da nake, Asad ya cireni ya maidani makaranta mafi tsada, a garin katsina, waya kuwa Iphone+8 ne a hannuna, Ga Mamy ɗinshi musaman take haɗamin mayukan shafawa,da kaywn cosmetic, dalilina suka fara abota da Imam Usman, wanda ya tayashi murna da jin an bashi aurena,.

           Yau juma'a tare muke dashi a gidan Annah sai shagwaɓa naketa lafta masa yayinda shi kuma ya ɗaukw duk abinda nake masa dan bai damu ba sai ma karin farin cikin da yake ciki idan yana tare dani yakan manta da kome da kowa shi burinshi ya mallakeni shi ɗayanshi, ganin haka yasani nima naki bawa kowa damar da zai takura min sai shi, kuma nake cin karena ba bu babbaka a cikin zuciyarshi dan nasan nice kadai babu wata domin ya gina cikinta da kaunata, cikin sakalci nace.
"Mine ina son ice cream, da cake me chocolat, sai shawarma" na tanɗe bakina cike da jin kwaɗayin abinda na lissafo masa.

           Girgiza kai yayi cikin rashin amincewa da abinda nake so sannan yace.
"Second love, kiyi hakuri ba zaki samu kayan zaki da sanyi ba, asalima sai da Abba yayi min gargaɗi da bai yarda nasaya miki koda chewgun ba dan hak...."

           Bai kai karshe ba na miqe cikin jin haushi da hasala na ɗauki wayata na fita ko sallamar Annah banyi ba, sabida jin haushin abinda Asad yace min.

          A hanzarce ya biyoni yana bani hakuri amma fir naki kulashi ran yan mata ya ɓaci, bai fasa bina nima kuma naki sauraranshi, a haka har muka iso, layinmu, ganin zamu ratsa mutane yasa na juya nace.
"Ya isa kawai kaje gida sai ankwana biyo dan zamu fara exam kaga dole na maida hankalina akan karatu,"

           Gyaɗa kai yayi cikin rashin kuzari yace.
"Toh amma muje na rakaki har gida kinji ko baby doll" ya karshe maganar cikin zolaya dan yasan na tsani kace min baby doll, kusan haka yan makaraɓtarmu suke ce min, baby doll, wai ina musu yanayi da biebis,

               Tura baki nayi kaman na fasa ihu ina tafiya ina kunkuni shima bai fasa biyoni ba, haks muka ratsa mutane suna ganimu sai nunamu suke da yatsa, sabida yanda muka dace, Imam Usman kanshi a sunkuye yana gyara Yaronshi Khalif takalminsa, yaji Nura da Sayyed suna cewa ai hakane sai kaga yarinya tagama watsewa karshe ka ganta ta buge da auren mutumin kirki, kaga yanda ya mutu akanta wallahi da zatace yabata zuciyarsa da zai ciro yabata, sabida son da yake mata,,"

        "Manzon Allah s,a,w yace idan baza kufaɗi alkhairi ba kuyi shiru." Abinda Imam Usman yace musu kenan take suka kame bakinsu.

          *Usman Shehu Usman shine cikaken sunan Imam Usman, Yafito daga jahar Yobe, ɗan babban gidane domin gidansu malamaine, ciki da wajensu, shine ɗa na Takwas a cikin gidansu baya ga kane da suke binshi maxa da mata,Zan iyacewa gidansu ilimin addini da zamani ya same mazauni. Acikin gidan, mahaifinsu ya jima da rasuwa, amma kafin nan yana da mata huɗu yara goma sha takwas, maza da mata, Babba yayansu Muh'd suna kiranshi da Yaya Abba lawan, yana aiki a babban asibitin abuja, sai Mai Abubakar, yana aiki a N.N.P.C, suna kiranshi Yaya Sadeeq, sai Aunty Aisha, tans aure a maiduguri,Sai Aliyu malamine a state poly damaturu, sai Xubair, yana kasuwanci a fataskum, Sai Hafsa, tana aure a Benin,sai Khadija ta rasu, sai Masur,sai Imam Usman sai Umma hani, Fatima Hauwa'u, sai Yan biyu Hassan da Usaina, sai karamarsu Balkisu,

          Mata biyune a gidan ɗakinsu Imam su tarane, ɗakinsu Abba lawan kuma su biyarne, gidan akwai kyakyawan fahimta a tsakanin matan, sai suka ɗaura yaransu akan tausayi da jin kan juna, haɗi da girmama juna, babu raini a tsakanin junansu.

           Imam Usman aiki ya kawoshi garin katsina, Inda shima alkaline, sabida ɗan kimanin Shakaru 46 zuwa da bakwai, ya karanci harkan shari'a a france, inda yayi degree ɗinshi a can, sannan ya koma jami'a madina yayi degree nabiyu an fanni shara'ar muslunci,  bayan ya hada sai ya dawo gidan anan Abba lawan ya nima masa auren Zahira, tunda mahaifinsu ya rasu shi ya ɗauki duk wata ɗawainiyar Yan uwanshi, bayan shekara guda Yar kanwar Umminshi Janeesha tatada rigima ita idan bashi ba zata shiga duniya,

       Faɗawa Abba lawan akayi take, ya nime masa aurenta akayi bikin. Yanzun haka yaranshi biyu, Zahira har yanxun Allah bai bata ba, sai Janeesha ita kuma bata kula da yaran sai Zahira ubansu.

           _Wannan kenan_

           
        Har gida ya rakone sannan ya zuba min ido kafin yace.
"Naiha Am so sorry kinji ba zan sake ba,"
      Murmushi nayi sannan na rausayar da kaina nace.
" Ya wucce."




Pls Share.....

*Matar Usman*
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }

   

🌹🌹👳
    *MATAR MALAM*
                           🌺🌺👳

       

     
     
       *Na:Real MaiDambu*

         '''Shafin nakine Aunty Aisha kina magamtuwa ainun kana idanuna cike suke da kunyarki ga wannan shafin dominke'''

*:~6*

           Zuciyar Ramlane ya shiga kisima mata wasu abubuwa, amma tunawa da tayi da kashedin Innaji tayi maxa tacewa Baby.
"Kaiii bana bukatarshi nafi son farin cikin innaji akan nawa, don Allah ki fita daga sha'anina, haka zai sama min nutsuwa," kashe wayar tayi baki ɗaya tafashe da kuka, domin tafara hango buhun damu atare da banzan tunanin da baby ta cusa mata,

         Hmmm ina makaranta amma zuciyata cike take da zulumi, gami da damuwa haka muka gama exam nafito daman shine final ɗinmu,

       .....A gidansu baby ajiye wayar tayi haɗi da shu'umin murmushi, kana ta rufe idanunta, tana hango balbalin bala'in da zai tunkaroni,

     *Wacece Baby*

    Sadaka yalla ce, kaman yandasu Annah suke bakin hawure haka suma suke amma su baby daga chad suke, tana da yayu maza guda biyu, sai ita maxan suna da mutunci, domin suna kokarin inganta musu rayuwa amma baby ta fanɗare, sakamakon ɗaurin mazaunin daga Mamansu, shi yasa yayun sukayi watsi da ita suka kame kansu, baby tagirmeni domin sa'ar Hajra ce, kenan har Ramla tagirma balleni, dake tana da karamin sanwa yasa ake mata kallo kamar sa'armuce,hmm kaɗan daga cikin halayarta kuwa bata damu da kasota ba idan kai mata ko kanka da k'awo sai tayi da kai, dan sam bata da girman kai asalima har faɗa muke da ita idan tana k'ask'antar da kanta haushi take bani a duniya na tsani wulakantakai, toh haka baby take sai abu biyu da ban faɗa muku ba,wato harka da maza ina mamakinta yanda tamaida rayuwarta, nabin maza, dukda saura kiriss tadulmeyar dani,Allah bai bata nasara ba toh a wannan bigirin ita karshece, dan ko kak'i Allah idan kayi mata, toh babu ruwanta dakanka zakazo har gurinta, idan tafagen surar jikine, akwai kome kyau diri balaifi ta haɗasu kan sai Hamdala,dan takace ni jikina shine jarina bana bara amma ina karuwa...! Wannan shine halayarta.

     .....•
    Bayan na dawo, daga makaranta tsame jikina nayi da kowa dan tsoronsu nake gani nake kaman suma sun sauya, da naga hutawa na tafi gidan Annah, ban dawo ba, sai dare dan yamzun nadaina zuwa islamiya, zaman gida nake,

  
         Sati guda dagama exam ɗina aka saka aurena nanda wata biyu, sune mafiya daraja a gareni sune watanin da bazan manta dasu ba,

          Takanas Annah ta ɗauken zuwa nijar, inda akaita min gyaran jiki, kafin afara naje nagaida Dangin Mamata, anan naga abin mamaki, inda muka haɗu da Yayata da muke uwa ɗaya, Neenah jin nazo yasa itama tazo daga gidan Babanta nan Annah take faɗa min ai neenah yayata ce, kallonta nayi idanuna daf da kwalla nace.
"Annah mi kike qoqarin ɓoye mana Annah ki faɗa min miye ke farune?"

      Murmushi Annah tayi sannan tace.
"Kwantar da hankalinki, Hafsatu itace mahaifiyarku, mun yan damagarane, muna can cikin wani kauye ne, Uballe shine ɗana na fari sai Hafsatu, tun suna kanana Mahaifinsu ya rasu, fari da rashin ruwa yasa Ubale ya dawo Niamy inda yazo yake niman kuɗi dukkarshe mako yana zuwa mana, dake akwai y'anuwana acan, cikin ikon Allah samu ya buɗe masa, har ya kamana haya,  acan lokacin Hafsatu tana makarantar gaba da firamari, muka koma can, nima mata makarantar gwanati yayi inda tacigaba da karatunta, tana aji uku, aka kori yayanta a gurin aikinsa sakamakon Satar da aka musu a ma'aikatar munshiga ta gayara, kafin wani me kuɗi yaga hafsatu yana so, yana da mata ɗaya bata taɓa haihuwa ba, idan yayi aure ita ke kore masa mata, shi kuma ya haukace akan mahaifiyarku muku ma tsoron kar a sake mana ita yasa mukak'i ganin haka ya nimawa Ubale aiki, a kamfaninsa nan dai muka hakura aka bashi haftsatu,

           Hmm bayan bikinsu kaman uwargida bazata ɗaga hankalinta ba, sai daga baya da taga Hafsatu da ciki, daman duk matanshi babu wacce take kaiwa sati uku agidan takoreta, sai Mahaifiyarku itace takai har wata huɗu, tunda takyala ido taga cikin fara shige shige har Alhaji Marwa ya saki Hafsatu, ta dawo gida inda tav cigaba da rainon cikinta har ta haihu, dukda ba a gidanshi take ba yayi mata bajinta sosai na haihuwa,

        Bayan suna yazo ya maida ita har an shirya zata koma daga baya yace ya fasa dole haka muka hakura har Aka yaye Khadija sunan Mahaifiyarshi suna kiranta da Neenah, lokacin da aka yayeta bata kara sati biyu a gidanmu ba yazo ya ɗauki yarshi ya kaiwa Yahanasu, dake Allah yayiwa khadija kyau sai Ubangiji ya ɗaura mata sonta abinda ya kwantar da hankalinmu kenan dan ita da kanta take kawo mana ita, ana cikin haka kawunku ya dawo Najeriya da sana'ar shayi, shekaranshi biyu ya bar shayi ya buɗe shagon saida kayan shayin daga nan yazo ya ɗaukemu baya ya auri yar kanina, jibirilla, Mubarakatu kenan, toh dawowarmu katsina nan yasaka hafsatu a makaranta har tagama tashiga makarantar horan Malamai na N.c.e, yau da gobe har Allah ya haɗasu Mahaifinki cikin kankani lokaci, akayi bikinsu, ashe rabonkine ya kaita gidanku inda Allah ya haɗata da kishiya tagari inda suka zauna zama na amana,har tahaifeki ko saninki batayi ba Allah ya amshi rayuwarta, kunji labarin mahaifiyarku....."

     Juyawa nayi narungume Aunty Neenah ina kuka, itama kuka take sosai sabida kaunar mahaifiyarmu, nan muka ɗinke kaman mun jima da sanin juna har muka gama kwanakinmu, muna waya da Asad kullum shi ke tuna min da yau saura kwana kaza.....
          Yanzun Labarina zai fara daga kwanakin da suka rage min na farin cikin da zan riski mijina abin alfaharina, kunshe yake da farin ciki da bakin ciki sanan kuka da kaɗaici Allah sarki idan na tuna

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment