Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu tayi min bayan wanda dangin mahaifiyana suka min, gaskiya ni yar gata ce dan har wash machin aka saya min ga manyan frig ɗina guda biyu, Baba yayi min baba kawuna shima yayi min na tsaye babba, plastma na guda biyu kome na biyu, Yar gatarere kenan, Inji goggo rabi tace" Kaza kanki da motsi " haka take kirana,

        Ji nayi ana zaunar dani sabida dogon tunanin da na shiga a hankali na zauna cike da kunya, raje karan tv akayi sannan suka shiga gaisawa, ina sanye da lace ruwan golder, sai babban mayafina cream wanda ya dace da shigar, kaina a sunkuya naji muryanta tana cewa.
" Taso kizo nan A'ishatu aini ba surukarki bace wa'incan ne surukarki ni Uwace zo nan uwata, kusadani zo nan A'ishatuna, jikina ne ya shiga rawa, haka Aunty Zuby ta mikar dani amma kamar mai karaya a kafafunta na gaza mikewa, rarrafawa nayi na isa gareta janyoni tayi sosai jikinta sai Addu'a take zuba min abinda yasa na fashe da kuka nasake narkewa jikinta kenan, sabida lokaci guda naji kaunar matar yasami muhali a zuciyata mutuntakarta ya kara min sonta fiye da kima, tana gamawa cikin jin daɗi tace.
"Bar kuka haka kar Falmata da Kaltuma su sami abin tsokanar dan ma ummul khairi bata fito ba ai yau da kinsha zoyala,"

    Dariya duk falon akayi ita wacce aka kira da falmata tayi karamin dariya sannan tace.
"Ni babu ruwana akan Ya ustaz zan fanshe dan cike nake dashi, yazo ya biyani kuɗin wayata da aka sace garin ɗauko amaryansa ni yanzun bana ta wannan ɓauren dashi uban gayyan nake tukun."
     Dariya sukayi nan dai suka yar barkwace sannan goggo Rabi tare da Inna Talatu, Goggo lantana Yayun Babanmu sai Inna Talatu ita kuma Yayar Innaji suka ce.
"Hajiya ga yarinya nan mun kawo muku, cikin amincin Allah idan tayi kuskure karku ji kome ku tsawata mata, dan nan ma gidane  sosai hajiya A'isha yarinya ce karama sosai ni a tunani na bata cika sha takwas ba tana tsakanin sha bakwai ne, don Allah ku sata a hanya yanda zata gane kanta yanda kuke ganinta ba haka take ba Yarinya ce ɗanya wacce shiririta yayi mata katutu. Don Allah ga A'isha nan mudai zamu bisu da Addu'a sauran kuma Allah zai gyara."

Kanwar Umma me suna Umma Khadi itace tace..
"Insha Allah A'isha tazo gidanan dakafar dama, domin itama yanzun Y'ace a cikin gidan nan da Yardan Ubangiji kaman yanda kuka kawota Insha Allah ba zakuyi danasanin kawota ba, tazo gidansune kuma idan ta fita daga cikin shi Muna fatan babu inda zata sai makavarta,  da yardan Ubangiji  ba zakuyi na dama ba idan shiriritane ai shima Imamun aikinsa kenan yarinta kuma ba damuwa gasu Kaltuma da Falmata insha Allah ta shiga sahunsu zata daina. Baku ga Yanzun Falmata itama tayi nata ba ai dukkansu Yarintar ce ke ɗawainiya dasu."

       Turo baki tayi tana kunkuni cikin raha tace..
"Umma khadi duk abinda,zaki ce kice amma sai ya biyani wayata."

   Tana rufe baki sai ga sallamar Yarta Zakiyya cikn siririn murya gaida kowa tayi sannan ta mika mata  farin laida tace.
"Mamie gashi inji Baba Imamu wai don Allah ki shika masa kurwa ya huta."

           Karɓa tayi ta buɗe murmushi tayi sannan tace.
"Kice masa ai kurwan da nashi da na A'isha na kama dan haka ba zan kunce ba sai nayi tsayuwar dare dan karta kwace min shi, sannan kice masa Allah ya dawwamar dasu shida ita a karkashin Al'arshin Ubangiji nagode duk shekara sai suɓ haifa mana Yan tagwaye masu albarka.'"
     "Amin "dukkan yan falon suka ce,

          Hmm farin ciki ta shiga yi, inda ta mikawa Umma khadi, da sauran Yan falon kowa sai san barka suke mata, barbanci Umma tayiwa Husaina ta mike ba musan me tace ba amma naga har dasu Falmata suka shiga ɗakinta sai gasu ɗauke da wasu ture masu ɗauke da kaya, suna zuwa suka dire a gabanta, buɗewa na farko tayi awarawarone da set na abin wuya, sai ɗaya shi kuma, lifayya ce ja, ɗaya kuma zunzurutun kuɗine, haka ta janyo tiren awarwaron ta shiga saka min a hannuwana, kallona tayi tana murmushi sannan tace.
"Nasan bazaki so ki buɗe fuskarki ba toh gashi kije kisaka, gobe da wannan lifayyar kiyi ado dashi."


Aikuwa ɗakin ya ɗauki "masha Allah" Yan uwana da dangina sai godiya suke, da zasu koma tace.
"A'a kubar min ita anan kuje da kayan ita anan zata kwana."

Cikin farin ciki suka ce "ba kome ai duk ɗaya ne," sai da safe suka musu sannan suka fita suna masu farin cikin dace da nayi na uwar miji tare da mamkin kyautar da tayi min na set ɗin gwal," lallai Naiha tayi dace da uwar miji." Inji Aunty Maryam, Aunty zuby tace.
"Ai ita matsala ɗaya gareta shine wauta amma indai dan girmama na gaba da itane bata damuwa yarinta da rashin ji ke damunta, kuma naga shima Ai yana sonta kuma danginshi suna sonta kuma itama ai bata da rashin kunya, kawai zasuyi fama da rashin kan gadone,kuma ai gidan malamaine bazatayi wannan gangancin ba, duk wautarta zata kare shi da itane, batun kishiya kuwa ai Naiha ba kanwan lasa bace, idan ta juye miskilancinta babu yanda zata iya mata, mudai Allah ya basu zaman lafiya."

"Amin Ya Allah" duk suka ce,

........
Dake ni ɗin Yayar mage ce, zamewa nayi na kwanta a jikinta sosai ina shirin bacci.

Su kuwa hiransu suka shiga yi ahankali kwance har na fara bacci Aunty Kaltume ta tashe ni, a hankali na mike rike hannuna tayi zuwa ɗakin Umman tace..
"Kwanta ki huta,"

Tana gama faɗin haka wayarta na kara, ɗauka tayi tana dariya cikin zolaya tace.
"Wallahi kaji kunya Imamu, kira goma toh gata nan a ɗakin umma bari na mika mata."

Mika min wayar tayi, kaman ba zan krɓa ba na karɓa na kanga a kunne na, ita kuma tafita, shiru nayi bance kome ba, hura min iska yayi "humm" nace masa,
Sautin murmushinsa naji inda yace.
"Naihaaa." yarrr naji tsigar jikina ya mike, har sai da nacire wayar a kunne na, sannan na maida cigaba yayi da magana.
"Barka da zuwa Yobe da fatan kin iso lafiya"
"Lafiya" nace tare da sake wani hamma dole yayi dariya yace.
"Kora da hali yafi kora da sanda, toh nasan bacci kike ji gani nan zuwa muyi baccin tare."

_Kan uban_ nace a zuciya ina zare idanu, wannan ba kunya ce da shi ba, ynz sai yazo ya yakura min. Kashe wayar nayi na ajiye mata a,side bed ai kuwa ina jefa kai a pillow dakyar nayi addu'a tuni bacci yayi gaba dani, jin shi yasa ta shigo tasami wayar a kashe murmushi tayi, sannan tafita, komawa falo tayi tana basu labarin irin abinda aka musu a katsina, kowa a falon sai da suka yaba irin kokarin da mukayi, gyara zama Husaina tayi sannan tace.
"Wato tun karfe uku muka isa maiduguri, har muka je kamu ba'a kawo mana ruwa ba, kai sai da nakare nakira Ya Abubakar na faɗa masa take sai gashi ya kawo mana abinci daga hotel ɗin da suka sauka, sai dare aka kawo mana biski miyar kuka, ai kuwa nayiwa Ya Imamu waya nace ko zan mutu bazanci abincin da aka kawo mana ba yasan yanda zai damu ina kashe waya sai ga Khalifan Ya Ali da manyan ledojin shake da namar kaji da drinks, shi muka ce, da safe ma akwai abokin Ya Imamu a g.a.r, shi ya kawo mana abin karyawa tare da Matarshi Fannah, kai munga tujara ai nun, haka mukayi hakuri, har aka ɗaura aure inda suka saka rigima sai ya biya gwal a madadin sadaki shi kuma yace ashirye yake da ya fasa auren dan bai ɗaga shi yanana da kasa ba, dakyar muka fito fa ana cikin wannan turmusheshen aka sace wayar falmata Lg ɗinta, ai danasan haka ne wallahi da zamana nayi banje ba,"


Mika musu jakunar waleemar da aka basu acan katsina Aunty Kaltuma tayi guda ashirin da uku sannan tace.
"Wannan na waleemar da mukaje anayi ne, daman mu bakwai ne nacire mana saura kuma gashi nan, sauran kuma gashi."

Buɗe jakar sukayi nan suka ciro kalanda wanda yake ɗauke da hotonshi dani, haɗawa akayi duk muna dariya, sai litafi,wanda babu hotonmu sunanmu ne kawai sai memo, da karamin litafin yasin, da 40 rabbana da husnul muslun, sai wasu litattafai na addu'o'i, sai roban cincin wanda yake ɗauke da har nakiya dubulam alkaki, gireba."

Rike baki Umma khadi tayi ta kalle sauran Yan uwanta tace.
"Mutanen nan sun san kan hidima, irin wannan abu haka."

Murmushi Umma tayi sannan tace.
"Keda bakije rasuwar Zahura ba ai nan zaki san mutanen dattawane,har kwana bakwai hidima Hajiya Saratu take mana, ai banyi mamaki ba,."

"Umma wallahi dai dae da ruwan shanmu nagorane, munzo da kayan drinks ɗin suna firji ɗina, sun san me sukeyi." inji Aunty kaltume,

Sallamarshi ya katse musu hira, a gurguje ya gaishesu ya wucce ɗakin Umma dake akwai kayanshi a ciki dukkansu basu damu ba, aikuwa yana shiga ya hango ni............




*Don Allah kuyi hakuri jikin yaki min sannan ku tayani sharen ɗinshi*

Voter,comments👍
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*



*:~•27*

       Shigar dani falon umma akayi, sannan aka watsa min ruwa ajiyar zuciya nayi sa'anan na rufe idanuna, kwalla na zuba daga idanuna a hankali nake tambayar kaina a zuciyata nake cewa.
_Wani laifi haka nayi me girma da kome nawa yake zama koma bayane, naga dai sauran mutane ba haka ake musu ba toh ni me yasa nawa ya kasance haka, wata irinyar qaddara take bibiyata ce haka,Ya Allah Alhamdulillah da kayo ni musluma..._ Sannan na fashe da kuka inda na juya musu baya sabida zuciyata na min zafi da,zogi, duk aka rasa mai rarrashina.

      Umma kuwa gidan Shatima ta shiga ranta a ɓace tayi sallama duk matan gidan suka fito sabida sunji muryanta a fusace kuma ita ba ma'abociyar fitina bane balle sunsanta a haka, mace ce mai mugun hakuri da kawaici koda zaka mata abu dan tayi magana toh bazata taɓa magana ba asalima sai tafita tsabgarka dan bata son damuwa.
               Hajja Yagana ce tafito daga ɗaki hankalinta a tashe cikin mamaki tace.
"Batula lafiya kuwa irin wannan sallamar haka. Da gani ranki a ɓace yake mai yayi zafi shi ba wuta ba,ki shigo muyi maganar a ciki tunda Alhaji yana waje."

      "A'a Yagana daman shatima ya karɓawa Imamu auren Yar gidan Yakolo dan atozartani ne? Ko yakarɓane dan tabashi wani abin duniya a cikin bainar jama'a Yan rakiyan Hauwa suna cin mutuncin Y'an uwan A'isha, toh tun muna shaida juna yayiwa Yakolo kashedi daga ita har Y'arta inba haka ba kuwa...."

      Ta juya tafita a fusace har takai bakin kofa sai ta tsaya cak sannan tace.
"Tabbas Yarta zata koma mata a matsayin karamar bazawara mara daraja da kima kamar budurwa kar akureni a barni a yanda nake, kar akaini bango domin idan tura takai can,toh abinda zai faru babu kyau, zan iya nunawa Yakolo nice na haifi Usman ba ita ba Y'arta ba anyi na farko kar ayi na biyu." Tana kaiwa nan tayi waje abinta zuciyarta na zafi, Innalillahi tacigaba da nanatawa tare da ambaton Allah,

           A falon Ya Ali da Ya Abubakar tare da Abba lawan, rutsa Imamu sukayi cikin faɗa babu k'akautawa, dafe goshinsa yayi da jijjiyar suka mike raɗa-raɗa, idanunsa sunyi ja, Ya Masur yace.
",Yanzun don Allah ka kyauta kenan wannan abun da meyayi kama, kasa Iyayen Yarinya da Y'an uwnta sun tafi wai meke damunka ne,?" ya jefa masa tambaya cikin damuwa.

      Abba lawan wanda ranshi yakai kwalolowan ɓaci yace.
"Gajin hakuri mana,duka duka yau xa'a baka, matanka amma sabida masifar rashin hakuri gashi kaje ka zubda mutuncinka a gaban mutanen da suka baka dukan yardansu,"

       Abubakar kasa magana yayi yana kallonshi sannan yace.
"Shawara ɗaya zan baka ka ɗauki A'isha ka tafi da ita, karka bari Umma ta fahimci haka dan idan kaci gaba da zama a garin nan ranka ɓaci zaiyi, dan Wallahi ba zata baka ita cikin sauki ba, shawarata kenan idan tasan ka tafi da ita vazata damu ba akan, kana zaman jiran tsammanin tavaka ita."

      Nan suka kare da bashi shawara shidai baice musu kome ba, har suka gama maganarsu godiya yayi musu sannan ya mike zai fita sai Mansur yace..
"Yau mai bada shawara kyauta shine ya karɓi shawarmu kyauta abu yayi kyau."

      Murmusawa yayi sannan yafita, yabar gidan gaba ki ɗaya, gidanshi dake locowst yaje ya shiga ya kwanta, idanunshi a rufe sabida matsanancin ciwo da kanshi yake masa, dafe kanshi yayi cikin damuwa jin danasani abinda ya faru jiya yake, inda ya ɗaura laifin akanshi baki ɗaya, a take yayiwa kanshi alkawarin ba zai  takura min ba indai haka zai sanya ummanshi farin ciki.

      Bai bar unguwan ba sai wajen karfe huɗu da rabi....

~~~
      Umma khadi tana zaune sai hakuri take bawa Umma wacce sabida ɓacin rai sai cira take, kaman zata tashi sama, gani ni kuma naki daina kuka, abun dai ba daɗi kowa ranshi bai masa daɗi ba.

       B'angaren Amarya hauwa kuwa iyayi da kinibibi sai wanda ya karu dan tunda tayi wanka ta shirya ta kwanta sai nishi take ita ta kwana da namiji ya dagargajeta, ko banɗako zata shiga kafafuwan a ware, kace yar kaciya(😂) Kawarta Safna ce ta gaza hakuri cikin jin haushi tace.
"Amma Lady da kin ajiye wannan iskancin nako idan mun tafi kya gumawa kishoyarki, ba mu ba kina tafiya a ware ke gaki kin kwana da namiji, Allah yabawa sauran matan auren da manyan da suka rakoki hakuri, dan kafin kisan namiji mata dubu sunsan shi, iskancin banza kawai, wallahi banga abin farin ciki ba da zan bawa namiji kaina kafin ayi buɗan kai, duk masifarka hakq zaka hakura dani, dan nayi Imani da Allah yagama ɗaukinki kenan,"

     Juyawa tayi gurin matan da suka zagi yan uwana, cikin ɓacin rai tana kallon cikin idanunsu tace.
"Kaman Yanda kuka watsa musu taro haka kuma zaku saka kai mubar garin nan ce muku akayi kima kuka ja mata, toh bari in faɗa muku, rigima kuka hadasa mata, ita mw shegen baki tazo tana faɗa muku karya toh kuna can kuna shuka musu rashin mutunci ita nankuka take, dan hankalin miji ba akant yake ba, da ita yake damuwa amma hankalinshi ba a gurinta yake ba yana can gurin matar mutunci, ai kunyi kuskure domin kodaga, girman gida ya nuna muku ita yake yi, amma dake ku jakuna ne kun ɓuɗe baki kuna zaginta, sisin gwal fa ya biya asadakinta nawa ya biya a na hauwa,ai wutsiyar rakumi yayi nesa da kasa, ki duba daga falonta nafarko zuwa ɗakunanta, kinsan tafi karfinta shine zaku musu hauka hmm yau duk zamu bar garin gwara ku tattara naku yanaku mubar musu gidan dan bazan iya kallon abin kunya da kuka shuka ba, kuma Aunty Hajja kuna ganin abinda akayi amma kun gaza kaɓarsu, mitssw" taja musu tsaki tafita daga gidan,
           Fita kofar gidan tasami Imamu da sauran Yan uwanshi suka gaisa, basu hakuri tayi sannan tace.
"Muma yau zamu bar garin nan, dan akwai masu uzurirrika a cikinmu, kuyi hakuri da abinda ya faru,"

          "A'a yanzun yamma yayi kubari sai gobe, sai ku tafi xaifi dacewa" Inji Imamu,

" A'a mun gode ma haka don Allah kubarmu mutafi yau, zaifi dan ni gobe ina da class karfe takwas nasake, zamuyi test idan bazamu takura muku ba."

Takarshe maganar tare da wasa da kasan mayafinta.
Shiru yayi sannan yace.
"Toh ba damuwa kushirya yanxun motar zai zo Insha Allah."

Godiya tayi sannan ta juya tabar gurin,

Koda tashiga kallo ɗaya tai musu sannan tace.
"Sai kusami shirya kayanku dan an jima motar zata zo mu wucce gida."

Tana gama faɗa musu ta shiga kintsa kayanta kokallon sauran manyan cikinsu batayi ba, Safna yar kawar Yakolo ce kuma mahaifinta me kuɗine sosai a maoduguri, ita ce mace ɗaya a cikin maza biyar da take bi, kusan da bazar Mahaifiyar Safna, Yakolo take taka rawa, dan Hajiya Zainab tana matukar yin Yakolo kodan hali yazo ɗaya ne shi yasa nasu, amma dukda haka ita hajiya zainab tana da kirki sannan tana kyautatawa mutane, bambancinta da Yakolo kenan dan masifaffiya ce ga kyashi da hassada, ita kome natane banda kowa.

Wani ikon Allah dukda halin hajiya zainab sai gashi duk yaranta babu wanda ya ɗauko kome a ciki sai ma hakurin mahaifinsu da rashin son shiga hayaniya, haka ma Safna sam bata da mugun hali korawan kai sa nuna ita wata ce, shi yasa da ta sullesu da faɗa babu wanda yayi yunkurin hanata dukda akwai manya a cikin ɗakin kuwa.

Bayan kaman mintuna goma sai ga motar da zai kaisu gida yazo nan suka fita, tsakar gida tsamo tsamo, ganin ana raban kayan garan da Y'an uwana suka kawo ganin yanda kowa kw faɗin "Masha Allah, Lallai Imamu yayi dace ai gara shine kimar mace, mace a auroki babu gara ai babu kima a ciki kodan gudun gori ai akawo mata"
Haka mata suke ta faɗa, sai jikinsu yayi masifar sanyi basu tsinke ba sai da aka ware kayan uwar miji da na Yayun miji a na Kane gami da kayan Matan Yayu da kane sannan na yaran gida, ai jikinsu na rawa sukayi sallama, zasu tafi fatan Allah ya kiyayye hanya suka musu, sannan suka fita koda suka fita babu wanda yasake bin ko takansu balle maganarsu.


Haka akayi rabon komi cikin farin ciki, wanka Umma tasa nayi sannan aka ciro min shaddar da zan saka, dakyar nabar Fahima tayi min kwalliya, ina zaune a ɗaki kaman mayya daman yaran gidan duk suna cikin ɗakin tare dasu muke zaune sai kaɗaici ya ragumin, cikin gida wajenmu kuwa an rufe min ɗakuna na,


Har dare babu ango babu dalilinsa, dan kuwa gidanshi na can yaje ya zauna abinshi, haka Amarya Hawwa kuwa anci kwalliya ana jiran miji, daman nikan bansa akaina ba, dan a yanxun haka sabon haushinsa nake ji, ba nawasa ba.


Wayata da take jikin chaji, dan Fahima ce tasa na zare na kunna dan ta mutu, tana gama lodin tayi seti sai na lalluɓe nomber Aunty Hajrah tana ɗaukar wayar na fashe da kuka, har da shassheka, a hankali tace.
"Haba my cutie Esha bar kuka haka kinji autar Innaji mukunsan isa gida zan miki magana idan muka isa kinji ga Aunty Zuby"

Aunty na karɓan wayar tace.
"Baby is crying eeeh eeehi, bar kuka jin kiyi hakuri, ko kina son ace Yan uwnki da suka zo kawo ki a aurenki sai da suka bar miki abin gori sukayi faɗa dan suna tayaki kishi, haka da mukayi mun nuna musu tarbiyarmu ce, dan matukar mukaci gaba da zama a Yobe zamuyi abin kunya, kuma kinga gidan mutanene masu mutunci da daraja, bai dace mu biyewa yan uwan kishiyarki ba, kuma ina jan kunnenki da karki kuskura ki fara cewa zakiyi tankiya da ita ki bawa iska a jiyarta, ki kuma cigaba da girmama Uwar mijinki da Yan uwanshi, karki bari abin duniyarki ya rufe miki idanu, koda wasa karki ce zakiyi kwauron abinci ki dafa sosai ki zubawa kowa a gidan, sannan Uwar mijinki ki ɗaurawa kanki ɗawainiyar kulawa da ita, nasanki da son Yara karki k'i yaranshi kijasu a jiki, ki nunawa Umman kinfita son yaran ma, Sai abu nagaba karki zama me rokonshi, akwai Atm card Babane ya buɗe miki accunt a First bank, idan Allah ya horre masa zaki ji alarm, karki zama kazama, dan yin haka zai ja miki raini, banda kai kara sannan wannan shegen kukan ki ajiyeshi a gefe guda, karki bari kishiyarki tasan sirrinki, koda faɗa kikayi dashi har Ummanshi karki bari tasani, duk abinda zakuyi kuyi a ɗaki karki fito waje duniya tasani ki girmamashi, dan basa'anki bane, idan da yayi aure da wuri da ya ajiye irinki, don Allah My Indo ki ajiye buhun wauta da shirmen nan ki rike mijinki, Ki tsayi da sallarki kiji tsoron Allah karki ce zaki ɗauki kobonki da sunan zakije niman maganin mallaka zuciyar miji a hannun Allah yake idan kika zauna dashi kika masa biyayya, Allah zai mallaka miki kome nashi bama shi ba kiyi hakuri lil sister ƙi zauna da kowa lafiya wallahi wata rana Allah zai bamu aron lokaci, ki sake faɗa min, wani cigaba da kika samu atare da dangin mijinki, Kiyi hakuri da abinda ya ringa faruwa Allah ya jarabbemu ta hanyoyi da dama kuma muna fatan Allah yasa haka shine mafi alkhairi, kibarku kan haka kinji zan barki haka banso muyi maganar ta waya ba karki bari Ya kawo mana karanki kuma kinsan Baba bai yarda da Yaji ba Allah yayi miki albarka sai munzo suna."

Muryana na rawa nace.
"Insha Allah Aunty zanyi duk abinda kika ce, da Yardan Ubangiji bazaku taɓa jin wani abu daga gareni ba, Aunty nagode Nagode Allah ya saukeku lafiya sai anjima ku gaidamin My Ramla da Innajina da Ya Ishaq da Babana ina kewar rankwashinku."

Dariya tasaka tace.
"Yar banza wato rankwashin ma abin kewane toh ai ba danuwa kice Malm Imamu don Allah kullum da safe ya dunga sake miki kusa akai idan yayi haka zai mantae dake kewarmu."

*_Sister Sadiya Zabura itace tace kar nayi muku typing sabida itama tana kaunar taga nayi Kuɗi da noɓel ko My Dear💃💃_*
[5/4, 06:19] Me Dambu:    🌹🌹👳
       *MATAR MALAM*
                             🌺🌺👳

          *Na:Mai_Dambu*
     
                *Wattpad:Mai_Dambu*


       *Happy Born A gain My Sultan yarona Allah ya karo shekaru masu albarka da nisan kwana*🍰🍦🍮🍬🍭
*:~•26*

       Murmushi yayi cikin jin daɗi tsuntsu daga sama gashashe kenan, ya fasha gemunshi yayi sannan ya karaso inda nake, ganin yanda najibga kaya a jikina, girgiza kai yayi sannan yayi magana a fili yace.
"Yanxun ba dan nazo ba haka zata kwana da shirgi a jikinta, sai tsabar wauta ba wayo da kata xakayi magana tafika da ambaliyar kwalla."

              Bakin gadon ya isa ya durkusa sannan ya zuba min ido, a hankali yana shakar kamshim jikina, wani irin shauki ke fizgarshi bai san lokacin da ya kai hannunshi kafin fuskana mikewa yayi ya isa fuskana ya sumbaci goshina zuwa bakina, ɗagowa yayi yaga dukda ac ɗakin bai hanani zufa ba, mikewa yayi ya shiga kiciniyar cire min kayana yake, dakyar ya samu ya cire min, lifayya sake jikina sannan ya zubawa ɗinki jikina ido, nan ma shagala yayi da kallona

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment