Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakaken kaya,gaisuwa suka diba a gurin shugabarsu sannan ta ba su umarni da kowa ya kawo mata rudunar sojojin tsafi guda dari biyu. Nan take kuwa kowa yakawo abinda ta bugata kafin a ce kwabo masarautar falashfur ya cika da tarin aljanu mayaka jikinsu sanye da kayan yaƙi baƙi,ga mugayen makamai a tare dasu.fuskarsu cikin hula baa iya ganin fuskarta tasu.

Tana darıya me cike da annashuwa ta furta “hakan ya min dadi matuka......masarautar Bayaan da al’ummar dake cikin sa gani nan zuwa gare kuuuuu”.



Tashin hankali ana wata ga wata🤭🤭🤭babu abinda zan ce sede in ce Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu.

Comment and share fisabilillah ☺️

Se kuma jibi in me duka yakaimu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207


⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥



🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚📚🖋️⚜️


❤️🔥Page 24–25–26


*Kamar yanda ku ka sani wannan littafin paid book ne,yanzu saura pages kaɗan free book ya ƙare,ya kamata tun yanzu ku fara biya kafin lokacin ya yi dan banason ɓata lokaci ina gama book one za'a ɗaura da book two*
*Ga duk me son biya, littafin ƊAYA CIKIN BIYU naira ₦300 ne only ga mutane 20 da zasu fara biya yanzu,zanyi discount ne ga first mutane 20 da zasu yi payment wayanda suka zo abaya zasu biya darı biyar ne 500,dan haka ku hanzarta kar wannan damar ya wuce ku☺️☺️☺️😘. Za'a biya via opay account 8166018849 Aisha Abbas bidami opay account,idan mutum ya tura da kudin se ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta whatsspp number ta 08166018849 or 09024503194 Mrs isham.
Ga wa'yanda basa iya tura kudi ta opay account,zasu iya sawa ta wannan account din 9132302657 Aisha abbas bidami Palmpay account,duk wanda ya tura ya yi screenshot na evidence of payment ya tura min.
Kar ku bari wannan labarin a yi sa batare da ku ba❤️😘yan Nijer kuma su min magana.




Yau ne ake gudanar da al’adar zaab al’ada ce da ake yi yayin gudanar da bikin aure in da za a kira kwararrun wa’yanda su ka iya henna su yıwa amarya da danginta. hakance ta kasance Sarauniya Muzna da su Jadwa suna main falo an yi musu henna masu kyau hannu da kafa suna sanye da farin sari masu kyau da ado ita kuma sarauniya amarya na sanye da yellow sari. henna da aka mata ya bushe ya yi brown wankewa ne ya yi saura ana jiran amintacciyar baiwa ta zo da ruwan madara a domin a wankewa sarauniya henna,a gefe guda kuma mata yan wasan kwaikwayo suke ta kiɗe-kiɗe da raye-raye a tsakiyar falon,duk wa'yanda suke waje mata ne zalla babu maza saboda baa bukatar maza da su ziyarci wajen gudanar da wannan al’ada.
Sarauniya Muzna da wakar da ake yi yake tsumata se gyada kai take yi tana kwaikwayan wakar.

“Tabbas sarauniya kına cikin farin wannan aure na ki”cewar Jadwah
“Kwarai kuwa ina cikin farin ciki domin wannan shine burin rayuwata auren wanda na ke tsananin kauna “

“Mu na me ta ya ki murna sosai”cewar Aliyah.
Murmushi kawai ta yi tana ci gaba da rawa da kanta,”Marwa zo ki gyara min wannan gashin nawa yana zubomin a fuska”cikin biyayya Marwa tazo ta gyara mata gashin ta mayar dasu izuwa baya.
Miƙewa Jadwah da Aliyah suka yi suka shiga tskaiyar filin da yan rawan suke taka rawa suma suka fara gudanar da rawa irin na su na larabawa,sarauniya dake zaune se darıya take musu ita da su Ummu zaheenat da gudu suka dawo inda take suna me riƙe damtsen hannunta yanda baza su ɓata mata henna ta ba ta miƙe tsaye.
“Ya Allah me ku ke yi ne haka Aliyah da Jadwa?” “Yau ranar ki ce sarauniya yakamata ki taka rawar farin ciki,nan da kwana uku za ki amarce tare da angon ki Sadauki Zubair”Jadwah ta faɗa mata suna shiga cikin filin nan suka fara rawa cike da farin ciki.wa'yanda su ke zaune suna kallon su kuma se tafi suke yi a garesu,shigowa falon amintacciyar baiwa tayı hannunta riƙe da bowl din silver me girma yana cike da ruwan madara ga furanni a cikin sa ta ajiye ta tsaya tana kallon yanda suke taka rawa saboda jin dadi murmushi kawai ta yi,can kuma se ta dafe goshi a hankali ta furta

“Ya Allah….na kasance ma’abociyar mantuwa lokacin da uwar gijiyata ke a raye ta bani wasika in bawa duk wacce ta hau sarauta amma na gagara yin hakan gaskiya inada da sakarci.dole in samu sarauniya Muzna in ba ta wannan wasika domin in sauke wannan nauyin da ke rataye akaina “

Suna tsaka da shagalinsu aka buɗe kofar falon dakatawa suka yi suna kallon wanda ya shigo din.
Rai a ɓace Ummu Zaheenat ta furta “ya kai Barmaki wanene ya baka izinin shigowa a yayinda sarauniya take tsaka da nishadi?” Zubewa ya yi a ƙasa yana faɗin “Ina me neman afuwar sarauniya na tuba nasan na aikata kuskure….nazo ne a domin sanar da sarauniya tana da baƙi a fada shugaban kasar Kuwait ne yazo a domin ganawa da ita”

“Sarauniya ta yafe maka….ka sanar dasu ta na nan tafe zaka iya tafiya”Ummu zaheenat ta faɗa masa haka tana me nu na masa hanya,bayan ya tafi ne sarauniya Muzna ta zauna akan kujerar da ta tashi,wanke mata henna aka yi ya yi matukar kyau ga ta fara sol henna kuma brown ya yi wa hannu da kafafuwanta kyau matuka,karamar towel aka miƙa mata ta goge hannunta da fuskarta

“Sarauniya kına da bukatar zuwa turakar ki a domin shiryawa”cewar amintacciyar baiwa
“Babu bukatar haka amintacciyar baiwa can je ne a domin ganawa dasu bawai zaman fada ba”
Ta yi maganar tana gyara zaman gashinta taname saukar da su izuwa kafadarta ta yi gaba su Marwa suna me rufa mata baya,fadawan dake tsaron kofa ne suka yi saurin buɗe mata babban kofar falo suka fita. Koda suka shiga falon sun iske shugaban ƙasa da mutanensa da kuma manyan fada,tana shigowa kowa ya miƙe tsaye

“Amincin Allah ya tabbata agareki yake yar sarki Taifur Rahman jika ga Muazzam Rahman,yarda da Rahaman ubangiji su sauka a gareki “cewar shugaban ƙasa

“Ameeen ameen ya tabbata a garemu gaba ki daya barka da ziyartar wannan daula ta mu”ta yi maganar tana me zama akan kujerar mulkinta ta kuma faɗin “na ji dadın amsa wannan gayyatar nawa da ka yi duk da an shaida min baka wannan ƙasa”.

“Babu wani wanda ya isa ya ƙi amsa gayyatar sarauniya da kanta”
Murmushi ta yi me aji tana me nu na masa gurin zama “Bismillah Shugaban kasa Dawood ibni Mansuur”

Zama ya yi a kujera na kusa da Galadima Abdul Aleem yana furta “Ina me tayaki murna. labarin auren ki nan da kwanaki uku ya riskeni tabbas wanda ya sa me ki a matsayin mata ya matukar dacewa domin ke din ta musamman ce”kallon Sadauki Zubair dake a kujerar sa ta commander a zaune yana kallon su tai. murmushi ta yi ta dawo da kallon ta kan shugaban kasa Dawood ibn-i Mansur.

“Nagode… mu je kan dalilin bukatar ganin ka…maganar karawa taswirar wannan masarautar girma da kuma yi mata tsare-tsare ne ya taso yin haka nada matukar muhimmanci”

jinjina kai ya yi “kwarai dagaske hakan nada matukar muhimmanci ga wannan babban masarautar da babu kamar sa a gaba daya ƙasashen larabawa”
Gyada kai ta yi ta kalli waziri shi kuma ya kalli Barmaki ya ce “ka je ma’ajiyar tarihin wannan masarauta ka ɗauko taswira “
Duƙawa ya yi sannan ya tafi a domin ɗaukowa.

Bayan mintuna goma ya dawo da gudu yana zubewa a ƙasa cikin tashin hankali ya ce “ki yafeni shugabata amma babu taswirar wannan masarautar a ma’ajiyar tarihi”

“What……”ta faɗa tana miƙewa tsaye. su ma cikin tashin hankali gaba daya suka miƙe jin wai babu taswirar Bayaan.

“Barmaki ba ka da hankali ne?kasan me ka ke faɗa kuwa ?taswirar da yake nan tun zamanin kaka da kakannin mu shine yau kwatsam za ka ce babu wannan taswirar?maza ku je ku nemo sa kar wanda ya dawo min nan ba tare da wannan taswirar ba” Galadima Abdul Aleem ya faɗa rai a bace,da hanzari dogarawa guda ashirin su ka fice a domin neman taswirar.

“Kowa ya zauna”ta basu umarni a yayinda ita take tsaye tana harɗe hannu a kırji,seda su ka zauna gaba daya tukuna ta soma magana

“Ban san ya kalar wannan taswirar take ba kuma ban san a Ina yake da zama ba. amma abu daya nake da tabbaci akai shine tabbas hannu aka sa aka sace wannan taswirar ko kokwanto bana yi akan hakan. Babu yanda za a yi taswirar da ya kasance yana nan tun tsawon shekaru aru-aru be taɓa samun ko da kuskuren wajen ajiya ba amma yau a wayi garı babu shi tabbas ɗaukesa aka yi amma to Waye wannan?”

“Wannan haka yake shugaba dole a nemo in da wannan taswirar ta shiga domin duk wani sırrın wannan masarautar yana rubuce da zane ne a cikin sa,in har wannan taswirar ɗauke sa aka yi to tabbas ana shirin kawo mana farmaki ne ta ko ta kwana,zamu fuskanci yaƙi domin hakan ya tabbatar da makiyanmu ne suka sa a ɗauke mu su wannan taswirar “cewar waziri Abdul Qadeer.

Suna cikin wannan tattaunawar wa'yannan dogarawan suka shigo suna sanar da su sun bincika ko Ina amma basu samu damar ganin taswirar ba.nan fada ta sake shiga cikin ruɗu da tunanin hanyar yanda zasu tunkari abinda ke tunkarar su.

Duban shugaban ƙasa Dawood ibn-i Mansur ta yi cikin son kawar da bacin ran dake fuskarta ta ce “ya kai shugaban ƙasa Dawood ibn-i Mansur na ba ka damar tafiya muddin wani abu ya taso zan tuntubeka yanzu dole in ka war da abinda ya tunkaro mu.”

Jinjina mata kai ya yi sannan ya dubi mukarraban sa nan suka juya suka bar fadar.

Batare da ta kalli fuskar Sadauki Zubair ba ta soma magana“Ya Kai commander sojojin Bayaan Ina da bukatar sanin labari akan inda aka kai taswirar wannan masarautar. bayan da haka kuma a gurbanar da wa'yanda alhakin gadin ma’ajiyar tarihi domin bincikarsu dangane da ɓatar da taswira me girma ya yi,sannan abu na karshe ka tura wasu daga sojojin mu izuwa tsibirin Bayaanul araf domin ganin ko akwai sansanin makiyanmu a gurin. ina me jiran sakamako nan da zuwa karfe takwas na dare ka sameni a lambu”
tunda ta soma magana bata dakata ba balle haɗiye yawu se da ta dasa aya.

“Da umarnin ki ya shugabata”cewar Sadauki Zubair.

tana gama jin abinda ya faɗa ta bar fadar da sauri su Marwa suka bi ta a baya ganin yanda ranta yake a ɓace abinda basu taɓa gani ba kenan,su kansu Galadima Abdul Aleem basu yi tsammanin za ta ɗauki al’amarin da zafi haka ba,yanda ta ɗau wannan zafi da nuna fushinta akan ɓatar taswira hakan ya tabbatar musu da jajircewanta akan dukkan al’amurar da suka shafi wannan masarauta.

Cikin kankanin lokaci suka fara gudanar da umarnin da ta ba su,ita kuma tunda ta tafi ta kadaita kanta a bedroom din ta tana safa da marwa tana tunanin wanene haka yasa hannu ya ɗauki taswirar nan,tabbas in har hasashen da Waxiri abdul Qadeer ya yi gaskiya ne to yaƙi ne ke nufosu kuma batare da sanın su ba ana shirin yi musu farmakin farat daya wanda hakan ze cutar da yara da tsofaffi hakan yasa hankalinta ya tashi.

Karfe takwas da yan mintunan ta nufi lambu tare da fadawa biyar masu kula da lafiyarta se kuma kuyangu uku zama tayı akan kujera tana jiran Sadauki Zubair,ba a jima ba kuwa ya shigo da sojoji ya basu umarnin dakatawa da ga gefe shi kuma ya karaso inda take yana sunkuyar da kai

“Yardar Allah ya tabbata a gare ki shugabata “
“Bismillah “ ta faɗa tana nu na masa gurin zama yana zama ya soma faɗin

“Ya shugabata nayi duk bincike na amma bamu samu wani shaidan da ze nu na ɗauke wannan taswirar aka yi. kuma masu alhakin kulawa da wajen sun tabbatar mana da babu kowa a gurin a domin gasgatawa har cctv camera se da mu ka duba amma babu komai babu wanda ya shiga ma’ajiyar tarihi,a dangane da mayakin mu kuma mun ziyarci tsibirin Bayaanul araf amma koda rumfa daya. Tabbas wannan al amari da ɗaure kai yake”

“Ina bukatar kebencewa da Sadauki “ cike da girmamawa suka sunkuyar da kai suna faɗin “tare da umarnin ki”sannan suka fita a lambun. Se da ta ga sun fice sannan ta sauke a jiyar zuciya

“Masayı duk hankalina ya gaza samun nutsuwa,shin su waye to zasu aikata hakan?ina matukar tsoro a kawo mana hari a lokacin da bamu da masaniya duk da inada kyakyawar yakini akanka da sojojinka amma in har ya kasance ana shirin kawo mana hari ne dole mu soma shiri “

Murmushi ya yi sannan ya sauka akan kujerar da yake zaune ya zare hular damisa dake kansa ya ajiye a inda ya tashi ya matso kusa da ita ya durkusa bisa guiwarsa yana me ruƙo hannunta na dama ya manna masa sumba “Sam bana son ganin ki a cikin damuwa,na miki alkawari bazan taɓa barın wani cutarwa ya afku a wannan masarautar ba se de in mutuwa na…..”hannunta me laushi ta ɗaura a bakinsa tana jujjuya mai kai alamar kar ya sake faɗar kalmar sede in mutuwa ya yi.

“Masoyi banason Jin wannan kalmar ta fito daga bakinka “murmushi ya yi yana janye hannun a bakinsa ya manna mai kiss a karo na biyu

“Afuwan nurul qalbi,,yanzu ki bar komai a hannuna zan ci gaba da bincike da sanya ido akan lamarin wannan masarauta se yanda karfina ya ƙare,amma Ina ganin me ze hana a ɗaga wannan auren namu se bayan komai ya lafa?”

“Mene ……?a ɗaga auren mu fa kace?babu abinda ze sa a ɗaga wannan auren koma me ze faru.aurenka shine burina “ta faɗa tana kawar da kai gefe saboda ba ta ji dadın maganar da ya furta ba,lumshe idanunsa ya yi ganin ranta ya ɓaci amma bawai da wata manufa ya faɗi wannan kalmar ba ya faɗe tane saboda yana ganin yakamata a fara shawo kan matsalar da ya tunkaro su.

“Tom amaryata zolayar ki kawai nake abar kaunata Allah ya nu na mana jibin da rai da lafiya”

“Ameen”
Zama ya yi akan kujerar da take a gefenta yana dafa kafadarta under his breath ya furta

“Tabbas ni me sa a ne,na samu macen da babu kamarta shin meye ze hanani san ki ?ni bawa ne a wannan masarauta haka zalika mahaifiyata da mahaifina ban taɓa tunanin zan yi taraiya da yar sarauta ba,ko a mafarki ban yi zaton cikin sauki zan samu aurenki ba,Tabbas ahalin Rahman nagartattu ne masu karamci da sanın darajan dan adam,batare da hantara ko duba da tazaran matsayi dake tsakaninmu daku na jinin sarauta mu kuma bayi,banida hanyar da zan godewa wannan bawan Allah da ya wuce in ta binsa da addua har abada”
Shanye hawayen da ke kokarin zubowa tayı tana me rintse hannunta a cikin nasa kanta a kasa “hakikanin gaskiya na yi tunanin tunda Ummi da Aba sun rasu bazamu taɓa samun yancinmu ba ko zaɓar abinda mu ke so ba a wannan palace,a lokacin da na faɗa matsananciyar soyayya da kai kullum da tunanin yanda yan uwan Aba zasu yarda da alakarmu nake saboda nasan abune mawuyaci su amince mana cikin sauki. amma wallahi nasa araina muddin basu amince ba zan tayar musu da hankali ko suna so ko basaso se sun aura min kai,se kuma da ikon Allah Abu Aleem ya bamu mamaki ta hanyar amincewa tabbas shi din dattijo ne me nagarta hakan yasa nake masa kallon Aba bana Jin na yi kewar mahaifina haka zalika matar sa tana bani kulawa fiye da yanda take ba wa yayanta shin me zan nema a wannan rayuwar ?sun zame min uwa da uban da na rasa Allah ya musu albarka “da ameen ya amsa yana kallon fuskarta yana sake yaba wannan kyakyawar halitta na ubangiji.

Hannu yasa ya ɗago habarta yana kallon cikin idonta a hankali ya furta “Muznaaaa” buɗe idonta ta yi ta sauke su a cikin nasa Jin yanda yakira sunan nata cikin wani irin salon rabon da ya ambaci sunan tun lokacin da basu fara soyayya ba. Gagara amsawa ta yi se kallon sa da take yi tana jin wani shaukin soyayyarsa na sake ninkuwa a zuciyarta,a hankali ya matso da fuskarsa izuwa nata har hancinsu na gogan na juna suna shakar numfashin juna

Manna mata kiss ya yi a saman hancinta yana kallon kwayar idonta “sarauniyata ki bani dama in sumbaci leben ki sau daya kawai dan Allah “dasauri ta ja baya kirjinta na bugawa kyaftawa kawai idanunta yake yi ta gagara sake haɗa idanu dashi

“Masayı meye ka ke cewa haka auren mu da jibi ne saurin me ye ka ke yi haka?”ta faɗa in nervous

“Nasani sarauniya sau daya kawai,a duk sanda nake tare dake zuciyata tana kwadaituwa da sumbatar wannan kyakyawar labban naki shin bazaki bani dama ba,ni da ke jibi zamu kasance ma’aurata shin laifine dan na bukaci hakan agurin matata?”

Matsowa ta yi tana rike hannunsa duka biyu a cikin nata ta ce “ka yi hakuri masoyi jiran da mukayi abaya in har ba mu gaji ba jiran awanni 48 baze mana wahala ba kar hakan yasa ka yi fushi .”

Murmushi ya yi yana miƙewa tsaye tare da ɗaukan hularsa da ya ajiye ya ce “Sam ban yi fushi ba nurul qalbi kuma kin yi gaskiya Allah ya nuna mana wannan rana me albarka,Ina bukatar umarnin ki domin tafiya ranki shi dade “
Hannu ta miƙa masa ya riƙeta ta tashi tsaye ta sumbaci hannun tana faɗin “zaka iya tafiya Sadaukin namiji abin alfaharina “

Murmushi ya sakar mata yana sunkuyar da kai sannan ya fice itama ta koma bangarenta wayarta ta zo ɗauka a domin yin kira ta ga baya kan gadon nan ta tuna ta bawa Marwa ajiyarsa hakan yasa ta kwala kiran “Balkisssss”da sauri wacce aka kira Balkis ta shigo tana faɗin

“Gani nan shugaba” “ki kira min Marwa”

“Da umarnin ki shugabata” ta fita bayan wasu lokaci Marwa ta shigo tana “shugabata ki yi min afuwa na manta wayarki na a tare da ni”
“Bakomai miƙo min shi “

Miƙa mata wayar ta yi tana tambayarta ko akwai abinda take da bukata tace mata babu komai za ta iya tafiya,tana fita ta zauna tana turawa Muzaina sako

“My twinning ykk ya masarautar Yemen?jibi aurena na yi bakin ciki sosai da ze kasance bakya tare da ni sam bazemin armashi ba,amma babu yanda mu ka iya kaddara ya riga fata ki kulamin da kan ki,Ina jiran reply din ki”ta tura tana kwanciya ruf da ciki tana wasa da wayar a goshinta,karar notification ne ya shigo da sauri ta miƙe tana buɗe replied din

“Ina cikin koshin lafiya fatan kema haka amarya?nima na so in halarci wannan auren na ki amma Allah be yi ba amma na miki alkawari bayan bikin zan miki bazata mu kwana lafiya Ina sanki “
Murmushi ta sake a fili ta furta “nima Ina san ki yar uwata”

Tashi ta yi tana tunanin abinda zatayi dan zaman ya isheta “bari in je bangaren su Jadwah mu yi hira ko zan rage wannan kadaicin “ta faɗa tana fice wa a bangarenta ta nufi nasu.
Tana isa ta ɗaura hannu akan handle din za ta buɗe amma maganar da ta ji suke yi ne yasa ta gagara buɗewa

“Aliyah wallahi nagaji da cin amanar Muzna,ita duk a tunaninta da yar uwarta suke chatting shin ya zataji ranar da ta gane gaskiya ?ina tsoron ranar da za ta gane wayar Muzaina na hannuna kuma ni ce ke mata reply a matsayinta”
Cewar Jadwah cike da damuwa,ajiyar zuciya Aliyah ta sauke tana faɗin

“The same thing nake tunani maganar da takeyi da ke tanajin dadi sosai saboda ta yi zaton da Muzaina take magana,tun farko se da na faɗa muku wannan ba shawara me kyau bace.tunda Muzaina ta bar wayarta kamata ya yi ace ankashe wayar “

Sarauniya Muzna was very shocked da jin maganar da suke yi nan take jikinta ya fara rawa tunda take a rayuwarta ba a taɓa mata abinda ya ɓata mata rai irin wannan ba,nan take idanunta ya rufe dan ɓacin rai,wannan abinda Jadwah ta aikata laifi ne me girma wanda bata tunanin zata iya yafe mata a tunaninta da Muzaina take magana ashe ba haka ba abin yake ba.

Danna kiran wayar Muzaina din ta yi tana buɗe kofar bedroom din na su,wayar Muzaina dake hannun Jadwah nan take ya soma ringing,jin an buɗe kofar ne yasa suka maida kallon su bakin kofar suna ganin ita ce suka miƙe tsaye a tsorace,takowa tayi har tsakiyar dakin tana bin su da wani kallo,tana kuma mayar da dubanta kan wayar Muzaina dake hannun Jadwah

“Why Jadwah? akan me yasa za ki ha’ince ni ?waye ya ba ki damar yin amfani da wayar yar uwata kına min magana kamar iits?na ce wa ya ba ki damar yin hakan?”ta faɗa a tsawace .

Murya na rawa Jadwah ta ce “dan Allah sarauniya ki gafarceni na san na aikata kuskure amma ki yarda dani bada son raina na yi hak…..”ba ta samu damar karasa maganar ba saboda marin da ta ji saukarsa a kumatunta dafe kumatun ta yi tana kallon Muzna da ta maretan tana
“İn de hakan ze sa ki huce ki sake mari na nasan na aikata miki ba dede ba”

“Sarauniya ki yi hakuri ki yarda da mu Jadwah ba ta aikata hakan saboda wani manufa ba”

Nuna su da yatsa ta yi “ku min shuru nace,wai yan uwana da nake kauna ne suke cin amanata unbelievable,how could you two did this to me?do you have any idea how happy I felt when ever I talked to her?ah ah ba ku sani ba kun mayar dani mahaukaciya wacce bata san me take yi ba kuna wasa da emotions dina” fisge wayar Muzaina din ta yi a hannunta tana kuma watsa musu harara,wayar babu password shiga ta yi ta ga chat din da suke yi har wanda suka yi yanzu ta yi deleting din su ta ɗago kai

“Jadwah tun kafin ki fuskanci bacin raina ki sanar dani waye ya ba ki damar yin haka “

Kasa magana Jadwah ta yi se Aliyah ce ta ce “Abu Aleem shine wanda ya ba ta umarnin yin hakan”

“Abu Aleem “ta maimata sunan tana ficewa a bedroom din a fusace da sauri suka rufa mata baya,kai tsaye main falo ta wuce saboda tana da tabbacin kowa yana can tunda ba a ci abincin dare ba tukuna,aikuwa tana shiga ta tarar da kowa suna hıra a falo suna ganin ta a fusace sun san ba lafiya ba,burki ta ja ta tsaya a tsakiyar falon tana duban Galadima Abdul Aleem ta nuna masa wayar Muzaina tana

“Abu Aleem shin menene abinda wayar Muzaina yake yi a hannun Jadwah har take tura min sako a matsayinta ?”runtse ido ya yi dama abinda yake gudu kenan kuma ga shi ya faru miƙewa tsaye suka yi cikin rashin gaskiya domin basu san me zasu faɗa mata ba

Yarıma Farasat ne ya ce “Sarauniya ba abinda ki ke tunani ba ne an yi hakan ne sabod…”katse sa Galadima ya yi yana faɗin “ka yi shuru Farasat….sarauniya ki koma dakin ki za a kawo miki abincinki “

“Really Abu Aleem in tafi daki za a kawo min abinci?ba wannan nake tambaya ba,yarıma Farasat maza sanar min saboda menene yasa aka bawa Jadwah wayarta,shin ko kun yi wa Muzaina wani abun ne ku ke boyemin menene ku ka mata?”ta faɗa da karfi duk se da suka sha jinin jikinsa,cikin dakiya Galadima babu alamun wasa yace “sarauniya ki tafi dakin ki nace”

“Bazan taɓa tafiya ba se na ji me ku ka yi wa yar uwata domin na san dukkaninku dama bakwa son ta”
Cikin tsawa ya ce “na umarceki da ki tafi dakin ki”

Cikin bushewar ido ta ce “a matsayina na sarauniyar wannan masarautar I command you to tell me abinda ku ka wa Muzaina kashe ta ku ka yi ?ko kuma wani gurin ku ka turamin

Please Login or Register in order to submit comment