Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

little one “. Ta tsinkayo muryar Muzaina dake bayanta juyawa ta yi ta kalle ta batare da tace mata komai ba ta raba ta gefen ta za ta wuce ta yi saurin rungumeta tana faɗin “ am so sorry my Muzna banason wannan fushin da ki ke yi dani ko kad’an “. Raba jikinsu ta yi tana me fuskantar ta ta ce
“ Ko kad’an bana fushi dake I just want you to realize what you did was very wrong,menene yasa ki ka aikata haka abun ya tashi daga kan Zubair ya koma har kan mahaifiyarsa me yasa zakiyi haka?am your very own sister nayi tunanin za ki so abinda nake so amma ba haka abun yake ba,in ba ki so farin ciki na ba waye ki ke so ya so ? Banida kowa da ya wuce ke then why?shin farin ciki na be da muhimmanci a rayuwar ki ne?ban taɓa juya miki baya ba a duk abinda ki ke I stood by your side and support you in any decision you made “.
Ruko duka hannunta ta yi “ I said am sorry komai ya wuce please “.

Taɓe Baki ta yi ta ce “ is okay ya wuce muje part dina “. Tafiya suka yi suna rike da hannun juna,yinin ranar a tare suka yisa koda dare yayi suna tare.
Haka rayuwa ya ci gaba da tafiya suna gudanar da rayuwar su cikin so da kaunar juna ko da yaushe Suna tare kamar da babu abinda yake raba su,duk yanda su Jadwah suke son zuwa wajen Muzna haka suke hakura domin basu samu fuska ba gurin Muzaina ba,hakan yasa basa shiga part din ta se sun tabbatar da Muzaina ba ta nan ko kuma in Muzna taxo wajen su,wani irin sosai ce ne karfi da shakuwa ya sake shiga tsakanin Muzna da Sadauki zubair ganin lokaci na tafiya ne yasa aka musu baiko har zuwa wannan lokacin Muzaina ba ta sake nunawa Muzna cewa bata son alakarta da Sadauki ba. Ummu Zaheenat da Ummu Zulaiha kamar yanda suka yi wa sarauniya alkawarin bawa su Muzna kyakyawar kulawa suna iya kokarin su duk da ciwon kai da suke samu ta bangaren Muzaina domin Sam ta tsani wani ya kusance su ita da yar uwarta amma basa biye mata.

Yau tunda aka wayi gari aka tashi da ruwan sama me karfi kamar da bakin kwarya,ga tsawa da iska me karfi hade da walkiya da ake ta yi,hakan yasa babu alamar ko da dabba ne a waje balle mutum kowa yana cikin gidansu a daki yana kwance domin babu Wanda ze yi gigin shiga wannan ruwan hakan yasa kowa ya nutsu a muhallinsa ga duhu da garin ya yi duk da kasantuwar wannan lokacin yammaci ne.
Se da aka fara kiraye-kirayen sallah mangriba tukuna ruwan ya takaita se dan yayyafi da ake yi kad’an kadan,hakan yasa mutane suka fara fitowa domin gabatar da Ibada kowa ka gani sanye za ka gansa da Kayan sanyi domin ko da ruwan ya tsaya sanyi me ratsa bargon jiki ne yake busowa wanda mutum ze ji kamar ze zama kankara tsabar madarar sanyi,Ni’ima ya sauka ta ko ina.

Wani kasurgumin daji ne me girman gaske me dauke da yalwantaccun bishiyoyi masu tsayi da girma wanda suka yawaltu da korayen ganye abin shaawa,ga wani kuka kwado da wasu kananun dabbobi dake tashi daji ne me matukar tsoratarwa Musamman duhun da yake dauke dashi da dogin bishiyoyi.
Galadima Abdul aleem da sheikh Abu Dhabi tsaye cikin wannan dajin ga wani dabba me matukar tsoratarwa a gabansu,me ban mamaki da ban tsoro tabbas wannan dabbar be yi kama da normal dabbobi ba,duba da yanayin halittar sa,gashin jikinsa kala biyu ne fari da baki gashin ya yi luf luf a jikinsa,daga ta bayan sa kuwa yanada yanayin halittar mazaunan mutane se bindinsa da ya Kasu kashi biyu,yana da manyan kunnuwa masu tsayi da idanunsa masu firgitarwa guda hudu ko wani bangare akwai ido bibbiyu wanda cikinsu ya kasance jajaye sannan babu eyeball a cikin idon nasa,ga wani kaho dake a gaban goshinsa daga hanci zuwa bakinsa kuwa yana da irin halittar bil adama.,duk yanda mutum ya Kai gq dauriya da cijewa in suka yi ido biyu da wannan dabbar se ya girgiza. Wani farin kyalle ne aka shimfida akan inda dabbar ke a tsaye.
Galadima suna tsaye suna jiran zuwan mai girma sheikhy suka ga iska ya soma tashi hakan ya tabbatar musu da ya iso daga Kai suka yi suna kallon sa yana tafiya akan iska yana sanye da shigarsa na fararen Kaya kamar ko yaushe ga rawanin sa dake kansa da sandar sa.
Saukowa kasa garesu ya yi yana duban ko wannen sh,gaishe sa suka yi cikin girmamawa ya gyada musu Kai.

Kallon dabbar ya yi ya furta “ Alhamdulillah bayan wasu shekaru da muka shafe muna jiran wannan rana gashi yau Allah ya nuna mana Allah yasa hakan ya kawo karshen komai bayan wannan sadaukarwan”.
“Ameen suka “ suka furta,fito da wani wuka me matsagaiciyar tsayi sheikh Abu Dhabi ya yi a gidansa ya nufo dabbar domin gabatar da abinda ya kawo su.

“ Ku dakata Ina da abinda zan faɗa muku,ku a tunanin ku in ku ka yi sadaukarwa dani komai ze dede ta?ko kuna tunanin zubda jinina ze tsayar da munanan abubuwan da zasu faru? To abinda baku sani ba shine wannan din kaddarar Bayaan ne,babu wata hanya,babu wani mafita da ze sauya komai abinda ku ke tsoro dole se ya faru domin kuwa tun farko hakan na rubuce ne cikin kaddarar wannan masarauta babu wani abinda za ku iya fa ce ku koma gefe ku tsaya ku zama yan kallo. Ko ku sadaukar da ni ko kar ku sadaukar dani abinda ku ke gudu se ya faru. Ko ku ɗaura sarauniyar da ta cancanci kujerar ko ku ɗaura akansinta dole Munanan abubuwa sun faru babu Wanda ya isa ya canza hakan ba ni ba koda jinin mahaifiyata zaku zubar tofa hakan se ya faru,dole ne wannan munanan abubuwa se sun faru wannan shine gaskiyar da baku sani ba,amma inde ba ku yarda ba ku yi sadaukarwan muddin jinina ya kasance a ja to babu abinda ze faru amma daga zaran jini na ya kasance baki to babu wani mahalukin da ze iya ceton wannan masarautar daga mummunar alkaba’in da ze faru”. Tunda wannan dabbar suka yi shuru suna sauraransa alama mai girma Sheikhy ya yiwa sheikh Abu Dhabi,nufar dabbar ya yi ya kwantar dashi akan wannan farar kyallen ya yankasa nan take jini ya soma bulbulowa daga wuyarsa da aka yanka,kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya ganin jinin ja ne basu gama farin ciki ba jinin suka ga jinin a hankali ya fara sauya kala yana komawa baki-baki kafin su farga ya koma baki wuluk sosai hankalin su ya tashi ganin damar su na karshe da suka sa rai ze yi aiki be yi ba shima ya tashi a banza sun kwashe shekaru suna jiran rana irinta yau amma bukata be biya ba.

Sauke gwauron Numfashi mai girma sheikhy ya yi ya dubesu gaba daya yace “ A shirya daura sabuwar shugaba Gobe goben nan tun kafin wani abu ya faru,dole mu de na bata lokaci mu yi abinda ya dace bamuda wani zabi,kar a bar kowa yasan me ake shiryawa har se kowa ya hallara a filin nada sabuwar shugaba”.
Dam haka Galadima abdul aleem ya ji kirjinsa ya fadi yana tsoron kawo abinda ze raba kan wa’yannan yan biyu mash kaunar junan su.

Kallon sa da kyau mai girma sheikhy ya yi “ Kar ka bari fargaba ya yi tasiri akan ka”.
Jiki a sanyaye ya gyada mai Kai.
Buga sandar hannunsa ya yi nan take suka bace a cikin dajin suna bacewa gangan jikin wannan dabbar shima ya bace bat.

10:30Pm na safe suka farka basu gaji da baccin baccin ba yunwa ne ya tashe su,wanka Muzna ta fara yi da brush ta zauna gaban mirror tana shafa lotion,wanka itama Muzaina ta shiga tayi tafito tana kuma kwanciya akan gadon domin wani masifaffen bacci ne a wannan manyan idanun nata.

“My Muzaina kar fa ki sake komawa baccin nan ya isa haka nan “.

“ Ya Allah wallahi am still feeling sleepy,amma dole in koma bacci bayan na yi breakfast “.
Bude baki tayi zatayi magana suka ji muryar Jadwah na fadin “ Assalamu’alaikum “
“ Waalaykum Salam ya ke Jadwah sarkin mantuwa ni za ki cewa zaki daukowa ki manta?”Muzna ta fada tana dubanta ta mirror.
“ laaah na manta amma ki min afuwa da yardar ubangiji yau kam zan kawo miki bazan manta ba”.

Gyada mata Kai ta yi tana Tana kallon hannunta dake fansy trolley me kyau ta jawoshi.

“ Meye a cikin nan kuma?”

Daura trolley din akan kujera ta ce “ Kayan da za ku saka ne a ciki akwai taro da zaa gudanar yanzu”. Muzaina da tunda Jadwah ta shigo bata dago Kai ta kalleta ba ne ta dubi in da akwatin yake.

Langwabe kai Muzna tayi cike da gajiya da wa’yannan taro na su da baya karewa tace “ Wai ku wannan masarautar bakwa gajiya da taro-taro ne?,kai wallahi banason shiga dandazon mutane.”
Zama akan mirror Jadwah ta yi “ hakuri za ki yi tunda de nasan taron ba wani jimawa ze yi ba”.

Babu yanda ta iya haka suka shirya cikin tsadaddun Kayan sarautar da aka kawo musu iri daya suka tafi in da ake yin taron. In da suka samu dandazon mutane masu yawan gaske Wanda in zaa kiyasta a cikin Bayaan mutane kalilan ne basu zo ba suma se irin tsofoffi wa’yanda bazasu iya tafiya ba se yara da kuma marasa lafiya.

Zama suka yi a wajen zaman au dake saman minbari daga gefen masa kuma ta hango farin cikin ranta cikin shigarsa ta jarumai yana sakar mata sanyayyan murmushi.

Se da kowa ya nutsu tukuna Galadima Abdul aleem ya mike da kanshi domin dole shine ze isar da wannan sakon.
Sallama ya yi wa kowa irin na addinin musulunci suka amsa ya soma fadar abinda ke tafe dashi.

“ Nasan da yawan ku kun san akan dalilin da aka yi wannan taro domin idan ba ku manta ba taro na karshe da aka yi an sanar muku taro na gaba da zaa yi shine taron daura sabuwar sarauniya,to yau Allah ya nu na mana wannan rana me albarka da za a nada sabuwar shugaba akan wannan kujera bayan mutuwar Sarki Taifur Rahman “.

Kallon kallo aka soma yi wasu sun mika hankalinsu ga abinda yake fada yayinda wasu suke kuskus,kallon juna Muzna da Muzaina suka yi,lumshe mata ido Muzna tayi akan ta kwantar da hankali tare da runtse hannun ta cikin nata,ido suka had’a dashi ya sakar mata murmushi itama ta mayar mai a Karo na sau babu adadi. Kowa ya nutsu suna jiran ya ci gaba da bayaninsa,a yayinda da dama kuma kirjinsu yake dukan tara tara a ciki kuwa harda shi Galadima dake jawabin. Ummu Zaheenat se kallon fuskokin twins Muzna da Muzaina take yi tsoro na tsanantuwa a zuciyar ta.

Ci gaba da magana ya yi daga inda ya tsaya “ Kafin Allah ya dauki ran sarki Taifur ya bar mana wasika rubutacciya Wanda ya sanar mana cewa wannan sakon yana so a karanta sa a gaban kowa da kuma ranar da ya zamana zaa daura sabuwar Sarauniya,to da yardar ubangiji a yau zamu isar da wannan sako da ya bari.

Wasikar ya kasance kamar haka!!!!” Ya fada yana bude wani littafi da aka yi rubutu da ruwan tawada.

“ SUNANA TAIFUR RAHMAN SARKI NA TAKWAS A WANNAN KARNIN,A WANNAN DUNIYAR KOMAI YA ZAMA ABUN TSORO DA RUDARWA,DUK WANDA YAKE SO YA CIMMA NASARA A RAYUWARSA SE YA SAKA HAKURI A KOMAI NASA DA TAWAKKALI ,DUK TSANANI YANA TARE DA CIKAR BURI A DUK INDA KA SHIGA WANI HALI TO KA SANI ALLAH YANA TARE DA KAI KAR KA BARI WUYA YASA KA KARAYA.
NASAN A LOKACIN DA ZAKU ISKE WANNAN SAKO NAWA BABU NI A DORON DUNIYA. DALILINA NA ƁATA LOKACI NA YI DOGON JAWABI HAKA SHINE AKAN ƳAƳANA GUDA BIYU?MUZNA DA MUZAINA?YARANA INA MATUKAR KAUNAR KU NA SO IN KASANCE TARE DA KU HAR ABADA AMMA SE DE HAKAN BA ME YU WA BANE DOMIN NIMA BAN ƘARE RAYUWATA DA IYAYENA BA SUN TAFI SUN BAR NI,KU KASANCE MASU HAKURI DA SON JUNAN KU DAN ALLAH KAR KU YARDA WANI ABU YA SHIGA TSAKANIN KU.
KAMAR YANDA KU KA SANI TUN ZAMANIN IYAYEN MU YANDA AKE ZAƁAN SHUGABAN DA YA CANCANTA SHINE TA WA'YANNAN HANYOYI NA FARKO TA HANYAR GANE WANENE ME TAUSAYI DA SAUKIN KAI DA KUWA SANIN DARAJAN DAN ADAM,NA BIYU TA HANYAR TURA RUHIN WA'YANDA AKE SON DAURAWA AKAN MULKI IZUWA DAJIN KADUR GURIN DODO GARTAMUS DA MACIJIYA MARKUSA DUK WANDA YAKE DA HANYAR SAMAR DA SULHU A TSAKANIN SA DA WAYANCAN HALITTUN TO TABBAS ZE IYA KAWO ZAMAN LAFIYA A DUK INDA YA TSINCI KANSA TO TABBAS YA CANCANCI KUJERAR BAYAAN. SE KUMA ABU NA KARSHE SHINE YIN GWAJI TA HANYAR AMFANI DA TAKOBIN BAAAR SHINE WANDA ZE ZAƁI WANDA ZE HAU KAN WANNAN KUJERA BAYAN CIKE DUKA KA'IDA. WANNAN SHINE ABINDA ZAN FAƊA.
ƳAƳANA INA ME NEMAN ALFARMA A GARE KU BAYAN JIN WACCE TA CANCANTA KAR KUJI HAUSHIN JUNA,KAR HAKAN YA KAWO RASHIN FAHIMTA A CIKIN ALAKARKU. KU YI RAYUWA CIKIN FARIN CIKI SHINE BURINA A KULLUM.

SAKO DAGA
SARKI TAIFUR RAHMAN".

Sosai wannan wasika na sarki Taifur Rahman ya taba musu zuciyoyinsu har seda yasa wasu daga ciki hawaye.

Bayan Galadima ya gama karanta musu wasikar ya kalli sheikh Abu Dhabi tare da sanar musu yanzu zaa karasa sauran gwajii daya da ya rage. Ya koma ya zauna.

Daga inda sheikh Abu Dhabi yake zaune ya soma wasu kalasmai na maganganu Wanda shi kadai yasan me yake fadi,cikin daga murya ya furta “Tokobin Baaar “.

Cak ya faɗo kasa ya caku a tsakiyar minbarin da suke zaune. Wani takobi (wuka) ne me girma da kyau wanda ya kasance na zinari se daukan ido yake jikinsa duk rubutu rubutu.
Kowa zubawa wannan takobi ido ya yi yana kallo da kuma son kallon me ze faru.

Rubutu-rubutun dake jikinsa ne ya soma fitar da hasken wuta me launuka daban-daban wanda se da aka dauki tsawon good five minutes kafin ya dakata yana fitar da wani kamshi me sanyin gaske.

Mikewa ya yi yana dogara sandar sa ya nufi inda takobin yake ya sunkuya yana leka wa’yannan rubutun da yake jiki bayan ya ga sunan wacce yake jiki ne ya taso yana sakin murmushi.

“ A YAU BAYAAN TA SHAIDA ƊAURA SABUWAR SHUGABA,WACCE TA SAMU SANYA ALBARKA DAGA KO WANI BANGARE BA KOWA BACE FACE GIMBIYA MUZNA WACCE YANZU TA KOMA SARAUNIYA MUZNA.”

dak!dak!dak haka zuciyoyin Muzna da Muzaina yake bugawa a tare a bisa Jin wannan sakamakon da aka fada,a hankali Muzaina ta zame hannunta dake cikin na Muzna sannan kafe sheikh Abu Dhabi da ido tana son karyata abinda ya fada amma kunnuwanta se sake tariyo mata abinda ya fada yake. Duk wasu abubuwan da aka tattaunawa bata fahimci komai ba komai tsaya mata ya yi lokaci daya Jin an daura Muzna a matsayin sarauniyar Bayaan ba ita ba hakan ya matukar karya mata zuciya.

A hankali ta mayar da kallon ta kan Muzna tana mata kallon kinci amanata,girgiza mata Kai kawai Muzna take yi hawaye na zuba a idonta,bata taba kawo ko tunanin faruwar haka ba tasan yanda Muzaina ke son Mulki hakan yasa ko da yaushe take mata addua Allah ya cika mata burinta.

Wani irin kallo me wuyar fassaruwa take binta dashi idanunta na zubar da hawaye murya a raunane ta furta “ why Muzna meyasa za ki dauke min farin cikina da mafarki na?”

Tana girgiza mata Kai ta ce “ Believe me Muzaina ban yi komai ba , ban San komai ba amma ki yarda dani wannan kujerar dole ya koma hannun ki.”ta yi maganar tana ruko hannun Muzaina da wani expression ta ce “ Ki daga hannun ki akan nawa “.

“ Please Muzaina ki yarda dani ban san komai ba ki tambayi Abu Aleem da sheikh bansan komai akan haka ba”. Fincike hannunta ta yi daga na ta mike tsaye tana share hawayen fuskarta “ Karya ki ke yi kin san da cewa wannan shine mafarkina shine ki ka rabani dashi meyasa za ki ha’inci yar Uwar ki ta jini Muzna? Dama ke ma akwai son mulkin aran ki shine ba ki taba sanar dani ba ?ki kalla yanda yau ki ka yi sanadiyar zubar hawayena Akan abinda nan fifita komai akan sa,kalla ki gani hawaye fa nake yi Muzna and you’re responsible for it “ yanda take magana kamar zautacciya ya isa ya tabbatarwa da mutum soyayyar da takeyi wa kujerar Bayaan ba karama bace jikinta se rawa yake yi tsabar tashin hankali.

Cikin kuka Muzna ta mike tana girgiza mata Kai hade da tausayin halin da yar uwarta ta shiga ta nufota tana rike ta “ ki yi hakuri banida sa hannu akan abinda ya faru yar uwata kar ki min mummunar fahimta sun yi rashin fahimta Ɗaya cikin biyu wa za su daura hakan yasa mistakely suka kira sunana amma ke ce nan ki ka cancanta.”hankadeta ta yi a jikinta ta yi tangal-tangal zata fadi cikin zafin nama Sadauki Zubair ya isa wajen ya riko ta.


Saboda kurewar lokaci wani gurin baby editing

Babu bukatar in bata bakina wajen ce muku yanzu ne littafi ya ɗau zafi,wannan labarin kar ku bari a ɗinga baku labarin sa.


ƊAYA CIKIN BIYU
KU KASANCE DANI DAN JIN YA ZA TA KQ YA.

don't forget to comment,like and share fisabilillah ❤️😍👍

Allah yasa muyi kyakyawar karshe.
https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207



⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩





❤️🔥Page 19

No editing


Wannan shine babban abinda kowa yake gudu da kuma tsoro, ga shi kuma ya faru ganin yanda Muzaina ta mayar da komai kan Muzna a tunaninta ta sace mata farin cikin ta,.
Jikin kowa se da ya yi masifar sanyi ganin lokaci daya kalma daya ya ruguza alakar shekara ashirin ,amma dan farantawa daya bazasu dau hatsarin ruguza masarautar ba,wannan shine iya kacin mafitar da suke dashi dole ne daya ta rungumi kaddara da hakuri. bakomai ne mutum yake nema a wannan rayuwar ya samu ba duk abinda ka ga ka samu rabon ka ne ya rantse akai. Al‘ummar Bayaan sun maida hankali izuwa kan su suna ganin abinda yake faruwa,mikewa ya yi ya isa inda Muzaina take tsaye cikin son fahimtar da ita da kuma rarrashinta ya rike ta

“ Muzaina kiyi hakuri ki bi komai a sannu duk abinda ka ga ba ka samesa ba alkairi bane a gareka. kar wannan abun ya samu gurbi a zuciyarki,ba mu yi haka dan mu bata wa kowa rai ba,ba mu ne muka zaɓi Muzna ba, haka zalika bata san komai ba kar ki riƙe yar uwar ki a zuciya ke musulma ce kuma duk musulmi ana so ya kasance me yarda da hukuncin ubangiji kin ji ko ƴata?”ya faɗa yana shafa kanta,

“Abu Aleem please ku sake dubawa am hundred percent sure ni ce nafi cancantar wannan kujera tun Ina karama nake son Bayaan har na girma,kowa ya san da haka daga Aba,Ummi da ku gaba daya dan Allah na rokeku kar ku ruguza min mafarki na” Karo na farko da ta yi masa magana nicely.
“ Kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki mu koma palace kin ga yanzu kowa hankalin sa na kan mu “.
“ hankalina baze taɓa kwanciya ba har se an bani abinda ya kasance mallakina,wannan rashin adalci ne Abu Aleem dan meyasa zaku yi haka,a ko da yaushe zuciya na yana samun nutsuwa ne da tunanin nice nan Sarauniyar Bayaan amma kun rusa komai.”
Ta yi maganar tana kuka ,sake Galadima Abdul aleem ta yi ta nufi wajen sheikh Abu Dhabi ta dinga rokonsa sede a bata kujerar Bayaan bayani ya mata dalla-dalla Irin masifar da za'a shiga in harɗe wanda ba shine zaɓabɓen shugaba ba ya hau kujerar amma sam ta gaza fahimtar su balle ta yarda,duk wani masu manyan mukami a Bayaan se da ta bi su one by one tana rokonsu amma sede su bata hakuri tayi matukar basu tausayi sede they can’t risk people’s life just to make her happy.

Muzna da tunda Sadauki Zubair ya riƙe ta take kuka duba da yanda lokaci daya Muzaina ta ɗaura mata laifin komai.
Cike da tausayin halin da masoyiyarsa ta shiga na rashin samun abinda take so yasa ya ji kamar ya rungumeta ya rarrasheta.
Miƙewa ya yi yaje gareta dan baze jure ganin tana kuka ba. ya riƙo duka hannunta biyu yana mata magana a kunne kan cewar ta kwantar da hankalinta komai ze dedeta cikin sanyayyar murya ta ce “Farasat me na yi na rashin dacewa da za'a min haka? ,na tare musu wani abu ne da suka min haka ko kuma banida qualities din da ake bukata ne?”ta jero masa tambayoyi lokaci guda. gaba daya kan sa ma ya kulle ya rasa me ze ce mata. Cire hannunsa a nata tayi ta nufi takobin Baaar ta tsaya tana kallon sa kafin ta saki murmushi me ciwo “ Wannan shine takobin da ya yi rejecting dina ko?shima bazan barsa ba “ tayi maganar tana buga kan takobin da iya karfinta nan take takobin ya nitse cikin karkashin ƙasa. Girgiza kai kawai sheikh Abu Dhabi ya yi ya buɗe baki ze yi magana ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu sannan ta soma magana cikin tsananin fushi.

“Dukkanin ku kun haɗu kun ci amanata.bazan taɓa barin hakan ya tafi a banza ba.and you".ta juya gurin Muzna ta nu na ta da yatsa
" I hate you Muzna,da a ce ni kadai nazo wannan duniyar da babu yanda su ka iya dole su bani abinda ya kasance mallakina,amma sanadiyar ki komai ya lalace i hate you Muzna.” Ta karashe maganar tana barin minbarin da gudu ko waiwaiyan bayanta bata yi ba. da sauri yarima Farasat ya rufa mata baya haka su Ummu Zaheenat duk bin bayansu suka yi.
Sake Sadauki zubair ta yi tana me bin bayan Muzaina cikin sauri da tsoron kar ta cutar da kanta.
Tana shiga part din ta dakinta ta shige direct ta murza key, tare da zama a bakin kofar ta haɗe kanta da guiwa ta fashe da kuka me taɓa zuciya.
Kwankwasa dakin suke yi suna tsaye bakin kofar haɗe da rokonta ta buɗe amma ko motsinta basu ji ba.
Kwankwasa kofar Muzna da isowarta kenan ta fara yi tana rokonta ta bude amma babu response.
A can kuwa Galadima Abdul aleem ya sallami kowa shima ya bi bayan su zuwa part din Muzaina da har yanzu bata motsa a inda take ba.

“Har yanzu ba ta buɗe ba?”ya tambaya yana ɗaga Muzna dake durkushe a kasa tana kuka. zaunar da ita ya yi akan kujera yasa aka kawo mata ruwa sede ta gagara sha.

“Abu Aleem dan Allah ku yi wa Muzaina bayani banida sani akan wannan lamarin ku ce mata ta dena jin haushi na “ “kiyi hakuri bata fahimta bane amma zan Mata bayani.”
Haka suka zauna gaba daya afalon na ta har lokacin sallah azhar nan ne suka tafi domin gabatar da sallah ko da suka idar waziri Abdul Qadeer ya hanasu komawa a cewar sa su barta ta sauko yanzu tana cikin tsananin fushi bazata saurari kowa ba.
Ranar haka suka yini har dare kowa jikinsa a mace kuma har time din kofarta a rufe Muzna sau uku tana zuwa ko za ta tarar ta buɗe amma ah ah ko alamar an buɗe ma babu.

Tunda ta shigo dakin tasha kukanta ta koshi ta cire kayan jikinta masu nauyi ta jingina kanta a jikin gadon tana kukan zuci duk wani bugawar da suke yi tana jinsu kawai bazata iya buɗewa bane, domin a halin yanzu ta tsanesu gaba daya ko fuskar mutum daya bata kaunar gani saboda a ganin ta sun ci amanarta,haka ta kasance zaune guri daya har dare tana tunanin wani irin hukunci za ta yanke

Please Login or Register in order to submit comment