Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da masarautar har na tsawon shekara goma sha biyar akai su can wani guri suyi rayuwar su acan.a yayinda shi kuma ze ke gabatar da aikinsa domin aikine me karfi na karya nufayya.badan sarki yaso ba ranshi babu dadi amma babu yanda ya iya domin hakan da za su yi shine kawai mafita. Haka suka koma Kuwait cikin jimantawa.

" sarki na!…. shin taya yaranmu zasu samu kulawa batare da suna ƙarkashin inuwar mu ba?,kar ka manta su din jinin sarauta ne gaba da baya. Shekara goma sha biyar ba ƙananun shekaru bane". Sarauniya fatim ta fada tana zubda hawaye kanta na bisa kafaɗar sarki Taifur Rahman. Shafa doguwar sumar Kanta da tsayinsa ya wuce misali yayi.shi ma hakan na matukar damunsa in ya tuna yaran nasa da ya mallaka guda biyu rak a duniya,zasu yi nesa dashi yana jin zafin hakan.amma babu yanda ze yi dole hakan shine mafita.

“ Ina me ba ki hakuri masoyiyata,nima ba’a son raina hakan ze kasance ba. Wannan shine ƙaddarar mu babu yanda Zamu yi mu guje masa. Daya cikin ya'yan mu hatsari ce ga al’ummar duniya. Ko Kina son a ce yau Kin haifi annoba a cikin ki ?”. Ya mata tambayar yana kallon fuskarta,girgiza masa Kai tayi tana ci gaba da share hawaye.
Haka suka kasance a wannan rana cikin Karyewar zuciya.sosai sarki Taifur ya kwantarwa da sarauniya hankali.

Sosai sarauniya Fatima tayi kuka a ranar da za'a tafi da ya'yan ta.domin tun lokacin da ta haife su bata kuma haihuwa ba har izuwa yau.basu da wani zaɓi da ya wuce suka ɗauki MUZNA da MUZAINA suka kai su ƙasar Russia domin yin karatu da rayuwa a can har tsawon Wannan shekarun da Sheikhy ya dibar musu.

Daga nan ne labari da kuma ƙaddarar wa'yannan yara mata kuma yan biyu MUZAINA TAIFUR RAHMAN da MUZAINA TAIFUR RAHMAN ya soma.
Domin jin yanda ze kasance a cikin rayuwar su ku kasance dani Mrs Isham taku........

To kun sani ba se na sake maimaita muku ba,a har kullum ina faɗa muku comment din ku shine karfin guiwana. Dan wallahi yawan comment din ku shine yawan read more din ku,in bakwa comment kuma se a hakura da littafin gaba daya. Dan babu yanda zaa yi kana abu amma baka samun goyon baya bana jure haka.


Comment,like and share fisabilillah 🫶🏼🌹❤️



⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔

🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥




🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩





❤️🔥Page 3____4






BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYAR

A wannan shekaru goma sha biyar da suka shuɗe, MUZNA TAIFUR RAHMAN da kuma MUZAINA TAIFUR RAHMAN basu taka ƙafarsu a kasar Kuwait ba,suna nan suna rayuwar su ne a nan Russia.a tankamemen gidan su da mahaifin su Sarki Taifur Rahman ya mallaka musu, anan suka girma suka yi karatun su da komai kamar yanda Mai girma Sheikhy ya basu umarni kar a dawo dasu gida.har se bayan shekarun nan,to tabbas basu dawo ba,sede dangi ana kai musu ziyara can ƙasar Russia domin dubo lafiyar su,,a yayinda sarki ya damka musu ragamar wani shahararren company sa da yake ƙasar. domin su tafiyar da komai yanda ya dace,se de Muzna ta ƙi bayarda yardar ta, saboda abin da ya shafi sarauta dasu kasuwanci duk baya gabanta hasalima baya burgeta ko kaɗan .mafarkinta shine ta zama jarumar finafinai,kuma burinta ya cika domin yanzu ta zama cikakkiyar model kuma jarumar finafinai da ake ji da ita, yawancin poster ko magazine ko tallan manyan products za'a ga hoton ta a jiki, Muzaina kuma yanzu ita ce wacce ragamar Company sarki Taifur yake hannunta. ita ke juya komai domin duk wani abinda ze d’aga mata daraja tana so,ga shi ta taso da masifar kaunar sarauta.




THE INTERNATIONAL HOTEL CHAIN IN RUSSIA.

Babban hotel ne me girman gaske a Ƙasar Russia,babban dakin taro wanda girmansa baze taɓa iya misaltuwa ba cike yake makil da al'umma mabambamta .daga wajaje masu nisa da kuma kusa. Taro ne wanda ya amsa sunan sa taro,mutane masu mabambamtan addini da kuma a kida suna ciki,musulmai da kuma wa'yanda ba musulmai ba,suna a zaune a high table.kuma in ka duba zaka ga manyan governors ne da presidents ,haɗe da manyan attajirai na manyan ƙasashe. duk sun hallara, harma ka san ba wajen k’ananan mutane bane.
Kama daga larabawa, turawa, indiyawa, africans da de sauran su.
wannan taro yanda ya tara manyan masu faɗa a ji a duniya ya isa ya nuna cewa gomnatin babban ƙasar Russia ce ta shirya sa. domin,taro ne da ake yin sa lokaci zuwa lokaci kuma ya samo a sali ne domin tantance sarauniyar kyau na ƙasar.

Wani Bature ne riƙe da mic a hannun sa,dayar hannun kuma na riƙe da jerin list din sunayen yan matan da suka ci wannan gasa ta kyau na ƙasar Russia, kyawawan yan mata ne jere bisa kan dandamalin ko wacce tasha ado da kaya me ɗaukan hankali tana jiran sakamakon gasar.face mutum daya da kanta ke kallon k’asa,tana tsaye so calmly ba ta wannan rawan kan da sauran suke yi hakan ne yasa ban samu damar ganin fuskarta ba.

Wannan Baturen ne ya soma kiran wacce ta zo ta hudu,tafito taƙarbi roses haɗe da wani dogon kyalle da ke rubuce da miss Russia fourth position,haka aka dinga kira har ya rage saura a kira ta farko, wa'yanda suke tsaye a gun ko wacce kirjinta se lugude yake suna addu'ar Allah yasa a zabe su.


Mutumin ne ya sa'ke furta

" The winner is............"Ya yi Shuru kowa ya matsu so yake kawai a ji wacece wannan wacce ta lashe wannan gasar kyau din.

Se da ya ɗauki mintuna uku kafin da karfi ya ce

" And the winner is......... MUZNA TAIFUR RAHMAN Miss Russia".

Kaurewa wajen ya yi da tafi, yan matan suka soma tafi. wannan kyakyawar matashiyar da kanta ke kallon k’asa ne ta d’ago Jin an ambaci sunanta. Allahu akbar,kyakyawace ta k’in k’arawa domin kuwa tafi ko waccen su kyau.
Tsalle ta yi sannan cikin jin dadi ta rungume wacce ta ke kusa da ita, ta soma tafiya cikin cat walk,tana nufan wajen wannan baturen,jikinta na sanye da doguwar riga me masifar kyau,riga ce tsukekke daga sama zuwa cikinta,kasan kuma ya bazu sosai launin pink da launin baƙi,yasha ado da wasu azababbun duwatsu k’ananu daga sama har kasa.yana da doguwar hannu da yanka-yanka,kafarta na sanye da doguwar takalmi me masifar tsini.ga wuyanta da ke daure da yar siririyar sarka wanda Kai da kanka in ka gani batare da an faɗa maka gold bane zaka fahimci hakan.Haka d’an kunnen shima bayi da hayaniya komai dinta so simple and breath taking. ko ina na jikinta a rufe yake se dogon gashinta da aka mayar dashi curl hair style,fuskarta yasha adoh .kyakyawa ce sosai ta ajin farko matashiya ce yar shekara ashirin kuma model and actress,.tana tafiya cikin burgewa tana daga hannunta fuskarta ɗauke da murmushi har ta isa gaban wannan mutumin yai shaking hand dinta yana faɗin

" Congratulations MUZNA".cikin zazzakar muryarta ta ce " thank you".

Wannan dogon kyalle da yake rubuce da winner miss Russia,aka rataya mata a wuya wani juyi ta yi sannan ta soma tafiya irin na models har ta isa tsakiyar stage din,ta ɗan jujjuya cike da farin ciki.ta koma wajen da ta baro aka saka mata crown a kai tare da bata wani hadaddiyar roses masu kamshi da kyau.nan wajen ya kuma ƙaurewa da tafi ga hasken Cameras ta ko ina ana ɗaukan ta a hoto,ba ta waje a ka yi ta yi godiya sannan ta sa'ke da bayar da ɗan takaitaccen tarihin ta,sannan aka bata kyautar makudan kuɗaɗe,abokan gasan nata daya bayan daya suka zo suna rungumeta domin tayata murna,ita kuwa bakinta ya kasa rufuwa murmushin dake kan fuskarta ya kasa gushewa wanda shine yabada damar fito da azababben kyawu da Allah ya mata me kid’ima duk wani dan adam.

Fara ce sol Jajajir da ita,farin ta yana d’aukan ido na fitan hankali,kun san yanda farin larabawa yake base na muku dogon jawabi ba,amma duk da haka farin fatarta ya zarce misali.tana da tsayi dede gwargwado domin baza'a sakata a sahun gajeru ba,haka zalika tana da jiki haɗe da diri me daukan hankali. idan muka dangana zuwa fuskarta kuwa,tana da dogon fuska matsakaici, me ɗauke da manyan idanu masu haske sosai,kalar kwayar idonta light brown,sun kasance lumsassu,ga dogayen gashin ido da suka yi wa idon kawanya,tana da dogon hanci wanda ya kasance bangaren hagu a ɓule yake an saka masa nose pin,gashin giranta kamar wanda aka yi caving dinsa alhalin a haka yake,idan muka gangaro zuwa bakinta kuwa tana da cute small lips da suka kasance pink sosai gwanin burgewa da ɗaukan hankali.wasu kwantaccun suma ne kwance a gaban goshinta da yai luf luf,tana da tsawon gashi wanda ya kawo har kunkuminta duk da kuwa an mayar mata da gashin nata din zuwa curl hair style.kalar gashin kuma se aka mayar da shi light brown color.in takaice muku dai kyakyawa ce ta kin ƙarawa domin duk yanda zakuyi tunanin kyawun Muzna to ta wuce nan, idan masu karatu basu manta ba, sarauniya Fatima wato mahaifiyar su da kanta ta shaida kan cewa kaf faɗin ahalinta da kuma ahalin Sarki Taifur Rahman babu wanda ya kai su kyau.

Kallon danƙareren agogon hannunta ta yi ta ga lokaci nata wucewa,turo baki tayi tana kallon cikin wajen ko zata ga wacce take nema,amma bata ganta ba hakan yasa ta sadakar bazata zo ba.nan take ta ji wajen ya isheta gida kawai take da bukatar komawa.

" MUZAINA ba ta zo ba ko!?,ai dama wannan yar uwar ta ki ba lallai ta zo ba,na kuma faɗa Miki".
Wata kyakyawar budurwa ta faɗa wacce ta kasance kawarta.

Sa'ke kallon agogon ta yi a karo na biyu.se sannan ne ta ɗan taɓe fuska kana cikin nutsuwa da kwantar da murya ta furta " Haseena!,ke kin san yanda MUZAINA take sona kawai nasan wani babban uzuri ne ya riƙe ta shisa bata zo ba,amma......".kasa karasa maganar ta yi ta riƙe fuska da hannun ta daya alamar mamaki.

" Meyafaru kuma,ke fa ko kaɗan bakya son a ce Muzaina ta yi laifi, ko yaushe ke ce ke mata uzuri uhmmm lallai kam". cewar Haseena.

" Ke kin san meye!?, na yi babban mantuwa wallahi,yau da safe kafin in fito naga ta min text, kan cewa tana da meeting yau in ta gama da wuri zata zo, in kuma bata gama ba,bazata samu zuwa ba"..

Ta faɗa tana sakin murmushi,ko gama jiran jawabin da ake yi bata yi ba ta ja hannun Haseena suka fito a wajen, murmushi itama Haseenar ta yi tana mamakin irin son da ita Muzna take yiwa yar uwar'ta Muzaina.

Farfajiyar hotel din suka fito bayan sun bar hall din nan suka samu yan jarida da kuma masu ɗaukan hoto suna ganin fitowar su, suka musu caa,haɗe da fara ɗaukar ta a hoto, tambayoyi suka fara yi mata kamar haka.

" Sarauniyar kyau shin za ki iya faɗa mana wani irin farin ciki kike ciki yau!?,shin kin taɓa tunanin za ki yi nasara a wannan waje duk da kin kasance model,kuma jarumar finafinai!?".

Tambayoyin de kowa da nasa .amma basu samu attention din ta ba, ga securities se tare yan jaridar suke domin rakasu zuwa Motar.

Wata baturiya a cikin yan jaridar ce ta soma yiwa wata dake kusa da ita magana

" Ita din fa yar Sarkin Kuwait ce, ai dole ma a bata lamba daya !, kin san su ya'yan manyan nan duk abinda suke so suna samu.as far as kudi yana aiki,tofa babu abinda ze gagara,ga ta da shegen kyau kamar ita ce ta halicci kan ta".
Daya na kusa da ita ta ce " haka ne kam,amma naji labarin cewa ba ita kaɗai bace,yaran Sarkin su biyu ne,akwai twin sister din ta komai din su iri daya babu abinda ya raba su,se de wancan she has a attitude mugun girman kai ne da ita ga kuma wulakanta yan adam, shisa Muzna take burgeni, domin ina yawan kallon finafinan ta".
Cikin gulma suke wa junansu wannan maganar, sede abinda basu sani ba gaba daya abinda suka faɗa ta ji yo su. hakan yasa ta dakatar da tafiyar da take yi ta dawo baya zuwa gare su.


" Ba kowa ni ɗan masu kuɗin bane yake neman abu kuma ya samu a lokacin da yake buƙata ba,domin a wannan rayuwar ba komai ne muke nema mu samu ba,ze yu ku kun san gidan ku,to mu har yau bamu san ya kalar masarautar mu yake ba, sede a nuna mana a hoto,idan akwai wanda yake tunanin cewa saboda ni yar sarki ce yasa na samu wannan damar, to kuyi gaggawan goge wannan a kwakwalwar ku. kokarina da kuma jajircewa na haɗe da taimakon Allah shine ya kawo ni wannan waje,in har kana son abu tofa bawai kana daga kwance bane zaka samu,put your efforts and energy.anan ne zaka samu abinda ka ke so.ka kuma haɗa da neman taimako a gun Allah,dan ina yar sarki ba shine ze sa ina kwance akan gado na in samu abubuwan da nake bukata ba fatan kun fahimta!?, sannan dangane da yar uwata Muzaina,kar ku sa'ke magana mara dadi akan ta,ita din macece me zuciyar zinari,wanda be Santa bane ze mata kallon arrogant amma she's so simple".

Tana gama maganarta ta juya ta barosu tsaye a wajen,ta ci gaba da tafiya tana manna sun glass a kyakyawar fuskar ta,har ta bar wajen yan jaridar suna bin bayanta da kallo suna jinjina self confidence da take dashi,isa inda ta bar Haseena da kuma securities tayi. suka k’arasa inda aka tanadar musu motar suka shiga suka dau hanyar zuwa gidan su dake cikin Rublyovskoye highway.


Wani danƙareren gida suka shiga bayan gate man ya buɗe musu.komai na cikin gidan abin burgewa ne, a tare suka fito suna takawa har suka isa cikin falon, da baki baze taɓa iya fasalta irin kyawun da yake dashi ba,a cikin wannan hadaddiyar falon suka tadda ita da wasu turawa zaune suna tattaunawa da gani magana suke yi akan kasuwanci,tana sanye da wando pencil na jeans ya kamata sosai se riga madaidaiciya me dogon hannu kan ta kuwa tayi donot da gashinta ,masifar kamar da suke yi da ita ne yasa Turawan suke ta kallonsu,. domin in bawai don kayan da ya bambanta su ba to babu abinda ze hana su ce mutum daya ne,.

Ɗago kai ta yi suka haɗa ido da juna kafin ta miƙe ta nufesu ta rungume ta tana faɗin

" Na tayaki murna sosai my Muzna ina matukar alfahari dake". Ta yi maganar tana shafa bayanta duk da fuskarta babu murmushi akai, murmushi Muzna ta yi ta ce

" Nagode,duk da ina fushi dake na rashin halartar wannan babban rana a gare ni,amma bazan iya dena sanki ba my Muzaina".

Dan murmushi ta yi kaɗan kafin ta sake ta,ta kalli turawan ta gabatar musu da ita suka gaisa.

Haseena na gefen su ba ta ce musu komai ba,da ta gaji da tsayuwar ne ma ta shige ciki ta bar su a falon.

Batare da ta zauna ba ta sa'ke furta " mun gama wannan tattaunawar se mun haɗu wani lokaci".

Tana gama faɗar haka bata jira amsar su ba ta rike hannun Muzna suka shiga ciki,a hanyar su ta zuwa bedroom din su se labarin abinda ya faru a wajen take bata .ita kuma bata ce mata komai ba domin ba me yawan son magana bace sosai.

Se da suka shiga ciki ne ta kalleta ta ce " My Muzna!.,ko da yaushe ina yawan ce miki ki rage wannan yawan surutun naki amma bakya ji,wa ya faɗa miki jinin sarauta suna dogon magana ko dogon jawabi!?,ko ni be zama a ce na zamo miki misali ba!?, haba mana in aka ga kina yawan yin abu kamar gama garin mutane za'a rena ki. wanda hakan kuma ze taɓa min carrier na, saboda nan gama in na zama sarauniyar masarautar Bayaan za'a dinga cewa yar biyun sarauniya bata da kamun kai,bayan ke kuma zan sakar miki ragamar Company din Aba,duk da ma yanzu kin ƙi yarda ki soma aiki tare da ni a company. kin mayar da hankali akan carrier ki na gasar kyau da films,anyway ina tayaki murna da kuma miki addu'a ".

Ta gama maganar ta tana warware gashinta da ta hade tayi donot dashi.

Muzna da wannan maganar ya zamo mata kamar ruwan sha ne ta sauke a jiyar zuciya domin in wannan karatu ne ya ci a ce ta haddace sa .domin kusan kullum se Muzaina ta mata wannan maganar yanzu har ta ga ji da saurara.

Cikin ko oho da maganganun nata domin ta gaji da jin su ta furta " to shikenan sarauniya Muzaina kar ki damu nima zan koma kamar ki har ma in fiki .se de ze dau lokaci kafin in koma haka, saboda abinda bawai ka tashi da shi ba yana da wahalar koya,. bari in yi wanka yanzu in fito".

Ɗage mata kafaɗa ta yi alamar she doesn't care,ko da Muzna ta fito daga wanka sanye da rigar towel bata iske Muzaina a ciki ba,hakan yasa ta yi zamanta a kan mirror tana busar da gashin kanta da ya kasance me matukar tsawo ta gyarasa, sannan ta yi shafe-shafe, ta saka riga da wando.sak irin kayan Muzaina ta sanya sede ita ta yi ɗan kwalliya,wayar ta da ya soma ƙara ta nufa domin ganin me kiran nata. number sakatarenta ta gani ɗauka tai ta soma magana,.

" Mubeen ya a ke ciki !?". Ta faɗa tana gyara tsayuwar ta,a bangaren wanda ta kira da suna Mubeen ya ce

" Ran ki shi dade, gobe akwai show din daukan hoto da ki ke dashi, wanda za'a sa a magazine,se kuma contract din da zakiyi signing na Film din THE GANG,wanda director din yake ta bin ki,kiyi sign amma kin ƙi amincewa".

" To shikenan se goben " ta faɗa tana kashe wayar ta, kafin ta fice a dakin ta nufi bedroom din Haseena, kwance akan gado ta sameta tana matsa waya.

" Ya Allah, yanzu ke Haseena shine da ki ka yi wanka ba ki taho dakin mu ba!?".

Ta faɗa tana zama a gefen ta, Miƙewa zaune ta yi tana " afuwan!,na baku damar yin magana ne ke da Muzaina,shisa na ɗauke ƙafa ". Girgiza kai kawai ta yi dan tasan saboda Muzaina ne yasa bata je ba,domin sam Muzaina bata son Haseena kamar yanda itama bata son ta,a cewar Muzaina Haseena yar talakawa ce be kamata ta ɗinga tarayya dasu ba,se de ƙawance yayi karfi sosai a tsakanin Muzna da kuma Haseena, wanda hakan yasa ta dawo da ita zama a gidan su,saboda dama su biyu suke rayuwa a cikin wannan makeken gida se kuma masu aikin su, hakan sam be yi wa Muzaina dadi ba tayi faɗa har ta gaji amma Muzna sun ƙi rabuwa da Haseena.


" Yanzu duk ba wannan ba kira min Aba a waya na san suna tare da Ummi" Muzna ta faɗa.

Video call ta kira su ta system aikuwa Kamar yanda ta yi tunani hakan ne ya kasance, sarki TAIFUR RAHMAN na tare da sarauniya Fatima, bakaramin farin ciki suka yi ba ganin fuskar Muzna. Saboda murmushin dake kwance a fuskarta ne yasa suka fahimci Muzna ce,sosai suka sha hira sannan suka tayata murna haɗe da faɗin ai sun gani a labarai hakan ya faranta musu rai matuƙa.

Dariya ita da Haseena suka yi,ta ce " Aba ya jikin naka!?, fatan ya yi sauki sosai!?,kana shan magani ma kuwa!?,kaima kar ka zama irin Muzaina, itama in bata da lafiya duk yanda zan yi da ita bata yarda ta sha magani". Dariya suka yi kafin,sarki Taifur Rahman ya ce

" Kar ki damu Muzna ina shan magani sosai, Ummin ku na ta min ɗure,ina ita Muzaina take!?, kai mata ko ki kirata ".

Ɗaukar system din ta yi ta fice a dakin ,suna ci gaba da wayar har ta isa falo anan ta iske Muzaina dake zaune kamar wata me yin bacci.

Ɗaura mata system din tayi akan cinya hakan yasa ta ware kyawawan idanunta ta ɗaura su akan iyayen nasu.

Hira suka ɗan taɓa saboda babu wani shakuwa sosai tare da ita da kuma su, ita abinda yake gabanta kawai take yi bata taɓa kiran su, in ba wai Muzna ce ta yi kiran ba,ko kuma in su suka kira,tun dabi'un ta na damun su har suka watsar,se de suna sonta kamar yanda suke son Muzna.

" Aba shin yaushe ne za mu zo Kuwait!?,ko da yaushe se de ku yi ta ce mana lokaci na zuwa lokaci na zuwa, se yaushe ne lokacin ze zo shi!?,ina son in zo in ga yanda ake gudanar da al'amuran masarautar saboda ko da na zama sarauniya ba se nasha wahalar koya ba ".

Ɗan jimantawa sarki Taifur Rahman da sarauniya Fatima sukayi jikinsu yayi sanyi,cikin karfin hali sarauniya ta furta

" Kar ki damu Muzaina lokaci na zuwa,kuma in sha Allah zamu kawo muku ziyara a ƙarshen wannan wata "".

" Allah yasa" ta faɗa tana miƙawa Muzna system din ta soma kiran baturiyar yar aikinsu.

Sosai ta ƙara yin hira dasu domin ko kaɗan bata gajiya da jin muryarsu haka zata ta basu labarai masu dad'i da ban dariya kuma suna samun nishadi sosai hakan yasa kullum se sun yi waya.

Bayan ta kammala wayar ne ta ajiye laptop din akan Centre table, ta je ta kira Haseena domin cin abincin dare da aka tanadar musu a dinning,har suka kammala cin abinci babu wanda ya yi magana,se da suka gama ne suka koma falo yayinda Muzaina ke zaune a dinning tana latsa wayarta.

" Elizabeth" ta kira me aikin tasu cikin rawar jiki tazo domin tana tsoron duk wani abinda ze haɗa ta da Muzaina domin yanzu zata ci mata mutunci ita ba wani abu bane a wajenta.

Cikin bada umarni ta ce " je ki kawo min hot coffee kar sugar ya yi yawa".

Dasauri ta shiga kitchen ta haɗa mata coffee din ta kawo har in da take zaune,kusan mintunan ta biyar da tsayuwa amma Muzaina bata daga kai ta kalleta ba,ɓalle ta karbi kofin coffee da ta kawo mata,hannun Elizabeth har ya gaji ya fara rawa,se da ta gama shan kamshin ta kafin nan ta sa hannu zata ƙarba cikin rashin sa'a kuwa coffee ya ɗan zuba mata a hannu, da sauri ta miƙe tana yarfa hannunta da hot coffee din ya zuba.

" Am really sorry ma'am". Ta faɗa muryar ta na rawa domin ta san yau na lahira se ya fita jin dadi,wasu kyawawan tagwayen mari masu zafi ta wanka mata a kumatu wanda se da wannan yar aikin ta ji komai ya tsaya mata cak,su Muzna dake zaune a falo ne suka waigo da sauri jin sautin marin da ta sauke mata.

Da mamaki suke kallon su,kafin su miƙe Muzaina ta watsawa yar aikin sauran coffee me bala'in zafi a jiki.

Ihu ta soma yi tana yarfa hannu cike da radadin zafi,Muzaina ko a jikinta ta dau wayarta ta bar dinning din,da hanzari suka isa inda take tsaye tana kuka,suka riƙe ta suna bata hakuri.

" Gaskiya Muzna ni abinda twinning din ki take yi bana jin dadi, wannan ai wulakanci ne, tsakani da Allah akan me zata watsa mata tafasasshen coffee ta konata,ko ta manta Allah ne kaɗai yake yin hukunci da wuta ?". Haseena ta faɗa cikin tausayin Elizabeth,jiki a sanyaye Muzna ta furta

" Kin san halinta ai, yanzu de mukai Elizabeth din bedroom din ta se a kira doctor ya duba ta".abinka da farar fata nan take inda coffee din ya taba ya yi jajir sosai. Da taimakon su suka kaita dakinta aka kira doctor ya duba ta ya basu magani.


" Muzaina gaskiya yakamata a ce i zuwa yanzu kin sauya hali domin wannan ba hali nagari bane,ni nagaji da dabi'un ki haba mana, yanzu yarinyar nan bata miki komai ba kin kona ta,in da a ce ya taɓa fuskarta fa? ". Ta faɗa rai a ɓace dan lamarin yar uwar'ta ta ya

Please Login or Register in order to submit comment