Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“ku saka musu kaca sannan ku kai su kurkuku gaba dayan su a can nake so su ƙare rayuwarsu,ita kuma inaso kejin da zaku saka ta ya fi na ko wannen su matsi da kankanta a can za ta ƙare rayuwarta ko abinci ban yarda a dinga kai mata ba har se yunwa da ƙishin ruwa ya kashe ta”
Cikin bin doka da oda na ta suka ɗaure ko wannen su da kaca. Muzna da idonta yake kan gawar Sadauki Zubair ko kyafawa ba ta yi kukan da take yi ma nemansa ta yi ta rasa.

“Karyar ki ya sha karya yake me son zuciyarta da bakar rai,ba ki isa ki kai sarauniya da manyan fada izuwa kurkuku ba”cewar sheikh Abu Dhabi da ya bayyana a gaban su yanzu

Murmushin gefen baki ta yi “dama ina jiran ka maci amana kuma na san zaka zo “

Sandar hannunsa ya ɗaga ya nu na ta dashi wani haske me kama da walkiya ya tunkareta.

Ɗaga nata sandar ta yi tarin tsafin dake ciki ya fara fita a ciki yana tare hasken da yafito daga sandar sheikh Abu Dhabi seda karfin sa ya kare ya wurgar da sandarsa nata tsafin na shiga jikinsa cikin azabar da yake sha ya ce

“In sha Allah Allah baze taɓa ba ki nasara ba ke shaidaniya “

Dariya ta yi ta sake matse sandar nan take ya faɗi ƙasa a mace.

“Dama na faɗa muku dawuwata baze muku dadi ba....ƙadan daga cikin rashin imani na kenan ku wuce da su kurkuku”kamar wasu bayi aka dinga jan su a ƙasa ana wucewa dasu.

Da ido ta kunce kacar dake ɗaure da yarima Farasat su kuma sauran aka wuce da su kurkuku.da mugun kallo kawai Yarima Farasat yake kallon ta kallo na tsana.

“Allah ya la’ance ki Muzaina tirr da wannan halin na ki “.



Hakikanin gaskiya page din yau yafi ko wanne zafi🥹🥹🥹 Allah ya gafartawa commander sojojin Bayaan sadauki Zubair da kuma mukarraban sa.


Don’t forget to share like and comment.

Tabbas duk wanda be biya kudin littafin nan ba labari ya wuce sa.
Se jibi in me duka yakaimu.

https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207

👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚📚🖋️⚜️


❤️🔥Page 27—28–29


Date:❤️ 23/08/2024❤️


*End of free pages*

ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN NAGODE WA ALLAH DA YA BANI DAMA DA IKON KAMMALA BOOK ONE DIN ƊAYA CIKIN BIYU🤲🏼🥹❤️😊se mun haɗu da ku a book two.


*Kamar yanda ku ka sani wannan littafin paid book ne,yanzu an gama free book ya ƙare,ya kamata ku hanzarta ku biya.
*Ga duk me son biya, littafin ƊAYA CIKIN BIYU naira ₦300 ne only ga mutane 20 da zasu fara biya yanzu,zanyi discount ne ga first mutane 20 da zasu yi payment wayanda suka zo abaya zasu biya darı biyar ne 500,dan haka ku hanzarta kar wannan damar ya wuce ku☺️☺️☺️😘. Za'a biya via opay account 8166018849 Aisha Abbas bidami opay account,idan mutum ya tura da kudin se ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta whatsspp number ta 08166018849 or 09024503194 Mrs isham.
Ga wa'yanda basa iya tura kudi ta opay account,zasu iya sawa ta wannan account din 9132302657 Aisha abbas bidami Palmpay account,duk wanda ya tura ya yi screenshot na evidence of payment ya tura min.
Kar ku bari wannan labarin a yi sa batare da ku ba❤️😘yan Nijer kuma su min magana.


Tunda ga wannan rana Muzaina ta karɓi sarautar Bayaan tana baza mulkinta son ranta,masarautar gaba daya ya tarwatse duk ta mayar da mutanen ciki kaskantattun bayi marasa daraja,kullum cikin bauta su ke in kuma ba su yi abinda aka sa su ba haka sojojinta za su azabtar dakai har se ka ji duniyar ya dena maka dadi,sojojin ta ne suke abinda suka gadama son ransu.Ummu zaheenat,Ummu Zulaihat,Jadwah,Aliyah ta mayar dasu bayi ba su da ikon yin komai ba tare da an ba su umarni ba. dukkansu da uniform din bayi suke rayuwa sun rasa yancinsu na ahalin Rahman gaba daya sun jame sun koɗe kamar ba su ba,tsabar mugunta ko dare ya yi ba ta barin su su yi bacci haka zata sa su sharan filin dawakai ko kuma ta turasu daji yin gyaran ciyawa,abinci sau daya suke samu a rana in suka ci na safe to kuma se gone,haka zalika ruwa ma se karshen sati-sati take bada umarni a buɗe Dam kuma ko an buɗe iya bucket daya kowa ze ɗiba dana sha da na wanka,haka in aka rufe Dam din babu wanda ze sake samun damar yin wanka se wani sati ya zagayo,bayın da suke dafa abinci da kansu amma basa da ikon ci kuma duk wanda ya ci ya ciwa kan sa mutuwa ne da kansa. dan babu ruwanta da tsufanka haka zata saka sojojinta su maka duka har se ka mutu,Masarautar Bayaan gaba daya ya susuce ya ɗaiɗaice babu me shiga haka zalika babu me fita, tsantsagwaran zalunci kawai take yi babu sani babu sabo babu kuma tausayi,Yarima Farasat duk yanda yake son ganin ya taimaki ahalinsa babu hali domin ta toshe duk wata hanya ta mayar dashi ja ni talau babu abinda ya ke iya taɓukawa saboda ta cire masa zafin zuciya da kuma rufe masa baki akan yi mata turjiya da jayayya,se de wani lokacin ya je ya tsaya akan su ya yi ta kuka yana ganin suna kukan yunwa amma babu abinda ze iya yi akai se de in ya faki ido ya kawo musu rabonsa haka za su kakkasa kamar almajirai.
Wa’yanda ta ba da umarnin a saka su a kurkuku tun lokacin bata sake waiwayan su ba su ma abinci sau daya ake kai musu a rana kuma shima ba shi da yawa wanda ya gadama ya ci wanda ya gadama kar ya ci.kurkukun da su ke babu wadataccen hasken rana sanan tunda aka rufe su a ciki ba a sake waiiwayar su ba har rana me kama ta yau.
Yumma mahaifiya ga sadaukin sadaukai jajirtaccen namiji wanda ya mutu akan ceton al’umma ta yi kuka sosai na rashin ɗan ta. tun daga lokacin ta zama cikin kaɗaici ga ciwon da take fama dashi na damuwa babu me zuwa dan rarrashinta saboda kowa ta kan sa yake a wannan masarauta yanzu babu wanda yake cikin nutsuwarsa,wata hudu ta ɗauka tana bautar dasu amma ji suka yi kamar sun yi shekara hudu a wannan ukubar.
Tsananin horon yunwa da azabtarwa yara da manya se mutuwa suke wasu sun kamu da cutar yunwa mutane sun fita hayyacin su,amma duk da haka ko kana kakarin mutuwa ne se ka yi aiki babu yanda ka iya.

Jadwah na sanye da uniform gabanta katon bucket ne ga moopper a ciki tana durkushe ƙasa hannunta akan cikinta se juya Kai take yi tana ya mutsa fuska alamar akwai abinda yake damunta

Wani sojane ya zo ya tsaya akan ta cikin tsawa ya ce “Keeeeeee tashi ki yi aikin da aka sa ki ko kuma yanzun nan ki gane kuranki “

Muryarta na fita dakyar ta iya cewa “ka tausayamin wallahi ba zan iya tsayawa akan kafafuna ba jiri nake gani. ga cikina dake murɗawa rabona da abinci tun jiya bazan iya yin komai ba”

“Ko da mutuwa ki ke kokarin yi ya zama dole ne ki yi aiyukan ki yake kaskantacciya kuma wulakantacciya” ɗago Kai ta yi tana kallon sa duk da fuskar sa na cikin hula,cikin tausayin kan su ta sunkuyar da kanta tana tuna yanda rayuwa ya juya musu baya tana jikar sarakuna yar gata a gurin iyayenta amma wai yanzu ita ce ke durkushe tana aiki kamar wata jaka,abincin da zata ci ma se ta roƙa kafin a bata nan ma se an mata wulakanci,yau ita ce aka wayı garı wani na kiranta da kaskantacciya nan take hawaye ya fara zarya a fuskarta wannan dama inda sabo ta saba wannan kukan,bama ita daya ba dukkansu kullum cikin kukan yanda rayuwa ya koma musu suke.

“Kafin in je in dawo ki tabbatar da kin gama Aiyukanki in kuma ba haka ba jikinki ze faɗa miki” ya faɗa yana tafiya.bata da wata hanyar da ya wuce ta yi aikin nata haka ta dinga yin mopping din da rarrafe tana yi tana hutawa dakyar ta samu ta gama,cikin rawar jikin ganin ta gama ba tare da ta ɗauke bucket din ba ta tafi inda ake raba abinci ta tsaya tana jiran layi yazo kanta.
"Kin gama dukka aiyukan ki na yau ?"gyada wa mai raba abincin Kai ta yi alamar eh batare da ya sake ce mata komai ba ya jefa wani yar karamar waina irin abincinsu na larabawa akan kwanon hannunta sannan ya saka mata miya da farar shinkafa.
Barın gurin ta yi ta tafi cikin palace din inda tasan an dasa Aliyah tsawon kwana uku saboda laifin da ta yi na rashin yin aiyukanta da aka sa ta,a gurin ta sameta a rakuɓe ta haɗa Kai da guiwa tana jin motsin mutum ta ɗaga Kai tana kallon Jadwah ce ta furta

“Jadwah dan Allah ki tafi kar laifina ya shafe ki” “bazan iya barın ki a wannan halin ba yau kwana biyu kenan ba ki ci komai ba. kuma wayannan marasa imanin ba baki abinci za su yi ba,yanzu ga abincina bari in baki ki ci”

Zama ta yi a gabanta ta soma ba ta har a baki har ta cinye abincin cikin damuwa ta ce “yanzu ke da ki ka bani rabon ki me za ki ci? Na san rabonda ki ci abinci tun jiya yanzu ga shi kin ban na ki “
Murmushin yaƙe ta yi tana “Kar ki damu...damuwa na ke kici kuma kin ci in sha Allah nan da zuwa dare na san yarima Farasat ze roki muguwa Muzaina ta cire wannan hukuncin da ta miki”

“Allah yasa,Ina su Ummu zaheenat ?”ta tambayeta “suna wanke wanke a madafa “cewar Jadwah

“Innalillahi wainnailaihi rajuun,har yanzu na ka sa gasgata wai mu ne rayuwa ta komar da mu haka. Mun koma wulakantattu a cikin masarautar mu Allah ina me rokonka da ka kawo mana wanda ze tarwatsa wannan zalincin Muzaina,Allah sarki sarauniya Muzna ko wani irin rayuwa ta ke yi a cikin kurkuku ?”shafa fuskarta ta yi “Allah na tare damu be manta damu ba komai ze zo karshe in sha Allah “


“Wa nene ya ba ki damar ciyar da ita bayan tana karɓar hukunci?”su ka ji muryar wani soja yana daka mata tsawa,a firgice ta miƙe tsaye tana girgiza mai Kai dan ta san yau Allah ne kawai ze iya kwatar ta

“Ka yi hakuri hakan baze ƙara faruwa ba”ta basa hakuri tana folding hannayenta.
“Ba ni ne ze yanke hakan ba sarauniya ce za ta yanke maza muje “ya karasa maganar yana damkar gashin kanta ya soma jan ta kamar kayan wanki.

“Ka rabu da ita batada laifi, ka yi hakuri kar ka sanarwa Muzaina”Aliyah ta faɗa tana kama kafarsa,duƙowa ya yi ya sa hannu yana matsa bakinta ya ce “ki kira sunan ta cikin girmamawa yake wawiya,ki kirataaa cikin girmamawa “ya tunkuɗata gefe ya ja Jadwah har cikin Fada in da Muzaina ke hakimce akan kujerar mulki tasha ado da golds ga hular sarautar Bayaan akanta fuskarta yasha kwalliya ta yi kyau se de babu ko da digon murmushi a fuskarta,. kujerar Galadima Abdul Aleem kuwa aljani gautam Suwami ne ke zaune haka kujerar Waxiri Ananniya yar sarki Damurdar da Muzaina ta dawo da ita wannan rayuwar ce zaune ita ma tasha ado da kayan sarauta ita ce ta zama na hannun damar Muzaina aljani gautam kuma na hannun hagunta. Se kujerar da sheikh Abu Dhabi yarıma Farasat ne ke zaune ya zuba musu ido,yana jin muryar Jadwah na kuka tana bawa sojan nan hakuri ya miƙe ya iso su yana riƙota ya gallawa aljanin harara

“Yarıma Farasat ka ba sa hakuri nasan nima hukuntani za a yi kamar yanda aka yi wa Aliyah”share mata hawaye ya yi ya ce
“Yi shuru babu abinda ze yi miki”

Muzaina dake hakimce ne ta kalli wannan aljanin nan ya sanar mata abinda ta yi na baiwa Aliyah abincinta.

“Keeeee wanene ya sa ki bawa wacce take karbar hukunci abinci?”
Tana ɓuya a bayan Yarima Farasat ta ce “bazan iya ganin yar uwata a wannan halin in gagara taimaka mata ba zata iya mutuwa saboda yunwa “

“To ta mutu mana waya damu?ke ma za ki karbi na ki hukuncin tunda kına da taurin Kai “
Ta faɗa tana ɗaukar bulalar wutar dake gefenta
“Ah ah Muzaina hakan sam ba adalci bane,abinda ki ke yi bayida kyau ki tuba tun kafin lokaci ya kure miki”

“Waye ya baka damar yi min magana irin haka Farasat?menene ka ke takama dashi?na barka a tare da ni ne saboda albarkacin soyayyar da ka nu na min kuma nake yi maka dabadan haka ba da kaima kana cikin kurkuku tare da ubanninka. Dan haka kar ka wuce gona da iri,dukkanin ku bayina ne dole ku bi umarni na in kuma ba haka ba zaku tsinci kan ku a inda ba ku yi tunani ba,dan haka ka miƙa ta ga wannan sojan ya mata bulala hamsin”

Cikin sanyin jiki da takaicin babu abinda ze iya yi domin taimakon ahalinsa ya matsa,cikin tsoro Jadwah ta rungumesa ta baya tana kuka
“Yarıma menene yasa ka ke tsoronta ita din ba kowa bace face azzaluma kuma babu abinda zata iya mana har se in Allah ya bata ikon yin haka”

“Wowwwww…wato bakinki baze mutu ba?,kai maza ladabtar min da ita”tai maganar tana wurgawa sojan bulalar wutar ya cabe ya ɗaga ze zula mata ya ji an riƙe kafarsa
“Dan Allah Muzaina ina me rokonki da ki kyale ta,ni ki hukunta ni “cewar Ummu zaheenat da ta riƙe bulalar wutar se kona mata hannu yake amma duk da haka ta daure ba ta sake ba.

Girgiza kai Jadwah ta yi tana hawaye “ah ah ummu bazan bari laifina ya shafe ki ba,wannan ba ta da imani,ni zan jure duk abinda za ta min “

“Banason shashanci ki sake wannan bulalar Zaheenat “sake bulalar Ummu zaheenat ta yi ta je gabanta tana me riƙe kafafuwanta haɗe da ci gaba da rokonta akan ta kyale Jadwah.
Runtse ido kawai ya yi zuciyarsa na masa radadi ji yake kamar yasha guba ya mutu da ya rinƙa ganin ana wulakanta masa mahaifiyarsa da kanwarsa.
Duk rokon da take mata bata ce mata komai ba,se ma zaman da ta yi tana buge hannunta da ta riƙe kafarta,kallon bulalar wutar tayi nan take ya dawo hannunta ta ajiyesa.

Yasan in ba ya kaskantar da kansa a gabanta ya roketa ba bazata kyalesu ba,yana haɗiye takaicinsa ya haɗe hannayensa yana faɗin “Sarauniya Muzaina ina me neman afuwarki akan abinda Jadwah da Aliyah suka aikata dan Allah ki yafe musu “

Murmushi me cike da nishadi ta sake ta ɗaura kafarta akan daya ta ce “Na yafe musu amma zan fanshe akan Muzna nan ba da jimawa ba”

Riƙe hannayensu ya yi suka bar Fadar shi da kansa ya je ya ɗauko Aliyah suka je bangarensa domin kuwa shi kaɗai ne yake kwana a muhalli me kyau a cikin su. ya karɓo musu abinci suka ci.

Haka suka ci gaba da wannan rayuwar kunci da azabar har na tsawon watanni shidda Kenan yanzu ba abinda ya sauya zani, abubuwan se ƙaruwa suke,tun suna sa rai da zasu samu taimako har suka cire rai suka fauwalawa Allah komai suka ci gaba da bautuwa ba dare ba rana.


“Sarauniya shin menene yasa ba za ki kashe ta ba kawai a wuce babinta,ko har yanzu kına jinta a ran ki kamar yar uwar ki ne yasa ki ka kasa fito da ita daga kurkuku ki kasheta?”Ananniya dake tsaye a dakin Muzaina take tambayar ta.
A fusace ta juyo launin idonta ya sauya ya koma ja,da hannu daya ta shaketa ta ɗaga ta sama kafafunta na rito a iska.

“Ita din ba yar uwata ba ce ba komai na bace,ni kaɗai na fito daga cikin mahaifiyata ,dan haka kar ki sake dangantani da wancan mara amfanin”ta faɗa da wani murya me ban tsoro sannan ta wurgata a cikin bangon dakin da karfi seda ginın ya girgiza.dakyar ta iya miƙewa zaune tana shafa wuyarta saboda shakar da ta mata bana wasa bane.

A kausashe ta sake faɗin “A yau din nan zan kawar da ita zan dena ganin ta har abada “tana gama maganar ta ɓace a dakin. miƙewa İtama Ananniyan ta yi tana gyara wuyarta da ya murgude gefe sannan ta ɓace.
Ko da ta ɓace ba ta ɓulla a ko ina ba se a fada bisa kan kujera,ta bayar da umarni da akira mata su Ummu zaheenat,bayan sun zo ne ta kalli wani daga cikin sojojinta ta yi masa magana ta zuciya batare da kowa ya ji ba sunkuyar da kai kawai ya yi ya fice.

ƙarar kacar da suka ji ne yasa suka yi saurin kallon kofar shigowa fadar,rufe bakinsu da hannu suka yi wani kukan tausayin kansu na zuwar musu ganin wacce aka shigo da iita.

“Sarauniya Muzna”Jadwah ta kira sunanta tana faɗuwa ƙasa ta zauna dabas tana kuka ashe su azabar da suka sha ma lafila ne. ashe su basu ga komai ba,ganin yanda Muzna ta koma,jikinta sanye da wani guntun riga da ya tsaya mata a iya guiwa yayi masifar datti ko iya gane kalar rigar ba a yi saboda yanda datti ya mayar dashi,gashin kanta ya hargitse kamar kan mahaukaciyar da ta dau shekaru me yawa tana hauka ya yi datti sosai ya yi buzu-buzu ko fuskarta ba a gani saboda ya rufe mata fuska.wuyanta da hannunta da kafafuwanta duka ɗaure da manyan kaca,ga ba ta iya tafiya se janta akasa da yake yi saboda tun caka mata wukar da Muzaina ta yi kafafunta suka samu matsala,duk sun mugun kumbura saboda basu samu kulawa ba balle magani har a yi tunanin za su warke.yana shigowa da ita ya wurgata a tsakiyar fadar,su ummu zaheenat kan su kafafunsu kasa ɗaukar su yayi hakan yasa suka zube akan guiwowinsu suna me fashewa da kuka ganin yanda Muzna ta koma kamar mahaukaciya kamar ba ita ba bama sa iya ganin fuskarta gaba daya ta susuce ta fita hayyacinta.

“A yau zan ka war da ita saboda in wuce radadin rashin albarkar da aka min a ta dalilinta a wannan masarauta,zan cıka alkawarin da na yi na ganin bayanta “ta faɗa tana gangarowa ƙasa hannunta riƙe da sandar tsafinta. Duk yanda yakai da danne zuciyarsa amma se da ya yi hawaye ganin yanda yar uwa kuma sarauniyar su ta koma abar tausayi,to ya su Galadima to suka koma?.runtse idanunsa kawai ya yi yana ne jin haushin kansa na rashin iya taɓuka komai.

Cikin sanyin murya Ummu Zulaihat ta fara faɗin “Muzaina yanzu dama za ki iya cutar da cikin ummanki?kar ki manta rana daya ku ka zo wannan duniyar,ku ka sha nono daya,ku ka yi rayuwa a guri daya.shin ɗaukar fansa ashe ze iya rufe miki ido ki hallaka yar uwarki ta jini da ba ki da kamar ta?”ta faɗa tana hawaye

“Banida wata yar uwa a wannan duniyar ni kadai a ka haifa,sannan wannan shishigin naki da ki ka yi kalarsa ne wannan matsiyaci Zubair din ya min na kashe sa dan haka ki iya bakinki ke tsuhuwar banza”

Cikin murya dake rawa wanda ta fita a cikin tunani da disashewa ta furta “Masoyina Zu….bair..kin kashe min masoyi naaaa,ko da zan yafe miki a gaba daya abinda ki ka aikata bazan taɓa yafe miki salwantar da ruhin masoyina ba,na miki rantsuwa da ubangiji se na ɗaukar masa mummunar fansa akan ki,duk abinda za ki min kimin,ko da kin kashe ni ko kin min wani abu amma ki sani zan dawo se na tarwatsa ki wannan alkawarina ne…….se na kuɓutar da masarautata da kuma mutane na daga sharrin ki” darıyar mugunta ta fashe dashi tana kewayeta ta ce “ba za ki samu damar hakan ba se de in ko a wata rayuwa,wannan Muzainar a yanzu babu me iya ganin bayanta saboda ta zama dauwamammiya ba me iya ka war da niiiiiiiiiiii”ta gama maganar tana se ta ta da sandar tsafi, nan take hasken dake ciki ya dinga fito wa yana shiga jikin Muzna,ihu suke yi suna bata hakuri akan ta dakata amma ko saurarar su bata yi haka ta ci gaba da abinda take yi,cikin kankanin lokaci Muzna ta koma farar tsuntsuwa tas yar karama gwanar burgewa dariya ta yi ta ce “Na umarceki ki yi ta tafiya a sararin samaniya har se kin mutu sannan ki faɗo ƙasa”nan take tsuntsuwar ta fara firewa a cikin fadar tana neman hanyar fita har ta samu ta fice ta window ta wulwuka can sararin samaniya.

“Allah ya la’ance ki Muzaina,ke kam da haihuwar ki da Fatima tayi da ma magani tasha ki ka mutu tun a ciki... Allah ya yi wadarai da ke,kuma ki sani in sha Allah se karshen ki yazo ba a hannun kowa ba kuwa face yar uwar ki da ki ka tsana…la’ananniyar yarinya kawai”Ummu Zaheenat ta faɗa cikin ɓacin rai da bushewar zuciya domin yanzu yanda take ji zata iya aikatawa Muzaina komai da tana da halin yin haka sede ko ta kasheta,cikin tsoron abinda ze biyo baya Jadwah ta sa hannu tana me toshe mata baki.
Zama ta yi tana tsareta da ido sannan ta mayar da idonta kan Yarima Farasat ta ga yanda ya lumshe idonsa,taune leben bakinta ta yi “kyaleta kar ki toshe mata baki bar ta ta fadi duk abinda ke ranta,a yau duk wanda ya yi abinda ba dede ba babu hukunci dan haka yau bata da abinci”

——————————————————————



Yana zaune yana gabatar da ibadarsa a saman babban dutse jikinsa sanye da fararen kaya tas babu ko digon datti. Matashi ne yana da kyau idanunsa kaɗai in ka kalla kasan akwai abinda ba dede ba. ɗaga hannuwansa sama yay yana addua kamar gizo yaga faɗowar abu ta gefen idonsa be motsa ba yaci gaba da ibadar da take yi, amma ran sa ya biya masa da son sanın menene abinda ya faɗo haka,se da ya idar da komai cikin nutsuwa sannan ya miƙe daga kan wannan katon dutsen ya fara kokarin saukowa ƙasa,ko da ya sauko nan ya fara dubawa ko ze ga abinda ya faɗo ƙasan amma be gani ba haka ya dinga duba tsakankanin manyan duwatsun ko ze ga ni amma be ga komai ba har koramar dake gurin se da ya duba amma ba komai. hakan yasa ya kutsa cikin Ƙasurgumin dajin dake kusa da wa'yannan duwatsun,ya jima yana neman abinda ya faɗo daga saman be gani ba kuma be sare ba haka ya ci gaba da kutsa kan sa ciki ba tare da tsoro ko fargaban haɗuwa da mugan namomin daji,wucewa ya zo yi ya hango abu na motsi a cikin ganyayyaki hakan yasa ya sunkuya yasa hannu yana yaye gayanyen dan ganin menene haka,idon sa ne ya masa tozali da farar tsuntsuwa na fitar da numfashi kaɗan-kaɗan alamar a galabaice yake shafa tsuntsuwar ya yi yana murmushi domin ya masa kyau hakan yasa ya ɗaukesa da hannu biyu yana murmushi.

“Masha Allah ,Allah kai ne ubangijin halittu wannan tsuntsuwar ta yi kyau”maganar da yake yi ne yawun sa ya ɗiga akan wannan tsuntsuwa haske ne ya wanzu a tafin hannunsa kafin ya gushe da mamaki yake kallon hannunsa ganin mutum a madadin tsuntsun da ya ɗauka.

“Ya Allah kai ne mafi sanın dalilin haka”ya yi maganar yana kurawa fuskarta ido kafin ya kalli ilahirin jikinta tausayin ta ne ya kamasa ganin yanda rauni masu yawa yake jikinta ga shi tana sume. hakan yasa ya miƙe tsaye tana a hannunsa tamkar jaririya cikin wannan dajin ya kutsa da ita nan ya isa wani bukka madaidaici ya shiga da ita ya kwantar da ita akan wani taburmar zana,taɓa goshinta ya yi yaji jikinta zafi rau. Barinta a cikin bukkan yai ya shiga daji bada jimawa ba se ga shi ya dawo hannunsa riƙe da wasu ganye nau’i daban-daban ya zauna ya fara mutsutssuka su akan wani dutse karami har ya yi laushj ya ɗauki

Please Login or Register in order to submit comment