Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za a dinga maganarsa,se de cikin rashin sa a hakan be yu ba domin wacce zata taimaka masa ya zamo abinda ze zamo din ba a riga da an haifeta ba wannan dalilin yasa ya fara binciken kananun jarirai duk inda yaji an haifi ya mace to se ya sa an bincika ko ita ce wacce yake nema amma sam baa dace ba.har tsufa ya fara riskarsa amma be samu cikar muradinsa ba kuma be janye akan bakarsa ba,Ana nan ana nan sarki Damurdar ya fara cutar ajali kafin ya mutu ya bar wasiyya ga matsafan duniya kan cewa in ya mutu a daga ruhinsa sannan kar a kona gawarsa a adanasa a cikin turakarsa aikuwa hakan akayi da ya mutu din,gimbiya Ananniya bayan mutuwar mahaifinta ne taji komai ya dena mata dadi yasa tasha guba ta mutu.a haka rayuwa ya ci gaba da tafiya babu sarki a falashfur nan matsafa da manyan aljanu suka dawo fadar domin cika abinda sarki Damurdar ya faɗa a garesu. Wannan shine kaɗan daga cikin tarihin su.

Washe garı tunda ta tashi ta yi sallah bata koma bacci ba tana zaune akan prayer mat tana karatun Qur’ani me girma da muryarta me dadin sauraro,se karfe bakwai ta ida karatunta sannan ta tashi tana cire hijab da kuma rigar da tayi sallah,ta saka riga da wando tana me daukar wayarta ta five. masu mata aiki already sun shigo sun fara gyare gyare suna ganin ta suka dakata haɗe da zubewa akan guiwowinsu suna gaisheta fuskarta ɗauke da faraa ta amsa tana kokarın riƙe handle din kofar Marwa dake kokarin shigowa ta buɗe kofar ja da baya tayı tana “barka da Safiya” “barka dai Marwa “

Ta faɗa tana ficewa da sauri Marwa ta bi bayanta suna tafiya har suka isa babban falon dake bangarenta inda anan zaa rinka bata horo,da mamaki take kallon cikin falon ganin Sadauki Zubair na zaune yana jiranta,abinda yasa tayı mamaki kuwa shine bata yi tsammanin yanda ta dako sammako zata iske sa ba.
Miƙewa yay “barka da Safiya shugabata “
Murmushi ne ya subuce akan kyakyawar fuskarta “barka dai masoyi na yi kewarka sosai”
Dukar da kai yayi alamar godiya “nagode sarauniya”
“Wayyo ni kam dan Allah ka bari kana sa ni jin kunya,ko ka manta aure za mu yi” murmushi kawai ya yi ya kalli Marwa da kanta yake kallon ƙasa tana murmushi jin conversation nasu.
“Ki ɗan ba mu guri “ seda ta durkusa kafin ta fice,a hankali ya tako izuwa gabanta ya riƙe hannunta yana me sumbata “nayi kewar ki yanda bakya tunani sauki da nake samu shine Ina ganin ki a fada,zuciyata kullum dake yake kwana yake tashi. Shin fada min ke kin yi kewata kuwa?”
Wani kallo ta yi masu me cike da nuni na tsananin son da take masa “nayi kewarka fiyeda yanda ka yi “
Ta ɓata fuska ta kuma furta “ Ni kwata-kwata bana son wannan rayuwar gaba daya a takure nake banida damar zuwa gurin mutane sede a zo gareni,jira kawai nake My Muzaina ta dawo ta karɓi mulkin nan ni kuma mu yi aure mu koma Russia “
Murmushi ya yi “Jiya galadima ya sanar da ni saura lokaci kalilan a fara shirye shiryen auren mu amma babu in da zamuje muna nan a Bayaan “ a shagwabe ta ce “whyyy please?” Yana kallon cikin idanunta da ta tsaresa dasu ya amsa mata da “Bayaan su na da bukatar mu sarauniyata in ki ka yi nisa da wannan masarauta abubuwa marasa dadi ne zasu faru”
Langwabar da kanta tayi gefe tana kallon sa batare da ta furta komai ba,barinta ya yi a tsaye a gurin ya koma inda ya tashi ya ɗauki takobi guda biyu ya bata daya shima ya riƙe daya,nan ya soma bata horo cike da kwarewa kuma Alhamdulillah tana kokari kasantuwarta me kaifin kwanya,awa uku suka ɗauka yana koya mata faɗa gajiya ta yi ta zauna dabas a kasa kamar me shirin kuka ta ce “ni de gaskiya na gaji masoyi se wani lokacin “
“Umarnin ki shine abinda zan bi shugabata “ “wayyooo ni dan Allah ka dena min haka bana so “ darıya ya yi dan dama yasani yanzu za ta ce bata so amma babu yanda ya iya dole ya bata girmanta a matsayinta na sarauniya.
Hannu ya miƙa mata ta kama ya dagota tsaye jikinsu na gogan na juna.
“Nagode da horon yau”ta faɗa tana sakar mai murmushi
“Aikina nake yi shugaba” “ya Allah..wai shin meye zan yi wannan kalmar shugabar ya fita a bakin ka ne fisabilillah?”

Cikin basarwa kamar bashine yay ya maganar ba ya furta “sumbata kaɗai ya isa ya sa bakin dena furta abinda bakyaso “
Zaro ido waje ta yi cike da jin kunya ta kwace a jikinsa ta fita a falon da gudu da dariya yabi bayanta dama yasan za a rina.

“Shugabata fatan lafiya na gan ki da gudu haka!?” Ta tsinkayo muryar Marwa dake jiranta a ba kin part din,cike da wayancewa ta dedeta nutsuwarta ta ce “mu tafi Ina bukatar yin wanka”


Wanka ta yi suka shiryata cikin dakakku kuma haɗaɗɗun kayan sarauta masu azaban kyau da daukar hankali saman kanta kuwa hular sarautar ta ce ya zauna daram akanta tayı kyau sosai cikin shigar kayan launin light purple da brown se duwatsun kayan farare. Kasancewar lokacin cin abinci yayi kuma wannan al adarsu ne cin abinci tare a matsayinsu na ahali yasa kullum suke cin abinci tare,tana isa main part din ta samu kowa ya hallara a falo ita kaɗai kawai suke jira,cikin tafiyarta na nutsuwa ta isa izuwa kujerar ta wanda yake a tsakiya ja mata kujerar aka yi ta zauna tana dubansu da murmushi,suna kokarin gaisheta ta yi saurin furta

“Assalamualaikum….barkan ku da safiya da fatan kowa ya tashi cikin aminci???”
Murmushi suma suka yi dan sun san meyasa ta yi hakan batason gaisheta da suke yi ne yasa inde ta zo se ta rigasu fara magana.

Amsawa suka yi Waziri Abdul Qadeer ya ce “sarauniya Muzna barkan ki da saukowa “
“Barka de Kawu Qadeer”ta faɗa tana faɗaɗɗa murmushinta.

“ƴa ta Sadauki Zubair ya fara baki horo yau ko?Allah ya taimaka”cewar Ummu Zaheenat
“ kwarai kuwa Ummu sede wallahi akwai wahala gaskiya jarumai suna kokari ai riƙe takobin ma kansa akwai wahala balle yin faɗan “ dariya dukkansu suka yi mata jin maganar da ta faɗa
Yarıma Farasat ya ce “to dama waya faɗa miki sauki garesa?dan ma Ina ga takobin da ki ka yi amfani dashi bame nauyi bane “

“Ai inda me nauyi ne yanzu da tana can turakarta tana kwance tana hutawa “yarıma Haysam ya yi maganar yana dariya duk dariyar suka kuma yi.
Hararan wasa ta masa ta ce “ehh de gwara ni kai da ban taɓa jin labarin ka shiga gym room ba balle kace zaka koya faɗa”

“In ji wa ya faɗa miki?!” “Jadwa ce ta banı labari”

“Ya Allah sarauniya yaushe mu ka yi wannan maganar dake gaskiya bani bace sede ko Hamra ce ta sanar dake”kallon Jadwa da tayı maganar sukayi suna dariya.

Galadima da yake kallon su yana faman darıyar shiriritar su ne ya ce “ah ah fa kar ku ga dan Hamra bata kasar nan ku ce zakuyi mata sharri”
“Abu aleem yaran nan sun mayar da ni rago wato gulmata ma suke yi in bana nan”yarıma Haysam ya fada yana binsu da hararan wasa.

Tafa hannunsa yarıma Farasat ya yi yana kunshe dariyarsa “yanzu kai Haysam kai ne nan ka fara takalo wannan dance,kawai ka fara karbar horo kaima”
Ummu Zulaihat da tun zuwanta batayi magana ba se yanzu tace “kai.. yaran nan kun fiya shiririta”
Serving din su abinci aka yi bayan sun kammala ci ne suka sake zaman wani hiran se 11 tukuna ta shiga fada.

“Hello Hamra ykk ya school din na ji kin fara attending lectures “
“Yes Aliyah nafara shiga school jiya,gaba daya nayi kewar ku nakosa in kammala wannan masters din in dawo”
Dariya Aliyah ta fashe dashi “lallai ke da za ki yi shekara uku kafin ki gama shine za kice kin kosa lallai yarinya me ma ki ka yi “
“Mtsssw ke kinada matsala,Ina sarauniya Muzna dasu Jadwa!?”
“Sarauniya na fada,kowa na lafiya Ina yarima Ishaq fatan yana lafiya ?”cewar Aliyah.

Numfashi ta sauke cikin sanyin murya ta ce “Yarima Ishaq ba ya cikin yanayi me dadi tunda muka dawo ya sauya kamar ba shi ba,ko magana baya son yiwa mutane,shaye shayen da yake yi da neman mata duk ya dena. Wallahi yana matukar kaunar sarauniya Muzna rashinta duk ya sanya ya zama wani iri,ko da yaushe se de in gansa yana kallon hoto ko film din da tayi.”

Sosai Aliyah ta ji babu dadi jin halin da yarıma Ishaq ya faɗa a sanadiyyar soyayyar da yake yiwa sarauniya Muzna.

“Na matukar tausaya masa ubangiji ya basa juriyar rashinta. Zancen da nake miki yanzu haka saura wata guda a yi auren Sarauniya da zabin ranta Sadauki Zubair.”

Cike da tausayin dan uwan nata Hamra ta ce “ubangiji ya zaba masa mafi alkairi “
Haka suka gama wayar.
Yau ma kamar kullum a gajiye ta dawo bangarenta tana shiga suka fara taimaka mata wajen rage kayan jikinta se da ya yi saura yar karamar rigar shara shara wanda ya tsaya mata a iya guiwa ta shiga toilet ta yi wanka da warm water towel ta zara guda daya milk color ta daura tana fitowa suka ajiye mata lallausan takalmi tasaka shiryata sukayi cikin kayan bacci masu tsantsi,riƙe kanta tayi kamar wata me tunani amma a zahirin gaskiya abu ne ke mata yawo ji takeyi kamar akwai abinda take son tunawa amma ta gagara kuma se kokarin zuwa mata kwakwalwa yake.

Duk zubawa shugabar ta su ido suka yi suna mamakin menene ya sameta haka. “Shugabata shin kan ki ne ke miki ciwo !?” Marwa ta tambayeta.
Girgiza kai tayi alamar ah ah ta samu guri ta zauna bakin gado. Sosai su ka shiga damuwa domin basu taɓa ganin ta a wannan yanayin ba hakan yasa suka ji babu dadi kasantuwarta mutum me nu na damuwa da damuwar mutane.
Jikinta ne ya bata ana kallonta hakan yasa ta kalli dukkannin su lokaci guda nan taga yanda duk suka koma abin tausayi,murmushin yaƙe tayi tana me faɗin “ku kwantar da hankalin ku babu komai fa “

“Hankalin mu baze iya kwanciya ba shugaba.....ba mu taɓa ganin ki a wannan yanayin ba kin kasance me damuwa damu dole mu ji wani iri in muka gan ki a wani hali”cewar wata daga cikin su,a wannan karon murmushi ne ya subuce akan fuskarta ta ji dadin yanda suka damu da damuwar ta.

“Kar ki damu ina cikin koshin lafiya” tana gama rufe bakinta aka shigo mata da abinci kokarin fara serving dinta Marwa tayi ta dakatar da ita “bana bukatar abinci kawai ki bani hot tea “
“Angama shugaba” nan ta haɗa mata tea din ta miƙa mata. “Ku je ku samu hutu Allah ya tashe mu lafiya”

“Ki yi bacci cikin amincin ubangiji “su ka haɗa baki wajen faɗa,gyada musu kai tayi tana murmushi gaba daya suka tafi bayan sun gyara komai.
Tea din da aka bata,,bata iya sha ba sipping uku kawai tayi ta ajiye sa a gefe bata jin zata iya shansa kuma haka kawai take jin ranta babu dadi.addua ta yi kawai ta kwanta batare da ta kashe wutar dakin ta ba.bata jima da kwanciyar ba bacci me nauyi nan take ya ɗauketa.
“Muzainaaaaaaaaaaa”ta kira sunan da karfi tana miƙewa zaune cikin firgici a sakamakon mafarkin da tayi,wani zufa ne yake tsatstsafo mata a wuya da goshinta. se haɗiye yawun dake kokarin ƙamewa a bakinta take yi tsabar tsorata da tayi,a hanzarce ta kalli dakin nata,kafin can kuma ta jawo wayarta a kasar pillow ta riƙesa tana kallo,bayan hannunta tayi amfani wajen goge zufan goshinta kirjinta na dukan tara-tara.kunna wayar tayi nan take hotonsu ita da Muzaina ya bayyana akan screen din sun yi hoton ne ranar graduation din su.

A karo na biyu ta sake goge zufan a hankali ta furta “I have to call her “ can kuma se ta yi wani tunani “to in ya kasance ta yi bacci Fa?yanzu karfe sha biyu zan takura mata in na kirata warhaka”
Ajiye wayar tayi tana rike kanta da duka hannunta tana jujjuyawa ta kusan minti biyar a haka can kuma ta dago ta dauki wayar da sauri ta lalubi number wayar Muzaina din ta soma kira.five missed calls ta yi mata a jejjere amma ko daya ba a yi picking ba hakan yasa ta yanke shawarar tura mata sako kamar haka.

“Hi my Muzaina nayi matukar kewar ki sosai,ban so takura miki a wannan lokacin ba sede nayi mummunar mafarki,na ganki a wani daji me ban tsoro a bayan ki kuma akwai tafkeken rami ina kokarin riko hannun ki kika faɗa wannan ramin,hankali na ya tashi sosai da wannan mafarkin fatan kına cikin koshin lafiya?”bayan ta tura sakon ta ajiye wayar akan cinyarta jiki a sanyaye ta jingina jikinta da gadon domin bacci ya kauracewa idanunta. Shuru tayi tana tunani kamar a mafarki ta ji karar notification a wayarta alamar an turo mata sako,tana dubawa taga Muzaina replied with

“Ina nan cikin koshin lafiya my Muzna fatan kına kula min da kan ki?and kar ki bar wannan mafarkin ya yi tasiri a zuciyarki babu yanda mafarki yake zamowa gaskiya,ki kwanta kiyi bacci dare ya yi yanzu love you so much.”

Ta karanta sakon yafi sau goma ga wani murmushi da ya kara mata kyau da take sakewa adalilin jin daga Muzaina hakan yasa ta samu nutsuwa sosai a ranta,ajiyar zuciya ta sauke tana tura baki cikin shagwaba kamar Muzaina din na a gabanta ne ta soma yi mata reply.
“Uhmmm bayan ma ke bakya nema na se ni da nagaji da kewar ki na nemo ki,nayi missing wannan arrogant face din naki bari in kiraki video call.”

Emoji dariya Muzaina din ta tura mata da rubutu a kasa saying
“ ah ah kar ki kirani video call sarauniyar shagwaba,idan mukayi haka kamar mun karya doka da ka’idoji ne tunda saura mana wata biyu mu ga juna kin ga mu yi hakuri kawai zan kwanta kema ki kwanta good night.”
Taɓe fuskarta tayi kamar me shirin yin kuka domin hiran sam be isheta ba.

“Good night I love you “ itama ta mata reply sanan ta kwanta bawai dan tana jin baccin ba.

Haka rayuwa ya dinga tafiya har izuwa yanzu da aka fara shirye shiryen auren Sadauki Zubair da Sarauniya Muzna da yayi saura kwana bakwai kacal ko ina a cikin masarauta in ga duba zaka ga shirin auren kawai ake yi babu kama hannun yaro,a kwana ashirin da hudu da Sadauki Zubair ya kwashe yana bawa Sarauniya horo bakaramin kwarewa tayi ba har tanaso ta yi dede dashi a iya faɗa,sannan tunda aka fara shirye shiryen biki ta ɗauki hutun zuwa fada, sede manyan fada suje su yi abinda ya dace in lokacin tashi ya yi su tashi.tundaga wannan rana da suka fara chatting da Muzaina kullum da dare se sun yi magana yanzu sosai hankalin Muzna ya sake samun nutsuwa.

“Wai ke Haseena me ki ke nufi ?kınaso ki ce min bazaki zo bikina ba ne ?”cewar Sarauniya Muzna dake waya da Haseena tana tsaye a tsakar dakinta riƙe da kugu.

“Wayyo ni yanzu yaushe ki ka ji na faɗi haka?,duk duniya banida aminiyar da takai min ke Abba ne bashida lafiya shi sa kwana biyun nan duk bana cikin nutsuwa likitoci sun ce za a yi masa aiki a zuciyarsa.”
Cikin tausayawa ta ce “amma meyasa ba ki taɓa sanar dani ba?babu boye-boye tsakanina dake ahalinki ahalina ne kamar yanda nima ahalina naki ne”
“ ki yi hakuri banaso kına cikin Jin dadin shirin aurenki in katse miki ne that’s why “

“Hmmm wannan ba dalili bane,in sha Allah bayan bikina nida masoyi zamu zo Russia din domin gaishe da Abba da jiki “.

“Nagode best friend “ haka suka ci gaba da waya cikin kewar juna bayan sun kammala ne Sarauniya Muzna tayi wa Haseena transfer makudan kudade a cikin asusun bankinta wanda a kudin Nigeria yawan su ze kai million sha biyar. Tasan ko ya zatayi Haseena bazata taɓa ce mata tana bukatar kudi ba kuma basu da kudi shisa ko da yaushe take taimaka musu ita da iyayenta.

MASARAUTAR FALASHFUR


“A yau mu ke tsammanin wannan aikin na mu ya kammalu in har komai ya tafi yanda ake so tofa ta gama dafuwa a tukunyar tsafi”alajni gautam suwami ya faɗa yana harɗe hannunsa a kirji.

“Hhhhhhhhhhh na samu abinda nake so burina na dimbin shekaru ya cika “sarki Damurdar ya karasa maganar yana kuma fashewa da wata dariyar.

Galuuur da bece komai ba yaci gaba da sambatu irin nasu na matsafa nan take wannan tukunyar tsafin ya soma girgiza da wani karfi kamar ze faɗo ƙasa turnakakin hayaki yana fitowa me yawa a ciki,se da ya share a wa guda yana wayannan sambatu kafin tukunyar tsafin ya tsaya cak ya dena wannan girgizan kuma a wannan lokacin duk wani hayakin da yake fitowa ya dakata guri daya shi baya kasa baya sama,wutar tsafin nan shima ya mutu a yayinda iska me karfi ya tashi guguwa se tashi da ƙasusuwan yake yi. Su ukun dariya me karfi su ke yi domin aiki ya yi kyau sosai darıyar da suke ne ya sake bawa guguwar damar yin karfi sosai nan take fadar ya soma jujjuyawa. Murfin wannan tukunyar ne ya buɗe ya faɗo kasa,shuru suka yi domin ganin waye ze fito daga wannan tukunyar.

Wani baƙin hayaki ne a dunkule guri guda ya fito ya dinga shawagi a saman fadar se gilmawa yake yi duk inda hayakin nan ya yi se sun mayar da kan su gurin suna kallon kafin daga bisani hayakin ya tsaya guri daya.

Nan take ya bule fadar ya koma bakikirin basa ganin komai har na wasu dakika kafin fadar ya washe ya koma yanda yake,ɗaga kai Galuuur ya yi yana me kallon sama ya gagara janye idonsa agun. ganin inda yake kallo ne yasa suma suka ɗaga kansu suna kallon saman tozalı idon su ya yi da ita tana tsaye a saman iska hannunta a buɗe duka biyu gashin kanta da yakara tsayi se kaɗuwa yake yi a iska,jikinta na sanye da bakaken kayan fata masu nauyi irin wayanda bosawa suke sawa. dogon wando ne se riga da ya tsaya mata a iya ciki kirjinta ya fito ta saman rigar se wani doguwar jacket me tsayi har sawun kafarta rigar yana da kauri a gefen cikinta wani irin bulalar wuta ne da yake ci da wuta amma be taɓa kayan jikinta ba. a dayan gefen kuma wasu irin kaca ne masu kusa a jikinsu shima sakale a gefen kugunta saman kirjinta tattoo ne na kwarangwal din kai se kuma aka yi cross a jikin skull din,takalmin ranbut dake kafarta shima baƙi ne,taƙara farı fiyeda yanda fatar jikinta yake bakinta yasha jan janbaki radau kamar wacce tasha jini tsabar yanda ya yi jawur,ga hular sarauta da ya kasance launin baƙi da silver akanta.

Kallon ƙasa ta yi taga yanda suke tsaye sun ɗaga kai suna kallon ta ne yasa ta sheke da wani matsiyaciyar dariya

“Sabuwar rayuwa,sabuwar dama,sabuwar muradin son daukar fansa hahahahhahahhaa”
Ganin hular sarautar duk wani matsafin duniya akanta ne yasa suka fahimci shu’umin tsafi ita ya zaɓa a domin ta zama sarauniyar matsafa.nan take suka zube akan guiwarsu. A hankali take saukowa ƙasa lumshe manyan idanunta da kalar ya dan sauya kala kaɗan tayi.

Kallon su ta yi da kyau kana ta ce “ku miƙe “
Da sauri suka miƙe ganin yanda take magana tana shan kamshi ne yasa Galuur furta “gaskiya ke me saa ce shu’umin tsafi ya zabeki a matsayin sarauniyar matsafar duk duniya,tabbas aiki ya yi kyau yanzu duk duniya babu wanda yakai ki karfin iko na gwada dukkanin bajinta ta akan ki kuma daga karshe an yi nasara”

A gadarance da izza ta ce “ohhh hakane!?” Da sauri ya gyada mata kai.
Ta ce “to bari in gani “ ta yi maganar tana rufe idanunta ta buɗe bakinta ta hura iska me karfi nan take babban fadar da su ke tsaye ya sauya daga kangon dake ɗauke da kasusuwan mutane izuwa me kyau da kayatarwa kamar sabon fadar da aka gama ginawa yanzu komai na Jin dadin rayuwa akwai sa a ciki hatta kujerar saurata shima yana ciki. Murmushi gaba dayan su suka yi harda ita,nan ta ɗaga hannunta sama nan take wani sandar karfe baki me ɗauke da wani kwalba asaman sa ya bayyana a hannunta kallon sandar ta yi kafin ta sumbaci saman wajen wannan kwalba dake fitar da wuta.


“Ai ni ne nan wanda na tsafanceki ki ka samu dukkan wannan karfi da ikon,sunana Galuuur a da ni ne hatsabibin matsafin da babu kamar sa amma yanzu ke ce shugaba”
Shuru ta yi kamar ba da ita yake magana ba se ma jujjuya sandarta take yi a hannu,kallon juna Galuuur da kuma aljani Gautam Suwami suka yi ganin yanda take abu kamar bata san da ita yake magana ba.

A karo na biyu ya sake furta “wannan kuma sunan sa sarki Damurdar sarkin wannan masarautar falashfur din,ya bayar da gudunmawa dari bisa dari wajen ganin an yi wannan aikin domin yana da bukatar ki taso masa da ƴar sa sannan ya samu damar dawuwa wannan rayuwar”. Batare da ta ce komai ba ta kalli sarki Damurdar din.

Jinjina kai ta yi kafin ta nu na wani kujera da hannunta nan take yakawo kan sa gabanta ta zauna tana ɗaura kafa daya kan daya.

“Ka ce yanzu babu wanda yakaini karfin iko kuma ni ce sarauniyar duk wani matsafi?”
Ta tambayesa tana tsaresa da idanunta masu kaifi cikin tabbatarwa ya ce “Kwarai kuwa “

Murmushin mugunta ta yi tana me faɗin “To bari mu gani “tai maganar tana ɓacewa bat nan take ta bayyana a gaban Galuuur kafin ya ankara ta zurma hannunta a cikin cikinsa ta tsintsinka duk wani hanji a ciki ta zaro su waje tana kallonsu haɗe da sakin murmushi,zare ido Sarki Damurdar da aljani Gautam suka yi cikin al’ajabi domin sam basu yi tunanin zata aikata haka ba.
Cikin azaba Galuuur ya zube a ƙasa yana sakin wahalallen numfashi domin dafin dake hannunta ya gama ratsa duk wani sassan jikinsa cikin radadi ya ce “kin ci amanata a matsayina na wanda ya baki dukkan karfin iko ban cancanci haka daga gare ki ba”

“Hhhhhh Kwarai kuwa ka cancanta,ko kaɗan be kamata in barka ka ci gaba da numfashi a wannan doron duniyar ba saboda bazan lamunci ace ina ganin wanda ya bani karfin iko a kusa dani ba. duk sanda aka samu ɓacin rana zaka iya cin amanata,kuma yanzu na tabbatar da nidin babu wanda ze sha a hannuna “. Tana gama yi masa magana ta buɗe bakinta nan take wuta yadinga fesawo a ciki yana sauka a jikin Galuuur a cikin sakanni ya babbake se toka ne kawai ya yi saura.

Mayar da kallon ta kan su aljani Gautam ta yi tana watsa musu wani irin kallo me wuyar fassaruwa “ku kuma yanzu ya zan yi da ku ko kuna so in muku abinda na masa ne?au na manta kai dama matacce ne ka rigada ka mutu kai kuma aljani ne,abinda ze faru kai sarki Damurdar dole zaka koma duniyar ku ta matattu saboda wannan masarautar taka ya zama tawa,kai kuma Gautam dama kai ka nuna min hanya har izuwa yanzu to zakaci gaba da nu na min hanyar ne ka zama na hannun hagu na”

Cikin tsoron abinda ta aikata suka ce sun amince da abinda ta faɗa domin kuwa sun ga zallar rashin imanı da tausayi da rashin sabo a tattare da ita,zuciyarta ya rigada ya koma baki kırın ta zama cikakkiyar mara imani,duk wanda be yi abinda ta sanyasa ba tabbas lahira ze yi bako.

“Na amince da tura ni duniyar matattu da za ki yi se de Ina neman alfarma daya a gare ki,na rokeki da ki taso min da ƴata a wannan duniyar ni kuma ki mayar dani inda ya dace sannan ki bata matsayı a fadar ki “

“Na amince da wannan roko na ka kuma zan cika maka shi,sannan ina son in ga duk wani matsafi a gabana yanzun nan domin nasan dacewa izuwa yanzu sun san sabuwar shugaba ta karɓi mulki “

Abinda ta bukata Aljani gautam Suwami ya yi ya wura wani usur nan take matsafa maza da mata suka dinga bayyana acikin fadar sanye da

Please Login or Register in order to submit comment