Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki ka tashi da wannan yammacin ?”.

“ bacci mana,me ya kawo ki kuma yau ?” Ta faɗa tana samun guri a gaban mirror ta zauna,da mamaki Muzna take kallon ta jin irin wata bahaguwar tambayar da ta jefa mata.

“ ban fahimci wannan tambayar taki ba abar kauna “.

Tabe baki Muzaina tayi “ ehh mana ai dole in tambaye ki,na ga alama wani na son shiga tsakanin mu,yaushe rabon da ki zo nan,se de in ni na matsu in biyo ki har sashen ki “.

Buɗe baki tayi tana kallon ta Jin yanda take magana kamar bata san ta dan yi rashin lafiya ba.

“ ki yi hakuri,yau ne na soma fita,yau ne na samu kuzari a tare dani “.

Tana kallon yanda fuskarta ya koma ta cikin mirror hakan yasata sakin murmushi

“ common on Beb am just kidding you “.

“ ke ko har kin sa naji babu dadi”.

“ hope you’re feeling much better now ?” Muzaina ta tambayeta tana gyara gashinta da cum.

“ yeah!. Abu aleem ya na da bukatar mu a teburin cin abinci”.
Bata ce da ita komai ba. se ma shafa da ta ci gaba da yi.


Zan dakata anan se kuma in na ji sauki,include me in your prayers. Wannan pages din ma already na fara typing din sa ne jiya shisa nayi update.

https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207



⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩





❤️🔥Page 13--14--15--16



" why ain’t you saying anything?”.

“ I don’t like that man at all wallahi” ta faɗa hankali kwance. Zaro ido waje Muzna tayi jin abinda Muzaina ta faɗa wai bata son Galadima Abdul Aleem.

Zama ta yi akan bed din ta “ wai Beb ke kowa bakya so,mutane fa rahama ne. In fact Abu Aleem is our uncle. Bayan Aba bamu da kowa bayan su”.

Mikewa ta yi ta nufi gadon ta zauna bisa gefenta.

“ Muzna!. kin san meye?, bana son ki dinga yawan tuna min abinda nake da masaniya akai,yeah of course nasan Abu Aleem uncle na mu ne. amma hakan baze sa in so shi ba. Yanzu bari in sa kaya se mu tafi dinning din duk da ma ke naga alamar bakya Jin yunwa.Aina ki ka ci abinci!? dan yau ba ki yini a palace ba!”.

Girgiza kai kawai ta yi tana me rolling eyes din ta haɗe da aza su bisa na Muzaina da ta gama magana yanzu

“. Well shikenan na fahimta amma ko me za ki yi I must tell you the truth,abinci kuma a wajen masaurata naci gurin wata dattijuwa me kirki sosai “.

Gaba daya idanunta ta ware tana bin Muzna da kallon al’ajabi “ Muzna kina da hankali kuwa?,do you want to kill yourself?,a gurin wa’yanda ba ki yarda da lafiyar su ba ki ka ci abinci!?“.

“ to meye a ciki?”.

Galla mata harara ta yi “ you’re so careless with your life”.

Girgiza kai ta yi kana ta shige ta saka kaya. Koda ta fito da mamakinta bata iske Muzna a bedroom din ba,se da taji Karan ruwa ne ta fahimci tana toilet zama tayi tana jiran fitowarta.


Gaba daya sun hallara a dinning suna cin abinci babu abinda ka ke ji se Karan spoons.
Bayan sun kammala ne masu aiki suka kwashe hade da gyara ko’ina. Galadima Abdul aleem ya bukaci da su basa aron hankalinsu.

" Abinda yasa na tara gaba dayan ku a nan shine, gobe in sha Allah za'a yi taron gabatar da Muzna da Muzaina wa masarauta . da yawa mutane basu san su ba. Kuma yakamata a ce sun san su. Allah ya jikan marigayiya sarauniya da kuma marigayi sarki”.

“ Ameen “ duka suka amsa,

Kallon juna jadwah da Muzna suka yi domin tunanin da suke yi ya zo daya.ganin alamun damuwa ɗauke akan fuskarta ne yasa Jadwah ta mata alama da ta kwantar da hankalinta.

Bayan kowa ya watse ne suka zo har bangarenta babu abinda suka sameta tana yi face safa da marwa. domin wannan gabatar dasu da za'a yi gobe dede take da tona mata asiri a gurin sadauki Zubair.

“ oh my god Jadwah shin dole ne yin wannan taro for goddess sake,yanzu shikenan Sadauki Zubair ze ɗauke ni a matsayin makaryaciya. Ya Allah gaba daya kaina ya ɗaure “.

Itama Jadwah ta shiga rudu domin wannan taro da aka shiryasa bakaramin girgiza su ya yi ba domin ko ta halin qaqa tabbas Sadauki Zubair se ya ganta.

Jan hannunta ta yi suka zauna sannan ta kwantar mata da hankali kana ta ce

“ Gimbiya abinda ze faru shine ki je ki samu sadauki zubair ki sanar masa da ko ke wacece ze iya yafe miki,amma muddin ki ka kuskura ya gan ki gobe wallahi ransa ze baci ze ɗauke ki maci amana. Da ya ji a gurin wani, gwara ya ji a bakin ki,Sadauki Zubair yana matukar kaunar ki ze fahimce ki “. Tabbas ta yarda da shawaran da Jadwah ta bata domin shine kadai mafita a gareta.

Shuru ta yi tana me ɗaura hannunta a habarta,tana tunanin yanda ze yi react.Kara mata kwarin guiwa sosai ta yi.

Yarima Ishaq kuwa ya baro bangarensa ya zo na Muzna domin so ya ke yi su yi magana, ko da ya riƙe handle din bedroom dinta ze shiga maganar da ya ji suke yi na zuwa tunkarar Sadauki Zubair shi ya dakatar dashi. wannan abu ba karamin dadi ya masa ba. Wata makirar murmushi ya saki domin kuwa ya samu hanya mafi sauki da ze shiga tsakanin su batare da ya wahalar da kan sa ba,be ko shiga dakin ba ya juya izuwa bangarensa yana me murmushi lokaci zuwa lokaci.
Waya ya ɗauka ya yi magana dan gajere sannan ya ajiye yana me harde hannu a kirji.

Muzaina tana zaune a bedroom dinta ga system a gabanta tana video call da business partners din ta da suke ƙasan canada. Shigo wa dakin Aliyah ta yi da wasu bayi guda biyu a bayanta suna rik
ƙe da kwalaye fashion.

“ barka da wannan lokaci gimbiya Muzaina “.
Batare da ta samu damar ɗago da kanta ba ta furta “ barka”.

“ Ummu Zaheenat ce ta aikoni da Kayan da za ki yi amfani dash na taron gobe”.
Hallau bata ɗago ba ta nuna mata gefen gadonta alamun su ajiye agun .
Taɓe baki tayi ganin yanda take nuna mata Izza alama ta musu da su ajiye,. Koda suka baro bangaren Muzaina na Muzna suka nufa domin ajiye mata nata.

Basu tarar da ita a bangaren nata ba se Jadwah dake zaune bisa kujera tana chatting.

“ Madam ke kuma Ina neman ki ashe kina nan”.
“ kuma fa nacewa Hamra in de kin nemeni to Ina nan”.

“ to ai shikenan Ina gimbiya?”.
Miƙewa ta yi ta nufi wajen bayin dake tsaye kan su a kasa ta karbi kwalayen tana me faɗin
“ kun yi saɓani ta je a domin ta warwarewa Sadauki gaskiyar ita wacece “.

Ta faɗa tana zama ta soma buɗe su ya hayyu ya qayyum wato iya saman su kadai da jikin Kayan ne ya samu bayyana,wasu irin arnayen daukar ido yake yi saboda tsnananin duwatsu da suka yi wa kayan yawa ga sheki da walwal da suke.

“ ya Allah!. gaskiya kayan nan sun masifar yin kyau fiyeda yanda bakya tunani”. Cewar Jadwah da ta buɗe Kayan ba Karamin tafiya da hankalinta suka yi ba shafa su take.

“ tun farko da na ce muku yakamata ta samu Sadauki ta fada masa komai ai ƙin saurarata ku Kai. se yanzu da ku ka ga gobe ze gano gaskiya shine ku ka saduda “. Faɗar Aliyah.

“ za ku iya tafiya”. Jadwah ta faɗawa yan mata da shigo tare da Aliyah suna sanye da kaya iri daya dukkansu,se da suka fita ne ta dawo da kallon ta kan Aliyah

“Yanzu se mu zauna mu jira dawuwarta “.
Suna zaune suna hira suka ga ta shigo jiki amace kamar wacce Kwai ya fashewa a ciki.
Duk miƙewa su ka yi suka tsaya ganin yanayin da ta shigo dashi hakan yasa suka ji jikinsu ya mutu sosai, domin sun san yanda suka gano tan nan sun samu sabani da Sadauki ne.
Riƙo hannunta suka yi haɗe da zama akan kujera.

Cikin jimami Aliyah ta furta “ Kiyi hakuri na san nan da zuwa wani lokaci ƙalilan ze sauko,yanzu ki ba sa lokaci ya gama fushin sa”.

“ Wallahi gaba daya jikina ya yi sanyi. Amma ga shawara me ze hana ki je ki samu Yumma ki faɗa mata abinda ke wakana nasan tunda ita mahaifiyarsa ce dole in ta masa magana ya saurareta “. Jadwah ta faɗa fuska ɗauke da damuwa.

Da kallo kawai take bin su cike da mamakin Jin abinda ko waccen su take faɗa batare da sun tsaya sun ji me take tafe ba har sun yanke abinda ya faru tsakaninta da Sadauki Zubair.

“ relax guys,gaba daya kun cikani da surutu”. Nutsuwa duk suka yi suna sauraranta.

Furzar da iska tayi daga ɗan karamin bakinta cikin sanyi murya ta kuma furta

“ ban same sa ba”.

“ kamar ya baki sa me sa ba to Ina yaje “.Cewar Jadwah da gaba daya ta matsu taji kan zancen.

“ yup ban same sa ba,na je filin daga amma ban same sa ba. ban kuma samu Arman ko hashim ba. Ina tsaye a gurin ne naga wani matashi yazo shine nake tambayar sa,nan ya shaidamin dakarun wannan masarauta gaba daya sun fita yaki,kuma Sadauki Zubair shine jagoran tafin.ita kuma Yumma ta je Libya duba kanwarta babu lafiya”.

“That’s good to hear, ta wani bangaren abun farin cikine kin ga in ya dawo za ki masa bayani cikin nutsuwa kin fa shi baya nan balle mahaifiyarsa”.Cewar Jadwah.
Jinjina Kai Aliyah tai saying

“ hakane kam amma shawaran da zan ba ki shine muddin ya dawo ki samesa ki fada Mai komai domin boye-boyen bayida amfani “.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta ji bayanan su “ shikenan. Meye a cikin wa’yannan kwalayen “. Ta fada Tana bude Kayan da aka kawo mata.
“ wow Masha Allah sun yi kyau sosai”.



ENGLAND 🏴󠁧󠁢󠁥󠁮󠁧󠁿

KINGDOM OF WISDOM

Wata kyakyawar matashiyar budurwace wacce jinin turawa da Mulki ke yawo a jikinta wacce bazata wuce shekara 20 ba a duniya tana tsaye hannunta da doguwar wuka irin ta masarauta da ake yaki da ita. se jujjuyasa take yi cikin kwarewa domin kuwa ta horu da irin wa’yannan horon faɗa hakan yasa ta girma cikin jarumta. Jikinta na sanye da riga da wando fari sun tsuketa se dede cikinta dake ɗame da belt baki. jan gashin kanta kwance a gadon bayanta. Se da ta gama tukuna ta mayar da wukar cikin gidanta tana me cusa hannunta cikin jan gashinta, taɓe fuska ta yi alamar ta ɗan gaji hannu ta miƙa alamar a miƙo mata abu, da sauri wata baiwarta ta miƙa mata towel da glass of water.

Ɗan goggoge zufa tayi tasha ruwan kafin ta soma tafiya cike da kasaita bayi kusan goma ne suka bi bayanta, kai tsaye wani hadadden part ta nufa tunda ta shiga bayi suke kwasar gaisuwa,bedroom din ta da ya gaji da haduwa ta shiga cikin nutsuwa ta soma cire rigar jikinta yayi saura bra seda ta cire Kayan jikinta sannan ta ɗaura towel ta shiga toilet tayi wanka ta fito.nan ta samu masu mata hidima suna jiranta zama tayi a kujera suka soma goge mata jiki haɗe da shafa mata lotions masu tsada bayan sun gama shiryata ne cikin doguwar riga matsatstse brown color sosai ya fito mata da shape dinta takalmin kafarta hill ne wanda ya Kara mata tsayi,sosai ta yi kyau se baza kamshi take yi.
Take mata baya suka yi izuwa Palace a hanyar ta zuwa ne wani dogari ya dakatar dasu ta hanyar sunkuyar da kan sa haɗe da faɗin

“ PRINCESS GABRIEL.,QUEEN na da bukatar ki a church domin gabatar da adduar neman tuba”.

Ɗan siririn tsaki ta ja cike da shagwaba ta ce “ ita da su waye a church din?.”

Cike da girmamawa ya bata amsa “ tare take da me girma president David Abraham da matar sa excellency Katrina Abraham”.

Babu yanda ta iya domin ba wani son ziyartar church take ba,daga bakin church din taji pastor nata zuba preaching.

Ɗago Kai QUEEN JESSICA ta yi ta ɗaura idanunta akan ƴarta daya tilo wato Princess Gabriel.

“ Ƴata Gabriel “ ta faɗa tana takawa izuwa gareta rungumeta tayi tana riko hannunta suka karasa gaban pastor. Murmushi President David ya yi yana shafa kanta “ lokaci na gudu sosai kin ga har surkarmu ta girma” ya faɗa yana kallon matar sa,murmushi tayi haɗe da rungume Princess Gabriel.

“ barka da warhaka Uncle David nayi kewar ku sosai” Princess Gabriel ta faɗa a shagwaɓe

“ hhhhh ƴata mu ma mun kewar ki sosai shisa muka zo domin cin abincin Safiya tare da ku”.

Queen Jessica dake kallon su ne ta yi murmushi.
Bayan pastor ya gama adduar ne President ya dubesa ya ce “ Pastor Emmanuel Ina so a duba lokaci mafi albarka da zaa yi wa wa ƴannan yara namu baiko domin in san yaushe zan faɗawa Jay ya dawo gida “.

Cikin gamsuwa Queen Jessica ta jinjina kai. rufe ido pastor ya yi yana ƙirge da yatsunsa kusan mintuna uku yana a haka kafin ya buɗe ido.

“ Mai girma president wato lokaci mafi sa albarka shine kwana talatin masu zuwa ranar da zaa samu lumshewar rana,zaka iya cewa Jay ya dawo gida domin su samu fahimta shi da Princess Gabriel “.

Sosai su ka yi farin ciki da Jin abinda pastor ya fada domin sun jima suna jiran wannan rana domin kara zumuncin dake tsakanin su ta hanyar had’a yayansu aure.
Queen Jessica ita ce Sarauniyar England kuma duk duniya Ƴa daya Allah ya bata wato Princess Gabriel. President David Abraham shine shugaban kasar England in da suke da ɗan su ɗaya ne Suna JAYSON suna mishi lakabi da Jay Wanda yake Karatunsa na masters a kasar Turkey.
Babban liyafa aka tanadar a teburin cin abinci kalolin abinci yafi ashirin Wanda aka tanadar.bayan sun gama breakfast ne Mai girma president suka tafi.

“ Mom ta ya za ki yarda da wannan haɗin auren bayan na ce miki banason shi,ni da shi babu jituwa tsakanin mu tun muna yara ya tsaneni kuma ni ma haka. Dan haka ni bazan taɓa auren Jay ba shine kawai “.

“A saboda hakane Ai yasa muke so mu had’a ku auren ai, tun kuna yara mu ka yi alkawarin had’a ku aure in kun girma , sannan kar ki manta tun kafin a haife ki nida president David abokai ne dan haka ki kwantar da hankalinki auren ki da Jayson kamar an yi an gama “.

Cike da sangarci ta hau bubbuga kafarta a ƙasa tana kwakulo kuka
“ Mom wannan sam ba adalci bane,bazan taba lamunta ba” ta yi maganar tana me barin bedroom din Queen Jessica.


MASARAUTAR BAYAAN


“ my Haseena na yi missing din ki matuka yaushe za ki zo”. Ta cikin wayar ta jiyo sautin dariyar Haseena tana faɗin

“ kar ki damu Ina nan zuwa amma ba nan kusa ba gaskiya,ya ki ke ya jarababbiyar twin din ki!?”. Dariya sosai Muzna ta yi Jin Abinda ta ce.
Buɗe baki tayi zata yi magana Muzaina ta shigo dakin cikin shirinta na bacci kashe wutar dakin tayi ta furta

“ ki ajiye wannan wayar mu kwanta “.
Jin muryarta da Haseena ta yi ne yasa ta faɗin

“ speaking of the devil “.
Sake tuntsirewa da dariya tayi a Karo na biyu. Watsa mata Harara Muzaina tayi ba shiri tayiwa Haseena sallama

“ Haseena ta ki yi bacci cikin aminci “.

Ajiye wayar tayi bayan ta sakata a silent ta je jikin Muzaina ta kwanta haɗe da musu addua.


Washe gari duk in da ka duba a cikin Bayaan se hada-hadan had’a taro a ke yi Ana ta preparation a babban filin masarautar me girman ika hamsin.

Karfe 2:30 an gama duk wani shiri kawai Gimbiyo a ke jira,suna can ana shiryasu sun sha light make up.

Hamra dake make up artist ce tana taya masuyiwa Muzna kwalliya gyara mata gashin kanta da aka mayar dashi baya gaba daya ya kwanta se aka dibi gashi kaɗan daga gefen hagu ta kitsesa haka gefen dama shima ta kitse guda daya ta kwantar dashi akan gashin ta ƙullesa da sauran. Wani mayen head chain da ya sha stones ta saka mata daga keyar gashin nata se walwali yake.

“ Gimbiya na rantse da Allah ban taɓa ganin masu kyaun ku ba,an ya za'a samu kuwa?” Dariya tayi jin shirmen Hamra din.

“ you’re so funny Hamra”. ta faɗa Tana shafa head chain da ta saka mata chains din ta shafa kafin ta cire hannunta tana kallon kanta a mudubi.

Se da aka gama yiwa gashin kwalliya sannan aka miko mata kaya nauyin da ta ji sun yi ne yasa ta ce “ tabb ɗijam wannan nauyi haka”.
Ɗan dariya masu kwalliyar suka yi.
Fice wa suka yi a ɗakin domin bata damar saka Kaya.
Warware Kayan ta yi taga abubuwa da yawa cike da rashin fahimta ta tsaya Tana kallon su domin yanda taga abubuwa daya wa yasa ta ruɗe domin tasan babu yanda zaa yi mutum ya shirga wannan Kaya gaba ɗaya a jikinsa.

“ Hamraaaaaaaa”. Ta ƙwala mata ƙira cikin daddaɗar muryan ta me zaƙin gaske. Shigo wa tai Tana tambayarta meyafaru

“ ke ni ban San ta Ina zan fara saka wannan Kayan ba naga pieces da yawa ga duwatsun da ya Kara musu nauyi na fitina”.

Dariya ta fashe dashi kafin ta ce “ dama na yi tunanin haka in ba an yi guarding din ki ba ba lallai ki iya sawa ba”.

Harara ta watsa mata “ kin San da haka shine zaki tafi ki barni da su”.

“ afuwan “ Ta faɗa

Daukar wata yar karamar Riga da iyakacinsa cibiya tayi ta mika mata. Bayan ta sane ta juya mata baya ta haɗe mata botul din rigar.

Wani skirt me tsayi yana nan pencil wanda ya haura saman cikinta ya rufe cibiyarta dake waje ta saka.
A cikin kayan wanda ya kasance yana da tsayi sosai Jadwah ta ɗauka ta soma nada mata shi Akan skirt din se ya yi faɗi sosai da girma Wanda ko kafafunta baa gani.
Da ta gama naɗa mata shi ne ta ɗauki wani sarka na zallar zinari Wanda ake ado dashi a ciki Ana ɗaura sa ne a saman Kaya,nan ta ɗaura mata shi,mayafin Kayan da ya gaji da haduwa ne me girman gaske ga ƙananun stone da manya da aka watsa a jiki yana nan shara-shara ana ganin komai kamar net ta saka mata akai Wanda tsayinsa har yana ja a kasa sak ta fito tamkar Sarauniya. Irin kyawun da Muzna ta yi duk yanda ka so ka faɗa tofa Baki baze iya zayyanawa ba kamar ba mutum ba tsabar wutar kyau.

“ ya Allah wallahi kin yi masifar kyau”. Cewar Jadwah da ta gama shiryata,murmushi tayi domin ita kanta tasan tayi kyau base an fada mata ba.
High hill ta saka kalar kayan ta fesa performs masu daɗin ƙamshi. Suna tsaye tana mata hoto wata baiwa ta shigo ta sanar dasu da yanzu zaa tafi

Bayin dake take musu baya ne suka rike mata bindin mayafinta.

A falo suka tarar da Muzaina da ita ma ta shirya cikin kalar kayanta komai sak iri daya babu abinda ya banbanta su se color Kayan na Muzaina orange ne da touches din white and peach,while na Muzna is orange da touches din silver da pink.

Zama ta yi a gefenta tana mata whisper a kunne
“ kin yi kyau sosai my Muzaina “
“ same to you honey”.

Dake tsakanin filin da za'a yi taron da kuma palace akwai tafiya hakan yasa aka tanadar musu da motar domin already kowa ya tafi jiransu kawai ake yi.bayan sun isa ne suka ga yawan al’umman da suke gurin ya cika fiyeda tunani,Har wajen zaman su dake saman minbari aka Kai su,akan kujera me masifar kyau na alfarma. Duk wani me mukami da yan uwa suna saman mimbarin zaune a yayinda yan masarautar suke daga kasa zaune akan plastic chair wa’yanda basu samu gurin zama ba kuwa na daga tsaye,tunda suka shigo gurin ido ya dawo kansu domin masifar kyau da suke dashi kamar ba mutane ba,ga kuma Kayan jikinsu da se manyan gimbiyoyi ke saka irinsa domin kayane na alfarma Wanda ko a wasu masarautun da yawa can’t afford it.

Ta rasa me yasa tunda suka iso gurin hankalinta ya kasa kwanciya ji take yi akwai ido me karfi akan ta yana kallonta wanda hakan yasa take Jin insure.

Hakimi ne ya tashi ya buɗe taro da addua sannan ya soma Jawabin dazeyi dake rubuce a littafi.

“ Kamar yanda ku ka sani sarkin mu me adalci me daraja marigayi yana da ƴa'ƴa mata guda biyu.wa’yanda rabon su da wannan masarautar shekaru sha biyar kenan se yanzu Allah ya yi musu dawuwa,ga su nan kamar yanda ku ke gani, Muzna Taifur Rahman da kuma Muzaina Taifur Rahman.sun dawo tushen su sun dawo kasar su ta haihuwa cikin koshin lafiya.babban abinda yasa aka tara ku anan bakomai bane fa ce gabatar muku dasu,domin da iznin ubangiji DAYA CIKIN BIYU ko Muzna ko Muzaina daya zata shugabance mu.lokaci ƙalilan na zuwa da za'a tantace muku wacece wacce aka zaɓa. dan haka taro na gaba da za#a yi shine taron sanar da shugaba".

Duk wannan jawabin da hakimi yakeyi hankalinta baya wajen in an ritseta bazata iya faɗar ko da kalma daya da ya faɗi ba,se wulwulga fararen manyan idanunta take,saboda kaifin idon da take ji ya tsananta hakan yasa ta baza idonta cikin taron ko Allah ze sa ta had’a ido da wanda yake mata kallon kurillan nan.

Sauka dara-daran idanunta suka yi akan idonsa da ya kafeta da su ya yi jajir tsabar bacin rai ga jijiyoyin kansa da suka fiffito.
Wani irin faɗuwa taji gabanta ya yi nan take hawaye suka cicciko a idonta, ga wani kunyarsa da ya rufe ta se da taji komai ya fice mata arai,sarƙewa idanunsu ya yi cikin na juna yana jifanta da muguwar kallo a yayinda take mishi kallon neman yafiya.
Magana Jadwah ta ke mata amma Sam taga hankalinta na wani gurin daban hakan yasa ta kalli inda ta miƙa attention dinta gaba daya,zaune ta gansa akan kujera dake ta farko-farko,ita da ba ita tayi karyar ba seda taji gabanta ya fadi a hankali ta furta

“ Sadauki Zubairrrr “.

Murmushi Kawai yake saki yana kallon fuskarta da kuma fuskar Sadauki Zubair yasan yanzu babu abinda ze hana basu rabu ba.

“ Gimbiya Muzna shin kina tare damu kuwa!?”. Galadima Abdul Aleem ya faɗa domin ya ga hankalinta be gurin,duk da kuwa ya mata magana amma sam bata jiyo sa ba,maganar da Galadima Abdul aleem da ya yi mata bata amsa bane ya jawo hankalin Muzaina,dasu yarima Haysam nan su ma suka mayar da hankali dan ganin menene ya ɗauke mata hankali har haka.
Sosai suka yi mamaki ganin kallon da suke yiwa juna ita da Sadauki Zubair. Murmushi kawai Galadima Abdul Aleem yayi.

Kallo daya Muzaina tayiwa Sadauki Zubair ta ganesa tsaki ta ja sannan ta taɓa Muzaina ta furta “ concentrate Muzna “.

Se a sannan ne hankalinta ya dawo kansu ganin suna kallon ta ne yasa ta sunkuyar da kanta tana me kokarin shanye hawayen dake son zubowa.
Bayan dogon jawabai da yin duk wasu abinda ya dace Wanda shine dalilin taro kowa ya watse ko bayan da suka koma daga ita har su Aliyah jikin su ya mutu

“ wait wai ma tukuna ta ya aka yi ya dawo shi da aka ce sun tafi war?”.

“ this is the same question am asking myself Aliyah,bakina da bakin wannan saurayin ya shaidamin Sadauki na sun tafi amma it turns to be a lie. Amma tukuna menene ze sa bawan Allah nan ya min karya ???”.
Ta faɗa tana yamutsa gashin kanta da suka zubo ta fuskarta.

“ Gimbiya ba ki da wani zabin da ya wuce ki same sa”.Cewar Hamra.
Girgiza Kai ta yi kamar zata yi hawaye ta ce “ banida wannan kwarin guiwar Hamra,na rigada na ci amanarsa,he lost his

Please Login or Register in order to submit comment