Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din,ko kuma zan wuce gida kawai nasan zan sameta a can" ta faɗa tana kashe wayar da sauri ta ɗauki wayar ta kawai ta fito cikin sauri-sauri. ma'aikatan ne suka tsaya kallon ta suna mamakin yau meye ya samu boss din tasu haka, manager din ta ne ya tawo da sauri yana tambayar ta meyafaru.


" Aba ne ya rasu " sosai ya ji babu dadi ya mata ta'aziya sannan suka fice a tare.


Suna zaune a falo Muzna har yanzu bata dena hawaye ba musamman in ta tuna yanzu fa sarki ya mutu bazata sa'ke sakasa a Idonta ba har abada,tana tuna watanni bakwai da ya wuce sun zo shi da sarauniya Fatima, kuma basu ga alamar bashi da lafiya har sosai ba? ashe yana fama da Cancer wannan abu ya tsaya mata a rai.

Haseena se hakuri take bata Elizabeth me aikinsu tana daga tsaye a gefe tana kallon su duk da bata jin larabci amma ta fahimci wani abu ne gagarumi ya faru hakan yasa jikinta yin sanyi sosai.


A falon ta same su zaune itama ta zauna tana dawo da Muzna jikinta haɗe da shafa bayanta tana bata hakurin rashin da suka yi.

Da mamaki sosai Haseena take kallon fuskar Muzaina wanda ko ɗigon hawaye babu a ciki se de yanayi na damuwa kawai, ita de kullum bata dena mamaki da kuma tambayar kanta wai Muzaina wata irin mutum ce,.

Haɗa ido suka yi ta kamata tana satar kalllonta hakan yasa ta watsa mata muguwar harara.

" Muzna addu'a zamu yiwa Aba. Allah da ya fi mu son shi ya karɓi abinsa".

" Muzaina mu tafi gida a yau bazan iya kwana a wannan ƙasar ba ". cewar Muzna.


" Kin san bazeyu mu koma gida ba ,saboda ba mu da password ɓalle viza,an ƙi yi mana ne saboda kar mu je Kuwait batare da sanin Aba ba".


A haka suka kasance a zaune har bayan ƙarfe tara babu abinda suka iya sawa cikin su,babu wanda ya yi sallah a cikin su,se da goma ya yi ne Muzna da Haseena suka yi sallah mangrib da ishai, a cikin wannan daren Elizabeth da Haseena suka haɗawa Muzna kayanta gaba daya da duk wani abinda take buƙata,itama Muzaina tana can bedroom dinta tana haɗa kaya.


A wannan daren Muzna bata rintsa ba bacci gaba daya kauracewa idon ta yayi.haka ta kasance a zaune a kan gadon dakin Haseena dan dama tun da safe ta yiwa nata dakin hijira saboda abinda taji a ciki.


Washe gari sallah suka yi aka fitar da kayan su zuwa compound ɗin gidan,dakyar suka rarrashe ta taci abinci duk da babu yaw. Abaya gaba dayansu suka sanya,haɗe da Pakistan hijab.bakaramin kyau suka yi ba dukkan su uku,duk da Haseena bata kamo su kyau ba,suna zaune a falon sun yi jugum suka ji dirin saukar private jet din masarautar su a compound ɗin gidan.

Se da jirgin ya gama dedetuwa kafin nan suka fito nan suka tadda ma'aikatan gidan suna a tsayayye dake Haseena ta sanar da su batun tafiyar da zasu yi din.


Zuro kyakyawar ƙafafun sa da suke cikin takalmin sarauta yayi, kafin ya fito gaba daya, masha Allah kyakkyawan tsayayyen namiji cikin shigan kayan sarauta da suka matukar dacewa dashi,ta ko ina ya haɗu ga tsayi da faffadar kirji,gashin kansa ya kwanta a bayansa yana da tsayi se sheki yakeyi yasha gyara sosai,kallo daya zaka masa ga ka ainihin jinin sarauta na yawo a jikinsa. isa inda suke tsaye yayi kafin suka rungume juna shida Muzaina

" Amincin Allah ya tabbata a gareku ya ku ya'yan sarki adali me adalci".

" Ameen Ameen Yarima Farasat ".cewar Muzaina.tana sumbatar hannun sa.

Wajen da Muzna take yaje suka rungumi juna ta sumbaci hannunsa.


" Ina me tayaku bakin cikin rashin mahaifin ku, Allah ya jaddada rahama a garesa ".

" Mun gode yarima Farasat" ta faɗa tana yin gaba cikin jirgin suka shiga su uku a yayinda suke jiran Muzaina da take sallamar ma'aikatan nasu.


Tunda suka shiga cikin jirgin babu wanda ya yi magana har suka sauka a cikin babban farfajiyar masarautar Bayaan me matukar kyau da tsaruwa haɗe da burgewa jirgin yayi.ya Salam masarautar Bayaan babba ce wanda duk bin kokkofin mutum baze taɓa ganin karshen sa ba,yana da girma wanda baze iya misaltuwa ba,ko ina ka duba yana da kyau ginunnuka masu kyau ne a ciki wanda suke a tsaftace tsaf kuma bana kowa bane face na bayin dake ciki,shashin su yana da girma da kyau ko na wasu masu ƙananan karfi ma iyakaci kenan,ga bangaren mayakan masarautar shima yana da kyau kuma ko wani shashin akwai gate me kyau da aka saka domin bada tazara tsakanin bangarorin maza da mata. Filin kuwa ko ina zaka taka intalok ne Malale a kasan duk inda ka juya akwai shukoki masu kyau.ga rumbu.

Design masarautar Bayaan kadai abin kallo ne,babu mahalukin da ze shigo beji ya kaunaci rayuwa ta har abada a ciki ba.in na ce zan ci gaba da zayyana muku kyau da tsari haɗe da girman masarautar Bayaan to ko pages biyu baze ɗauke mu ba. Ga bayi da kuyangu ta ko ina se shawagi suke yi kowa na harkokin sa,mata na sanye da doguwar riga jikinsa babu kwalliya launin shuɗi,mazan kuma na sanye da kaya launin ja da shuɗi.


" Wowwww wai dama wannan shine masarautar mu da aka hana mu rayuwa a ciki!?, gaskiya ya haɗu oh my god Muzna duba ki gani " Muzaina ta faɗa tana ta waige-waige a cikin masarautar domin kyau da komai na masarautar nasu ya gigita mata lissafi da kuma ƙara kwadaita mata son mulki.

" Uhmmm ".

Kawai Muzna ta faɗa duk da itama masarautar ya tafi da ita,amma abinda ke damunta daban,haka itama Haseena se kalle-kalle take yi komai na cikin masarautar was so unique.

Wasu bayi ne masu sanye da kaya iri daya wanda ya kasance launin shuɗi me haɗe da baki hannun su riƙe da Kwando dake dauke da furanni masu yawa a ciki,wanda aka tanada domin yi musu Barka da zuwa.
mata guda ashirin suka iso gaban jirgin da sauri-sauri suka tsaya bisa layi duk mutum goma sun yi layi daya.

Wasu zaratan maza ne jikin su sanye da court bakake jikinsu murde fuska babu walwala suka taho ɗauke da wani babban jan carpet me girman gaske. suka soma shinfida sa wanda tsayin sa yakai daga inda suke tsaye har cikin entrance din palace din nasu, kafin duk suka tsaya hannunsu a baya kan su a sun kunye,kallon carpet din da jikin sa aka rubuta WELCOME da manyan baki suka yi, soma takawa suka yi,suna tafiya akai wa'yannan bayi matan ne suka soma musu wanka da furanni. Cikin nutsuwa suke tafiya duk inda suka wuce se bayin sun runsuna a ƙasa har su wuce, sannan su biyo su a baya.

Cikin babban palace din suka shigo, Allahu Akbar, tundaga kofar mashigar palace din ma abin kallo ne, domin da zallar zinari aka yi sa ɓalle kuma abubuwan kayatarwan da suke ciki,baki baxe taɓa iya faɗan yanayin tsaruwan cikin ba sede kawai ku masu karatu ku ƙiyasta, fada ya matukar haɗuwa, kuma a cikin babban fadan sarki ake zaman makoki inda kowa yana sanye da fararen kaya ga kuma makaran da sarki Taifur Rahman ke kwance a ciki lifeless,an masa wanka,an yi mai komai kawai jiran zuwan gudan jinin sa ake yi kafin a sallace sa. Kowa ka gani a cikin faɗa zaka fahimci mutuwar sarki Taifur Rahman ya jijjiga sa, domin sarki ne da yayi mulkinsa a bisa gaskiya da amana.

Tunda suka shigo faɗa nan fa Muzaina kwadayinta ya sake hauhawa,duk da ta kama kanta ta nutsu kar a fahimci abinda ke zahirin fuskarta da gangan jikin ta,amma hakan baya hanata satan kallon fadar.

Kallo ne ya dawo kansu cike da girmamawa kowa ya miƙe haɗe da sunkuyar da kawunan su a garesu a domin kuwa suna da yakinin tabbas a cikin su daya zata shugabance su,.

Kamar yadda suka yi a gare su haka suma suka mayar musu da martani. wajen Ummi dake tare da matayen galadima da waziri Muzna ta nufa tana me rungumeta, sarauniya Fatima da Idonta yake jajir saboda kukan da tayi ne tayi hugging ƴarta back,a cikin kunne Muzna ta dinga yiwa sarauniya rada me kwantar da hankali. Isowa wajen su Muzaina tayi tana me rungume su duka.

Addu'a suka yiwa sarki Taifur Rahman suna yiwa fuskar sa kallo na karshe,duk yanda ta yi domin ta shanye hawayen ta amma abu ya ci tura se da ya gangaro,suna a durkushe a gaban makaran da aka saka shi,taji an dafa mata kafaɗa,a hankali ta juya dan ganin waye, tsohon da ta gani ne yasa ta sunkuyar da kai ƙasa alamar girmamawa.


Murmushi ya yi ya mayar da hannunsa bisa kanta na tsawon dakiku arba'in kafin ya cire yana sauke numfashi.

" Muzna akwai haske a tare da ke,ke me kawo gyara ce da zaman lafiya bayan ran mahaifin ki,da kuma ni din nan abubuwa da yawa zasu faru wanda ni bana kusa ɓalle in nuna miki hanya,amma tunda har aka haife ki to da yardar Ubangiji za ki bawa wannan masarautar da kuma ko ina kariya ".


Tunda ya soma magana take satan kallon sa,ita har yanzu ta gagara gane wa'yannan maganganun ina suka dosa, a ina yakamata ta yi musu mazauni,.gaba daya zantukan sa ɗaure mata kai yayi,ya kuma jefata a duhu.

Har zuwa lokacin da yake maganganun bata dago kai ta ɗaura Idonta akan fuskar sa ba sede satan kallon farar fuskar sa me ɗauke da farar kasumba me matuƙar tsayi da yawa wanda tsayin sa yakai kusan kirjinsa,kansa kuma yasha rawani irin na manyan malaman larabawa.

" Meyasa ka ke faɗa min wannan maganar!?,meyasa nake shiga rudu a cikin yan kwanakin nan!? " Ta jero masa tambayoyi a lokaci guda, murmushi kawai ya mata ya furta


" Hhhhhhhh, Muzna ke yarinya ce qarama.Za ki fahimta yanzu ai lokaci ya yayi ".

Still fuskarta na cikin damuwa domin kuwa be bata amsar da ya dace ba,ba ta samu amsar da zata gamsu dashi ba wanda ze kwantar mata da hankali ba.

" Shin ko zan iya sanin ka!?" Ta fadi hakan a hankali domin lakar jikinta ya gama narkewa lakwas.

" Sheikh Abu Dhabi,shine sunana " yana faɗar haka ya miƙe tsaye riƙe da sandarsa yana dogarawa ya soma tafiya,da kallo kawai ta rakasa.


" Meye abinda wannan tsohon yake faɗa miki Muzna " Muryar Muzaina ya dawo da ita cikin tunanin ta.

" Manta kawai" ta faɗa tana duƙo da kanta izuwa fuskar mahaifin su ta manna masa sumba a goshi haɗe da ci gaban da yi masa addu'o i,bayan sun gama ganawa da shi ne, aka zo aka ɗauke sa domin kai sa gidan sa na gaskiya.

Amintacciyar baiwa ce ta yiwa ko waccen su rakiya izuwa shashinta da ke ɗauke da komai na bukata,wanda Haseena da Muzna suka tafi tare. Makeken falon dake sashen Muzna na zagaye da wasu luntsuma_ luntsuman kujeru wa'yanda suka kasance royal cushions white color ga throw pillows din su blue color, carpet din dake malale a falon me laushin gaske da idan mutum ya taka se ya ji kamar ya taka katifa tsaban laushi ya kasance blue in color haɗe da touches din fari,a tsakiyar kujerun akwai center table da saman sa ke ɗauke da mini glass flowers,se tafkeken Tv plasma dake zaune akan standard Tv. Kamshi ta ko ina yake tashi sai sanyin AC dake ratsa jikin ɗan Adam, yanayin design din falon, bedrooms da komai kana gani kasan manyan kuma shahararrun magina ne suka ƙawata sa.


Bayan sun yi wanka ne suka shirya cikin fararen kaya kamar yanda kowa yayi suka fito aka zauna a faɗa ana ci gaba da zaman makoki. Muzna na tare da sarauniya Fatima sabanin Muzaina dake zaune a ɗan gefe da su.

" Barka yar uwa " ta ji anyi mata magana daga bayanta, slowly ta waiga nan suka haɗa ido da wata kyakyawar matashiya dake zaune a gefen su tana sakar mata murmushi.

" Barka dai Hamra" ta faɗa,tun daga nan babu wanda ya sake magana saboda basu wani saba sosai ba se de a waya ne suke ɗan gaisawa duk da ba sosai ba.

Bayan an yi sallah la'asar ne kowa ya watse aka bar iya shakikan sarki tare da iyalan sa,se a sannan ne sarauniya Fatima ta samu magana da ya'yan ta.


" Ummi nayi kewar Aba sosai" cewar Muzna da fuskarta da har yanzu yake a marairaice domin mutuwar ya shigeta sosai.

Murmushi kawai sarauniya tayi kasancewarta jarumar mace ce me juriya da tawakkali ta furta

" Muzna Aba din ku yana wajen da ya kamata,wajen da mu ma duk daren daɗewa tofa se mun je".

Gyada kai ta yi, Muzaina ta ce " amma Ummi dama Aba bashida lafiya ne ko kuma!? ".

Se ta sauke numfashi kafin ta amsa mata

" Aba din ku,ya kasance yana fama da ciwon hanta an yi magani iri-iri amma Allah be sa an dace ba ".

Da kallon mamaki Muzna da Muzaina suke kallon ta domin basu taɓa sanin wannan maganar ba,basu taɓa sanin cewa sarki Taifur yana da ciwon hanta ba,.

" amma Ummi yarima Farasat ya shaidamin ciwon daji ne yayi fama dashi “. Cewar Muzna.

“ ah ah hanta ne ba daji ba,kamar yanda bakuda masaniya su ma ba dukan su bane suka sani”.


Koda jin maganarta shuru suka yi. babu wanda ya kuma iya magana a cikin su,ko da dare yayi babu wanda ya iya saka abun kirki a cikin sa,duk suna zaune a dinning,Ummu Zaheenat matar galadima Abdul Aleem ta ce

" Muzna wannan kawar ki ce !?" Ta faɗa tana duban Haseena.

" Ehh ƙawata ce,Ummu Xulaihah. Sunanta Haseena Abdul Muxxalib".

Murmushi suka yi suna yaba nutsuwar Haseena,dan ta burgesu.

Tsaki Muzaina ta yi jin yanda suka cika mata kunne da zancen wata Haseena,duk dubanta suka yi, Yarima Farasat dake gefenta ya ce

" Meyasa ki ke tsuka ? ".

" Nothing " ta yi maganar tana haɗe fuska tare da Miƙewa ta ɗauki tissue tabar dinning din tana goge hannunta.

Girgiza kai Muzna ta yi domin tasan abinda yasa tayi haka,har ta shige basu dena bin bayanta da ido ba.

" Muzna je ku kwanta dare ya yi ". Cewar Ummu xulaihat matar waziri,. Miƙewa Muzna da Haseena suka yi suka wuce part din ta,maida kallonta kan Su Hamra tayi

" Hamra, Aliyah,Jadwah kuma kuje ku kwanta".

Miƙewa suma suka yi suna barin dinning din. Ya yi saura yarima Farasat ne da Yarima Haysam,se kuma su.


" Sarauniya Fatima, bana ganin boyewa yaran nan halin da ki ke ciki abu ne me kyau,yakamata su san da rashin lafiyar ki" cewar Ummu Zaheenat.

Ajiyar zuciya ta sauke " haka ne amma,in suka samu wannan labarin hankalin su tashi ze yi ni kuma banason su sa'ke shiga matsananciyar damuwa akan wanda suke ciki ,taya zan iya samun kwarin gwiwar sanar da su cewa nima ina da ciwon hanta kuma ina matakin karshe,ah ah bazan iya ba Zaheenat,na san lokaci ƙalilan nake dashi a wannan duniyar. kwanaki kaɗan ne suka rage min in bi mijina in da ya tafi,abun da nake sa'ke roko a gun ku shine,ku riƙe mun ya'yana domin marayu ne su,ku riƙe su kamar ya'yan ku " jiki a sanyaye suke kallon ta suna jin wani irin karyewan zuciya,.

A hankali ta furta " Haysam, Farasat ku nasan bayan raina baza ku bar kannen ku su kauce a kan hanya ba ".


" Mun miki wannan alkawarin Ummi " cewar yarima Farasat.

Murmushi tayi tana tunanin wani irin hali yaran nata zasu shiga bayan mutuwarta,domin lokaci ƙalilan gareta.


" Yarima Ishaq na hanyar dawuwa gobe" yarima Haysam ya faɗa yana Miƙewa da nufin barin falon babu wanda ya ce masa komai har ya fita.


Cire kayan jikin ta tayi ta daura lallausan towel ta nufi hanyar toilet domin yin wanka .har izuwa yanzu fuskarta a haɗe yake,ita kaɗai se jan tsaki take yi.
Kunna shower tayi ruwa ya fara zuba a jikinta kafin ta ɗauki sinadaran wanka masu kamshi ta fara gogawa lallausan fatar jikinta se da ta kwashe mintuna goma tana abu daya domin ba iya wanka tayi ba harda gashin kanta ta wanke sa.
Sauke numfashi tayi lokacin da ta gama, sannan a hankali ta nufi jikin hangan dake sakale da towels a jere a jiki. hannu tasa ta janyo daya,abinda ta gani ne yasa ta yi saurin jan baya tana ɗaura hannu akan al_auranta.

Bakomai ne ta gani ba face wani dattijon ba indiye sanye da jajayen kaya goshin sa na shafe da wani farar powder da ja,duk da tsoho ne amma tarin sumar kan sa baki ne,ga wasu manya-manyan hatimai ɗaure a damtsen hannayensa idanunsa a rufe yana fuskantar ta.

" Waye kai?,meyasa zaka shigo min nan?, wanene ya baka izinin hakan !?". Ta faɗa tana kuma ja da baya,tana kakkare jikinta.

A hankali ya buɗe jajayen idanunsa da kwayar bakin cikin yan ƙanana,ya ɗaura su akan fuskar ta.


Da wata iriyar murya me amo ya soma magana,wanda duk magana daya da ze yi se ta ji tsigan jikinta ya tashi.


" Muzaina,na zo wajen ki ne badan komai ba se dan taimaka Miki,nasan kina matukar son ki mulki Bayaan,wanda kina ganin za ki samu a ruwan sanyi,to ba haka abin yake ba, wannan mulkin da ki ke kwadayin sa kina ji kina gani a gaban idonki za'a bawa wata,bayan kuma kin fi ta cancanta,kin fi ta bukatar wannan kujerar,zasu juya miki baya a lokacin da kike kuka kina rokon da su bar miki kujerar amma ba zasu taɓa baki ba,sannan....."

" Dan Allah malam dakata,.kai din waye zakazo kana faɗa min wa'yannan maganganun marasa kan gado?,,tayama kasan duk wa'yannan abubuwan zasu faru,to bari ka ji yar uwata Muzna bata bukatar wannan kujerar, saboda babu kaunar abinda ya shafi sarauta a ranta koda kuwa akwai ni nan nafita cancanta " ta faɗa bayan ta katse sa.

Dariya ya bushe dashi wanda se da yayi sanadiyar bangon toilet din suka fara daddarewa.

" Yaro yaro ne,zaki fahimci hakan a lokaci kɗan dake zuwa,a yayinda danasanin ƙin karɓan tayina ze zo miki. domin kuwa ni aljani Suwami gautam bana faɗar abinda yake ba haka ba,amma bazan juya miki baya ba,kofa abuɗe yake a duk lokacin da kike da buƙatar taimakona kawai ki furta, zurfa_zurfa narash mani gumaaaaaal zaaararrrr,hamkam_hamkam zurfa-zurfa, za ki ganni tsaye a gaban ki batare da bata lokaci ba,hhhhhhhhhh ". Ya gama maganar yana bushewa da wani dariyar da yasa toilet din ya soma girgiza da karfi iska me karfi yana tashi wanda madubin dake manne ta ko ina suka soma fashewa suna fitar da wani ƙara na tsoratarwa,da karfi ta toshe kunnenta tana duk
ƙawa a ƙasa.

Ɓacewa ya yi bat,nan take komai ya dawo dede,tsit,kamar babu wani abinda ya faru komai ya koma mazaunin sa,a hankali ta cire hannun ta a kunne tana miƙewa tsaye haɗe da bin toilet din da ido. ganin komai na nan yanda yake hakan yasa ta fara zullumin ko mafarki take yi towel din da ta zaro zata daura ta gani yashe a ƙasa da hanzari ta ɗauka tana me ɗaurawa a jikinta ta fice da sauri.



" Bamu taɓa tunanin zamu gan ku a nan kusa ba gaskiya, saboda tun muna yara muke tambayar yaushe zaku dawo. se a ce mana kun kusa " cewar Hamra dake zaune akan makeken royal bed din Muzna,ita da Jadwa, Aliyah,se kuma Muzna da Haseena dake zaune a tsakiyar gadon,suna saurarar Hamra.
Domin tun lokacin da suka shigo su ma suka biyo su a baya domin tayasu hira,da samun lokaci tare da su,kuma hakan yayiwa Muzna dadi sosai sede ta fuskanci duk yanda take da surutu tofa su Hamra sun fita.


Murmushi tayi ta ce " to ai mu ma haka yanzu ga shi dalili me ƙarfi ya dawo damu batare da mun shirya dawuwa ba" ta faɗa a sanyaye,dafa kafaɗar ta Haseena tayi.

" Gimbiya Muzna duk sanda wani sabon magazine din ki ya fito tofa se na kalla wallahi kina burgeni,nima zaki koyamin yanda ku ke tafiya da tsayuwa ko?,domin nide ina son jaruman finafinai sosai,ba domin ni engineer bace da na shiga harkan film gaskiya " cewar Jadwah da tunda ta soma magana ko haɗiye yawu batayi ba.

Dariya sosai Muzna tayi domin Jadwah ta sata dariya sosai duk da yanda take cikin damuwa,.

" Gaskiya Jadwa kina da abin dariya". Ta faɗa hakan tana me kwanciya,.

" Ke gobe yaya Yarima Ishaq na hanya" cewar Aliyah.

" Wani ya'ya Ishaq din !? ".

Hararan Hamra da ta yi tambayar Aliyah tayi tana faɗin

" Ya'ya Yarima Ishaq nawa muke dashi !?".

" Tabb dijam ki ce kwallon kwankwalatin ɗan iska na hanyar dawuwa de ". In ji Hamra.

“ ahhhh lalllai Hamra kin riƙa ya'yan naki ki ke cewa dan iska ?“.

Muzna dake jin su batace komai ba,amma tana tunawa da Yarima Ishaq din da suke magana akai tun suna yara,amma tunda suka baro masarautar Bayaan bata sake ji daga garesa ba sede taji ana kiran sunan sa.


Se da dare ya soma yi sosai ne kowa ya tafi in da yake kwana domin yin bacci,a yayinda Haseena suka kwana tare da Muzna, Muzaina kuma tana can bacci ya kauracewa idanunta se tunanin abinda aljani Suwami Gautam ya faɗa mata take yi.


Washe gari da wuri Muzna ta shirya cikin doguwar riga fara ta ɗan saka ƙaramar farin gyale akan ta ta rufe gashinta,komai fari tasa sannan ta fita zuwa bedroom din Muzaina zaune ta sameta akan gado ta mike ƙafa jikinta na jingine da gado,tana sanye da kayan bacci da alamu ko sallah batayi ba,ɓalle kuma wanka,zama tayi a gefenta tana kallon yanda ta lumshe Idonta, tabbas idonta biyu amma ta tsunduma cikin kogin tunani wanda hakan yasa batama san da shigowar ta ba.

Daura hannu tayi akan cinyar ta wanda hakan ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi,...

" Wai Muzaina lafiya na gan ki haka,ko wani abu na damunki ne? ".

Sauke ajiyar zuciya ta yi kafin a hankali ta ɗaura hannunta akan na Muzna ta runtse da nata hannun kafin ta soma faɗin

" My Muzna ina cikin wani yar damuwa ce kaɗan daga daren jiya zuwa yau ".

" Daga kallon fuskar ki na fahimci hakan, menene abinda yake damunki yake yar uwata!? ".

" Muzna na san yanzu babu yanda za'a yi abar Bayaan babu sabon shugaba,dole a cikin ni ko ke za'a zaɓi ɗaya,kin san yanda nake son mulkar wannan ƙasar,nasan bazaki taɓa tsayawa akan hanyata ba ko da wasa,domin ke babu sha'awar hakan a ranki kuma farin cikina shine naki ".

Tunda Muzaina to buɗe baki ta soma magana, Muzna ta tsareta da ido tana me bin ta da kallon al ajabi,tabbas tasan Muzaina na masifar kaunar mulki amma batayi tunanin jin wannan maganar daga bakinta ba musanman yanzu da ake jimamin rashin sarki Taifur Rahman ba.

Girgiza kai tayi kana ta furta " ban taɓa sha'awar rayuwa irin na sarauta ba saboda ina da nawa burinkan daban,as far as kowa ya amince da ke to ni banida matsala da hakan,amma ki sani muna cikin jimamin mahaifin mu be dace ki kawo wannan maganar yanzu ba ".

Wani irin dadi taji yana ratsata ga kuma sanyin da taji zuciyarta yana yi,kamar wacce aka daurawa kankara akan zuciya,duk wani damuwa da tantama ta ji ya warware mata lokaci guda.

Rungumeta tai tana " nasani,ke me son farin cikina ce ".


Murmushi ta mata kafin a zuciya ta furta " Muzaina ba za ki taɓa sauyawa ba".

Kafin a fili ta ce " Yanzu ki tashi ki yi wanka ki shirya ina jiranki a fada".
Cewar Muzna.

" Okay".

A haka suka rabu ita ta fice a yayinda Muzaina kuma ta shiga wanka.


Ko da ta fito,tana cikin tafiya a babban bangaren me girman gaske tana koƙarin fita daga ɓangarorin domin nufan faɗa ta ga an sha gabanta.

Baya taja domin ta tsorata ganin yanda mutum ya faɗo gabanta kamar wanda ze rungumeta.


Ɗaura Idonta ta yi a kan fuskarsa tana ganin waye ta haɗe rai kamar wacce bata san murmushi ba,a irin haka yanda fuskarta babu wasa zakayi tunanin Muzaina ce,domin ita ce wacce fuskar ta ko da yaushe yake a turbune.


Kyakyawa ne sosai yanada tsayi ga jiki me ɗaukan hankali komai din sa abin burgewa sede kyawun nasa a iya fuska ne kawai,domin kallo ɗaya zaka masa ka fahimci,irin wayayyun samari din nan ne wa'yanda idanun su ya gama buɗewa da bariki,mazan da idanun su ya goge da rayuwar turai.

Wani munafukin kallo yake binta dashi daga

Please Login or Register in order to submit comment