Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani kofi irin na da ya zuba ganyen a ciki ya sa ruwa,inda ya barta ya je ya ɗagota ya buɗe bakinta ya tsiyaya mata ruwan maganin duk da tana a sume bata hayyacinta seda yasan hanyar da ya bi dan ganin ta haɗiye maganin,sannan sauran da ya yi saura ya shafa mata a jiki.
Kayan jikinta da yaci datti yake son sauya mata amma yana tunanin ta yanda ze aikata haka tunda shi ba muharraminta bane hakan yasa ya hakura ya rufe mata jiki da wani kyalle,kafafunta da suke da rauni sun kumbura , ya zauna ya ɗaura hannunsa akai yayi addua nan kafafunta suka koma yanda suke da,tamkar babu wani abinda ya taɓa samun su a baya haka ya bi duk wani raunj yana yi masa addua nan take raunukan suka ɓace a jikinta se de zafin jikin ya na nan.

Bayan rana ya faɗi ne yana wajen bukkan yana alwala ya ji kamar ana motsi hakan yasa ya shiga bukkan nan ya iske ta kwance yanda yabaro ta, se sambatun da take yi ga jikinta ya haɗa zufa kamar wacce aka watsawa ruwa sannan kalma daya a cikin abubuwan da take faɗa ba abinda ya fahimta.
Cikin nutsuwa irin nashi da Kamala ya ce “ya ke baiwar Allah menene sunan ki,kuma daga ina ki ke ?”

“Bansanı ba,ban san komai akaina ba,bansan wacece ni ba,ban san daga ina nake ba” ta faɗa cikin sambatu
Ganin idonta a rufe yasa ya fahimci har yanzu bata dawo hayyacinta ba kawai zafin ciwo ne ke damunta hakan yasa ya ɗaura hannunsa akan goshin ta tun daga nan bata sake cewa komai ba ta ci gaba da dogon baccin da take.
Haka wannan bawan Allah ya ci gaba da jinyarta har tsawon kwanaki ashirin da daya kuma har yanzu ba ta farfado ba har kawo yanzu.
Yau ma kamar kullum bayan ya gama shafa mata ruwan rubutu a goshinta ne ya tashi ya fice a bukkan ya tafi saman dutse domin yin sallah.

A hankali ta soma buɗe gajiyayyun idanunta da suka mata nauyi tana jin su tamkar ba na ta ba,hasken da ya ziyarci idon ne yasa ta yi saurin maidasu ta rufe tana “asshhhhh” saboda zugi da ta ji tamkar an watsa mata barkono,se da ta dau wasu lokuta kafin ta sake yunkurin buɗewa a wannan karon ta yi nasarar buɗesu se de ba gaba daya ba dishi-dishi kawai take gani bata kallon komai yanda ya dace.miƙewa zaune ta yi tana sa hannu ta mirza idanun nata,kamar wacce ta yi aiki haka take Jin ta a gajiye likis ga jiri jiri da take ji duk da tana daga zaune. se da taji ta soma dawuwa dede tukuna ta ɗaga kanta tana ƙarewa cikin bukkan kallo tana mamakin ya akayi ta tsinci kan ta anan da sauri ta miƙe tsaye tana kallon yamma da kudu na bukkan babu wasu abubuwa a ciki sosai wani karamin tebur din katako ne ɗauke da Qur’ani se littatafan addini a gefe,a daya bangaren kuma dutsen da yake amfani dashi gurin yi mata magani ne ta gani se sauran ganye da kofi shi kenan iya abinda ke cikin wannan bukkar kenan se taburmar da ta tashi akai.

“Ta ya aka yi na tsinci kaina anan”tambayar da ta yiwa kan ta kenan matsawa ta yi gaba ta sunkuya ta ɗauki falle daya na ganyen tana gani bata fahimci komai akan ganyen ba hakan yasa ta sunkuya ta ajiye sa a inda ta ɗauka,tana kokarin miƙewa kawai ta kalli kafafunta,da wani speed ta miƙe tsaye tana kuma kallon su kamar ba nata ba tana mamakin ya a kayi babu ciwo a jikinta,tunani da tambayoyi ne masu yawa aranta amma babu me ba ta amsa hakan yasa tasa kafa tafito waje ko zata samu me amsa mata wayannan tambayoyi na ta. Da jin da ta ci karo dashi a gabanta ne yasa ta ja baya tana komawa cikin bukkan. “Shin meye yake faruwa ne me nazo yi cikin wannan ƙasurgumin dajin?”ta yi maganar a zuciyarta tana sake leko kanta waje sadakarwa kawai ta yi ta fito tana karewa dajin gabanta kallo,cikin sanɗa-sanɗa take tafiya kamar akwai abinda take tsoron kar ya ji sautin tafiyar ta,ci gaba da tafiya a ƙatuwar dajin ta yi tana yi tana waiwayon baya,motsi ta ji kamar ana tsaye a bayanta hakan yasa cikin sauri ta juya ko da ta gansa baya dashi ta ja tana bin sa da kallon tuhuma

Hannu ya ɗaga sama yana “Alhamdulillah Allah abin godiya,Allah na gode maka da ka tada kafadar wannan baiwa ta ka”ya faɗa yana sauke hannun sa sannan ya kuma faɗin

“Yanzu kam kin dawo hayyacin ki Masha Allah “
Tana binsa da kallon tuhuma da kuma dan fargaba saboda yanda idanunsa suke kamar na kuliya daya idon blue ne me haske se kuma dayar na gefen dama green me haske.

“Wanene kai malam”ta faɗa tana danne tsoronta,murmushi ya yi ya ce” kar ki ji tsoro na,ni din ba me cutarwa bane. Sunana ALma'amoun,ni ne wanda ya tsinceki a dajin nan kuma na yi miki magani a cikin wancan karamar bukkar tawa,na miki imani da Allah ni ba me cutarwa bane”
Se yanzu ta ji relief jin shi ne ya mata magani kuma musulmi ne yasa ta ji dama-dama amma idanunsa ne suke ba ta tsoro.
Cikin sanyin murya ta ce “Allah ya biyaka da mafificin alkairi “

“Ameen….bismilah”ya matsa mata a hanya ya yi gaba ita kuma ta bi bayansa,ko da suka isa ta tsaya a wajen bukkan shi kuma ya shiga ciki,can ya fito hannun sa riƙe da ninkakkun kaya launin fari da peach color se kuma sabulu ya miƙa mata da mamaki take kallonsa take kuma kallon kayan da ya miƙo mata din ganin yana mata murmushi ne yasa ta sa hannu ta karɓa tana tunanin to aina ya samo wayannan kayan bayan kuma cikin bukkar babu su taya aka yi ya samesu nan take ta dasa ayar tambaya akan sa,tana wannan tunanin ne ta jiyo muryarsa yana cewa....

“Bayan wannan bukka akwai ruwan dutse me wucewa zaki iya yin wanka a gurin”
Kai ta gyada masa ta soma tafiya har ta kusa isa bayan bukkar jikinta yabata ana kallon ta hakan yasa ta juya ganin sa ta yi ya tsareta da wayannan idanun nasa masu tsoratarwa yana kallon ta. kirjinta ne ta ji ya buga da sauri ta sha kwana tana rokon Allah da ya kare ta.
Sosai ta wanke jikinta musamman gashinta da ya yi dukun-dukun se da ta dirje jikinta kal ta tabbatar da ta fita sannan ta ɗauki kayan ta warware nan taga katoton wando ne me faɗi sosai se riga da ya tsaya mata a cinya kayan suna da laushi sakawa ta yi se karamin mayafin da ta gani a saman kayan shi kuma ta naɗe gashinta a ciki lokaci daya ta koma yanda take tafita daga dattin da take ciki.
Barın gurin tai ta koma bukkar,ja ta yi ta tsaya turus ganin taburman da ta bari a cikin bukkar an fito dashi bakin bukkar ga abinci a cikin kwanuka jere ga ruwa a gefe shi kuma Al’maamoun yana zaune akan wani dutse gefe da taburman ganin yanda ta ja ta tsaya ne yasa ya ce

“Bismillah zauna ki ci abinci “cikin shakku ta zauna akan taburman ta zuba wa abincin ido amma ta gagara fara ci.

Ɗago kai ta yi ta kalle sa nan ta iske shima ita din yake kallo,tsarguwa ta yi ta rasa wannan kallon da yake bin ta dashi na menene da ko da yaushe se ta kamashi yana kallon ta kuma ba ya janye idon sa,ga shi ita tsoron wannan idanun na sa take

“Alma’amoun a lokacin da na farka a cikin wannan bukkar ban ga komai a ciki ba daya wuce al Qur’ani se kuma littatafai da ganye baya ga haka banga kayan girki ko kuma kayan abinci balle kuma kayan sawa a ciki ba,dan Allah ka sanar min su ku ma daga ina su ka fito ko kana da wani bukkar ne bayan wannan ?”

“Tabbas na san abinda ki ke tunani amma ki kasance me kyakyawar yakini a ko da yaushe,kar ki bari zuciyar ki ya dinga saki cikin wasi-wasi,ki nemi kariyar ubangiji a duk inda za ki taka kafarki,kamar yanda na faɗa miki ni ba me cutarwa bane. Ki ci abinci sannan ki bani takaitaccen tarihin ki”

Bata sake masa magana ba se gyada kai da ta yi sannan ta ci abincin kaɗan ta wanke hannunta tasha ruwa,gyara zamanta ta yi,kamar yanda ya bukata nan ta soma ba sa tarihinta.

Gwauron numfashi ya sauke bayan ta gama faɗa masa komai akanta ya jinjina kai “Kenan ke Sarauniya ce a ƙasar ku?in de wannan tarihin da ki ka ban gaskiya ne to tabbas kasarki da duk makobtar ƙasarki suna cikin hatsari,yar uwarki yanzu ta rigada ta rikiɗe izuwa shedaniya me hatsarin gaske,amma kar ki damu duk karfin da take dashi Allah ya fita. Da iznin ubangiji zan taimaka miki da iya karfina dole se an nemo hanyar da za a karya wannan shu’umin karfin iko da take dashi,done a dakatar da ita..zan yi magana da kakana na biyar mu ji ko akwai wani taimako da ze iya yi mana”

“Kakan ka na biyar fa kace?”ta faɗa da zallar mamaki,kai ya gyada mata yana murmushi ganin yanda ta tsorata

“Sarauniya Muzna kamar yanda na sanar dake a farko sunana Alma’amoun,sannan ni ba mutum ne kamar ke ba ni bana cikin jinsin bil adama amma kar ki tsorata da jin haka yanda ki ke musulma kuma ki ke bautawa ubangijinki haka nima. Ina ziyartar ko wani daji dake wannan duniyar ina gabatar da ibaduna da neman tuban ubangijina,kuma duk dajin da naje kwana biyar nake yi ina gabatar da ibadu,amma wannan karon se da na yi kwanaki bakwai na rasa dalilin da yasa na gagara tafiya ashe Allah ne yake son haɗamu,cikin ikon sa na gan ki kuma na taimaka miki,kuma zan ci gaba da taimaka miki”

“Har karshen rayuwata zan ci gaba da tuna allairinka a gareni,shin wannan dajin ina ne?”

Dariya ya yi me sauti wanda se da fararen hakoransa suka bayyana a hankali ya furta “dajin ina ne? Wannan ba daji bane…..ba dajin duniyar bil adama ba wannan duniyar Aljanu ne da mugayen halittu zalla”

Zare ido waje ta yi ta ce “duniyar aljanu?”


Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah.


Anan na kawo karshen book one,
Book two din na kuɗi ne ga duk me bukata ya min magana ta whatsspp number ta 08166018849 or 09024503194 mrs isham.

Don’t forget to comment,like and share much love Habibties🥹❤️🌹

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment