Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruhi.

" Kar ki fasa wannan kwan na miki alkawarin zamu mayar da ke har inda ki ka fito,kar ki kashe mu,ina me dukar da wuya a gare ki".

Makirin murmushi Muzaina tayi tana suburbudawa macijiya Markusa albarka da ta ba ta wannan kwan yanda suke kururuwar rokon ta hakan ba karamin dadi ya mata ba.
Sa'ke kwan tayi ya faɗi a ƙasa ya fashe nan take wani koren hayaki ya gauraye wajen gaba daya haka suka dinga zubewa a ƙasa matattu,ita kuwa wani guguwa ne me karfi ya yi wurgi da ita.

Faɗowan da zatayi ta fado a cikin toilet din ta,zama tayi a tsakar toilet din tana karewa ko ina kallo hannunta da ta ɗan buge take mulmulawa kafin ta tashi ta fita,zama tayi a bakin gado tana me duban lokaci nan taga karfe biyar saura minti biyu,ga shi an fara kiraye kirayen sallah asuba. A maimakon ta jira tayi sallah se ta kwanta kawai tana jan bargo tana rufe jikinta harda fuskarta gaba daya.


Mai girma Sheikhy ne tare da Sheikh Abu Dhabi tsaye a gaban mudubin duba suna ganin duk wani abinda ya faru.

Hannu mai girma Sheikhy ya saka ya ja maki a kan sunar ta,.

" Tun daga yanzu mun riga da mun san wacece shugabar mu ta gobe, yanzu gwaji biyu ne ya yi saura ".

" Ya shugabana kawai ban taɓa sanar dakai bane, amma tun ranar farko da na fara ganin wannan yarinyar naji a jikina tana tare da abubuwa na al'ajabi ".

Murmushi irin nasu na manya mai girma Sheikhy yay " lokaci ne ze nu na hakan Abu Dhabi"..


Yau ta makara batayi sallar asuba akan lokaci ba se karfe takwas ta farka da matsanancin ciwon jiki.


To masu karatu anan zan dasa alkalamina se kuma in Allah ya haɗamu monday.


Yanzu labari ya soma tafiya in har kun bani haɗin kai tofa zamu tafi,in kuma kuka ki bani haɗin kai se mu hakura da wannan daddadar labarin,yawan comment din ku yawan read more din ku.




Comments,like and share fisabilillahi.🥰🥰🥰🫶
⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩





❤️🔥Page 11____12





Matsa cinyarta da ta ji yana mata ciwo tayi tana yar ya mutsa fuska, ga zuciyarta da yake mata babu dadi domin tarin kewar sarauniya Fatima da take ji,tagumi tayi ta faɗa duniyar tunani,tunawa da tayi kan cewa bata yi sallah bane yasa ta miƙe tana takawa sannu a hankali har ta shige toilet din tayi alwala,sannan ta taso ta gabatar da sallah.
Sosai tayiwa Sarauniya Fatima addu’oi. Tana a bisa kan sallaya taji ƙarar bude kofa amma doesn’t mind to see who is at the door. ta ci gaba da azhkar dinta,jin wanda ya shigo din bece komai bane yasa ta d’an waiga,amma da mamakinta se bataga kowa ba hakan yasa ta ci gaba da abinda take. Ta jima sosai Kafin ta sallame ta miƙe haɗe da barin sallayar a inda tayi sallah ta hau gado ta kwanta bawai dan tana jin bacci ba.

“ shin jiya a bacci ne nayi wannan mafarkin ko kuma de a zahiri domin na matukar shiga rudani ya Allah ka kawo min mafita “.

Duk wannan maganganun da take yi a cikin zuciya take yin sa.

“ haba Muzna menene ze sa kice wai a mafarki ki ka ga komai!?,a zahiri ne bawai bacci ki keyi ba,yakamata ki san da haka “.

Da tsananin mamaki ta kalli bangaren da taji maganar,me Kama da ita sak ta gani hatta Kayan da take sanye dashi sune a jikinta babu abinda ya rabasu,tana tsaye tana ninke sallayar da tayi sallah bata ɗauke ba.

Murya na shaking ta furta “ Muzaina ke ce?”

“ ah ah ba ita bace. ke ce,ni kece, kuma ke nice na fito daga gareki ne”.

Mannewa tayi a jikin gado tana mata kallon tsoro,domin tabbas ta gamsu wannan ba Muzaina bace saboda yanda take ta mata murmushi. Ita kuwa me masifar kama da ita din babu abinda take yi se d’an gyare-gyaren dakin.

Kofar toilet aka buɗe ana faɗin “ yau sam ba’a shigo an tsaftacewa Gimbiya Muzna muhallinta ba, nasha wahala wajen gyaran bandaki “.

Da wani irin speed Muzna ta kalli me magana abinda ya sa’ke tayar mata da hankali shine itama wacce ta fito daga toilet din komai din su iri daya.

Hannunta da yake kerma ta nuna ta dashi tana fadin “ ke kuma wacece ke?”.

Wacce tafito daga toilet ne ta furta “ nidin fa ke ce,ba ki ga muna tsananin kama ba!?”.

Itama ta jefa mata tambaya a madadin ta bata amsar abinda ta tambayeta.

Ita ta farko me gyaran daki ne ta matso kusa da wacce ta fito daga toilet ta ce “ meye na ji kin faɗa yanzu?, karya ki ke yi nice ita bake ba”.
Kallon banza ta watsa mata ta furta “ karya ne nice ita ba wai ke din nan ba,ke hoton fuskarta ne kawai amma ni din na kasance nafito daga its ne”.

Muzna dake dukunkune a can kuryan gado ta haɗe kai da guiwa tana kallon su hankali a tashe Ganin fadan ya kaure a tsakanin su.

“ ni ki ka zaga ko!?, to bari ki gani se na nuna miki gimbiya Muzna nice ita” ita wacce ta fito daga toilet ta faɗa tana juyawa zuwa ga Muzna.

“ shugabata ki ce mata ta bar nan ba ma bukatar ta,ni kaɗai na isa in miki duk wani hidima da yakamata “.

Itama dayar matsowa tayi Idonta taf da ruwan hawaye ta ce

“ gimbiya nice na dace da in kasance tare da ke domin yi miki dukkanin abubuwan da ki ke bukata dan Allah kice ta tafi “.

Gaba daya sun gama dugunzuma tunanin ta,hayaniyar da suke tana jinsa ne har tsakiyar kanta,muryoyin su yana fita bibbiyu wanda hakan ya haddasa mata jin jiri ga shi sun gagara yin shuru.
Hannu biyu tasa ta toshe duka kunnuwanta ta saka wani razananniyar k’ara tare da yin magana da karfi cikin tsawa ta furta

“ ku rabu dani bana son ku,ku bar ni. zan kashe kaina muddin ku ka ƙi tafiya “

Muryoyinsu da ke fitowa bibbiyu ne suka soma fadin

“ yake Sarauniyar mu!yake Sarauniyar mu,zamu tafi-zamu tafi,amma ki sani-amma ki sani,za mu dawo a duk lokacin da ki ka zama shugaba-zamu dawo a duk lokacin da ki ka zama shugaba “.

Duk da ta toshe kunnuwanta da karfi amma se da taji muryoyinsu a tsakar kanta.
Suna gama wannan maganar suka b’ace bat, jin shurun da dakin ya dauka ne yasa a hankali ta zame hannunta Tana dago kanta a hankali.ganin dakin wayam sun tafi ne yasa ta miƙe da gudu daga ita se riga da wando na roba kanta babu hula dogon gashinta ya sauko a gadon bayanta ta fice a dakin da gudu. Tana fita ta samu masu yi mata hidima a bakin kofar falon ta. dedeta nutsuwarta tayi ta ci gaba da tafiya da dan sauri- sauri. Bin bayanta suka soma yi domin mata rakiya

“ kar ku damu base kun zo ba”.
Direct sashen marigayiya sarauniya Fatima ta nufa a bakin kofar falon ta tsaya tana bin ko ina da ido se take ji kamar zataga fitowarta daga daki amma shuru hawayen da bata san da taruwar sa a idonta bane taji ya sauko mata a kunci sharewa tai tana karasa shiga ciki ta kwanta akan doguwar kujera na zaman mutum uku,tana kwanciya kuwa bacci ya dauketa.


“ why can’t you understand bro!, I so much love that girl,ta ya za ka ce wai nabar batun son da nake mata haba impossible “.
Yarima Ishaq ya faɗa yana me hargitsa gashin kansa.

Murmurshin leben baki yarima Haysam yai “ amma de kasan Abu Aleem baze taɓa aura maka ita ba muddin in ta nuna bata sanka.gwara ka nemi wata kawai”

Tsaki ya ja domin yarima Haysam ya fara ɓata masa rai,a madadin ya basa shawara amma ya tsaya yana karya masa guiwa.

“ please Haysam inde bazaka ban shawara ba jeka kawai,you’re not needed here “.

Yana dariya ya fice masa a part.

Har azhar tana kwance tana bacci kamar yar karamar yarinya ta rungume pillow a kirjinta.

“ amintacciyar baiwa shin ko kin gane min gimbiya Muzna?”.

“ eh naga lokacin da tashiga bangaren marigayiya da na duba se naga bacci take.Ina tunanin kewa ne yake damunta “.

Cike da tausayawa Ummu Zaheenat ta ce “ shikenan dama na dubo ta a sashenta ne kuma bata nan. Ina ita Muzaina din take?”.
“ meyafaru a ke nemana “.
Suka ji muryar Muzaina ya katse su.

Maida dubansu zuwa kanta suka yi tana sanye da wando me fadi sosai kamar buje se vest kanta kuma ta kwashe gashin ya koma gefe daya kana ganinta zaka fahimci daga bacci ta tashi.

“ ohhh na ɗauka ba kya nan ne” Ummu Zaheenat ta faɗa tana miƙawa amintacciyar baiwa keys din wasu sashen masarautar da babu kowa cikin sa.
Bayan tafiyar amintacciyar baiwa Muzaina ta zauna tana ɗaura kafarta daya kan daya.

Sau biyu ta kalleta tundaga nan kuma ta mayar da hankalinta akan abinda take, domin ta lura Muzaina bata da kunya shisa bata bi ta kanta sosai.

“ kin yi sallah ne?”

“ banyi ba kuma ba yanzu zan yi ba “ ta faɗa tana miƙewa haɗe da tafiya tabar Ummu Zaheenat sa’ke da baki tana kallonta.

Yau tsawon sati guda kenan rabonda Sadauki Zubair ya saka Muzna a ido gaba daya ya shiga damuwa na rashin ji daga gareta.ya yi zarya a sashen manyan bayi har ya gaji amma bega ko me Kama da ita ba ya gani kuma be taɓa tambayan yan sashen game da ita ba se de yaje ya tsaya ya ɓata lokaci a gurin a tsaye amma baya ganinta. Hakan yasa shi ya shiga damuwa Yumma da ta lura da gaba daya yanayin sa ya sauya a cikin yan kwanakin ne ya sa ta tambayesa ,be boye mata komai ba ya sanar da ita ya jima be sa Muzna a ido ba be san a wani hali take ba. Kwantar masa da hankali tayi ta hanyar ce masa ze iya yuwa aiyuka ne suka boyeta.
Haka ya ci gaba da zuba ido a domin jiranta .

Tun ranan da ta fara ganin masu kama da ita suna zuwa mata ta koma zautacciya domin sun raba mata hankali. Ko fita batayi ko da yaushe tana sashen sarauniya Fatima. Haka kurum zata dinga jin jikinta na mata ciwo ko kuma ta gaji shisa duk wani abinda take bukata ake biyota dashi su Jadwah a ko da yaushe suna a tare da ita domin debe mata kewa.

A bangaren Muzaina kuwa hakan ne ya kasance da ita duk wani abinda yake faruwa da Muzna itama yana faruwa da ita face ganin masu kama da ita,su bata ganin su.

Tana a kwance akan gado su Hamra na gefenta suna danne-danne a wayoyinsu,ta yi zurfi cikin tunani ta ji muryar Jadwah na mata magana,fahimtar bata ji bane yasa Jadwah sa’ke fadin

“ shin yaushe za ki bayyanawa sadauki Zubair gaskiyar ke wacece,Ina miki gudun ya ji a wani gurin ba'a bakin ki ba “.

Numfashi ta sauke domin kuwa tunanin da tayi shuru tanayi kenan.

“ Jadwah Zubair ya tsani karya da cin amana. ina tunanin muddin na sanar masa da ni yar sarki ce ze tsane ni domin na masa karya “.

“ ki same sa ki yi masa bayani ze fahimce ki sadauki Zubair a yanda naji ana magana mutane sun ce yana da matukar saukin Kai “. Hamra ta sako baki a zancen nasu.

Dan jimantawa Muzna tayi kafin nan ta mike daga kwancen da take ta kalli kayan da suke jikinta rigace doguwa da tasha duwatsu koren kala.

“ Ina za ki je haka ?”.
“ wajen sadauki na yau kimanin kwana bakwai kenan ban gansa ba “.

“ amma kar ki tafi da wannan Kayan domin kuwa hakan ze ƙara sawa ya dasa tantama a kan ki ".

Tabbas ta yarda da maganar Hamra domin tasan Sadauki Zubair da kwakkwafi.

" me yakamata in saka kenan!?". Ta yi maganar tana kallon su.

" ban minti daya " Hamra ta faɗa tana shigewa dressing room din Muzna da gudu.shuru suka yi suna zaman jiran fitowar ta.

Fitowa ta yi hannunta riƙe da wani plain gown black colour babu kwalliya a jikinsa ko ɗigo yana da dogon hannu se de kayan kallo daya zaka masa ka ji ya masifar burgeka. rigar tana da kauri.

" kin ga wannan in ki ka saka baze kawo komai a ransa ba”.

Shagwabe fuska ta yi “ kin tabbata ?”.

Miƙewa Jadwah ta yi ta nufi inda Hamra ke a tsaye ta karɓi rigar tana duddubawa.

" uhmm to rigar babu laifi amma ko Wanda be San kan kaya ba in ya ga Rigar nan yasan tafi karfin dinar dari ko ( dinar shine kudin kuwait ).
".

" eh hakane amma na duba kayanta gaba daya walllahi shi kadai ne kawai wanda bashida adoh da kuma tsada".

Ita de ido kawai ta zuba musu tana kallon su,nan ta ji Hamra na faɗin " to kawai mu ya mutsa sa yanda ze yi kamar ba'a masa guga".

Dariya ta fashe dashi jin al’amarin harda su ya mutsa kaya.
a gaban idonta suka ya mutsa kayan nan take kuwa ya yi sequeezing.

" tom amshi ki sa ka".
Tana murmushi ta ƙarba ta shiga toilet ta sa ta fito.
Daure mata gashinta suka yi jelarsa ya kwanta a bayanta.

" good to go,amma basaja zakiyi dan kar a fahimci ke ce".

" to shikenan bari in je in dawo"


Cikin badda kama ta samu ta sulale ta fice a cikin royal palace. filin daga ta fara zuwa domin dubasa sede babu kowa a gurin hakan yasa ta tsaya tana kare fuskarta da hannu saboda ranar da ake yi.tana tsaye a gun wani matashi yaxo ɗaukan wasu karafuna,da sauri ta dan matso kusa dashi tana fadin

" shin ko ka gane min sadauki Zubair ?".

" eh yanzu na baro su a murin dawakai ".
Shuru ta yi saboda bata san ina ne murin dawakai din ba.har matashin ya soma tafiya tai saurin bin sa a baya

" ka taimaka ka rakani wajen ban san ina ne ba ".

seda ya rakota kafin nan ya juya ya barta tsaye a gun.bisa rashin saninta domin da yawan bayi da al'ummar cikin masarautar basu san Muzna da Muzaina a fuska ba,in ba wa'yanda suke musu hidima ba da makusantan su.

A kan dawakai ta hange su suna tafiya,a madadin taje ta samesa se ma shagala da tayi da kallon sa,Sadauki Zubair makurar kyau ne komai nasa is so good and unique. a duk lokacin da take kallonsa manta kanta take yi kamar yanda yanzu ma ya kasance.
Wani doki ne ya ɓalle daga cikin murin dawakan ya yo kanta gadan-gadan,amma dake hankalin ta ya yi nisa bata ji maganar da mutanen wajen suke mata ba.

Da ga nesa ya hango abinda yake shirin faruwa hakan yasa cikin azuma ya taho da gudu yana sukuwa akan kosassan dokin da yake Kai,ganin gudun da dokin yake yi be masa bane yasa ya zuba mata bulala nan take tayi wani girgiza ta Ƙara gudu cikin dakika kaɗan ya iso gunta wanda ya yi dede da isowa wajenta da shima wannan dokin ya yi.

Hannu daya Sadauki Zubair ya yi amfani dashi ya dagota sama har zuwa kan dokin a gabansa.shi kuma wannan dokin ya bugi iska.

Se a sannan ne Muzna ta dawo hankalinta dago kai ta yi tana me kallon tazaran da take dashi da ƙasa kafin ta saki kara haɗe da runtse ido cikin tsoro domin bata taɓa hawa doki ba ko da wasa.

Hannun sa guda ya ɗaura akan kafaɗarta yayinda dayar hannun ke rike da linzamin dokin.


" Nurul qalbi ki dena ihun nan za ki kashe min dodon kunne".

Jin daddadar muryar sa da tayi yana mata raɗa a kunne ne yasa ta yi saurin juyawa garesa da mamaki,dage mata gira ya yi fuskarsa na ɗauke da murmushi.

" Ta ya aka yi na hau dokin nan".

Girgiza kai ya yi wato ita ba ta ma san ya akayi ta hau ba.

" a lokacin da ki ka mace a kallona a wannan lokacin ne doki yazo da gudu domin taka ki,ni kuma bazan iya barin wani abu ya cutar min da masoyiya ba hakan yasa na zo da gudu na ɗauke ki sama ". Ya faɗa cike da barkwanci

" rayuwata bata da wani muhimmancin da za'a cetosa nidin tamkar fanko nake babu komai cikinsa " ta faɗa a zuciya batare da tasan ya fito fili ba.

" Nurul qalbi meyasa za ki faɗi haka,ko da kin kasance bakida kowa ki tuna kina dani zan tsaya miki a ko wani hali".

Se da ta ji abinda ya faɗa ne ta fahimci maganar nata ya fito fili.

Hawayen dake kwance cikin idonta ta yi kokarin shanyewa amma ta gagara seda suka gangaro.

" Masoyi duniyar ta dena min dadi,na rasa mutane masu muhimmanci a rayuwata,wa’yanda nake gani in ji dadi duk sun tafi sun barmu “.
Sanyi jikinsa yayi Musamman sa’In da ya ji ruwan hawayenta na zuba a akan hannunsa nan ya fahimci kuka take yi hakan yasa ya juya akalar dokin Izuwa Lambu wajen da suke haɗuwa.

Tsayuwar da taji dokin ya yi ne yasa tayi saurin share hawayen kan kuncinta tana kallon inda suke,sauka akan dokin Sadauki Zubair yai yana me miƙa mata hannunsa,riƙe hannunsa tayi ta sauko ƙasa,jan ta ya yi wajen da bata taɓa shiga ba a cikin lambun wani irin hadadden guri ne da ya yawaltu da korayen shuke-shuke ta ko Ina in ka duba zakaga furanni da suke da tsayi madedeta,zama suka yi akan korayen ƙananun ciyayin da suka zagaye wajen.

“ Nurul qalbi!,bani son ganin ki cikin damu wa shin fada min da akwai abinda kike boye min ne kar in sani?”.

Lumshe idanunta tayi wasu zafafan hawaye na sake gangarowa daga idonta. Bawan Allah sadauki Zubair duk ya shiga cikin damuwa ganin masoyiyar sa a wannan irin damuwan yasa ya ji shima duk ya shiga damuwa.

“ ban taɓa tunanin zan taso in yi rayuwa batare da iyayena ba amma yanzu na wayi gari banida ko daya,Nima yanzu Ina cikin wa’yanda za'a kira Marayu,a duk sanda na rufe idona fuskokinsu ne yake ta dawo min idona.shin taya zan ji dadin wannan rayuwa”.

“ Allah yana tare dake nima Ina tare dake,iyayen ki addua su ke bukata daga gareki. A duk sanda ki ka tuna su ki yi musu addua. Sannan ki dena kiran kan ki marainiya Ina tare dake duk da nima Maraya ne na rasa mahaifina tun ina karami,amma nayi alkawarin kulawa dake har karshen rayuwata ko da kuwa za'a d
ɗauki raina akan ki Muzna bazan taɓa barin a cutar dake a gaban idona ba.zamuyi aure yanda zamu kasance a inuwa daya,zan yi iya kokarina in maye miki gurbin mama da baba da kika rasa”.

Sauke shanyayyun idanunta tayi akan nasa tana kallon sa batare da kyaftawa ba,so da kaunarsa suna kuma yin tasiri me girma a zuciyarta wani bangaren kuma tsoro ne fal a ranta na tunanin ya zasu kaya in ya gano wani abu akanta.

Ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin
" hakikanin gaskiya kai din masoyi ne na gaskiya kuma nagodewa Allah da ya turo minkai cikin rayuwata “.

Murmushin sa da ya saba yi mata shi ya yi,yana kwantar da kanta a kafadarsa.


Yana gama daukan su hotuna da videos ya bar lambun da gudu har yana tuntube,be tsaya a ko Ina ba se a bangaren yarima Ishaq.
Be samu ganin sa ba seda aka basa iznin shiga. cike da makirci wannan bawa ya shiga makwancin yarima ishaq inda ya iske sa tsaye a bakin window yana sanye da Kayan sarauta gashin kansa se daukan ido yake.

“ Ina me miko gaisuwana a gareka yariman da bayida tamka “.

cikin salo irin nasa na tsantsan mulki da izza ya juyo ga wannan bafaden kafin daga bisani ya zauna akan lallausan kujera yana daura kafa daya kan daya

“ me ke tafe da Kai”

Sake rissinawa ya yi kamar ze masa sujjada yana me miƙa masa wayar sa,karban wayar yarima ishaq yai duk da be san menene a ciki ba. Abinda idonsa ya ci Karo dashi ya matukar basa mamaki domin kuwa beyi zaton wannan shine abinda ze gane wa idanunsa ba. Nan take ya ji wani kuna hade da bakin ciki ya dabaibaye sa.a fusace ya mike kamar mayunwacin zakin da ya jima be ga abinci ba shi Kansa bafaden da ya kawo tsegumin seda ya tsorata.

“ Dama na san ruwa ba ya taɓa tsami banza,yanzu akan wannan wulakantaccen bawan gimbiya Muzna take yi mini wulakanci akan wannan?,Aina ka gan su ??”

Ya tambayesa yana daka masa razanannen tsawa

“ a cikin lambu ,Allah ya wuce zuciyarka amma ni a nawa gani wannan abinda gimbiya take yi zubarwa da wannan ahali mutunci take yi,Tana yar sarki jikar sarki,tattaɓa kunnuwan sarki. me kuma za tayi da bawanta,Kai ne nan ka dace da ita,matashi me jini a jika,ga kyau ga naira ga kuma Mulki da ya bi Jinin jikinka,wannan bawa ya cancanci hukunci me tsananin gaske “.

Tabbas wa'yannan kalamai da ya fada sun matukar yin tasiri a zuciyar yarima ishaq Wanda ya ji take kamar ya kashe Sadauki Zubair tsabar yanda wutar kishi ke balbaluwa a ran sa.

“ je ka zan ne me ka”
Fita ya yi sum sum yana me adduar Allah yasa ya samu tukuicin wannan labari da ya kawo.

Safa da marwa kawai yake yi a filin dakin nasa yana me cizon lips din sa na kasa.

Maganar zuci ya fara yana me gyada Kai
“ tabbas wannan cin mutunci ne a gareni a ce wacce nake so ta juya min baya saboda wani kaskantacce da ba kowan kowa ba,.Gaskiya bazeyu ba dole in takawa abin burki dole ne in mallaki gimbiya Muzna in kuma ba haka ba,ta biya rashin amincewarta da rayuwar shi masoyin nata “.

Wannan sune ire iren zantattukan da yarima ishaq yake.


" Menene ya faru mako guda har suka shude ban samu haduwa dake ba ?”.

“ maahaifiyata ce ta koma ga mahaliccin mu “.

Cikin tausayawa ya furta “ Ina me miki taziya Allah ya gafarta mata”.

“ nagode, na yi kewar Yumma sosai Fatan Tana lafiya?”.

“ lafiyan ta kalau,babu ranar da ze zo ya shude bata tambayeni Ina ki ke ba”.

Murmushi tayi Allah ya sani tana matukar kaunar tsohuwar sosai Tana Jin ta aranta.

Jin tayi shuru ne yasa shi furta “ ko za ki je ku gaisa ne ?”.

Slowly ta dago da cute face din ta,ta ɗaura akan nasa fuska a marairace ta ce “ yakamata domin na kwan da yawa ban sa ta a ido ba ".

Rakasa tayi har murin dawakai ya mayar da dokin da ya ɗauko sannan su ka tafi gidan su. Sosai Yumma ta yi farin cikin ganin Muzna. A gidan ta wuni cur anan tayi sallah har lokacin da Yumma ta gama abinci ta saka musu tare suka ci su uku,kun san larabawa babu ruwan su da wannan kunyar surkanun nan. Ba tare da nuna kyama ba ta ci abincin sosai,se bayan sallah mangriba tukuna ya rakata sashen manyan bayi.

A falo ta iske waziri Abdul Qadeer da kuma Galadima abdul aleem,ko da jin motsin mutum yasa suka ɗago suna kallon ta.

" ƴata daga ina haka !?".
" na jima ban fita bane hakan yasa na je shan iska".

" zo ki zauna to ". Zama ta yi a kusa da galadima.

" ina yar uwar ki take ko tare ku ke da ita?".
waziri ya tambayeta .

" nima yau sam ban sanyata a idona ba,nafi tunani tana bangarenta "

Cikin gamsuwa ya jinjina Kai kafin ya ce “ shikenan in mun hadɗu a wajen cin abincin dare akwai maganar da zamu yi gaba daya dangane da ku”.

“ Allah ya Kai mu” ta faɗa tana me kuma cewa “ zan iya tafiya? “.

Bayan sun bata iznin tafiya ne ta miƙe Kai tsaye sashen Muzaina ta nufa shigowanta ya yi dede da fitowar Muzaina daga wanka tana me ɗaure da towel fuskarta a dan kumbure kadan ga dukkan alamu daga bacci ta farka.

“ Uhmm kar ki ce min daga bacci

Please Login or Register in order to submit comment