Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan yar mutane duk nasani, idan aka taɓashi ya nunawa kowa shine wanda yafi kowa sanin Allah da nasan akan wannan banza zaku ajiyeni Wallahi Umma da ban zo ba, Kuma ni sai nasake hura msa wuta yanda zai nimo musu yar mutane."Inji Ya Ali knn, kuma babu wanda yayi yunkurin dakatar dashi,

Kowa nakawo shawaranshi kuma anyi na'am dana abba lawan, umma suka bawa damar magana cikin jin daɗin haɗin kan da suka bata tace.
"Nagode Allah yayi muku albarka ynx abinda za'ayi Aisha ta sauka a abuja ta haihu a can dan matukar tazo nan wasu zasu faɗa masa, sai kuwa Abubakar bayani inyaso kome kukayi dai daine, amma ina rokonku da kar wani ya nuna masa inda take."


Duk sunyi na'am da shawaranta haka suka watse ran kowa a ɓace da imamu.......

«»
Cikik ikon Allah nasami jirgin da zai zo, lagos ana shirya kome, zama nayi dan sunce yanayin garin akwai ruwa da cida (tsawa) dole ajira har garin ya koma dai dai,......



Hawayene yake bin fuskana ina rungume da jakata, ina kallon yanda kowa yake harkanshi, kusan awa uku mukayi kafin aka fara shirin tafiya(Nasan wasu zasuyi mamaki ta yanda nayi kome da kaina haka ba wani abu bane,dan shi da kanshi ya faɗa min yanda zanyi visa koda wani abu ya taso, kuma a halin rikicin da mukayi zuciyata ta kagu takoma gida, zan iya kome dan nabar inda yake, dan ko ba kome ainayi karatu kuma na iya english dan haka ba wani abu bane dan nayiwa kaina kome, nayi haka ne dan nanuna masa cewa ni ba jahila bace da ilimina kuskure ɗaya tak nayi shine wautar da kaina da nayi.)


Ajiyar zuciya na sauke lokaciɓ da naganni cikin jirgin emirate, farin cikine fal raina da son komawa gida. Ana gama mana kome muka ɗauki hanya addu'a nayi na rufe idanuna, cikin damuwa......


«»
Bayan fitana kuwa sai gashi ya shigo gida jin dariyar Hauwa da shewa yasa ya dakata tana faɗawa Uwarta abinda ta aikata jo yayi kamar kafanshi bazai ɗaukeshi ba bai san lokacin da ya zuɓe dake da kanshi yana faɗin.....
"Innalillahi wa'inna'ilahin rajuon....." abinda yake faɗa kenan yana nanatawa cikin tashin hankali, tare da danasani mara amfani, da ya aikata mikewa yayi ya shiga gidan cikin zafin nama ya fauce wayar hannunta yana murmushi wanda yafi kuka ciwo, batayi tsamaninshi ganinshi ba kawai sai gashi a gabanta....

Ja da baya tafara cikin tashin hankali tace.
"Don Allah kayi hakuri bazan sake ba nima hajja ce tace nayi haka, wallahi sharrin shaiɗane da zuciya, kayi hakuri bazan sake ba"

Zama yayi a kujera yana kallonta ji yake kamar zuciyarsa zata buga, dafe gefen yayi cikin wata irin murya yace.
"Zauna Kasa nace"

Zuɓewa tayi tana makarkata, lumshe idanunshi yayi cikin tashin hankali yana hango cikin kwayar idanun A'isha wanda yake hango zallar gaskiyarta babu tsurki kome a ciki a hankali ya lashe fatar bakinshi sabida bushewar da yayi, kafin yace.
"Zan tambayeki abu biyu zuwa uku, iya gaskiyarki iya kyaleki da zanyi amma matukar kika nuna min bazaki fada gaskiya bazan baki mamaki dan sai na sauya miki halitta."

Gyaɗa masa kai tayi tana share kwalla, cike da jin haushin abinda tayi garin bawa uwarta labari gashi tajazawa kanta masifar Imamu.

"Kina da hannu a cikin zubda cikin jikinta? Sannan taya kina gidan nan tashigo da wani baki sani ba, sai kawai kika kirani wai nazo akwai damuwa, a cikin gidan? Sannan ya akayi kome yake faruwa ban sani ba,"

Kuka ta fashe da shi tana ja da baya sabida tsoron, juyawa yayi gurin kayan kallo ya janyo wata wayar destop ɗinshi mai muguɓ kauri da tsaho ya mike ya finciko sai da computer ta fashe, ya tsaya yana gyara zaman wayar kafin yace.
"Kinjima kina shirya min abubuwa ba tare da sanina ba, keda Uwarki nagodewa Allah da ba saketa nayi ba amma da na kaɗe har buzuna, zaki faɗa min ko sai jikinki ya gaya miki."

Mikewa tayi zata gudu Allah ya bashi sa'a yasa mata kafa ta faɗi sannan ya shiga tsula mata ta ko ina a jikinta babu sassauci yana faɗin. "Kun cuce ni kun zalumunce ni ina son gasgata yarinyar nan amma kuka maidani jahili, wani irin magana ne ban faɗa mata ba mi banyi mata ba, na tozarci duk akanku nakirata dabba jahila ashe ni nine anan guda banga amfani ilimina ba tunda nagaza zame mata majingini, na gaza zame mata farin ciki, kullum ina cikin gumtsa mata bakin ciki, bata san daɗins ba sai wuyana akanku idan na kyaleki Allh ba zai barni ba gwara na miki yanda zaki ji a jikinki."


Sai da yaga bata motsi ya yasar da bulalar ya sanna ya shiga kitchen ɗinta ya ɗauko ruwa ya haɗa da kankara ya watsa mata a jiyar zuciya ta sauke kafin yace.
"Zaki faɗa min mi kuka shirya min ko sai kinji kamshin lahira"


Dakyar ta buɗe baki tace.
"Duk......."

*💁 #.......Truelifestory a cikin awa ɗaya da rabi, kafin ku cinyeni ɗanye da tambayoyinku😂 au ta hakurane page uku zan karasa muku nima na huta*
[5/4, 06:21] Me Dambu: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/7DaVfCxttKX4eDefmrqLu9

🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*


*49*


Shiru tayi cikin shashekar kuka tana girgiza kai, tare da murza yatsun hannunta cikin tashin hankali,dan bazata iya faɗa ba, abinda suka aikata,

Tsawa daka mata cikin ɓacin rai yace.
"Zakiyi magana ne ko a'a"

Kallonshi tayi cikin rawan murya tace.
"Zanyi amma.."
"Amma me? Ko sai kinji wuyane zakiyi magana,
"Bazan faɗa ba karabu dani, ni ina son mahaifiyata dan duk abinda muke aikatawa sai da muka bada sadaukarwa duk ranar da gaskiya tafito hajjana mutuwa xatayi dan haka kayi min duk abinda kake ganin yadace zanyi Accept ɗinsa." Cikin kuka da hargowa ta faɗa masa,

Ranshine yakara ɓaci wato abin rainin hankaline yana ne, mike yayi cikin zafin nama ya janyota ya makata da bango, sulalewa tayi kasa, tana sake wani irin kuka, gashi ya rike mata wuya, sai kakari take saketa yayi yazauna a gabanta yana kallonta yana jini ke fita ta hancinta da bakinta ɗagowa tayi cikin taurin kai tace.
"Koda nafaɗa maka. Babu wani amfani domin a ynx haka Ita yar gwal ɗin tana hanyar gida kuma burina ya cika, abinda zan faɗa maka shine ka zauna dani matukar ka sakeni wallahi babu kai babu saura kwanciyar hankali da Ita, idan kuma kana ganin zaka iya kacigaba da dukana ko gaskiya zai fito, na wucce tunaninka, koda mi zaka min"

Dariya tasaka, tabbas Hauwa tayi nisa dan zuciyarta ta bushe mutumin da ya iya kisan kai aikuwa babu abinda bazai iya ba. Duk yanda yaso tayi magana taki, mikewa yayi ya barta sama ya haura, can sai gashi ɗauke da takarda da biron zama yayi ya rubuta mata saki uku, sannan ya cilla mata, ɗaukar takardan tayi ta kalleshi, take maganata ya faɗo mata *Ni yau na bar gidan lafiya lau gobe ke,zaki barshi bayan kinci duka da kuma sakinki. Ki kirga kwnakinki daga yau*
Ihu ta takarkare ta kurma sannan ta mike cikin layi tace.
"Wallahi sai na hanaku zaman lafiya, sai kayi dan dana sani. Zakayi da nasani mara amfani yanzun muka fara wasa matukar ina numfashi sai karasa nutsuwarka kuma sai na haramta maka ita A'ishan ta hanyar fesa muku dafi mara magani mu zuba ni daku.."

Dakyar tashige ɗakinta tayi wnka da ruwa mai zafi sannan ta shirya kayanta taja tafita, bayan ta ɗauki passport ɗinta.


«»
Tunda ya mika mata takardanta ya koma sama, zama dirshan yayi a tsakar ɗakin ya cusa hannunshi a cikin sumar kanshi da ya tara, cikin tashin hankali, yafi mintuna arba'in a gurin kafin ya tashi ya nufi Airport, koda yashi tambayarsu ya fara tare da musu kwantancena, da nuna musu hotona dake cikin wayarshi, nan suka ce masa ai ɗazun jirginmu yabar london zuwa lagos......


Dafe kanshi yayi ya dawo gidan yana parking sai ga yan sanda, sun zo gurinshi, bayan sun gaisa, nan suka ce ana nimanshi a asibiti, kamar bazai jeba ya bisu.
«»

Karfe goma nasafe muka sauka a airport na kasa da kasa dake birnin lagos kiran umma nayi na faɗa mata ina lagos zan wucce katsina, ce min tayi a'a na bi jirgin abuja, babu kuɗin naija a hannuna dan haka sai na nemi inda zan samu chanji, kuɗin kasata, aikuwa aka haɗani da wani bakano take ya canza min, naje nasayi ticket ɗin Abuja, nima dai naji daɗin yanda Umma tace min kar naje katsina dan bansan ya zan musu bayano su fahimta ba,


Sai karfe biyu muka bar lagos zuwa Abuja ina sauka naga Aunty Abida matar Ya Abubakar, karasawa tayi ta amshi jakana, drv ya karbi a kwatin tana murmushin karfin hali, dan taga na fara share kwalla, koda muka shiga motar kaina a sunkuye har muka isa gidansu dake Gwarumfa, dakyar nsfito daga motar kafafuna duk sun kumbura, muna shiga, ta fara nuna min ɗakina wanda yaji kome, harta gadon baby, murmushi nayi nashafa cikin wanda yake motsi sosai, banɗaki nashiga nayi wanka da alola nafito na tadda sallah dake kaina,


Bayan na idar sai gata ɗauke da tiren abinci mikewa nayi zan karɓa ta kauce ta ajiye min, zama tayi muka sake gaisawa, sannan tace.
"Aisha bamu ji daɗin abinda ya faru ba wallahi karki ga yanda brothers ɗinshi suka tsaya zasu kwatar miki hakkinki, don Allah kiyi hakuri."

"Aunty Ba laifinshi bane, nice mai laifi ana girma hankali ake karawa ba wauta da shirme ba, ni kuwa na manta da haka na,zauna zuciyata cike da shirme, na manta zama aure nake, na manta ibada ya kaini,ni nazata yanda Innaji da Umma suka zauna da kishiyoyinsu lafiya ba cuta ba cutarwa nazata nima haka xan zauna da tawa, ashe green sneak ne, under green grass, wanda a koyaushe so take taga bayana, Aunty duk tsaya min da zasuyi matukar ba,zasu bani ilimi ba toh babu amfanin haka ba Usman ba wasu ma sai sun kirani da jahila, dabba.." kukanr mara sauti ya kwace min, na kifa kaina da jikin gadon sai da nayi mai isata kafin na cigaba da cewa.
"Ako yaushe, ina mantawa da niman tsari da mugayen mutane da mugayen Aljanu, amma na manta da haka sai juya rayuwata nake cikin kiriniya da Sakalci Aunty taya zan zama mai ilimi nima na wucce gorin miji,"


Daga bakin kofa muka ji yace.
"Wani course kike so zakiyi?" Ya Abubakar wanda duk abinda muke faɗa yana jinmu...... Dan ya jima da shigowa gidan,

Kaina a sunkuye cikin kuka nace.
"Daddyn Hamra Law nake so."

"Shi knn zaki bani hotonki gobe zan miki takardu, dan zaki bi Abba lawan japan yasamu aiki a can zan tura da takardunki" Yana gama faɗin haka ya juya yafita Aunty Abida tacigaba da rarrashina da bani hakuri. Kafin tabi mijinta......


Ruwan zafi kawai nasha na kwanta, ina juya abinda Imamu yayi min,..........


«»
Washi gari sai ga Umma da yamma aka kawota, duk yanda nayi farin cikin ganinta sosai nan muna zauna muna hira, bayan sallar isha ma muka sake buɗe hira a falo, Hamrah tana min matsar kafana, wanda suka gama kumbura, sai goma muka watse, a ɗaki ma mun jima muna hira kafin muka kwanta......


Kusan uku nadare na tashi da wani mugun ciwon mara, dakyar nake iya cira kafafuna sabida jin kamar abu zai diro min tagaba, dakyar na isa ban ɗaki, na dukusa nayi fitsari ina gamawa wani irin ruwa mai kauri haɗi da jini suka zuba,.

Naji tsoro amma bana son umma tashiga damuwa sai na share, na koma na kwanta, tun daga lokacin nake sintirin ban ɗaki, har umma tatashi sallarta ina,zarya da ta tamvayeni nace kawai cikina ne ya ɓaci,


Hmmm naci azaba har gari ya waye naki faɗawa kowa kuma ban fita falo ba, umma kua tasan nakuda nake kawai zuba min ido tayi dan bata son ta karya min kwarin gwiwata, amna ganin har sha biyu yasa tayiwa Aunty Abida magana dan ta faɗa mata cewa ina nakuda amma naki faɗar mata.


Sun shigo lokaci salati kawai nake, ina yarfe hannua, buɗe zip ɗin jakata sukayi suka ciro kayan baby da card ɗina nacan, suka shiga jerawa a wani karqmin trolly sannan suka taimaka min na mike na, durkusawa nayi kafin na mike nasake wani irin nishi tare da ambaton Allah lokaci naji saukar abu kamar an zare min kaya naji fitar abu baki ɗaya komawa nayi zan zauna umma tayi maza ta rike ni cike da tasbihi, Aunty Abida ta zaro babyn fara sol katuwa tabarkallah, nishi nasake a karo nabiyu ina rumgume a jikin Umma sai ga wata ta sake dirowa, "Alhamdulillah Umma tace, " kafin ta fashe da kuka, ajiyar zuciya nake kamar wacce tafito fili daga, naɗe babys ɗin Aunty Abida tayi sannan suka kwantar dani, gefe,....


Fita Aunty tayi takira makociyarta dan babban metro ce a wani asibiti a nan abuja, aikayi dace bata da duty rana, sau dare tare suka shigo ita ta gyara babys ɗin, sannan ta dubani tace babu ɗinki allura da tazo dashi tayi min sannan ta rubuta min magani, har waje suka rakata, tsintar kaina nayi da jin kunyar yaran da su Umma wato nice na haihu yara har biyu, ajiyar zuciya na sauke Umma tashiga ban ɗaki ta haɗa min ruwa naje nayi wanka nafito kwanon dabino da tazo dashi da kuma dafaffiyar zuma, ta mika min tace.
"Maza shanye wannan, shima dabinon kicinye min su."

Lokaci guda nakafa kaina a goran sai da nasha rabi, wanda yake ɗauke dasu citta,kanunfari, masoro, da barkono, lokaci guda na sha rabi na ajiye, dabinon na sunkuya ci sai da naga bayansu tass, sannan ta mika min ruwan tea nasha, ina zuba can sai ga drv da Aunty ta aika yasayo mata maganin mika mata yayi ta kawo min nasha, sannan ta mike nabi lafiyar gado........


Kafin kace kobo aunty takira kowa tafaɗa masa, yayinda tasaka hoton yaran akan dp ɗinta sai Family grp ɗin na shehu Usman family grp maza da matane zallah a ciki har da Imamu amma shi baya whatspp, sai face book, dan yakance wasup hayqniyace zallarta.......


Sai grp ɗin matan Yayu da kane mai suna Matar Alfarma shima sun saka hoton, sai grop ɗinsu Fahima suma sun saka amma an jawa kowa kunne da ya iya da bakinshi.........


A face book Hassan yayi posting Alhamdulillah Allah ya Albarkace nida Haihuwar Yan biyu duk mata...... Hotonsu yasaka....



«»
Umma takira Innaji ta faɗa mata haihuwar, da kuma abinda ya faru inda tayita bata hakuri, sannan ta faɗa mata matakin da suka ɗauka batace kome ba saima murmushi da tayi sannan tace.
"Ai yarki ce duk abinda kikayi dai daine"


Godiya tayi sannan tace.
"Don Allah karki nuna masa tana nan, sai yaji ajikinshi."

Dariya tayi sannan tace.
"Matukar naga zaku bashi wahala zan faɗa masa babu wnda yafi karfin kuskure idan da laifinshi ita kunji abinda take masane nifa......"

"A'a wallahi hajiya Saratu dashi da ita wye babba."

Nan sai suka rabu kowa nakare nashi........

«»
Har asibitin suka isa aka shiga dashi ɗakin yan hatsari zuwa wani gado zaro ido yayi sakamakon ganin wanda yake kwance yana nuna da yatsar shi.........



Toh waye haka.........😂
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*

   *_Hmmmm.....Tow mi zance bayan haka kuyi hakuri na gajine shi yasa na huta nima jinina ya dawo😠😣 Yaseen matukar baku kawo kayan dubaiya ba toh sai bayan sallah zaku sake jina😎_*

*51*



Farin cikin da nake ciki ya hanani magana kuka nasaka musu ina yunkurin rungume Aunty Zuby, wacce itama danne hawayenta take sabida karta karya min zuciya, tuno abubuwan da suka faru yasa na fara kuka wiwi-wiwi kamar yarinya karama,

Mai dani inda ake lalle tayi tana share hawayen da dake bin gefen idanunta, kallon Aunty Hajra da Mamin Abiee ɗan Yaya Isahq, nayi cikin murmushi ina share kwallar da take sauko min, kallon Yaran suka kafin Aunty Hajrah tace.
"Auta Innaji tace a gida kika haihu yaushe kika daina jin tsoro dan nasanki da mugun tsoro."


Murmushi nayi a karo na biyu kafin nagyara zamana nace.
"Ayayinda kunci da damuwa, haɗi da bakin cikin suka maka dabaibayi, toh alokacin kake nima tsoro karasa, babu abinda zaka iya samu sai bushewar zuciya, da hakuri da juriya, kinga knn babu mazaunin tsoro tunda an fatattakeshi."

Kowa a ɗakin sai da ya zuba min ido sabida babu wanda ya fuskanci maganar da nayi......

"Eyyeee Auta ta girma, tayi hankali irin wannan maganar haka ai sai na ɗauka wata babbar macece" Inji Aunty Zuby,

Girgiza kai nayi cikin raha nace..
"Kuci abinci auntys, a wani kaulin magantuwa akan abinda bai da alfanu shiru yafishi, dan babu abinda mutun xai tsinta sai zunzuruntun nadama da, danasani mara amfani, ita duniya makarantace malamarta kuwa yau da gobe ce."

Ɗago kai nayi ina kallonsu ina wani irin murmushi mai tattare da damuwa, amma ba lallai bane ka fahimci haka,

Ɗaukar yaran sukayi suna kallona ina share kwalla amma lokaci zuwa lokaci ina murmushi tare da kllonsu,...... Bayan mai lallen ta gama ta mike, kallona tayi sannan tace.
"Sauda dama zuciya takan iya rike damarmaki da yawa, wanda koda makusancinka baka kaunar faɗa masa, ɗinbu damuwarka amma idan ka adanata wataran zata zame maka makami mai linzami. Sai anjimarku Allah ya raya jarirai."


"Nagode sosai" nace mata,

Nutsuwa yayuna suka na kallesu cikin farin ciki nace..
"Ku uku kukazo kawai"
Murmushi mamin Abiee tayi sannan tace.
"Eh can ma zasuyi nasu taro, amma sai mun koma dake sgi ys basu zo ba"
Gyaɗa kaina nayi cikin jin daɗi. Ina kallon kasa, tabbas ina da damuwa amma bana,son rabata da kowa nafison jinta a raina kamar yanda mai lalle ta faɗa zai zamemin makamin yakar duk wanda ya cutar dani...

Dakyar suka ci abincin da aka ajiye musu, sai kallona suke idan na tsurawa guri guda ido ina tuna wasu abubuwan marasa amfani.....
Ajiye min Amatullah Aunty hajrah tayi cikin tarin damuwa tace.
"Dukda bamu cancanci shiga damuwarki ba amma yana da kyau ki rage zurfaffa tunani haka, ki rungume kaddaranki karki juya masa baya, ita rayuwar aure ta gaji haka ko fiye da haka, kafin ke anyiwa mata dubu kuma sunyi hakuri an wucce guri...."

Ajiyar zuciya na sauke kafin nace.
"Nagode"

A hankali na ciro nonon na saka mata abaki karɓa tayi har da niman kwarewa gaskiya Hassana ko nace amatullah tana da hakuri dan ko Amatujalal bata kaita hakuri ba, ita kome dare kafarka zaka sameta tana tsotsar bakinta ko kuma shawel ɗinta gashi bata cika kuka kamar Yar uwarta ba, amma idan ana niman cinye du aka sami Amatuljalal har tsoro take bani idan batayi bacci ba nazare nono da sauri take cafko shi, dan kar ya gudu yabarta babu abinda zance sai Hamdalkasiran ɗayiban mubarakan Masha Allah.


Zubawa yarinyar idanu nayi cikin damuwa wanda ya danne min zuciyata.......

Hira muke jefawa lokaci zuwa lokaci.har dare bayan sunyi sallar isha muka sake baza hira nasiha suke min mai shiga jiki har zuwa lokacin da muka kwanta.


«»‹›
Washi gari sunah acan yobe aka raɗa suna, cike da farin ciki. Irin abubuwan al'adarsu, abinda yafi burgemu ba kome bane sai kayan goyon da Yayun Imamu suka haɗa min tare da ragunana guda uku, wayata da take hannun Mamin Abee tayi kara mika min tayi hankalin na duba sako nagani coder ɗin Uk nagani kamar zan buɗe sai na share kuma na cigaba da hidimar gabana....


«»‹›
Kusan sati knn da barina uk, duk ya shiga wata irin damuwa gashi ya nemi Phone ɗinshi a gidan babu ita babu daɗinta, ya rasa ta inda zai fara duk ya lalace ya tara wani kasumba sai yayi muni, tap ɗinshi ya ɗauka ya shiga buɗe social media, face book, nan yaga sakon Hassan nan yaga duk yan familysune suna masa barka da fatan alkhairi, ganin sakon yayi kusan sati knn, wani updater yq gani nan ya buɗe sai ga hoton yaran anyi musu, suna hannun Umma sai murmushi suke ga wanda akayi da sauran Yan uwan... Gabanshi ne yayi mugun faɗuwa take na faɗo masa, mikewa yayi ya fita, da sauri ya isa inda ake waya kwandala ya jefa sannan ya jera nomber Ummarshi. Tana cikin mutane amma haka tafita suka gaisa, shiru sukayi dukkansu dakyar yace.
"Umma Aisha ta iso kuwa"
Murmushi tayi a ranta kuwa tace.
*Anzo gurin abinda nake jira knn*
"Dama katuro musu yar mutane ne baka faɗa min ba,"
Wani

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment