Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ban san ki sosai ba to tabbas zan ce bake bace domin yau naga wani barayi naki da yasa min dasa shakku akan ki, shin kina ganin marin da ki ka min ya dameni ne?, kalaman ne suka min zafi,dan Allah bayan ni kar ki sa'ke faɗawa kowa haka,domin Wannan sune kalmomi mafi tozartarwa".

Maganar sa sosai ya karya mata zuciya se da ta ji tayi nadamar yi masa karya da tayi ga shi ta daure kanta da jijiyoyin ta,batada damar da zata ce masa wacce ya haɗu da ita yau ba ita ba ce yar biyun ta ce amma babu hali.

" Ka yafe min " ta faɗa hawaye na fita a idonta.

" Ai ba zan iya dogon fushi da ke ba ya Nurul qalbi".

Sosai ta basa hakuri haɗe da masa alkawarin hakan baze sa'ke faruwa ba,daga nan suka bage da hirar soyayyar su kusan awan su biyu a bakin rafin kafin suka tafi.

" Amma taya ki ka kasance kawa da baiwar ku kasantuwar ki yar galadima Abdul Aleem amincin Allah ya tabbata a gare sa!?". Arman ya tambaye ta.

" Saboda ta kasance me hankali haɗe da biyayya kuma ai kaga shekarun mu kusan daya ba laifi bane dan mun yi ƙawance ba " ta faɗa musu domin tun dazun suke mata tambayoyi har ta gaji a ranta kuwa tace bazata sa'ke rako Muzna ba.

Karaso su suka yi,ta riƙe hannun Jadwah suka tafi.
" Lallai masu iya magana sun ce so hana ganin laifi, yanzu kasha mari da safiya amma har an maka dadin baki ka hakura".

Kallon Hashim da yay maganar Sadauki yayi yana murmushi " bazaku fahimci komai ba se kun fara soyayya,bari in je gida na bar yumma ita daya".

Ko da shigowar su babban falo suka samu mutane tsaye kowa ya yi carko carko,ga Muzaina dake daga tsaye a bakin kofar mashigar bangaren sarauniya Fatima tana zuba ruwan masifa,kan su ne ya kulle domin basu san menene yake faruwa ba se jin Muzaina da suka yi tana faɗin

" Babu wanda ya isa ya hanani shiga domin kallon mahaifiyata ku gaggauta bani hanya ko kuma kuyi nadama".
Da sauri suka karasa inda take ganin yanda a ƙasa wasu kuyangu guda biyar suka tsare mata hanya.

" My Muzaina menene abinda ya faru! ".

" Wa'yannan banzayen ne suka min shamaki da shiga wajen Ummi,kuma wai Abu Aleem ne ya basu umarni".

Kallon kuyangun Muzna ta yi cikin mutuntawa ta ce " ko zaku iya min karin bayani!?".

" Ran gimbiya ya daɗe, galadima ne ya hane mu da barin kowa ya shiga ciki".

Gyada kai tayi alamar ta fahimta hakan yasa ta riƙo hannun Muzaina din ta jawo ta falo suka zauna amma duk da haka batayi shuru ba se masifa take yi wai an hanasu ganin mahaifiyar su.

Su Ummu zaheenat da Ummu Xulaihah kam sun kasa ko da tashi daga zaunen da suke.
Gefe guda kuma su yarima Haysam ne zaune jikin su a matuƙar mace,.

Fitowa galadima Abdul Aleem suka yi shida wani likita kana ganin fuskokinsu zaka fahimci akwai damuwa a tattare da su,da sauri Muzna ta nufe su.

" Ya Abu Aleem shin menene ya faru da Ummi!?,bacci take yi ne ko kuma batajin dadi !?".ta tambaye sa tana tsare sa da manyan idanunta,cike da tausayin su ya sunkuyar da kai yana me jin nauyin su,ya furta

" Zaku iya shiga ke da Muzaina".

Da sauri ta wuce sa ta shiga ciki Muzaina tana me rufa mata baya.

Koda suka shiga dakin sarauniya Fatima turus suka yi ganin ruwa da aka daura mata ga mashakar iska manne a hancinta ( oxygen).tana kwance.

Kamar wa'yanda kwai ya fashewa a cikin su,suka karaso Muzna ta zauna a gefen damar ta muzaina a gefen hagu.

" Ummi.....".

Muzna ta kirawo sunan ta,a hankali ta buɗe idonta da ya shige ciki tsabar a zabar ciwo ga bakinta da ya bushe,se ta ƙara wani haske.

" Ya..yara na" ta faɗa dakyar murya a dashe.

" Ohh my god Ummi menene Abinda Ya same ki haka jiya fa you're quite well amma yanzu kamar wacce ki ka shekara kina jinya ya Salam " cewar Muzaina dake riƙe da hannun ta a cikin nata.

Murmushin yaƙe ta kwakulo ta yi,ta maida kallonta kan Muzna,ta ga yanda take zubda kwallan ganin ta a cikin wannan halin.

" Ku dena daga hankalinku akan halin da nake ciki,bana son in gan ku cikin wani hali,ko bayan mutuwata ban yafe ku zubar mini da kwalla ko da digo daya bane, addu'ar ku kawai nake buƙata ba kukan ku ba domin kukan ku baze taɓa dawo dani ba. Se kuma ku riƙe min alkawarin da ku ka min duk rintsi duk wuya kar wani abu ya shiga tsakanin ku da ze tarwatsa muku tarayyar ku kunji ko!?".

In banda rawa babu abinda zuciyoyinsu yake yi ga wani tsoro da ya mamaye ransu wani nauyi suka ji kirjin su ya yi kamar an a za musu gungumen dutse.

Dakyar suka iya motsa kan su,suna kallon fuskar ta kamar yau suka soma ganinta a gaba da rayuwar su.

Murmushi ta yi musu me kayatarwa wanda zasu iya cewa tunda suke da ita basu taɓa ganin ta yi irin sa ba,Idonta ne ya soma juyawa ya koma kallon sama.

Da labban bakinta kawai suke iya gane abinda take fadi ba komai bane face kalmatu shahada.

Rintse idanunsu suka yi a tare a lokacin da suka fahimci Allah ya mata cikawa,neman hawaye da kuka suka yi suka rasa zuciyar su ya yi tauri sosai sun alakanta hakan da cewa da tayi bata yafe musu ba in suka yi mata kuka.

A hankali Muzna ta zare mata oxygen din tana me dakatar da ruwan.

Hannu Muzaina tasa ta jawo farar blanket din dake rufe a jikin ta,ta rufe mata fuska.

Barin dakin tayi tana tafiya kamar wacce ta sha abun maye sannu a hankali take tafiya bata ganin kowa a gabanta har ta iso falo,tunda suka ganta a wannan hali suka fahimci me faruwa ya rigada ya faru.

Riƙe hannunta Ummu zaheenat tayi tana hawaye " kar ki faɗa min sarauniya ta tafi ta bar mu".

Gyada mata kai ta yi sannan tace " Ummi ta tafi ta bar marayun ya'yan ta".

Kuka suka fashe dashi banda mazan da idon su ya cika da hawaye karfin hali ne ya hanasu kuka kamar yanda matan suke yi.

Sashen ta ta shiga tana me rufe kofar ta sa key,ta zame a hankali ta zauna a bakin kofar ta haɗe kanta da guiwa,tana tunanin tun da ga farkon rayuwar su har zuwa yanzu tana tuna wai yanzu sune basu da uwa basu da uba. Tunani iri iri haka ya dinga zuwa mata a rai,daga zaran ta yi yunkurin kuka se ta tuna abinda sarauniya ta faɗa musu se ta nemi kukan ta rasa,ta kai kusan awa biyu zaune a bakin kofar dakinta,ta ji ana knocking,dago kanta dake masifan ciwo ta yi ta furta

" Waye ne !?".

" Hamra ce, gimbiya Muzna ana da bukatar ki a fada".
" Okay ina fitowa".

Toilet ta shiga ta sakar wa kanta dake mata ciwo ruwa ba tare da ta cire kayan jikin ta ba se da ta jiƙe sannan ta cire su ta watsar a tsakiyar toilet din ta ɗaura towel ta fito fararen kaya ta saka.


Cikin lokaci kililan mutuwar sarauniya Fatima ya zagaye masarautar Bayaan dama cikin Kuwait da sauran ƙasashen duniya gaba daya.


Ko da Muzna ta fito fuska babu annuri a falo ta iske masu yi mata hidima.bata bi ta kansu ba ta fice suka bi bayanta,duk inda ta wuce bayi take gani zaune jugum-jugum har suka isa fadan da ya cika sosai, Muzaina ta hango cikin fararen kaya irin nata zaune a gaban makaran da sarauniya Fatima ke ciki an shiryata tsaf ga yan uwanta dake gefe suna kuka ƙasa-ƙasa.

Zama dabas tayi a gaban makaran cikin tausayin kansu ta kwantar da kanta a jikin Muzaina,shafa kanta Muzaina tayi itama tana kallon mahaifiyar su dake kwance lifeless.

Sosai suka mata addu'o i na samun rahaman Ubangiji,suna ji suna gani aka ɗauketa aka tafi da ita izuwa gidan ta na gaskiya.rungume junan su suka yi, sosai suka bawa duk wani wanda ke cikin fada tausayi.

Haka aka ci gaba da zaman makoki a fada babu wani abinda yake daga su a gurin se in zasu yi sallah zuwa dare wa'yanda suka zo daga nesa duk sun koma aka bar iya ahalin cikin kewar mutumiyar arziki.


Ko da ta dawo sashen ta ji tayi komai na duniya ya dena mata dadi,jin ta take kamar mara lafiya hakan yasa ta shiga toilet ta murza key ta kunna shower ruwa na zuba a ƙasa, sannan ta shiga cikin jacuzzi da ya kasance cike da ruwa a cikin sa.

Wani Marayan kuka ta saka me taɓa zuciyar duk wani me imani da mara imani tana dukan ruwan da take ciki domin raɗaɗin da zuciyarta yake mata baki baxe taɓa iya furtawa ba.

" Kiyi hakuri ki yafe min Ummi, na kasa cika abinda ki ka faɗa a gare mu. kukan shine kawai ze sanyani samun nutsuwa,ki yafe min Ummi " ta faɗa da wani gunjin kuka me cin rai.

Sosai ta yi kuka na tsawon lokaci wanda ta ji nauyin da take ji a zuciyar ta ya ragu se de ciwon kai da take fama dashi,har karfe tara tana zaune a cikin ruwan bata fita ba.har bacci ya soma ɗaukar ta.

10:00 ta soma jin kukan tsuntsaye wanda hakan yasa ta yi saurin buɗe idonta da suka kasance a lumshe,ga wani masifar sanyi da iska dake kaɗata, hakan yasa ta ɗaga kai, abinda ta gani ya girgiza ruhinta,ganin kan ta tayi a cikin wani ƙasurgumin daji da babu alamar bil adama ko guda daya,ga wasu dogayen bishiyoyi masu tsoratarwa da firgitarwa,babu abinda ka ke iya jiyowa a wannan dajin face kukan namomin daji da tsuntsaye se wasu sauti me firgita zuciya. Cikin ɗari-ɗari ta ziro santaleliyar ƙafafun ta waje ta fito daga cikin jacuzzi da take ciki tana waige-waige, ganin gaba daji baya daji ne tsoronta ya sake ninkuwa,ƙarar zubar ruwa ta ji wanda hakan yasa ta juya baya dan ganin menene jikinta na rawa sosai,wani mummunar halitta ta gani bakinsa na tsilalar da ruwa kamar korama,ga wasu kwarangwal din mutane dake biyo ruwan suna fitowa babu kyan gani hannun su riƙe da takobi,ja da baya ta yi tana jin wani jiri na kokarin zubar da ita,hankalin dodon ne ya dawo kanta bayan ya gaba aman ruwan kwarangwal din cikin murya me firgitarwa ya ce

" Bil adama a sansanin mu!?,ku yi maza ku kamo min ita ku kashe ta ".

Cikin tafiya irin na horori suka soma binta suna har ba mata takobi,ita kuwa gudu take yi da iya karfin da Allah ya bata tana kuka. Kutsa dajin ta dinga yi ba tare da tasan a inda take a za ƙafafuwan ta ba, ƙafafunta ne taji sun yi mata nauyi ta soma gajiya da gudun da take yi hakan yasa ta faɗi a ƙasa tana ja da baya su kuma suna tunkaro ta, riƙe ƙafafunta suka yi suna janta tana ihu,da iya karfinta ta shure su da ƙafa ta soma rarrafe da gudu wani karkashin bishiya me duhu ta gani cikin hanzari taje ta boye a ciki,tana haki domin ba karamin wahala ta sha ba, ƙafafunta duk sun ji ciwo sun fashe.

Babu abinda takeyi banda sauke numfashi ganin ta samu tsira,inda ta tsuguna ne taji ya soma numfashi yana motsi,wani harbawa kirjinta ya yi ganin masifar a she be ƙare ba,( ni ko nace ai Muzna masifa bata ƙare ba kam). cikin rashin sani ashe akan wata tsohuwar macijiya take zaune batare da ta sani ba,a tsorace ta soma kokarin barin kasan bishiyar se ta ji ana faɗin

" Sarauniyar gobe ina ki ke kokarin tafiya?,shin ba ki san in ki ka fita waje zasu kashe ki bane!?". Ba kowa ne ke magana ba fa ce wannan macijiyar da take zaune akai.
Wani sabon tashin hankali ta kuma shiga,da gudu ta yi yunkurin sauka a jikin ta amma macijiyar ta hanata ta hanyar harɗe ta da bindinta,.

" Ki saurara! ni ba cutar dake zan yi ba,sunana macijiya Markusa,na kasance a wannan dajin kadur din tsawon shekaru dubu biyu ina rayuwa anan,kuma bana taɓa cutar da kowa batare da ya yi yunkurin cutar dani ba,se de ina da matukar hatsari ga duk me muguwar nufi,zan taimaka miki domin zasu iya kashe ki ".
Nutsuwa Muzna ta yi tana sauraran ta jin da tayi ta ce bazata cutar da ita ba amma har yanzu tana ɗari-ɗari dan jikinta se rawa yake . Wani farin haske ne ya mamaye inda take din nan take ta fahimci a cikin kogon dake ƙarƙashin bishiya take.dawo da kallon ta gabanta ta yi ta ci karo da macijiya Markusa da ta kasance rabinta mutum rabinta macijiya gata kyakyawa bazaka ce takai adadin shekaru har dubu biyu ba,daga saman gammon gashinta kuwa wasu macijai ne masu sheki se fitar sa dafi suke yi wanda a ƙalla yawan wannan macizan zai kai hamsin ko fiye da haka.

" Kar ki tsorata da ni, riƙe wannan a hannun ki".ta faɗa tana miƙa mata wani abu kamar kwai.karba tayi tana kallon sa a hannun ta.

" Dole ta inda ki ka fito ta nan ne zaki koma gida ruhinki dole ya koma gangan jikin ki,in ko ba haka ba awanni takwas ki ke dashi,daga zaran kin fita zasu kamaki sukaiwa dodo gartamus shi kuma ze kashe ki ya bawa yaransa su yi farfesun namanki su cinye,amma wannan kwai din shine ze cece ki daga gare su domin sun sani sarai daga zaran wannan kwan ya faɗi a ƙasa ya fashe to duk gabaki dayan su se sun mutu murus.

Zabi biyu gare ki,na farko.. za ki iya neman sulhu da su ta hanyar yi musu daɗaɗan kalamai in sun saurare ki tom in kuma basu saurare ki ba kin zama gawa.

Na biyu... Za ki iya fasa wannan kwan a ƙasa nan take zasu mutu zaki kuma koma gida cikin koshin lafiya da aminci ".

" Nagode sosai macijiya Markusa,bazan taɓa manta halaccin ki a gare ni ba". tana gama faɗin haka suka fara jin takun sawu masu yawa alamun har yanzu ita suke nema,.

Murmushi suka yi wa juna ta fito,tana fitowa kuwa suka ganta suka ɗauke ta sama kamar yar tsana suka fara tafiya da ita,har suka iso ainihin sansanin su,nan taga wasu kwarangwal din masu yawan gaske. Ji ta yi sun direta a ƙasa sun sauke ta gaban dodo gartamus.

Cikin wannan muryar tasa mara dadin sauraro da tsoratarwa ya soma faɗin

" Ke bil adama menene ya kawo ki cikin dajin kadur,ko baki da masaniya kan cewa wannan dajin duk wani bil adama kai bama bil adama ba hatta su kansu aljanun duk wanda ya shigo baya fita da ransa,kin ga wa'yannan duk matattu ne wa'yanda suka mutu na tayar dasu suke min hidima,ke wato gaki tantiriya shine ki ka shigo ko!?".

Muryar ta na ɗan rawa ta ce " wallahi bani na kawo kaina ba ina wanka ne na buɗe ido na nagan ni a nan dan Allah kar ka cutar da ni".

" Hahahahahahahaha,yarinya kin makaro" ku ɗaure min ita ".

Ɗaure ta suka yi a jikin wani bishiya,suna kalllonta suna lashe baki sun ga nama.

Ta jima a wajen daure tana kallon su suna ta harkokin gaban su tayi ihun ta yi maganar har ta gaji babu wanda ya kulata hakan yasa ta soma waka


" Muyiii adalci ga wa'yanda suka kasance marasa laifi......muyi afuwa ga wa'yanda suka kasance masu kyakyawar zuciya.....
Kowa na iya rikidewa ya koma mugu..... Nasan kana da kyakyawar zuciya bazaka cutar da wacce bata son cutar da ku ba,ina ɗauke da muguwar gubaaaaa da ze hallaka kowa......" Haka ta ɗinga maimaita waka tun basu saurareta ba har suka saurareta.

Dodo gartamus ne ya taho gaban bishiyar ya ce

" Kin samu haɗuwa da macijiya Markusa,ta ba ki abinda za ki kashe mu to bazamu baki damar hakan ba ".


Cikin kwantar da murya Muzna ta ce " ko kaɗan bawai na karɓi wannan guban dan in hallaka ku bane,babu ma manufar hakan a raina, wallahi bazan taɓa iya cutar da abinda be cutar dani ba,ko wanda ya cutar da ni se de in barsa da Allah amma dede da kaxa bazan iya kashewa ba,dodo gartamus nasan Kanada zuciya me kyau,samun dodo irin ka a wannan duniya ze yi wahala sosai,shin meze sani in saka muku guba!?, sulhu kawai nake da bukata,naji na yarda na shigo muku sansani amma kasani namaka imani da mahalicci na bani na kawo kai na ba,ka yi min afuwa".

Shuru dodo gartamus yayi kafin ya fitar da wani huce da ya kusan tayar da guguwa.

" In har kina so in yarda dake ki wurgo min wannan gubar " babu ko shakku ta wurgo masa shi ya cafe.

Tabbas ya yarda da ita,kuma ya ji baze iya cutar da ita ba hakan yasa yai wa kwarangwal din ya'yan gidan sa alamu da ido da sauri suka kunceta haɗe da sauko da ita kasa,.

Hannun sa me tsoratarwa da gashi ya ɗaura akanta yana shafawa " tabbas za ki iya shugaban ci aduk inda ki ka tsinci kan ki,za ki iya kawo gyara a cikin duk jinsin da kika shiga jeki,jeki gangan jikin ki na jiranki ".

" Nagode sosai dodo gartamus,bazan taɓa manta halaccin ka a gare ni ba".

" Kin cancanta".

Rakiya suka yi mata har zuwa wajen da ta fara tsintar kan ta,a wannan karon bata kalli jacuzzi din da ta fito a ciki ba,hakan yasa ta kalle sa

" Dodo gartamus taya zan koma kenan yanzu!?".

" Kar ki daga hankali". Ya faɗa yana busa mata iskar bakinsa me karfi nan take guguwa ya tashi da ita.



" Muzna ki farka menene abinda ya sameta ne!?". Muzaina ta faɗa tare da damuwa akan fuskarta tana riƙe da hannun Muznar gam taki saki.

" Wallahi ke kam nima baiwa ce ta kirawo ni,wai ta shigo dakin ta domin sanar mata da tazo taci abinci shine taga ruwa a malale a tsakar dakin hakan yasa ta dinga bin inda ruwan ke fito nan ta fahimci daga toilet ne,aikuwa tana buɗewa ta ganta kwance cikin jacuzzi ruwa ya cika tabb ita kuma bata numfashi".
Cewar Ummu Zaheenat.

Galadima dake daga tsaye ya ce " kar ku damu za ta farka in sha Allah ".

" Abu Aleem taya zan kwantar da hankali na ina ganin yar uwata kwance kamar wata matacciya?".

Dafa kafaɗar ta Ummu Xulaihah ta yi alamar tayi shuru.

Duk suna tsaye a cikin dakin Muzaina ce kawai zaune a bakin gadon da Muzna ke kwance kamar matacciya.

Firgit ta miƙe tana kokarin saukowa akan gadon riƙe ta tsam Muzaina da Ummu Xulaihah suka yi ganin bata hayyacinta .se da ta gama fisge-fisgen kafin ta yi lakwas ta kwanta jikin Muzaina tana sauke numfashi.


" Muzna shin kina tare da mu !?". Galadima Abdul Aleem ya faɗa yana dafa kanta.

" Abu Aleem shin ya nagan ni anan ni da nake daji ".
Tana magana ne tana kuma kallon dakin ta da kuma kan gadon da take. abun kamar almara tasan de wannan ba mafarki bane haka zalika be yi mata kama da zahiri ba.

" Ki nutsu babu abinda ya same ki mafarki ne kawai ".
Haka suka dinga gamsar da ita kan cewa mafarki ta yi,ita de ko kaɗan ta kasa gaskata hakan jin su kawai take yi.

Abinci Ummu Zaheenat ta bata da kanta domin ko breakfast batayi ba, duk da bataci da yawa ba amma tasa wani abu a cikin ta.

Ko da aka ce ta shiga ta yi wanka ƙin yarda tayi a ganin ta in ta koma toilet din abinda ya faru ze iya maimaita kansa.

Kowa tafiya ya yi izuwa sashen sa aka barta tare da Muzaina da Jadwah,se da ta ga ta samu tayi bacci kafin nan ta kalli Jadwah ta furta

" Bari in je in kwanta seda safe ". Kai ta gyada mata tabi bayanta da kallo.


Wanka Muzaina ta yi ta yi duk wani abinda ta saba yi kafin kwanciya bacci bayan ta shirya cikin kayan bacci ta hau kan makeken royal bed din ta ta kwanta.


2:00Am sanyin da ta ji ya mata yawa ne yasa taja blanket ta dukunkune a ciki,amma se ta ji sanyin kamar sa'ke huro sa ake, cikin bacci ta soma mita.

" Waye kuma ya ƙara AC din mtsssw" ta faɗa cikin bacci tana kuma dunkule kanta waje guda,wani sauti me kuka-kuka ta soma ji yana tashi haɗe da kiran sunanta.

Gaba daya wannan ƙaran ya dameta ya fitine ta, hakan yasa ta zauna tana mutsike ido game da yin hamma.

Ware manyan idanunta tayi waras at The same gurin da Muzna ta tsinci kanta.a hargitse ta mike tsaye tana rarraba ido kamar ta kai ajiya.

Wani gurnani mara dadin ji ta soma ji a bayanta nan take zuciyarta ta soma rawa,a hankali kamar wata mutum mutumi ta soma juyawa har ta juya gaba daya.
Ihu ta fasa sakamakon dodo gartamus da tayi arba dashi a gabanta, ga kwarangwal da yawan su baze taɓa misultuwa ba tsaye bayansa.


" Bil adama a sansanin mu!?,shin ko kin san menene ake yi wa wannan dajin lakabi da shi kuwa?, dajin kadur in de ka shigo tofa babu fita.ku yi maza ku kamo min ita ku kashe ta ".

Ganin wa'yannan kwarangwal din sun fara matso ta ne yasa ta fara ja da baya. ganin sun kusan cimma ta ne ta ɗiba a casa'in ta fara gudu kamar ƙafafuwan ta zasu bar jikinta,daga zaran ta juya se ta gan su daf da ita,hakan yasa tana hango wani karkashin bishiya me yalwantaccen duhu tayi sauri ta faɗa a ciki,tana sauke ajiyar zuciya.
Ji tayi abinda ta zauna akai ya fara motsawa hakan yasa ta yi kokarin tashi akai amma se macijiya Markusa ta dakatar da ita ta hanyar ce mata

" Sarauniyar gobe ina ki ke kokarin tafiya,shin ba ki san in ki ka fita waje zasu kashe ki bane!?". Nan fa hankalinta ya kuma tashi jin magana kuma Muryar mace.

" Wacece ke dan Allah kar ki cutar da ni" ta fadi hakan cikin tsoro.

" Ki saurara ni ba cutar dake zan yi ba,sunana macijiya markusa,na kasance a wannan dajin kadur din tsawon shekaru dubu biyu ina rayuwa anan,kuma bana taɓa cutar da kowa batare da ya yi yunkurin cutar dani ba,se de ina da matukar hatsari ga duk me muguwar nufi, zan taimaka miki domin zasu iya kashe ki ".

Shuru Muzaina ta yi tana sauraran maganar ta sede har zuwa yanzu a matuƙar tsorace take.

Bayyana mata kanta macijiya Markusa ta yi,se da ta ɗan razana ganin macijiya me Suffar bil adama samanta mutum kasanta macijiya.iya tsorata ta tsorata da macijiya Markusa sede ta yi karfin halin nutsuwa.

" Kar ki tsorata da ni, riƙe wannan a hannun ki".ta faɗa tana miƙa mata wani abu kamar kwai.karba tayi tana kallon sa a hannun ta..

" Shidin menene wannan,nagansa kamar kwai !?".

Murmushi ta yi kafin ta ce

" Dole ta inda ki ka fito ta nan ne zaki koma gida ruhinki dole ya koma gangan jikin ki,in ko ba haka ba awanni biyar ki ke dashi,daga zaran kin fita za su kama ki sukaiwa dodo gartamus shi kuma ze kashe ki ya bawa yaransa su yi farfesun namanki su cinye,amma wannan kwai din shine ze cece ki daga gare su domin sun sani sarai daga zaran wannan kwan ya fadi a ƙasa ya fashe to duk gabaki dayan su se sun mutu murus.

Zabi biyu gare ki,na farko.. za ki iya neman sulhu da su ta hanyar yi musu daɗaɗan kalamai in sun saurare ki tom in kuma basu saurare ki ba kin zama gawa.

Na biyu... Za ki iya fasa wannan kwan a ƙasa nan take zasu mutu zaki kuma koma gida cikin koshin lafiya da aminci ".

" A gaskiya Nagode miki sosai " tana faɗar haka cike da kwarin gwiwa ta fice a kogon ranta fess tunda ta samu abinda zata kare kanta.

Fitowarta ya yi dede da karasowan su,suna zuwa kuwa suka ɗauke ta cak basu tsaya a ko ina ba se a sansanin dodo gartamus.

Ko da isan su suka ajiye ta gaban sa, dubanta yai da firgitattun idanunsa ya daka mata tsawa

" Ke bil adama menene ya shigo dake dajin kadur".

Shuru ta yi tana aiyana wani abu a ranta,baya ta ja kaɗan ta fito da kwan guban da ta boye a bayanta. Suna gani suka fara ihu da kururuwa me matuƙar razana

Please Login or Register in order to submit comment