Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yar biyu na?”ta tambaya tana tsaresu da idanunta da babu ko da digon hawaye,tashin hankali tunda suke basu taɓa tunanin Muzna itama tana da zafi da fushi haka ba se yau amma dake masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce ku guji ɓacin ran me hakuri da faram faram amma a duk sanda ran su ya baci abun babu kyau.

A nitse Galadima ya ce “ a matsayina na mahaifi a gareku gaba ki daya na umarceki da ki tafi dakin ki za ki san komai nan ba da jimawa ba” girgiza kai ta yi ta bar falon a fusace kamar zata tashi sama da kallo suka bi ta har ta ɓace musu.

Zama Galadima ya yi yana dafe goshinsa ya furta “ya hayyu ya qayyum,me yasa komai yake kokarin rincabewa ne?ta Ina na san zan bullowa Muzna dangane da maganar yar uwarta muddin ta tuna abinda ya faru komai ze koma baya domin bazata yarda ta ci gaba da mulkin wannan kasar ba,kuma bazaa yi auren ta ta cikin dadin rai ba “

“Shin yanzu kana nufin wani karyar za a sake mata galadima?Tabbas Muzna yarinya ce me hankali da hakuri amma wannan abinda ya faru dole ya sosa mata zuciya domin an yi wasa da hankalinta wajen bawa Jadwah wayar Muzaina,da lokacin da aka ce mata tana masarautar yemen da ba a dau wayar a bawa Jadwah ba ga shi komai ya rincabe ba lallai ta sake yarda damu ba yanzu mun karya mata zuciya”cewar Waxiri yana zama.

Duk zama su ka yi suna tunanin yanda zasu ɓullo mata.
Tana shiga dakinta ta hau tsakiyar gadonta ta fashe da kuka ita se yanzu ma abubuwan da Galadima ya faɗa mata na cewa Muzaina na masarautar Yemen ya dawo mata saboda ta san haka kurum Muzaina bazata bar wannan palace din ba,ita tsoronta shine Allah yasa ba cutar da ita suka yi ba duk da tasan abune mawuyaci ahalinsu su cutar dasu ganin yanda su ke nu na musu soyayya.

“Yar uwata kına ina ne?ina suka kai ki?”ta tambayi kanta cikin muryar kuka.
Sosai tasha kuka har ta ji babu dadi se da kanta ya soma mata ciwon kai sannan ta dakata ta shiga gallery wayar Muzaina tana kallon hotunansu da nata,koda kuyangu suka kawo mata abinci umarni ta basu da su komar dashi bazataci ba haka ta kwana babu komai a cikinta.da garı ya waye kasancewar bata sallah yasa wanka kawai tayı ta saka riga da wando na jeans ta yi bakin gashinta ya zuba a baya,fuskarta fayau babu kyalliya se idonta da ya kumbura saboda kukan da ta yi kallon lokaci tayı taga time din breakfast ya yi hakan yasa ta sauka downstairs zuwa dining table nan ta samu kowa ya hallara,ido kawai suka zuba mata har ta samu guri ta zauna tana

“Assalamualaykum” bayan sun amsa bata kuma cewa komai ba se umarnin da ta bayar aka zuba mata abincinta ta fara ci a tsanake,tana kammalawa kuma ta ɗauki tissue ta goge bakinta da hannunta ta miƙe zata tafi

“Muzna”Galadima ya kira sunan ta,tsayawa ta yi batare da ta zauna ba.
“Ki zauna “ zama ta yi tana kallon gefe

“Muzna nasan fushi ki ka yi,tabbas bawa Jadwah wayar Muzaina kuskure ne amma hakan da aka yi bawai da wani manufa bane an yi ne dan a rage miki kewar yar uwarki.sannan kuma babu abinda ya faru da ita tana cikin koshin lafiya babu wani wanda ya aikata wani abu agareta na miki rantsuwa,yar uwar ki very soon zata dawo gareki,kin ga gobe ne auren ki be kamata aga ran amarya a ɓace ba”

“Ka yi alkawari?”
Ta faɗa a shagwabe “na miki alkawari ƴata tashi ki zo” miƙewa ta yi ta je ta rungume sa tana murmushi shafa kanta yai yana sanya mata albarka.
Kayayyakin da akayi order wanda sarauniya kuma amarya za ta saka aka shiga da su izuwa sashenta tare da duk wani abubuwan da zatayi amfani dashi,kama daga kayan da zata saka anjuma na liyafar cin abincin ahalinta da na Sadauki Zubair da za a yi anjuma komai is ready.

Karfe 2:00Pm an gama duk wasu girke-girke an yi decoration din babban falon ganawa da baƙin dake bangaren Sarauniya,an shimfida carpet me girman gaske da laushi a falon an jera abinci na alfarma iri-iri akan carpet din ga drinks da fruits babu abinda babu a gurin sosai falon ya kayatu..biyu da rabi iyalan Rahman suka taru a falon sun sha ado matuka sun yi kyau sosai su Ummu zaheenat an sha ado da gwala-gwala haka su Galadima sun yi kyau sosai,basu jima da zuwa ba Yumma,Sadauki Zubair,Arman,Hashim suka shigo su ma sun yi kyau sosai cikin sutura na alfarma ga wani ƙiba da suka yi na hutu da kwanciyar hankali cikin mutuntawa da girmamawa suka gaisa da juna suka zauna ana hıra cike da raha.
Sadauki Zubair kuwa tunda ya zauna yake zuba ido yaga masoyiyar ta sa amma shuru har yanzu ba ta shigo.
A bangaren Sarauniya Muzna tsaf an gama shiryata cikin doguwar riga me tsananin kyau black color bakaramin daukar fatar ta yayı ba. kun san yanda baƙın abu yake wa farare kyau,tasha jewelries tsayawa zayyana kyan da tayi ɓata bakine su jadwah ne suka riƙe hannunta har izuwa cikin falon,kamshinta ne ya musu sallama hakan yasa duk suka ɗaga kai suna kallon ta suna sakın murmushi.

Miƙewa yumma ta yi ta je ta rungume ta tana fadin “kai!kai Tubarkallah Masha Allah ƴata kin yi kyau sosai”murmushi ta yi tana sakin numfashi tayı hugging din ta back dan ta yi kewar tsohuwar sosai da sosai “nagode ya Yumma ɗi ta”riko hannunta ta yi suka zauna tana ci gaba da yaba irin kyau da tayi tare da sanya mata albarka.
Sadauki Zubair da tunda ya shigo ya kasa Kanye İdonsa akan ta se kallon ta yake yi tayi matukar tafiya da imaninsa haɗa ido suka yi yana kallon ta daga masa girar sama,murmushi kawai ya yi yana lumshe mata ido tare da fakan idon mutane ya mata alamar kin yi kyau sosai da yatsunsa,itama murmushin ta mayar masa hade da masa farı da ido.

Bayan an yi hira,wasa da dariya ne aka ci abinci Suna gamawa aka yi hotuna sannan aka mike tsaye domin bawa juna kyaututtuka,sosai sukawa juna godiya tare da yin adduar Allah yakaimu gobe daurin aure karfe shabiyu na rana a cikin fada.
Da haka su Sadauki Zubair suka tafi suma suka koma falo suna me hira irin nasu na ahali.


Kwance take a kan royal bed dinta tana tunanin iyayenta da kuma yar uwarta da yanzu basa tare ta ji muryar Marwa na fadi “shugabata..amintacciyar Baiwa ce a tafe”
Batare da ta motsa ba ta ce “ki ce mata ta shigo”

“Da umarnin ki”ta fita se ga amintacciyar baiwa ya shigo hannunta rike da envelope.

“Barka da hutawa sarauniya”
“Barka dai “
Ya yi maganar tana mikewa zaune daga ita se wando three quarter da singlet.
“Na zo ne a domin ba ki wasikar da uwar gijiyata ta bari”

“Kına nufin Ummi ta bar wasika kafin ta rasu?”
Ta tambayeta tana gyara zamanta jin abinda ya shafi mahaifiyarsu ce.

Amintacciyar baiwa ta ce “Kwarai dagaske sarauniya Fatima haske da Rahaman ubangiji ya isketa har cikin kabarinta ameen.ta bar wasika kan cewa a cikin ke ko gimbiya Muzaina duk wacce ta hau kan mulki a bata wannan wasika,tun ba yau ba nakeso in ba ki shi amma ina da mantuwa duk sanda na yi yunkurin hakan se in mata ga shi nan se yau Allah ya yi”ta karasa magana ta na miƙa mata envelope din karba ta yi tana kallon sa

“Nagode amintacciyar baiwa za ki iya tafiya”bayan tafiyar ta ne ta soma kokarin buɗe envelope din amma se Kira ya shigo wayarta hakan yasa ta ajiyesa a gefen fillow da cewar in ta gama wayar zata karanta,sosai suka yi waya da tsohon sakatarenta Mubeen ya kirane domin tayata murna aurenta da za a yi gobe. Ko da ta gama wayar se bata bi ta kan wasikar ba ta shiga ta yi wanka sannan ta shirya ta sauka downstairs domin yin dinner.

Ko da ta shigo bedroom din shirin bacci ta yi ta jawo waya ta turawa angonta sako me ratsa zuciya sannan ta yi addua ta kashe wutar dakin tare da yin addua ta kwanta.
Cikin dare tana baccinta peacefully kishin ruwa ya tasheta kunna wutar dakin ta yi tana hamma ta zuro kafafunta kasa ta kallon agogo taga har uku da rabi na dare yayi goran ruwa dake bedside locker ta dauka tasha ta ajiye sauran. Baccin dake idonta ne ya dan washe hakan yasa ta tura hannunta karkashin fillow tana laluben wayarta hannunta ya sauka akan envelope din da bata bude ba zaro ta yi tana me dafe goshi

“Ya salam wai me yasa a yan kwanakin nan mantuwa na ya yi yawa ne?”ta tambayi kanta tana buɗewa ta fito da takardar dake ciki ta nutsu sosai ta fara karantawa,tunda ta soma katantuwa take haɗa zufa tare da zaro manyan idanunta waje kamar zasu faɗo kasa,tana gama karantawa ta ajiyesa tana goge zufanta cikin damuwa ta ce

“Amma menene yasa Ummi ba ki sanar da mu ba lokacin da ki ke raye innalillahi wa innailaihi rajuun in sha Allah zan cika miki wannan burin naki”. Dasauri ta ɗauki wasikar ta mayar dashi cikin envelope din ta ɗaga fillow ta saka sa.
Ta yi shuru tana tunani iri iri aranta har karfe hudu na asuba ya yi bata rintsa ba.

Wani uban sautin gudun sautin lafiyayyun dawakai masu tarin yawa ne ke tashi tako ina babu wanda ze ce yana cikin Bayaan be ji wannan sautin gudun wa'yannan dawakan ba duk kuwa nauyin da baccin ka ya yi se ka farka domin tsabar yawansu da sautin gudunsu har girgiza ƙasar masarautar yake yi domin da masifar karfi dawakan nan suke gudu wanda ya tayar da hankalin mutanen cikin Bayaan,ta ɓoyayyiyar hanya suka shigo sun fi runduna dari hudu duk kan su na sanye ne da muguwar shiga na yaƙi,akan kosassun dawakai masu masifar girma ga makamai dake jikinsu fuskarsu na cikin hular kayan yaƙi ko idonsu ba a gani balle fuskarsu,suna shigowa suka fara kashe duk wanda suka gani akan hanyarsu katangar masarautar kuwa da manyan dawakansu suke rusa su yana zubewa kansa,babu abinda suke yi se kashe kashen bayın Allah da rusa cikin masarautar,da gudu wani dogare yaje gurin Kararrawar sanarwa in wani abu na faruwa ya dinga bugawa da karfi yana cikin wannan bugawar ne aka harba masa kifiya akai ya faɗi matacce a gurin.

Sadauki Zubair yana cikin bacci ya ji wannan sautin gudun dawakan nan ya farka daga bacci domin yasan ba lafiya ba,cikin azama da zafin nama ya shiryawa yaƙi cikin kayansa na mayaka ya ɗauki takobinsa ya fito ya nufi dakin Yumma ya taso ta ya boyeta a cikin ƙuryar dakin sa ya boyeta tana kuka hade da masa addua Allah ya basu nasara yana fita ya haɗo kan sojojinsa.suka fita domin gwafzawa da su.

Tana wannan tunanin taji sautin dawakan nan ta miƙe zumbur hankali tashe a ranta ta furta “sun kawo mana farmaki”tana gama faɗin haka da mugun gudu ta sauko downstairs nan ta iske kowa tsaye sun yi cirko-cirko.

“Ya Allah...Abu Aleem wa'yannan sun shammace mu “ta faɗa tana isa kusa da Galadima abdul Aleem ya buɗe baki ze yi magana kenan suka ji ana buga kararrawar fitar yaƙi

“Ku shiryawa yaƙi bamuda lokaci ku kuma su Jadwah ku ne mi gurin ɓuya”cewar galadima da ya bar falon da sauri ya shiga dakin kayan yaƙi,gaba daya mazan watsewa su ka yi suka bar iya matan a falo cike da tsoro ,tafiya ta zo yi zata koma bangarenta ummu zaheenat ta rike hannunta tana girgiza mata kai

“Ah ah Muzna ki bar maza su yi wannan yaƙin dan Allah kar ki fita “ girgiza mata kai itama ta yi tana faɗin

“Ah ah Ummu zaheenat fita ya zamomin wajibi dole in je a gwabza dani kar ki manta nice sarauniyar wannan masarauta kuma na yi rantsuwa zan kareta har karshen rayuwata”ta gama magana tana cire hannunta ana ummu zaheenat ta haura part din ta da gudu.su Galadima fitowa suka yi cikin shiga na yaƙi da makamai a hannunsu baa kallon fuskarsu se ido saboda hular kwanon dake kan su.

“Ina sarauniya”yarıma Farasat ya tambaya
Amsa ummu Zulaihat ta basa da “ta haura bangarenta a domin shirya fita yaƙi”

Da sauri ya girgiza kai “noooo bazata je ko ina ba “

“Kwarai zan je”suka tsinkayo muryarta daga saman bene da hanzari suka maida dubansu inda muryarta ya fito zaro ido gaba daya suka yi ban da galadima abdul Aleem da ya saki murmushi

Saukowa ta soma yi cikin shiga na manyan mayaka kuma kwararru,ko ina na jikinta rufe yake da karfe ga gashinta da ta ɗaure sa guri guda hannunta na dama na riƙe da hular kwano na kayan yaƙın da take sanye dashi me kan shanu hular na da kaho kamar de yanda kan saniya yake,se dayan hannun dake riƙe da takobinta da ya kasance maganadisu,sosai Kayan yaƙin da ta sanya ya mata kyau ta fito a asalin jaruma,cike da azama take saukowa kasa ta kalle su ummu zaheenat ta na faɗin

“Duk abinda za ku ji kar ku yarda ku buɗe wannan kofar ku boye kan ku a ciki Allah na tare da mu in sha Allah “
Cikin sanyi jiki suka gyada mata kai babu yanda suka iya ne amma basu so fitar ta ba.

Dafa kafadarta Waxiri ya yi “tabbas ke jinin sarki Taifur Rahman ce yanda mahaifinki yake kema haka ki ke ban hango tsoro ko fargaba a idanunki ba mu je”

Suna fita su ummu zaheenat suka yi yanda sarauniya Muzna ta umarcesu. ko da fitowarsu wajen nan suka ga yanda aka yi musu barna me masifar yawa musamman rayukan sojojin su,yakLƙi suke gwabzawa kamar basa yi domin ko sun kashe su sake tashi suke ga shi se kashesu akeyi.cikin jarumta ta sanya hular yakinta ta shiga filin ta soma gwabzawa kamar yanda ta ga masoyinta Sadauki yake kai musu farmaki,babu abinda ka ke ji da ya wuce karan makamai da ihu ta ko Ina yaƙi ya dau zafi amma sojojin Bayaan ake ta kashewa domin wa'yannan basa mutuwa abinda ya matukar ɗaure musu kai Kenan.

“Sarauniya menene yasa ba sa da mutuwa ne “Arman abokin Sadauki Zubair ya tambayeta,tana kai wa wani sara da wuka ta amsa mai da

“Ban sani ba Arman amma kamar basa jin takobi “

Har garı ya waye ana abu daya sojojin Bayaan wa'yanda suka rage basu wuce soja dari da hamsim ba duk an kashe su gawawwaki ne zube a Ƙasa kamar na kiyashi gaba daya sun jigata.
Wani daga cikin su ne yakaiwa sarauniya farmaki ta baya batare da ta sani ba tana faɗa da wa'yanda suke gabanta,da sauri Sadauki Zubair ya yi tsalle ya saresa da wuka juyowa ta yi suka haɗa ido ta ga ya ceceta jinjina masa kai ta yi wanda ya saran ne ya kuma tashi yana dariya mara dadi hakan yasa Sadauki ya caka masa takobin akai nan take hular kwanon ya rabe gida biyu fuskarsa ya bayyana daga ita har Sadauki ja da baya suka yi ganin fuska me tsoratarwa irin na dodonni babu kyan gani nan suka fahimci wa'yanda suke gwabza yaƙi da su din ba mutane bane aljanu ne,nan take sadauki Zubair ya sanar da mayaka kan cewa wa'yanda suke gwabzawa dasu ba mutane bane aljanu ne kuma faɗa da aljani babu dadi.shawara galadima ya basu kafin su kai musu sara su kira sunan Allah haka kuwa sukayi cikin ikon Allah hakan ya yi aiki suna addua suna kashe su amma duk da haka an kashe sojoji masu yawa. gaba daya wayanda suka rage daga su sarauniya se sojojin da basu wuce mutum arba’in ba amma a haka da yardar Allah su ke kaiwa aljanun farmaki kuma suna samun nasara.
Suna cikin wannan yakın sukaga wa'yannan aljanu sun kame guri daya sun dena motsi da mamaki suka tsaya suna kallon su ganin sun tsaya cak kamar gumaka.
“Shin meye yasa suka dakata” ta tambaya tana rike hannun Sadauki,kafin su ankara iska me karfi ya tashi har tsabar karfin da ya yi yana zubar da mutane seda ya dau lokaci kafin ya tsaya ganin guguwar ya koma sama ne yasa su ɗaga kai suna kallo. a hankali baƙin guguwar ya koma mutum. Cikin zallar mamaki da al’ajabi suke kallon wacce ta bayyana ,cikin shigarta na yaki bakaken kaya ga sandarta a hannu kan ta da hular sarauta

Dakyar sarauniya Muzna ta iya samun karfin guiwar furta “Mu…zai…na?” Ba ita kaɗai ba haka kowa ya dinga furta sunanta a labbansa.

Kanta ne ya sara lokaci guda ta sa hannu ta riƙe “Gaba dayan ku,dukkanin ku babu ko mutum daya da zan yafewa wannan cin amanar,Ina kuka haka na dinga rokonku kamar wata wulakantacciya amma ku ka juya min baya ku ka take muradina a karkashin takalman ku cike da isgili.Ku sa a ran ku lokacin yin rayuwa me dadi ya kare a gare ku.zan dau fansa me muni akan ku domin ku ba mutane da zaa yafewa bane,zan tarwatsa farin ciki da walwalar ku da jiji da kan kan da kuke ji dashi.zan tarwatsa masarautar da ku ke gadara dashi komai se ya zamo muku kuncin.ke kuma dawuwa na baze miki dadi ba se kin roki mutuwa da sake fatan rayuwa dani.dukkanin ku na muku tsana na musamman,zan bar wannan masarautar amma ku kasance masu adduar Allah yasa kar in waiwayo ku “ wannan maganganu na Muzaina na karshe nan take ya dawowa sarauniya nan ta tuna duk wani abinda ya faru na rigimgimun da suka faru da barın masarautar da ta yi komai seda ta tuna tsaf.dama idan masu karatu basu manta ba mai girma sheikhy ya sanar dasu duk sanda ta ga Muzaina se ta tuna abinda ya faru kuma hakan ne ya kasance.

Saukowa ƙasa ta yi tana bin su da shu’umar murmushi musamman Muzna “wai ya na ga kun tsareni da ido kuna min kallon mamaki shin ba ku yi farin ciki da dawuwa na bane ?”

Tsananin mamaki ne ya hanasu iya cewa komai se kallonta da suke yi.

Wa'yannan aljanun ne suka buga kafafunsu a kasa sannan suka zube ƙasa a tare suna faɗin
“Barka da bayyana yake shugabar mu “

“Shugaba?”suka tambayi kan su

“Kwarai kuwa shugaba ni din shugabar su ce,kuma sabuwar shugabar ku”

“My Muzaina menene ki ke faɗa haka yana ga kin sauya kamar ba Muzaina ta ba dan Allah ki watsar da komai “cewar Muzna da ta cire hular kan ta ta ajiye takobinta a Ƙasa. Murmushi Muzaina ta yi

“Ai ya rigada ya wuce Muzna yar taifur Rahman komai ya wuce ni da ke muna duniya mabambanta ne a yanzu,ni din ba wai Muzaina da ki ka sani bane,wannan sarauniyar matsafar duk duniya ce. Muguwar son zuciyar ku ya turani izuwa faɗawa cikin wutar ketata kamar yanda na yi rantsuwa da kuma alkawarin wulakanta ku to se na tabbatar da wannan alkawari nawa,bakomai ne ya dawo da ni ba face ƙarbar sarautar da ya kasance mallakina ku kuma in ga bayan ku “

“Mayakana ku gurbanar min da su a ƙasa”cike da bin umarni aljanun nan suka je wajen su suka kwace makamin su suka jefar a ƙasa. sannan suka tilasta musu gaba dayansu suka zube akan guiwarsu. Dariya ta yi me sauti

“Du be ku a gabana kamar wasu mabarata. Mayakana ku jigatar dasu yanda jini da ruwan jikinsu ya haɗe guri daya”
Ko da gama maganar ta nan take aljanun nan suka rufa musu da mahaukacin bugu kamar Allah ne ya aikosu.kujera ta jawo ta zauna ta ɗaura daya kan daya tana kallon su,tana jin dadin yanda suke fitar da numfashin wahala,babu wanda take jin nishadin ganin ana jibgarta kamar Muzna da ake mata mahaukacin duka a ciki tana numfashin wahala.

Se da suka dau lokaci suna gana musu azaba sannan ta basu umarnin dakatawa,sosai wayannan aljanun mayakan Muzaina suka jigatar dasu,jikinsu se zubda jini yake.
“Menene ya sa ki ka koma haka Muzaina,wannan kina tunanin ze kawo karshen komai ne?kamata yayi muyi sulhu”
Muzna ta faɗa dakyar tana riƙe cikinta

“Tirrrrr da sulhun waye ya faɗa miki ina da muradin zaman lafiya?na yi rantsuwa da wannan sandar tawa se na tarwatsa Bayaa. sannan in kashe duk wa'yanda suke ciki in kuma mayar da wasun su bayina “

“Ni kuma in har ina raye bazan taɓa ba ki wannan damar ba duk da kasantuwar ki yar uwata ba zan bari ki cutar da ko da dabba a cikin masarautar nan ba balle mutane na”

“Shi ya da za ki mutu”ta faɗa tana miƙewa tsaye ta kuma faɗin “duk wanda ya iya kayar dani ƙasa a cikin ku to tabbas zan zubar da makaman yaƙina “ko da jin haka sauran sojojin Bayaan da suka yi saura suka nufeta da niyar kai mata farmaki amma da kwayar idonta da ya koma fari tas ta kashe su ba tare da yin amfani da takobi ba,nan take suka zube matattu a ƙasa.

Kallon su ta yi “galadima abdul Aleem Rahman Kawu a gun Muzna shin bazaka iya taɓuka komai bane?”

Ƴa ta Muzaina na roƙe ki da ki dena wannan abinda ki ke yi...kar shaidan ya rufe miki ido”da ido ta kalli wani takobi dake jikin mayakanta ya tashi sama ta kalli kafar nasa nan wannan takobin ya sauka akan kafar galadima cike da jarumta ya rintse ido duk da ya ji azaba amma be sa ya yi ihu ko kururuwa ba.

“Abu Aleem “Muzna ta kira sunan sa da karfi tana isa gabansa ta sa iya karfin ta ta zaro wukar daga kafarsa dakyar.

A fusace ta kalli Muzaina “ba zan barki ki dinga kashe min mutane na ba,zan ajiye yan uwantakan dake tsakanin mu,zamu gwabza ko ni ko ke Muzaina cikin ni da ke se de daya ya mutu”.

“Dama haka nake son ji daga gareki ya ke Muzna dole daya cikin biyu daya ta rayu,ni de kam bazan mutu ba”Muzaina ta faɗa tana sakin murmushi

“Haka nima bazan mutu ba se nakawo karshen wannan girman kan na ki Muzaina”ta yi maganar tana ɗaukar takobinta ta nufi Muzaina da gudun gaske,faɗa ne ya barke tsakanin yan uwa biyu babu abinda ake ji da ya wuce karar takobinsu Muzaina se murmushi take yi takobin Muzna babu abinda ze mata ,da ta so yanzu za ta kashe ta amma nishadi take ji ganin yanda take kokarin kayar da ita.

Iska ta hura mata a ido nan take ta tsaya cak jikinta na rawa. wukar da yake hannunta Muzaina ta karɓa tana caka mata a kafafuwanta guda biyu sannan ta sake ɗagawa za ta caka mata a ciki Sadauki Zubair ya yi wani tsalle ya buge hannunta yana riƙe Muzna dake kokarin zubewa a kasa.

“Shugabata babu abinda ze same ki ina tare da ke “ “Masoyi bana son rasa kafuwana banajin zasu iya ɗaukata a yanzu “

“Babu abinda ze same su “ya faɗa yana shafa kafafun nata da suke zubar jini.

“Ya kai la’ananne wulakantaccen bawan da na tsana fiye da kowa a rayuwata fansa ta akan ka me zafi ne “
“Ita din yar uwar ki ce me yasa za ki cutar da ita?”
Wukar da ke hannunta ta luma masa a makoshin sa nan take ya sake Muzna dake hannunsa ya faɗi yana me riƙe wuyarsa cikin gigitaccen tashin hankali sarauniya Muzna ta furta “Zubairrrrrrrrrrrr” ta kira sunan sa ta na rufuwa akan sa jini me guda-guda se zuba yake yi a makoshin sa İdon sa sun sauya kala

“Zubair katashi kar ka tafi ka barni ka tashi Zubair yau ne ranar auren mu ni dakai kar wani abu ya sauya hakan masoyina “ta faɗa cikin gigitaccen kuka

Jini na zuba ta wuya ta baki ta hanci dakyar ya furta “duk abinda ze faru kar ki juyawa Bayaan baya sannan ki bawa yumma hakuri,sannan ki dawo da yar uwar ki kan hanya in ta ki kuma ki dawo da ita ta karfi ina san ki “wannan shine kalmomin sadauki Zubair na karshe yana gama faɗar su Allah ya ɗauki ransa.

Da karfi ta furta”Zubairrrrrrrrrrrr” tana gunjin kuka kamar ranta ze fita ji tayi za ta iya kashe kowa domin fansar ran masoyinta da Muzaina ta kashe.

“Hahahaha irin wannan tashin hankalin na ke son gani a tare dake Muzna se kin wulakanta har karshen rayuwarki “

Ta kalli aljanun mayakanta ta ce

Please Login or Register in order to submit comment