Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

trust in me “.

Haka suka zauna cikin yanayi na rashin jin dadi ko kad’an abinda ya faru be musu dadi ba.

Abinda ya faru shine,lokacin da yarima Ishaq ya ji me suke tattaunawa nan ya koma bangarensa anan ya kira dan leken asirinsa ya faɗa masa duk abinda yake so ayi,shi kuma ya sa wannan saurayin ya mata karyan cewa Sadauki Zubair baya nan.

Haka ta wuni sukuku da ita tana idar da sallah mangriba ta saka bakar abaya tare da yin rolling din veil ta daura niqaf ta sulale ta bar palace batare da kowa ya gane ita bace.
Direct gidan Yumma ta nufa tasan yana gida tunda yanzu dare ya soma yi,duk da zuciyarta na mata ɗari-ɗari tashiga gidan bakinta da sallama. Abakin madafa ta samu Yumma na kwashe abinci a kula tana ganin ta tasaki murmushi tana fain

“ lale da kyakyawar surkata “. Ta mata magana as usual hakan ya tabbatarwa Muzna be sanar da ita ba.
Zuwa ta yi ta rungume Yumma haɗe da sumbatar kumatun ta
“ barka da wannan dare ya Yumma “.
“ shin kina lafiya ƴata ?”. “ alhmdllh “.

Cikin son hira irin na Yumma domin ba ta san abinda ya faru ba,ta ce
“ yau Zubair bakin hali yake ji dashi,tunda ya dawo ya ƙi yin magana ya shige daki be kuma fitowa ba”.

“ Bari in sa me sa”. ta faɗa tana nufan dakin na sa da yau shine rana na farko da zata soma shiga,cikin madedeciyar dakin sa dake ɗauke da Katifa a ɗasa se akwatin Kayansa se wata kujera one sitter.
Yana zaune a kan kujera yana karanta wani littafi.
A hankali ta isa inda yake ta tsaya daga gefensa

“ masoyi….” ta Kira sa,shuru ya mata bece komai ba.

Ɗaura hannunta tayi bisa nasa hakan da tayi be sa ya ɗago Kai ya kalleta ba kuma be mata magana ba.

“ Masoyi nasan ni me laifi ce a gareka,amma soyayyar da nake maka ne yasa na gaza faɗa maka Gaskiya. Masoyi ban taɓa yiwa wani mahalukin haka ba ni ba maciya amana bace ka yafe min”.

Kamar Wanda take magana da gungumen itace ko kuma dutse haka ya shareta.

Ganin be kulata bane yasa ta soma hawaye haɗe da soma kuka me sauti tana tsaye akan sa.

“ Masoyiiiiiiiii”. Ta fada tana jan sunan,
Ka yi hakuri dan Allah nasan ni me laifi ce amma ba da niya nayiii”.

“ Ki rufe min baki,har ni za ki kalli idona kice min ba da niya ki ka yi ba”
Tsawan da ya daka mata ne yasa se da ta ji hantar cikinta ya kaɗa tayi saurin jan baya ganin ya miƙe.

Nuna ta da yatsa yay calmly ya furta “ Dan Allah cikin girmamawa ki fice mana a gida kar ki ja min abinda bazan iya ba na roke ki yar sarki Muzna Taifur Rahman”.

“ Masoyi dan Allah ka…” katseta ya yi ta hanyar fadin
“ please ki tafi gimbiya ni bawa ne agare ki Ina rayuwata ne dede matsayina,tun Ina ganin girman ki ki tafi”.

“ Masoyi dan Allah ka dena fadin haka,ko ka manta soyayyar dake tsakaninmu “. Ta faɗa murya a sanyaye sosai.

“ babu wata alakar fili ko ta boye a tsakani na da ƴar sarkin mu,..komai ya ƙare “.

Share hawayen idonta ta yi ta matso kusa dashi idonta bisa kan fuskarsa ta ce “ Haka kace?,Masoyi wannan abunda ya faru be isa ya rabani dakai ba.ni na ce ina sanka dan haka ko me ze faru se mun yi aure””.
Murmushin takaici ya yi cike da takaici ya nu na mata hanya alamar ta fice masa da gani.

Kin motsawa ta yi tana tsaye ki kam.

“” ki tafi kar ki sa ke nuna min wannan maciya amanar fuskar ta ki”.

“ zan tafi amma ka sa ni kai din nawa ne”. Kamar za ta tashi sama ta fice a dakin nasa tsabar yanda idonta ya rufe ko Yumma dake a bakin kofa bata gani ba tasa kai.

Yumma da ta gama jin komai ne jikinta ya yi sanyi dama tun kallo daya da tayiwa Muzna bata mata yanayi da baiwa ba ko kad’an.
Shiga dakin nasa ta yi ta samesa a inda Muzna ta barsa tsaye .

Riƙo hannunsa ta yi suka zauna akan katifarsa.

“ Zubair na ji duk abinda ya faru,nasan Muzna ta maka karya akan gaskiyarta,bakomai ne ya jawo haka ba fa ce son da take maka.ka yafe mata “.

Furzar da iska me zafi ya yi yana dafe goshin sa.

“ Yumma Muzna ta karyamin zuciya babban abinda nake gudu kenan shisa se da na mata tambayoyi amma duk da haka ta zaɓi ta min karya,Yumma kin sani ina iya kokarina na ganin na kare mana martaban mu bana taɓa lamuntar duk wani abu da ze jawo mana zubewar kimar mu.dalilin haka yasa bana taɓa Kai kaina inda Allah be Kai ni ba”.

Cike da tausayin ɗan nata ta sauke ajiyar zuciya ta ce “ mun kasance bayi kuma masu yiwa wannan masarauta hidima.bazamu taba yin wani abu na jan magana ba. Yanzu a madadinta Ina me baka hakuri da ka yafe mata sannan ka nisanta kan ka da duk wani abinda ya shafeta babu Kai babu ita.domin ita din ba sa’ar mu bace ba,ka ji ko!?”.

Gyada mata Kai yai alamar eh ya ji.

Tunda ta fito daga gidan Yumma ta shigo palace zuciyarta ke mata zugi musamman in tana tuna yanda suka yi ita da Sadauki zubair,kokarin shiga falonta take ta ji sauki muryarta

“ Wait a minute Muzna”
Kallon direction din da take tayi ta ganta tsaye fuskar nan kamar ko yaushe babu fara’a.
Cak ta tsaya,tana kallon Muzaina dake dunfarota. se da ta iso gabanta tasa yatsarta guda daya ta lakato hawayen dake kan fuskar ta ta kalla kana ta ce

“ Me ki ke kokarin aikatawa Muzna !?”. Ta tambayeta tana tsareta da ido

“ Bangane”.

Langwabar da Kai gefe tayi tana bin fuskarta da kallo “ na ga kin shiryane tsaf na zubar mana da mutunci,menene hadin ki da wancan kaskantaccen!?”.

Sunan da ta Kira Sadauki zubair dashi ya sosa mata rai matuka hakan yasa ta tsuke fuska haɗe da faɗn
“ Muzaina stop it”.

“ you knew what am saying is the truth,kina royal blood gaba da baya bazaki nemi kalar ki ba ?. Meyasa kaf cikin mazan duniya idon ki ya rasa Wanda ze hasko miki se wannan uncomplete human being din”.

“ cin mutuncin ya isa haka,if you don’t like him that’s your opinion.so ni ya min “. Ta fada tana tafiya dan ta lura in ta biyewa Muzaina za ta ƙara mata bacin rai ne.

“ shikenan ko me za ki faɗa ki faɗa amma ba za ki taɓa auren sa ba. Domin babu yanda za a yi in yarda ki kawo mana wannan abun cikin ahali”.

Murmushi kawai tayi ta sa Kai yanda take jinta rai a bace bazata iya biyewa Muzaina ba,hakan yasa taa shige falo ta barta tsaye.lokaci ta duba ta ga har an idar da sallah isha I,hakan yasa ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah bayan ta idar ne tana zaune akan sallayar se tunani yake zuwa mata iri iri,shin ya su galadima Abdul aleem za su karɓi lamarin?,sune irin abinda ke mata yawo aka.amma tasan duk abinda ze faru se ta auri Sadauki Zubair domin bayan rashin iyayensu shine mutum na biyu dake iya kokarinasa ganin yasata farin ciki.

“ nasan da yau Ummi ko Aba wani na raye da hankalinsu baze taba kwanciya ba se sun cika min muradina “. Ta faɗa a zuciyarta tana lumshe idanu slowly,ita fa gaba daya masarautar ya fice mata arai so take ta koma Russia ta ci gaba da harkokinta da ta saba,ta tsani takura da matsi she wants to live her own lifestyle batare da abubuwan sarautar nan ba.

Ko da aka tura a kirata tazo taci abinci bata samu fitowa ba a Cewarta bata Jin yunwa seda suka gama ne ummu Zaheenat ta zo da kanta take tambayarta me ya faru domin kuwa bata San abinda yake faruwa ba.
Bata boye mata komai ba ta faytace mata abinda ke faruwa sosai ta ji mata ba dadi na rashin fahimtarta da Sadauki zubair beyi ba tare da Kara mata kwarin guiwa kan in sha Allah komai ze dedeta.

Bata kyaleta ba se da ta bata abinci da kanta ta ci sannan ta tafi,kwanciya ta yi tana addua dan yau ranta babu dadi ba abinda za ta tsaya yi.

Karfe daya ta farka ta gabatar da nafilfilu haɗe da yi wa iyayensu addua.ba ita ta samu komawa bacci ba se karfe uku da rabi ta koma.

Karfe goma na safe tana bacci ta ji hayaniya ya ki ci yaki cinyewa surutunsu duk ya addabeta ga shi bawai baccin ya ishe ta bane.ɗan buɗe idonta kad’an tai ta kalle su suna zazzaune akan gadonta Suna hira.. ɗan tsaki ta ja aranta ta kuma juya kanta.

Duk abinda suke yi tana Jin su sam sun hanata komawa bacci.,

“ ya hayyu ya qayyum. Yanzu dan Allah ba za ku barni in yi bacci cikin Salama ba!?”.

“ To ki tashi ki yi breakfast kin san karfe nawa ne kuwa?”. Cewar Jadwah

Kallon agogo tayi ta ga pass 10:00Am lalle tasha bacci sosai saboda tunda tayi sallah asuba ta koma bacci.
Sauka ta yi akan gadon ta nufi toilet tayi wanka haɗe da brush ko da ta fito ta samu an shirya mata breakfast dinta shiryawa tayi sannan ta ci abinci.



ENGLAND


KINGDOM OF WISDOM


Tana zaune a tsakiyar gadonta hannunta na riƙe da wayarta tana cikin instagram tana kallon posting na mutane wani dogon tsaki taja lokacin da ta ci Karo da hoton sa a shafinsa na IG kyakyawa ne sosai yana sanye da farin Cout hannunsa riƙe da bakar Gucci bag fuskarsa manne da glass wuyansa na sanye da wani sarkan diamond dake da design din cross.

“ Mtssw shi nan yana ganin wani kyakyawa ne shi aikin banza”. ta faɗa cike da kin sa aranta.

( princess Gabriel are you okay kuwa wannan handsome guy din ne za ki kalle sa ki ce masa mummuna 😂😂😂😂😂).

Scrolling down ta yi kafin kuma tayi wurgi da wayar saboda kallon sa kadai da tayi spoiled her mood completely.

Tura baki tayi tana fadin “ ban ma San dalilin da yasa na hau IG ba”. Ta faɗa tana sauka daga kan gadon jikinta iyakacin mini skirt ne se yar riga tasa headband akan ta. Fitowa ta yi daga part din ta tana tafiyarta kamar yacce ta saba,daga nesa ta hango sa hakan yasa ta ihun murna ta nufosa da gudu tana faɗin

“ Oyoyo my uncle Joseph “.
Dariya ya yi “ oyoyo my princess Fatan kina lafiya”.

“ lafiya ta kalau nake”.
“ haka nake so. Rayuwarki za ta yi albarka da sahalewar uwa marry. Na zo miki da tsaraba sosai ki je gurin antynki Jennifer ki karba “.

Tsalle ta yi ta sake sa cike da murna ta ruga da gudu domin zuwa wajen Anty Jennifer da ta kasance Matar uncle Joseph.har ta yi nisa ta waigo haɗe da faɗin

“ Ina sanka sosai uncle Joseph “.

Cikin farin ciki ya ce mata shima haka,nufar part din nasu tayi taname Jin dadin dawuwarsu daga Jerusalem.tana matukar kaunar uncle din nata da ya kasance kani ne a gurin Queen Jessica,Musamman yanda yake nuna mata soyayya zallar sa ko yayansa baya nunawa.

A bangaren uncle Joseph kuwa tana bacewa ganinsa wannan murmushin fuskarsa ya gushe lokaci daya yana bin bayanta da kallon tsana.

“ Makirar yarinya kin kusa barin wannan masarautar domin ni ne nan magajin wannan masarauta “.


PRESIDENT HOUSE

“ Jay ka dena sa min ciwon kai ka dawo gida domin lokacin baikon ka da Princess Gabriel ya karato.ku samu fatimtar juna shine burin mu,da yardar almasihu wata na gaba a yi auren ku “.
President David dake waya da ɗan sa ya faɗa cikin lallami domin yasan inde dole yace ze yiwa Jayson to fa yasan baze dawo nan kusa ba.

Shuru yayi yana sauraran abinda Jay din yake fada.murmushi ya yi ganin ya samo ta yanda ze bullowa Jay.

Katrina dake zaune tana jin su ne ta yi dariya sannan ta amshi wayar a hannunsa sosai suka yi waya da ita da Jay kafin ya kashe.




MASARAUTAR BAYAAN


Muzna na zaune a garden tana shan fruit gefe guda kuma Aliyah ce ke chatting duk kansu suna sanye da Kayan sarauta a jikinsu me masifar kyau.

Jadwah kamar wacce aka wurgo ta garden din ne ta shigo dasauri suka kalle ta.
“ Jadwah lafiya kuwa irin wannan faɗowa haka?”.
Aliyah ta tambayeta

“ Muzna you can’t believe what your sister have done “.

Jin ta ambato Muzaina ne yasa suka sake karkata hankalinsu akanta.

“ wallahi ban taɓa tunanin Muzaina za ta aikata haka ba,. gidan mahaifiyar Sadauki Zubair taje ta mata warning kan cewa tajawa ɗanta kunne ya dena kula ki,shin hakan da tayi ta kyauta fisabilillah?”.

“ What!?????” Muzna ta faɗa da karfi tana miƙewa tsaye.

“ Muzaina ce ta aikata hakan?,ita Ina ruwanta da zata je gurin Yumma”. Ta fada rai a bace.daukar wayarta tayi ta fice a garden din su ma suka rufa mata baya.

Yana cikin warriors chamber aka zo aka faɗa masa abinda ya faru tunda ya ji haka yasan Muzaina ce domin Muzna ko a mafarki bazata aikata haka ba.

Rai a matukar bace ya bar wajen direct lambun da aka sanar masa Muzaina na shan iska ya nufa luckily ya same ta tana akan tattausan carpet bayi na danna mata kafa ita kuma laptop na kan cinyarta.

Yana isa batare da fargaba ko kuma tsoron abinda ze je ya dawo ba ya sa hannu ya fisgota tsaye seda ta kusa faɗowa jikinsa dayan hannun sa yay amfani dashi wajen ɗauketa da kyawawan mari lafiyayyu guda biyu left and right. Marin da ya mata ya yi dede da isowar su Muzna da yarima Farasat lambun wanda duk se da suka ji marin tamkar a kuncinsu,rintse ido Muzna tayi Muzaina aka mara amma ita ce ta ji zafin.

Ita kuwa Muzaina dafe kuncinta tayi cikin radadin abinda ya mata agaban mutane wannan abu ya soya mata rai ko zafin marin be dameta ba kamar Marin da ya mata a bainan nasi.

A fusace yarima Farasat ya daka masa tsawa “ how dare slapped your princess “.

Juyawa ya yi garesa ya wurga masa muguwar kallo da lion eyes din sa,se da gaba daya suka sha jinin jikinsu. Maida kallon sa yay kanta ya nuna ta da yatsa

“ Wannan kad’an daga cikin abinda zan iya aikata miki akan mahaifiyata kenan,gigin hauka ya sake ɗibanki ki ka nufi inda gidan mu yake wallahi nayi rantsuwa da mahaliccina abinda zan miki babu Wanda ze ji dadin sa,.dubeki tambadaddiyya mara kamun kai,.ke kowa kin mayar dashi abin wulakantawa bayan kece nan wulakantacciya,ke a ganin ki abinda ki ke yi burgewa ne?,to jahilci ne domin babu wanda ze ringa wulakanta dan adam da ya wuce jahili sam bakiyo halin Sarkin sarakuna me adalci ba balle sarauniyar mu,kin san da cewa Muzna ta fi ki komai?,to in ba ki saniba yau bari in faɗa miki yar uwar ki ta fi ki hali me kyau,ta fi ki sanin darajan dan adam ta fi ki zuciya me kyau,komai ta fiki.ke kawai hoton fuskarta ne amma you’re nothing compared to her,in kina gadara da wannan matsayin da ki ke tunani za ki samu to bari kiji da wannan bakin halin naki babu wanda ze kaunace ki”.

Wayannan kalaman Sadauki Zubair duk kalma daya Muzaina ji take tamkar yana zuba mata narkekken dalma a zuciyarta ne,wasu zafafan hawaye ne ke bin kuncinta wannan shine bakar rana a gareta Wanda ba kowan kowa ba shine ya tsaya a gabanta yana kallon cikin kwayar idanuwanta yake faɗa mata wa’yannan kalaman.

Ba yarima Farasat ba,ba su Muzna,bayinta gaba daya they were shocked jin bakaken maganganun da Sadauki zubair ya faɗa mata. Yau sun ga bacin rai da fushin gwarzon namiji shi kansa yarima Farasat dake namiji ɗan uwansa be isa yace ze tunkaresa ba domin duk inda ake neman cikekken Jarumi tofa Sadauki zubair ya Kai har ya wuce.

“ Ma…masoyi”.Muzna ta kirasa muryarta na shaking,hannun ya daga mata.

“ se kuma ke daga yau ki gaggauta cire ni a rayuwar ki”.

Kallon fuskar Muzaina dake tsaye tsam kamar gunki hawayene kawai ke zuba a idonta,Rabawa yayi ta gefen su ze wuce ya tsinkayo muryarta

“ Tunda nazo wannan duniyar babu mahalukin da ya taɓa ɗaura hannunsa a jikina da sunan duka se Kai,ban taɓa zubar da dede da digon hawayena ba.amma yau ka ci min mutunci a gaban duniya. Nayi rantsuwa da ubangijin da nake bautawa se na wulakanta rayuwarka.se na jefa rayuwarka a taskon kunci se na kaskantar dakai. Se kuma alkawari na karshe kai da Muzna bazaku taɓa zama a inuwa daya da sunan maaurata ba in ban yi haka ba ni ba halastacciyar jinin Taifur Rahman bace”.

Tsaki ya ja tare da gyada mata kai yana kallon fuskar Muzna da itama hawayen take yi,wasu dagarai ne kusan su goma suka shigo.

Cikin girmamawa suka isar musu da sakon cewa Galadima Abdul aleem yana bukatar su gaba daya a fada domin daya daga cikin masu yiwa Muzaina hidima ta sulale ta je ta sanar da amintacciyar baiwa shine ita kuma ta samu Galadima Abdul aleem ta sanar masa hakan yasa ya neme su gaba dayan su.



Galadima Abdul aleem,waziri Abdul Qadeer. Se su yarima Haysam.da sauran manyan fada su suka tarar a cikin fadan.

Galadima Abdul aleem na daga kujerarsa ya soma magana

“ Na ji duk abinda ya faru,kuma dukkanin ku kowa na da nasa laifi ke Muzna Bari in fara ta kan ki,kin san dacewa ke yar sarki ce shine ki ka je ku ka fara soyayya a sirrance ke da Zubair kuma hakan be miki ba se da ki ka ƙara da boye masa ke din wacece. kin karya masa zuciya kuma kin ha’ince sa.da ya faɗa soyayya dake yana tunanin duk matsayin ku daya a wannan masarautar kawai kwatsam ya gano ke din ba baiwa bace kamar yanda ki ka mai karya shin kin yi wa kan ki adalci da kuma shi!??” Ya tambayeta yana kallonta,sunkuyar da kanta ƙasa tayi saboda Jin kunya domin ita kan ta ba se an tsaya faɗa mata ba tasan ba ta kyautawa Saduaki Zubair ba.
Shurun da ta yi ne yasa Ya jinjina kai ya mayar da kallon sa kan Muzaina ya dora da cewa

“ Ke kuma Muzaina wanene ya yarje miki da ki taka kafarki izuwa muhallin su ki ka ci wa mahaifiyarsa mutunci,a dalili dame za ki aikata haka,wannan dattijuwa ta haifeki amma saboda rashin na ido irin naki har ki ka iya kallon cikin kwayar idon ta ki ka mata rashin kunya,shin in wani ya yi wa ta ki mahaifiyar haka ya za ki ji a zuciyar ki!??”.

Kawar da kanta gefe tayi kamar ba da ita ake magana ba. Girgiza Kai kawai yay ya koma kan Sadauki zubair

“ A madadin abinda gimbiya Muzaina ta aikata nida fada muna baka hakuri da mahaifiyar ka.tabbas babu dan da ze ji dadin ganin an ci mutuncin wacce tayo sanadiyar zuwan sa duniya.na fahimce fushin ka sede kaima ka aikata laifi. Domin kana da damar da zaka kawo karar abinda ta je tayi saboda abi muku hakkinku amma zuciya da fushi ya rufe maka ido ka daura hannunka a jikin gimbiyar ka,a wannan kaci bashin bayar da hakuri a fada.zaka bawa fada hakuri”.

Kallon Muzna Sadauki Zubair yay yaga itama shi take kallo ya tako izuwa tsakiyar fadar cike da girmamawa ya furta

“ Nasan na yi kuskure Ina me bayar da hakuri game da abinda ya faru”.

Murmushi manyan fada suka yi tare da sake yaba hankalinsa da biyayya da ya nuna.


“ Muzna dan uwanki yarima Ishaq ya nu na sha’awar sa na son auren ki a saboda yana San ki,shin kin amince da neman auren ki da ya yi?”.cewar galadima.

Kamar saukar aradu haka ta ji maganar Galadima abdul aleem a kunnenta a zabure ta ɗago kai ta kai dubanta izuwa kujerar da yarima Ishaq yake da zama taga shima ita yake kallo a domin jin amsar da za ta bayar.

Ɗauke kallonta akan sa tayi ta mayar da dubanta kan Sadauki Zubair taga ko kallonta be yi ba kamar ma baya cikin fadar ake maganar.

Shuru fada ya ɗauka kowa ya zubawa Muzna da tayi shuru ido ana son jin amsarta amma ta yi shuru bata ce komai ba se ma kallon Sadauki da take yi.

Katse shurun ta yi ta hanyar faɗin “ Ban amince ba domin Ina da nawa zabin,kuma bana tunanin zan canza masa matsayi. Sadauki Zubair shine muradina “.

Wannan amsa nata bakaramin bakanta ran mutane biyu yay ba wato Muzaina da yarima Ishaq da se da yaji kamar an watsa masa ruwan zafi a ilahirin jikinsa.


Murmushi Galadima yay domin dama yasan wannan shine ze zama amsarta ya tambayeta ne domin fita a hakkin yarima Ishaq tunda de baza’a mata dole ba.

“ Zubair shin ka amince za ka auri Muzna!?”. Sadauki zubair a sukwane ya dago Kai yana duban Galadima Jin abinda ya faɗa wanda ko a mafarki be taɓa tsammanin jin wannan maganar ba. Ba shi kaɗai ba kowa ya yi mamakin jin wannan maganar a bakin galadima.

“ ka yi shuru”. Ya sake maimaita mai.

“ mahaifiyata,ta haneni da sake kusanta ta”.
Ya faɗa.

“ Kar ka damu da wannan,nasan mahaifiyar ka bazata ƙi amincewa ba dan haka ni Abdul Aleem Rahman na baka Muzna “.

Alhamdulillah wani sanyi Muzna ta ji tun daga tafin kafarta har zuwa tsakiyar kan ta,lumshe idanunta tayi tana sakin lallausan murmushi,Allah ne kaɗai yasan irin farin cikin da ta tsinci kanta a ciki.

Su Jadwah hamdala suka yi suna rungume Muzna a tare domin karshen damuwar su suma yazo.

Me magana da yawun galadima ne ya miƙe ya soma faɗin

" a yau ne ranar laraba wannan babban fada me albarka ta shaida mayar da Sadauki zubair surki a garemu gaba daya,daga yau ka zama daya daga cikin wannan ahali,an yanta ku Kai da mahaifiyarka”.

Cikin nuna godiyarsa ya rankwafa alamar girmamawa ya yi musu godiya.

Murmushi waziri Abdul Qadeer ya yi sannan ya ce

“ daga yau zaku dawo rayuwa a cikin palace a daya daga cikin bangarorin cikin palace, Sannan kai ne commander duk wani mayakan wannan masarauta “. Ya faɗa yana miƙewa tsaye ya kalli dogarawan da suke tsaye ya musu alama da ido.

Wani babban tray na gold suka dauƙo ɗauke da abubuwa akai an rufesa da jan kyalle suka tsaya a gaban Sadauki zubair.isowa gaban su ya yi ya yaye kyallen ya ijiyesa gefe nan take hular karfe me kan damisa da gwarazan mayaka suke sawa ya bayyana akan tray din se wani riga itama ta yaki ne da jajirtattun mayaka suke sanyawa na zallar karfe ga wani wuka me daraja shima a ciki.

Hular wani babban dogare ya saka masa akai nan take ya sake bayyana a Sadauki me tarin karfi baka kallon komai a fuskarsa illah lion eyes din sa me razana masu laifi.rigar aka miƙa mai haɗe da basa takobin.

Tafa masa gaba daya suka yii banda wa’yannan mutane biyun. Ɗaga takobin ya yi sama with his husky voice ya furta
“ Ni Zubair Abdulturaf nayi alkawarin zan kare wannan masarauta da al’ummar ciki,zan kasance ne basu kariya har karshen numfashina “.

Dogon tsaki ta ja ta fice daga fadar rai a hassale domin iya kunna ta yau an kunna ta kowa haushi yake bata hakan yasa tunda ta fita ko waiwayowa baya batayi ba,.
Babu Wanda ya bi ta kanta,sallaman kowa Galadima ya yi suka tafi.
A wannan ranan su Yumma aka dawo dasu cikin palace batare da an ɗauki ko da tsinke daga gidan su ba,part din da aka basu yana da matukar girma me 4 bedrooms da manyan falo guda biyu da two kitchen iya haduwa part din ya haɗu.Yumma seda tayi kukan farin ciki taje har fada ta Miƙa godiyarta. Cikin ɗakunan Kayan su kuwa an cika musu shi da sutura masu yawa kaya na alfarma ga Kayan abinci da komai na bukata.



Anan zan dasa alkalamina se kuma in mun hadu wani lokaci a domin Ina da internal exam a gabana dis Saturday in sha Allah,ga shi ko karatu ban fara ba saboda rashin lafiyan da na yi kwanaki shisa yau na had’a muku pages 4😍🥺❤️💔

Masoyana Ina matukar godiya da adduar ku

Please Login or Register in order to submit comment