Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️

( ⚔️THE CHOSEN ONE ⚔️ )


🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥




🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN KAI,ME KOWA ME KOMAI.ME RAYAWA,ME KASHEWA.ME YIN YANDA YA SO KUMA A LOKACIN DA YA SO. TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU ƘARA TABBATA GA MASOYIN MU ANNABIN RAHAMA,FIYAYYAN HALITTA DA BABU KAMAR SA ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM❤️💯*

Ina sake miƙa godiya ta ga Allah Madaukakin sarki da ya nuna min wannan lokaci haɗe da banI damar sake rubuta wani labarin.
Masoyana ina farin cikin sake kasancewa da ku a cikin wannan littafin nawa me Suna ƊAYA CIKIN BIYU. ina fatan yanda ku ka bani hadin kai a sauran littatafai na wannan ma zaku bani. to akafta kawai,wannan littafin yazo da Salo daban-daban, Wanda ban taɓa kawo muku shi ba. Ku kasance dani Mrs isham dan Jin wannan kayitacciyar labarin.🔥😍❤️❤️❤️

Ina masu son tallata hajarsu?,masu son a yi musu tallar kayan sana'ar su domin samun kostomomi to Kar ku yi Kasa a guiwa ku garzaya ku Kira wannan layin nawa 08166018849 Mrs isham.



🤍Date: 01/07/2024 💘📚🖊️







❤️🔥Page 1__2




*KUWAIT*


Ƙasar Kuwait, ƙasa ce a yammacin Asiya,tana arewacin gefen gabashin larabawa a bakin tekun Farisa,tana iyaka da Iraki zuwa arewa da Saudiyya a kudu. Kuwait ƙasa ce ta larabawa.an san Kuwait don al'adar wasan kwaikwayo na gida, Kuwait ita ce kawai ƙasar Larabawa a yankin gulf Farisa masu al'adar wasan kwaikwayo, kungiyar wasan kwaikwayo ta labarci a Kuwait ta kasance wani babban bangare na rayuwar al'adun larabawa na ƙasar.
Dinar Kuwaiti wato kudin Kuwait, ita ce mafi girman darajar kudi a kaf faɗin duniya,a cewar bankin duniya, Kuwait ita ce kasa ta biyar mafi arziki a duniya.

Yawancin yan ƙasashen waje suna Ƙaura zuwa Ƙasar Kuwait,suna samun sha'awar yawan albashin su ne,domin suna daya daga cikin manyan Ƙasashen da suke bada albashi me tsoka da gwabi, sannan kasantuwar babu haraji da za'a biya da ze cutar da yan kasar.masu ƙaura zuwa ƙasar kuwait sun yarda cewa ƙasar na iya bada kyakyawar rayuwa tare da duk abubuwan jin dadi domin ƙasa ce da Allah ya albarkaceta ta fannin arziki me tarin yawa.


MASARAUTAR BAYAAN DAKE ƘASAR KUWAIT.


Masarautar Bayaan babban Masarauta ce da babu irinta akaf faɗin nahiyar ƙasashen Larabawa, Masarauta ne da yake riƙe da al'adu na gargajiya da kuma ilimi da wayewa akan harkokin rayuwa,masarauta ce me karfin gaske wanda suke faɗa a ji a ko ina,tana da rundunar sojojin mayaƙa masu tarin yawa. sannan akwai arziki sosai a cikin masarautar Bayaan.akwai su da doka me tsanani .hallau masarauta ce me adalci da kuma sanin hakkin bayinsu da suke mulka,duk da ako ina ba'a rasa ɓata gari ,amma sarakunan da duk suke mulkar Bayaan to sun kasance masu adalci da kuma kwazo da jarumta.
tun daga kan sarki na farko har izuwa kan sarki na takwas wanda shine yake mulkar kasar a yanzu, abubuwan da masarautar suke dashi kuma suke tunkaho dashi shine,yawan dukiya da mafi yawancin masarautu suna zuwa gare su karɓar bashi domin ciyar da bayinsu,suna da yalwatacciyar abinci da suke wadata bayinsu dashi shisa inde ka ga bawa babu alamun yunwa a jikinsa tofa daga masauratar Bayaan yake,suna da tsaro da kuma sojojin yaƙi masu yawa da kuma tsorata abokan gaba an horasu ne domin bada rayuwar su da kuma karfin su bawa masarautar Bayaan kariya,sun samu horo me tsananin gaske kuma dukkansu gwarazane masu jini a jika,ma'abotan tsorata zuƙata.
masarautar tana da albarkar ruwa me dadi da kuma yawa wanda suke amfani dashi domin yin noman abinci,ga kuma girma da ƙa wa da masarautar take dashi.ga kayan ado na gwala-gwalai na danyen lu'ulu'u hatta kujerar sarautar na lu'ulu'u ne,duk wani wanda ya shiga masarautar baya taɓa kwadayin fita .saboda yanda aka ƙawatar da lungu da saƙo na masarautar da zallar fari,game da haɗi da jan lu'u-lu'u.suna da riko da addini duk da acikin Bayaan akwai wa'yanda suka kasance ba Musulmai ba haka zalika babu bambancin addini a masarautar.
Babban abinda ma'abota rayuwa a masarautar basu sani ba shine Bayaan tana samun kariya da tsaro ne daga wajajen rauhanan aljanu da suke lura da komai na Bayaan.


A shekata ta dubu ɗaya da sittin da shida,sarki Mustapha Abdullah Rahman shine sarki na farko a masarautar Bayaan,sarki ne me adalci da imani,haɗe da tausayi.yana da ahalinsa da suka kasance matarsa ɗaya se ya'yan sa maza guda biyar wanda sune sulaiman Abdullah Rahman, Muhammad Abdullah Rahman, Abraham Abdullah Rahman,nooradeen Abdullah Rahman, Yousuf Abdullah Rahman. Dukkanin su sun taso ne masu kaunar mulki har sukayi aure suka hayayyafa,a lokacin da sarki Mustapha Abdullah Rahman ya tsufa sosai nan ya sauka daga kan karagar mulkin sa,domin bawa daya daga cikin ya'yan sa saboda yanzu ya yi tsufar da baze iya cigaba da mulki ba,kuma dole a samarwa Bayaan sabon Sarki haka yasa aka duba wanda yafi chanchanta a cikin ya'yan sa guda biyar din man.domin masarautar Bayaan bata bi ta kan cewa waye babba waye karami wanda yake da tausayi da kuma nagarta shine wanda ake bawa sarauta.hakan yasa aka ga Yousuf Abdullah Rahman yafi ko wannensu cancanta yasa aka naɗasa a matsayin sabon sarkin Bayaan,wasu daga cikin yan uwansa sun yi farin ciki wasu kuma sun ji haushi sosai saboda yanda suke kwadayin hawa kan karagar kuma babban takaicin su shine koda a ce ya mutu ya bar duniya.
Su bazasu taɓa samun wannan kujerar ba,har se in beyi aure ba kuma be haihu ba,amma muddin yana da yara ko mace ko na miji to dole ɗan sa za'a bawa Sarautar,wannan shine doka da kuma tsarin Bayaan. duk Sarkin da yake mulki ya zamana ya mutu ko kuma yanason ya yi murabus tofa baza'a bawa dan uwansa ba ko kuma wani bare ba, dole ya'yan cikinsa ne ze mulki Ƙasar. Hakan yasa wannan sarautar da aka bawa Yousuf Abdullah Rahman ya yi wa dayawa zafi a cikin su da har suka yi wani nufi a ransu.
Bada jimawa ba kuwa sarki na biyu wato sarki Yousuf Abdullah Rahman ya fara mulki kamar yanda mahaifin su yai yi cike da gaskiya da amana,har lokacin da sarki Mustapha ya mutu.

A haka rayuwa yaci gaba da tafiya a yayinda mulki yake tafiya kan ya'ya da kuma jikokin Mustapha Abdullah Rahman domin yanzu haka ana kan sarki n biyar wanda ya kasance jikan jikan Yousuf Abdullah Rahman,wato Khalid Mudassir Rahman haka shima yana gabatar da mulkinsa yanda ya dace,a yayinda zuriyar Rahman suke cigaba da haɓaka to ko ina domin aure suke yi kuma haihuwa suke kowa da matansa da ya'yensa har ma da jikoki.

Bayan shekara ɗari huɗu,wanda ya zama shekara ta dubu biyu da daya(2001) a wannan karnin Sarki na takwas ne yake mulki waƙo sarki TAIFUR MUZZAM RAHMAN shine wanda yake mulkar masarautar da yake sa'ke haɓbaka.komai ya sauya kamar yanda zamani ya sauya,Sarki ne me ƙima da daraja wanda yasan kan mulkin da yake yi.kowa yana son shi saboda yanda yake da adalci da kuma tausayin talakawa da kuma kyautata musu.wannan ne ya sake wanzar da soyayyar sa a zuciyar talakawan sa.

Sarki TAIFUR MUZZAM RAHMAN yanada mata kwalli daya me suna Sarauniya Fatima.kuma ita din yar Sarkin yammacin ƙasar Yemen ce,yanda mijinta yake da hali nagari haka itama domin ko a Masarautar su na Yemen kowa na kaunar ta,kuma bugu da ƙari jaruma ce.suna matukar son juna ita da sarki TAIFUR har Allah yasa ta samu cikinta na fari sosai suke nunawa wannan cikin so da kauna,basu damu da menene a ciki ba ko mace ko namiji su de suna kaunar cikin.haka talakawa da bayi kowa yana iya kokarin sa wajen nuna bajintar sa ta hanyar yin kyauta da iya karfin su wajen matar sarkin su me adalci .kuma hakan na faranta musu rai sosai, haka suka cigaba da renon wannan cikin da ko da yaushe girman sa ƙara wuce misali yake.


Tun lokacin da Sarauniya Fatima ta samu ciki ta ke wasu irin munanan mafarkai marasa kan gado,kuma masu caza kwakwalwa in de aka bi komai da ki-da ki,sede waye ya wani damu da ya san ma’anar mafarki?.wannan dalilin yasa bata taɓa sanarwa da sarki ire-iren mafarkan da take yi ba domin ta dauke su a zubar gado shirme.


Masarautar Bayaan yanada wani babban malamin duba dake duba musu lamarin masauratar daga mummunar abinda ze faru,har zuwa kyakyawar abinda ze faru, me suna Sheikh Abu Dhabi.kuma ya kasance yana tare dasu ne tun lokacin da sarki TAIFUR RAHMAN ya hau karagar mulki.
kamar yanda yake tun zamanin kaka da kakanni. duk Sarkin da ya hau sarauta to za'a naɗa sabon malamin duba da kuma sanin lamurran masarautar ta hanyar duba.

Tun lokacin da sarauniya Fatima ta samu ciki, sheikh Abu Dhabi ya zo ya samu sarki da maganar cewa wannan cikin nata da take ɗauke dashi ze zo ne da abubuwan al'ajabi masu tarin yawa.
Cikin da take ɗauke dashi ze wanzar da zalunci da kuma adalci, ze wanzar da ƙangin bauta,Kuma ze wanzar da zaman lafiya da ƙare talakawa,ze kuma tarwatsa kan masarautar da wa'yanda suke cikinsa zalunci ze gudana a yayinda bashi da rai, komai ze tarwatse sede komai ze dedeta daga karshe......

Ko da jin wannan al'amarin ya girgiza Kuma ya ɗagawa sarki TAIFUR RAHMAN da matar sa hankali,jin abinda Sheikh Abu Dhabi ya faɗa sun shiga cikin matsananciyar damuwa da tunanin ya goben wannan masarautar ze kasance,hakan ne yasa sarki TAIFUR ya saka Sheikh Abu Dhabi ya masa binciken abinda ke a cikin Sarauniya Fatima.ko da ya yi bincike abinda ya iya ganowa shine haske da duhu.wato akwai tsananin haske me yawa acikin,da kuma duhu me tsananin tsoratarwa a ciki,nan ya fahimci yan biyu ne a cikin nata sede saboda launi biyu da suka bayar fari da baki yasa ya gagara gane kan cewa mazane ko kuma mata,bayan ya gama bincike ya sanar da sarki abinda ya gani.nan ne hankalin sarki ya kuma tashi yana me addu'ar Allah ya ƙare masarautar sa daga abinda zasu haifa domin sharri ne da alkairi.

Lokacin haihuwar Sarauniya Fatima na yi ta soma nakuda. takai kusan kwana biyar tana nakuda sede bata haihu ba,hankalin kowa ka gani a masarautar zaka gane kan cewa a tashe yake,duk wasu ungonzoma da aka san suna karban haihuwa a kasar seda aka kawo su amma shuru bata haihu ba.
Hankalin sarki Taifur Rahman ya dugunzuma ya tashi abu da yawa suna masa yawo a tsakar ka,yana zaune akan kujerar karagarsa a cikin babban fadar da babu kamar sa,ga manyan fada su ma suna zaune kowa da abinda yake tunani . damuwa ƙarara ya bayyana akan fuskokin su,da kuma tausayawa Sarauniyar tasu da yau shine kwana na shida tana nakuda amma bata haihu ba se shan baƙar azabar da take yi.

Wani Bafade ne ya shigo fadar da sauri kamar ze tashi sama hannunsa rike da wata gora mara girma ya nufi kusa da wazirin sarki ya ajiye masa yar goran a gabansa.yana zubewa bisa guiwowinsa.
Cikin fitar da numfashin wahala da nuna alamar yasha uban gudu ya soma fadin

“ Ina me Neman afuwar fada,domin na kawo abinda ba'a saka ni ba,amma shugabana a mini afuwa na tuba bazan iya jure wahalar da Sarauniyar mu take sha bane yasa na dau doki na tafi birnin Iraqi wajen kakan mahaifiyata da ya kasance Malami na karbo ruwan addua wa Sarauniyar mu”.

Shuru fada ya kuma ɗauka,se kallon wannan bafaden a ke yi hatta sarki shuru ya yi ya tsura masa ido yana gyada Kai,kallo daya da ya masa ya Karance sa tsaf ya hango zallar tausayi da kuma Gaskiya a kwayar idonsa.

Kallon sarki waziri yayi na neman amincewar sa, gyada masa kai sarki yayi alamar yayi na'am dashi,duban wani bawa dake tsaye a gefensa ya yi nan take ya soma magana.

“ ya Kai bawan wannan masarautar!, sarki ya yi na'am da kokarin ka,kuma ya jinjina maka ga bisa jajircewarka,amma muddin Sarauniya tasha wannan rubutu wani abu ya sameta zaka biya farashin hakan da rayuwarka “.

Katse sa sarki Taifur Rahman ya yi ta hanyar daga masa hannu sannan ya furta

“ babu bukatar saka kokonto akan abinda yake tafe dashi domin hakan ze zama kamar an disashe kyakyawar manufar dake cikin wannan abinda ya kawon.A ko da yaushe a na son dan adam ya yi abu da zuciya daya. kuma manufa daya,bawai ka kasance mara kyakyawan yakini ba,ka zama me zuciya me kyau da kar ban ƙaddara a ta duk inda yazo maka.
Dan haka ni sarki Taifur na yi Imani da Allah wannan ruwan addu'ar baze zamo cutarwa ga mai dakina ba,kuma na jinjinawa wannan mutuntaka irin naka dan saurayi”.

Kowa ya gamsu da bayanan sarki se gyada kai suke yi,kamar wacce aka hantsilota cikin fadan ta fado tana zubewa a kasa.
Ko da suka ganta a wannan hali bakaramin girgiza zuciyoyinsu ya yi ba ,domin suna tsoron kar taxo musu da Mummunar labari.

MiƘewa tsaye sarki Taifur Rahman ya yi ya dubeta yana fadin

“ amintacciyar baiwa shin wannan shigo war ta lafiya ce ?”.

Muryarta na rawa ta furta “ Allah yaja da ran sarki ya daɗe,. Uwar gijiyata na matukar shan wahala. har ila yanzu bata sauka ba, tayi galabaitan da batama tasan su waye a kanta ba, idanunta sun soma sauya launi ya shugabana wannan al’amarin ya girmi tunanin mu “.

Kowa ita kawai ya kasa kunne yana saurara.
Komawa kan kujerar karagarsa ya yi ya zauna yana cire hular sarautar .
Ganin halin da sarki ya shiga ne yasa waziri ya bata umarnin ta ɗauki ruwan rubutun ta tafi dashi a bawa sarauniya.

Cikin saurin da take yi amintacciyar baiwa ta shiga sashen sarauniya. tun kafin ta Kai da isa take jiyo nishin wahala da azaba da take yi,a hanzarce ta faɗa dakin,ungonzoma guda biyu suna rike da hannunta kan su gaba daya ya dau zafi.
Dan sun gama sadakarwa bazata tashi ba.koda suka ga shigowar ta tambayar ta suka yi shin ya ake ciki domin su sunyi iya kokarin su fa abu ya gagara.
Miƙawa daya daga cikinsu goran rubutun tayi.

Buɗe bakin sarauniya Fatima da bata ma San a wata duniya take ciki ba,shin lahira take ko duniyar dake cike da tarin radadin azaba ta kasa fahimta. Ruwan rubutun suka saka mata a baki tasha sosai.

Shuru nakuda ya tsaya cak duk wani radadin ciwo seda ya tafi ta soma dawuwa hayyacinta.hamdala suka yi ganin ta somu sa’ida ba kamar dazun ba har ma tana magana.
Cikin abinda be fi mintuna talatin ba ta sake birkicewa sakamakon wani bala’in ciwon mara da ya hasasota a gaba. wani irin jijjiga jikinta ya somayi kamar wacce zata bar wannan duniyar hatta idanunta sun soma rikidewa.

“ innalillahi wainna’ilaihi rajuun amintacciyar baiwa shin guba ki ka kawowa Uwar gijiyarki ko me!?”.
Matar waziri ta faɗa hankali a tashe ganin abinda sarauniya take yi.
Gaba ki daya wa’yanda suke dakin hankalinsu ya dugunzuma ya tashi in banda kerma babu abinda jikin su yake yi musamman ma da suka ji abinda Matar waziri ta faɗa.

" na yi imani da ubangijina bazan taɓa cutar da uwar gijiyata ba.wannan ruwan rubutun na karɓo sa ne a fada.
Dan Allah ku rufamin asiri".

Suna tsaye akanta suna zazzare idanu cikin dimauta,suka ji tayi wani nishi me karfin gaske tana kiran sunan Allah.a sukwane suka dawo kanta suna dubawa nan suka iske kan jariri ya fito cikin gagga wa suka taimaka mata suka fito da santaleliyar kosasshiyar jaririya me ji da lafiya.
Ungozomar da ta fito da jaririyar ce ta dagota suna kallonta,domin babu wanda ya yi tunanin wannan yarinyar yar bil adama ce saboda yanda kamaninta yake na tsantsagwaran kyawu da ubangiji ya mata.
Tana kokarin yin magana suka ji ta sake yin wani sabon nishi Wanda ya fi na farko ,sake komawa kanta suka yi a wannan Karon ma sun fito da wata jaririyar da ta kasance sak yar uwarta babu abinda ya rabasu, komai din su iri daya kamar wa’yanda a ka yi zannen su tsabagen kyawunsu duk wani mutum in ya gansu se ya ji ya tsorata.ita ta biyun da aka fito da ita se callara kuka take yi.

Ɗaga su duka biyu Matar waziri tayi tana kallon su,hakikanin gaskiya tunda Allah yakawota wannan duniyar bata taɓa kallon mutane masu muguwar Kama da juna da kuma kyau ba se a kan su.

“ tabbas tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin halittu,wannan yara da abin mamaki ku ke “ ta fada tana kuma kallon fuskakinsu daya se kuka take a yayinda ta farkon ko tari batayi ba.

Gyara jariran aka yi aka bawa amintacciyar baiwa domin tajewa da sarki babban tsaraban da Allah ya basa,su kuma suna gyara sarauniya da baccin wahala ya sureta.
Ko da ta shiga fada gaba daya miƙewa suka yi.hatta shi sarki da Kansa ya taso yana nufarta haɗe da buɗe hannayensa.
Sarki TAIFUR RAHMAN ya yi murna tare da kaunar ya'yan nasa guda biyu ya manna su tsam a jikinsa yana miƙa godiyarsa ga Allah. yayinda wani bangare na zuciyarsa kuwa tsoro ne fal a ransa.
se san nan ne hankalin kowa ya kwanta. inda labarin haihuwan sarauniya Fatima ya karaɗe masarautar,nan kowa ya fara murna ana jin dadi.
Amintacciyar baiwa ta samu kyautar dinar masu yawa da zinari a wajen sarki Taifur,tukuicin albishir da tazo masa dashi. Shi kuwa wannan bafaden da yazo da ruwan rubutun sarki ya sa an basa wani mukami a cikin matsagaitan manyan fada.

Galadima Abdul Aleem Rahman bayan ya samu labarin abinda ze faru nan gaba yasa ya tafi har birnin sin.dan samo makarin da za'a basu wanda ze kashe baƙin ƙaddarar dake a tattare da daya daga cikin su, domin bazasu iya gane wacce me farar haske da kuma wacece me baƙin duhun ƙaddara ba.

Sarauniya Fatima ta ji dadi sosai da Allah ya sauke ta lafiya,bata gajiyawa da kallon ƴaƴanta din domin masifar kyau da suke dashi. ta yi imani da Allah kaf cikin ahalin Rahman da kuma ahalinta babu wa'yanda suka kai su kyau,kowa ya shigo yana marmarin ɗaukan su hatta kishiyoyin balbalinta suna ta santin yaran,har zuwa lokacin hannun su na kankame da na juna sun ƙi saki sannan kuma acikin jariran guda dayace kawai take kuka amma dayar ko tari batayi ba, kuma an duba an ga lafiyarta kalau amma sam ta ƙi kuka.har irin abin nan da akewa jarirai dan su yi kuka seda aka mata amma fa ta ƙi koda taɓe baki ne,hakan be wani dame su ba tunda an tabbatar musu da lafiyarta kalau.

Haka aka cigaba da kulawa da jarirai da uwar su har zuwa ranan suna an yi kyaututtuka sosai dan nuna farin ciki da samun ƙaruwa da suka yi manyan sarakuna na kusa da ketare sun halicci sunan,in da yaran sukaci suna MUZAINA TAIFUR RAHMAN da kuma MUZNA TAIFUR RAHMAN.

Galadima ABDUL ALEEM shi ya kasance babban ya'ya ne a gun sarki TAIFUR RAHMAN,yana da mata me suna Ummu zaheenat,yaran su uku maza biyu se mata biyu, babban ɗan su shine Farasat,se me bi masa sunan sa Haysam,se kuma Jadwah da Aliyah. Se kuma waziri Abdul Qadeer da ya kasance dan uwansu ta wajen uwa,matar sa ita ce Ummu Xulaihah,yana da yaran sa biyu Ishaq da kuma Hamra.

To rayuwa yaci gaba da tafiya a yayinda yaran suke girma kuma a nan ne aka soma gane bambancin dake tsakanin su.
bawai na kama ba,domin inde za ka bi ta kamanni ne tofa bazaka taɓa gane su ba .komai din su iri daya hatta tsayi yanayin magana duk da suna yara kuma masu shekaru biyar-biyar, amma ba zaka iya cewa wancan ce MUZAINA ko kuma wancan ce MUZNA ba,ta inda za ka gane su shine dabi'a da sakin fuska, MUZNA akwai ta da wasa,kowa in yana mata wasa zakaga tana dariya ko yaushe cikin dariya take,. hakan yasa ta shiga ran kowa a cikin masarautar kowa yana ɗaukanta yana mata wasa,a yayinda MUZAINA kuwa ko kaɗan bata dariya ko za'a shekara ana mata wasa tofa bazata taɓa sakin fuskarta da sunan tana dariya ba.se de ta tsare mutum da idanu,amma ko alamun murmushi babu a fuskarta ɓalle na dariya,hakan ne kaɗai ake iya bambance su,kuma ko tana tafiya ta faɗi a ƙasa bazaka taɓa jin tayi kuka ba,tun lokacin da aka haife su har zuwa yau bata yi kukan ba.
Tana da taurin zuciya da taurin rai.ga kuma rashin tsoro.ko sarauniya Fatima da ta haife su ko tana mata wasa bata dariya,hakan yasa fa sarki TAIFUR RAHMAN da ABDUL ALEEM RAHMAN da kuma Sheikh Abu Dhabi suka ci gaba da neman musu magani a gurin manya-manyan bokaye da malamai. domin karya wannan bakin duhun dake a tattare da dayarsu.ko kaɗan basu yi sanya a neman makari ba.

Wajen wani babban Sheikhy dake can arewacin birnin japanise suka je,nan ne ya basu wani makari kan cewa ze yi aiki sosai akan matsalar su.sede yana da buƙatar a nisanta su

Please Login or Register in order to submit comment