Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu,wani irin fansa zata ɗauka akan su domin sun cutar da rayuwar ta.

Tana tsaka da wannan tunanin kawai maganar sa ya faɗo mata arai inda yake faɗi... “ Yaro yaro ne,zaki fahimci hakan a lokaci kaɗan,a yayinda danasanin ƙin karɓan tayina ze zo miki. domin kuwa ni Aljani Suwami gautam bana faɗar abinda yake ba haka ba,amma bazan juya miki baya ba,kofa abuɗe yake a duk lokacin da ki ke da buƙatar taimakona kawai ki furta, zurfa_zurfa narash mani gumaaaaaal zaaararrrr,hamkam_hamkam zurfa-zurfa, za ki ganni tsaye a gaban ki batare da bata lokaci ba,hhhhhhhhhh.”

“ Aljani Suwami Gautam na yi danasanin ƙin amincewa da kai tun farko da yanzu an wuce wannan wajen tabbas na yi ganganci,ban taɓa tunanin ahalina za su munafurce ni ba".
Runtse idanunta ta yi nan ta hasaso lokacin da sanar da ɗaura Muzna a matsayin sabuwar Sarauniyar Bayaan.hakan yasa ta buɗe idonta da sauri tana jawo kwalban wani turare dake gefen bedside durowanta ta wurga a jikin mirror ta da ke da girman gaske,tas!tas!tas!tas ka ke jin ƙarar fashewar mudubin da ya tarwatse a ƙasan dakin na ta,cikin bushewar zuciya da jiji da kai da izza da sarauta ta miƙe tana tafiya kamar wata yar maye tana layi, ta fara tafiya jikinta na sanye da doguwar rigar bacci launin shuɗi da launin fari, doguwar sumar kanta ya hargitse kamar wanda aka kwato sa daga bakin kura,inda gilashin madubin suke zube ta nufa ko tsoro ɓalle fargaba babu a tare da ita, ta fara taka gilashin yana shige mata ƙafa yana yankanta jini na zuba,amma tsabar dakiyar zuciya irin na ta ko a jikin ta,kallon kanta ta yi a jikin sauran gilashin madubin da suka kasu gida uku a ko wanne tana ganin kan ta a ciki.
Magana ta farayi da wata iriyar dakakkiyar murya me cike da son ɗaukan fansa"ni ce!ni ce nan!ni Muzaina Taifur Rahman ni na fi dacewa da wannan sarautar,ni na fi cancanta da in mulki masarautar Bayaan ba wai Muzna ba, shin da meye Muzna ta fi ni!?,menene za ta nuna min wanda bani dashi!?,akan me za'a zaɓe ta a matsayin Sarauniyar Masarautar Bayaan?me ta fi ni da za'a a zaɓe ta abar ni?,na yi rantsuwa da wanda ya halicce ni se na ɗau mummunar fansa akan yar uwata kuma ƴar biyu na MUZNA TAIFUR RAHMAN,se na raba ta da duk wani farin ciki na rayuwarta,duk wani hanyar da ze saka murmushi akan fuskarta to se na daƙile sa.,bazan taɓa barin ta ta yi mulkin ta yanda ya dace ba se na mayar da ita mujiya a idon duniya,in kuma ban yi haka ba,to ni ba halastacciyar jinin TAIFUR RAHMAN ba ce,dole in mulki wannan masarautar,mulki shine burina da muradi na. duk wanda ya ce ze tsaya akan hanyata se na ga bayansa ko da kuwa yar uwata mafi soyuwa a gare ni ce wato MUZNA."
ta karasa maganar ta na sakin murmushin da ya fi kuka ciwo.

Knocking kofar da ta ji ana yi ne yasa ta kalli kofar tana me jan tsaki ta soma tafiya toward the door duk inda ta taka se tabar sawun kafarta dake zubda jinin gilashin da ta taka.Tana buɗewa Muzna ta shigo tana rufe kofar.ganin yanda duk tabi ta susuce kamar ba ita ba ga idon ta da ya ɗan kumbura yasa ta riƙo fuskarta da duka hannunta biyu cikin damuwa ta ce

“ Muzaina me haka ?za ki wa kan ki illa a banza, ki duba yanda ki ka dawo lokaci guda nasan baki ci komai ba zo ki zauna in kawo miki abinci”. Tsare ta tayi da shanyayyun idanunta da suka sauya kala saboda kuka tana bin ta da wani kallo wanda duk yanda kaso fassara wannan wani irin kallo ne bazaka iya ba,bata damu da kallon ba, ba kuma ta damu da rashin mata magana da ta yi ba ta soma jan hannunta domin ta zaunar da ita akan bed,idanunta ne ya sauka akan sawun kafarta da jini ya maye gurbin su zaro ido ta yi cikin tashin hankali ta dubi Muzaina sannan ta toshe bakinta da tafin hannu

“ ohh my god Muzaina are you crazy ? kafarki ne fa yake zubda jini, ya Allah wannan wani irin bakar rana ce,zauna bari to in miki dressing din kafar “.

Tureta ta yi tana wurga mata mummunar kallo “ stay away from me Muzna meyasa ki ke da fuska biyu ne ? Kina tunanin zan sake yarda dake ne a Karo na biyu?babu abinda za ki fada min na dadin baki kin ji ko?.ba kowa ne ya jefani a wannan halin ba face ke!ke din nan kece silar komai na tsane ki ko me fuskar ki bana kaunar gani daga rana irin ta yau bazaki sake daura idanun ki akaina ba za ki yi danasani har karshen rayuwarki za ki bakin cikin had’a dangantaka dani a wannan duniyar.”

“ ki dena magana irin haka Muzaina ki de na magana kamar wacce baki san halina ba kin sanni kin san abinda zan iya aikata da wanda bazan iya aikatawa ba then meyasa ki ka yanke min hukunci lokaci guda kina tunanin zan ruguza miki farin cikin ki ne domin bukatata?”ta gama maganar tana son riko hannunta,Baya da ita ta ja ganin tana son tabata

“ Dan adam ze iya sauyawa a ko wani lokaci,baa taba shedan mutum abinda nake so dake yanzu shine ki bacemin da gani.”

Dafe goshinta tai ganin duk yanda ta bullo mata ta ki nutsuwa ta fuskanceta.

Cikin sanyin murya ta furta “ Yanzu akan wannan shine ki ka dau fushi dani ?akan abinda bani na aikata ba?,kar ki manta alkawarin da muka daukawa mahaifiyar mu da mahaifin mu kan cewa komai tsanani muna tare da juna babu wani abinda ze rabamu,baza mu taɓa yarda wani abin duniya ya shiga tsakanin mu ba me……” katse ta Muzaina ta yi cikin tsawa ta ce

“Alkawarin da muka yiwa mahaifi da mahaifiyar mu sun mutu a tare da su.daga lokacin da suka bar wannan duniya sunta fi ne da wannan alkawarin dan haka ni da ke bamu da wata alaka ko na kusa balle na nesa “.

“ Mu….Muzaina ke ce ki ke fada wannan maganar yau ni ce fa your Muzna your twinny sister “.Tana magana ne a yayinda da muryarta yake rawa.

“Ba ki yarda bane ?to bari gani yau shine rana ta karshe da za ki sake gani.”ta fada tana fincikar hannunta cikin karfin tsiya ta suka fita a bedroom din.

“Auuuuch Muzaina you’re hurting me “.ko sauraranta bata yi ba ta ci gaba da jan hannunta har tsakiyar main part inda kowa ke zaune da sauri suka mike ganin yanda Muzaina ta rike hannun Muzna tana janta ga shi sun nufi hanyar barin main part izuwa waje rufa musu baya gaba daya suka yi. Dogarawa da masu tsoron kofar fita suka yi kokarin dakatar da ita ganin yanda ta rike sabuwar sarauniya tana jan ta wani mugun kallo ta watsa musu da yasa suka kalli kasa domin itama a shugaba take a garesu tunda ya take a gurin sarki. Se da suka je tsakiyar farfajiyar palace kafin ta sake hannunta hakan yayi dede da isowar su Galadima dama kowa bayi ne hankalinsu ya soma karkatowa kansu hakan yasa suka tsaya da abinda suke yi suna kallo duk da ana iska ga hadari sosai da ya hadu alamun zaa iya fara ruwa any moment.


Ja da baya ta yi tana kallon duk wa’yanda suke wajen daya bayan daya cike da tabbatarwa ta soma magana

“ Gaba dayan ku,dukkanin ku babu ko mutum daya da zan yafewa wannan cin amanar,Ina kuka haka na dinga rokonku kamar wata wulakantacciya amma ku ka juya min baya ku ka take muradina a karkashin takalman ku cike da isgili.Ku sa a ran ku lokacin yin rayuwa me dadi ya kare a gare ku.zan dau fansa me muni akan ku domin ku ba mutane da zaa yafewa bane,zan tarwatsa farin ciki da walwalar ku da jiji da kan kan da kuke ji dashi.zan tarwatsa masarautar da ku ke gadara dashi komai se ya zamo muku kuncin.ke kuma”ta juya kan Muzna ta dora da cewa

“ ke kuma dawuwa na baze miki dadi ba se kin roki mutuwa da sake fatan rayuwa dani.dukkanin ku na muku tsana na musamman,zan bar wannan masarautar amma ku kasance masu adduar Allah yasa kar in waiwayo ku “.Tana rufe bakin ta aka soma ruwa me karfi ga iska da aka soma yi da karfi wanda se da kowa yasa hannu yana kare fuskarsa gudun kar wani abu ya shige mai ido.

Dariya ta yi ta kalli sama ganin yanda har lokacin iskar be tsaya ba yasa ta kalli fuskar Muzna da se kare fuskar ta take da duka hannunta domin iska ne da ya taso bana wasa ba.ga ruwa dake dukansu.

Kayan baccin dake jikinta ya kwanta luf a jikin dama me tsantsi ne ga kuma ruwa da ya sauka a jikinta wanda haka yasa ya kuma mannewa a jikinta ga gashin kanta da shima ya kwanta a bayanta. Juyawa ta yi ta soma tafiya batare da ta kuma waiwayan bayanta ba.tafiya tayi Wanda be wuce taku ashirin ba kawai ta ganta a wajen masarauta tsaye a bakin babban gate din Bayaan ta baya babu kowa daga gate din se daji domin shine gate na uku da yake masarautar kuma shine yake rufe kirif babu wanda yake zuwa gurin tun shekaru dari da suka shude.

Ganin ita daya ce a wajen babu alamar ko da dabbobi yasa ta rufe idonta ta soma faɗin " zurfa_zurfa narash mani gumaaaaaal zaaararrrr,hamkam_hamkam zurfa-zurfa." idan masu karatu basu manta ba wannan sune kalmomin da Aljani gautam Suwami ya fadawa Muzaina ta furta a duk lokacin da take bukatar sa.

Wani irin guguwa ne ya dunfaro inda take me karfi baki kirin Aljani gautam Suwami ne ya fito daga ciki yana wannan dariyar tasa mara dadin ji.

“Muzaina yar sarki Taifur dama na fada miki zuciyoyin bil adama babu komai a ciki face yaudara da cin amana.na fada miki zasu tauye miki hakkin ki amma kin ki yarda se yau ga shi sun nuna maki matsayin ki a wannan masarauta.shin yanzu kin shirya zama sarauniya hade da daukar fansa ?” Cike da rashin tsoro ta ce “ Kwarai kuwa na shirya”. Dariyar da tafi na dazun tsoratarwa ya sake bushewa dashi sannan ya kuma tayar da iska da bakinsa nan take suka bace bat.


Seda aka kusan kwashe mintuna goma ana wannan iskar kafin ya tsaya kallon ko Ina suka yi amma me babu Muzaina a gurin nan take a ka bazu ana nemanta amma babu ita a duk inda aka duba.
Fashewa da kuka Muzna tayi hade da zubewa a k’asa tana tunawa da kalmomin da Muzaina ta fada na cewa daga yau bazasu sake ganin ta ba ashe da gaske take bada wasa ba ga shi ta tafi din.

Komawa palace suka yi mai girma sheikhy ne ya shigo ya zauna bayanin abinda ya faru Galadima ya yi yace mai ai yasan komai yanzu ze duba yaga Ina ne inda Muzaina take.bayan dan binciken da ya yi nan ya gano wani shu’umin Aljani ne ya tafi da ita amma be iya gane wanene ba amma tabbas aljanin da ya tafi da ita me matukar hatsari ne.bayani ya musu hankalinsu ya tashi sosai.
Mikewa Galadima ya yi ya zo kusa da shi ya zauna cikin kwantar da murya ya ce

“ Yanzu ya zamu yi da Sarauniya kasan irin soyayyar dake tsakanin su kuma bugu da kari yan biyu ne abin baze fita aranta nan kusa ba tabbas kewar yar uwar ta ze hanata tabuka komai.”
Kallon Muzna dake zaune kanta jingine a kafadar ummu Zaheenat ya yi tayi kuka har manyan idanunta sun kumbura tana kallon mutanen da ke cikin falon amma bata cewa komai saboda yanda komai ya fice mata arai ta daurawa kanta laifin komai tana ganin ita ce silar da Muzaina ta tafi ta barsu ta koma abin tausayi lokaci daya har ta fada.

“Tabbas shakuwa da soyayya abu ne me karfi. Rashin Muzaina a tare da ita ze iya haifar mata da ciwo Musamman yanzu da ta daurawa kanta laifi ko da yaushe zata kasance me tunanin yar uwarta wanda hanata sakat,dole yanzu a cire mata tunanin abinda ya faru yau a goge mata shi a kwakwalwarta tas.”

Jinjina kai ya yi alamar gamsuwa da maganar sa goge mata abinda ya faru din shine kawai mafitar su inde suna so tayi Mulki yanda ya dace.

Tsare ta da idanu mai girma sheikhy ya yi nan take idanunsa suka koma fari fat babu digo a ciki a hankali wani farin haske da bakowa ne yake ganin sa ba ya je ya shiga kan Muzna.

Mikewa da kyau ta yi ta taba ummu Zaheenat “ ummu Zaheenat me muke yi a palace haka ? “ ita da bata San me ya faru just now ba ta kalleta da mamaki jin tambayar da ta watsa mata,Tana kokarin yi mata magana ta sake jefa mata wata tambayar
“Ina Muzna dazun muna tare da ita “.

Murmushi mai girma sheikhy ya yi ya amsa mata da “Muzaina ta yi tafiya amma bazata jima ba ta je kula da kamfanonin ku da suke Dubai”.

“To meyasa ba mu tafi tare ba kuma meyasa baa gaya min ba?”


No editing


don't forget to comment,like and share fisabilillah ❤️😍👍

Allah yasa muyi kyakyawar karshe.

https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207


⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚📚🖋️⚜️





❤️🔥Page 20




“To meyasa ba mu tafi tare ba kuma meyasa ba’a gaya min ba?”

“Saboda ki na bacci, kuma kin yi nisa wannan dalili yasa ba mu tashe ki ba.” Galadima Abdul aleem ya ba ta amsa a wannan karon.
Bata kawo komai aranta ba ta bi ummu Zaheenat da ta riƙe hannunta domin yi mata rakiya zuwa part din ta duba da dare ya yi sosai yanzu.

“Ka tabbatar da ta fito fada gone. kuma ka faɗa mata matsayinta a yanzu in ta kawo maka zancen yar uwarta ka nemi abinda za ka ce mata,sannan a duk lokacin da Muzaina ta dawo to Muzna za ta tuna komai da ya faru”. Mai girma sheikhy ya faɗa yana ɓacewa.

koda suka shigo kashe mata wuta ummu Zaheenat tayi sannan ta mata se da safe.da murmushi akan fuskarta ta ce mata se da safe tana kwanciya tare da zaro wayarta da taji yana vibrating murmushi ta saki lokacin da ta ga sunan Haseena akan screen wayarta ɗagawa ta yi suka sha hira sosai har sha biyu kafin ta kwanta.

Washe gari da kyar ta iya tashi tayi sallah asuba shima se karfe shida da kusan rabi sakamakon wani nauyi da ta ji kanta yake mata na fitan hankali. Ko da ta idar da sallah bata bar kan prayer mart din ba tana zaune tana azkar din ta da ta saba kamar ko da yaushe. Wata baiwa ce ta shigo tana me tsaya wa a bakin kofa ta zube kasa tare da faɗin " Barka da safiya yake shugabata mu na me neman izinin shigowa"
Kallon ta ta yi kawai ta gyada kai saboda bata idar da azkar din da take ba.

Fita ta yi se ga su yan mata kyawawa wa’yanda bazasu wuce shekarunta ba suna sanye da Kaya iri daya dogayen riguna fari me ratsin ja gashin kansu yana daure da ribbon fari saura ya kwanta a bayan su.hannayensu na riƙe da manyan tray da aka rufe da jajayen mayafi gaba dayan su. Tsaya wa suka yi a layi haɗe da sunkuyar da Kai k’asa.
Daya bayan daya take bin su da kallo ganin su da yawa haka sun kai su goma ga trays din dake hannun su,sallamewa ta yi ta miƙe tana ɗaukar prayer mart din ta naɗe haɗe da a jiyesa a hannun kujera.

“Amincin Allah ya tabbata a gare ki yake sabuwar shugabar mu”. Su duka suka faɗa a lokaci guda. Tsaya wa kawai tayi tana gani da jin ikon Allah tana son musu tambaya amma yanda take ji yasa bazata iya doguwar magana ba hakan yasa ta ce

“Ameen. Menene a hannun ku?”
“Kayan adon ki ne Sarauniya”. Wata daga cikin su ta faɗa tana ajiyewa akan bed din nan su ma suka ajiye na su kamar yanda tayi.
Kusa da bed din ta matso ta soma buɗewa,gaba daya manyan trays din nan bakomai bane a ciki face kayan ado na gwalagwalai Kama daga kan sarkan wuya,dankunne,sarkan kai,sarkan damtsen hannun dana awarwaro,sarkan kafa,sarkan kwalliyan ciki,komai da ya kasance zaa yi ado dashi a jiki na zinari duka suna a cikin wannan trays din se dauke ido suke yi.
“ kuma nan wajena aka ce ku kawo su?”

“Kwarai kuwa shugabana mu ne zamu shirya ki izuwa fada”wata matashiya ta faɗa batare da ta ɗago kan ta ba.
Shuru ta yi tana kallon yan matan kafin daga bisani ta nufi hanyar kofa da nufin barin bedroom din,saura kad’an su ci Karo da Galadima Abdul aleem dake kokarin shigowa ciki ga fadawa dake tsaye a bayan sa,ja da baya ta yi tana me gaishe sa. Sunkuyar da Kai ya yi alamar girmamawa tare da fadin
“ Barka da Safiya shugabana”. Zaro ido waje tayi cike da jin kunya da zallar mamaki ta ce

“Ya Allah,Abu Aleem me ka ke yi haka?”
“Zo nan mu yi magana” ya faɗa yana riƙe hannunta suka shigo dakin nata kallon yan matan ya yi suka fice.

Zaunar da ita yay akan kujera yana nazarin ta Ina ze fara yi mata magana.

Taɓa sa tayi “ Abu Aleem ba ka ce komai ba meke faruwa ne”

“Abinda yake faruwa shine kin san na sanar miki da Muzaina tayi tafiya ko?”gyada masa Kai ta yi,ya ci gaba da fadin

“Ta tafi yemen masarautar marigayiya sarauniya Fatima,saboda sun bukaci a basu daya daga cikin ku wacce za a bawa sarauta a can daya kuma anan. to bayan mun tattauna da Muzaina shine ta ce ita zata tafi yemen din ke kuma se a baki kujerar Bayaan,sannan kuma a watanni uku na farko na fara mulkin ku bazakuyi communicating da juna ba,domin ana so ku nutsu ku kula da masarautar ku yanda ya kamata wannan shine abinda ya faru.”ya ƙare maganar yana duban cikin idanunta da take ta yawo dasu a k’asa alamun tana nazarin maganar sa. Miƙewa tsaye ta yi bayan ta gama sauraransa ta soma safa da marwa a tsakiyar dakin tana me cizan yar karamar yatsar ta.

“Ya Allah yasa ta yarda da abinda na faɗa mata.” Ya faɗi hakan a zuciyar sa.

Da sauri ta juyo gare sa “amma Abu Aleem kun fi kowa sanin kan cewa bana bukatar abinda ya shafi sarauta me yasa za ku ban?,and tunda na ke da my muzaina ba ta taɓa cewa tana son kujerar wata masarauta ba,muradita da kaunar ta a iya Bayaan ne kawai,ta ya ita da kanta za ta zabi masarautar yemen ta bar inda take mafarkin mulka?na yiwa Muzaina sanin da ko ni nan ban yiwa kaina ba,ko de kun yi forcing din ta ne kan cewa dole se ta je Yemen?nooo na ma san halin kayana bata yarda a juya ta ba tana bin raayin kan ta ne kawai,kenan ita ce ta amince da gaske?”ta karasa maganar tana kure sa da ido.

“ ya Salam itama wannan haka take da bin diddigi kamar mahaifiyar su”Galadima ya faɗa a zuciya a fili kuma ya miƙe yana cewa
“Sarauniya kin fi kowa sanin wacece yar Uwar ki dan haka ki bawa kan ki amsa,kin san ta sarai babu wanda ya isa yace dole se ta yi abinda yake so”.

Gyada Kai ta yi cikin gamsuwa da bayanin sa domin ta sani ko mutuwa zaa yi babu wanda ya isa ya juya Muzaina musamman akan abinda yake na rayuwarta.tabbas ta yarda Muzaina ita ce nan ta amince da komawa Yemen.amma ya zaayi a ce wai bazasu yi waya ba har se watanni uku na farkon Mulki ya cika.
“ kin san masarautun nan da ka’idoji maybe hakan yana cikin ka’idar su”wani ɓarin zuciyarta ya faɗa.

Galadima Abdul aleem kuwa ganin yanda ta ke gyada kai alamar gamsuwa ne yasa,ya sauke numfashi a boye domin tun jiya yake ta tunanin ta yanda ze zayyana mata wayannan zantattukan.

"Astagfurullah Allah na tuba na karyar da nayi mata"ya faɗa aran sa.

"Abu Aleem amma ni bana mafarkin zama sarauniya. Hakan be taɓa burgeni ba,ni Russia zan koma in ci gaba da rayuwata a can,a samu wata ko wani wanda ze maye muku gurbina kawai”.

Wannan shine abinda ya jiyo tana faɗa masa,a hankali ya furta" ina tunanin darun ya ƙare ashe akwai saura"

"Shin kin san cewa kece zaɓaɓɓiyar da takobin Baaar ya zaɓa?,dole ke ce nan za ki Mulki Bayaan cikin aminci in ba haka ba wannan masarauta ta mu me albarka muna ji muna gani haka ze taɓe."

Hiran da su ka yi da Yumma take ba ta tarihin Bayaan ta tuna in da take ce mata muddin wani ya hau kujera in de bashi ne asalin shugaba ba masarautar za ta tagaiyara.

"Ya salam.tabbas Yumma ta sanar da ni haka amma why Bayaan za ta zaɓi wacce ba ta da raayi akan ta?"

Godewa Allah ya yi da ta san da haka da yanzu kam be san ya ze kare da ita ba.

“Ƴata na san ba za ki so wannan masarautar ya shiga mawuyacin hali ba,ki rungumi wannan sarautar Allah ya rigada ya kaddara ke ce sarauniyar Bayaan babu yanda mu ka iya dukkanin mu."

shuru ta yi ba ta san me za ta kuma cewa ba,duk da babu sha'awar zama wata a wannan masarautar a ranta, bazata so tabar wannan mummunar abin ya faru ba bayan kuma tana da hanyar zamewa kariya a gare su.

“Yawwa yarinya ta wa’yannan yan matan bayin ki ne masu miki hidima,Allah ya ja kwanan sarauniya.”ya fice ya barta tsaye tun kafin ta sake dauko masa wata zancen.
A Karo na biyu wa’yannan matasan yan matan su ka shigo rike da wasu trays din a hannayen su wasu suka ajiye sa bisa kan gado wasu daga cikin su kuma suka shiga toilet Sauron suka tsaya kamar yanda suka jero bisa kan layi dazun.abinci suka ajiye mata ta zauna ta soma ci dama tafara jin yunwa.

Fitowa suka yi cikin girmamawa wata tace “ ya shugaba ta an tanadar miki da ruwan wanka shin kina bukatar mu taimaka miki ne ?” “ ah ah babu bukata” seda ta gama breakfast sannan ta shige toilet din ta bar su tsaye.

Ko da shiganta tozali idon ta ya yi akan jacuzzi dake cike da ruwan madara ga wasu red roses dake kan ruwan.tun kafin ta isa ga ruwan wani sanyayyen kamshi ne ke dukan hancinta.cikin nutsuwa ta cire Kayan jikinta sannan ta taka izuwa cikin jacuzzi ta shiga tana me sauke ajiyar zuciya Jin yanda ruwan yake warm ga masifar kamshin dake ratsa ta.kwanciya ta yi a cikin ruwan ya kasance iya kacin kan ta ne a waje idanunta suna a lumshe. Se da ta ɓata kusan 20 minutes a toilet kana ta fito ɗaure da jan towel se baza kamshi take yi.yanda ta bar su a haka ta iske su tsaye ko motsawa basu yi ba.
Jinjina Kai tayi ta dan saci kallon su kad’an kafin ta zauna a gaban mirror,gaba dayan su ne suka karasa in da take zaune biyu daga ciki suka ɗauki towel suka soma goge mata jikinta kafin suka soma shafa mata lotion masu kamshi,ita dai duk abinda suke yi da ido kawai take bin su. Ko dan yau ba ta wani jin dadin jikinta ne?amma ta alakanta haka da rashin sabo ne,da su Jadwah ne da yanzu suna ta shan hira,amma wa’yannan yan matan ta ga basu saki jiki da ita ba kodan ta kasance sarauniya ce a gare su.gyaran gashi suka yi mata gashin aka raba sa gida biyu daya aka zubo dashi gefen hagu, haka daya aka dawo dashi gefen

Please Login or Register in order to submit comment