Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gare jiki ya yi sauki sosai Allah yabar zumunci.



Don’t forget to like,comment and share fisabilillah❤️😊


Allah yasa mu yi kyakyawar karshe.
https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207




⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩





❤️🔥Page 17–18




Tura kofar dakin nata ya yi ya shiga,takawa ya yi izuwa inda take tsaye a bakin window ta harɗe hannayenta a kirji ta zubawa guri daya ido. Numfashi ya sauke kafin ya iso gareta batare da ya furta komai ba. Sunfi tsawon minti goma a haka bawai dan bata san da zuwan sa ba se dan tana cikin ɓacin ran da bazata iya furta kalma daya ba a dalilin abinda ya faru.

Gajiya ya yi da shurun? ya ɗan sauke ajiyar zuciya tare da ɗaura hannunsa akan kafaɗarta.

" Gimbiyata"
Kallon sa ta yi na wasu sakanni kana ta kawar da kanta gefe taci gaba da kallon waje.

Slowly kamar wacce a ka wa dole ta furta "Farasat bana yanayi me dadi,ina bukatar kasancewa cikin kaɗaici."
Ta karasa maganarta tana zame hannun sa a kafaɗarta. Dama yasan za'a rina ko kaɗan be ji dadin abinda ya faru yau ba duk da ita ce nan ta jawo komai.

" Gimbiyata nasan abinda ya faru yau ya baƙanta miki matuƙa,amma kema kinada laifi.Muzna yar uwace a gareki wacce take tsananin kaunar ki da kuma kaunar abinda ki ke kauna,so why don't you respect her decision? tana matukar kaunar Zubair so why don't you support her? Bayan baki bata goyon ba ki ka je har gidan wanda take so ki ka yi abinda be dace ba,wanda kema da kan ki kin san hakan ba dede bane.ban taɓa ganin Muzna cikin ɓacin rai irin na yau ba,kin karya mata zuciya,ya dace ki sameta ki bata hakuri”

Duk abinda ya faɗa tana jinsa tunda ya fara magana ta tsura masa ido,bawai dan ta yi danasanin abinda ta aikata ba se dan tunawa da tayi Muzna na fushi da ita.

“ Zan bata hakuri ,yanzu ka tafi ina da bukatar hutu.”
Tunda ya ji haka ya ɗan samu relief a zuciyar sa saboda baya son abinda ze shiga tsakaninta da yar uwarta na ɓacin rai saboda alkawarin da ya ɗaukarwa marigayiya,baze taɓa barin wata yar tsama ya had’a su ba,yanzu tunda ta amince zata bata hakuri magana ta ƙare. Fita ya yi daga bangaren nata ya kyaleta,Tana Jin fitarsa ta taka gently ta nufi kofar bedroom din ta murza key tare da hawa royal bed din ta tayi kwanciyarta.


Yana cikin bedroom din sa zaune a bakin gado gabansa kuma bedside table ne ɗauke suke da kwalaben giya ga wasu kwayoyi masu yawa watse akan table,shi kuwa yana cize lebensa da suka dan tashi kad’an sakamakon taunesu da ya rinka yi ga idanunsa sun yi jajur se lumshewa da kan su suke,gashin kansa kam ya gama hargitsasu. Kallo daya zaka masa ka fahimci tun dazun yake shan wa’yannan giya da kwayoyi.ɗaukar kwalba daya ya yi ya buɗe ta ya kafesa a baki yana kwankwaɗa kamar wanda ya samu ruwan lemo haka yake shan sa. Be cire a baki ba seda ya shanye gaba daya tukuna ya daga kwalbar ya wurga a jikin bangon dakin nan take ya tarwatse cikin maye murya na fita a hankali ya ce

“ Muzna why?why meyasa za ki min haka?duk irin soyayyar da nake miki bakya gani idon ki ya rufe akan wanda be Kai ba.tabbas Zubair yana daya daga cikin mutane masu matukar sa'a a rayuwarsu domin duk namijin da ya mallaki mace irin ki ya yi dace matuka. Zan tafi in yi nesa dake yanda bazan dinga kallon ki da wani namiji ba”
Wa’yannan sune abubuwan da yarima Ishaq ya ke faɗa cikin sambatun maye shi kaɗai yasan abinda yake ji a ransa musamman in ya tuna amsar da Muzna ta bawa Galadima Abdul aleem nacewa Sadauki Zubair take so ba shi ba.

Kwayoyin ya ɗauka kusan guda biyar ya jefa a bakin sa yana taunesu ya kuma buɗe wata kwalbar giyan ya kora da kwayoyin da ya gama taunawa.
Yafi awa daya yana abu daya se da jikinsa ya yi mutuwar da ko yar yatsarsa baze iya ɗagawa ba sannan ya mirgina ya kwanta bacci me nauyi yayi awon gaba dashi.


“ Finally mafarkin ki na zama matar Sadauki Zubair ya cika “ Jadwah ta faɗa tana faɗuwa akan makeken gadon Muzna cike da farin ciki.
Murmushi kawai ta yi tana balla botil din wuyar rigar da take sanye dashi kafin tasa hannu a bowl dake cike da fruit ta ɗauki slide na apple tasa a baki.

Jadwah ta sake cewa “ shin yanzu hankalin gimbiya ya kwanta?wannan rana ya kasance babbar rana ce a garemu “.

“ Tabbas wannan babba rana ce kuma bazan taɓa manta wannan rana a cikin tarihin rayuwata ba”.

Murmushi su ka saki a tare kafin Jadwah ta furta “ Zan miki rakiya gurin Sadaukin ki ne?”
“ ah ah bazan barsa ya kuma haɗuwa dani ba se kwanaki sun ja”.

Duk da bata san menene dalilin da ya sa ta faɗi haka ba amma tayi shuru se ma sa hannunta da ta yi acikin bowl din ta soma shan fruits din.
Suna shan fruit su biyu suna kuma hira su Hamra suka shigo aka ci gaba da su,tunda wannan abun ya faru sam bata bi ta kan Muzaina ba saboda yanda ta bata mata rai dukda hakan ya juya ya zame mata alkairi.


“Dubeki tambadaddiyya mara kamun kai,.ke kowa kin mayar dashi abin wulakantawa bayan kece nan wulakantacciya,ke a ganin ki abinda ki ke yi burgewa ne?,to jahilci ne domin babu wanda ze ringa wulakanta dan adam da ya wuce jahili sam bakiyo halin Sarkin sarakuna me adalci ba balle sarauniyar mu,kin san da cewa Muzna ta fi ki komai?,to in ba ki saniba yau bari in faɗa miki yar uwar ki ta fi ki hali me kyau,ta fi ki sanin darajan dan adam ta fi ki zuciya me kyau,komai ta fiki.ke kawai hoton fuskarta ne amma you’re nothing compared to her,in kina gadara da wannan matsayin da ki ke tunani za ki samu to bari kiji da wannan bakin halin naki babu wanda ze kaunace ki”.
Wa’yannan bakaken maganganu na Sadauki Zubair su ta din ga ji a cikin baccin ta wanda hakan yasa ta farka babu shiri tana had’a zufa,hannu tasa ta ɗauki bottle water dake gefen gadonta ta balla murfin ta kafa a baki se da Tasha fiye da rabi kafin ta ajiye batare da ta rufe ba.

“ Hakikanin Gaskiya Zubair se na kawo karshen rayuwarka zan samu salama ka wulakanta ka kaskantar dani a gaban jamaa,hakan be wadatar ba har se da ya Kai Ina mafarkin munanan maganganun ka a bacci na?Muzaina bata barin bashi wannan alkawarina ne “. Ta faɗa haka tana me huci da zare ido.


KINGDOM OF WISDOM


Wasu chinawa ne guda biyu daya dattijo daya kuma matashi sanye cikin jajayen Kaya a jikinsu se kuma wani kyalle da suka ɗaura fari a kunkumin su da kansu dashi. Kallo daya za ka musu ka fahimci horarrun masu bayarda horon dabarun caskale ne duba da yanayin tsayuwar da suka yi kamar masu jiran ko ta kwana.
Tafiya take kamar bata son taka kasa saboda yanda baccin safen be ishe ta ba amma Queen Jessica ta bada umarnin a taso ta domin masu bata horon faɗa sun zo.jikinta sanye da wando da Riga masu girma wanda zasu bada balance wajen training din farare se kuma abinda ta ɗaura kunkuminta da shi baƙi.
Shiga fighting Area din ta yi Wanda an waresa ne na musamman a cikin palace din domin irin haka ko ta Ina ka kalla a jikin bangon wukakene farare sol se sheki suke yi da daukan ido,babu kalar makamin da babu a gurin se wanda Baka nema gani ba.
Tana shigowa idanunta ya sauka akansu cike da girmamawa suka gaishe ta cikin harshen Chinese kasancewar tana Jin yaren ne ta amsa musu.kamar yanda aka sanar da su abinda zasu yi nan suka faɗa mata cewa an kawo su ne domin bata horo na Musamman na iyakacin kwanaki goma sha hudu. Gyada Kai ta yi sannan wannan dattijon ya fita ya barta ita da matashin nan ya soma bata horo dake ta saba da wasu saboda tun tana yarinya ake koya mata caskalen faɗa iri-iri yasa bata ga wahalar wannan din ba sede salo ne da ya kasance ba kala daya ba,wannan caskalen faɗa da hannu ne da kuma yanda zaka kaiwa abokin gaba farmaki da yatsun hannunka da kuma yin amfani da kafa,kasantuwar wa’yanda aka koya mata a baya yawanci yanda ake fada da takobi ne masu hatsari kuma ta kware fiye da tunani domin Princess Gabriel akwai hazaka in ta sa kanta a koyan abu tofa sam bata ganin wahalar komai saboda naciya irin nata.

Awanni biyu kaɗai suka kwashe ana bata horo yunwar da ta soma Jine yasa ta dakata tana squeezing face din ta cikin harshen Chinese ta ce musu an gama na yau zataje ta yi breakfast se sun hadu gobe.

Bayan ta fito ne ta wuce sashenta tayi wanka ta kimtsa cikin mini skirt da ya wuce cinyarta kad’an arch color se riga me guntun hannu gaban rigar da hoton katoton teddy black color hula me gashi gashi a jikinsa baki tasaka akan jan gashinta da ta kwantar dashi a gadon bayanta ta saka flat shoe shima baki ta yiwa jikinta barin Turare. Masu yi mata hidima suna daga falo tare da tunanin yau meyasaka Princess Gabriel bata basu damar sun shiryata ba suka ga fitowarta durkusawa suka yi tayi gaba suka biyo bayanta.
Dining area dake part din Queen Jessica ta nufa kanta tsaye dakata wa bayin suka yi daga farfajiyar falon ita kuma ta wuce dining,langwabewa tayi kamar wata me shirin yin kuka ta ja kujera ta zauna kallon ta duk suka yi cike da kulawa.
“ Princess wanene ya taɓa ki naga kina kokarin yin kuka?”
Uncle Joseph ya tambayeta yana shafa kumatunta , sake tura ba ki tayi bata furta komai ba ta rike hannun uncle Joseph din
Ta ce
“ uncle Joseph Ina son in je k’asashe da yawa domin ganin yanda duniya take da faɗi,Ina son in ga abubuwan ban mamaki wa’yanda basa wannan ƙasar amma Mom ta hana hakan tunda ta haifeni ban taɓa taka kafata a wani ƙasar ba,daga Ina ki ka fito England,Ina ki ka je England. Ni shikenan a wannan ƙasar zan karasa rayuwata ne? Ni ma Ina da yancina kuma na gaji nima na girma yanzu “. Ta faɗa tana ɗauke kai nuna alamar tayi fushi.
Girgiza Kai kawai Queen Jessica ta yi ta ɗauki coffee ta soma sha.
Murmushi Anty Jennifer ta yi tana duban Princess Gabriel,buɗe baki tai zata yi. Magana mijinta ya rigata ta hanyar faɗin

“Yi shuru Shaleleta ki kwantar da hankali zan yi magana da the Queen kin ji ko?”gyada masa Kai tayi sannan ya mayar da kallon sa kan Queen Jessica
“ yar uwa a wannan Karon yakamata ki duba bukatar da Princess ta zo dashi,akwai gundura ace mutum be taɓa barin ƙasar da yake yaje wani gurin yawan buɗe ido ba,kuma yanzu ta mallaki hankalin kanta,itama tana bukatar da taje wannan yawon duniyar koda na sati guda ne kar ki ce min ah ah “.
Ajiye glass cup din tayi cikin zallar Mulki ta ajiye hannunta akan table din ta kalle sa kana ta soma faɗin

“ Joseph ka sani Sarai yanda nake da makiya kuma suna nan suna baza ido domin ganin ta in da wannan yarinyar tawa ta fito daga wannan Ƙasar,shisa ka bazan bari ta fara fita ba se ta samu garkuwa na musamman wannan dalilin yasa zaa musu aure ita da Jay domin in ya aure ta zata fi samun kariya a tare dashi a duk inda take".
Taɓe baki princess Gabriel ta yi haɗe da buga hannunta akan table cike da sangarta da yin komai a matsayin bakomai ba wanda ya zamewa turawa sabo ta miƙe tsaye.

“ na gaji da Jin wa’yannan kalmomin naki mom,ko da yaushe da irin uzurin da ki ke kawowa ban yarda dake ba kina abu kamar mara Gaskiya. Su waye zasu farauci rayuwata? Ni yanzu ba yarinya bace da za ki dinga juyawa Ina bukatar yancina na gaji tir.” Ta faɗa tana me barin dining area ba tare da tasha koda ruwa ba,miƙewa Anty Jennifer tayi da sauri ta bi bayanta domin rarrashinta.

“ kin ga abinda nake faɗa miki ga shi yanzu ran shalele ya ɓaci ki yi nazari akan maganar nan “.
Numfashi ta sauke kafin ta dubi Alexander yaron uncle Joseph ta ce
“ yarona bi mommynka ku bawa princess hakuri.” Cike da yarinta yaron ya bar gurin da gudu.ya yi saura su biyu ne a dining

“ nasan tayi hakuri sosai shi sa na shirya mata bazatar yawon cin amarci kafin aure ita da Jay in ya dawo nasan zata ji dadin haka”.
Tasowa yay daga kujerar da yake zaunee ya zagayo ya rungume yar Uwar tasa cike da farin cikin abinda ta faɗa na amincewa Princess Gabriel ta fita yawon duniya.

“ tabbas wannan batu na ki ze matukar sanya princess farin ciki “ Cewar uncle Joseph,

“ na sani shi sa ban sanar da ita komai akan hakan ba “.

MASARAUTAR BAYAAN


Yau kwanaki uku kenan da abinda ya faru,a wannan kwanaki ukun Sadauki Zubair da Muzna basu samu haɗuwa ba domin ta kudurta aranta cewa bazata bari ya ganta nan kusa ba,sede duk sanda ta tabbatar da baya nan tana zuwa gurin Yumma su sha hiran su sosai amma duk da zuwan da take basu taɓa haɗuwa ba,A bangaren Muzaina kuwa tun wannan ranan ba ta sake fitowa a bangarenta ba saboda kunyar kanta da take ji gani take in ta fito kowa ze tsaya yana kallonta ne saboda abinda Sadauki zubair ya aikata mata yasa ta zabi ta kasance a bangarenta bata son hayaniya.kullum tunanin ta tayaya ne zata dau fansarta Akan sa saboda Marin da ya mata gani take yana nan akan fuskarta kowa in ya gani ze mata dariya.
Har wannan rana Muzna bata bi ta kanta ba tayi alkawari bazata taɓa neman Muzaina har se ta biyo ta bata hakuri tare da nu na nadamar abinda ta aikata.
Yarima Ishaq a daren jiya yabar Kuwait tare da yin karyar ana neman sa a gurin aiki,haka ya tafi cike da kewar Muzna da kuncin za ta kasance da wani bashi ba.
Ko da ya tashi tafiya bashi kaɗai ya tafi ba tare suka tafi da kanwarsa wato Hamra zata karo course.
Yau ma kamar yacce ta saba zuwa wajen Yumma tana part din su suna shan hira Yumma se laborin abubuwan da suka faru na tarihi take bata da wa’yanda tana nan suka faru da kuma wa’yanda itama labari kawai ta iske,ta nishadantu sosai da Jin wa’yannan labaran da kuma jin yanda wannan masarautar yake da ɗinbin tarihi na ban al’ajabi. Cike da yarinta da rashin sani ta tambayi Yumma

“ Yumma kenan yanzu duk wanda aka bawa sarautar Bayaan inde bashi bane asalin sarki ƙasar za ta ɗaiɗaice?" Gyada mata Kai tayi alamar kwarai kuwa sannan ta kara da faɗin

“ yanda magabata suka bayar da labarin lokacin da sarki na hudu ya hau karagar Bayaan mutane sun azabtu sosai yunwa da kishin ruwa shi ya fara hallaka al’umma,babu wanda yasan menene yasa hakan yake faruwa domin baa taɓa shiga tsananin matsi irin haka ba. duba da tun fil azal Bayaan Allah ya albarkacesa da dukiya da abinci hakan ya ɗagawa sarki da mukarraban sa hankali ,ko da suka tsananta bincike nan suka gano halin da aka shiga yana da nasaba da ɗaura sarkin da ba kujerar Bayaan ta zaba ba shine ummul aba’isin komai basu yi wata-wata ba suka sauya sa da ɗan uwansa,Kinsan wani babban abin al’ajabin da ya faru kuwa?”.ta tambayeta tana kallon idonta. Muzna da tsoro ya gama cika ta ta tsurawa Yumma ido ta girgiza Kai kamar kadangaruwa .
Dora wa da magana yumma ta yi

“ A na ɗaura sabon sarki kwatsam albarkar wannan masarauta ya soma dawuwa har se da ya fi na da, wannan dalilin yasa tun daga zamanin can har zuwa yanzu se an yi tantancewa sosai kafin a ɗaura mutum akan sarauta”.
Ta gama ba ta labari cike da tabbatarwa domin Yumma akwai son hira da bayarda tarihi.
tabbas tana jin dadin kasancewa da wannan baiwar Allah domin ta dauke ta ne tamkar mahaifiyarta da ta rasa shisa ta ware lokaci na Musamman da take kawo mata ziyara.
Suna wannan hira tasu suka ji takun tafiyarsa cikin jarumta ya shigo falon jikinsa sanye da Kaya na shahararrun Gwarazan mayaka hannunsa na rike da hula me kan damisa takobinsa na ajiye a gurin zaman ta a kugunsa. Ɗago Kai da tayi ya yi dede da ɗaura idonsa akan kyakyawar fuskarta ,sunkuyar da kanta ta yi kamar bata gansa ba ta ɗauki remote control na tv ta soma kamo tasha sam ba tayi tsammanin dawuwar sa yanzu ba da ta jima da fecewa.Tana Jin Yumma na yi masa sannu da dawuwa.

“ Bari in kawo maka ruwa”. Ta faɗa tana barin falon domin basu guri. Ta na Jin Yumma ta fice tayi wup ta miƙe tana me gyara mayafin kayanta da yake ja da ƙasa ta ratsa ta gefensa ta tsaya a tsakiyar falon,duk abinda takeyi da ido kawai yake binta Kayan da ta saka ya masifar mata kyau Kaya ne de irin na sarauta masu nauyi da fitinar kyau wa’yanda suka sha ado da duwatsun diamond doguwar riga ce me dogon hannu se doguwar mayafin da aka ɗofana mata a saman gashin kanta da aka yi mata donot dashi sauran aka dawo dasu gaba.

Daga inda take tsaye ta ɗan ɗaga murya ta na faɗin “ Yumma ni na tafi se wani lokaci.” Dake tana ciki bazata jiyo ta ba shisa bata samu amsa ba. Murmushi ne ya subuce masa wato shine bazata yi wa magana ba.
ɗan riƙe rigar ta tayi kaɗan saboda ya ɗan mata tsayi ta soma tafiya kamar bata san da mutum a falon ba,Gajiya ya yi da wannan diramar na ta yasa ya bi bayanta taku biyu me kyau yai ya iske mata yasa hannu ya riko na ta hannun tare da dawuwa gabanta ya tsaya yana binta da kallo murguda masa baki tayi tana kallon gefe.
Cikin muryarsa me dadin sauraro ya furta “ Gimbiya Ina miko gaisuwa ta a gare ki” Galla masa harara tayi ta bi ta gefensa zata wuce ya kuma shan gabanta a Karo na biyu ajiye hular ya yi da cire takobin ya ajiyesu akan table ya fuskanceta ya riƙe kugu kamar mace
“ wai wannan bata fuskar duk na menene ni da yakamata in yi fushi dake na boye min kan ki da kika yi,shine ke zaki dinga bata rai!”
Harara da murguda Baki masa dan karamin bakinta ta yi a Karo na biyu tai.

“ Nikam kabani hanya in wuce ana jirana “.

Dariya ce taso kubce masa ganin yanda ita a dole ta dage se ta had’a fuska amma bata sani ba her face looks very funny.

Duka hannayensa ya Kama kunnensa dasu alamar ban hakuri “ Tom shikenan na ji na ƙarɓi laifina a yafe min,in kuma za ki min hukunci ne a shirye nake inde za ki hakura”
Ko da Jin haka taɗan saci kallon sa tare da fakar idonsa ta ɗaura hannunta akan takobinsa da ya ajiye tare da hula,ɗauka tayi taja baya dashi,wani irin shock ne ya ja ta lokacin da ta zaro wukar daga mazauninsa ta ɗaga sa sama ta soma jujjuyasa a bisa iska kamar me farautar abin hari cike da kwarewa,hannunta daya ta mayar baya taci gaba da amfani da dayar hannunta ,zallar mamaki ne ya hana Sadauki Zubair iya motsawa ganin yanda take sarrafa wukar kamar don ita aka yi sa ko kuma jarumar da ta jima da sanin salo na fafatawa.A iya rayuwar da suka yi bata taɓa basa labarin ta iya ko da iya rike takobi ba balle har iya aiki dashi ba,In fact ba ma wannan ba Muzna kallo daya zaka mata ka fahimci hutu da son jiki ya ratsa jinin jikinta wa’yannan abubuwan duk bazata iya su ba domin ko doki bata iya hawa ba, in takaice muku ma tsoro take ji tana da raki,yana wannan tunanin ya ji ta aza masa wuka a setin zuciyar sa kallonta ya yi yana me ɗaga mata gira,itama girar ta ɗaga mai tare da furta
“ So nake yi in buɗe ajiyar zuciyar ka in zaro soyayyata da take ciki domin yanzu nasan kaɗan ya rage a cikinta “.
ɗauke idonsa ya yi akan fuskar ta ya ɗaura akan wukar dake setin kirjinsa sannan ya saki kayitacciyar murmushi ya ce

“ inde hakan ze faranta miki a shirye nake tsaf “.
“ Tom taya ma zan iya ciro zuciyar ka waje bayan rigar dake jikinka ya min shamaki “ta faɗi hakan a shagwabe,ɗauke kallon sa ya yi daga kan fuskar ta ya mayar dashi kan wukar da ta ɗaura bisa kirjinsa a hannunsa ya ɗaura yatsunsa ya ɗaura akan bakin wukar ya soma tafiya dashi,zaro idanunta waje tayi ganin yanda yasa hannunsa a Kai batare da tsoron ciwon da ze ji ba sede abinda ba ta sani ba wukar ya zama mallakin sa babu abinda ze yi masa na cutarwa.Karaf ya riko hannunta da take rike da wukar ya karba ya maidasa cikin gidansa.
“ Nurul qalbi wannan wasar buyar ya isa haka na tuba,Kinsan de kin azabtar dani,amma meyasa baki taɓa faɗa min kina da horon amfani da takobi ba?”

“Nifa ban taɓa amfani da takobi ba ban ma san ya ake yi ba”. Cike da rashin yarda da abinda ta faɗa mai ba ya sake jefa mata wata tambayar “ To taya aka yi ki ka iya sarrafa sa kamar wacce ta jima tana amfani dashi ?”

“ ni ma ban sani ba,ban san ya hakan ya kasance ba lokacin da na ɗaura hannuna akan wukar naji wani al’amari a tare da ni,bani ce ke sarrafa makamin ba shine yake sarrafani “. Tunda ta soma magana yake kallonta kafin kuma cikin hanzari ya zaro sa daga gidan sa yana kallon jikinsa ko da ze ga wani rubutu a iya sanin sa wannan wukar ya zama mallakin sa babu ta yanda zaa yi wani ya iya amfani dashi,sede in har abinda yake tunani gaskiya ne wukar kenan mallakin sa mutum biyu ne ko ma fiye da haka,duk wani abu da ze duba wanda ze zamo masa shaida ya duba amma be ga komai a jiki ba hakan yasa ya canza zancen ta hanyar fadin.

“ shikenan to zo ki zauna mu yi hira na jima ban gan ki ba”. Noƙe masa kafaɗa ta yi tana me faɗin “ naɗi din tafiya na zan yi tunda ko yaushe se de ni in neme ka amma Kai ba ka taɓa nemana “.

“ naƙi din tafiya na zan yi tunda ko yaushe se de ni in nemeka amma Kai ba ka taɓa nemana “. Ya kwaikwayi yanda ta yi magana dariya ta tuntsire dashi haɗe da rufe fuskarta da hannu,murmushi ya yi yana kallon yanda take dariya gwanin burgewa komai din ta yana matukar jan hankali ya kasa ɗauke idon sa akan ta.
Cike da so da kauna ya ce “ Gimbiya ta bazan taɓa gajiya da faɗa miki ke din kyakyawace me kyawun dabi’un ba komai na ki na Musamman ne”.tsagaitawa da dariyar ta yi “ Kai ma haka masoyi ban taɓa ganin me kyau kamar ka ba”.Lakatar hancinta ya yi yace “ mu je in raka ki”.
Fitowa suka yi har zuwa gate din main part ya rakata bayin dake tsaye a gurin suka gaishesu cikin girmamawa,tafiya ya yi a yayinda ita kuma suka bude mata kofa ta shige.
Tsaye take an upstairs tun fitowarsu da rakota da ya yi take kallon su tsaki ta yi kafin ta bar wajen ta nufi hanyar da tasan Muzna nan za ta bi.

“ Hey

Please Login or Register in order to submit comment