Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama se kyalli yake yi ga shi baki kirin.bayan an gama gyaran gashin ne suka fara kokarin mata kwalliya dakatar dasu ta yi ta hanyar girgiza musu Kai alamar bata bukata,cikin bin umarni suka gyada kai. Da hannunta ta sanya kazal a dara-daran idanunta se kuma lipgloss da ta shafa.fuskarta fayau se ainihin wutar kyawunta ya sake bayyana.
Wata ce ta shigo da wani azababben doguwar riga me nauyin gaske saboda yanda yasha duwatsu masu tsada manya da kanana ko wani lungu da sako na rigar nan yasha fararen duwatsun lu’ulu’u se sheki suke yi yana da girma sosai rigar yana sakale a jikin hanger.rigace irin wa’yanda ainihin hamshakan sarauniyoyi suke sanyawa wa’yanda suka isa.Taimaka mata suka yi ta sanya rigar da ya kasance me doguwar hannu daga saman kirjinta zuwa cikinta ya rike ta tam,amma daga cikin nata rigar ya bazu k’asa sosai saboda yana da faɗi.zama ta yi bayan sun sanya mata shi,nan suka ɗauko trays din da suka fara shigowa dashi wasu irin manyan sarakunan zinari masu nauyi da tsayi hade da jan hankali aka sanya mata a wuya kasancewar sarkan nada tsayi ne yasa ya sauko har cikinta,aka sake ɗauko mabi dashi aka sanya mata sannan Karami a cikin su.dan kunnensa da ya kasance me nauyi shima aka sa mata,hair chain me design din gashin dawisu aka sa mata a gashinta dake kwance luf ya kwanto har kan cikinta,sarkan hanci da ya kasance mahadin sarkan gashin na ta aka sanya.bayan an sanya mata sarkan ciki akan rigar ne wata yar kyakyawa a cikin su ta dauki sarkan kafa da niyar sa mata,zama ta yi a k’asa ta ɗauki kafar sarauniya Muzna ta daura akan cinyarta ta soma saka mata na kafar dama,kallon ta Muzna tayi kafin a hankali ta furta

“ ya sunan ki”. batare da ta ɗaga Kai ba ta amsa mata da “Sunana Marwa.”

Bata sake cewa komai ba tana kallon ta,har ta gama saka mata sarkan kafar a dukkanin kafafunta biyu,wani box ta buɗe takalmi half cover ne da aka yi sa da zallar gold ya bayyana ga duwatsun takalmin ya kasance irin kayan da sarauniya Muzna ke sanye dashi wato dark blue da golden se kuma ratsi-ratsin fari,yana da tsayi amma sosai takalmin kan sa abin kallo ne balle kuma rigar da take sanye dashi.
Miƙewa tsaye ta yi aka kuma buɗe wani tray se ga wani wuka da shima kallo daya zaka mai ka fahimci na zinari ne ya bayyana a cikin gidansa in banda walwal babu abinda yake yi yana nan madedeci.

Shafa wukar tayi,sosai ya burgeta musamman yanda ya kasance matsagaici bashi da girma sosai ga gidansa da aka yi wasu irin zane a jiki me wuyar fahimtar menene aka zana .

“ Wow wannan takobi ya yi kyau,amma meyasa aka saka sa acikin kayan da zan sanya?”
“Ya shugabata wannan makami ya kasance mallakin ki ne a koda yaushe ze kasance a tare da ke ne.” Cewar Marwa.

Murmushi ta mata kawai,daukan wukar ta yi ta sanya mata shi a jikin rigar ta da ya kasance akwai guri na musamman da aka tanadarwa tokobin a jiki,wani mayafi blue me shara-shara yana da duwatsu a bakinsa gaba daya,aka dofana mata shi a saman gashinta sauran kuma ya tafi baya yana ja da kasa.kamshin perfumes dake tashi a jikinta kuwa kamar zeyi magana.Masha Allah Sarauniya Muzna tayi masifar kyau ga wani daukan ido da Kayan dukiyar dake jikinta yake yi se walwal suke ko makaho inta tsaya kusa dashi tabbas se ya san tare yake da sarauniya,ga wani gwarjinin da ta ƙara.


Yarima Farasat yana kwance akan gadon sa abin duniya ya ishe sa tun jiya yake cikin damuwar tafiyar Muzaina gaba daya ya susuce ya shiga tunanin aina ze samo ta hakan ne ya haifar masa da ciwon kai haɗe da rashin karfin jiki dan in be yi karya ba ze iya cewa ma bayida lfy,tsoro yake kar ta je ta faɗa mugun hannu ko kuma wani mugun abu ya same ta,Allah shine shaidan sa yana matukar kaunar Muzaina.son da yake mata baze taɓa iya fasaltuwa ba. Saboda yanayin da ya ke ji yasa ya hana kowa shigowa bangarensa tun daren jiya.ko da dare ya yi be rintsa ba salloli ya yi haɗe da yin addua Allah ya kare masa sahibarsa.

Duniyar tunanin da ya faɗa ne yasa be ji knocking door din bedroom din sa da ake yi a karo na hudu ba,knockkng da ya yi yawa ne ya dawo dashi tunanin sa hakan yasa ya ce

"bana ce kar wanda ya shigo min ba?"ya tambaya a tunanin sa masu gyara ne ko masu kawo abinci.

“Farasat! Haysam ne zan iya shigowa ?”

“Okay “ da sallama ɗauke a bakin sa ya shigo yana bin bedroom din da kallo kafin ya Kai idanun sa kan yarima Farasat dake kwance da mamaki ya isa gadon yana zama a bakin yasa hannu ya taba sa.

“Farasat shin menene abinda yake damunka?ga shi ko shiryawa baka yi ba ko shin ka manta cewa yau ne za a rantsar da Muzna a matsayin sabuwar shugaba a Bayaan ?”

“Haysam ba na jin zan iya fita komai ba ya min dadi,ka je kawai.”
“ shin ko kana damuwa akan bacewar gimbiya Muzaina ne?in sha Allah za ta dawo.abinda ni na fi yarda dashi shine tayi fushi ne amma daga zaran ta wuce Ina me tabbatar maka da za ta dawo cikin aminci.abinda nake so dake yanzu shine ka yi hakuri ka shirya mutafi please my bro”ya faɗa ta tsigan magiya. se da ya dau kusan mintuna uku kafin ya miƙe ya shiga toilet ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kayan sarauta me tsadar gaske shigen na jikin yarima Haysam ya matukar amsar sa bayan ya kammala suka tafi.

Tafiya take yi kamar wacce take tausayin taka ƙasar,hakan ya samo asali ne ta dalilin nauyin da kayan jikinta yake dashi ga kuma takalmin kafarta da yake da tsayi sannan ga ido da take ji yana mata yawa a jiki bugu da Kari kuma yau ta tashi da rashin karfin jiki,gabanta da bayanta bayi ne masu sanye da Kaya Kala daya mata zalla da suka zagaye ta,mutum biyu rike da mayafinta dake ja a ka’sa ta baya,se kuma bodyguard da suke sanye da bakaken suit a gabansu,a yayinda sarauniya Muzna ta kasance a tsakiya. Buɗe musu gate din palace aka yi suka shiga cikin tafiya me cike da nutsuwa. Tunda suka tako kafarsu a ciki mutanen dake cikin fada gaba daya suka miƙe tsaye domin nuna girmamawa ga sarauniya hatta sheikh Abu Dhabi se da suka mike.

Ga sojojin Bayaan dake kame guri daya suna sanye da Kayan yaƙi ko wanne ka kalla zakagan sa da makamai a tattare dashi.a tsakiyan su kuwa commander sune wato Sadauki zubair cikin shigarsa shima na Kayan yaki kan sa sanye da hular sa me kan damisa,ko da ta had’a ido dashi murmushi me sanyi ta sakar masa,kasancewar fuskarsa na cikin wannan hular bata iya ganin komai face kyawawan idanunsa hakan yasa bata gano murmushin da shima ya sakar mata ba.dakatawa wa’yanda suke takewa sarauniya Muzna baya suka yi suka tsaya a tsaye kamar gumaka har ta haura kan inda kujerar Bayaan yake da aka sake masa ado yafi na da kawatuwa,wani fisganta kujerar taji yana yi kamar magnetor tun kafin ta kai ga zama,ji tayi kamar ana jawota izuwa kan wannan kujerar duk da haka ba ta yi saurin zama ba domin tabar mutane tsaye dole se ta basu umarnin zama kafin su zauna hakan yasa ta had’a hannayenta guri daya alamar godiya sannan ta zauna bakinta dauke da bismillah tana zama ta dena jin wannan fisgan da ake mata.
Se da ta zauna kafin suma suka zauna,wani Malami ya tashi ya yi mata addua sosai tare da kasar su ta Kuwait dama masarautar su me albarka. Manyan masu mukami da kananun sarakunan dake yankin Kuwait da shugaban kasan Kuwait sun yi gajeran bayani da kuma tayata murna ,amintacciyar baiwa ta zo da madaidaicin tray wanda ke dauke da hular sarauta me tsananin kyau da daukan hankali,tsaya wa ta yi a gefe kafin daga bisani waziri Abdul Qadeer ya taso ya iso inda suke ya ɗau hular ita kuma ta tafi,ɗaga hular sama ya yi yay addua kana ya sauko dashi,matsowa ya yi kusa da ita ya ɗaura mata hular akai tafi aka sa ,kowa ka gani fuskar sa da murmushi musamman su Jadwah se washe hakora suke yi.
Wannan hular ba karamin kyau ya yi wa Sarauniya ba nan ta sake fitowa a asalin Sarauniyar ta.ko motsi me kyau ba ta iya yi se lumshe idanu kawai.
Shigowa aka yi da abun sha aka soma rabawa mutane da snacks na alfarma,daga nan kuma masu rawa da raye-raye suka shigo suka soma rawa da waka,kamar yanda ku ka sani kungiyar wasan kwaikwayo ta labarci a Kuwait ta kasance wani babban bangare na rayuwar al'adun larabawa na ƙasar.shisa a duk wani muhimmin abu da za a yi se an yi wannan al’adun da ya kasance na wasan kwaikwayo.
Kusan awa biyu ana ta raye-raye,wasu sun tashi sun shiga ana rawa tare da su wasu kuma suna hirar rayuwa haka al amarin ya kasance.bayan sun gama ne aka sallame su da tarin kyaututtuka masu yawa domin jin dadin nishadantar dasu da suka yi.
Se bayan da aka gama nutsuwa tukuna aka mike tsaye a domin rantsar da ita,inda aka ajiye Qur’ani me girma akan wani glass table me tsayi.wannan malamin dazun da ya yi addua shine yanzu ma ya iso inda glass table din yake.a hankali ta isa gurin ta tsaya faɗa mata yai duk abinda ya faɗa itama ta faɗa,kawai nodding head na ta tayi.

“Ni Muzna Taifur Rahman “
Nanatawa ta yi “Ni Muzna Taifur Rahman “

“Nayi rantsuwa kuma na yi alkawari .”

“Nayi rantsuwa kuma na yi alkawari “

“Zan bi dukkanin doka da ka’idojin da suke wannan masarauta kamar yanda yake a gindayance tun kafin in hau sarauta,ba tare da jin babu dadi ko kuma jin haushi araina ba,sannan na yi rantsuwa da kuma alkawari zan kare wannan masarauta da duk karfina,da duk lafiya ta,da duk abinda na mallaka,zan kare hakkin wannan k’asa da masarauta da kuma duk wani abu me rai da ke cikinsa daga kan mutane,dabbobi,da kuma mutanen boye.zan tsaya da kafafuwana gurin ganin na wanzar da adalci, farin ciki ,nutsuwa ga mutane na,bazan taɓa barin mugun abu ya same su ba.bazan yarda wani mugun bata gari ya shigo ya tarwatsa wannan masarautar na wa ba,ko da kare masarautar nan shine abu na karshe da zanyi bazan taɓa janye kalamaina ba har karshen numfashi na.”
Ƙara sanyi jikinta yayi,bu de baki tai zata yi magana muryarta ya soma shaking se kuma hawaye ya soma zuba a idanun ta gaba daya she’s so nervous,.

“Sarauniya ki dedeta nutsuwar ki” Cewar malamin
Numfashi ta ja sannan ta sauke slowly sannan ta ce

“Zan bi dukkanin doka da ka’idojin da suke wannan masarauta kamar yanda yake a gindayance tun kafin in hau sarauta,ba tare da jin babu dadi ko kuma jin haushi araina ba,sannan na yi rantsuwa da kuma alkawari zan kare wannan masarauta da duk karfina,da duk lafiya ta,da duk abinda na mallaka,zan kare hakkin wannan k’asa da masarauta da kuma duk wani abu me rai da ke cikinsa daga kan mutane,dabbobi,da kuma mutanen boye.zan tsaya da kafafuwana gurin ganin na wanzar da adalci, farin ciki ,nutsuwa ga mutane na,bazan taɓa barin mugun abu ya same su ba.bazan yarda wani mugun bata gari ya shigo ya tarwatsa wannan masarauta na wa ba,ko da kare masarautar nan shine abu na karshe da zanyi bazan taɓa janye kalamaina ba har karshen numfashi na.”
“Allahu akhar “ kowa yake faɗa cikin jin dadi.

ina son yin amfani da wani dama wajen isar da sakona,wa’yanda su ka bibiyi littafina na Ashe zamuga juna sun san irin tsarin da nake posting.a sati sau uku nake update banda weekend,a wannan kwana ukun Ina yin 6 pages wato in nayi pages biyu yau bazaa yi Gobe ba se jibi.to wannan Karon ma haka za a yi domin Ina da nawa uzurin in na ce zan takura kaina kullum se na muku update gaskiya baza ku dinga samun update ba sosai.

Daga yanzu zaa koma posting 6 pages sau uku a sati thank you.


don't forget to comment,like and share fisabilillah ❤️😍👍

Allah yasa muyi kyakyawar karshe.
https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207


⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚📚🖋️⚜️





❤️🔥Page 21





ONE MONTH LATER


KINGDOM OF WISDOM


“Mommy ni fa ku dena min maganar yarinyar nan, bana son ta kuma bazan taɓa auren ta ba. da nasan za ku matsa min da bazan taɓa dawuwa wannan k’asar ba,kuma in dad ya dawo ki faɗa masa na tafi na koma.”Cewar Jay da yake tsaye akan excellency Katrina se faman masifa yake yi saboda president David ya tabbatar masa da gobe ne za a yi masa baiko shi da princess Gabriel hakan yasa yake ta musu masifa kamar shi ya haife su basu suka haife sa ba.

“Jayson ka bari idan mahaifinka ya dawo se ka yi masa amma ni yanzu banida rights din da zan baka goyon bayan dakatar da wannan baiko,tun kuna yara Queen Jessica da president suka yi alkawarin aure a tsakanin ku.ta ya ka ke so a janye wannan magana cikin sauki?ni yanzu zan shiga ciki “ta gama tana miƙewa tsaye.

“Mommy tunda haka ku ka ce ni zan samu ita Gabriel din in na mata rashin mutunci nasan za ta ji bata kwadayin aure na kuma in ba ku janye ba zan ba ku mamaki “. Ya fice a fusace girgiza Kai ta yi tana me shigewa part din ta.


Yana fita compound din gidan securities suka nufo sa tsabar bacin rai ko bi takansu be yi ba ya faɗa motar ya bar gidan cikin mahaukaciyar driving.

Gudun da yake zubawa ne yasa ya yi saurin isa kingdom of wisdom cikin kankanin lokaci,dake an san shi hakan yasa ba su yi yunkirin dakatar dashi daga shiga ciki ba,yana shiga main part direct part din da ya kasance na Princess Gabriel ya nufa luckily ya same ta tana latsa wayarta,jikinta sanye da doguwar wando na pencil da riga yar karama.ba ta san da shigowar mutum ba kawai se ji ta yi ya furta

“Wato ki na nan hankalin ki kwance saboda za a yi miki aure da ni,to bari in faɗa miki abinda ba ki sani ba ni Jayson David ko da mata sun kare gaba daya a duniya bazan taɓa san ki ba balle har in aure ki”.

Dariya ta tuntsire dashi ta isa inda yake tsaye tana masa kallon sama da k’asa
“ yanzu kai in wani ya ce maka zan so ka zaka yarda ?sannan da ka ke maganar ko da matan duniya sun kare bazaka aure ni ba kai a tunanin ka in ba taimaka maka aka yi ba akwai abinda ze sa in kalli ko da inuwarka ne ? Kana jiji dakai bayan Kai ba wani kyau ba ba komai ba se jiji da kan tsiya.”

A duniya tun da yake a taɓa faɗa masa mugayen kalamai irin wannan ba se yau,babu wani mahalukin da ya taɓa yunkurin ko da nuna masa yatsa ne balle faɗa mai wa’yannan maganganun.taku biyu zuwa uku ya yi ya shigo dakin ya je har gaban gadon ta ya tsaya yana bin ta da kallon tsana ganin ya tsaya Akan ta ne yasa ta ajiye wayarta ta sauko a kan gadon ta tsaya gabansa itama tana kallon sa ido cikin ido kamar yanda yake kallon ta.

A cije yana fisgar maganar ya furta “Na tsane ki Gabriel uwa merry se ta kwashe miki albarka “

“Haka nima na tsane ka albarkar dake tare da Kai duk se sun tagayyare “ ta faɗa tana galla masa uwar harara.
Wannan ba shi ne na farko ba ƙiyayya ce tun na yarinta tun tasowar su ba su son juna ko kad’an tsanar ya kuma yin karfi ne a lokacin da suka samu labarin shirin aure da ake yi musu.

“Dama daya ki ke dashi gobe wajen yin wannan baiko in har pastor ya tambaye ki kina son wannan baikon ko ba Kya so ki taimaki kan ki kice baki amince ba,agaban jamaar dake cikin church,in kuma ba haka ba zan tabbatar da rashin jin dadi a rayuwarki ta har abada.”
Cike da izza ta matso gab dashi kamar wa’yanda suke shirin haɗa jiki ta soma magana cikin nutsuwa da sanin hanyar kuntatawa mutum.

“Zan kuwa tabbatar da na yi hakan,bazan taɓa barin a haɗa ni da Kai ba a matsayin abokin rayuwa ba,ka sa ido ka kalla a gaban idon ka zan zabi bawa akan ka,na gwammace in auri bawa mara daraja da tushe da in kasance da Kai. se na nuna maka kaskantaccen bawa ya fi min Kai sau dari million.”

“Gabriellllll” ya Kira sunan ta a fusace haɗe da dunkule hannunsa yakaiwa iska naushi.tana tsaye a gabansa ko motsi bata yi ba se ma kallon idonsa da take cikin rashin fargaba.

“Zan tabbatar da na hukuntaki zan nu na miki ni ne nan shugaban k’asar England na gobe”
“Ni kuma nice sarauniyar England me jiran gado” ta tari numfashin sa.

A zafafe ya juya ze bar dakin nata ya ci Karo da Uncle Joseph dake tsaye a bakin kofar ya gama Jin duk abinda suka tattauna,ko kallon Joseph be yi ba ya raba ta gefensa ya wuce,da kallo kawai uncle Joseph ya bisa har ya yi nisa. Cike da makirci ya karasa shiga dakin nata ya ɗaura hannunsa akan kafadarta domin bata san da wanzuwarsa a dakin ba.
Koda ta juyo ta ga shine nan take ta soma zazzaga buhun masifa kamar shine ya aiko Jay ko kuma shine ya mata wani abu.

“Tirrr. Ka ga abinda mommy ta ja min ko?duk wani abu da ze faranta min sam bata kaunarsa,tasan kan hanya da zata bi domin ganin ta bakantamin,yanzu ka duba ka ga yanda wannan mara mutuncin ya shigo har cikin masarautar mu ya gaya min magana..kuma ba kowa bane ya bada kofar haka ba face yar uwar ka…tir da wannan rayuwar da mutum bashida yancin kan sa.” Ta karasa maganar a masifance.
Murmushi ya yi Wanda shi kadai yasan ma’anarsa ya jawota suka zauna a kan royal bed.

“Shin in faɗa miki wani sirri?” Ya tambayeta yana kallon fuskarta.

“Uncle Joseph rai na a matukar bace yake ka adana wannan sirrin ba yanzu ba tukuna.”

Murmushi ya sake saki a Karo na biyu “Wannan sirrin ze matukar nishadantar dake,amma in bakya so zan iya ba ki guri”ya miƙe still looking at her facial expression.

Jin da tayi yace abinda ze faɗa mata din ze nishadantar da ita ne yasa ta riƙe hannun sa “ ka yi hakuri uncle Joseph Ina cikin fushi faɗa min Ina Jin ka”

Bayan ya koma ya zauna ne ya ce “shin ko kin san mahaifiyarki na shirya miki bazatar barin wannan ƙasa zuwa yawon buɗe ido a kasashe mabambamta?”wani ihu ta saka ta miƙe tsaye tana tsalle haɗe da faɗawa jikinsa tana dariyar Jin dadi.

Se da ya bari ta soma tsagaita wa da dariyar kana ya kuma faɗin “za ta ba ki damar haka ne kadai in aka yi baikon ku ke da Jayson zaku fita yawon cin amarci kafin aure.” lokaci daya duk wani walwalar dake kan fuskarta ya gushe kamar ba yanzu ta gama tsalle da ihun murna ba.

“Tirrrr.,a rasa da wanda za a haɗani se da wannan mara mutuncin?! bazeyu ba”

“Ki tsaya ki gama saurara na wannan wata dama ce da ze amfane ki domin fita yawon bude ido da ki ke muradi,kin sani sarai ko mutuwa za ki yi mahaifiyar ki bazata amince ki fita daga wannan kasar ba dole se da wanda ta aminta dashi kuma ta yarda ze zame miki kariya.mafita daya gare ki gobe ki amince kawai a yi muku baiko ke da Jayson ta haka ne za ki samu ki bar kasar nan,domin kuwa wannan bazatar an shirya sa ne bayan baikon ku da wata daya rak.ni kuma duk kasar da ku ka je zan tura mutane na se su dauke ki su Kai ki airport ki hau jirgin duk ƙasar da ki ke so “

Tunda ya soma magana ta ke gyada mai kai domin 100% ta aminta da plan din sa,ta kuma sawa ranta hakurin yin baiko da Jayson a domin cıkar muradinta.

“Gaskiya na matukar jin dadin wannan shawarar taka uncle Joseph,kuma zanbi hakan.ban taɓa sanin kana so na ba se wannan karon “ ta rungume sa bayan ta gama magana.
Ran sa fes se murmushi yake yi cikin sauki ya yi amfani da yarintar ta da kuma rashin wayonta ya samu abinda yake bukata.

9:00Pm lokacin ne president David da matar sa da Jay suka gama addua a gaban gunkin Jesus dake babban falon su,dama haka ya zame mu su dabi’a duk karfe taran dare bayan sun ci abinci za su zo gaban gunkin su yi addua sannan su je su kwanta ko kuma su yi hira,ko da suka gama Jay miƙewa ya yi ya bar su a gurin ya nufi part din sa domin tunda ya dawo ya ƙi kula kowa saboda haushin su da yake ji.

“Jay fushi yake yi da mu saboda maganar baikon gobe”Cewar Katrina
“Ina sane amma wannan baiko da kuma auren dole se an yi sa”ya faɗa yana tafiya shima.

Koda ya kwanta bacci kauracewa ganin sa ya yi duk wani dabaru da ze yi dan ganin ya yi bacci yayi amma sam beyi aiki ba,bakomai ne ya tsaya mai a rai ba irin yanda princess Gabriel ta ce da ta kasance dashi gwara ta kasance da kaskantaccen bawa,wannan magana yafi komai bakanta mai nan ya sake jin sabon tsanarta a ransa.ga wani karin bakin ciki gobe za a musu baiko amma in ya tuna kan cewa bazata amince ba se ya samu relief.a haka ya samu bacci ya yi awon gaba dashi.


Mumunanan halittu da su ka kasance wasu abun tsoro a idanun bil adama. Ga kuma dabbobi masu hatsarin gaske sun kewaye su gaba da baya babu hanyar kuɓuta se kawo musu hari suke,Cike da tashin hankali yake kallon wa’yannan munanan halittu yana zare ido domin be san ta Ina ze fara ba shi ba makami ba bakuma wai ya iya faɗa ba balle ya bawa kan sa kariya. yasan kawai nasa ya kare a yau din nan,farmakin da suke kawowa ya jijji masa ciwo a gadon bayan sa se zubda jini yake amma ya ɗaure yana tsaye akan kafafunsa duk da cewan yasan baze iya taɓuka komai ba hakan yasa ya sadakar kawai. Ji ya yi an take masa kafa cikin tsoro ya daka tsalle ya koma gefe yana juyawa domin ganin menene haka.karo suka yi da ita tana tafiya cikin sanda-sanda tana kewaye gurin cikin salo irin na jarumai,duk da tashin hankalin da yake ciki amma hakan be sa ya daskare yana kallon ta ba,fara ce sol kyakyawa yanda baa tunani tana sanye da fararen kaya day. masu tsantsi doguwar riga me filla-filla a jiki iska se kada su yake suna bin iska bayanta goye yake da kwari da baka se hannun ta da take rike da zarbalelen wuka sabo.rigar da take sanye dashi yana da hula da ya rufo mata fuska gashinta ya zubo ta cikin hular ya fito.

Wani dabba ne yakai masa wawura cikin azama da zafin nama ta kaiwa dabbar sara da wukar hannunta. Sauran dabbobin ganin hakane yasa duk suka yo kanta babu kakkautawa ta fara raunata su da tokobin dake tare da its, yanda take kashe su cikin salon jarumta kaɗai abin kallo ne.duk yawansu haka take far musu da tokobin dake tare da ita ,kayan jikinta da suke fari tas nan take suka koma ja tsabar yanda jini ya bata su hannun ta ya jike da jini.

“Ka bawa kan ka kariya “ ya jiyo siririyar muryarta na faɗa masa,kallon gefe da

Please Login or Register in order to submit comment