Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefen sa ya yi yana neman inda ze buya amma sam babu ko Ina gawawwakin dabbobi da kuma halittun da ta kashe ne sheme a kasa babu ko hanyar da ze bi ya wuce haka ya tsaya yana ci gaba da kallon ta har ta gama kashe su tas.cikin tafiya a galabaice ta iso sa a inda ta barsa,ko kadan be samu damar ganin fuskarta ba saboda hular ya bada gudunmawa wajen kare mata fuska.

“Shin menene ya kawo ka wannan daji me hatsari ?” “Gani na na yi,yanda ki ke fadar ki ya burgeni sosai ko ni da nake namiji na yi rantsuwa da yesu bazan iya ba”

“Nagode “ ta faɗa haɗe da kokarin juyawa ta tafi da sauri ya miƙa mata hannu “ Sunana Jayson David Abraham amma ana ce min Jay,ke fa?” Kallon hannun san ta yi sannan ta kalli na ta dake ta zubar jini fahimtar abinda take nufi ne yasa ya sauke hannun sa.

Magana za ta yi masa aka harbo kifiya setin kanta amma dake bata da tsayi can can hakan yasa kifiyar ya tafi da hular kanta nan take fuskarta ya bayyana.da Hanzari ta jaro kwari da bakan bayanta ta harbi dodon da ya harbo kifiyar nan take ya faɗi ya mutu.

“Ohh my God Gaskiya ke kyakyawa ce”bata ce masa komai ba se murmushin da ta mai ta komar da gashinta bari guda.

“Ba ki sanar da ni sunan ki ba”

“Sunana sarauniya Mu…..”

“Jayson ka farka daga wannan baccin wani irin mafarki ne haka kake yi kana ta sambatu ?” Cewar Katrina.

A zabure ya mike zaune yana furta “Jesus Christ “
“Meyafaru?”
“Mom na sake yin mafarkin wannan sarauniyar a karo na uku kenan yanzu” ya fada mata

Nisantawa ta yi kana ta ce “Jay tun kana yaro ka ke da wannan baiwar duk sanda ka yi mafarkin abu se ya faru,tabbas tunda ka yi mafarkin wannan yarinyar akwai yuwuwar zaku hadu da ita a kaddarar rayuwar ka”

Rike goshin sa ya yi sannan ƙasa ƙasa ya ce “har izuwa yanzu ban samu damar sanın sunanta ba. a ko da yaushe se de ta ce min sunanta sarauniya Mu,se kuma in farka amma duk sanda mu ka hadu se na ga fuskarta “

Ɗan Numfashi ta sauke ta kalli dankareren agogon bangon dake dakin sa taga karfe 5 na safiya har ta yi.

“ se ka samu kaje ka yi wanka akwai zuwa church karfe takwas lokacin baikon ku” ta fita.

“Dam it wannan dan iskan baikon da ku ka wani damu dashi Mtssw “ ya karisa da tsaki kafin ya shiga toilet ya yi wanka da brush ya fito dogon jallabiya fara ya saka sannan ya dauki bible ya bude yana me tsugunawa akan guiwowinsa ya soma a addua idonsa a rufe.

PALACE

Cikin babban church din dake palace din an masa decoration na musamman,ga mutane Cike a ciki zaune kowa ya hallara hatta pastor ya zo Jay da princess Gabriel kawai ake jira.

Shigowa president David suka yi da Katrina se Jay dake gefensu cikin wani mayen suit da ya masa masifar kyau gashin kansa ya sha gyara ga agogon diamond dake daure a hannun sa takalmin kafarsa ma abin kallo ne,fuskar nan a hade se shan kamshi yake yi shi a dole za a masa dole.

Zama suka yi a kujera yayinda shi kuma ya tsaya a kusa da pastor,ba da jimawa ba kuwa anty Jennifer ta fito tana rike da hannun princess Gabriel dake sanye cikin gown black color me bala’in kyau rigar ba yi da hannu saman breast din ta a waje,ga diamond necklace a wuyanta ga kuma earrings nasa hannunta da bracelet na diamond,kafarta na sanye da hill shoe black color,fuskarta babu make up sosai and babu walwala a tattare da ita tayi kyau sosai her dress is very unique and simple.
Tsaya wa itama tayi a kusa da pastor se suka sa a tsakiyar su kadan,dukkan su kallo daya sukawa juna suka watsar.

Murmushi pastor yay ganin yanda duk suke shan kamshi,wasu adduo’i ya yi sannan ya soma da “Jayson David Abraham shin ka amince da wannan baikon da za maka da Gabriel Sam smith?”kallon inda President ke zaune ya yi yaga yanda ya ke kallon sa,se da yayi tsaki aransa kafin ya ce

“Na amince.” A takaice,ajiyar zuciya kawai President ya sauke domin yasan halin Jay sarai ko dan ya ɓata mutane rai ze iya cewa be amince ba.

Mai da duban sa kan Princess Gabriel ya yi “ Gabriel Sam smith shin kin amince da baikon da za a miki da Jayson David Abraham?”

Tun kallon da ya mata na farko be sake kallon ta ba se yanzu ya dago ya zuba mata rikitattun idonsa domin jin me zata fada.
Kallon sa ta yi kafin ta sake masa munafukin murmushi

“Na amince pastor”
Tafi aka kaure dashi cikin jin dadi a yayinda Jay ya ji kamar ya hada kanta da jikin glass din dake gefen su Wanda aka ajiye rings din da zasu yi exchange.babu abinda yake yi se watsa mata mugun kallo ita kuwa ko a jikinta domin inde za ta samu tabar kasar babu abinda bazata aikata ba.

Wata cousin sister Jay ce ta kawo zobe princess Gabriel ta saka masa a hannu nan aka kaure da tafi,dauka shima ya yi ya rike hannunta ya saka mata zoben nan aka ake yin tafi.
Umartar su ya yi da su sumbaci juna cikin basarwa ya rike hannunta ya sumbata.
Nan a ka fara watsa musu flowers masu dadin kamshi.
Nan yan uwa suka shiga taya junan su murnan wannan alaka da aka kulla.



MASARAUTAR BAYAAN

Yau ki manın wata daya kenan da sarauniya Muzna ta fara gudanar da mulkinta a Bayaan kuma Alhamdulillah komai yana zuwa mata da sauki domin kuwa manyan fada sun koya mata duk wasu harka ta masarautar shisa bata ganin wahala amma babban abinda yake azabtar da ita kuma har yau ta gagara sabawa shine saka wa’yannan kaya masu nauyin da sarakuna da manyan dankunnaye,har ciwon jiki take ji duk sanda ta saka.


share,comment and like.
https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207


👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚📚🖋️⚜️


❤️🔥Page 21—22–23



MASARAUTAR BAYAAN

Yau kimanın wata daya kenan da sarauniya Muzna ta fara gudanar da mulkinta a Bayaan,kuma Alhamdulillah komai yana zuwa mata da sauki domin kuwa manyan fada sun koya mata duk wasu harka ta masarautar shisa baya bata wahala,amma babban abinda yake azabtar da ita kuma har yau ta gagara sabawa shine saka wa’yannan kaya masu nauyin da sarakuna da manyan dankunnaye,har ciwon jiki take ji duk sanda ta saka. Kasantuwar ta sarauniya yanzu yasa ta koma bangaren marigayi sarki Taifur Rahman domin kuwa wannan bangaren nan ne inda duk Wanda ya hau karagar Mulki yake komawa tun daga zamanin kaka da kakanni,babu abinda babu a ciki kamar Aljannar duniya tsabar haɗuwa ga masu yi mata hidima ta ko Ina komai yi mata ake yi ta kara wani fresh da kyau ga ƙiba da tayi ɗan dede hankalinta a kwance. sede kullum da Muzaina take kwana aranta kuma take tashi. har Allah Allah take wannan watanni biyu su karaso ta ƙagu ta ji muryar yar uwarta. Acikin bayi masu yi mata hidima kuwa ta sakar musu fuska kamar yanda yake asalin dabi’ar ta sun saba da ita sosai musamman Marwa da ta kasance yar hannun damar ta.


Bayan dare ya yi an tashi a fada Galadima ya tura a Kira masa Sadauki Zubair ba da jimawa ba kuwa ya zo sa ya tarar dasu su biyu wato Galadima Abdul Aleem da sheikh Abu Dhabi cike da girmamawa ya gaishe su suka amsa tare da nu na masa gurin zama,bayan ya samu guri ya zauna akan lumtsuma-lumtsuman kujerun ne ya nutsu domin jin dalilin kıran da aka yi masa.

“Sadauki Zubair dalilin kiranka shine magana ce akan sarauniya Muzna. Kasantuwar ta shugaba be wadatar ba har se ta zama cikakkiyar jaruma wacce za ta iya kare al’ummar ta da kuma bawa kanta kariya.dole ta iya faɗa saboda ko da yaƙi ya tunkaro mu itama zata bi sahu domin an san shugaba da ceton na kasa dashi”

“Wannan haka yake “Sadauki zubair ya faɗa.

“Yanzu wannan nauyi ne da ya rataya a wuyanka a matsayinka na commander sojojin Bayaan kuma wanda ze auri sarauniya za ka koya mata duk wasu dabaru da nau’ikan faɗa wannan shi ya sa na nemeka.”

Gyara zama Sadauki Zubair ya yi kafin ya ce “ Wani hanzari ba gudu ba,sarauniya na ga ta iya sarrafa takobina cikin salon kwarewa da jarumta.”
Kallon juna sheikh Abu Dhabi da Galadima suka yi jin abinda ya faɗa,hannu sheikh ya miƙa masa yana fadin
“Ya kai Zubair in ga shi takobin naka “

Se da ya tashi tsaye kafin ya zaro wukar a gidan sa dake a kugunsa ya basa.

Bayan ya amshi wukar ne ya rufe idon sa yana wasu kalamai wanda basu iya jin me yake cewa ba. can kuma ya buɗe ido yana sakın yar murmushi akan lebensa.duk kallon sa suke suna jiran su ji me ze ce.
“Ka yi gaskiya Zubair,wannan wukar me maganaɗisu ne,yana jin kamshim shugaba,kwararren mayaki,matsafa da kuma rauhanai ko da ace mutum be iya taɓuka komai a bangaren faɗa ba wannan wukar na shiga hannun mutum ze dinga sarrafasa kamar wanda ya yi shekaru aru-aru yana yaƙı,wannan dalilin yasa ka ga sarauniya ta yi amfani dashi.yanzu za ka fara koya mata faɗa da takobin da be kasance maganadisu ba”
Se yanzu ya sake tabbatar da maganar da ta faɗa masa na cewa ita bata taɓa yin amfani da takobi ko yin faɗa ba,domin ko lokacin da ta sanar mai kawai ya ji ta ne amma ba wai ya yarda da ita ba.

“Da yardar ubangiji gobe za a fara atisaye nagode.”

“Yawwa Zubair se kuma magana na gaba nan da wata daya ko kafin wata daya za a yi auren ku “

“Nagode” ya faɗa yana dukar da Kansa kafin ya tafi.

“Sheikh Abu Dhabi na rasa dalilin da yasa nake yawan jin faɗuwar gaba,na maka Imani da Allah Ina cikin tsoro da kuma fargaba. Yakamata izuwa yanzu na samu nutsuwa da kwanciyar hankali tunda mun yi abinda ya dace,amma sam yanzu na rasa menene ya hanani samun kwanciyar hankali.”
Dogon numfashi sheikh Abu Dhabi ya sauke “Ka yi la’akari da ɓatar da gimbiya Muzaina tayi wannan kadai ya isa ya hanaka samun sukuni,tabbas za ta dawo masarauta tana nan zuwa, babu wani abu da za mu kuma yi yanzu da yawuce mu tsumayi zuwan ta. Kuma ka yarda dani fansa ne ze dawo da ita daga mutuwa izuwa rayuwa,Allah shine kawai wanda ze iya kawo sauki ga wannan lamarin amma muddin tana raye wallahi za ta dawo ga yar uwarta”


”ubangiji ya kawo mana sauki da kariya “

Sarauniya Muzna na cikin bahon wanka dake cike tab da ruwan wanka me ɗauke da furannin wanka masu masifar kamshi,Tana ciki babu abinda zaka iya hangowa face kanta dake waje ta lumshe manyan idanunta,hannunta kuwa tana wasa dashi abayanta ta hanyar goga masa sabulu.masu yi mata hidima kuwa suna daga tsaye a jikin babban labule mara nauyi da ya kasance transparent ana iya hangota daga toilet din da take ciki amma sun durkusar da kansu ƙasa. A tsanake Marwa ta shigo kanta a kasa ta tsaya a gefen labulen da ya musu iyaka

“Ya shugabata an umarceni da in sanar dake gobe za a fara ba ki horo”
Bata amsa mata ba har se da ta fito daure da towel se baza kamshi take yi dayan hannunta na rike da karamar towel tana goge dogon gashinta da sauri wata ta karɓa tana taimaka mata har ta zauna akan kujera nan suka soma yi mata hidima kamar yanda suka saba ko wacce da abinda take yi mata ana mata shirin bacci.
Marwa da ta shiga ma'adanar kaya ne ta fito rike da wata haɗaɗɗiyar doguwar riga na bacci fara sol se bakin less dake hannun rigar da ƙasan rigar da ya kasance bakƙ,bayan ta gama shiryawa cikin kayan baccinta ne ta zauna akan gadonta tana me jan pillow ta kishingiɗa ta kalli masu mata hidiman ta ce “ Za ku iya tafiya se zuwa gobe in Allah ya Kai mu,ke kuma Marwa ki tsaya”
Layi sukayi sannan suka fice suna mata Allah ya ta she mu lafiya.

Kallon Marwa da ta yi saura ta yi “Yawwa dazun kina magana akan horo?” “Kwarai ya shugabata Ummu zaheenat ta banı sako in faɗa miki cewa gobe za ki fara karɓan horo daga hannun Sadauki Zubair”

Kayitacecciyar murmurshi ta saki domin tayı matukar jin dadın wannan labarin da ya risketa,tunda ta hau kan mulki dede na minti daya bata samu damar yin magana da Sadauki Zubair ba sede kullum suna ganin juna a fada,amma babu damar yin magana in bawai wani zance akan abinda ya shafi sojoji ze yi ba ko kuma magana akan horon da za a bawa sabobbin matasa,wannan ne kaɗai ke haɗa su,tında bayi da halin zuwa turakarta domin ganin ta haka itama dole se sun jira an yi musu aure tukuna,yanzu ba karamın dadin wannan opportunity tayı ba zata samu ta dinga kasancewa da farin cikinta.

“Shin kin ji dadi ko?ai dama na san shugabata za ki ji dadin wannan maganar domin kuwa za ki samu damar kasancewa da mai girma Sadauki Zubair”.cewar Marwa da ta ga yanda sarauniyar tasu take ta faman sakin lallausan murmushi akan fuskarta.

Cikin jan magana ta ce “Kwaraiii kuwaaaaa Marwa,tsawon kwanaki talatin rabon da in kasance tare dashi, kin ga kuwa dole in yi farın ciki da jin wannan zance,in ba haka ba zafi biyun ai se ya min yawa,ga zafin rashin ji daga yar uwata ga kuma na rashin samun kulawar masoyina “

Darıya Marwa ta yi tana zama a carpet kusa da inda kafar sarauniya yake

“Shugabata kulawa yawuce wanda muke samu daga gareki? Gaba ki dayanmu a karkashin kulawarki muke har shi kan sa”
Miƙewa zaune ta yi tana tallafe kumatunta da hannu

“Ohh god yanzu dan Ina sarauniya shikenan se a ce bana bukatar nima a bani kulawa?”
“Sam ba haka nake nufi ba,abinda nake nufi shine kece inuwar mu me bamu kariya “

Dan hararar wasa ta jefa mata sannan ta kalli agogo “dare ya yi Marwa karfe sha daya da rabi na dare yanzu ki je ki samu hutu kar in riƙe ki da surutu “

“Nagode sosai kyakyawa kuma tauraruwar sarauniyar mu me kaunar duk wani halitta da ze raɓeta,ki yi bacci cikin aminci da yardar ubangiji,ki Kasance cikin kariya na ubangiji.Allah ya nuna mana gobe da rai da lafıya in ci gaba da hidimta miki har iya rayuwata “

Wayannan addu’oi da kalamai masu dadi da Marwa take ratsata dasu ne yasa ta ji yarinyar ta matukar kwanciya mata a rai musamman in ta tuna yanda take marainiya haka Marwa take marainiya se ta sake jawo ta a jiki har se da ta mayar dasu kawaye sannan ta samu nutsuwa. Bayan tafiyarta adduar bacci ta yi sannan ta kashe wutar dakin da switch remote dake hannunta ta bar iya dim light ta kwanta.



INDIA

babban masarauta ce me girman gaske amma girman ne kawai babu wani abun kayatarwa a ciki, domin daga ganin wannan ginın masarautar yana da dimbin tarihi a duniya baya da haka ya kwashe shekaru masu yawa babu wani mahalukin cikekken bil adama da yake ziyartar wannan masarauta a sakamakon hatsarin da yake dashi,wannan masarauta yana da tarihi me tarin yawa,masarautar ya kasance a can wata kauye da ake kira FALASHFUR.izuwa yanzu babu wani mutum me rai a wannan masarautar falashfur dake zaune duk sun gudu wa rayuwar su domin in basu gudu ba da jininsu da gangan jikinsu za a dinga ƙarawa duk wani azzalumin matsafi karfin iko. A babban fadar masarautar kuwa kana shiga babu abinda zaka faracin karo dashi da ya wuce ƙasusuwan mutane jibge kamar zasu cika fadar,hatta kwalliyar fadar da kwarangwal din al’umma aka yi su.ga wasu abubuwan tsafi daban-daban Kallo daya kawai zakawa masarautar ya baka tsoro, wannan kaɗak ya isa ya maka nu ni da azzaluman aljanu,azzaluman matsafan duniya haɗe da azzaluman ruhi ne ke rayuwarsu a wannan tankamemen masarauta suna cin karensu ne babu babbaka. A tare dasu akwai kwararre kuma shahararren hatsabibin matsafi da duk duniya babu wanda yakai sa iya mugun tsafi da sihiri.duk da ya tsufa tukub kana kallon sa zaka masa tsammanin mutuwa ko yanzu ko anjuma amma an buga dashi an barsa in de tsafi ne tofa babu wanda ya kama kafar GALUUUR. Inde ya tsafance mutum tofa se ka samu biyan bukatarka ka je ka ta aikata zaluncin ka.

Wasu irin zane ne a gabansu ga jini a cikin wani kwarya me tarin yawa,cikin zannen an saka ƙashi akan duk wani zane ga wuta dake gabansu suna wasu irin maganganunsu na tsafi me kama da sambatu suna watsa wasu jan gari a wutar,a duk sanda suka watsa se wutar ya tashi yakara karfi,dukkansu jikinsu na sanye da jajayen kaya da baki kana kallon fuskarsu kasan babu alamun rahama ko sauki atattare dasu idanunsu a rufe se zuba wannan garin suke a wuta suna sambutu da iya karfinsu. A can nesa dasu kuwa wani katoton tukunya ne me girman gaske wanda mutum biyar zuwa goma zasu iya shiga wannan takunyar tsabar girmarsa. se girgiza yake hayaki me turnukaki na fitowa daga ciki alamar abune yake tafasa cikin tafasar tashin hankali da gaggawa.wutar dake tafasa wannan tukunya kaɗai in mutum ya kalla yasan ba wutar lafiya bace wannan shi ake kira da wutar tsafi. wutar be bayar da kalar asalin wutar da in an kunna murhu ko kuma in an kunna gas ake gani ba shi wannan wutar launinsa korene sharrr da yellow hayakin wutar kuma baƙi kirin. A ta murfin wannan tukunya kuwa jini ne ke zuba a ƙasa dis!dis!dis hakan ya kuma tabbatar da bayan wanda ke cikin wannan tukunya yana bararrraka tofa cike yake tab da jini.

Matsafa biyu da aljani daya dake wannan tsafin suna ci gaba da yi suka ji sautin tafi rap!rap!rap ana tafa musu dakatawa da tsafin su ka yi kasancewar sun san waye ke tafin . cikin ɓacin rai Galuuur ya buɗe idanunsa da fatar suka tattare guri guda saboda tsufa ya miƙe tsaye suma sauran miƙewa tsaye suka yi suna kallon wanda ke saukowa daga matattakalar benen.

Cikin shigarsa ta sarauta na zamanın da,wanda yanzu duk wanda aka gani da wannan shiga a san ba cikekken mutum bane saboda shiga ce da sarakuna na shekaru sama da dari biyar suka sanya.

“Sarki Damurdar shin menene ya sa zaka dakatar damu daga wannan aiki da mu ke yi ?kasan me hakan ya janyo?shin ko kasan da cewa saura kiris mu kammala abinda mu ke yi amma ka mayar damu baya?”

“Ni ban damu da ku yi nasara a wannan aikin ko kar ku yi ba,abinda na damu dashi shine kawai cikar muradi na Ina son in samu karfin da zan mulki wannan duniyar ko ma ta halin qaqa ban damu ba,ina son in samu ikon da babu wanda ya isa ya ja dani “

Aljani Gautam Suwami ya ce “to ta ya ka ke tunanin haka ze faru ba tare da ita ba?ita ce nan za ta baka wannan damar cıkar muradin naka,abinda ake bukata a gareka shine ka nutsu a guri daya ka zuba mana ido babu abinda zaka iya taɓukawa har se an kammala wannan aikin,ko ka manta Kai din matacce ne se in ta farka ne za ta baka damar dawuwa rayuwar bil adama?”

A fusace sarki Damurdar ya ɓace nan take ya bayyana a gaban Aljani Gautam suwami “Ina sane da cewa na mutu shekaru dari hudu da suka wuce amma kaima ka dinga tunawa da matsayinka na aljani dan haka kar ka wuce iyakarka “
“Ka dakata kar ka yi gangancin cin mutuncina domin yanzun nan zan mayar dakai in da baka yi niyar komawa ba”


Ganin faɗar nasu da suka saba ko da yaushe zasu ci gaba ne yasa Galuuur furta “shin menene amfanin wannan sa’in san da ku ka tsaya yi da junan ku ?yakamata izuwa yanzu ku gane wani abu daya ba tare da dukkanku kun bayar da haɗin Kai ba babu abinda ze kammalu in kuma haka ku ke bukata ni zan iya tafiya tsibirina “

Numfashi Sarki Damurdar ya ja kana ya ce “shikenan yanzu a yi min bayanı akan abinda yake faruwa “

Kallon tukunyar dake masifar tafasa Galuuur ya yi “a yanzu mun ci rabin aikin da muka fara rana ku kaɗan ne suka yi saura komai ya kammala,yau kwananta talatin kenan a cikin wannan tukunyar tsafin tana dafuwa duk wani nau’in tsafina babu wanda ban yi mata shi ba na maka rantsuwa da gemun kakana wannan yarinyar zata zamo barazana ga kowa in na ce kowa Ina nufin har da mu kanmu “

“Ban fahimce ka ba ta ya ya? “sarki Damurdar ya tambaya
“Kwarai kuwa ka sani ba tilasta mata aka yi ta zo garemu ba ita ce nan ta kawo kanta domin wutar daukar fansa dake ruruwa a cikin ranta duk wani tausayinta ta watsar dasu,ko da Suwami ya kawota wannan fada na sanar da ita in de tana son daukar fansar ta se an bata karfin iko,amma Ita abinda ta faɗa se da mukasha mamakinsa “Ina son ka mayar dani mafi karfin iko da mafi hatsari a cikin bil adama da aljanu yanda zan dau fansar abinda aka min a kuwait” ko da jin abinda ta se ka fado min a rai domin kana bukatar macen da ta kasance me ikon da babu kamar ta wanda za ta baka damar dawuwa wannan duniya a karo na biyu,hatta ni nan da na tsafanceta se ta ninkani karfin tsafi da rashin imani fata na shine ta bada hadin kai wajen dawo dakai wannan rayuwa,a gaba daya tarihin duniya ba a taɓa yiwa wani mahalukin irin wannan tsafin ba”

Ko da Jin wannan bayanı na Galuur nan take hayaki na ɓacin rai suka soma fita a kunnen sarki Damurdar idanunsa lokaci guda suka juya izuwa baki babu farı ko kaɗan a ciki.

Dariya me sauti aljani gautam suwami ya fashe dashi ya na faɗin

“Shin kishi ka ke yi da ita don tafika karfin iko ? Mutum in ya yi sati daya a cikin tukunyar tsafi yana dafuwa wani irin tarin karfi da tsafi yake samu balle a ce mutum ya kwashe wata kuda da yan kwanaki yana dafuwa a ciki shin ka kiyasta wata irin masifa zata fito dashi domin asalinta dama bata da sauki balle yanzu,wallahi Ina tausayin duk wanda ya shiga hanyarta “ ya karasa da wata dariya.

“Sam babu kishin haka a raina babban damuwata shine in ga na dawo wannan rayuwar na samu karfin iko,Ina son in dawo da ƴata izuwa wannan duniyar itama domin cikar muradinta”dafa kafadarsa Galuuur ya yi “kar ka damu kai de ka bamu hadin kai kawai in muna gabatar da aikin mu karka takura mana” bece musu komai ba se ma bacewa da ya yi hakan yasa suka zauna suna ci gaba da abinda suke yi.

TAKAITACCEN TARIHIN MASARAUTAR FALASHFUR.

A shekaru dari biyar da suka gabata masarautar ya kasance me karfin Mulki da yake baza ikonsa a gaba daya india kuma masarautace da ake baza zalunci na fitar hankali,bayın wannan masarauta sam basuda yancin kan su an mayar dasu kamar dabbobi.
Sarki Damurdar shine yake mulkarsu ya kasance mara imani da tausayi yana da yarinyarsa kyakyawa guda daya da yake masifar ji da ita me suna Gimbiya Ananniya mahaifiyar ta ta mutu ne wajen kawo ta wannan duniyar hakan yasa sarki ya dauki son duniya ya daurawa wannan ƴa tasa,baya son ko da ƙuda ne ya taɓa fatar jikinta. Sarki ya kasance yana da matukar kaunar ya ga ya samu karfin ikon da babu me irin sa a wannan duniyar hakan yasa ya dinga haduwa da manyan matsafa ta ko Ina domin su mayar dashi shahararren matsafi kuma babban sarki da ko Ina

Please Login or Register in order to submit comment