Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sama har ƙasa.


Kafin cikin murya irin ta isassun yan iska ya ce " Barka dai gimbiya" yana me ɗan rangwafawa alamar girmamawa domin ya fita tsayi.


Shuru ta masa tana me kallon gefe,ganin ta ƙi kulasa ne yasa ya kuma faɗin.


" Shin da wa nake tare gimbiya Muzna ce ko kuma gimbiya Muzaina? Domin ba iya tantance ku ake yi ba ".

Ya faɗa yana sake matsowa kusa da ita.

" Yarima Ishaq kauce ka bani hanya in wuce".

" Wayyo na ji tsoro,na ji tsoro zan kauce miki" ya faɗa cike da shakiyanci yana me yarfa hannu alamar ya ji tsoron.


Ganin in ta tsaya biye masa ɓa ta mata lokaci ze yi,yasa ta bi ta gefen sa zata wuce, hannu daya yasa ya dawo da ita baya,yana me haɗe jikinta da nasa.

Kallon fadawan sa dake tsaye a bayan su yayi,ya ce

" Ku ɓace min da gani zan tattauna da yar uwata ".

Gyada kai suka yi kafin duk suka bar wajen cikin sauri dan kar ya kuma yi musu magana.


Da karfi ta turesa kafin tayi amfani da iya karfin ta ta wanke sa da kyakyawar mari a makwanci.

Hannu yasa ya shafa inda ta marensa kafin ya dawo da hannun wajen labban sa ya sumbata.

" Yanda ki ke hadaddiya haka marin ki ya kasance, gaskiya ke din ta musamman ce dan Allah dan ƙara marina mana ". Ya faɗa yana ruko hannunta da karfi, yana kokarin kai hannun kan fuskarsa ya ji an damki hannunsa ta baya juyawa yayi dan yaga waye,kafin ya fahimci komai ya ji an sharara masa mari a dayan makwancin nasa.

Da sauri Muzna ta koma gefen Muzaina dake tsaye a gaban Yarima Ishaq ta harde hannunta a kirji tana watsa masa harara.


Yana shafa dede inda ta marensa ya ce " yanzu na fahimta,kece boss din gimbiya Muzaina,yanda nake jin labarin ki ba haka nayi tsammanin ganin ki ba,se kuma naga kin ma fi gwarjini a ido,zafin ki ya burgeni,na san bakisan ni din waye ba da farko de sunana......." Katse sa ta yi ta hanyar daga masa hannu kana ta furta


" Sanin kai waye ko kuma sanin sunanka ba abu ne da ya shafe ni ba, babban abinda zan faɗa maka me amfani shine kar ka kuskura in sake ganin ka ɗaura wa'yannan kazaman hannayen naka akan Muzna ".

Ta faɗa cike da gadara da kasaita. Murmushi ya yi ya ce

" In kuma ba haka ba kuma fa ?".

Taku uku tayi ta matso kusa dashi Idonta na kallon cikin nasa kwayar idanun ta furta

" Zaka fuskanci hukunci me tsanani ".

" Muzaina ki rabu dashi mu tafi kawai " cewar Muzna dan tasan halin yar uwar'ta.

Jan hannunta tayi suka yi gaba suka bar sa tsaye kamar wanda aka dasa a gun yana bin bayansu da kallo,marukan da yasha a wajen su a maimakon yasa shi jin haushi se ma wani nishadin da ya riske sa,tafiya suke yi amma tana jin idanu a jikin ta hakan yasa ta waiga suka haɗa ido, kashe mata ido yayi sannan ya mata blowing kiss ,harara ta watsa masa tana me tunanin ya akayi Yarima Ishaq ya fito daban a cikin su yana abu se kace ba royal blood ba,haka Muzna ta dinga sa'ke-sa'ke a ranta har suka isa faɗa suka samu ana zaman makoki.su ma zama suka yi, aka ci gaba da ƙarban gaisuwa tare dasu,bayi sun shigo sun yi nasu gaisuwan, haka kowa ya dinga yin nasa gaisuwan.


Yau mako guda kenan da rasuwar sarki Taifur Rahman,an gama zaman makoki duk baƙin da suka zo kowa ya koma se kuma in za'a yi taron naɗa sabon shugaba a Bayaan. Tundaga ranar da Yarima Ishaq ya zo masarautar yasaka rayuwar Muzna a gaba muddin zasu haɗu a hanya tofa se yayi kokarin haɗa jikinta da nasa. tayi masifar hatta gaji domin ita ba mafadaciya bace. kuma babu wanda yasan da abinda yake mata,hakan yasa ta kauracewa duk wani abinda ze haɗa ta dashi kama daga hanya har inda ta san yana zama,domin ta lura Yarima Ishaq tantirin ɗan iska ne,haka kuyangu suma basu tsira ba duk wacce yaga ta masa tofa se ya kwanta da ita,kuma basu isa su yi magana ba.

A bangaren Muzaina kuwa,bayi da duk wanda yake shigowa cikin fada ya gama sanin wulakanci da rashin mutunci irin na Muzaina.domin daga zaran ka yi ba dede ba bata duba da girman mutum ko shekarar da mutum ya bata.haka zata shararawa mutum mari da mugayen kalamai,ba ma iya bayi ba hatta su Jadwa basu tsira ba,hakan yasa basa rabanta domin gudun rashin mutunci,sam bata san ƙara ba,ko kai waye baka fi karfin wulakanci a wajenta ba. Galadima Abdul Aleem Rahman al amarin ya matuƙar kulle masa kai domin ya yi tunanin kamar yanda Sheikhy ya faɗa in an nisanta su da gida komai ze gyaru amma be ga alamar haka ba, domin shi kansa se da ta kusa masa rashin kunya sarauniya Fatima ce ta tsawatar mata.

Muzna da Haseena da suka riga suka san halinta hakan be dame su ba sede abinda suka fahimta shine tunda suka dawo,jiji da kai,izza,da kaisata nata sa'ke ninkuwa yayi,. wannan dabi'ar nata yana matuƙar damun sarauniya Fatima wacce ta sha samun ta domin yi mata nasiha amma sam bata dauka.


Shiryawa ta kammala yi cikin doguwar rigar Egyptian launin ja,jikinsa ko ta ina ado ne se ɗaukan ido yake yi, batayi kwalliya a fuskarta ba, gashin kanta ta haɗe a tsakiyan ta ɗaure su sun zuba ta baya se kuma na gaban ta sauko dasu gefen hagu da dama, bakaramin kyau tayi ba,tana tsaye tana fesa turare Jadwa ta fado dakin tana faɗin


" Gimbiya Muzna shin kin kammala in rakaki ganin cikin masarautar!?".

A jiye kwalban turaren Arabian Oud da ta gama fesawa ta yi a gaban mirror ta juyo a hankali tana sakar mata murmushi ta ce

" Jadwa!.." ta kira sunan ta a hankali kafin ta kuma cewa.

" Yanzu kin ga na gama shiryawa, Haseena zan tambaya ko in zata je ".

" Ah ah ni ba zuwa zanyi ba,kawai se kun dawo ".

Haseena dake kwance ta faɗa dan yau tunda ta farka bata jin dadin jikinta.

Tunda ta ce bazata samu zuwa ba,suka fita suka barta a dakin,suna tafiya suna hira sama sama ga bayi dake take musu baya.duk inda suka wuce se bayi sun gaishe su,da murmushi a kan fuskar ta take amsa musu.

Duk wani ɓangaren da suka shiga se Jadwa ta mata bayani a kai,haka suka dinga tafiya tana nuna mata wasu gurare a masu girma da kyau a ciki.

Wani babban fili da aka ke waye da wasu sanduna Jadwa takaisu,tana faɗin

" Nan wajen kuma,an tanada sa ne domin jarumai kuma sadaukan Bayaan,wato nan shine filin dambe a nan mayakan Bayaan suke fafatawa na atisayi ". Ta faɗa tana tsayuwa haɗe da harɗe hannu a kirji ta zubawa filin damben ido tana ganin gwarazan maza guda biyu da suke ciki suna dambe. Muzna itama gyara tsayuwar ta tayi kamar yadda Jadwah tayi,ta maida hankalinta akan damben da ake yi duk da ma ita irin wannan basa burgeta daga wrestling, boxing,da sauran su duk ba burgeta suke ba,amma haka kawai ta samu kan ta da son maida hankalinta akan fafatawan da ake yi a filin dagan.


Dukkan su biyu babu riga a cikin su se wando irin na yadi me fadi fari,duk da baya suka juya amma kana iya hango karfaffan jikinsu da kuma damatsan hannun su da yake a murde,dayan ya kasance fari dayan kuma fatarsa yana da duhu wato he's chocolate in color,daga ta baya kana hango sumar kansa da yake a gyare,dambe suke yi kowa na son samun nasara akan dan uwansa, wannan chocolate color guy din ne ya samu nasarar kayar da dayan,ihu da sowa mayakan suka yi kafin wani ya daga hannunsa yana nuna sa a matsayin wanda yayi nasara.

Haka kawai ta tsinci kanta da sakin lallausan murmushi tun kafin ta kai da ganin fuskar sa ta ji ya burgeta domin jarumtar sa ya yi tasiri a zuciyarta.

Cikin salo ya juyo yana tafawa da wani dake gefen sa suna faman dariya.kafin ya miƙawa wanda ya kayar din hannu ya miƙe suka rungume juna.


" Ohh my god he is so dam handsome" ta faɗa tana lumshe Idonta, Murmushi Jadwah ta yi jin abinda ta faɗa ta ce


" Kwarai kuwa yanada kyau sosai duk da ya kasance bakin fata kuma ba dan Afrika bane baƙin balarabe ne,sunan sa Sadauki ZUBAIR, jarumi ne da Bayaan take matukar alfahari da shi, mahaifiyar sa ta kasance baiwa ce a wannan masauratar kuma shima a cikin masaurata aka haife sa,shi kaɗai ta haifa, mahaifin sa ya rasu tun yana ƙaramin yaro,duk da shi kaɗai ne wanda ya rage mata amma haka ta turasa cikin mayakan Bayaan domin samun horo shima ya zama me bawa Masarauta tsaro da kariya, kuma ga shi burinta ya cika,yana da saukin kai sosai wannan kaɗan kenan a takaitaccen tarihin sa ".


" ZUBAIR..". ta kira sunan a cikin zuciyarta,a fili kuma ta riƙe kugu haɗe da kallon Jadwah ta furta

" Kai ya Salam Jadwah!. duk wannan dogon jawabin yaushe na tambaye ki!?,dubi yanda ki ka tsaya kina min bayani dalla-dalla kamar wacce na bukata,kai gaskiya Jadwah you're too much ".

Dariyar da ke taso mata take ta son dannewa amma ta ƙasa saboda yanda taga Muzna ta hakikice tana mata masifa,bayan kuma ita ce ta bukaci hakan tunda har ta ce yana da masifar kyau.


" Shikenan!, shikenan, wallahi gimbiya kin ban dariya ke fa ki ka ce yana da kyau shin laifi ne dan na miki bayani akan sa !?".

" Ehh laifi ne babba ma kuwa,and ni bance yana da kyau kar ma ki min sharri ".

Dariya ta fashe dashi harda riƙe ciki ganin yanda ta wayance mata,ita kuwa Muzna dariyar da take yi ne ya kular da ita ta galla mata harara, tsagaitawa tayi ta ce

" Na tuba kimin afuwa gimbiya ".
Ta faɗa tana danne wani sabon dariyar dake kokarin tasowa suma bayin dake tsaye a bayan su dramar ta su ya basu dariya.amma babu wanda yayi gangancin darawa domin kuwa sun san halin Jadwah itama akwai zafin kai.


" In kin gama min renin hankalin se mu tafi ko?".
Ta faɗa tana yin gaba da sauri bayin suka take mata baya kafin Jadwah ta biyosu a baya,har sun yi nisa taji tana me son juyawa domin ganin sa,kallon filin tayi taga babu su a gun su ma sun watse,bataji dadin hakan ba domin ta so ta kuma sakasa a ido kafin ta tafi sede hakan be yu ba.


" Ya ke amintacciyar baiwa , wannan sakon ina sone ki damka sa a hannun duk wacce a ka tantance a matsayin sarauniyar masarautar Bayaan,domin yana dauke da muhimmiyar sako a ciki ". Sarauniya Fatima ta gama faɗa tana damkawa amintacciyar baiwa wani farar takarda a cikin envelope, ƙarba ta yi tana cewa

" Yake uwar gijiyata na miki alkawari in sha Allah,zan yi yanda ki ka faɗa duk wacce aka tantance a matsayin wacce zata hau karagar mulki tabbas ita zan damkawa wannan sako ".

Fuska ɗauke da yar damuwa ta zauna akan royal bed din ta,.

" Na so a ce ina da tsawon rai da zan kai lokacin da zan ga wacece a cikin ya'ya na za'a bawa sarauta da zan yi farin ciki matuƙa,se de kash hakan ba me yuwa bane,kin san shi rayuwa kana naka Allah na nasa". Ta faɗa tana jingina jikinta da gadon.

" Wannan haka yake uwar gijiyata, Allah yakara miki lafiya fara me farar aniya, Allah ya cika miki burikan ki,mace me zuciyar zinari,takawar ki lafiya uwar gijiyata baya goya marayu,duk wani me jin haushin ki sede ya mutu domin kin yi musu nisa kin musu fintinkau, kin sha gaban su,makiyan ki fadawanki,su ƙi biyayya kuma su shiga tashin hankali,.da yardar Ubangiji aljannatul Firdausi ita ce makomar ki". Wannan kirarin da amintacciyar baiwa ta yi mata ne yasa ka ta yin murmushi me sanyaya zuciya,domin a duk sanda take mata kirari har cikin bargon jikinta take jin dadin sa,hakan yasa ta mayar da ita ta hannun damar ta,ta kuma amince da ita dari bisa dari.


Suna tsaka da wannan tattaunawa wata baiwa ta tsaya daga bakin kofa tana kallon ƙasa ta soma magana

" Ina me neman afuwar katse muku tattaunawar da ku ke na tuba,nazo ne domin nemawa Ummu Zaheenat izinin karasowa ne ".


Amintacciyar baiwa ta furta " sarauniya ta yafe miki,ki mata iso an bada izni".

Shigowa Ummu Zaheenat ta yi ta zauna akan gadon tana me kallon amintacciyar baiwa alamar ta basu waje, cikin girmamawa ta sunkuyar da kai kafin ta fice.


" Amincin Allah ya tabbata a gare ki sarauniya,,na zo miki da labari me dadi ".

Gyarawa daga kishingiden da take sarauniya Fatima tayi hannun ta na riƙe da casbi,.

" Menene abinda ki ke tafe da shi Zaheenat!? ".

" Magana ce akan sadaukarwar da Sheikhy ya ce za'a yi domin kammala aikin da aka soma kuma Alhamdulillah an samu kalar dabbar da a ke nema,muna da yakinin da yardar Ubangiji in aka kammala komai ze tafi yanda ake so, za'a karya mummunar ƙaddara dake bin Muzna ko Muzaina ".

Ba se an faɗa ba fuskar ta ma kadai ya isa ya yi nuni da cewa wannan labarin ya matukar kayatar da ita, abinda suka jima suna jira ne ya lokaci yayi,domin irin dabbar da ake nema yau tsawon shekaru goma kenan ana jiran a haifesa amma aljanar dabban da zata haifi abinda suke jira din ruhinta ya yi tafiya me nisan gaske,duk yanda Sheikhy ya kware wajen aikinsa amma be iya gano inda ruhin yayi wannan doguwar tafiyar ba se yau ta haifi yar jaririyar dabbar da za'a yi sadaukarwar da shi.

Cikin nutsuwa ta riƙe hannun Ummu Zaheenat haɗe da manna mata sumba ta furta

" Kin kawo min labari mafi abin bukata a gare ni,na miki imani da Allah tunda mijina ya bar wannan doron duniyar ban kuma tsintar kaina cikin farin ciki ba irin na yau ".

Murmushi itama Ummu Zaheenat din take ,saboda wannan babban abin farin ciki ne a garesu domin muddin wannan dabbar bata haihu ba tofa ba iya wannan masarautar ba su kansu suna cikin halin ha'ula i.


" Godiya ga Ubangiji, godiya ga Ubangiji,shin ko kin san cewa nan da sati biyu masu zuwa za'a yi wannan sadaukarwar. Duk da de banida wani masaniya akan hakan amma ya Abdul Aleem shi ze zo da kan sa,duk wani al'amari ze fayyace Miki su dalla dalla". Ummu zaheenat ta faɗa tana sakin murmushi.

Haka suka ci gaba da tattaunawa.




Yanzu labari ya soma tafiya in har kun bani haɗin kai tofa zamu tafi,in kuma kuka ki bani haɗin kai se mu hakura da wannan daddadar labarin,yawan comment din ku yawan read more din ku.




Comments,like and share fisabilillahi.🥰🥰🥰🫶

https://whatsapp.com/channel/0029VaXVieoAYlUKGrPTW207








⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️




🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥




🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩





❤️🔥Page 7____8





Galadima Abdul Aleem ne haɗe da waziri Abdul Qadeer,se kuma wa'yanda suka kasance manyan fada,zaune suke a fada suna magana, Sheikh Abu Dhabi da be jima da shigowa ba ne ya yi murmushi bayan ya ji duk jawabin da galadima Abdul Aleem ya yi.


" Ya kai Abdul Aleem yau sati biyu kenan da mutuwar sarki Taifur Rahman,kuma a wannan lokacin ne ya kamata a karanta sakon da ya barwa ya'yan sa,domin mu ji menene zamuyi saboda tantance Shugabar mu a cikin su,kar ka manta kana matsayin ubane a wajen su, tsoro ko kuma fargaba, babu bukatar ya samu gurbi a cikin zuciyarka, ka sani a bari ya huce shi ke kawo rabon wani ".


Cikin sanyi jiki galadima Abdul Aleem ya zauna akan kujerar sa,yana me riƙe habarsa domin shi gani yake abubuwan da zasu biyo baya babu wanda ze kauna ci hakan.


" Babu tsoro a raina se de akwai fargaba, wallahi ɗaukan mulki a bawa mutum daya a hana daya shine babban tashin hankali da kuma barazana da zamu fuskanta . idan kuma muka bawa daya wacce ba ita bace asalin shugabar to tabbas mun siyawa kan mu masifa ne haɗe da jalala ".


" Babu wani jalala da ku ka siyawa kan ku,har se bakuyi abinda ya dace a lokacin da ya dace ba. nan ne za ku san kun tafka babban kuskure wanda, samuwar mafita ze matukar tsanani a gare mu baki ɗaya ".Muryar wannan tsoho ya dira musu a cikin dodunan kunnuwan su kamar a mafarki

Duk juyawa suka yi domin kallon ta inda maganar ya fito. a gefe da su suka hango mai girma Sheikhy yana sanye da fararen kaya har suna ɗaukan ido,komai na jikinsa fari ne kama daga sumar kansa kasumban sa,gashin ido,gashin gira da komai fari ne tas haka zalika sandar hannun sa.

Cikin girmamawa duk suka miƙe domin basu tsamci ziyartar sa a wannan rana ba,amma dake ze iya zuwa a ko wani lokaci da ko wani rana, se hakan be basu mamaki ba,domin shi me tafiya ne akan iska,se de ku gansa kawai a cikin ku.


Yana dogara sandar sa me ɗauke da wani irin abu kamar kwalba a saman sandar yana fito da wuta kaɗan-kaɗan .ya soma takowa zuwa cikin su,se da ya samu guri a kusa da kujerar da na galadima yake ya zauna yana me daga musu hannu alamar su zauna,zama duk suka yi kafin ya soma ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya.

Sheikh Abu Dhabi ne ya furta " ya shugabana ba mu yi tsammanin zaka kawo mana ziyara a wannan lokaci ba ".

Yar dariya yay kafin ya ce " bana buƙatar izini domin shigowa masarautar Bayaan,domin yau shekaru sama da dari da saba'in ban taɓa tambayar izinin ko wani mahaluki domin shigowa masarautar da ta kasance ni ne nake bata kariya ba ".


" Wannan haka yake ya kai mai girma Sheikhy,shin akwai wani haske ne da zaka ƙara mana dangane da babban al amarin da muke ciki!? ".

Waziri Abdul Qadeer ya tambaya cikin girmamawa.domin kuwa babu wanda ya isa ya yiwa mai girma Sheikhy magana cikin gadara ko kuma gatsali domin shi ba ko wani irin gama garin mutane bane ya kasance farin rauhanin aljani da ya yi sama da shekara ɗari biyu a doron duniya, sannan kuma shi ne ya kasance yana bawa masarautar Bayaan kariya,sannan shine wanda ya bada umarnin da a mayar da Muzna da Muzaina zuwa wata ƙasa daban.


" Abdul Aleem,kar ka bari abubuwan da kake mafarkin su,su yi galaba akan ka,ko Masarautar Bayaan ya samu adalin shugaba ko akasin haka to tabbas zata shiga cikin gagarumin mawuyacin halin da ko wani ɗan adam din dake cikin masarautar se ya roki mutuwa da bakinsa, hakan yana cikin ƙaddarar wannan masarauta . se de abinda nasani shine me bawa wannan masarautar kariya an haifeta kuma ta shigo duk halin gwagwarmayar da za'a shiga ita ce nan zata gyara komai zata mayar da komai iya zuwa mazaunin sa ".


" Amma in hakan be faru ba fa ya Sheikhy!?". Wani daga cikin amintaccen bafade ya yi wannan tambayar cikin tsoro.

Kallon sa Sheikhy ya yi na wasu yan lokuta kana ya ce

" Kowa ze mutu,kasar Kuwait gaba daya zata koma kamar babban filin da ba'a taɓa halittar wasu yan adam ba,zata bushe, bishiyoyi zasu bushe su sandare
,haka zalika ganyaye da ciyayi zasu bushe su dinga tsinkewa da kansu daga zaran iska ya kada domin rashin samun ruwa,a yayinda ruwan kuwa ze ƙame kamas tamkar ba'a taɓa samun ko da digar ruwa a wannan nahiyar ba,tsananin yunwa da zafin rana ne ze sa dabbobin da suka yi ragowa su dinga fadowa ƙasa a mace babu rai a jikinsu, aljanu masu ƙanana hali zasu shiga masifa, bala'i muddin hakan ya kasance,bazasu samu inda zasu kebe ko kuma yin hidimomin rayuwar su na yau da kullum ba ".

Ya gama faɗa yana bin ko wannensu da kallo, shurun da cikin fada ya ɗauka kaɗai ya isa ya fayyace Irin tsoro da firgicin da ko wannensu ya shiga.


" Uhummmmmmmmmm" galadima Abdul Aleem ya sauke wani Gwauron numfashi kafin ya ce

" Shin ta ya'ya ne za mu gane wacece asalin shugabar mu a cikin su !?".

" Ta yin gwajin tantancewa,wanda ake yi tun zamanin kaka da kakanni,sede na wannan lokaci ze fi ko wanne tsauri da zafi.domin a gabaki daya tarihin Bayaan ba'a taɓa shiga tsaka me wuya wajen tantance shugaba ba se wannan lokaci.

Aby na biyu kuma shine, yin aiki da abinda sarki Taifur Rahman ya rubuta a wasikar sa da ya bari ".

" In sha Allah,shin yaushe ne za'a yi sadaukarwar!?".
Galadima Abdul Aleem ya yi tambayar.

Sheikh Abu Dhabi ya basa amsa

" Ranar da za'a naɗa sabuwar shugaba,daren da wata ze faɗa".

Yau ma kamar yadda ta saba ta gama duk wani shirin ta cikin wandon jeans se doguwar riga da tsayin sa ya wuce guiwa yanada faɗi,gashin kanta ta mayar da shi asalin natural din sa baki ne wuluk me tsantsi da sheki, fuskar ta babu wani yalwantaccen kwalliya.kafarta na sanye da takalmi flat shoe ta yi masifar kyau,komai dinta yana da kyau kamar wacce ta zauna ta zana kanta. Murmushi take yi haɗe da sauri domin ta gama,fita ne kawai ta rage mata dan zuwa ganin sa,tsayawa tayi tana kallon kan ta a mudubi tana murmushi.

Shigowa dakin Haseena ta yi ta gama ƙarewa kawarta ta kallo, ta ga yanda take ta sakin murmushi,ita yanda ta sauya ne abin ke bata mamaki domin yawanci da rana bazaka taɓa samun Muzna ba ka gama nemanta amma ba zaka sameta ba.


" Muzna why are you acting so strange nowadays!?".

Ta cikin mudubin ta kalle ta hallau tana murmushin ta ce

" Kamar ya bangane ba,acting strange like how!?". Itama ta mayar mata da tambaya. Karasowa gabanta ta yi,ta soma binta da kallo daga ƙasa har sama kana ta harɗe hannu a kirji,ta kuma furta


" Ehh mana gaba daya kin sauya,bana taɓa samun ki se dare lokacin kuma kinyi bacci,ina ki ke zuwa ne!?, yanzu haka na haɗu da Muzaina a falo tana neman ki".

Duk maganar da Haseena take mata ita de murmushi kawai take yi tana me ɗaukan turare tana fesawa jikinta, batare da ta kula ta ba.

Da mamaki Haseena take kallon Muzna ganin a maimakon ta bata amsa amma ta tsaya batacewa komai se murmushin da take sakar mata.

Cikin dogon nazari da kuma son gaskata abinda zuciyarta ke ayyana mata,da matuƙar al'ajabi ta ce

" Wait!,wait!, dakata, Muzna shin kin faɗa soyayya ne!?".

Dakatawa da fesa turaren da take yi ta yi,batare da ta kalleta ba ya ce

" Meyasa ki ka faɗi haka Haseena".

" Saboda wannan sauyawar ta ki yafi kama da wanda ya faɗa soyayya sabon shiga,ki duba yanda ki kayi light make up mara hayaniya ga kuma yanda ki ka yi dressing and abu mafi la'akari shine yanda ki ke ta wani sakin murmushi ba kaukautawa".


" Hhhhhhhhhh lallai Haseena,to ni babu wani soyayya da na faɗa kwantar da hankali".
Ta gama magana tana fesa mata turare.sannan ta damƙa mata kwalban ta nufi hanyar barin dakin tana ce mata

" Bari in dan zaga in dawo ".

Ko da Muzna ta fice a dakin murmushi itama Haseena ta yi a zuciyarta tace

" Tabbas kin faɗa soyayya ƙawata,ina fatan za ki samu farin ciki a rayuwar ki ".



Tsaye take a jikin bishiyar darbebejiya me girma,wanda ke kusa da filin daga,ta labe a bayan bishiyar tana leken yanda suke gabatar da motsa jiki. Yanda yake gabatar da komai cikin nutsuwa da jarumta hakan na matukar burgeta a yayinda take jin son sa na sake dankaruwa a birnin zuciyarta.

A karo na sau babu a dadi ta kuma leƙo kanta domin ta gansa,yana tsaye yana daga wani nannauyan karfe,juyowa yayi ta bangaren da take dasauri ta boye a jikin bishiyar tana sauke numfashi tare da godewa Allah da yasa be ganta ba,se da ta nutsu sosai wanda a ƙalla ta kai kusan minti biyar kafin a hankali ta kuma lekawa sede cikin rashin sa'a bata ganshi a filin dagan ba. iya wa'yanda suke tare ne

Please Login or Register in order to submit comment